Reading TABARMAR KASHI 1&2 complete by SAFIYYA HUGUMA Chapter 36 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

amsa.a maimakon haka ma ruwan hawaye ne ya biyo baya.

Ajiye spoon din yayi yana tsareta da idanu

"Meye kuma?"

"Anty N" ta fada hawaye na sake sauka a idanunta. Sosai ranshi ya sosu,don ko sunanta bayason yaji daga bakin fadeelan

"Idan kika sake yimin maganarta.
.. saina zane
bakinki tas" ya fada yana zare idanunta cikin
baraza

"Oya,gate up" muryar sajjad ta ratsa tsakaninsu ya fada yana migawa fadeela hannu. Da hanzari ta miga masa hannun nata hawayen da suka magale suna garasa zubowa,ya tayar da ita tsaye yace

"Muje ki gayawa sister nadeeya ta canza miki kaya,ki barshi yaci kansa shi daya,ya
Allah.
..ina rogonka ka danqara masa
soyayyarta azababbiya naga ya zaiyi da wannan zafin kan da zafin zuciyar" ya fadi maganar yana wucewa gaba abinsa.

Ji yayi kamar ya tashi ya shago sajjad ya nannausheshi,adduar da yayi masan yazun jinta yayi bata da maraba da mutumin daya rogar maka saukar ajalinka a kurkusa. Shima sajjad din yasan me ya aikata,don haka ya dauki fadeela cak suka fice da sassarfa daga sashen,yana jiyo muryarsa yana sake kira masa wani alkaba'in na zurmawa soyayya.

Sumar kansa ya shafa yana furzar da iska,zuciyarsa tana gogarin bashi nutsuwa ta hanyar jaddada masa babu ta yadda zaiyi a yanzun yaso wata diya mace, babu wata d'iya mace da zata iya galabar tsallakawa takai ga zuciyarsa,an gama yiwa ruhi da zuciyarsa barna,bazai kuma sake bari hakan ta faru ba,kai kwata kwata ma yanajin cewa a yanzun babu wani abu waishi SOYAYYA dake existing,zaifi kyau a canza masa suna da sha'awa ko son zuciya.

A lokacin ne ya samu damar shiga toilet yayi wanka,duk yadda yaso ga yaci jerin abincin alfarmar da Jacob ya saba dafawa ha ajiye masa amma yau ya kasa dora komai saman harshensa,kukan da fadeela keta faman yi a kwanakin ya tsaye masa a rai,yau ta bugaci wani abu da yakejin bazai taba iya bata shi ba,sai kuma rashin walwalar nadeeya,duk gidan sun maidashi wani so silent, damuwa ce fal cikin zuciyarsa,wadda har sai data taba kuzarinsa.

Yana tsaka da duba wasu ayyuka a system dinsa,ya shanya abincin da tun daxu Jacob yayi serving nasa amma ya kasa ci,aka gaya masa baaba ramatu nason ganinsa. Kafafunsa ya sauke yana bada izinin shigowarta,ta shigo cikin kamala da nutsuwarta,yayi mata da nuni ga saman kujera,ta koma ta zauna

"Barka da yamma" baaba ramatu din ta fada,cikin girmamawa yace

"Barka kadai,ya aiki?"

"Alhamdulillah " ta amsa shi tana murmushi

"Idan babu damuwa shawara ce dama nazo da ita" ta furta a nutse tana dubansa.

Kansa kawai ya gyada mata alamun ya bata dama,ta danyi gyaran murya kadan tana tauna abinda zata fada

"Nikam nace me zai hana kayi haquri da korar nannies din fadeela,saboda dole sai ana haquri da halaye da dabi'un mutanen da kake rayuwa da su,ba ta yadda za'a yi kowa yayi maka abinda kakeso dari bisa dari,yarinyar cikin watannin da tayi qalilan tayi aikin da babu wanda ya taba yiwa fadeelan shi,tana da kula da takatsantsan da iya raino,idan ba damuwa kayi haquri ka dawo da ita taci gaba da kula da fadeela don Allah" kansa ya dago ya kalleta,sai kuma ya maida kan abinda yakeyi, kamar bazaiyi magana ba kafin daga bisani yace

"Ba zata taba dawowa ba,ta tafi kenan,so ku koya mata haquri,tunda tun farko dama ba da ita ta saba rayuwa ba,dole zata ci gaba da rayuwa ko bayan babu ita" tunda baaba ramatu taji ya fadi hakan ta tabbatarwa kanta saahar ta tafi kenan. Kaifi daya ne shi,wanda tsanani baya sakashi sauya zancansa ko
dawowa da baya. Migewa tayi sali alin ta fice a gurin,cikin ranta tana jin matugar kewa da takaicin subuce musu da yarinya kamar sãahar tayi,ta tabbatar ba za'a maida kamarta
ba.

Sai yamma sosai sajjad suka dawo da fadeela,ko bayan sun dawo din bata ma shigo sashen toufeeq din ba. Tana lafe jikin nadeeya,wanda kafin kace meye wannan wani mugun zazzabi yayi ram da yarinyarnar wani irin rawan sanyi takeyi. Sosao hankalin nadeeya ya tashi,ta dauki waya ta sanarwa toufeeq. Daga masallaci ya dawo, kwanakin tunda suka fara wannan rigimar saboda tafiyar sãahar din shima baya fita ko ina,a gida yake wuni,duk wani aiki ta system dinsa yake gudanarwa.

Hankalinsa yafi na kowa tashi,saidai zuciyar 'yan maza wadda bata bari aga rauni a tattare da ita. Mota ya kaita,ya sanya baaba ramatu ta shirya tazo su kaita asibiti.

Nadeeya na zaune tana sharar qwalla har suka fice,zuciyarta a mugun karye,ta tabbatar wannan zazzabin na fadeela yana da nasaba da yadda tayi mugun sanya sãahar a ranta,da qulafucinta da takeyi. Gaza jurewa tayi ta mige ta isa daki,ta cire wayarta dake saman dressing table ta budeta,ta zauna bakin gado tana lalubar number sãahar.

Dai dai lokacin da suke zaune a falo ita da afifa suna hada fruit salad din abincin dare,cikin kwanakin gaba daya itama ta sake zama so silent,babu wani karsashi ko kadan a tattare da ita. Duk da yadda fadeela ke tsaye a ranta,amma taqi bawa zuciyarta damar da zata karaya. Har a ranta tana jin hukuncin data yanke shine dai dai,babu gudu babu ja da baya,ta yadda sabo turken wawa ne,amma idan tayi haquri wataran zuciyarta zata rusuna,taji tamkar ma bata taba rayuwa da fadeelan dama duk wani ahalin gidan ba. Gefe guda kuma dukka kunnuwanta na kan motsi da kai kawon gidan,duk da ta tattara lamarinta ta miqashi ga Allah,saboda ta tabbatar tunda har ta bawa Dr girema wuga da nama akan lamarin mahmud,to tasan fa babu fashi aure ne zai zama tabbatacce a tsakaninsu. Abu mafi razani dake jijiga zuciyarta,kaddarar auren adam me daci ce da hallaka dukkan buri da gusar da fata ko sha'awar ci gaba da rayuwa ta aure dama ta duniya gaba daya..
...ita kuma qaddarar auren mahmud fa? yaya zata zo mata?. Tambayar kenan dake barazanar fasa mata zuciya a duk sanda tazo kanta. Ta sani cewa saidai suyi zaman haquri ita da mahmud kawai,amma babu ta yadda za'ayi ya samu yadda yakeso daga gurinta,ta gaya masa wannan ta sake nanata masa,ya shaida masa yes......a shirye yake yayi haquri da ita ya kuna zauna da ita koma a yaya ne.

Wani sashe a zuciyarta kowacce rana nana ya mata cewa JINSIN MAOARYATA
NE,JINSIN MAHA'NTA NE,duk abinda suka gaya maka bashi kake tararwa ba bayan aure,yaudara da cin amana da karya alqawari sun lullube zukata da harsunansu, bata tunanin akwai wata kalma ta soyayya da jan hankali, nuna zallar kulawa da rayuwa yare har bayan mutuwa wadda adam bai furta mata ba,amma yaya sakamakon hakan ya kasance?. To auren me zatayi? ‚AUREN BIYAYYA kenan ko me? tunda dai ita din batakai lokacin da za'a ce tayi auren kai buta da ruwan wanka bandaki ba.

Tsakiyar wanann tunanin wayarta tayi burari,ta waiwaya a nutse tana duban me kiran,zuciyarta na gaya mata mahmud ne, wanda zuwa yanzu ta fara tsanarsa tare da tsanar komai daya shafeshi, yana yaiwata kiranta da sunan caring,caring din da ita kuma bata sonshi, don duk abinda yayi sai taga kamar yana bin footprint na adam ne.

Mamaki yadan kamata gain sunan nadeeya.
Bawai bata kiranta ba,a'ah,tun daga randa ta baro gidan,har tayi kwanaki bakwai babu ranar da bzata fito ta fadi bata kirata ba tana roqonta akan ya dawo. Randa tayi alqawarin ba zata sake kiranta ba tayi fushi ne saboda ta tabbatar mata ba zata dawo ba,suyi haquri ta kula da fadeela,tun daga ranar bata sake kiranta din ba,saidai kullum zata bar mata good morning massage through watsapp dinta.
Wugar hannunta ta ajjiye ta miga hannu ta dauki wayar,ta daga kiran ta karashi a kunnenta. Gabanta yayi mummunar faduwa jin sautin kukan nadeeya,tayi saurin kama sunan
Allah sannan ta samu qwari gwiwar tambaya

"Sister nadeeya,me ya faru?"

"Fadeela ce.

" Sai kuma maganar tata ta
tsaya,abinda ya haddasawa sãahar wani irin muguwar faduwar gaba,ta sake kiran sunayen
Allah

"Karki cemin wani mummunan abu ya faru da ita"
*HUGUMA*

* TABARMAR KASHI_*6

Book 02 Page 02

"Ke da mahaifinta dama ba burinku kenan ba? vanzu haka tana asibiti, kuma ko meye ya faru da ita kune ke da alhakin hakan" daga haka ta katse wayar,tabar sãahar da waya a hannu.
"Gaskiya ta fada,meye laifin yarinya da zaku shiga rayuwarta ku gigita mata ita?,rana daya saboda baki shiri da mahaifinta ya birkitaki ke kuma ki tattaro ki bar yarinya kwatsam?"

"Bai isa ya birkitani ba,baida wannan qarfin ikon,abinda na sani kawai bazan taba iya rayuwa dashi a muhalli daya ba muna shagar iska daya”

"'I dan kukayi kisan kai ai ku kuka sani" afifa ta fada cikin jin haushi tana migewa a wajen.
Maganar Allah itama zuwa yanzun haushinsu takeji,kamar masu ganin hanjin juna? babu dama su hadi guri guda sai kowa ya hau tashi kamar kububuwa?.

Tun daga lokacin da nadeeya ta kirata har zuwa wayewar gari ta gaza moruwa gaba daya, lokaci lokaci sai ta samu kanta da duba wayarta,tanason kiran nadeeyan amma kuma batason tayi abinda zai sanya zuciyarta karyewa. Ko a daren jiya baccinta rabi da rabi ne,iya baccin data samu yi din cike yake da mafarkan fadeela na koke koke,abinda ya hadu kenan yayi mata rubdugu ya kassara duk wani walwala da karsashinta. Don ko da safe kwance tayi a daki,ta kasa fita ko ina. Ba abinda takeson gani a wannan lokacin irin fuskar fadeela,ta rungume yarinyar a jikinta kamar yadda suka saba,to amma kuma ta yaya?,batason cin fuska da cin zarafi don haka ya zama dole komai wuya komai daci ta nisanci dukan abinda yake da jibi da MT JARMA.

Zuwa la'asar juriyarta da dukka
haqurinta ya qare,wunin daki tayi ita kadai afifa yau tana asibiti gaba daya,ta kalli agogo,biyar saura,lokaci irin wannan lokaci ne nayin karatunsu ita da fadeela,ko ya halin karatunta ya shiga ciki?,duk yadda taso ta jure sai da qwalla ta cika idanunta,saboda ta tuna algawarin da tayi mata na har ta gama exam tare zasuyi karatun,to saura guda biyu ta kammala ta baro gidan,batasan waye ya tallafeta sukayi karatun biyun da sukayi saura ba. Batasan ya akayi ba sai kawai ta samu kanta da laluben number nadeeya cikin jerin calls dinta na yau,ta danna number tayi dialing.

Hannunsa zube a aljihun silky trouser dinsa daya dace da short sleeve shirt din dake jikinsa,yana takawa a nutse tamkar saboda shi daya akayi hanyar da zata sadaka da dakunan AMENITY na asibitin. Manyan dakuna dake dauke da dukkan wasu kayan buqata tamkar kana gidanka. Ko baka sanshi ba kalli fuskarsa kasan wani kwantaccen fushi ne zalla a samanta,saidai tarin nutsuwar da yake da ita data cakude da miskilancinsa ya sanya ba lallai ka lura da hakan ba kai tsaye.
Babu abinda ke amsa kuwwa a kunnensa sai bayanan Dr anwar,wanda yake jaddada masa dole ya kiyaye yasan meye asalin abinda ya sanya fadeela a wanann mummunar damuwar,dole ne yayi qoqarin sama mata abinda zai sanya hankalinta kwanciya ya dawo da ita walwalarta,ko don lalurar da take da ita, wadda ta ragu sosai fiye da baya. Shi kansa dr anwar mantawa yakeyi wani lokaci da lalurar tata,saboda komawa baya da takeyi tana raguwa da kadan da kadan a yan watannin da sãahar din ta kasance da ita. Idan yayi zuzzurfan tunani hakan yana nufin babu makawa sai ta dawo cikin rayuwarsu?,kenan tayi galaba dukka shirinta yayi tasiri kenan?,sai ya furzar da iska me zafi daga bakinsa,ransa yana gonewa,yana jin wani irin zafin yarinyar a ransa. Daga ranar da ya shata layi tsakaninsa da kowacce diya mace,babu macen data sake shigowa rayuwarsa tayi masa wannan karan tsayen sai ita. Dai dai sanda ya isa gofar dakin,ya sanya hannu ya murda handle din ya bude,saidai kafin yakai ga shiga yaji sautin siririyar muryar fadeela da ko yaushe bata rabuwa da kuka tana kiran sunan

"AUNTY N,don Allah ki dawo, Allah bazan zauna ba nima idan baki dawo ba,kinmin alqawari amma shine baki cika ba? kullum kuka nakeyi,amma abby yace bazanzo ba,a nan zan zauna,kema kiyi zamanki". Dukkansu ita da nadeeya basuga shigowarsa ba,bare baaba ramatu dake sallah saman abun sallah.

Kai tsaye ya sanya hannu ya zare wayar dake magale a kunnen fadeela,ya juya a nutse yana fita a dakin,ransa na zafi.

"Hello..
...hello,nadeee" sautin lallausar
muryarta ya sauka a kunnensa lokacin da yake magala wayar a kunnensa,ya lumshe ido yana jin tsanar

"Nawa kike da bugatar a biyaki ki dawo cikin ravuwar da kika riga kika shigeta cikin shirin faruwar hakan?" Cak komai ya tsaye mata,cikin mamaki ta kalli number,ta sake tabbatarwa number nadeeya ce,don dama ita din bata taba ajiyar number dinsa a wayarta ba,saita sauke wayar daga kunnenta kawai ta katse kiran,saboda bata jin zata iya tsaiwa ta saurareshi.

Komawa tayi ta lafe a gado,zuciyarta na wani bugawa a jejjere,kwata kwata ta manta da sautin murvarsa cikin kwanyarta,don bata sake iinta ba sai a yau din. Idanunta ta mayar ta kulle,sautika biyu na tsalle tsakanin qirjinta da kunnuwanta,sautin innocent fadeela,da kuma sautin deep and husky voice dinsa.

Labbansa na qasa ya cije lokacin da ya fahimci ta kashe masa waya ne,abinda yafi tsana kenan a rayuwarsa,sai ya sake tunzura ya kuma dannawa number din nata kira.

Karar wayarta a karo na biyu ya
sanyata bude idanunta,ta kalli wayar,kamar ba zata daga ba sai kuma taga nadeeya dince,ta dannan Koren shudi ta sanya kiran a handsfree

"Muddin kika sake kashemin waya sai na baki mamaki,don har cikin gidanku zan iskeki,nace nawa kikeso a biyaki ki dawo bakin aikinki?"
Yayi maganar cike da wata izza da gasaita.
Tunawa tayi da matsayinta a rayuwa,da kima da kuma darajarta ta diya mace,wannan ya bata qwarin gwiwa,ta mige ta zauna sosai saman gadonta

"Bazan dawo ba!" Ta gaya masa kanta tsaye,ta kuma dakata tana jiran abinda zaya fadi. Har tsakiyar kansa yaji saukar muryar tata da kalaman da suke nuna rashin toro ko daga gafa

"Dole ki dawo,ki qarasa abinda kika fara shiryawa,dole ki dawo inason naga iya gudun ruwanki na kuma qurewa wasanki gudu donki tabbatar da banbamcin dake tsakaninmu" ya fadu a zafafe. Katse wayar kawai tayi saboda yadda deep voice dinsa ke shiga kanta sosai,tana ratsa jijiyoyin jikinta tana jin kamar yana a cikin dakinne. Ba iya katse kiran ta tsaya ba,gaba daya wayarma ta kashe,ta koma ta kwanta rub da ciki idanunta a lumshe,muryarsa naci gaba da yawo a kanta.

Abu guda daya data sake amincewa dashi,yana da izza izgili da girman kai,ta fahimci akwai damuwa sosai cikin muryarsa, damuwar kuma bata rasa nasaba da ciwon fadeela daya sanyasu dukka a damuwaryanaso ne ta dawo taci gaba da kula da fadeelan duk da ransa baiso hakan ba.amma shi baisan hanyar da zai lallaba mutumin da yake neman abu a gurinsa ba,a haka zata koma? kai koda da sigar lallashi yazo mata bata jin zata koma,bare a yadda yazo mata cikin izza da gadara,sai ta gyara kwanciyarta ranta na turereniyar abubuwa guda biyu,tausayin fadeela da kuma takaicin kalamansa.

Hannayensa ya yarfar,nadamar karbar kiran dayi mata tayin dawowa na lullubeshi,tunda yake babu wani mahaluki daya taba masa abinda tayi masan, ji yayi kamar yayi jifa da wayar,ya juya wayar a hankali yana qare mata kallo

"Ta yimin dai dai, kuma haka shike nuna baka shirya samarwa 'yarka lafiya ba" sautin murvar Dr jarma ya ratsa kunnuwansa. Da sauri ya waiwaya bayansa yana duban mahaifin nasa,sam baiyi zato ko tsammanin ganinsa a gurin ba,tunda ma tun wancan satin sukayi sallama dashi ya tafi china,kuma a galla zai kwashe wata guda bai dawo ba. Rusunawa yayi ya rage tsahonsa

"Barka da warhaka"


"Aikai za'a yiwa barka muhammadu" daga furta hakan da yayi sai ya juya kawai ba tare da yace dashi komai ba. Da hanzari ya rufa masa baya sukaci gaba da takawa yana qoqarin cimmasa,abinka da sabon jini nan da nan ya tarar dashi,suka jera kafada dashi ya sake russunawa yana gaidashi sanda suke shiga verandar da zata sadasu da dakunan

"Barka kadai,ya goqari?" Ya amsa masa cikin salon gatse, kafin ya samu amsar mayar masa nadeeya ta fito daga dakinsu riqe da hannun fadeela wadda ke takawa da gafafunta,fuskarta a washe matuqa,tamkar ba ita ya fita ya bari da hawaye shabe shabe ba

"Yauwa,ku qarasa mota ku jirani ina zuwa" Dr jarma ya fadi yana takawa zuwa office din likitan. Hankalinsa rabuwa yayi biyu,sallamarsu akayi ko kuma Dr dinne ya sallami fadeelan da kansa?,ganin zai batawa kansa lokaci sai kawai yabi bayan dr jarma da tuni ya isa office din Dr anwar.

"In sha Allah nan da gobe ma zakuga ta mige sarai, damuwa ai matsala ce a zuciya,ita kuma zuciya idan ta samu cikakkiyar lafiya ta kubuta daga damuwa,to dukka gangar jiki ma zata samu cikakkiyar lafiya da kuzari" kai dr jarma da yaga shigowar toufeeq ya gyada

"Gaskiya ne dr,zama da damuwa dama a zuciya saidai idan kai kaso,sai kayita zamanka a haka tunda haka ka zaba,kowa kuma yayi rayuwarsa cikin farinciki" sarai dr anwar ya fahimci magana ce me harshen damo, tunda bawai yau ko jiya yasan familyn JARMA ba,kusan abubuwa da dama tare dashi akayi.
Hannu dr iarma ya bawa dr anwar yana masa godiya,sannan ya tako yana fita. Kallo daya touteeq yayi masa sai yayi masa nuni da zasuyi waya,yabi bayan abban nasa.

Motocinsa hudu ne a parking lot na asibitin, motar da yafi zama a ciki yaga ya nufa ya bude,sai yabi bayansa. Har ya sanya kai ya tsaya ya waiwayo yana kallonsa

"Af,bari na maka bayani don sauke haqqinka na uba ko? zan kaita inda aka saba kula da ita,idan ta samu lafiya kaje ka daukota,idan kuma kaie din,ba ita kadai nakeso ka dauko ba,har wadda ta kula da ita din zataci gaba da kulawa da ita nakeson su dawo cikin gidan suci gaba da rayuwarsu yadda suka saba" daga haka ya shige motar sajjad ya rufe,ya sanya drivers suka tashi motocin suka bar harabar asibitin.

Sam kanshi ma a sanann a daure yake,bai kawo masa tunanin inda dr jarma din zai kaita ba

"Sir....zamu tafi ne?" Muryar jibril ta shiga kunnensa,sai ya amsa alamu da hannu,ya matso da motar ya bude masa ya shige ya rufe suma nasa motocin sukabi kwalta.

*HUGUMA*

* TABARMAR KASHI *

Book 02 Page 03

Fitowarta kenan daga kitchen bayan ta gama shan coffee ta maida mug din,qofar falon da taji an bude da sauri ya sanyata waiwayawa da sauri,cikin zallar mamaki ta tsaya cak,tana duban fadeela dake takowa da gudu tamkar almara ta cukukiyeta tana kiran sunanta da garfi. Zubewa tayi saman gwiwarta tana riqe yarinyar da kyau tare da tattaba likinta a rude

"Fadee,waye ya kawoki? kinsan gidan nan? ya jikin naki? kin warke ne?"

"Babu wani ya jikinta,kamar dai irin da gasken nan kin damu da ita" muryar afifa da sautin muryar fadeela ya fiddota daga daki ya wanzu a falon

"Wallahi,gashi mu mun laluboki mun kawo kanji" nadeeva ta fadi tana takowa Sosai cikin falon,tare da kallon kusurwoyinsa,mamaki yana saukar mata tare da tarin tambayoyi fal cikin kanta. Migewa tayi dauke da fadeela tana murmushi

"Babu yadda zanyi ne sister nadeeya,kada kiji haushina" ta furta tana mata tayin gurin zama

"Fushi nake dake saboda haka bazan zauna ba,rakiya kawai na yowa abba" idanu sãahar ta fiddo waie cikin mamaki

"Wai Dr?" Sai ta jiniina kai

"Suna waje shida abban gidan nan" sosai mamaki ya kama sãahar,sai ta sauke fadeela ta kama hannunta sukayi kitchen don samarwa dr jarma din wani abun shan.

Falon sai ya zamana babu sai su biyu ita da afifa,afifan ta qaraso tana murmushi

"Yaudai naga sister nadeeya,ki zauna mana" tana murmushin itama ta zauna,sannan tace

"Don Allah bestie kiyi haquri, kaina ya kulle,tambayoyi ne dani fal bakina,kuma nasan aunty N ba zata taba tsaiwa tayimin dogon sharhin da nakeso ba,and na tabbata kedin kina da amsar kowacce tambaya tawa" hannu afifa ta miga tana murmushi

"Kaina ya kawomin wasu tambayoyin da kike dasu,nasan kuma dole ki bugaci amsarsu,zo muie ciki" tsam ta mige tabi bayanta,suka wuce kai tsave zuwa dakinsu säahar din.

Ko afifa bata fada ba nadeeya tasan dakin na saahar ne,don kusan yadda ta tsara dakinta na gidansu haka wannan,har yafi wancan nesa ba kusa ba,komai a kammale cike da tsafta da qamshi da wani irin tattausan yanayi.

Tana dauke da babban tray din fadeela na biye da ita tana zuba mata labari a nutse daya bayan daya,riqe take da gefan doguwar rigarta tana biye da ita kamar jela,kai kace guduwa zatayi ta barta. Tun kafin su qarasa sai kunya ta kamata ganin yadda Dr da abbanta suka bisu da idanu kamar dai irin kana zancan mutum sai kuma kukaga tahowarsa daga nesa. Ta qarasa gabansu cikin girmamawar nan da kuma mutuntawa takai qasa tana gaida dr jarma,tare ta bude murafun abubuwan shan da tazo dasu tana zuba masa fadeela na matso mata da cups din. Cikin matugar kulawa ya amsa

"Amma daa saura kadan nima nayi fushi dake,kin biyewa wancan tsatstsauran kuna shirin yin sakarci?" Sai ya maida dubansa ga dr girema

"Ban taba sanin ita ke kulamin da jikata ba sai da muka iso gidan nan na fahimci hakan,bana fatar wannan alaqar ta yanke ta tsaya iya haka" dr mahmud ya fada yana jin wani karsashi yana shigarsa. Tun farkon saninsa da sãahar ta kwanta masa,yanayin kamun kanta,sanin kima da martabar dan adam, da tsantsar tarbiyyar daya gani daga gareta,duk kuwa da zurfin karatun bokon da take dashi...hakan ba qaramin burgeshi yayi ba, dabi' unta sun banbanta dana sa'o'i da takwarorinta masu matakin karatu da gata irin nata.

"Ga 'yarki nan na kawo miki,zata zauna tayi jinya a gurinki" kalaman da dr mahmud ya fada kenan lokacin da sukayo masa rakiya zasu koma shida nadeeya,maganar da tadan daurewa sãahar kai,anya da sanin wancan dan wulaqancin Dr jarma ya kawo mata fadeela?.

"In sha Allah zaka jini,na gode qwarai da ziyara,duk da ba takanas akazomi ba,sahun diyarka ka biyo" muryar dr mamman girema kenan yake fadiwa dr jarma

"Diyata ta cancanci a biyota,idan ban jika bama mamman ni zaka iini,ni zan fara nemanka ma"
"Karka damu" ya fada yana murmushi,sannan ya maida masa murfin motar,suka tayar da motocin suna ficewa a gidan.

Zuzzurfan tunani nadeeya ta shiga,daya bayan daya qwaqwalwarta ke mata bitar maganganun da sukayi da afifa,akwai abubuwa da suka bata mamaki tausayi da kuma daure kai,ashe already yaa toufeeq da anty N din sunsan juna?,but itafa laifin yayanta take gani to be frankly,a nan bataga laifin sãahar ba,cikar diya macen kenan ko ita ba zata dauki izzar d'a namiji ba. Amma abinda yafi gigitata rayuwar da säahar din ta fuskanta,wadda ta tilastata sauyawa daga ainihin dabi'unta. Abu mafi ban mamakin shine daya zamana wai ta taba aure,babu abinda zai nuna maka alamun hakan tattare da ita tafi miliyoyin 'yammata cikar haiba da komai na halitta. Sake juya kanta tayi wata shawara me girma na tsargawa cikin ranta,sai ta kira sunan
Dr da

"Abbana"

"'Ya akayi?" Ya tambayi nadeeyan yana qoqarin ajiye wayarsa bayan ya gama duba wani abu.
Idanunta suka dan kai kan wayar,sai taga kamar hoton MAJI dinta

"Abba dama kana da hoton maji ne?" Bakinta ya subuce ta jefa masa tambayar,don basu taba magana makamanciyar irin wannan baidanunta a kansa tana kallonsa. Harara ya watsa mata

"Yau nine na koma abokin wasanki?" Janye dubanta tayi zuciyarta da gwiwarta tana karyewa

"Kayi haquri" ta fada a sanyaye,sai yaji tausayinta ya kamashi

"Me ya faru kika kira sunana?" Gara zamanta tayi

"Ka taba sanin wani abu akan anty säahar?"
Shuru ya danyi sannan ya girgiza kai

"A'ah,akwai wani abunne?,mahaifinta Dr mamman munyi karatu dashi tsahon shekara biyar,sanann musan juna sosai a wancan lokacin,yanayi da lokaci ya jefa kowa inda yaso sai kuma aka rabu,sai bayan dogon lokaci bayan mun hadu da muhyiddeen na
fahimci dansa ne,shekaru masu yawa kuma
sai yau Allah ya gaddara ganawarmu" kai ta
jinjina,sannan ta warwarewa dr jarma din
kome data ji daga afifa.

Tsahon lokaci yana jinjina kai ba tare da
yace komai ba

"Amma abba ni ina da shawara" juyawa yayi ya
dubeta
"Wacce irin shawara ce?"

******Tun daren ranar da aka kawota take
magale da sãahar,duk inda ta motsa sai ta
bita gafarta qafartaji takeyi kamar zata gudu
ta barta. Ko da sukazo kwanciya sai data
rungumeta sosai,a haka bacci yayi awon gaba da ita.
Afifa na gefe tana kallonsu,dariya tayi lokacin da take zare jikinta daga na nadeeyan a hankali

"Ah kin hadu fa da chewing gum" murmushi sãahar tayi,tana shafa kan fadeela gami da maida mata gashinta da ya ya mutse baya

"Ta saba aiko a gida sai tayi bacci kafin na koma dakina" kai afifa ta gyada tana kallon fuskar fadeelan cikin tausayawa,farat daya taji yarinyar ta shiga ranta.

Kwana uku cakal amma sai ka dauka fadeelan ta shekara a gidan,ta sake sosai tana ta walwalarta da harkokinta,zuwanta sau ya sake raya gidan,baya rabo da motsinsu da kai kawonsu ita da saahar,maama dai 'yar kallo ce,amma ita kanta yarinyar ta shiga zuciyarta,idan ka gansu zaka dauka itama daya ce daga cikin jikokinta,hadda da dr girema fadeelan ta shiga zuciyarsa,yana kallonta kamar su Aleena,idan ka shigo gidan zakayi tunanin itama jikar gidan ce kamar su khalifa.

Fadeelan bata

Please Login or Register in order to submit comment