Reading TABARMAR KASHI 1&2 complete by SAFIYYA HUGUMA Chapter 42 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sanda taga
sunan anty farheen,sai ta nutsu da kyau tana
amsa kiran tare da fatan jin lafiya?.

A galla akwa biyu suka kashe
suna maganata cikin wayar,sanda sukayi
sallama jikinta a sanyaye ta ajjiye wayar a
gefanta,tabbas wannan dai tasan agenda ce
afifa ta shirya mata,don dukka maganganun
da anty sukayi da anty farheen din sai tga
sunayi mata kama da mutumin da yasan
AUREN MAFAKA tayi.

Duban lokaci ta sakeyi bayan ta gaji da
zaman tunanun,ta shafa cikinta plate tummy
dinta da babu komai a ciki sai ruwan dumin
dazu rabonta data zauna taci cikakken abinci
har ta manta,tana ta kasa kunne taji motsin
fadde ko nadeeya amma shuru,sai ta mige da
mug din don maidashi kitchen ta hada coffee ta sha.

Sanye yake cikin gym wear na company track Smith dan gasar england,qaramin hannu ke da rigar daya tsaya a damtsensa ya kamashi tsam tare da fidda qirar jikinsa data jiqe da zufa har tana nunawa a jikin rigar,hakan ya sanya rigar ta sake manne masa,shafaffen cikinsa dake lullube da wasu muscles ya fita ta cikin rigar,dogo wando ne da kayan sai qafarsa dake sanye da wani irin takalmi dava dace da shigar tasa. Yadda fuskarsa da jikinsa suka hada zufa hakan ya bawa gashin kansa damar kwanciva sosai daga goshinsa zuwa qeyarsa,jikinsa sai fidda sassanyan qamshin turarensa yakeyi, yana rige da qaramin towel a hannunsa yana sake goge zufar hannunsa zuwa wuyansa. Kai tsaye ya doshi kitchen don yasha mutumin nasa wato coffee,duk da cewa tun wancan ranar bai sake samun dandanon da yayi dai dai da nata ba.

Kamar dai dazun jacob da ya kammala hada breakfast yana tsaftace gurin ta shigo. Batayi zaton ganinsa ba shi yasa a yanzun Vail ne kawai saman kanta wanda santsin gashinta duk da cewa a kitse yake yake haduwa da santsinsa yake zamewa daga kan nata lokaci lokaci

"No,ci gaba da aikinka" ta sake cewa wannan karon,sai yaci gaba da gyaran gurin,ita kuma ta matsa gaba kadan wajen coffee maker machine ta soma hadawa.

Yana zare safar hannunsa da yakanyi amfani da ita saboda daga qarfe yana sako gafarsa kitchen din,dukkansu sun bawa gofa baya ita tana nata aikin shima yana nasa. Daga inda yake tsayen yana iya hangen doguwar jelar kitsonta ta cikin mayafin nata wandda ta hadesu cikin wani siririn band,ya janye idanunsa a hankali ya dora kan jacob dake aikinsa,wani abu yana dan taba zuciyarsa

"Jacob" yayi kiransa with husky voice dinsa,sarai ta jishi,amma hakan bai sanya koda motsi tayi ba,sai Suger cubes da take qoqarin dauka ta jefa a hadin coffee din nata

"Sir" ya fada da sauri yana waiwayowa. Da ido kadai yayi masa nuni da ya fita,sai ya ajiiye cups din da yayi nufin shiryawa ma'adanar kwanukan kitchen din dake ajiye daura da saahar din.
Da ido yabi Jacob har ya kammala fita daga kitchen din,a nutse yaci gaba da takowa ciki yana ajjiye hand socks din nasa saman fridge.

Sanda ya iso ta gama hada komai,hannuwanta na harde a qirjinta ta zubawa na'urar idanu tana jiran ta gama tafasa mata shi ta juye abinta ta wuce ciki.

"Ke" taji ya furta da kakkaurar muryarsa dake cike da wani irin sauti me ratsa kunne da fusgar hankali sanda yake kunna tap din kitchen din ya tara hannayensa yana wankesu.

Bata motsa ba kwata kwata,tamkar babu kowa a wajen har zuwa sanda ya kammala wankewar yasa kitchen towel ya goge farare tas din hannun nasa da babu wata alamar
datti.

A nutse ya zube mata idanunsa,fuskarta sam bata a wajen,amma duk da haka yana iya ganin gefan fuskar tata dake da wani kwantaccen gashi da baya iya kitsuwa,wanda hakan yake masifar qara mata kyau. Sarai yasan fa jishi,wannan halin nata ne kuma abinda yafi tsana kaf rayuwarshi rainin hankali da halin ko in kula

"'Dake nake magana" ya fada a zafafe saidai cikin nutsuwa. Sai a sannan fa sauke hannuwanta ta kuma sanya nata idanun cikin nashi

"Baki iya gaida na gaba dake ba?" Yayi mata tambayar tana sake nutsa idanunsa cikin fararen qwayar idanunta. Second biyar ta dauke dubanta daga kansa,ta karanci izzar da girman kan nasa ne ya motsa da safen nan,bata kuma da ra'ayin kulashi saboda ba zaman da tazo suyi dashi ba kenan,a yanzun jira kawai takeyi gidan ya zama daga shi sai masu shi,bata tunanin ma zai sake ganinta a wanann sashen nasa,zata koma inda tafi wayo ne.

Batasan ya akayi ba,bata kuma san daga ina ba,tana tsaka da juye coffee din nata tajishi dab da ita tamkar zai take yatsunta kwatankwacin abinda ya taba yi mata a company. Wancan karon taji babu dadi qwarai da gaske,don haka a yanzun cikin hanzari taja da baya tana dubansa da razanannun idanunta da suke nuna yadda ta firgita,coffee din data fara juyewa yayi tangal tangal ta fantsama a gasa da jikin machine din.

Wani irin duba yake mata dake nuna fushi cikin idanunsa

"Ko naira biyar na biya a matsayin sadakinki tana da daraia da kima a wajena,saboda
halal dina ce gumina ce,sannan nasan zafin
nemanta.bazan bari a keta alfarmarta ba,don
munyi auren biyan bugatar kawunanmu
hakan ba yana nufin nidin sarakai bane,bazan
dauki rashin kunya ko tsiwa ba,koda zaman
dadiro mukeyi dake,daga yau ya zama dole
ki gaidani kamar yadda kowa cikin gidan nan
yakeyi,kamar yadda nima ya zama dole na
bawa duk wanda vake samana girmansa"
wasu hawaye ne suka fara taruwar mata cikin
idanu,shi kuma irin nashi salon kenan?,tun
daga ranar farko?. Kai ta girgiza,cikin jarumta
da dakiya ta ajjiye cup din hannunta a gefe

"Ai ba haka mukayi da kai ba mr jarma,ba
auren gaishe gaishe mukayi zamuyi da kai
ba,zan kula da fadeela,ni kuma zan rayu
independently" taku biyu ya qaro gaba ya sake
rage kusancin dake a tsakaninsu,sai a sannan
ma ta fuskanci ba dab da ita yake ba,akwai
sauran tazara a tsakaninsu,tsoratar da tayi
yasa taji kaman yayi kusa da ita

"Idan kina tunanin zan nemi wani abu daga gurinki ni ki cire wanann memory din daga kwanyarki ki qoneshi,har abada,saboda nidin tataccen dan iska ne da nake iya samun budurwa kowacce rana nayi disvirgin nata,kinga ko ke kinyimin kadan,abinda nakeso ki fahimta shine,har abada sama nake dake, you must give me a respect, koda ban saka kudina na biya sadakinki ba,ko kece ne kika biya sadakina mrs Khadija?" Ya jefa mata tambayar yana dubanta irin kallon kai tsaye,hannuwansa cikin aljihun wandonsa.

Idanunta dake walainiya da gyallin
hawaye ta daga ta dubeshi,yadda ya kirata kai tsaye da sunan da dukkansu suke sakayawa suke mutuntawa saboda sunan mahaifiya ce ga mahaifinsu ya bata ranta,taci gaba da tsirashi da ido haushinsa da tsanarsa tana kamata,duk yadda tace zata buda baki tayi magana ba shakka hawayen idanunta ne zasu balle,abinda kuma bataso ya sake gani daga gareta

"Maganata itace dai dai,ni dinne kenan na biya,so that's all i need from you ba wani abu can na daban ba" yayi maganar yana dage faffadan kafadunsa guda biyu,sannan ya zare hannunsa daga aljihun ya sake matsowa kadan gaban na'urar dafa coffee din,ya dauki mug din data fara juyewa a ciki ya juye dukka coffee din a nutse ya juya yana barin kitchen din,sai kuma ya tsaya cak ba tare da ya juyo ba

"Ki shirya nan da hour daya zamu shiga cikin gida,maji nason magana dake" sai ya sanya kai yana ci gaba da ficewar,can qasan ransa yana jin wani nishadi da dadin yadda yau ya samu coffee din daya jima yana mararin sha ba tare da ya zubar da kansa ya nema a dafa masa ba.

Wani baqinciki ne yazo mata iya
wuya,ga mari ga tsinka jaka? ta rasa me zatayi masa ta huce,sai kawai tace dashi

"Idan ka shamin coffe ban baka ba,gaisuwa
kuma ni ba auren gaisuwa mukayi da kai ba,so
kayi harkar gabanka kayi abinda ya dameka
nima nayi nawa,idan hakan bazaiyiwu ba ka
fadi nawa ka biya na maida maka abinka kowa
ya kama sabgarshi yaji da damuwarsa" ido
ya lumshe yana sipping coffee din, dadinsa
ya ratsashi,ya sake dakatawa daga tafiyar da
yakeyi ya hadiye sannan ya juyo

"Ki ragewa kanki rashin kunya da tsiwa,if
not kuma zakisha mamaki tare da wahala a
hannuna,zaki rayu ba tare da na shiga harkarki
ba,but dole ki bani respect, you get it?" Yayi
mata tambayar bawai don yana bugatar amsa
ba,sai yasa kansa ya fice.

Yana fita hawayen data riqe yana silmiyo
mata,tabi jikinta da yadan baci da coffee din da kallo sai kawai ta sake sakin hawayen nata
sosai,magoshinta ya cika da wani abu,anya
batayi kuskuren aurensa ba?,anya ba shirya
wannan abun yayi ba?,anya bawai ya shirya
aurenta bane bawai don fadeela kawai ba?,bai shirya hakan bane anya don ya gasata saboda ta samu kubcewa daga kamfaninsu?. Wannan tunanin ya sake daga mata hankali,amma kuma sannu sannu wata murya daga can gasan zuciyarta ke gaya mata

"Kema kina da taki damar karki wani damu da koma meye ya shirya" famfon ta kunna ta tara hannuwanta ta daurayesu ta kuma dauraye jikinta ta baro kitchen din, kamar zuciyarta zata fashe. Da yake zancan jacob ma ita ina ruwanta da wani kukunsa,bashi ya ajeshi ba?, shi yaga zai iya,amma itakam ba zata dauki wannan abubuwan ba sam,don ba wannan auren suka tsara zasuyi shi da ita ba.


*HUGUMA*

* TABARMAR KASHI_*

Book 02 Page 15

Kayan jikinta ta zare kaf ta shiga wanka,tanata qoqarin controlling kanta da fushin da yakeson taso mata a kansa,batason taje wajen maji fuskarta da wani yanayi maras dadi. Cikin miti hamsin ta kammala Shiryawa cikin wata qawatacciyar lallausar atamfar exclusive super me matugar kyau da tsari, dinkin tea boubou akayi mata wanda ya zauna mata a jiki qwarai da gaske, ya kuma fidda sigar kyau da dirin da Allah yayi mata,siririyar sarqar dake wuyanta ta gara fidda tsaho da hasken wuyanta. Medium chantilly vail ta yafa wanda ya dace qwarai da shigarta,ta wadata iikinta da turarukanta masu sanyin qamshi. Har tayi taku biyu gaba qafafunta sanye da wasu plate shoes na kamfanin saint Laurent sai ta dawo ta tsaya gaban mudubin tayi folding hannayenta a qirji,kenan yanzun tare dashi zasu jera zuwa cikin gidan?. Qaramin tsaki taja tana juya abun cikin ranta,ita sam ko hanya batason hadawa dashi,duka yadda ma ta lissafa abubuwan yadda zasu kasance sunata zuwar mata da sabanin hakan,totally ma bata taba kawowa zatayi koda rabin kwana bane a sassansa bare kwana guda cur,saidai ta riga ta tsarama kanta yadda komai zai tafi,bata yarda da wannar tsarin ba.

Duk da tare suke da jibril suna tattaunawa akan ayyukan da ya fara a Australia ya barosu ya taho nan,amma hankalinsa yana kan agogon hannunsa,lokaci lokaci sai ya daga ya duba,ransa yana sake baci. Ya tsani jira, kuma yana tsammanin ya sanar mata zasu shiga maji na son ganinta. Sam baiso ma main ta umarci ganinsu a tare ba,to amma yadda ya fuskanci maji na cikin murna matuga da auren nasa,bayason sam abinda zai tauye wannan farincikin nata.

Mintunan da ya diba mata suna cika ya miqe hannayensa zube a aljihun wandonsa yana yiwa jibril bayanin abinda zai tattara masa ya kuma tura masa duka bayanan ta email,sannan kai tsaye ya fice daga falon zuwa farfajiyar gidan yana takawa majestically kamar yadda ya saba.

Dab da zai isa ainihin sassan gidan nadeeya ta fito dauke da wasu trays. Har zata gota taji husky voice din nan nasa na kiranta. Da sauri kuma cikin murmushi ta sauya akalarta zuwa gareshi,idanunta a kan miskilar fuskar nan da kullum take a dinke tsaf,banda ita,kaf duniya batajin akwai wadda ke iya tunkararsa haka,sau da dama ita dinma yana mata kwarjini,wannan dalilin ne ya sanya ko yaya tayi masa wani laifi take shiga uku,iya idanunsa kadai sun isa sakaka a tara

"Good morning yaa moha"

"Morning" ya amsa mata a taqaice yana duban trays din
"Kayan dasu banaan sukayi breakfast ne na debo,kasan sun wuce"

"Ban tambaya ba.. ki wuce ki taho da
ita, kusameni a nan zamu shiga tare" ya fada cikin basarwar nan tasa. Dadi ne ya Kama nadeeya,dama tun dazun take jiran shigowarsu,don ta matsu taga aunty N din,fadeela kuwa baccin daya debeta da safen shi ya kawo sauqin rigimarta,maji ta hana kowa zuwako kai abinci ma tace a gyalesu tunda akwai cook a sassan. Cikin azama ta qwalawa daya daga cikin masu aikin gidan kira,ta qaraso ta jingina mata trays din tayi gaba

"Idan kuka dade ranki ne zai baci" ta jiyo muryarsa, saita gyada kai tana qara hanzari
kadan.

Muryar nadeeya da taji tana sallama bayan knocking din da take mata ya sanyata miqewa tana murmushi,ta isa bakin qofar ta bude.
Rungume juna kawai sukayi,fuskar nadeeya cike da fara'a kamar wadda ta shekara bata ga sãahar din ba

"Ina faddee na?"

"Tayi baccin gajiya,tun da safe tafarka tana rigimar zuwa gurinki,amma maji tace ba yanzu ba,babu wanda zai tasheku" murmushi säahar ta saki tana in nauyi da kunyar majin tun kafin ma su hadu

"Yaa moha ne yace muje nayi miki jangora,yana jiranki a bakin part dinmu" nadeeya ta fadi tana qarewa sãahar kallo.

Wani sassanyan kyau da tayi ita kanta yaja hankalinta ina ga yaayanta? tayi imanin nan kusa za'a yi barin wannan jan ajin da kamewar tasa tayi fata fata,fatanta dai daya lah ya kawo komai da sauqi,saboda ta sani shi din bai iya
Kama komai da sauqi ba.

Tare suka jera nadeeya din tana ta mata hira,kamar yadda suka saba a baya ba amsa sai murmushinta me sanyin nan da yake sake qawata fuskarta.

Tun daga nesa inda yake tsaye ya hangi tahowarsu bayan ya daga kai daga latsa wayarsa da yakeyi. A hankali ya zare idanunsa daga kansu ya mayar ga hadiman gidan,wanda kusan duka maza ne suna kai kawo kowa yana gudanar da nasa aikin.
Qwayar idanunsa ya juya kadan ya rufeta sannan ya bude a lokaci guda yana gogarin controlling kansa game da mayafin jikinta.
Cikin jininsa qin mayafin yake,tun daga lokacin da ya fara ganinsa jikin nadeeya ya hanata amfani dashi,bata kuma sake ba.
Iska yaja sosai yana fesarwa hadi da dauke kansa yana kallon gefansa,so yake ya lalubi zuciyarsa yayi kaya control,meye nashi na shiga sha'anin shigar da duk taga dana ta zabawa kanta? nadeeya qanwarsa ce,jininsa ce wannan kuma fa?.

"'Matarka ce" yaji ana bashi amsa daga can wasan zuciyarsa. Kai ua girgiza a hankali
•ya juya da kansa yana sake maidawa kansu sanda suke gab da qarasowa inda yake.

Sarqewa idanunsu sukayi cikin na
Juna, kallon second biyu rak suka yiwa juna kiwa ya janye idonsa yana jun haushin kansa, toufeeq kam kasa jurewa yayi sai da ya saki qaramin tsaki yana jin hausnin abinda ya sake maidashi ga kallon fuskarta da tayi wani haske,skin dinta data dauki gyara fiye da zato ta hadu da hasken ranar safiyar,ranar da bata kammala budewa ba saboda gajimare daketa haduwa yana alamta haduwar hadari, irin hadarin farko farkon damina.

Suna isowa nadeeya bata tsaya jiran komai ba ta zame ta wuce ta barsu a gurin.
Shuru ya ratsa gurin,kowa a cikinsu yana ji da kansa,yana jin kuma faduwa ce ya yiwa dan uwansa magana. Iska ya sake furzarwa yana son abinda ya tsaya masa a maqoshi ya wuce,kamar bazai motsa ba kafin daga bisani ya fara takawa a hankali zuwa ciki. Bayansa ta gallawa harara,ta motsa bakinta zata ia tsaki amma saita hadiye abunta saboda tunawa da tayi da abinda ya faru da ita company sanadin tsakin,ta murguda bakinta wai duk ko zata huce sannan ta bishi a baya tana gunaguni gasa gasa

"Girman kai,fadin rai,bagin rai duk mutum shi daya" ta furta can qasan zuciyarta ba tare data bari ya fito sarari ba.

Tun tana hararar bavan nasa har taji kamar idanunta na neman juyewa,a hankali ta janye idanunta,tana dan rufesu kadan sannan ta sake budesu,kai tsaye saman baqar sumarsa da a kullum take cikin gyara ta sauka,ta kwanta sosai da wani irin gyara daya dace da shigarsa ta wani creamy color din yadi na maza,mara nauyi wanda kana iya hangen vest din jikinsa ta zallar cotton fara qar gar da ita.
Yadda yake dauke gafarsa da saukewa kadai zai nuna maka yawan kuzari da baiwar lafiya da Allah ya bashi,wani irin taku me cakude da
'yar sassarfa kadan wadda take sanyawa yake danyi mata nisa,har sai tadan qara nata saurin kadan. Shi kansa takun gani takeyi kamar akwai izza da gasaita a cikinsa

"Aikin kawai" ta furta tare da jan tsaki. A wannan karon tsakin nata ya bayyana,sai taga ya rage adadin takun nasa da yakeyi.
Gabanta ya fadi,ta dora zara zaran yatsuntsa da suka sha lallae saman bakinta tana dan fidda idanunta waje,ba tare da ya waiwayo ba sai taga yaci gaba da tafiyarsa,ta sauke boyayyar ajiyar zuciya yaci gaba da bin bayansa tana kame kallonta daqa kansa,kada wani tsautsayin yasa ta sake wani abun da dukkansu shi da ita zasu raba hali gaban suruka.

Da sallama a bakinsa ya tura gofar dakin maii,ita da 'var uwarta wassila suka hada baki wajen amsawa. Fuskar maji din fal da murmushi,wani farinciki yana sauka a zuciyarta. Ganinsu kadai tare ya haifar mata da farinciki me tarin yawa,tana ii a jikinta sãahar din itace addu'ar data jima tana yiwa toufeeq wajen roqa masa ubangiji yayi masa musaya mafi alkhairi da zai wanke dukkan quncin da ya samu kansa a ciki

"Qaraso mana ibnaty" maii dake duban sãahar cikin kulawa da murmushi ta fada. Tsananin kunya ce ta dabaibayeta,ta tako a hankali ta qaraso gabanta,sannan ta zame saman gwiwoyinta tana fadin

"Barka da asuba" gogarin dagota maji keyi amma sãahar din ta kasa sakewa bari ta mige kamar yadda maji keda buqata,dole ta barta fuskarta da murmushi tana dubanta tace

"Barkanmu ibnaty,ya kwanan bagon waje?"

"Alhamdulillah" ta amsa da gyar tana wasa da yatsunta

"Allah yayi muku albarka,yasa albarka a tarayyarku" maji ta fadi. Kasa amsawa tayi,sai daga kanta da tayi a hankali tana gaida wassila wadda suke magana qasa qasa da toufeeq,bata kuma iya jin ainihin abinda suke fadi. Itama kamar maji din,tana da matuqar kirki,hakanan ta karanci kamar akwai kyakkyawar mu'amala tsakaninta da toufeeq.

Qasa qasa maji ke janta da hira,saidai sam ta kasa sakewa da ita,surukuta sosai takeji,a gefe guda wanzuwar sa a waien yasa take jinta gaba daya a takure,saboda basu saba zama a muhalli guda ita da shi ba har irin haka. Duk da ta gefen idanunta tana lura da yadda ya karkata hankalinsa ga wayarsa,abinda ta karanta kwata kwata babu sabo ko shaquwa me yawa tsakaninsa da mahaifliyarsa. Inda itace tayi missing maama haka,ta tabbatar zuwa yanzu tana magale da ita.

Cikin harshen larabci wassila tayi magana da maji sannan ta juya ta yiwa toufeeq shima magana,ta cewa da saahar cikin gurbatacciyar hausarta

"Zanje na dawo surukata" sai ta gyada kai caking jin nauyin sunan data kirata dashi. Zata fita baaba ramatu na shigowa, fuskarta itama yalwace da fara'a tayi musu barka da fitowa suka kuma gaisa

"Ki hado mana breakfast din duka tare dasu,a nan zamuci" maji ta bada umarni, cikin girmamawa baaba ramatu ta juya ta fice.

Ba jimawa ta shigo ita da masu taimaka mata dauke da manyan trays guda uku,ta ajjiye a gabansu ta juya ta fita. Wayar hannunta maii ta ajjiye bayan ta kashe,ta jawo dukka trays din tsakaninsu ta dubi sãahar

"Matso maza diyata,cin abinci tare da juna yana gara dangon gauna soyayya da kuma fahimtar juna.
..tafaddal moha" ta garasa fada
tana sauke idanunta akan fuskar toufeeq,cikin zuciyarta tana juya halayyarsa da har yanzun bata barshi ba,a gefe guda kuma tana sake yarda da hirarsu da nadeeya ta daren jiya.
Tabbas akwai aiki a gabanta,wanda kuma zata aiwatar dashi. Sãahar nada kyakkyawar zuciyar da bazataso ahalinta su rasata ba,zatayi dukkan me yiwuwa ta tabbatar ta riqeta cikin iyalinta.

Bata taba kawowa zai sauko din kamar yadda maji ta buqata ba,sai gashi ya ajiye wayar tasa,ya kuma zamo daga saman sofa din da yake zaune,ya balle links din rigarsa yana tattare hannun rigar tasa sama. Bugun zuciyarta ne taji yana qaruwa saboda kusancin da suka samu sosai dashi,ya zamana yana tsakiyarsu ita da maji,qamshinsa me wani irin taushi,irin gamshin nan dake tashi a hankali ya fara karakaina a wajen,yana cakuduwa da nata
qamshin.

Dukka su biyun suka kai hannu lokaci guda a tare saman fararen plate din da baaba ramatu ta hado dasu don fara zubawa maji abinci,ya damqi saman hannunta a tausashe yana tsammanin plate din zai dauka. Karon farko kenan da hakan ta fara faruwa a tsakaninsu,a tare kowannensu ya dauke nashi hannun,wani irin abu yaji ya tsarga yarrr a jikinsa,tun daga hannun nasa ya aika sagon kowanne sashe na jikinsa. Yayin da saahar taji kamar wutar lantarki ce ta jata,cikin rashin saninsu kowannensu sai ya shiga yarfar da hannu,maji dake karantarsu a fakaice tace

"'Zuba mana moha" sake maida hannunsa yay,,ya buda komai ya zubawa maji ya ajjiye a gabanta

"Wannan yayimin yawa,kuci kai da
matarka,samu plate ka zubamin kadan" ta fada idanunta akan wayarta kamar batasan ta fadi wani abu ba. Sam bai taba mata musu ba,don haka ya dauki wani plate din ya zuba matan ya ajjiye mata,ya sanya cokali biyu cikin plate din kamar yadda ta umarta,sai ta ajiye wayartata tana gyaran zaman glass din fuskarta,ta jawo nata plate din da cup din tea tana murmushi tace

"Toh.... bismillah ko?"

"Dangari" sãahar ta furta a ranta,maji ta gama daureta da dukka jijiyoyin jikinta,batasan ta inda zata fura buda baki tana cin abinci a gaban wannan dan rainin hankalin ba,tana jin ta bata wani babban aiki ne da batasan yadda zata alwatar da shi ba.

Idanunsa ya lumshe shima vana budesu duka lokaci guda,ya motsa bakinsa kamar zalyi magana,sai yaga idanun maji din a kansa,don haka ya cinye duk wani uzuri da yaso bata,ya gyara zamansa yana lanqwashe gafafunsa ya dauki spoon daya tare da fara motsa abincin,ya riga ya fahimci abinda majin keso,zai kuma amintar da ita. Yadda taga yayin itama hakan tayi,saidai a nata bangaren ko loma daya ta kasa kaiwa bakinta,abin yayi mata yawa tako ina,gefe daya ga maji da takejin nauyi matuqa,daya bangaren kuma ga uban 'yan girman kan nan da takejin yadda ya sanya mata ido sosai. A nutse yake juya lomar abincin a bakinsa,duk da cewa bawai wani yunwa yakeji ba,amma saboda ya faranta ran maji din yake cin abincin. Yadda ta takura din shi hakan yayi masa,yana karantarta tsaf ta gasan idanunshi,wanda ba lallai bane ka karanci hakan kai tsaye.

*HUGUMA*


* TABARMAR KASHI_*

Book 02 Page 16


Ko a fuska ba zaka taba zaton karantar tata yake ba,har zuwa lokacin da maji ta magantu

"'Ki saki ilkinki dani khadijatu,ina jinki ne tamkar moha da nadeeya,ke yanzun diyata ce halak malak,zan iya raba kowacce damuwa tawa da sirrina dake" garamin murmushi ta saki tana jinjina kai. Tabe baki yayi kadan yana matsawa gefe daga gaban kwanukan alamar ya qoshi,duk wadan nan abubuwan gani yakeyi kawai salo ne irin na mata wanda kaidinsu ba qarami bane,sai yanzu ya karanci dalilin da ya sanya dukkansu ta tafi da hankalinsu,cikin ransa yake gulmarta,ta wani sadda kai qasa,tamkar ba itace wannan mara kunyar ba me shegen tsiwa dake iya yarfa masa maganar da duk duniya ba macen data isa ta gaya masa bayan maji

"Ban baku kowacce gudunmawa ba ko?" Maji ta fada tana murmushi,a nutse toufeeq ya waiwaya ya dubeta

"Wacce iri maji?"

"Ta aurenku mana" kasa cewa komai yayi,don baisan wacce gudunmawa kuma maji keson bayarwa ba bayan dukka abinda tayi da uwar kudaden data kashe,tamkar zaiyi auren fari ne ko kuma auren autarta nadeeya takeyi. Wani envelope ta ciro ta ajjiye a tsakaninsu

"Maldives, turkey Malaysia,su sajjad ya zaba muku as Honey moon destination" bashi
daya ba,hatta da sãahar sai da taji gabanta
ya fadi,yayin da toufeeq din yaji abun gazo
masa a mugun ba zata,yayi imanin akwai
gudunmawar sajjad a zancan,tunda yafi
kowa sanin abinda ke gabansu,duka duka
da niyyar yij sati hudu kacal wato wata guda
yazo,amma gaddarar da baisan da faruwarta
ba ta rigeshi har yayi watanni biyu. Bayajin zai
iyayin wannan tafiyar da yarinyar,ya dauketa
duk inda suka shiga suna tare idanuwa a
kansu,dauriyarsa ta qare don haka a tausashe
.ya hada envelope din da hannun maji ya riqe
cikin nasa hannun

"Indai bakiyi booking ba sannan baki biya
kudaden ba ki zaremu a ciki please maji,na
tara ayyuka da yawa da suke jirana,inason na
idasu cikin watan nan" idanu ta sanya masa
sosai tana kallonsa tare da gasgata zarginta

"Moha,sabon aure fa kayi,akwai Cabinda
yakai iyalinka muhimmanci?" Kai ya girgiza a
tausashe

"Ba haka nake nufi ba maji,koma inane kikeso taje din zata je,amma a yimin uzuri na kammala ayyukan gaba na,zan biya da kudina na kaita ko ina ne ma indai yawo ne,amma kinga tun yanzun bai kamata nabar ayyukana na tafi ba" ran sãahar ya dan sosu,indai yawo ne wato gata shanshani wadda bata taba hawa jirgi ba.

"Shikenan,amma wannan tafiyar bata soku ba,koma wanne aiki ne ka kammalashi nan da watanni biyu kacal zaku tafin, daga nan inason ku sauka a Algeria"

"In sha Allah" ya fada yana lumshe idanu yana jin nutsuwa na saukar masa ta yadda yayi nasarar soke tafiyar ba tare da wani dogon turanci ba,yasan ya taki sa'a ne kawai,amma maji har yau tana nan a yadda ya santa tun yana da gananun shekaru.

A nutse ya bude fararen idanun

Please Login or Register in order to submit comment