Reading TABARMAR KASHI 1&2 complete by SAFIYYA HUGUMA Chapter 59 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

qananun qwarika dake cikin tsirran dake baibaye da gidan.

Babu tsoro ko fargaba ta sanya spare key ta bude qofar falon ta kuma saka kai cikin takatsantsan. Bata tsava a ko ina ba sai dakin fadeelan, ta tura ta shiga ta sauke ajiyar zuciya ganin babu kowa,ranta ya bata yau a sassan toufeeq din zasu kwana kenan, don tana lissafe da duk sanda basu kwana a nan din ba suna sashensa

"Bagar matsiyaciya,kin kusa fita daga rayuwata, kin kusa barin gidan nan,gidan nan gidan meenal ne, toufeeq da abinda ya mallaka dama wanda ubansa ya mallaka duka na meenal ne da abinda zata haifa" ta sake fadi a fili cikin sumbatun da batasan tana yi ba.



Zafafa biyar
🔥🔥🔥🔥🔥🔥
🔥🔥🔥🔥🔥🔥
*HUGUMA*


* TABARMAR KASHI *

Book 02Page 48

Loko da saqo na dakin ta dinga bincikawa tana neman robar maganin fadeelan,sai data gaji sannan ta samu nasarar ganota. Saman gadon fadeelan ta zazzage maganin duka,ta lissafa wasu ta kwashe,ta debo iya wannan adadin ta zuba ta cakuda su da kyau sannan ta maidata kamar yadda take ta ajjiye, ranta fes, zuciyarta na mata dadi. Har abada ba zata taba bari maji ta huta completely ba,babu wata hanya mafi sauqi da zata ci gaba da razana rayuwarta irin wannan hanya,kafin zuwan lokacin da. zata maidata marainiyar da bayan rasa uwa da uba,yaya da jikokinma suyi ma rayuwarta sallama su barta ta rayu cikin maraicinta na haqiqa,ledarta ta dauke ta juya tana fita a dakin cikin nutsuwar da sai a yanzu ta sameta.


* Shuka a idon makwarwa_☺️☺️

Kira daya maji ta dauka,sai a sannan kuma yaji wani nauyi yana kamashi sanda amintacciyar muryarta Re furta sallama a gareshi, idanunta na tara ruwan hawaye,yau itace Muhammad da kansa ya daga waya ya kirata bisa radin kansa?,wacce irin farar rana ce yau a gareta?.

"Muhammad" ta kirayi full name dinsa cikin karyewar murya,duk wani qunci da take ciki a dan kwanakin saboda abinda mahaifinsa ke shirin aiwatarwa a kanta sai taji yana kwaranyewa

"Kiyi haquri maji,qila na tasheki a barci ko?"

"Bacci Muhammad?, ina daku a wani muhalli da ban aminta da amincinsa ba ina ni ina bacci?,shekara ashirin da wani abu rabona da bacci a irin wannan lokacin, kada ka kashe Muhammad, gayamin dalilin kiran" sosai yaji zuciyarsa tayi wani mugun karyewa,duk yadda yaso ya rige hawayen da suka taso masa abun yaqi yiwuwa,UWA wata halitta ce da kaf duniya babu inda zaka samu rahamar da tayi dai dai da wadda ke cikin zuciyarta akan d'anta,shin sau nawa ya hana idanunsa bacci kamar haka ya yiwa maji din addu'a koda na sati guda ne? ya sani duk salla ya sanya goshinsa a qasa sai ya musu addu'ar

"Rabbirhamhuma kama rabbayani saghira" saidai yasan ko kaso daya cikin dari na wadda ita ke musu baiyi ba

"Ki yafemin majl,am sorry for all the....." Sargewa
muryarsa tayi,sai kuma maji din ta tari numfashinsa
"Muhammad kai da 'yaruwarka baku taba yimin laifi ba,kuma ba zaku taba yimin ba,idanma kunyi na yafe muku har wanda zaizo a gaba" furucin da ya sake kashe masa jikinsa kenan,ya cikata da godiya sai kuma ya kasa cewa komai

"Baka neman matarka Muhammad?" Ta tambayeshi kai tsaye,saboda tasan basuyi waya ba, hakanan ta tambayi nadeeya ko ya karbi number a wajenta tace a'ah

"Ya zanyi maji? ji nake kaman ni kadai ne a gidan" Yayi subutar bakin fada,bai kuma farga ba sai da murmushi me sauti ya qwace mata

"Zan tura maka number dinta,ka kira matarka,
Muhammad ka riqe matarka fiye da rigon da zaka yiwa duk wani abu me muhimmanci cikin rayuwarka" kai yake jinjinawa

"Ka tayani addu'a,wani al'amari ne ke son sake waiwayowa cikin rayuwata ya kuma tunkareni, Allah yayimin zabi mafi alkhairi koda zuciya ta bataso" maji ta fadi a sanyaye. Hankalinsa yaji ya tashi a lokacin farko da ya fara jin haka

"Me yake faruwa maji?" Murmushi tayi

"Ba wani abu bane, karka daga hankalinka, addu'a kawai na bugata daga gareka"

"Amma dai kina lafiya ko? ‚ba wani abu dake damunki?"

Idonta ta rufe hawayen da take tattali suka sauka,lallai babu wani abu tabbatacce sai ikon Allah,yau itace toufeeg din da aka nesanta tsakaninsu ta kowacce fuska ke tattalin farincikinta da tambayarta lafiyarta?

"Lafiya galau nake Muhammad ta kowacce fuska,ka kira matarka, Allah yayi maka albarka" daga haka ta yanke kiran saboda kukan da taji yanason kubce mata. Bata daga cikin mutane marasa yafiya,to amma kuwa anya zata iya yafewa fauziyya?.

Ba jimawa number wayar ta shigo wayarsa

"Germany?" Ya fada a hankali bayan ya gama qarewa
number kallo ya kuma fahimci code din wanne country
ne maqale a jikin phone number din.

"Me sukeyi a Germany? ‚basa tare kenan da maji" ya
gayawa kansa sanda wayar ta soma shiga tana ringing.

Idanunta da sukayi nauyi saboda kuka da bacci
ta daga,a kasalance takai hannunta ta jawo wayartata,batare data duba ba ta daga,saboda jikinta ya bata afifa ceko maama,tafi zaton afifan ma don haka tace

"Bestie" cikin wani irin sanyi sanyin da ya sanyashi jin
saukar muryarta cikin kowanne sashe na jikinsa,ya
lumshe idonsa sannan ya sakar mata sallama cikin taushi.

Tashin farko ta nemi baccin da yake idanunta ta
rasa, saita maida jikinta ta jingina da jikin gadon dake
kusa da ita tana amsa sallamar zuciyarta na wani irin
harbawa

"Matata nake nema,tana kusa?" Ya fada a nutse. Rasa amsar bashi tayi don haka tace

"Bata nan" garamin murmushi ya saki

"Matar toufeeq fa?" Salon yadda yayi maganar ya sake daburtata tare da kashe mata jiki gaba daya

"'Idan sago ne ka bayar sai a bata" jikinsa ya amsa gaba daya,sai ya gyara zamansa tsakiyar gadon sosai yana sakin mata murmushin da sautinsa ya sauka har kanta,ya kuma tayar mata da kowacce tsiga ta jikinta

"Sago ne me nauyi,wanda babu kunne da zai iya dauka,hakanan babu harshen da zai iya isar dashi,saboda kebataccen sirri ne da ya shafi mijin da kuma jarumar matarsa.....Please tell her, her taste,scent and feel of her skin next to mine.....its all i want every single night,but ta barni cikin kewa da matsanancin so, ki gaya mata am falling and falling and falling for her entirety,ki sake gaya mata i want to feel her skin and i want breath her in i want her in the worst way,| want kisses every corner of her body to express all love which ¡ have in my heart,a million feelings all for one person" gam ta rintse idanunta, tana jin wani abu me nauyi yana saka saman zuciyarta,wani irin yanayi da bata taba tsintar kanta a cikinsa ba,wani irin saqo da ya isa kowanne sashe na gangar jikinta dama zuciyarta,wasu kalamai masu matugar nauyi da zafi da bata taba sauraren kamarsu wajen zaqi da qawata zukata ba. Duk da kasnacewar adam a baya gwani wajen iya tsara kalamai, amma a yanzun sai takejin wadan nan kalaman da kuma kalaman adam,tamkar an dauko ginin gargajiya na ainihi an sakashi tsakiyar fadar white house ta amurka

"SAHR" ta tsinci kalmomin sunanta a bakinsa da wani irin amo me narkar da zuciya kamar yadda ya saba kiranta

"Am too late to be your first. But right now am preparing my self to be your last" kasa jurewa daukan nauyin kalamansa tayi,tsarin yadda yake furta kalaman kadai sun banbanta da muryarsa da yake magana da ita ko da yaushe,wani irin shauqi da soyayya me tsananin tasiri ta sanya ya rasa kowanne kuzari a jikinsa,yana jiran yaji koda kalma daya daga bakinta, amma maimakon hakan sai katse kiran yaju tayi. Zare wayar yayi a kunnensa yana dan sakin qaramin murmushi, kafin ta katse wayar ya iya tsinkayar yadda taja numfashi da sauri cikin sheshsheqa. Wayar ya sulale ya ajjiye a gefansa,ya miqe yana sake jin wani irin shauqi tare da tsananin tausayinta yana fusgarsa. Diary din ya rungume a qirjinsa yana jin tamkar ita ya runguma,ya zura slippers dinsa ya sauka a gadon a hankali ya fice daga dakin.

A nutse ya murda qofar dakin nata, idanunsa da hancinsa suna sake tabbatarwa lallai nan din muhallinta ne, ko ina a tsaftace a kuma gyare da sassanyan qamshinta me wani irin sanyin da bai taba jin irinsa ba.

Kai tsaye ya wuce gadonta,ya haye abinda tare da jan duvet dinta ya kawoshi saman fuskarsa,yakuma dauki pillow dinta guda daya ya rungumeshi saman fuskarsa yana sansanar sassanyan qamshin hair mist dinta. Har cikin kwanyarsa ya zuqi qamshin da kyau sannan ya saki pillow din ya dawo qirjinsa. Sake bude dairy din yayi duk da ya gama karanceshi, idanunsa suka sauka saman page na goma layi na farko

"FAKE MEDICATION" ya karanta zuciyarsa na harbawa,yanayin fuskarsa ya canza ya rufe littafin a hankali tunaninsa yana komawa baya

"Ko shine dalilin da yasa taqi yarda da kulawar kowa akan fadeela? ko wannan ne dalilin da yasa ta dauki nauyin siya mata magani tare da bata maganin da kanta ba tare data bugaci kowa ya kusanceta ba?. Meye ya sanyata wannan tunanin? ,wannan matakan tsaron masu garfi haka

"Hasbiyallahu la'ilaha huwa alaihi tawakkaltu wa huwa rabbul arshil azim" ya fada yana nutsa yatsunsa cikin sumar kansa me santsi da laushi, sunan hajiya qarama kawai ke yawo cikin kwanyarsa,wani irin gumi ya yanko masa, ya sauko a hankali daga saman gadon, cikin jikinsa kawai yaji yana bugatar bibiyar footprint na CCTV cameran da bai samu bibiya ba a yau.

Saman qawataccen madaidaicin study table
dinsa ya zauna,ya fara bibiyar motsin komai na dukka guraren da ya sakawa CCTV camera din. Cikin mintunan da suke na qarshe,wadanda suka nuna masa awanni biyu da suka shude kenan yana gab da kammala kalla ya koma parlor din hajiya qaraman, inda yayi ajiyar CCTV camera din ba tare da saninta ba.

Fitowarta daga dakinta afujajan yaja
hankalinsa,yayi zooming na video din take komai ya bayyana,sak irin robar da me aikinta ta yar,tablet din da a ido suke kama da irin na fadeela,gama irgasu da ficewarta,sai yayi hanzari ya koma sashen CCTV din dake sashen su nadeeya din.

Yaga wucewarta falo ya duba ta dakin sãahar ba alamar motsinta,gabansa yana faduwa tare da ambatar

"'La'ilaha illa anta subhanaka inni kuntu minazzalimin" ya shiga bangaren dakin fadeela,cikin tsananin tashin hankali jikinsa nason rikicewa,saboda tuni zuciyarsa ta gama hasaso masa komai.

Ko ina na jikinsa ya dauki kyarma,ya saka tafin hannunsa guda daya yana lullube fuskarsa sanda hajiya garaman ta gama musayar qwayoyin tare da bin aikin nata da wadan nan kalaman. Gumi ne ya jiqashi sharkaf bakinsa yana rawa kamar wanda iskar qanqara ke kadawa

"Hajiya why?,why hajiya why!" Ya fada da mugun qarfi yana dukan table din har sai daya amsa kamar zai balle gida biyu

"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" yayita maimaitawa,hawaye suna sauka daga idanunsa zuwa fuskarsa. Duk da yana iya tuna wasu abubuwa kadan kadan da suka faru zamanin quruciyarsa, amma bai taba tunanin hajiyan zata iya aikatawa fadeela irin wannan mummunar ta'asar ba

"Me tayi miki?! me tayi miki?!, ni zaki yiwa haka!, ni zaki illata ba ita ba,she's innocent, batasan me duniyar ke ciki ba har yanzu!" Ya furta da qarfi kamar mahaukaci,ya kasa controlling kansa gaba daya,wani irin tashin hankali da matsanancin fushi yakeji sosai yana cin zuciyarsa

"Ya Allah, ya hayyu ya qayyumu,la takilni ila nafsy darfata ainin,aslih li sha'any kullahu ya Allah, astagfirullah wa'atubu ilaihi" harshensa ya samu ya kama wadan nan addu'o'in, yayita maimaita su babu adadi. A hankali nutsuwa ta fara saukar masa,saidai kuma hade take da wani irin mugun ciwon kai mara misali,bai shiryawa kwanciya ba sam amma tilas sai da gangar jikinsa takai ga gadonsa, idanunsa a runtse yana kiran sunan Allah kowanne sakan,yanason tuna wanne zunubi fadeelan ta aikata mata?, meye takeson cimmawa?, tabbas säahar ta hango abubuwa masu tarin yawa,abubuwan da yaci ace ya zauna sun tattauna komai zafin kanta da dojewarta, amma zuwa yanzun anzo gurin da bazai iya jurewa dawowarta ba.

Sosai ta dinga bitar kalamansa cikin kwanyarta.
Juyi kawai takeyi cikin duvet tana jinta so lonely,gadon yayi mata wani irin fadi,ba fadeela,wata zuciyar tace
BABU KUMA ABBYNTA ko?. Kamar zata qaryata amma sai ta kasa qaryatawar, saidai kuma tana mamakin ta saba da shine da har zataji kewarsa? bata da amsa face maida idanunta da tayi ta lumshe kawai.



Zafafa biyar
🔥🔥🔥🔥🔥🔥
🔥🔥🔥🔥🔥🔥
"HUGUMA*

_TABARMAR KASHI_*

Book 02Page 49


Washegari har qarfe sha biyu na rana bai fito ba,yana kwance yana jinyar jiki da zuciyarsa gaba daya.
He's ready to meet them ko ina ma suka tafi ba tare daya gayawa maji ba,don bayason ta hanashi ko ta rogesa don yasan bazai iya ba,wannan ya sakashi ba shiri ya nemi Dr anwar,ya iskeshi cikin yanayin matsanancin zazzafan zazzabi,wanda dole ya sanya aka daura masa drip a parlor dinsa.

Ranar sukayi da Jacob zai dawo, amma baikai ga isowa ba, sannan Dr anwar yace lallai yaci wani abu,dole ta sanya ya turama nadeeya gajeran tex,sai gata ta iso parlor din a gigice

"Yaa moha,dama baka da lafiya?,jiya ba lafiya ka kwanta ba? me ya sameka?"

"Relax, relax" ya fada cikin coolness da jigatacciyar muryarsa da abubuwa da yawa suka tarar mata, idanunsa akan fuskar nadeeya wani irin tausayinsu yana ratsashi,waye yasan yawan adadin cutarwar da ta yi musu ne ma?. Ita dinma kallon toufeeq din takeyi,tana mamakin wanne irin ciwo ne haka farat daya da ya sanya fuskarsa ta faada?.

"Ki samo min tea da wani abu lite zanci kafin ruwan ya aare"

"Okay yaaya" ta fadi tana juyawa da hanzari ta fita a sashen,ya rakata da ido har ya gama fita sannan ya maida idanun nasa ya kulle.

Shawaginta na biyu kenan cikin gidan, saidai sam sam bataga wulgawarta ba,hakanan bataga motsin fadeela ba koda wasa,duk kuwa da cewa yau din weekend ne,baka rasa zirga zirgar yarinyar a farfajiyar gidan wunin ranar gaba daya,musamman idan basu fita ba, sannan shi kansa toufeeq an shaida mata yana cikin gidan,amma tun daga wayewar gari zuwa yanzun ace bai nemeta ba?,duk da ta dade da lura abubuwa nata canzawa, tun daga ranar da yarinyar ta amsa sunan matarsa kawo yau,to amma kuma lokaci ta bawa kowa,jira take ta gama yiwa kowa shirinsa na daban.
Ko ubansa jarma da yayi tafiya ba tare da ya shaida mata inda yaje ba,da kuma adadin kwanakin da zaiyi kamar yadda ya saba shaida mata, tana sane da wannan, kuma ba zata taba bari hakan taci gaba da faruwa ba
Nadeeya na fitowa sukayi clashing da hajiya garama

"Ke,ke lafiya?" Hajiyan ta kira nadeeya da sauri,dan datakawa tayi

"Ba komai yaa toufeeq ne bashi da lafiya zan sama masa wani abu yaci kafin a gama qara masa ruwa" gaban hajiyan ya fadi, saboda a yanzun bata shirya wani abu ya samu toufeeq ba sam, shine hope dinta, shine kuma matakala sannan kuma tsananta na dukka plans dinta

"Me ya sameshi?" Ta tambayeta cikin damuwa, dan goge zufar goshinta tayi da tafin hannunta

"Ban sani ba mommy, kinsan sanin ainihin ciwon yaa moha ba abu bane me saugi tun asali"

"Na sani, jeki kawo masan" ta fadi tana wuce nadeeya zuwa sashen toufeeq din.

Sallamarta kadai yaji ya maida idanunsa ya rufe, ko da wasa baison gain fuskarta, domin har zuwa lokacin bai gama yanke matsaya akanta ba ganinta da idanunsa a wannan yanayin da yake ciki na iya tunzurashi, kuma. komal yana iva faruwa

"Muhammad" ta kirashi a hankali amma sai yayi banza da ita duk kuwa da hannuwansa suna motsawa kadan kadan. Sake kiran sunan nasa tayl a karo na biyu amma ya bawa banza ajiyarta,saukar muryarta cikin kunnensa dai dai yake da saukar tafasashen ruwan dalma.

"Ko ya samu bacci? na dawo anjima" ta fadi qasa qasa sai ta juva tana fita daga falon. Tun bata gama fita ba ya bude idanun nasa, yanajin kamar ya jawota yayi mata mugun dukan da sai ta gaya masa laifin da fadeela tayi mata a rayuwa,amma dole yayi aiki da hankalinsa a dukka hukuncin da zai yanke, saboda ya riga ya sani girman matsayinta wajen mahaifinsa, after all hausawa sukace idan baka iya kama barawo ba shi sai ya kamaka, saidai daga rana irin ta yau, koda fadeela tana gasar, to ba shakka ya haramta mata ganinta kwata kwata.

A gurguje nadeeya ta hada masa duk abinda zai bugata, tana fitowa falo zata wuce meenal ta shigo, ba wani sabo bane me yawa a tsakaninsu ba duk da cewa shekarunsu tazarar kadance ga kuma dangantakar dake tsakaninsu amma ko yaushe kamar bagin juna suke. Ita nadeeya mutum ce me faran faran da son jama'a ko kadan bata dauki duniyarta da fadi ba bata kuma dauki kanta ta aje can da nisa ba yayin da meenal take akasin haka tana da matugar fadin rai da jin kanta cewa ita din wata ce ta daban, gwanar girman kai da fadin rai, kamar zata wuce sai kuma tace

"Sister nadeeya baqo mukayi ne?" Sai da tayi gaba sannan ta amsa mata

"Yaa toufeeq zan kaiwa, bayajin dadi ne" ajiye komai tayi ta biyo bayanta da sauri, kwanaki kusan bakwai kenan tanason ganinsa amma kuma tana hagura saboda zazzafan warning din da ya aje mata kan shiga sashensa haka siddan ba tare da dalili me qarfi ba,a yau din kuwa ta samu dalili me qarfin.

Idanunsa da har yau basu gama dawowa dai dai ba va zubawa meenal,wani kwarjini nasa tare da zazzafan gaunarsa na sake hudata

"'Tsaya a nan" ya fada cikin tsawa, maganar tasa data sanyata jan burki ta tsaya din tana dubansa gabanta yana faduwa

"Daga yau sai yau, daga kuma rana irin ta yau, koda wasa, koda ganganci idan na sake gain gafarki a sassan nan sai na ballaki balluwar da bazaki moru ba kin gama tashi a aiki kenan har abada, bacemin a gun idiot!" Ga fada da tsawa me garfi wadda hatta nadeeya sai da hantar cikinta ya kada. Har takai qofa ta jiyo muryarsa yana cewa


"Ki hada dukka kayanki ki koma bangaren babarki, daga yau kar na sake ganinki a wannan sashen" kamar zata kifa haka ya garasa ficewa tana sakin kuka me sauti, bata ko damu da ma'aikatan gidan dake binta da kallo ba,har ta isa sashen hajiya qaraman ta sameta a parlor ta fadi a jikinta.

A rude ta dagota tana tambayarta

"Ke lafiya? me ya sameki haka?" Cikin sheshsheqar kuka ta gaya mata

"Banason qarya da sakarci, yanzun nan na shiga dubashi na sameshi yana bacci,sannan bugu da gari ma babu ta yadda za'a yi toufeeq ya gaya miki haka" masifa da fada sosai ta rufe hajiya garama dashi

"Haka kike gani ko? zan miki qarya ne?, komai nace yayi sai kinyi shakka, bayan a gaban idanunki yakeyin wasu abubuwan?, ina dukka tutiyarki da alfaharinki? ina abubuwan da kike alfahari da su? duk ni a wajena a banza suke tunda toufeeq kawai kin kasa mallakamin shi to wallahi wallahi nan da watanni biyu masu zuwa indai baki mallakamin muradin zuciya ta, kema ba zakiga abinda ranki yakeso ba" tsananin bacin rai ya sanya hajiya garama ware hannunta ta mari haseena, karo na farko da hakan ta faru tsayin rayuwarta

"Baki da hankali ni kike gayawa haka?" Dafe da kuncinta take duban hajiyan

"Ni kika mara momy?" Yadda tayi tambayar a tsaye tamkar hajiyarce diya ta mari mahaifiyarta haseena. kallon da take binta da shi ya sanyaya jikinta,sai a sannan ta tuna, mahaifinta sai da yayi mata bayani kafin va barta ta taho

"Ba'a bata mata rai,saboda tana da wani hali me kama da cutar tsananin fushi" da sauri ta kamo hannunta ta rige tana fadin

"Kiyi haquri, nayi miki alqawarin mallakar toufeeq a wata guda kacal, qasa da abinda kika buqata"

"Ashe zan take faranti kenan kowa ya rasa" muryar hajiya Muneera ta baqunci kunnensu, abinda ya sanya suka maida hankalinsu bakin qofa. Kaifin idanunsu bai hanata ci gaba da qarasowa falon ba, itama su take kalla

"Ashe da gaske ke din 'yar kunama ce fauziyya?,ni zaki yaudara kiyi wasa da tunani na? ki lasawa diyata zuma a baki yanzun kuma ki maye mata gurbinta da madaci?, tunda haka abun ya zama nafsi nafsi, kowa divan cikinsa ya sani to ki kwana da sanin muddin labiba bata samu toufeea ba haseena ma ta rasashi har abada" tana sauke furucin haseena na sauke mata lafiyayyen mari a fuska. Tsananin mamakin dava zarta zafin marin da shi hajiya Muneera ke kallon haseena baki bude

"Shashasha. ke har kin isa ki hanani samun muradin raina? ba mutum ba, ko mutuwa banajin tayi wannan isar"

"Kinyimin dai dai,ai da kin barta ma baki maretan ba" sai hajiya qarama ta matso gaban hajiya Muneera din tana mata wani kallo

"Bazance karki taka faranti ba,ki taka,amma ki takashi kina da sanin cewa idan zai bare zai bare ne harda aurenki da YAYA NA, zakiga mummunan sakamakon da baki taba tunanin aukuwarsa ba,karki manta inada qarfin sawa a auro a kuma saki a duk sanda naso hakan" Sai a sannan ta sauke hannuwanta daga kuncinta inda haseena ta mareta

"Bavan kuma va bare da aure na alagarki da yayanki shine abu na garshe da zai garasa zirarewa daga farantin,wannan marin da 'yarki tayimin ki rubuta ki ajiye,sai ya zame muku nadama da ba zaku iya kauce mata ba, fauziyya kada ki manta,ni dake kar tasan kar ne‚wanda ya fasa a tsakanina dake baya ya raina Allah"

"Da kyau!" Hajiya garama ta fada sai haiiya mansuran ta tsugunna ta dauki jakarta data fadi a gurin,ta kuma juya tana fita daga sashen cikin matsanancin baqinciki vau ace yarinya kamar haseena da aka haifa a gabanta?,yarinyar da ko autarta ya girmeta ita zata daga hannu ta sauke a fuskarta?.

Gaba daya hankalinsa bai kwanta ba har sai daya tabbatar ya sanya a nema masa visan Germany. Duka duka so yayi ace ya samu cikin sati guda kacal,amma aka shaida masa bazaiyiwu ba,short stay ma zata iya daukan sati biyu kafin ta samu

"It's too long ya rabbi* ya furta qasa qasa yana karanta bayaman da aka turo masan. Hakanan don babu yadda zaiyi yayi accepting a hakan ya sanyama ranshi salama da dangana, amma ji yakeyi ranar kamar ba zata zo ba, kamar ba zasu hadu ba.

A ranar bayan Dr anwar ya cire masa garin ruwan yayi booking na daki a bristol palace, suit din da ya saba kamawa ya kama na tsahon sati biyun, sabodia baya jin zai iya ci gaba da zama gida daya tare da hajiya garaman. Ya riga ya saita camera din da wayarsa, koda yana can zai iya ganin dukkan abinda yaso. Nadeeya batasan abinda yake faruwa ba kawai taji toufeeg din yace ta shirya kayanta kaman na 2weeks zasu bar gidan su sha iska, hakanan ya tura baba ramatu gurin abokiyar zaman mahaiffyar sajjad, gidan ya rage daga hajiya garama sai masu aiki.


*******Cikin nasara fadeela ta kammala kwanakin da suka diba mata kafin aikin, duka gwaje gwaje sun kammala,hakama shirin aikin nata,aka sanya mata rana da kuma lokaci.

Zuwan ba zata sajjad da afifa sukayi mata ana ya gobe za'a yi aikin,batasan cewa tana da rauni ba sai da taga bestie dinta,ashe dai tana bugatar wani a kusa,ta rige hannun afifa da kvau hawave nason sauko mata

"C'mon bestie meye haka? u are strong woman,kinyi abinda ba kowa ne zai iya ba, kici gaba da addu'a,it will be successful surgery in sha Allah".

A ranar babu wani wadataccen bacci da tayi,kamar ko yaushe ta kwana tana sallah tare da addu'a me tarin yawa.


***K'arfe takwas na safe afifa ta shigo musu da lafiyayyen breakfast da sajjad yayi musu order. A tsaye gaban madubi ta samu säahar cikin black laffaya me adon silver a jiki. Agogon hannunta silver color take daurawa, komai nata cikin sanyi take yinsa,saidai tayi wani irin mugun sassanyan kyau,kayan sun haskata sosai tare da gara mata wani irin kwarjini, Wayarta ta jawo ta sake duba sagon toufeeq na daren jiya,wasu irin sagonni yake aike mata masu taushi da narkar da zuciya cikin kwanakin saboda koda ya kirata bata dagawa,haka kawai takeii a ranta kamar tayi masa wani babban laifi da bazai gogu ba,ta dinga jin kamar ta shaida masa abinda sukeyi a Germany. Idanun afifa a kanta har ta garaso, dai dai sanda fa ajjiye wayar ta maida dubanta kan afifa

"Afifa, am afraid" a nutse ta tako ta dafa kafadarta tana murmushi

"Karki saare bestie,khairan in sha Allah" sai ta miqa hannu ta dauko cup na tea data hada mata da plate dindake dauke da tarkacen chips dasu ketchup

"Kici wani abu kafin mu fita" kai ta girgiza

"'Bazan iya ba bestie, tunda nazo garin nan sau daya
nake iya cin abinci" ido ta fiddo

"Saboda me?" Kafada ta dage

"Ban sani ba afifa, kawai inajin cushewar ciki ne,sannannayi loosing apatite gaba dayaa, bakina bashi da taste"

"Kuma a hakan sai a duka yawon shaqatawa
kikazo fatarki tayi wani mugun fresh da haske kamar
wadda ke wanka da madara" wani marayan murmushi tasaki tana kaiwa afifan duka

"Ke har yanzu baki girma ba wai?,ga baby kina shirin ajemana,mutumin da bai iya cin abinci yaushe zai samu

Please Login or Register in order to submit comment