Reading TABARMAR KASHI 1&2 complete by SAFIYYA HUGUMA Chapter 44 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

gamuwar idanunsu, kada taga yana kallonta ta rainashi.

Isowarsa gurin ya dawo da hankalin maji kansa,ta saki garamin murmushi lokacin da yake duqawa har qasa saman gafafunsa yana gaidata,abinda ya sanyawa guard dinsa saurin juyawa suka basu baya. Ido itama sãahar ta dauke tana jin wani abu yana ratsa zuciyarta,karon farko da bataji feeling na rashin burgeta ba tattare dashi.

Dabi'arsa guda daya da zata iya zanawa tace me kyau ce,daga kan maji har dr jarma ba zatace ga lokacin da taga ya gaidasu a tsaye ba. Fadeela ce ta matso tayl kissing kumatunsa dake da wani kwantacciyar qasumba me laushi wadda bata cika yawa ba,tana ta fitar d qamshin hair mist da kuma qyallin mayukan da tasha gyara dasu,sai ta zame ta tsugunna tana gaidashi kamar yadda taga ya yiwa maji,dama kusan tun bayan zuwan sãahar gidan ta dorata akan hakan

"Barka da asuba abby" ta fada da salon da sahar din keyin gaisuwa, murmushi ya saja yana dan jan kumatunta

"Barka da asuba abby, a ina kika canza yadda aje gaisuwa?" Tana dariya ta kalli sahar da sam tagi tsaida idanunta a sashen

"Aunty N ce, haka take gaida mutane" basarwa yayi kamar bashi ya tambayu fadeela ba. Hannunsa maii ta kama ta migar dashi, tasa daya hannun ta kamo hannun sãahar,rigota din da tayi shine ya sanyata waiwayowa tana duban maji din. Hade hannayen nasu tayi guri daya,lallausan tafin hannunsa ya sauka cikin nata tafin hannun me wani irin taushi da dumi. A take tsigar jikinsa ta zuba wani irin dumin hannun yana ratsa jikinsa da wani gudu kamar gudun jini a kowanne sashe na jiki.

Itama motsa hannun nata tayi saidai ba damar ta janye saboda maji ta lullube nata hannayen da nasu tana duban idanun kowannensu

"Na baki amanar d'ana da jilkata na baki amana" sai ta waiwaya ga toufeed

"Na baka amanar diyata, ka kula da ita ka kula da mutuncinta, ka tsare mata dukka
buqatunta,mutuncinta naka ne, amanar Allah ce a wajenka daga gurin iyayenta kamar yadda abbanka ya gaya maka". Dukkansu babu wanda baiji ta dora masa wani nauyi ba,ba wanda jikinsa baiyi sanyi ba a cikinsu. Karo na biyu hannuwansu suka sake gamuwa wajen qoqarin da kowa keyi tsakanin shi da ita na budewa maji qofar mota, sahar dince ta fara janye hannu kamar wadda wuta ta jata, tayi gefe da hannun tana yarfarwa,ya ganta amma sai yayi kamar bai ganta ba,saida maji ta shiga ya sakewa nadeeva gofar suka shiga ita da fadeela. Da hannu ya yiwa elyas magana, sai gashi ya matso da sauri ya bashi key din motar,ya shiga seat din driver duk sai sukaja baya,don haka yana nuna musu da kansa zai tuga mamarsa
kenan.

"Yayi wuri ki fara fita diyata,da sai nace kema ki shigo." maji ta fada tana murmushi, cikin alkunya sãahar tayi qasa da kanta taja baya tana daga musu hannu sanda motar ta fara fita a gidan.

Ana kammala rufe makeken gate din gidan ta juya cikin jin kewa,muryar daya daga cikin masu aikin gidan taji a bayanta

"Madam hajiya garama tana kira" da mamaki ta waiwayo tana kallonta,mamakin kiran da take mata na meye? batajin zata iya taka sassan matar bare ta saurareta,gaba daya babu wata daraja tata data rage mata yanzun a idanunta sai 'yar kadan, ita dinma ta dosaneta ne a dalilin martabar dr jarma

"Kice mata zan shigo" kawai iya abinda ta fadi kenan ta wuce sassan su fadeela tana juya kiran a ranta.

Gyaran dakin fadeela ta soma,wanda ya tsaye mata a
rai,tun lokacin takeson gyarawar, amma nauyin maii bazai
barta ta sake ta gyara din ba.

Ta kammala gyara komai tana goge dressing table na
fadeela tare da kwashe hoodie towels dinta na wanka taji
an buda gofar,a nutse ta waiwaya, idonta ya sauka kan
hajiya qarama,sai ta ajjiye dukka towels din dake
hannuta ta juyo tana goye hannunta a qirjinta tana
dubanta kamar vadda itama take kallon nata. Tunda take
bata taba jin qwarin gwiwa akan kowanne mutum ba
kamar yadda takeji yanzu akan hajiya qaraman ba,daga
sanda ta fahimei magungunan bogi take baiwa fadeela
taji tayi mata wata muguwar tsana,sai take mata kallon
kamar wata jini ko 'yaruwa ga adam, amma har yau tana
cike da mamakin dalilin da yasa take bawa fadeela
magungunan da ba likitanta bane ya rubutasu ba, meye a
cikin ranta? me vasa take yiwa yarinyar da take qaunarta
haka?,a zahiri kowa.yana yaba yadda fadeela ke
sonta kowa kuma vana yaba yadda itama take nuna
damuwarta da kulawarta akan yarinyar.
"Fada da aliani fa ba dadi......Ina kyautata zaton baki taba
sanin wacece ni ba ko?" Tsaf tayi karatun fuskarta na
wasu 'yan mintuna
"'Me sanin hakan zai amfana min?" Ta maida mata amsa
kai tsaye, a yanzun bata jin zata qyale duk wani wanda
baisan darajarta ya takata ba. Wani shu'umin murmushi

hajiya qarama ta saki
"Yaro baisan wuta ba sai ya taka,sanin ni wacece bazai miki dadi ba sam,abu daya zan zaya miki,ki samawa kanki lafiya da salama,ki watsar da dukka wata huduba da uwar mijinki tayi miki muddin kinason ki qarasa kwanakinki da suka rage miki a gidan nan lafiya lau" murmushi sãahar ta sakar mata ta juya tana ci gaba da aikinta,zatonta da zarginta akan matar yana sake qarfafa,dukka wani haushi nata dake tattare da adam tana jin a yanzu ta samu damar saukeshi akan hajiya qaraman ne,tayi imanin idan akwai banbanci tsakanin hajiya garama da adam to na jinsi ne kawai ,komai nata ya gama bayyana a idanunta,a yanzun tana jin zargi me garfi da rashin yarda da matar yana shigarta

"Duk wannan ba matsalata bace, matsalata daya kibar rayuwar fadeela ta samu salama,ki daina ci gaba da birkita kwanyar da take neman ta rayu da cikakken hankali da bawa gangar jikin data mallaketa kariya da ingatacciyar rayuwa" Wani mugun shock hajya qarama taji

"What!" Ta furta a rude tana duban fuskar säahar. Kallon tsakiyar idanu sãahar din tayi mata tana gyada mata kai

"Basai kince min eh kinayi ko a'ah ba haka bane, umarni

dava ne zan bayar, a matsayina na matar ubanta...wadda a yanzu take a mazaunin uwa a gareta,daga yau kula da lafiyarta da alhakin shan magungunanta yana wuyana,ban yarda ba ban lamunce kowa va sake baiwa fadeela magani ba, koda uban da ya haifeta ne!" Ta fada da kakkausar murya. Kamar ba zatayi respond ba saita saki murmushi tana duban saahar
"Kada ki qirqiri game din da bazaki iya kai qarshenta ba"

"Ba game nakeyi ba,ba kuma maganarta nakeyi ba, saboda ni din ba 'yar wasa bace, ina gaya miki magana ne ta zahiri" ta sake jaddadawa hajiya qaraman ba tare data dubeta ba bata kuma fasa aikin da takeyi ba

"Idan kina ganin abune me sauqi yin hakan ki gwada aikatawa" hajiya qarama ta fada tana juyawa ta fita a dakin,don dukka kalaman bakinta sun gama qarewa,abu daya ta sani ya zame mata dole ta fara gamawa da saahar. Sai a yanzu ta fuskanci ba qaramar barazana bace a gareta, ita din wata babbar barazana ce da zata iya wargaza shirinta na shekara da shekaru. Abinda ta yita gudu kenan,ta sake tsanantawa wajen gain toufeeq bai rabi kowacce mace ba sai d'iyarta MEENAL AJI.

Dogon tsaki säahar ta sauke bayan fitar hajiya qaraman, gefan kanta ya saara tadan dafeshi kadan,a duk sanda zata tuna abinda ya shafu rayuwarta a baya saita shiga yanayi,ashe har yanzu akwai ragowar

azzaluman mutane irin adam a duniya? bama cikin jinsin maza ba kawai harda wai mace?,macen da aka santa da rauni? waishin meye dalilin hajiya qarama ne?, me take shiryawa?.
"HUGUMA*


_TABARMAR KASHI_*

Book 02 page 19

Da gyar ta garasa gyaran dakin, zuwa lokacin kanta ya fara ciwo sosai saboda damuwoyin da take ta tunawa ta kowanne sashe wanne rayuwa fadeela zata fuskanta daga gurin hajiya garama lokacin da zata rayu babu wani a gefanta da zai zame mata garkuwa?, meye shirin hajiya garama ne? me dame ta sarqa a rayuwar wadan nan bayin Allah wanda basu da babanci da marayu?, tsananin tunanin da ya tsananta mata ciwon kenan. A nan dakin fadeela ta duqunqune ta kwanta tana fatan bayan wasu mintuna kan zai sauka. Bata wuce awa guda kwata kwata da dawowar ba taji muryarsu da alama sun dawo, ba jimawa kuwa sai gata ta iso tana kiran sunanta.
Daurewa tayi ta bude idanunta ta zauna sosai, garasowa tavi ta kama hannunta ta riqe

"Anty N gidan uncle sajjad zamuje ni da sister nadeeya,tace na gaya miki, tana cikin mota tana jirana abby ne yace kada mu batawa driver lokaci" murmushin garfin hali ta saki, tana tunawa yau kwanaki shida kenan amma sau daya tak sukayi waya da afifa, abinda bata taba kawowa ba akwai randa zasu dauki kwanaki basuyi waya da bestie dinta ba,saidai bawai hakan yana nufin ta qullaceta ko taji haushinta ba, ko kadan, uzuri kawai ta bata.

"Ki cewa bestie na ina godiya da kulawa,a gaidarmin da uncle sajjad" maimakon taga yarinyar ta mige ta tafi sai ta kama hannunta sosai tana kallonta

"Anty N. kaman baki da lafiya" kai ta girgiza

"Gajiya nayi sai kaina dake dan ciwo kadan" säahar din ta fada tana kallon tsakiyar idanun yarinya zuciyarta na karyewa,tare da mamakin meye tayi da za'a cutar da ita ne? ita ba kudi ko dukiya ba kaman dai ita,ita ba wata babba ba bare ace ta aikata wani abu,bata mallaki komai ba sai rayuwarta da numfashinta da soyayyar makusantanta, a ciki me ake nema?.

"Bari na gayawa sister nadeeya‚mu zauna dake" yarinyar ta fada a karye. Kai ta jinjina mata

"A'ah, karki gayawa kowa,inajin sauqi,kafin ku dawo na warke in sha Allah" saita sakar mata murmushi don bata qwarin gwiwa. Duk da haka yarinyar tana tafe tana waiwayenta har ta fice a dakin, abinda ya sake karya zuciyar säahar din kenan, ta koma ta kwanta tana lumshe idanunta zuciyarta a cunkushe.

Ajiyar zuciya ya sauke mai nauyi yana duban hajiya qarama dake sharar hawaye hadi da fyace majina bayan kukan data sharba, fuskarta na nuna zallar alhini da bacin rai. Har cikin ransa baiji dadin vadda take kuka tana gaya masa sãahar ta zageta ba tare da gaya mata bat iva kula da fadeela ba, daga yau kuma kada ta sake kusanto inda take, magungunanta da komai nata ta haramta mata tabawa saboda wai bata yarda da ita ba.
Iska ya furzar me dumi daga bakinsa

"I will talk to her,stop crying mommy" ya fada calmly. Kai ta girgiza

"Kada kaie ka tareta da zancan toufeeq taga kamar na hadaku rigima kuna zamanku lafiya " baice mata komai ba,ya dai fara takawa yana barin wajen.

Bayason kuka gaba daya,bare kukanma na babba,babban ma macen data rainesu har suka kawo haka. Amma kuma ta wani gefen zuciyarsa ta kasa nutsuwa da statement na abinda ya farun,haka kawai kuma yakejin zuciyar tasa ta gaza karba. Ba kasafai yake yanke hukunci kai tsaye ba ba tare daya ji ta bakin mutum ba,wannan ya sanya ya wuce sassansa kai tsaye.

A parlor ya samu Joseph yana sake tsaftace falon,duk da bawai yayi datti bane, a'ah wannan tsarinsa ne, ko yana nan ko baya nan,sharar safe data yammaci irin haka. Rusunawa yayi ya gaidashi, ya amsa sama sama ya wuce yana jiyo motsin jacob daga kitchen,shi kuma yaci gaba da aikinsa yana maida earpiece din kunnensa.

A nutse yake takawa cikin hallway din har ya isa bakin gofar dakin, hannu vasa ya murza handle din sannan ya tura qofar baya ya shiga a nutse. A kintse dakin yake,komai fes fes cikin wadatacciyar tsafta da kulawa,ba abinda ke tashi a dakin sai wani nau'in qamshi me sanyi d kwantar da zuciya. Tsaiwa yayi yana qarewa dakin kallo karon farko tunda aka shirya dakin cikin gidan, komai cikin favourite colours dinsa yake ya sauke hannunsa yana takawa zuwa ciki, duk kuwa da ya fuskanci ba kowa cikin dakin. Gefan gadonta ya qarasa ya zauna,haka kawai yaji weather din dakin tayi masa qwarai, ta kuma saukar masa da kasala,ya cire hannuwansa daga aljihun wandonsa da zummar dorawa saman gadon,sai yaji ya dora saman wani abu ne taushi da santsi. Waiwayawa yayi yana duban gurin. Panties dinta ne da braziers dukkansu farare gal gal kamar hannu bai taba tabasu ba. Janye hannun nasa yayi da sauri tsigar jikinsa tana zubawa,sai ya kauda kansa,idanun nasa suka sauka saman bedside drawer dinta. Hannunsa ya miqa ya dauki litattafan da suke kai na farko al-qur'ani ne ya maidashi ya ajjiye, na biyun littafin azkar dinta ne,ya buda ya karanta wasu daga cikin addu'o'in da suke ciki na wasu mintuna sannan suma ya mayar ya ajiyeshi,na ukun kuma MY DIARY shine abinda ke rubuce a fuskar littafin da manyan harufa da aka yiwa aloo da ruman azurta. Har ye maida ya ajiye ya mige sa ya koma ye sake dauka, ya bude shafin farko. Rubutu ne ekin tsari da daukan hankali kamar haka

-the worst feeling in the worid is knowing you've been used and lied to by someone you trusted, and the saddest thing about betrayal is that it never comes from your enemies_

Ya maimaita kalaman sun kusa sau biyar yana jin wani abu yena taba zuciyarsa yana jin kamar saboda shi akayi duke weden nan maganganun, akwai wani abu clin reyuwarta bayan wanda ya bincika ya saniyes... ya san da hakan duk da a wancan lokacin yace bashi da bugater ya sani din, amma a yanzun sai yaji yana da she'awar haken. Maida littafin yayi ya rufe, a maimakon ye maidashi wajensa sai ya fice dashi daga dakin gaba daya

Guri yayi masa a davinsa sannan ya juya ya fito, tunda bai ganta a sassansa ba ya tabbatar tana sahensu nadeeya. Zai iya cewa a kwanakin shida su biyu rak yaga gilmawarta a sashen kwata kwata,duk da cewa shima din ba wai zama yake a gidan ba, yanata qoqarin ganin ya fara hada kan ayyukan da zaiyi a company din dr, so yake yana cika wata guda yabar qasar dawowarsa kuma sai baaba ta gani, abu daya zai masa cikas,ya tabbatar Dr shine mutum na farko da zai fara masa maganar yana da iyali a yanzu, amma yasan yadda zai tafi da komai,yanason ya danyi nesa kadan ya samu zafin da kansa ya dauka ya sassauta.

Sanda taji anyi knocking migewa tavi ta zauna sosai duk da yadda kanta yake ciwo kamar zai cire ta dauka baaba ramatu ce, da muryarta da tayi sanyi qwarai tace

"Shigo" ya murda gofar ya turata ya sanya qafarsa. Ta lumsassun idanunta da kanta data jinginar a fuskar gadon taga shigowarsa, bata tsamamci ganinsa ba,ta miga hannunta a da hanzari ta jawo dankwalinta ta budeshi tana rufe gashinta. Kansa ya dauke kaman bai gani ba,ya qarasa shigowa ya jawo stool zuwa gaban gadon ya zauna sosai yana dubanta. Kwarjini taji yayi mata kamar yadda yake mata wasu lokuta,kanta ta juyar wani bangaren gasan rabta tana mamakin abinda ya shigo dashi. A nutse ya kafeta da kallonsa, mayun idanun nan nasa suka dinga ratsa jikinta suna bata alamun akwai kakkaifan idanu a kanta,batasan me yasa ba,duk sanda zai kalleta sama da second biyu sai taji kallon har cikin jininta,abinda kaf rayuwarta bata taba ji ba akan wani. Yadda baice komai ba haka itama,bataga amfanin zuwan da yayi ya sakata a gaba yake mata kallon daukan alhaki ba,wannan ya sanya ta yaye duvet din ta fara yunqurin saukowa daga saman gadon

"Koma ki zauna" ya fada still idanun suna kanta. Kamar ba zata koma din ba kamar yadda yace,sai kuma ta tuna

da gargadinsa, batason wani abu da zai kawo haduwar jikinsu waje daya ya sake faruwa,don haka ta dakata daga gogarin saukar da takeyi fuskarta na kallon gabanta,baya iya hangen fuskarta da kyau,sai gefen fuskarta dake dauke da kwantaccen gashi ta gefen kunnuwanta. Kansa yadan gyada kadan ya fuskanci gwanar taurin kai ce

"Kina da masaniyar matsayin hajiya a gurina?" Ya tambayeta adan kausashe, tun kafin ya gara komai a kai ta fahimci inda maganar tasa ta sanya gaba

"Ko na sani ko ban sani ba ba wanna bane ya kawo ni gidan nan ba,nazo ne don kula da fadeela, kuma na dauki alqawarin bata dukkan kariya da dukka iyawata,bazan taba barin wani abu ya cutar da ita ba alhali ina da ikon dakatar da shi, saboda haka na dakatar da ita daga bata magani don aiki nane". Fuskarsa ta dan sauya yana mamakin qarfin halinta

"Kika dakatar da wa?‚are you in your sense?" Zuwa lokacin kasancewarsa a gurin kawai matsi ne da takura a wajenta don haka ciwon kan nata zuwa lokacin kamar an ninka mata shi, har ya fara sauka zuwa idanunta kamar yadda yake mata a yawancin lokuta idan yazo da tsanani. Waiwayawa tayi ta dubeshi kai tsaye

"Yes, na fada na dakatar da ita, bama ita kadai ba kowa a gidan nan, ciki harda kai mahaifinta". Karon farko kuma lokaci na farko da garfin halinta tare da qarfin gwiwarta ya burgeshi yaso kuma bashi dariya har ya murmusa da wani kalar miskilancin murmushi wanda gefen bakinsa ne kawai ya motsa, saidai hakan ba qaramin qara masa kyau yayi ba. Gefe daya kuma yana karantar yanayinta da ya canza, tabbas akwai abinda yake damunta,yasan kuma ba zata taba fada ba,sannan muddin ya barta ta kwana a haka kota galabaita yayi imani daya daga cikin haqgoqinta kenan da ya gaza saukewa ne.

Ci gaba tayi da sauka daga gadon, tana ganin ta gama bashi amsa,no need ta tsaya wani dogon magana,gefe daya zuciyarta na sake cika da mamakin hajiya qarama,tare da jin cewa ta shiryawa tunkararta da dukka wani nau'in abu da zatazo dashi.

Sai daga gama sauka kaf yana kallonta ba tare da ya sake cewa komai ba yana sake nazartar garfin hali da kafiva irin nata. Sunkuya tayi da zummar gyara takalminta ta saka,sarawar da kanta yayi ya sanyata tallafeshi tana furta

"Wash" ba tare data tuna ma yana wajen ba. Sai a sannan ya mige a nutse, ya tako a hankali zuwa inda take,qamshinsa ya tabbatar mata da garin kusancinsa da inda take
*H U G U M A*

*_TABARMAR ƘASHI_*💔
Book 02
Page 20


Bude idanunta tayi a hankali ba tare da ta daga kanta ba,saboda tsaiwarsa a gabanta dava gefe ya bata damar ganin doguwar fara qal din qafarsa. Sake yunqurawa tayi da nufin tashi

"You can't do it,lemme help you" ya fada yana miqa mata hannunsa. Kau da kai tayi,ta yaya zata bashi hannunta?,gobe yayi mata sharri yace ta taba masa hannu?. Wannan abun ya sanya ta qarfafawa kanta gwiwa,ta yunqura a karo na biyu ta miqe gaba daya,saidai ko taku biyu bata yi ba duhu ya mamaye idanunta,wani irin jiri ya debeta yayi baya da ita zai zubar a wajen. He is ready akan kome zai faru already,saboda yanayinta ya gama nuna masa babu lallai ta iya barin dakin kamar yadda taso,tsabar dai taurin kaine da kafiya irin nata,don haka cikin zafin nama ya tallafota,yayi mata kyakkyawan masauki saman qirjinsa. Duk da yanayin da take ciki amma hakan bai hana hancinta zuqar ni'imtaccen qamshin dake fita tun daga ainihin skin da gargasar qirjinsa,vest zuwa rigar jikinsa ba. Wani irin abu taji wanda ya tilastata damqe gaban rigarsa da hannunta,ya lumshe idanunsa kadan yana sauke ajiyar zuciya saboda yadda dumin jikinta ya fara ratsa rigar jikinsa zuwa fatarsa yana ratsa jikinsa sosai

"stubborn girl" ya furta qasa qasa da wata irin murya me taushi. So take ta tureshi daga jikinta amma ta kasa saboda jirin da takeji,yasa hannunsa ya tallafeta sosai,sannan ya fara takawa da ita sannu a hankali suna fita a dakin.

Hankalinta a tashe yake,bata son kasancewarta cikin jikinsa,tana jinta ne kamar a kan qaya,batason wani ya gansu a haka,to amma yadda takejin garin yana juya mata tasan tayi qarya tace zata iya takawa da kanta. A hankali suke takawa,bugun zuciyarsa na sauyawa da wani irin bugu na daban,qamshin turarenta na shige masa hanci,kamar yadda qamshin hair mist dinta ke ratsa dan kwalinta yana fitowa zuwa qofofin hancinsa. Duk taku daya da zatayi sai tudun qirjinta ya gogeshi,idanunsa yake rufewa yana jin abun yana tabashi har tsakiyar kansa,hakan ya sanya jikinsa ya fara weakening,ya dinga kokawa da kansa ya sake aro jarumta ya yafa,sai ya dinga Allah Allah su isa ya zareta daga jikinsa. Dab da zasu shiga sassan nasa yaja ya tsaya saboda muryar Joseph da yake jiyowa,ya tuna ya barsh ne yana goge goge. A nutse ya juya gefan damansa yana kallonta,rigar atamfa ce a jikinta,duk da dinkin boubou ne amma hakan bai hana tudun qirjinta fita ba sosai,da alama tana daga cikin matan da suke da baiwar cikarsa da kuma tsaiwarsa,ganin sun tsaya sai ta danso janyewa baya kadan,ya dauka zata fadi ne,da hanzari ya zanya dukka hannayensa ya tallafota don kada ta fadi inda kai tsaye yayi mata masauki a karo na biyu cikin qirjinsa ya maida hannuwansa ya rufeta gam a tsakiyar faffadan qirjin nasa,jikkunansu suka mannu guri guda dumin jikinsu kuma ya sake gauraya yana ratsa jikinsu da kyau. A tare suka sauke ajiyar zuciya wadda ta fito duka lokaci daya,sãahar ta lumshe idanunta zuciyarta na quna ta yadda yau din ya samu damar hada jikinsa da nata,jikin da yake iqirarij batasan darajarsa ba. Tattara dukka hannuwanta tayi ta tureshi daga gareta,abun yazo masa a bazata don haka ta zamu nasarar raba kanta da shi,idanunta da suke adan jirkice ta dubeshi dasu

"Kada ka sake tabani,zan iya taimakon kaina" daga wannan ta fara takawa zuwa cikin gidan kai tsaye hannunta riqe da dankwalinta daya zame. Binta yayi da kallo cike da mamaki,wanne irin taurin kaine da ita?,tana tafe tana layi amma duk da haka bata fasa tafiya ba,normally yana da wani irin tausayi ga mara lafiya. Dab da zata shiga parlor din muryar Joseph ta qara tashi da alama suna hira ne shi da jacob cikin dariya da kakaci,sai a sannan ya tuna suna falon,kanta kuma babu dankwali,kuma a haka zata ratsa ta tsakaninsu ya tabbatar,wannan tunanin ya sanyashi daga qafa don ya risketa ya tsaidata,saidai tun kafin ya isa tuni ta shige abinta.

Sanda ta shigo din da kallo Joseph ya dan bita dashi,kallo daya yayi qas da kansa yana ci gaba da mopping din da yakeyi,lokacin da yake yunqurin dauke dubansa daga kanta dai dai lokacin toufeeq din ke shigowa. Cak ya tsaya yana zura hannuwansa a aljihun wandonsa tare da hadiye wani irin yawu. Haka kawai yaji ransa yayi mugun baci.

"Joseph" yayi kiran sunansa da wata murya me kaushi,cikin rawar jiki ya amsa ya kuma ajjiye mopping stick din ya qaraso da sauri ya zube a gabansa. Fada sosai ya shiga zubawa cikin bacin rai,ta inda yake shiga ba ta nan yake fita ba. Daga Joseph har jacob tsuru tsuru sukayi,don sautin fadan nasa ne ya fiddo Jacob daga kitchen shima,at last yace

"Get out from here,you All" ba wanda ya sake cewa komai sai ajjiye kayan aikinsu da sukayi suka jera suka fice,su duka suna mamakin abinda ya bata ransa,iya tsahon zamansu dashi bai taba musu fada irin haka ba.

Wayarsa ya fidda daga aljihu ransa a bace,ta yaya zata ratsa tsakanin masu aikinsa a haka?,tsabar taurin kai ne kawai da kafiya irin nata,kuma zaiyi maganin wannan taurin kan nata surely. Har ya fara kiran Dr anwar,sai ya katse ya koma kiran Dr raheema,bugu uku kacal ta daga

"Ki sameni gida yanzu" abinda ya fada kenan ya gintse kiran. A hankali ya koma saman hannun kujera ya zauna,har yanzu yana jin zuciyarsa na masa quna,ya daga hannunsa ya kalli tsadajjen agogon dake maqale a lafiyayyar fatarsa. Yana da schedules da yawa yau dinma,akwai baqin da yasa aka ajjiye a tahir guest palace amma cikin jikinsa yakejin kamar bazai samu zuwa ba. Kamar kuwa jibril yasan abinda yake saqawa sai ga shigowar kiransa,ya kalli wayar da kyawawan fararen qwayoyin idanunsa,sai ya daga wayar ya saka a kunnensa

"Sir,i think kamar ka manta,we have an important with the guest who is staying at the guest house,sunce morning flight zasu bi gobe,seven pm dot,They asked me to tell you, if you don't mind, the conversation should be over tonight" kai ya gyada

"Alright,kazo ka daukeni after one hour,banason rakiyar kowa"

"Yes sir" jibril ya amsa masa cikin girmamawa. Yana sauke wayar dr raheema na shigowa. Kai tsaye yayi mata nuni da hallway na dakunansu. Nauyi taji sosai,saboda bata taba yin nan gefan ba hasalima part din nasa yaune karon farko data fara shigowa,so sai abun yayi mata kwarjini

Please Login or Register in order to submit comment