Reading TABARMAR KASHI 1&2 complete by SAFIYYA HUGUMA Chapter 41 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

bata zaton akwai wanda ya isa ya sakashi yiwa bangaren irin wanna tsarin da kowa zaiyi burin kasancewarsa a ciki.

Bata fahimci cewa babu kowa a tare da ita ba sai bayan shudewar mintuna goma da sumaira ta shigo tana gaya mata yaa Saifullahi ya bada dokar kada wanda ya zauna. Hannun sumaira ta riqe da kyau,qwalla na sauko mata.
A irin wannan gigitaccen yanayin da take ciki inama acw afifanta tana kusa da ita? itace qwarin gwiwarta,saidai kuma inaaa,zagin soyayya ya sanya dukkan wani qarfi nasa ya nesantata da afifan,tana can itama domin fuskantar sabuwar rayuwa, rayuwar da säahar ke mata fatan ta zama me tsananin zaqi,ba me daci ba kamar yadda ta fuskanci tata.

Bude gofar da taji alamun anyi a
karo na biyu ya sanyata kasa kunne. A nutse take takowa zuwa cikin dakin, idanunta akan rufaffiyar fuskar sãahar,zuciya nata yi mata saqe saqen abubuwan da zata iya aiwatarwa a kanta,saidai duk abinda zuciyar ke gaya mata tana ganin bai dace da ya faru a wannan muhallin ba,a kuma dai dai wannan lokacin ba.

*HUGUMA*


*_TABARMAR KASHI_*

Book 02 Page 12

Gyaran murya ta danyi,idanunta akan
sãahar tana sake takowa kusa da da ita,daga
gefan lallausar sofa bed ta zauna tana
dubanta da kyau
"Maraba da shigowa mahmud JARMA
family,na tayaki murna qwarai bisa samun
wannan nasara da kikayi,sannan kuma ina
miki alhinin cewa....nasararki zata kasance
ta gajeran zango ce,sakamakon toufeeq ba mallakinki bane,dukka tsahon rainon
da nayi masa,na raineshi ne don ya zama
mallakina,wato mallakin 'vata meenal haseena"
wani dan banzan haushi maganar hajiya
qarama ta saukar a zuciyarta,tayi qoqarin
tsaida hawayenta tana son fahimtar abinda
matar take fadi, idanunta na kallon tafukan
hannayenta ba tare data yaye rufin kanta ba

"Na jinjina miki yadda kika shirya komai ya
kuma tabbata lokaci kadan bayan tafiyata,to
amma ki sani,sauyawarki daga sunan nanny
boyi boyi zuwa ga matar auren toufeeq
babu abinda zai canza daga dokoki da
tsare tsaren gidan nan,fatan da nake miki
ki iya kiyayewa,sannan ki jirayi sakamakon
da zai biyo baya nan da kwanaki bakwai
masu zuwa,batun jikata fadeela,banason
ki fiya zaqewa cikin lamuranta saboda
shine samun lafiyarki,kiji kigi ji ki gani kigi
gani,na barki lafiya,asha amarci lafiya" tana
kaiwa nan ta mige,saidai taku uku kacal
tayi sãahar da zuciyarta ke a dugunzume
ta gaza daurewa kalaman hajiya qaramar,ta
tunzura qwarai,itama irinsa ce kenan? me tarin
Izza taqama da izgili,ashe ga inda ya debo dabi'arsa,lallai akwai wani boyayyen abu cikin taku da rayuwar matar cikin gidan,jikinta da zuciyarta sun gama aminta da hakan,adam ya yiwa rayuwa ruhi zuciya da gangar jikinta mugun horon da yasa nan da nan take iya fahimtar wani abu daga wasu mutane da dama.

"Inda kinsan abinda ke qasan zuciyata da baki bata bakinki kina wannan b'ab'atun ba.don haka na roqeki ki kama girmanki,zan nanata miki tun a daren farko na cikin gidan nan saboda daga ke har shi ba zamanku nazo yi ba" zallar madarar mamaki ya saukar mata.wani abu yayi mata tsawa a kanta,ta waiwayo tana son tabbatar da abinda kunnuwanta suke jiye mata,sai sukayi idanu hudu da saahar data dage hular kanta,wanda hakan ya bawa kyakkyawar fuskarta data sake wani sassanyan kyau saboda gyara data ci kamar babu gobe,da kuma haske da annurin
AMARCI dake sauka a fuska da jikin kowacce diya mace data amsa wannan sunan. Kamar ko yaushe yanzun ma kwarjini tayi mata,amma hakan bai hana hajiya qarama ritsata da ido ba,tana mamakin qarfin halin yarinyar.

Tabbas dole ta shiga cikin mutanen da take
targeting,ta yiwa kanta wannan alqawarin,sai ta gyada kanta ta juya ta fice a hankali daga dakin.

Qaramin tsaki säahar ta sauke bataii
zata zauna matar ta sanya mata wata
damuwa,ita sam bata cikin damuwarta bare
tace zata takura mata,ba ita ba,koda shi kansa
toufeeg din ba zata yarda ya zamar mata
damuwa ba bare wata ganwar mahaifi data
fuskanci zuciyarta akwai ayar tambaya.

Ta jima zaune a gurin tana saga da
warwarar yadda zata tafi da rayuwarta cikin
gidan,zata bawa kowa girma,amma sam ba zata dauki raini cin zarafi ko cin fuska ba. A
yadda taji gidan ya fara shuru ya tabbatar
mata dare ya fara yi,sai ta dubi agogon
dake jikin bangon dakin nata,fitsari takeji
sosai hakanan ta tabbatar wadan nan kayan
jikin nata ba zasu barta sakewa ba,don haka
ta miqe ta zare rigar saman,tanar doguwar
rigar wadda ta fidda shape dinta qwarai da
gaske,tun daga girji zuwa qugunta,ta tattareta ta nufi qofar da take tunani bandaki ce da zummar idan ta fito tasan yadda zatayi ta raba kanta da rigar itama yadda zatafi jin dadin kwanciya.

Ya kusa mintuna talatin zaune
cikin motar tasa bayan fitowarsa daga gurin maji,a yau addu'o'in da yasha a bakinta zai iya cewa bai taba jin makamantasu ba daga bakinta.farincikin da ya gani kwance a fuskarta ya taba zuciyarsa,duk yadda yake zaton ta dauki auren ya wuce nan,ta mashi wani babban matsayi da yayi imanin ba nan kusa ta ajiyeshi ba. Motar na a kunne ac naci gaba da aikinta,hakanan fitilun cikin motar. Sanye yake da wani baqin yadi da aka yiwa dinki tamkar na buzaven qasar nijer,dinkin ya zauna matuqa da gaske a jikinsa, kamar yadda baqin yadda ya kwantawa farar fatarsa ya sake fidda ainihin haske da kyanta tare da bayyana zallar hutu da in dadi hadi da kulawar da take samu,bagar sumarsa ta ainihin halfcast na nannade saman kansa tana bada wani sheqi me kyau da sassanyan gamshi kamar ko yaushe.
Waiwayawa yayi a nutse ya kalli tarin ledojin alfarma dake gefansa,wanda duka maji ce ta bashi tace ya shiga gurin iyalinsa dashi,don shi babu abinda ya riqo a hannunsa,duk da yanajin sanda abokansu ke hadawa sajjad,sunyi la'akari da cewa shi din tsohon aure ne,sunsan zai tanadi abinda ya kamata ba sai an gaya masa ba. Su kansu kayan qarin nauyi ne a wajensa,don ya tabbatar tilas ya sadasu da wadda aka siya saboda ita kodon cika kima da martabar maji.
Sashen nasa ya sake saukewa

idanunsa a karo na barkatai,sam baya gaunar shiga sai don babu yadda zaiyi,a duk sanda ya tuna cewa akwai wata mace a ciki me amsa sunan matarsa duk sai yaji kamar dai an takureshi ne kawai. A karo na gaba da qarfi yaja tsakin hadi da balle murfin motar a zafafe ya fito,jibril dake jingine jikin motar ya qaraso da sauri,kafin yace komai toufeeq din ya rigashi magantuwa

"Ka gayawa Jacob ya shigomin da kayan cikin falo, ka kashe motar na sallameka,sai kuma da safe"

"Sir,da safe kuma? na dauka zakaje hutu ko?, ko don madam" jibril din ya fada zuciya daya yana murmushi,saidai kallon da toufeeq din yayi masa ya tabbatar ya tafka baranbarama,sai yayi saurin jan bakinsa ya tsuke yana yunqurin bude daya side din ya fiddo kayan kamar yadda ya umarta.

Hannayensa zube a aljihun wandonsa yake qarewa falon kallo,ya sake jan qaramin tsaki, komai nashi sajjad ya canza masa,duk da kyawun da sassan ya qara ya kuma zuna favourite colours dinsa,to amma shikam bai shiryawa dukka wadan nan abubuwan ba. Da kansa ya gaji da tsaiwa,ya sunkuya ya kwashe kayan da jacob ya shigo masa da su,ya nufi hallway din da zai sadashi da dakunan baccinsu,ransa yana sake baci,komai a yanzun sai yayi sharing da wani,gurin mallakinsa ne a baya,shi daya yake shiga yayi rayuwarsa,idan zao shekara bai fito ba motsin kowa bazai dameshi ba,amma a yanxun bashi da wannan tabbacin.

Tsaye tayi a gaban madubi bayan fitowarta daga toilet din tana kallon fuskarta data fito sosai saboda qananun kitson da aka zauna aka yarfawa gashinta me santsi,abinda zata iva cewa tsahon rayuwarta ba zatace ga lokacin da irin hakan ta faru ba,hasalima kwata kwata kitsonta baya wuce manyan kalba guda hudu,saboda tsaho da santsin gashinta, amma a yanzun an samu wata gwana jarababbiyar iya kama gashi ta kitse mata kan tsaf,kuma hakan ba qaramin qarawa fuskarta kyau yayi ba,jelolin kitson gaba daya sun kwanta sosai a gadon bayanta har tsakiyar bayan nata. Hannu ta sanya tana qogarin zuge zip din rigarta wanda afifa ce dama ta zuge matan,da qyar hannun nata yakai,ta fara jan zip din ya fara saukowa,har yakai rabi taji an taba qofar,saita tsaya cak tana kallon madubi dake haska mata bakin gofa,tanason tantance qofar dakin nata aka taba ko kuma sauran qofofin dake wajen.

A hankali qofar ta bude,ya bayyana daga bakin qofar da daurarriyar fuskar nan tasa,tashin farko qamshin da dakin ke fiddawa ya marabci hancinsa kafin a sannu idanunsa su suka a bayanta da fara qal don brassiere dinta ta bayyana. Sosai ta razana don batayi tunanin ganinsa ba wannan lokacin,tunawa tayi da zugaggen zip dinta data tabbatar a vadda ya sauka har brassiere dinta za'a iya gani,wanann tunanin ya sanyata juyawa da sauri kamar numfashinta zai dauke ba tare data tuna yadda rigar ta fidda tudun qirjinta ba da kyau.

Kamar daukewar majigin tv,gushewar baya zuwa bayyanar qirjinta ga idanunsa duka sun faru cikin abinda baiyi damanda second uku ba,bazaice ga yadda akay ba ya samu idanunsa dumu dumu suna kallon qirjin nata ba da suke a cike,farar fatar dake lullube ko ta ina ta jikinta ta bayyana daga samansu tana nuna mizanin cika da suke da ita. Wani mugun fusga ya yiwa numfashinsa da idanun nasa ma gaba daya yana sanya qarfin zuciya dana ruhi gurin janye kallonsa daga kanta. Yayin da sãahar din gaba daya ta qarasa rudewa,ta fisgi dankwalinta dake ajjiye saman madubin ta yafa ranta a bace.

Tamkar baiga komai ba ya sanya kansa cikin dakin yana furta sallama can qasa,kanshi tsaye yake takowa dakin tamkar dai mallakinsa bawai nata ba,bai tsaya ba har sai da ya isa kusa da bedside drawer ya zube dukka ledojin a kai ba tare da ya dauki ko daya ba,sannan ya juya abinsa zai fice daga dakin. Kasa jurewa tayi,tadan daga muryarta kadan

"Ba kowanne daki bane mallakinka a yanzu,kafin shiga kowanne daki a gidan nan ya zama dole ka nema izini" tsaiwar mashi maganar tayi masa bisa kansa,har ya rage saurin tafiyar tasa,sai kuma yaci gaba da ficewar,saboda wata kasala dake sauka a kowanne sashe na jikinsa,muddin kuma yace zai tsaya cewa wani abu,a matsayinta na me aure na biyu dole zata fuskanci wani sauyi tattare dashi, wanda hakan mugun abun kunya kasawa da kuma gazawace a tattare dashi but yayi alqawarin zai saita mata bakinta da wasu dabi'u nata,bazai yarda da rashin girmamawa ba,she can live duk yadda taso,amma dole tasan girmansa.

Tsuka tayi ta murguda bakinta saboda baqincikin da ya cikata,batasan tsautsayin da ya sanyata barin qofarta a bude ba,bata taba kawowa wai zai shigo ba wannan shine dalili,amma dole daga wannan karon ta tabbatar bai sake shiga mata daki ba. Har tayi banza da ledojin daya shigo dasu,sai kuma taga duk abinda ta bari ya lalace zai shiga sahu ne na almubazzaranci.

Short note din data gani jikin wata
leda ya bata tabbacin babu abinda ya siya da kansa ko daya,dukka sagon maji ne.
Murmushi ya subuce mata,tana qaunar mata sosai har cikin ranta,sonta majin take da gaske har hakan baya iya boyuwa,ta miqe ta adana komai ta dawo ta rage kayan jikinta ta kwanta.

"HUGUMA*


•_TABARMAR KASHI_*

Book 02Page 13

Cikin nutsuwarsa ya gama komai na shirin bacci,saidai gaba days baccin ya gagara zuwa a idanunsa,ganin dazun yayi affecting tunaninsa sosai,abinda bai taba kawowa cikin ransa zai zama wani abu har haka ba. Da kansa ya buda qofar dakinsa ya wuce kitchen ya hada coffee ba tare daya bi takan abincin dake jere a dining ba,aikin jacob kenan, baya wasa da aikinsa,duk wata hidima da ake muddin yana qasar yana kuma gari baya fashin dafa masa abinci,ko a yanzun duk hidimar da akeyi cikin gidan part dinsa baisan anayi ba,shi yasa yakeji da jacob din shi da wanda yake tsaftace masa sashensa.basu da wasa sam a aikinsu

Dakinsa ya dawo,ya buda balcony
din dake manne dashi,duk da cewar dare ne amma bai damu da hakan ba,bacci kawai yake nemawa idanunsa tare da hutu da nutsuwar
ruhi da gangar jiki.

Kurba daya yayi masa kamar lokutan
baya ya ajjiye saman dan qaramin table din dake a gefansa,tun daga waccan ranar daya dandani taste din coffe dinta kowanne ya daina masa dadi a harshensa,saidai yasha Black tea Kawaltunda bava snan madara kwata kwata,ko ya gwada shan madaran da nufin ko zai yi masa irin taste din milk tea dinta
sai yaji gaba daya basu hada hanya ba.

Tafin hannayensa ya hada yana murzawa
guri guda da sauri da sauri,lokaci guda ya dakata yana furzar da iska daga bakinsa,dai dai lokacin da wayarsa tayi qara. Mamakin wanda zai kirashi a dai dai wannan lokacin da sha daya na dare tayi ya kamashi,ya qarasa inda ya aje wayar a hankali ya dauka yana duba me kiran,sai kuma kiran ya katse,sagon da ya gani da number sajjad yaja hankalinsa,yayi sliding ya bude wayar ya shiga saqon

_Duk wani nutsuwa farinciki walwala da kwanciyar hankali yana tattare da diya mace muddin ka dace,ka raya darenka na yau da kyau da soyayya da kawo jituwa da fahimtar juna tsakaninka da iyalinka,zaka fahimci inda maganata ta dosa_ tsaki yaja,sajjad yana bashi ciwon kai,baisan mata bane,amma yana da tabbacin zai dawo daga mararin gardin da yake ganin ya samu. Muddin diya macace tabbas wataran sai ta bashi madacin da zai maye gurbin zaqin zumar data lasa masa a harshensa,duk kuwa da cewa baya taba yiwa wani wannan fatan bare sajjad din da dadi wuya ko tsananin yana tsaye tare dashi.

Kira ne ya shigo wayar tasa lokacin da kwanyarsa ke shirin nutsawa duniyar tunani.
A nutse ya dauki wayar ba tare da tantama shakka ko mamakin kiran da akayi masan a dai dai wannan lokacin ba,saboda waya ce da dukka kiran da zai biyo ta cikinta ya tabbatar kira ne me muhimmanci da ya shafi duk wani makusanci a gareshi.

Cikin lallausar muryarsa da ta gara yin wani irin sanyi saboda yanayin da yakeji yana bibiyar kowace gaba ta jikinsa. Saidai a maimakon amsar sallamar,sai sautin kukanta cikin siriryar muryartan me matugar siranta qwaral ta maye gurbi. Wayar yadan cira yana duba number din ya tabbatar babu wanda zai kirashi da number wannan qasar sai mutum daya wato HASEENA

"Yaa toufeeq wai da gaske ne?,da gaske ne don Allah?, kayi aure?" Tambayar tata ta daure masa kai,meye manufar wannan tambayar? duk da ya jima zuciyarsa da hasashensa suna son kaishi gurin,amma sai ya jaddadawa kansa ba hakan bane,saboda sam baya fatan yarinyar ta jefa kanta shingen da bazata iya samun aminci ba a cikinsa

"Yaa toufeeq,wallahi bazan iya jurewa ba,yaa toufeeq kai na yiwa zuciya tanadi,dukka tsahon shekarun nan,mommy ce takeyimin burki" sai ta sake sakin kukan da yake nuna ciwone daga zuciyarta na gasken gaske yake motsawa. Mamaki gaba daya ya sanyashi kasa cewa komai, yarinyar da yake kallonta bata da maraba da nadeeya a gurinsa saboda rainonsu da hajiya qaraman tayi? ‚bugu da qari sam babu hira da tayi kamanceceniya da wannan a tsakaninsa da ita

"Relax meenal,calm down" ya fada ta sigar lallashi,saboda gaba daya abun nata yana daukarsa ne kamar wani wasan kwaikwayo

"Ta yaya zan iya kwantar da hankalina yaa toufeeq,kasan yadda kake a zuciyata?"

"Are you okay?" Ya samu kansa da tambayarta kai tsaye wannan karon,saboda gaba daya mamaki ya gama cikashi

"I lost what i love most,i can't keep calm"

"Kisha magani ki kwanta,Allah ya sawwaqe" ya fadi yana sauke wayar a nutse daga kunnensa. Kafin ya kashe yana iya jin yadda take kiran sunansa,ya sake kallon wayar yana sake tabbatarwa kansa kodai akwai abinda tasha,ko kuma lallai dole ya dauki tsattsauran mataki a kanta,muddin dai meenal zata ce tana sonsa,to ba shakka raini ya fara shiga tsakaninsu kenan saboda yadda yake treating nata like nadeeya.

Qarar shigowar tex ya sake sanyashi
waiwayawa ga wayar. Dukka saqon ya gama bayyana saman screen din, kasancewarsa gajeran sago bame tsayi ba
BARKA DA WARHAKA ANGON NANA
KHADIJA,KA MOREWA WANNAN DAREN
TARE D AMARYARKA,AMMA KA SANI
AMEESHA NA NAN DAWOWA CIKIN
RAYUWARKA,SABODA BA ZATA IYA BARWA WATA KAI BA HAVE A NICE NIGHT_ Samun kansa yayi da maimaita karanta saqon,a hankali a hankali wani abu me zafi yana taba zuciyarsa, emotions dinsa marasa dadi sunason motsawa,how and when ameesha ta samu wannan courage din da zata masa saqo haka kai tsaye?,saboda ya daga mata qafa? ya bata damar taje ta rayu ta tuba?. Har ya dauki wayarsa da zummar nusar da ita kuskurenta,sai kalmar

"La haula wala quwwata illa billahil aliyyul azeem" ta subuce daga harshensa. A hankali yaji yana komawa daidai dinsa,sai ya maida akalarsa zuwa blocking number tata,sannan ya goge saqon,ya jefa wayar a aljihunsa yana migewa daga gurin,yana ji a zuciyarsa bashi da lokacinta Sam,bama yanzu ba,har abada baya jin zata sake samun lokacinsa,bawai ita kadai ba,dukka wata diya mace ma idan ka debe jininsa dinnan daya zama lazim ya rayu dasu,yake kuma da yaqinin babu cutarwa a tsakaninsu har abada.

Cikin wani yanayi yake fita dag balcony din har ya riski lafiyayyen bedroom din nasa,cikin qanqanin lokaci ya gama shirin kwanciya,ya maida hasken dakin zuwa dim light,idanunsa na lumshe yana jin kewar rashi ganin fadeela saboda cinkoson gidan,yau din tun sassafe da ya fita yabar musu gidan,duk da sashen nasa baisan me cikin gidan ke ciki ba,amma sai yakejin kamar hayaniyar gidan a tsakiyar kansa take. Bacci yake da bugatar yi sosai,to amma yanayin da yake ciki ya tabbatar idan baiyi wasa ba zaici wuya ko ya dade a haka,wannan ya sanya yana daga kwancen ya miqa hannunsa ya jawo wata mp4 me siffar qwallo fara qal ya kunnata,take sautin karatun alqur ani me girma ya karade dakin da muryar sheik mahir almu'aiqaly,karatun ya fara saukar masa da nutsuwa sosai a zuciya ruhi dama gangar jikinsa,sannu a hankali baccin da bai taba zata ba yayi awon gaba dashi.

_sai muce asuba ta gari angon nana kadija_

**********A nutse ta ajiye wayarta data gama karatun qur'ani ta ciki saboda rashin hado mata da qur'aninta da ba'a yiba ta mige tana kallon agogon dake manne a bangon dakin daidai algiblar sallarta. Qarfe shida da mintuna talatin,tana da buqatar ruwan dumin da ta saba sha a kowacce safiya,bata qaunar fita sam sam saboda batason koda tsautsayi yasa su hadu dashi,duk da bata tunanin a dai dai wannan lokacin akwai wanda ya farka cikin gidan. A nutse ta ninke abun sallar tayi masa guri,sannan ta zura lausasan slippers din da suke set da kayan jikinta,wanda couple prayer set ne,ta zari nata ta saka. Blur black ne masu taushi,kala ce ta farare, don haka ta fidda hasken fatarta da kyau wani irin haske dake cakude da amarci da kuma zallar gyaran da tasha daga hannun me gyaran jikin da maii ta ajjiye mata.

Duk yadda taso dauke idanunta daga kallon yadda aka tsara hallway din hakan ya gagareta. Wani irin kyakkyawan tsari aka yiwa gurin wanda hatta weather da qamshin da yanayin iskar dake kai kawo a gurin na musamman ne. Fitilunsa na musamman, kamar yadda kome da akayi amfani dashi wajen qawata gurin ya zama favourite colour dinta ne,zaka rantse da Allah ita ta zauna ta rubuta yadda takeson a shirya komai din. Qafafunta na nutsewa sosai cikin
Tallausan carfet din da aka malale gun dashi har zuwa sanda ta sada kanta da falon.
Hallway din yafi burgeta, amma kuma yadda falon ya tsaru da wasu irin kujeru curtains da carfet carfet sai ta rasa wanne guri ne yafi wani?,nan dinma komai dake dake cikinsa zabin kalolinta ne,kamar tana gurin aka shirya komai. Duk qoqarinta da son ganin abun sam bai burgeta ba hakan ya faskara,ta dinga ratsa falon tana laluben inda kitchen yake,lallausan qamshi me kwantar da zukata yana yawo a hancinta har zuwa zuciyarta. Bata jima ba ta hangi hanyar da zata sadata da falon wanda ke daura da waje na musamman da aka tanada aka kuma qawatashi da dining na alfarma.

Bata fahimci da mutum a ciki ba saboda girman kitchen din har sai data kammala shiga

"Good morning madam" jacob daketa aikin
kintsa kitchen din don shirya abinci na
musamman da zai burge matar ogansa ya fadi
a ladabce.

Turus ta danyi tana dubansa, ya afron
da zungureriyar hular kansa kadai ta isa yi
mata bayanin waye shi,saidai duk da hakan
baiyi qasa a gwiwa ba wajen gabatar mata da
kansa

"'Sunana Jacob,nine cook din sir,akwai wani
abu da kike bugata ne yanzu?" Mamaki ya
saukar mata,shi komai nasa ya banbanta dana
kowa?,ya kawo qatoton gardi kuma arne ya
ajjiye cikin gidansa yana dafa masa abinci
yana ci?, iyakacin zamanta a gidan ma bata
taba ganinsa ba,ko don ita din bata fiya zurfafa
kanta a lamuran da basu shafeta bane?. Ta
yaya zata zauna itakam wannan qaton yana
mata girki tana ci?.

"Bana buqatar komai, just warm water zan diba,and i can handle it" ta furta tana matsawa sashen da aka jere glass mug cikin tsafta da burgewa ta cire guda daya,ta taka a hankali ta isa ga dispenser ta debi ruwan. Saidai yayi mata zafi da yawa,batason kuma sirkashi, wannan ya sanya ta jingina bayanta da kitchen cabinet tana motsa ruwan a hankali,tana so ya rage zafi tasha tabar masa cup din a wajen.

Cikin kamewa tare da tarin nutsuwar
da sallar asuba ke haifarwa ga zuciya da ruhin kowanne musulmi yayi sallama a kitchen din. Wannan al'adarsa ce,yakan manta da cewa jacob ba musulmi bane,shima Jacob din tsabar sabo da hakan ya sanyashi ya koyi cikakkiyar amsa sallama.

Lallausar muryarsa da bacci yasa ta qara zama husky and deep voice ta ratsa kunnuwanta,idanunsa ya fara sauka a kanta,zagayayyar fuskarta dake tsakiyar hijabi tayi fayau da wani irin haske. Zare idanun nasa yayi daga kanta yaci gaba da takowa ciki a hankali, daura da ita ya tsaya shima yana daukar glass mug din ba tare daya sake duban sashen da take ba

"Good morning sir" jacob ya gaidashi cikin tsantsar girmama

"Morning Jacob"

"Kana bugatar wani abune sir?"

"Warm water" shima ya fadi a taqaice yana sake cirar spoon bayan mug din. Wani mugun kusa taji sunyi ita dashi, duk da kuwa akwai tazara a tsakaninsu,yadda ya ganta a jiya ke dawo mata fes cikin kanta,a hankali haushinsa ya soma sauka saman zuciyarta,tanason ta matsa daga gurin amma ta gaza,wani irin kwarjininsa da bata taba ji ba ya mamayeta. Ta lumshe ido tana kai cup din bakinta duk cikin son nuna bata ganshi a kitchen din ba gaba daya,gefe guda na zuciyarta yana mata bitar abinda afifa ta taba gaya mata

"Aure yana da wata irin daraja,yana garawa namiji kwarjini a idanun macen daya aura din albarkacin wanann igiyoyin guda uku, kibi a sannu bestie, toufeeq ba irin kalar mazan kike kalla bane ba irin adam bane,yadda banbaci da tazara yake a bayyane muraran tsakanin sama da qasa,haka yake tsakanin adamu da toufeed" a lokacin tsaki taja,akwai abinda take son saurara amma gaba daya afifa ta hanata sakat,motsi kadan ta fara mata wa'azin aure

"Kina tsammanin don kawai ya biya sadakina sai yayimin kwarjini afifa?"

"Bestie" bata barta ta gama magana ta dakatar da ita

"Bestie, idan akwai mutumin da ya cancani a duniva nayi masa kara na aureshi ma to mahmud ne,amma saboda har yanzun zucivata bataii akwai wani amintaccen namiji a duniya ba na gwammace na kawoshi,izzarsa dagawa da tsantsar jin kansa ba zasu taba razanani ba,zai kuma ci gaba da tabbata ne a mijin AUREN MANUFA, yayi rayuwarsa nima nayi irin rayuwar da nakeso" a lokacin murmushi afifa tayi ta miqe tana cewa

"Ba zaki gane ba"

"Ke kai ba zaki taba ganewa ba".

*HUGUMA*

* TABARMAR KASHI_*

Book 02 Page 14

Lokacin da yake amsar ruwan dumin daga hannun Jacob sai ta juya tana fita a kitchen din. Bai waiwaya ya dubeta ba,amma yana iya tsinkayar adadin takunta har zuwa sanda ta kammala fita. Zare cup din yayi daga bakinsa yana jin zuciyarsa na motsuwa da abinda tayi. Idan abaya shi din bai hada komai da ita ba,a yanzun musulunci ya danqa masa igiyoyi ukunta bayan an zarga mata su aka bashi ragamarta,ko ba komai a yanzun akwai suna me girma nashi a kanta wato MIJI, zai dauki kuwa wannan dabi'ar?,a gaban wadanda ke martabashi tare da ganin girmansa?.

"He deserve respect from her" ya gayawa kansa yana jin gamsuwa da hakan har qasan ransa.

Saman sofa bed ta yiwa kanta mazauni tana kurbar ruwan dumin nata a nutse,bangarori biyu na zuciyarta kowanne akwai sagon da yake qoqarin kai mata. Sashe guda na zuciyarta na gaya mata rashin dacewar abinda tayi na wuceshi ba tare data gaidashi ba,saboda hakan sam baya cikin tarbiyyar gidansu. Fuska ta yamutse tanason amintar da kanta rashin aibun abinda ta aikata din. Gefe guda na zuciyarta na hasaso mata yadda ya shigo da wanann murtukakkiyar miskilar fuskar tasa,tana iya tuna yadda yake takowa da jin izzar nan tasa,sannan kuma ya dauke kansa tamkar baisan tana a kitchen din ba.

Tsaki taja ta dire cup din abinta,bata jin tayi ba dai dai ba,don har abada ba zata dauki duk wani izza tasa da tsarinsa ba,don aure sukayi na yarjejeniya da biyan buqatar kowannensu,ba batun boos ko oga.
Kiran da ya shigo wayarta ya dauki
hankalinta,mamaki sosai ya cikata

Please Login or Register in order to submit comment