Reading TABARMAR KASHI 1&2 complete by SAFIYYA HUGUMA Chapter 61 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

inda yake kalla.

"HUGUMA*

_TABARMAR KASHI*

Book 02 Page 52

Fadeela ce ke motsawa tana bude
idanunta, likitocin da basa rabo da gurin suka isa gareta,sai dukka hankalinsu shi da ita ya koma kai. Suna ganin sanda suka yi wasu dube dube jikin na'urorin dake tare da ita,suka zare mata na'urar ventilator din dake tare da ita,sannan suka kamata suka zaunar da ita sosai suna jinginata da pillow, daya daga cikinsu yana magana da ita tare da yi mata tambayoyi. Batasan ta rungumeshi ba sai data ji yana goge mata hawaye, abinda bata taba yi ba ta rigeshi cikin jikinta tsam tana hawaye,cikin haka aka buda gofar aka fito.

Likitanne, sai hankalinsu ya tattara a kansa

"Ta farfado, kuma muna saka ran lafiya lau take, amma yanzun zamuyi mata gwaji don tabbatar da dawowar memory dinta da kuma bangaren dake da alhakin magana na brain dinta vana nan lafiva nan da awa uku kacal zamu fiddota daga nan icu zuwa ward na gaba (inda zaku iya ci gaba da ganinta" sake rugungume toufeeq din tayi da kyau tana rasa inda zata ajjiye kayan farincikin da takeji,har cikin qashinsa yakejin rungumar tata,ya maida kansa ga likitan

"Mun gode likita,muna fata jin labari me dadi game da hakan" yayi maganar yana miga masa hannu

"'Da yardar ubangiji" shima ya maida masa cikin murmushi, soyayyar da yake hanga a idanunsu su biyun kullum ya kallesu burgeshi sukeyi, baiyi zaton samun irin wannan soyayyar daga gurin baqar fata ba.

"A cikani don Allah na samu damar zuwa na shaidawa su maji" da hanzari taja da baya tana sakinsa a kunyace tare dauke kanta gefe guda kamar ba it bace yanzu tabar iikinsa ba,dariya ta kubce masa,sai ya girgiza kai kawai yana soma yin gaba,yanzun ya fara dawowa hayyacinsa,zai dora daga inda ya tsaya,saboda har yanzu baiji kalmar i love you daga bakinta ba.

Tunda suka tsaye a gurin sun magana hankalinsa yake kanta,kamar yadda hankalin hajiya qarama yake kansu su dukka.

Ta fahimci bayan wucewar kowanne second hamsin zuwa sittin sai yayan nata ya waiwaya ya kalleta, saidai ko sau daya ita maji din bataga ta juya ta dubeshi ba,tamkar ma basarwa takeyi batasan da zamansa ba.

Isowarsu ya sanya maji migewa kunnuwanta suna sauraren albishir din da yake tafe dashi. Gaba daya kowa dake gurin rudewa yayi, yana sake kiran sunan Allah tare da qara tsarkake girma da buwayarsa. A hankali ta zame ta koma da baya ta zauna bugun zuciyarta na bugawa da matsanancin garfi,can gasan ranta taji tana fata da addu'ar samuwar tabuwar memory din yarinyar ko kuma sashen maganar na qwaqwalwarta ya tabu,roqo me tsanani cikin ranta, saboda ita daya ce hanya qwal dsya tilo mafi saugi da zata zare sãahar daga rayuwar kowannensu cikin ruwan sanyi, ta kuma maye gurbinta da haseenarta.

Kowanne mode na hajiyan da ya sauya yana bibive dashi yana kuma karance da ita,ba kuma wai shi daya ba,daga maji har sãahar suna ankare da hakan, gefe daya afifa itama tana monitoring komai, tana sake samun limani da yaginin matar da gaske akwai wata guba a tattare da ita,walwalarta ta banbanta da walwalar duk mutumin dake gurin.

Cikin gasa da awannin da suka fadi komai ya
kammala, suka samu tabbacin komai nata ya davo
normal, abinda ya rage mata kawai shine kwana bakwai
da zatavi a asibitin ana sake kula da ita. Cikin mintuna
galilan suka dawo da ita general ward dake qarqashin
neurology department.

Sãahar ce mutum ta farko da fadeelan ta fara
runguma sannan abby dinta. Maji taja da baya tana dan harararta

"Au, haka zamuyi dake? lallai sai kin nuna kishina kikeyi ko?" Ta furta cikin wasa,wasan da yasa fadeelan dariya

""Sorry grandma,dukka nayi kewarku fa, kwana na nawa ban ganku ba?" Ta furta tana son lissafa kwanakin, to amma ita Ranta batasan kwana nawa bane. Duka kowa sai data ambaci sunansa, fuskarta cikin murmushi don ita din tun asali nadeeya tayo wajen fara'a ba oga toufeeq ba Duk wani kai kawo säahar ita ta dinga yi,wajen bawa fadeelan abinci da sauransu. Tsakanin toufeeq dr mahmud da maji bansan waye yafi yabawa tare da jin qaunar säahar din cikin ransa ba, taqi yarda kowa ya karba hidimar fadeelan.

Tana tsaka da bata abinci kadan kadan tace

"Ina mommy garama?" Tambayar da aka rasa me amsa mata tsakanin toufeeq da ita sahar da aka yiwa tambayar. Idanu sãahar ta maida kan toufeeg,don shi yafi cancanta ya amsa tambayar, ita kadai taga lokacin da yake magana da security kan kada su bari ta shigo dakin. Ido daya ya kashe mata tare da vi mata nuni da taci gaba da aikinta,saita maida kanta ga fadeelan dai dai lokacin da yace

"Zaki ganta angel, bata kusa" daga haka bata sake tambayar ba.

**Rubuce rubuce likitan ya sakeyi gefe daya yana sake musu bayani tare da tabbatar musu da komai lafiya yake

"Kuna iya tafiya gida, likitocinmu zasuci gaba da lura da ita har wayewar gari kamar yadda aka saba" ya fada yana ajjiye musu file din sannan ya fice.

Sassanyan boyayyar ajiyar zuciya toufeed ya saki, dama yana da buqatar hakan,a kwanakin gaba daya ta hautsine ta hautsinashi,ko dumin jikinta bata bari yaji.

Kai tsave kawai sai va ciro wayarsa ya fara yi musu booking daki na hotel, don yanaji a jikinsa hotel din da yake ciki vanzunma yayi masa kadan.

Daki daya tal ya kama musu me hade da komai
da komai,sai kuma ya sake laluba wani hotel din ya sake kama dakuna uku. Daya na Dr jarma,daya na maji dasu nadeeya,daya kuma na sajjad. Kadaici yake buqata, bayason su hada hotel da kowa nasu,shi yasa yayi hakan. Sai daya kammala komai sannan hankalinsa ya kwanta dai dai da isowar taxi guda uku. Da daya da daya suka yiwa fadeela sallama suka fice, saura shi da sãahar din suka rage. Maimakon yaga tayi hanyar waje kamar kowa,sai yaga ta samu gu ta zauna

"'Let's go" ya fada idanunsa a narke a kanta, dan daga kai tayi ta dubeshi

"Ni ba zasu hanani kwana ba,nayi magana da wata nurse" idonsa ya dauke daga kanta,ba tare da yace mata komai ba ya isa gabanta, yasa hannu ya zare wayar dake hannunta ya jawo jakarta ya jefa a ciki qasa qasa yana cewa

"Na fuskanci har yanzu yarinyar nan baki da wayo, sai na fara miki magana da manyan baqi a gaban kowa" baice da ita komai ba ya qarasa yayi kissing hannun fadeela yayi ficewarsa.

Komai nata yana cikin jakar, kuma ya hada ya fice dashi, babu yadda ta iya dole ta matsa gaban fadeelan tayl sallama da ita,tare da yi mata alqawarin dawowa gobe da wuri.

Dukka taxi's din su maji sun bar gurin da alama sun tafi, saishi ta samu a tsaye yana danna waya rige da jakarta yana jiran isowarta. Qofar yabar mata a bude ya zagaya daya sashen ya shiga. A nutse ta shiga itama ta rufe, driver din taxi din ya tayar da motar suma suka fice daga asibitin a hankali.

Tun basuyi nisa ba lalubi hannunta ya matse cikin nasa ta daga idonta a hankali ta zube cikin nasa. Kafeta yayi da kakkaifan kallonsa har ta kasa janye nata idanun, cikin taushi da laushin murya yace

"'Baki ganewa a duk sanda mijinki yayi missing dinki ne? duka kin hautsina ni kamar ance fadeela zata wuce ta barki?, finally fadeela ta warke ina bugatan kulawarki" ya fadi da idanunsa da suka rusuna kamar wanda yakejin bacci

"Please please, ko kwatan kulawan da fadeela ta samu nima adan sanmin" da car ta zare idonta daga cikin nasa tana jin bugun zuciyarta na qaruwa, kamar wanda va zubawa sassan jikinta wani guba ko dafi da suka kassara gabobinta. Tana jin wani yanayi sosai a likinta matuga da gaske, irin vanavin da bata taba in kamarsa ba, amma cike take da tsoro da kuma firgicin sake afkawarta wani rami, kada sai ta saki zuciyarta tayi nisan kiwo kuma ya zamana ta barota a inda daukota zaivi mata mugun wahala.

Daga shi har ita ba wanda va sake cewa wani abu, har zuwa sanda suka isa hotel din.

Shine va bude dakin sannan va matsa vana bata hanyar shigowa. A nutse take kallon dakin,wani irin daki dake da wani tsari me kyau burgewa da kuma sanyaya zukata. A nutse ya maida gofar ya rufe yana takowa tsakiyar dakin idanunsa har vanzu vana kanta, sai kuma ya kauda kai vana wucewa gaban wardrobe na dakin ya bude ya zube kayansu a ciki.

Kayan jikinsa ya fara zarewa saboda wanka da yake bugatar yayi,ya gaji sosai kuma dare na sakeyi yanaso yayi bacci yadda ya kamata saboda gajiyar da ya dibawa jikinsa ta kwana da kwanaki..

Idanunta ta kawar gefe, don ba kadan ba qirar jikinsa take mata kwariini. Qaramin murmushi ya saki yana karantarta,har yau bata taba tsaida idanunta a jikinsa ta gare masa kallo ba,yana lura da duk wani motsinta tun ba yau ba. Ya gama fidda kayan daga shi sai pant,ya fara takowa a hankali,bai tsaya ba har ya cimmata, ya tsaya dab da ita yana dan taka yatsunta da nasa yatsar ta vadda zatasan da isowarsa. Sarai ta jishi, amma bugawar
da zuciyarta keyi ya hanata motsawa
"A bani towel" va furta vana kallonta. Cikin rawar jiki ta
waiwaya tana duban gefanta ko zataga towel din, suna
ninke a kusa da ita,hannu ta miga ta dauko ta miga masa ta baya ba tare data waiwayo ba. Hannunsa ya miga ya riqe towel din hadi da jawota gaba daya sai gata a tsaye a gabansa,dukka qugunta ya kama ya rigeta tsam yana matsowa da ita jikinsa ya mannata da qugunsa. Wani irin shock mai qarfi ya fusgeta ya kuma ratsa kowanne sashe na jikinta ya tayar mata da tsigar jiki, dumin fatarsa yana ratsata qwarai

"'Look into my eyes" yafadi qasa qasa shima yana jin
wani yanayi na sauka a nasa jikin sanadiyyar haduwar
jikkunansu guri guda. Na second daya tak ta iya daga kai ta kalleshi sai taji ba zata iya jurewa ba. Ya sani dama saboda abinda ya sakar mata ta cikin idon zaiyi wahala ta iya jura,sai ya saki qaramin murmushi na gefan baki yana kallon lips dinta. A duniya labbanta na daya daga cikin abinda ke tafiya da tunaninsa yake kuma jin marmari, iya kallonsu kadai suna haifar masa da tarin bugatuwa zuwa gareta

"You are one person with the power to give me a
thousand feelings...can i order a large tight hug until I
feel okay please?" Ya fadi yanason kallon tsakiyar
qwayar idanunta da har yanxu taqi yarda ta kalleshi dasu, saboda wani irin feeling da yake saukar mata

"Please" ya fada a narke, nan ma bata amsa ba,kasa jurewa tayl a karo na biyu,yanzun kuma taji duk duniya idanun nasa takeson kallo,tanason ta tabbatar da salon muryar da kuma wannan shagwabewar ita MT JARMA yake yiwa.

Sosai vaja numfashi sanda idanunta suka shiga nasa,ya kama kanta da hannunsa dukka biyun ya riqe, numfashinsa na kai kawo da sauri cikin zafin nama ya matso da fuskarta dai dai tasa

"You just stole my words" ya garashe fada yana hade bakinsu guri guda.

Wani irin kiss me zafi yake sauke mata ko ta ina, tuni ya sanya jikinta itama ya dauki rawa, lokaci kadan ya fara juye mata tsantsar kewarta da yayi da kuma yadda zuciyarsa ta azabtu da soyayyarta, tun tana iya dauka har ta fahimci abun nasa nisa yakeyi, kamar yana shirin ficewa daga hayyacinsa. Kasa tsaiwa sukayi dukkansu suka zube saman lallausan carfet din dake iya area din da suke a tsaye. Sai tayi qarfin halin tureshi, muryarta na fita da qyar saboda gudun da zuciyarta keyi

“Am in...am in.... miscarriage bi.." Bai bari ta garasa ba
ya zame jikinsa va tsani ya tuna wai tayi
miscarriage, shikenan ya rasa babynsa? bai kuma san ranar maida wani ba, sai kawai ya zura jallabiyyar daya fidda ya nufi gofar fita zuwa parlor yana hada hanya. Ta jima zaune a gurin tana maida numfashi kafin ta iya migewa ta shige toilet don cire pad din jikinta ta sauya wata.

Cikin mamaki take sake kallon pad din, tayi tsammanin zata sameta da jini a jiki, tun ranar da akace tayi miscarriage din bata sake ganin jini ba,sai dan sports data gani zuwa jiya,yau kam babu komai ma a jiki, yau kwanaki hudun yadda ta saka pad din haka take cireta,sai ta jefata dustbin tayi tsarki ta kuma daura alwala tana yankema ranta zuwa asubahin yau idan bataga komai ba zatayi wanka taci gaba da ibadarta.

Saman sofa din dake dakin ta koma ta cure guri daya, tana jin mararta na daurewa sosai, idanunta a lumshe har zuwa sanda ya sake turo gofar ya shigo. Ta lumsassun idanunta take satar kallonsa har ya wuce bandakin, sai daya rufe qofar sannan ta sake maida idanun nata. Zurfi qwarai zuciyarta tayi akan nazarinsa da nazarin halaye da dabi'unsa, bata tana tsammanin samunsa da wannan fuskar ba, MT JARMA, mutum mara uzuri mara dagin gafa, mutum me tsananin zafi,wanda bai maida korar ma'aikata a bakin komai ba, bata taba zaton samun wanna side din daga gareshi ba.

Duk wasu qarin dabi' u da take tsammanin samu daga gareshi sai taga akasin hakan. Zafin kai izza tagama da kuma tarin qasaitarsa takan rasa ina sukayi a duk sanda suke kebe,wani mutum daban take gani a mafi yawancin lokuta,bawai MUHAMMAD TAUFEEQ JARMA ba.


Zafafabiyar
"HUGUMA*

_TABARMAR KASHI-

Book 02 Page 53


Mintuna kusan talatin ya sake fitowa,saita sake bude idonta kadan tana ci gaba da satar kallonsa. Daure yake da towel yanzun a qugunsa, duk wata siffa da gira da Allah yayi masa ta bayyana,idan tace tsahon rayuwarta bata taba ganin namiji me qira koda kusan tasa ba batayi garya ba,inda za'a dauko adam a tsayar dashi a gabansa,tabbas zai tashi kamar siffar jikin mace ne da kuma wani ingarman namijin.

Zame towel din da yayi ya sanyata maida idanunta ta kulle da garfi harda juya kanta wani sashen. Murmushi me sauti ya saki yana sane yayi hakan, tun daga shigowarsa har yanzun da ya fito daga wankan ya fahimci tana satar kallonsa

"Idan kin gama qaremin kallon ki tashi kiyi wanka,ki fidda wadan nan kayan ko zakiji dadin bacci" ya fadi yana sanya short necker sannan ya fara feshe jikinsa da tattausan turarensa mai kwantar da zuciya. Har ya gama bata motsa ba. Bai sake ce mata komai ba,sai ya taka cikin kamewarsa ya isa gareta sai kawai ji tayi an dagata cak

"Na daina magana biyu daga yau, komai zan vishi ne a aikace". Bai saurari magiyarta kan ya sauketa ba

"It's too late" yace da ita yana isa toilet din, sai kawai ya tsumbulata gaba daya cikin bathtub. Qanqame jikinta tayi guri daya

"Pleaaaaaaaassssseee" ta fada murvarta na rawa.
Murmushi ya saka yana fasa shiga cikin kwamin kwankan da yayi niyya,yaja da baya yana nufar qofa sai-kuma ya tsaya cak yana kallon dustbin din data jefa pad, har zaice wani abu sai kuma ya fasa ya sanya kai ya fita.

A reception na hotel din sajjad ya karba musu keys na dakunan sannan suka haura zuwa floor na biyu.

Migawa Dr jarma key din nasa dakin yayi cikin girmamawa sannan yayi gaba yana cewa nadeeya

"'Muje ga naki key din" afifa da nadeeya suka bi bayansa.

"Shifa" Dr jarma ya kira maji wadda sai yanzu ta iskesu ganin tana marawa su sajjad baya. Tsaiwa tayi cak sannan ta waiwayo tana duban idanunsa. Nauyinta kadan ya kama Dr jarma

"Ga namu dakin, naga kina shirin bin yara"

"Eh tare dasu zan kwana" ta amsa masa kai tsaye. Kai ya girgiza

"Kada kiyi haka don Allah shifa,tsahon shekaru talatin ba wani abu,yau dai ki yarda mu hada makwanci, koda kwanan zaune zamuyi ni dake,aqalla ko hira mayi,ko bitar bayan rabuwa mayi"

"Dakai da wa?"

"Da shifa dina" ya amsa mata kai tsaye yana kallonta. Ta fuskanci lagonta yakeson karyawa,sai kawai ta dauke kai tayi gaba ba tare da tace masa komai ba.

Caraf ya kama luggage dinta ya riqe,nan ma bata ce mas komai ba ta sakar masa tayi gaba abinta
Zare ido nadeeya ta hauyi da gain maji ta shigo dakinta,daga ita sai afifa ne kadai sukasan yanzun maji tana amsa sunan matar Dr mahmud jarma a karo na biyu

"Maji ai munyi sallama ko?" Harara ta watsa mata, dole ta tsuke bakinta ta bata qofa ta shigo. Tana kintsa dakin tana satar kallon majin, amma bata da bakin magana dole ta qunshe abinta a ciki, saidai gasan ranta tausavin abban nata sai ya kamata.

Kusan minti biyar yayi a tsaye a gurin rige da luggage din shifa data bar masa,jiki a matuqar sanyaye yaja luggage din ya bude dakinsa ya shige da ita. Yana shirin zama kira ya shigo wayarsa,koda ya duba sai yaga fauziyya ce,ya daga kiran yana zama saman stool

"Fauziyya ya akayi?"

"Wai yaaya ina kuka shiga?"

"'Meye ya faru?" Wani abu me daci ta hadiye

"Yaaya,wanne irin mutane ne marasa mutunci cikin asibitin da fadeela ke jinya? kodai yarinyar ta shirya wulagantani ne kawai?"

"Wai meye fauziyya ya faru?" Ya fada cikin qagauta da jin gorafinta.

"Yanzu yaaya kamar ni?..…... ni fauziyya za'a hana shiga ganin fadeela? bayan na gaya musu matsayina a gurinsu? wai ba'a basu izini ba? wallahi yaya muddin kana sona kana kuma gaunata saika binciko wanda yasa a hanani shiga ganin jikata" ta fada da murya mai rawa dake nuna hawaye takeyi

"Yanzu kina ina?"

"(na Mercure hotel"

"Ki saki wannan dakin ki samu taxi,zan turo miki address din hotel din da muke"

"Tom" ta fada cikin zafin da ita kadai tasan yadda takeji a zuciyarta. Wayar ta ajiye tana furzar da iska,ta fara fahimtar fissafinta na neman wagajewa ne,a yanzun kuma tana buqatar nutsuwa qwarai tare da takatsantsan wajen fidda sabon takunta

"Bansan wanne kaidi ne zaiyi dai dai da abinda kika
aikatamin ba säahar, maji…...maji....bazan taba bari kici gaba da rayuwa kusa da yayana ba bare gaddarar sake zamowa matarsa a karo na biyu ya afka min ba".


Abindata furta kenan tana kallon fuskarta ta cikin
madubi, zuciyarta kamar zata fito ta bakinta saboda
zallar bacin rai.

Da kansa ya fito bayan isowarta hotel din,ya sauka qasa ya shigo da ita. Suna shigowa veranda din nadeeya na fitowa a dakinsu

"'Mommy ina kika shiga ne tun dazun?" Harara ta ballawa nadeeya din,saboda a yanzun dan sauran tausayin nadeeyan da takeji wanda shine silar da yasa take daga mata qafa bata sakata cikin budget yanzun ya fara ja baya

"Sai yanzu kikasan da ni,saboda kinga uwarki ko?" Yar
Daria kawai ta saki,dr jarma da yanzu bayason jin zancan maji daga bakin fauziyya yace

"Nadeeya,maza ki cewa ummanki ta fito muyi sharing dakina,ke sai ku kwana da mummynku"
"Toh abba" Nadeeya da hakan ya yiwa dadi ta juya zuwa dakin nasu.
Wani razanannen kallo hajiva garama ta sakarwa dr jarma
"Yaava? va zaka hada dakin kwana da matar da ba halalinka ba? ka manta ba aure a tsakaninku shekaru kusan talatin?" A nutse ya kalli fauziyya din,karon farko sai mamaki ya mamayi zuciyarsa saboda tsananin tashin hankalin da ya gani saman fuskar fauziyya
"Kinsan dai ni musulmi ne kuma babu ta vadda zan aikata abinda yake Haram, ko 'ya'yana yanzun ba zasu barni ba, bare na jima da mallakar hankalin kaina"
"Kanaso kacemin ka maida aurenka da SHIFA?" Hajiya qarama ta jefa masa tambayar cikin matsanancin tsoron amsar da zata fito daga bakinsa.

Kai ya jinjina mata, kafin yakai ga bude baki yayi mata bayani har ta fashe da kuka me sauti sannan ta juya cikin sassarfa tana nufar stairs da sassarfa.
"Fauziyya,meye haka?" Ya fada yana bin bayanta da sauri. Gabanta yasha yana kallonta, mamaki yana sake kamashi tare da irin kukan da takeyi,kuka ne irin wanda yake fita kai tsaye daga cikin zuciya kuma bilhaqqi
"Wanne irin kuka kikeyi haka fauziyya?, na dauka zakiyi farinciki ki kuma taya 'ya'yanki murna akan daidaito da muka samu da mahaifiyarsu bayan shekaru masu yawa bama tare?" Yayi mata tambayar idanunsa cike da ayar tambaya. Cikin rai da zuciyarta gangar jikinta ta bata muddin batayi da gaske ba zata fallasawa kanta asiri
"Ba wannan bane damuwata ba yadda yaaya a watannin nan kai da toufeeg baku daukeni a bakin komai ba, tamkar ma kuna shirin fara juyamin baya, kunata al 'amuranku ba tare da shawarata ko sanina ba, saboda kaga qasa ta lullube idanunsu ummee?, wayyo ni Allah fauziyya,sai da girma yazomin sannan zan fara ganin ainihin abinda maraici yake nufi?,said.....
" Bata garasa fadin abinda tayi niyya ba qirjinta taji ya riqe kamar ana sukarta,kadan kadan ta fara jin jiri da wani irin ciwo da wani sashe na kanta ya riqe dashi,sai numfashinta ya fara mata wahalar jaa,abinda yaja hankalin Dr jarma kenan,.ya fahimci akwai matsala va matsa kusa da ita vana rigeta tare da tambayarta lafiya?. Tuni ta fara wani irin haki,Allah ya taimakeshi a sannan daya daga cikin ma'aikatan hotel din yazo wucewa.
Shi va taimaka masa suka rigeta bayan yay kira zuwa clinic na hotel din, aka dace akwai likita,kai tsaye suka nufi dakin nadeeya da ita.
Sanda suka tura gofar suka shiga nadeeya na tsaye tana yiwa maji nacin taje abbanta yana kiranta
"Nadeeya,wai yaushe na zama kakarki ne? ki fita a idona fa?" Kafin nadeevan ta sake cewa komai suka shigo da hajiya qaraman a rirriqe,sai maji ta mige tsam tana dubansu har suka kwantar da ita saman gadon, ma'aikacin hotel din ya juya ya fita don ya garaso da likitan.


Zafafabiyar
*HUGUMA*


* TABARMAR KASHI *


Book 02Page 54

_Assalamu alaikum warahmatullah_

_Zan danyi wani qarin haske game da hukuncin jinin b'ari_

_Duk cikin da akayi b'arinsa gasa da kwana tamanin da daya,ya zamana a b'arin gudan jini ne ko jini ba wasu alamu na halittar dan adam ana daukan jinin da ya biyo baya ne a mazaunin jinin cuta,zakiyi sallah da dukkan ibadunki,me gida kuma yana iya zuwa miki_


_Cikin da yayi sama da kwana 81 sannan akayi barinsa,ko kuma cikin barin anga was alamun halitta kamar hannu ko qafa ko yatsa da sauranu,to hukuncinsa hukuncin jinin haihuwa ne_

_Jiya na sha'afa cikin rubuta na,cikin sãahar yana qasa da wadan nan kwanakin,duka duka bazai wuce kwana talatin ba,so kunga kenan sallah da sauran ibadu zataci gaba dayi,sannan me gida na iya zuwar mata,saidai ya danganta,wani yana da tsantsamin da bazai iya aikata wannan ba,wannan zabinsa ne,yana iya jira har ya dauke,ina fatan an fahimceni_



*Wallahu A'alam*


Duk yadda taso ta boye hawayenta,ko don kada ta bawa maji damar ganin rauninta amma ta kasa,tana jin zucivarta kamar zata fita daga qirjinta,duk wahalar da tayi?,duk shekarun data kwashe tana tanadi?,duk shekarun data diba tana qullawa tana kwancewa yanzu ya tashi a banza?, tayi wahalar banza kenan tunda har gashi maji ta dawo cikin rayuwar dan uwanta? lallai matar nan,da wadanne irin manya manyan bokaye take aiki da suka tsaya mata haka tsahon shekarun?, taketa wahala bata samu nasara dari bisa dari ba? ‚guntuwar nasarar kuma da take ganin ta sameta yanzun lokaci guda ta shammaceta ta sanya hannu ta tankwabeta?.


"ita kuma me ya sameta haka?" Maji ta fadi tana duban Mahmud kai tsaye, shima ita ya kalla

"Ban sani ba shifa,muna cikin magana da ita naga tana shirin faduwa" idanunu maji ta mayar kan hajiya
qaraman,ta santa ba qaramin sani ba,kalar kuka da
hawayen da fauziyya ke zubarwa a yanzu tabbas bana
banza bane. Miqewa tsam maji tayi tana maida dan
madaidaicin hijab dinta

"Hala ka gaya mata wani abune daya tayar mata da
hankali ko kuma yayi mata zuwan ba zata?" Tayi
maganar da sigar tambaya saidai kuma bata kalli dr
jarma ba tana laluben jakarta, don a yanzu ji takeyi ya
kamata ta fita zuwa dakin jarma din ko don idanun
fauziyya su sake gane mata abinda take tantama a
kansa,don tayi imanin labarin gizo baya wuce qoqi

"Wannan family matter ne, Allah yasa kaffara ce" ta fadi tana ratsa tsakaninsu ta fice a dakin. Hajiya qarama na kallon sanda Dr jarma yabi maji da kallo,ya kuma sauke ajivar zuciya lokacin da ya tabbatar dakinsa ta nufa,wani sashe na hanakalinsa yaji ya kwanta dari bisa dari.

A nutse likitan ya cire abun awon bugun zuciya
dake wuyansa,ya kuma fara tattara abun gwajin B.P
dinsa yana rufewa

"Jininta ne yayi mugun hawa lokaci guda,kuma dole ta
kiyaye abinda zai sanyata bacin rai,idan ba haka ba komai zai iya faruwa da ita,zata iya samun matsala a zuciyarta,kuma zata iya haduwa da paralyse".

Bayanan na likitan ba qaramin girgiza mata zuciya sukayi ba, abinda ya sanya hawayenta yaqi tsayawa kenan,ta sake saka Dr jarma a gaba da kuka

"'Indai farinciki na kakeso yaaya da kuma lafiyata dole sai idan ka rabu da maji, har yanzu shifa bata qaunata" duban nadeeya data zubawa hajiya qarama ido dr jarma yayi

"Jeki tava mamanki zama nadeeya,ina zuwa" tsam ta miqe tana jin wani daci cikin zuciyarta,karo na farko fuskar hajiya qarama na komawa baqiqqirin a idanunta,ta dauka ita din me lallashin abbansu ne akan ya maida musu majinsu suyi rayuwa tare da ita kamar kowanne d'a

Please Login or Register in order to submit comment