Reading TABARMAR KASHI 1&2 complete by SAFIYYA HUGUMA Chapter 39 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

zare rigar jikinta tana jin duniyar na juye mata cike da tashin hankali, tashin hankalin data jima bata afka cikinsa ba,tsahon shekaru batasan tashin hankali ba,saboda dukka abinda ta nema tana samu,zallar farinciki da wanzuwar kwanciyar hankali kadai ta sani,sai gashi yau yarinyar da suka dauka aiki a matsayin nanny tana neman ruguza duk wani lissafi nata data dauki shekara da shekaru tana yinsa. Inda ace tana da masaniyar abinda zai faru kenan,da kanta zata koreta kafin tabar gidan,amma inaa.…..sai gashi wani qatoton tsautsayi ya gifta wanda ba zata taba barinsa ya zama qaddara ba.
Dole ta qara gaba itama, haseena ce kadai tafi dacewa ta mallaki toufeeq din,yadda ta qarasa rainonsu har suka girma,lallai su sukafi cancanta suci amfaninsa.

Qara kadai wayarta tayi amma sai da gabanta ya fadi,bakinta yahau addu'ar Allah yasa ba haseena bace don batason tayi kiranta ta fuskanci akwai wani abu. Hajiya mansura ce,sai da taja tsaki sannan ta koma ta zauna,cikin ranta tana jin me yasa ma ta
¡awo matar nan ta maidata daya daga cikin ahalinta?,a shekarun nan gaba daya tsanarta takeji cikin ranta. Sai da wayar ta kus tsinkewa sannan ta daga. Akwai tashin hankali me yawa cikin muryar hajiya mansura sanda take magana da hajiya qarama

"Kinji abinda yake faruwa?"

"Naji,menene?"

"Baki tambayi halin da labiba take ciki ba,kin ganta can ta kulle kanta a daki,nayi mata maganar duniya taqi fitowa,ki taimaka don
Allah ki kirata kuyi magana ko hankalinta zai kwanta" yatsine fuska hajiya qarama tayi tana iin kamar ta rufeta da duka ta wayar

"'Mansura!" Ta kirayeta da tsurar sunanta,mamaki ya hanata amsawa,itama kuma bata jirayi ta amsa din ba ta dora da jawabinta

"Yanzu labiba ta fara kuka ai,don bata dace sam da toufeeq ba" mamaki ya kusa sanyawa hajiya mansura faduwa,sai data lalubi gurin zama

"Me kike fada ne?,ko kin canza daga alqawarin da kikayi mata?"

"Tun wacce shekarar?,ai daga lokacin da haseena tazo hutu tun tana da shekara sha takwas,ta nuna muradinta akan TOUFEEQ alaqawarin dake wuyan labiba ya sauka ya koma kan haseena,ko don kinga inata muku kara ke da ita?,ban fito kai tsaye na nuna mata bazata sameshi ba?" Ta qarashe maganar da tambaya,tambayar da rawar da bakin hajiya mansura yakeyi yasa ta gaza amsa mata

"Ai na dauka kuna da qwaqwalwar da zata gaya muku gaskiya,me muka hada daku da zamu dauki TOUFEEQ mu jingina shi da yarinyar da har yanzun ba'a da tabbacin ubanta ubanta ne!"

"Ke fauziyya dakata!,ya isheki haka!" Hajiya mansura ta fada cikin matsanancin bacin rai.
Shu'umin murmushi hajiya garama ta saki tana jinjina kai

"Uhmmm,ni kike dagawa murya ko mansura? ni ba? inajin kin manta cewa ba yau na fara fidda matan wana daga gidansu ba,wadda ma take da zuri'a damu na kadata ta koma qasarsu ballantana ke da babu abinda muka qaru dake sai gatoton kashi da kike ajjiyewa suckaway,ki iya bakinki idan ba haka ba nan gaba kadan zakiyi nadamar da zata zame miki har qarshen rayuwarki"

*HUGUMA*

*_TABARMAR KASHI_ *


Part 02 Page 8

gintse kiran hajiya qaraman tayi tana zake jan tsaki mai qarfi sosai,can gasan ranta tana in zafin tsawar da mansura tayi mata
"'Lallai duniya tayi lafiya" ta gayawa kanta da kanta,banda haka mansura ko kallon banza bata isa tayi mata ba bare tsawa har irin wannan. Qwafa taja tana dukan tafin hannunta da dayan hannun,ko a yanzun ta tabbatarwa kanta bashi mansurar taci,sai kuma ta biyashi da abu mafi zafi.

*_DR JARMA_*


Suna gama waya da fauziyya din ya ajiye wayar a gefansa yana binta da kallo,cikin shekarun nan yana samun kansa cikin nazarce nazarce,kamar ana yi masa bitar wasu kura kurai da ya tafka a shekarun raywarsa na baya. A yanzun bayajin zai sake tilastawa wani cikin 'yayansa yin wani abun daya zama ba bisa ra'ayi ko son zuciyarsu ba,hakan yasa duk yadda yaso ga kawo SÄAHAR cikin ahalinsa bai aikata hakan ba kai tsaye,saidai yayi wani abu da ya zama yayi pushing toufeeq din zuwa ga neman auren da kansa,ta yadda ko a gaba sunansa bazai fito cikin wanda yake ganin ya tilastashi ba,duk da yana jin alkhairai masu tarin yawa zasu fita daga gurinta tun saninta na farko da yayi a rayuwarsa kafin ma aje ga ganinta.

Wayar tasa ta sake qara a karo na biyu,ya waiwaya yana duban number da ake kiransa. Zumbur yayi yana sake zama sosai yana duban wayar,yakai hannunsa ya murza idanunsa cike da dumbin mamaki number wayar da ya mallaketa shekara guda kenan ya kuma gaza kiran mamallakiyar number, yau sai gashi number tana yawo saman screen dinsa a lokacin da bai taba zata ko kawowa ba. Haka kawai yaji ya gaza daga kiran,sai wani fat fat fat da girjinsa yakeyi,yau shi SHIFA ke kira? ,bayan tsahon was shekaru da suka shude da tarin galubale ZAQI DA MADACI?

Kamar wanda aka fuzga bayan tsinkewar kiran va sanya hannu hannun nasa yana rawa ya dauki wayar ta shiga bin kiran.

Shuru kaman ba za'a daga ba,yanata addu'a cikin ransa akan ta daga din,ya tabbatar bata da number dinsa ne kuma ko yanzu baya saka ran tayi saving kafin kiran nasa,yadda ta alqawarta masa a can bayan sai data tabbatar da halaccin haihuwarta,ta cika alqawarin,kamar yadda tace ta barshi har abada,amma akwai wata eana da zata waiwayi abinda ta haifa a cikinta. Ta barshi din,wanda kod wasa bata taba gwada nemansa ba,yaranta dai batayi fushi dasu ba ko ganqani,bata bari komai ya shafesu ba.

Tana dab da tsinkewa,kamar ba zaa daga ba sai kuma yaji an daga din,shuru ne ya biyo baya,abinda ya tilasta masa yin magana a wani yanayi dake nuni da kamar yana d'ari d'ari

"Assalamualaikum warahmatullah"

"Waalaikumus salam warahmatullah" ta maida masa amsa har sai da kowanne lungu na jikinsa ya amsa da muryarta,muryar da ya dauki shekaru masu tsaho ba tare da kunnuwansa sun jiye masa su ba,muryar da bazai taba mantawa da ita ba har abada

"Barka da wannan lokaci,na kira ke na shaida maka ni da ahalina zamu sauka a nigeria bikin d'ana kuma d'an uwa a garesu,zamu sauka cikin gidan d'ana in sha Allah,bawai ina gaya maka wannan labarin ba saboda neman izini

kamar yadda ake bugata,na shaida maka
ne saboda kayi magana da 'yaruwarka,ka
gaya mata jiya ba yau bace,sannan muna
da buqatar zaman lafiya ayi biki lafiya
a gama lafiya kowanne bago ya koma
muhallinsa,gargadine wannan daga gareni,ina
fatan zaka isar mata" iva abinda ta fada kenan
ta yanke wayar.

Sosai qirjinsa yayi masa nauyi,ya fara jan
numfashi tare da fesar dashi

"Shifa,har yanzu tana nan da halinta bata
canza ba,babu daukan raini ko qasqanci,babu
gudu babu ja da baya akan gaskiyarta,sai
yaushe abubuwa zasu canza tsakaninta da
FAUZIYYA?" wannan din dukka halave da
dabi'arta ne. Bata yarda ta sakarwa abokin
adawa wasa ba,muddin ita ke da gaskiya sai
taga abinda zai turewa buzu nadi. Bai wani
damu da maganganunta ba,abinda yake kai
kawo tsakanin ruhinsa da zuciyarsa ya shafe
wannan. Gaba daya jikinsa ya saki,ya rasa
shifa shekaru masu yawa,kuma har yanzu
qaryarsa ta sha qarya yace ya samu koda rabi rabin madadinta ne. Shin meye abinda yasa ya kasa haquri da ita a wancan karon ne?.
FAUZIYYA sunan da yazo kansa, zalunci suka aikatawa shifa da gudunmawarsa kenan?, tambayar da tasa kansa sarawa har sai da yasa hannu ya riqe goshinsa da kyau. Dai dai lokacin da hajiya mansura ta shigo falon afujajan,zuciyarta cike da tsoro da fargabar abinda fauziyya zata iya aikatawa,gwara tun yanzu tasan wanne tudu ta dafa.

Guri ya samu ta zauna ba tare da tayi aakari da sauyawarsa ba

"Yanzu fisabilillahi Dr labiba tana da uba kamarka amma har ta rasa toufeeq? yaron da take mutuwar so?" Idanunsa ya aza a kanta,ransa ya darsu da mamakin me yasa kowa sai toufeeq?, cikin daurewa da son sake kashe wannan wutar yace

"Bance ya auri kowacce ba kamar yadda ban hanashi auren kowa ba,kawai abinda na sani shidin mijin mace hudu ne,kuma kowacce mace yakeso an bashi damar aurenta" shuru tayi ta rasa abun fadi,ranta na sake zafafa da abinda hajiya qarama tayi mata

"Haka ne,amma gaskiya ka jawa qanwarka kunne,na fara gajiya da gadararta da rashin ganin girmana,waishin ni ba matar yayanta bace? matsayin yaya kuma uwa nake dashi a wajenta fa" ji yayi kamar tana son hautsina masa kai,sai kawai ya miqe yana cewa

"Kunfi kusa" ransa a mugun quntace, da alama sam bata lura da yanayinsa ba,sai ya tuna wan! lokaci can baya,ko tuntube yayi muddin yaji zafi sai shifa ta gane,ya tuna wani lokaci acan baya sanda zuciyarsa ta afu ga rabuwa da ita.
Kamar haka yana zaune saita iskoshi,tayita tambayarsa abinda yake damunsa,a tsawace yace mata

"Kinga dalla malama kada ki dameni" bata yi zuciya ba,hakanan bata qosa ba ta juya zuwa daki ta dauko masa magani,ta fuskanci akwai ciwon kai saboda yadda yake riqe da kansa,fauziyya dake zaune a gefe tana masa sannu a jere babu gaqgautawa,ta biya kitchen ta debo ruwa ta dawo ta zauna gabansa,fauziyya na daga gefe tana balla mata harara,amma ko sau daya bata bi ta kanta ba,ta balle maganin ta miqa masa hade da ruwan

"Ka sha zaka samu relief, zuwa anjima idan bai sauka ba,akwai ragowar canji cikin salary dina dana yiwa yaro siyayya saika karba kaie asibiti"

"Yaaya,kada ka karba,wallahi ban yarda da maganin nan ba,don dazu wata qawarta tazo kuma na ganta da qulle quile a leda,suna ganina suka boye" ta juya da mamaki tana kallon fauziyya,daidai lokacin shi kuma yasa hannu ya tankwabe ruwan da maganin data siya da kudinta. Kallo daya tayi masa ta miqe tana zazzage rigarta data jiqe,ta waiwaya ta kalli fauziyya

"Shima wannan ya shiga sahun abinda nake neman haqqi a kansa a gurin Allah" daga haka ta taka ta bar musu gurin.

Tunaninsa ya yanke sanda ya isa bedroom dinsa,sai ya zauna yana sake dafe kansa da kyau gami da kiran sunan Allah

"'La haula wala quwwata illa billah"

********Tuni sãahar taci gaba da harkokin gabanta,don bata dauki auren a bakin komai ba,bata kuma daukeshi wani abu me muhimmanci ba,sam kai ba zakace itama daya daga cikin amare bace. Komai afifa ta zabar musu sai tace da ita

"Yayi?"

"Yayi" kawai take cewa,wani lokacin ma kO daga kai ta kalli abun bata tsaiwa yi take amsa mata da yayin,saboda a nata ganin dukka wadan nan abubuwan bata lokaci ne kawai,meye na dukka wadan nan abubuwan akan auren da bashi da maraba da auren haya?

Yadda suketa shirye shirye gadan gadan shine ya fara dawo da ita cikin hayyacinta,ya kuma ja hankalinta,tun tana daukan abun da wasa har ta fuskanci da gaske fa ake. Kamar zaa aurar da wata shahararriyar budurwa?, hidimar da sam a aurenta na farko ma baa yita ba,sai gashi yanzun shi wannan auren yanata samun tagomashi. Abun ya fara taba ranta,har taji bata qaunar ma ayi mata zancan auren,saboda ita gaba daya a yadda ta dauki abun,zai kawo sadaki ne akwai a daura auren,ta tattara dan abinda take da ra'ayin dauka ta wuce gidan ta tare a dakin fadeela suci gaba da rayuwarsu kamar baya. Saidai abun yazo da akasin tunaninta,siyayya taga anata yi babu kama hannun yaro.

********Misalin qarfe hudu na yammacin ranarta qule a dakin tayi zamanta tana chart,tun bayan isowar charifa qanwar mahaifiyarta daga nijer gaba daya ta sake quntata a gidan,kullum akwai tsirfar da inna charifa zata tsiro da ita wai da sunan gyaran jiki,abun har ya fara cikata,yau dai tayi mata tawaye tace babu me bata mata jiki da wasu kwabe kwabe. Baki inna charifa ta sake tana kallon säahar din,ba wani shekaru ta bata masu yawa ba,duka duka bazai wuce shekara bivar ko shida ba

"Wai nikam wannan auren na soyayya ne kuwa? ina cewa afifa ita ke tayani ma hada kayan,kafin na gama kintsawa ita ta shirya"

"ita tanaso inna charifa kiyi mata,ni ki barni hakanan,ban buqatar komai"ta fada tana murie dilka din data fara murza mata a hannu,sannan ta fice a dakin.

Ko yanzun da take zaune a dakin sai takejin zuciyarta na mata wani quna,wannan abun da aketayi ita bashi takeso ba,bashi da faida ma sam a gurinta, tamkar ana shelantawa duniya ne,abinda ita a ganinta bai zama dole ba.

Turo gofar dakin akayi,kuma koda bata daga kanta ba tasan afifa ce,saboda wani irin gamshi da inna charifa ke jigasu dashi ita da afifan. Duk da taqi bataso, taqi kuma bada hadin kai,amma tana gaunar qamshin sosai,yana mata dadi qwarai. Saman kanta afifan ta tsaya itama tana basarwa

"Ummu chamsiyya tace na gaya miki,ki hada kayanki yau,gobe za'a fita dasu tare da kayan kafi gaba daya" a wani matuqar qufule ta daga kai daga wayar da take dannawa ta kalleta

"Ya isheki haka afifa,ke idan kina rawar kanki a kan saiiad ki daina sakowa da säahar,kaya na a nan za'a barmin su,ba inda zani dasu"

"Hehehe… ...ke kikace kinaso,da bakice kinaso ba da ba'a baki shi ba" afifa ta fadi harda tafa hannaye. Al'amarin daya sake qular da sãahar kenan,sai ga idanu da muryarta dukka sun dauki rawa,afifan sam bata kulata,duk wasu tambotsai da takeyi bata taba biye mata,saidai ma ta manna mata hauka kamar yadda tayi mata a yanzu. Bata da zabi illa ta barwa hawayen damar zuba,zuwa yanzu ji takeyi kamar tace ta fasa auren,to amma tasan qaryarta tasha qarya,babu me kallonta ma bare ya saurareta,kuma ma idan tace ta fasa....wani dole za'a sanyata aura,wanda zata zauna garqashinsa ta zama cikakkiyar mata a gareshi,gara wannan,da an gama wadan nan filile fililen dole kowa ya sama mata lafiya, uwa uba ma kuma bawai binta gidan za'a yi ba bare aga yaya zatay zaman auren.

Ranar wuni tayi a daki,don inna
charifa tayi rantsuwa indai ta ganta a waje ba abinda zai hanata danneta ta shafeta da kayan gyaran,tasan tsaf zata aikata,don ita din cikakkiyar buzuwa ce wadda ke tafe da tsananta da qiba,tasan kuwa muddin ta tausheta a kalankasin jikin nan nata ko motsi cikakke ba zata iya ba bare ta qwaci kanta.
Koda inna charifa bata fadi haka ba dama yau din bata da niyyar motsawa ko ina,hatta da wayarta a silent ta barta,tana daga kwance saman gadon da yake tana fashin sallah,duk wani motsi da kai kawo dake faruwa daga falonsu zuwa farfajiyar gidan tana jinta. Gidan kwanakin nan da bikin ya matso ya fara rayuwa da shige da ficen jama'a.

Taji shigowar anty farheen ma amma sai ta qudundune a duvet,don ita kanta anty farheen din nemanta take yau kusan sati amma taqi zuwa,tasan muddin taje fiye da rabin zancanta na auren ne,auren da daga ita har wanda zai biya sadakin nata basu saka a ka ba,amma su anty farheen din duk sunbi sun addabi kansu,wai lallai sai sun gyarata,bayan abubuwan data dinga yi mata sati dayan da sukayi a Dubai, wanda sai da tayi da na sanin binta ma saboda dirke dirke da abubuwan data bata ta tilastata amfani dasu. Acewarta irin gyaran da za'a yiwa afifa ita ba irinsa za'a yi mata ba,amma dai tanason tsakanin afifa da ita a kasa banbancewa acan cikin turaka.
Randa ta fadi wannan maganar yini sãahar din tayi batayi magana da kowa ba,idan ta tuno maganar sai taji kamar ta dora hannu aka ta kurma ihu. Wai da waye zata hada gado ma?,da toufeeq?,wannan mutumin da ko sunansa bata qaunar ji? tanata qoqarin danne action dinta akan auren don kada duniya ta fahimci AUREN MANUFA ne,to amma yadda suke nan nan da bikin idan ba'a yi wasa ba zata kai inda zata gaza ci gaba da boyewar.

Sake turo gofar dakin akayi,aka dan tsaya kadan a kanta na was mintuna kafin daga bisani ta magantu

"Maji nata kiranki amma tace no answer"

"Maji”?Ta maimaita sunan cikin ranta,a guri daya tasan me wannan sunan,kakar fadeela,ta kuma san afifa bawai sanin maji din tayi ba.

Mamakinta ya gaza bayyanuwa,ta yaye duvet din tana kallon afifa daie tsaye tanata gyalli hadi da baza qamshi

"Wacce maji din?"

"Uwar mijinki" ta fada gatsal kai tsaye. Duk duniya afifa ce kadai zata yi mata haka ta ayaleta,sai taja siririn tsaki ta ja duvet din da nufin komawa ciki, dai dai lokacin kira ha shigo wayar afifa dake hannunta
"'Yauwa gashi ta sake kira" afifan ta fada tana matso da wayar kusa da sãahar din.

Koda ta tsani toufeeq tana qaunar fadeela,hakanan tanason maji tana kuma qaunar nadeeya. Mutanene masu wani irin karamci tare da maida dan kowa nasu,suna da wani irin saugin kai tamkar ba daga jininsu toufeeq ya fito ba,ba maji ba,duk wata dake da shekaru irin nata ma ba zata iya wofantar da ita ba,do ta samu cikakkiyar tarbiyyar wannan daga gida,tilas ta miqe ta zauna sosai,ta miga hannu tana amsar wayar tare da jefawa afifa harara sannan ta daga kiran tana
karawa a kunnenta,dai dai sanda afifa ta watsa
hannunta alamun ko a jikinta ta fita tabar mata dakin.

*HUGUMA*


* TABARMAR KASHI_*


Book 02 Page 09

Muryar maji dake dauke da wani allausan sauti me cike da nutsuwa ce ta mamayi kunnenta. Wata nutsuwa ta saukar mata wadda ta sanyata amsa sallamar cikin tsari.

"Ina fatan binty bakiyi fushi da ni ba,inataso na kirayeki amma ban samu damar hakan ba‚nadeeya kamar rowar rak'am(number) dinki takeyi" murmushi säahar ta saki me cike da kunya,ai ita ya dace ace ta nema maji din,don rashin kyautawa tunda tabar gidan bata sake nemanta ba

"'Masa'al khair" säahar ta gaidata

"Masa'an nur ibnaty kina lafiya ko?,ya iyayi ki?"

"Bikhair walhamdulillah"

"Ma sha Allah, ya kuma shire shiryen aure? muna hanya cikin satin nan in sha
Allah" nauyinta ta sake ji ya kamata,saita kasa magana

"Ina fatan za'a yi haquri da halin moha,ya taso me wani irin zafi da rashin son raininaso qwarai na saisaita wannan dabi ar tasa,saidai ban rayu dashi ba,ya sake zuwa kuma bayan ya girma Allah ya jarabceshi da wata irin jarabawa data sanya dabi'unsa suka sake zafafa,ina rogon alfarma ayi haquri da shi,a kuma yi qogari a saita min shi, kyawawan dabi'u da na san dasu na haifeshi su dawo gangar jikinsa suyi tsiro, zuciyarsa ta zama irin ta kowa"

"In sha Allah" kawai ta fada,don batasan fadin kowacce kalma da zata nuna ta dauki alaqawarin,saidai daga qasan zuciyarta tana mamaki,dama shi din bai rayu da maji ba”?

"Inason diyata tafi kowacce amarya kyau a duniya,don wannan shine karon farko da za'a aurar da moha a gaban idanuna,akwai me gyaran amare da zata iso nan da jibi daga nan gasar tare da 'yar uwata,ina fatan diyata zata bada hadin kai?" Sosai abun ya yiwa sãahar girma,suma da gaske suka dauki bikin?,sun dauka auren gaske ne kenan?,ba yadda ta iya ta amsa a sanyaye da

"To,mafi mishkila,jazakillah bi khair"

"Nice da godiya da shigowa rayuwarmu da kika yarda zakiyi" maji ta amsa mata cikin qauna da kulawa,har cikin jininta takejin qauna da soyayyar sãaharita din ma'abociyar sallar dare ce,a duk sanda ta roqawa rayuwar toufeeq da nadeeya abokan rayuwa na gari sai taii sãahar ta sake kwantawa qwarai a ranta,tana ta qoqarin ganin yadda zata qulia al amarin tana daga can,sai gashi cikin hikimar
Allah komai yazo cikin sauki darajar istikhara din data dinga yi tana neman zabin Allah.

Ganin kamar saahar din tana kunyarta ya sanya tayi mata sallama,tare da gaya mata tayi serving number dinta a wayarta,koda tana da bugatar wani abu kada taji komai,kai tsaye ta kirata.

Gudun mantuwa da girman majin ya sanya tana ajjiye wayar afifa ta dauki wayar tata ta fara duba tarin miscall din data samu,wasu na cousins dinta ne wasu na yayunta,wasu numbers dinma batasan nasu waye ba.

Tana tsaka da saving kira ya shigo wayar tata,kamar ba zata daga ba,saboda batasan number din ba sai kuma ta dauka din ta kara a kunnenta. Baquwar murya ce a kunnenta,ta amsa sallamar da akayi mata

"Sunana elyas,ina daya daga cikin ma'aikatan
MT JARMA,na kira ne bisa umarninsa,yace na shaida miki,idan akwai wasu kudade da kike bugata na hidindimu ki fada sai a tura miki" wani irin baci ranta yayi qwarai ta mige ta zauna sosai,ma'aikacinsa ne,tasan kuma irin respect din dake tsakaninsu dashi, uwa uba ma shi din dan aike ne gaba daya bashi da laifi sai ta rasa abinda zatace masa,ta lumshe ido takaici yana cin zuciyarta

"Hello madam,kina jina?"

"Ina jinka,elyas ko?" Kai ya gyada

"Yes madam"

"Bari na baka shawara,koda gaba kada ka sake yarda ka shiga irin wadannan abubuwan,saboda bai dace ba,kudi kuma kace masa har yanzun dai bashi da kudin da zai bawa sãahar…." Cikin kunnuwansa ta
qarasa fadin kalaman,yadda yaga elyas yayi shuru yana qifta idanu yasan akwai matsala,ya fahimci tana da tsiwa da rashin barin kota kwana,zata iya fadin wata maganar ma da zata iya zubda masa girmansa a idanun yaransa.

"Da wa kike?" Sautin murvarsa dake da wani irin zurfi da haiba suka sauka mata a kunne a lokacin da bata zata ba,dalilin da yasa batace komai ba kenan har ya sake maimaita tambayarsa. Cikin dakiyarta tare da son fanshe bacin ran da afifa da sauran family ke gasa mata saboda yadda suketa shirin biki tace

"Ni ba wulagantacciya bace, kuma bana neman komai a gurin kowa,ka rige arziqinka na rige mutuncina" wani irin zafi maganarta tayi mata,yaji babu dadi sosai a ransa,saidai takaicinsa ragagge ne tunda umarnin maji ya cika

"Hey!,watch your words.…karki dauka
kiranki yana da alaqa da damuwa da akayi dake..
bazanvi tolerating nonsense ba,don bazan biva sadakinki sannan na dauki wadan nan tsiwar da rashin kunyar ba" daga haka ya kashe wayar yana furzar da iska me zafi daga bakinsa. Lallai idan batayi wasa ba sai ya mata horo me tsanani, ya cire duk wannan jin isar tata da rashin kunya,abinda takeyi masa kaf tarihin rayuwarsa ba wanda ya taba gwada masa irin hakan sai ita. Wani mugun tsaki yaja ya jefar da wayar,maji ce sila,inda ta fahimci maganarsa tun farko da bata sanya yasa ay! kiranta ba. Ya miqe tsaye yana boye hannunsa a aljihun trouser dinsa,yana jin zuciyarsa na sake zafafa,dai dai lokacin da sajjad ya shigo dauke da wasu manya manyan kwalaye shi da jibril. Har suka gama ajjiye kwalayen jibril ya juya ya fita baice musu ta tafas ba. Zama sajjad din yayi ya fara bude kwalayen,wasu irin shegu suit ne da yadiddikan vicuna,qiviut fabric guanaco da baby cashmere wadanda duka aka viwa wani lafiyayyen kwantaccen dinki. Kallo daya zaka yiwa kwalayen zuwa sutturun ciki kasan maqudan kudade kamfanin da yayi kwangilar aikin ya lasa daga hannunsu

"Here's our wedding attire,ya ka gansu?" KO duban inda yake toufeeq baiyi ba,don dama yana cike da sajjad din. Tafiya yayi ta sati daya,amma kafin ya dawo sajjad din ya sanya an canza komai na sassansa,an canza tsarin komai ma,ya zuba masa dukka wasu kaya da suke favorite dinsa a design da kuma color,sannan ya fidda sashen da aka zuba jeren säahar din. Yayi masifa kamar zai ari baki har sai da girjinsa ya dinga zafi kasancewar bame doguwar magana ba,yana ganin kaf girman gidan da sassan da yake dasu amma ya rasa inda zaiyi mata matsugunni sai cikin sashensa? haka ya haqura ya gaji,don sajjad ya gaya masa yayi din waye zai aureta da za'a ajjiyeta a wani muhalli na daban,sanann muddin yaci gaba to zai sanarwa da Dr girema auren meye zaiyi,da kuma abubuwan da yaketa yi din,wanda sam basu dace ba,don meye bazai sassauta zafin kansa ba?. Haka ya gama qure sajjad da zazzafan kallon nan nasa ya debe fararen idanunsa yabar masa wajen,yasan indai yaci gaba da tsayawa sajjad bazai gaji da gasa masa magana a fakaice ba,shi kuma bazai iya doguwar magana ba.

Yanzun ma key din motarsa ya dauka
ya fice daga gidan shi daya,ransa a bace,shi dinma bai duka duka wannan hidimar zaa yita yiba me hana mutun sakewa,hatta da fadeela yanzun ganinta sai lokaci lokaci,duk sun yamutsa gidan da shirye shiryensu,yau basu nan gobe basu can,cire wancan canza wannan siyo wannan ajjiye wancan,duk Dr girema ya daure musu qarqashin ko nawa sukeso zai dauka ya basu. Ko su jibril da sukayi yunqurin biyoshi hanasu yayi,bai tsaya ko ina ba sai bristol palace,ya kama royal suit da ya saba ya wuce ciki bayan ya kashe dukka wayoyinsa yana fatan samun relief ya kuma daidaita kansa,shi kansa yasan yanata misbehaving ne,yana kuma batawa sajjad wanda dama shi kadai yake iyawa dashi,yasan abinda ya faru dashi a baya yake hunting mind dinsa,yanaso yayi cooling temper dinsa kafin ya dawo cikin gidan.


*******Kayanta taketa hadawa guri
daya,amma fiye da rabin hankalinta ya dilmiya a zuzzurfan tunani. Idan lissafinta yayi dai dai,ranar da zata isa Nigeria ya kama saura kwana biyu rak a fara bikin,kamar yadda kwanan wata ya nuna mata jikin dallelen invitation din me rubutun ruwan gold a jiki, wanda har yanzu hasken katin da tsarinsa basu bacewa idanunta ba,don sam baiyi kama da katin biki ba. Jagwab ta koma ta zauna saman kujera,ba qwarin zuciya ba har gwarin gangar jikinta tana nema ta rasa, komai gani takeyi yana fara zuwar mata a cakude,ko a mafarki bata taba tunanin akwai wani abu

Please Login or Register in order to submit comment