Reading TABARMAR KASHI 1&2 complete by SAFIYYA HUGUMA Chapter 51 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kitchen din har sai kin gama,idan ta rage kuma a zubar, kada a ajjiye" Nadeeya ta danyi mamaki, amma kuma tasan sahar din kulawarta ga fadeela ta musamman ce, don haka ta amsa mata da

"To,in sha Allah, sannu Allah ya bada lafiya,ki huta sosai don nasan akwai rashin samun cikakken bacci ma jiva,gwara ma da yaa toufeeq ya hana zuwa aikin yau,kya samu ki huta"

"To nadeeya‚na gode,ki cewa fadde na i missed her " murmushi nadeeya ta saki, sai itama fadeelan dake kan cinyar toufeeq ta saki murmushin, don duk a kunnensu tayi maganar.

Maganganunta suka sake sakashi zurfin tunani vana da bugatar zauna ya tattauna da ita, amma ya sani a yanzun kamar ya bar mata wani ciwo ne a zuciyarta,ya tabbatar a quilace take dashi, ba lallai bane ta tsaya ta saurareshi. Special care da take bawa fadeelan wani abu ne da bau taba ganin kwatankwacinsa ba,bata da lafiya amma dukka hankalinta da tunaninta yana kanta.

Maida idanunta tayi ta rufe itama ba tare data motsa din ba, tana jin yadda qasusuwanta suke ciwo,cinyoyinta kamar wadda tayi wasan tsere na kwana guda,ko yaya ta motsasu sai tail wannan ciwon,hakanan ta cikin qashinta takeiin zazzabi yana mamaye ilahirin jikin nata,sannu sannu wani gantalallen bacci ya dauketa.

Cikin baccinta ta dinga jin kamar muryar fadeela na gwala mata kira. A hankali ta bude idanunta ta miqe ta zauna saman gadon tana sake jin sautin muryarta daga bakin gofa tana hadawa da knocking. A hankali cikin lallaba jikinta da ya qara tsami ta sauko a gadon, ta isa bakin gofar ta bude.

Fadeela dince, toufeeq yana tsaye daga bayanta,guri daya idanunsu suka hadu,ita ra fara janye nata idon ta taka a hankali cikin takatsantsan tana komawa cikin dakin gami da laluben dankwalinta da ya zame, sassalkan gashinta me santsi wanda ko ribbon bata samu damar saka masa ba tunda tavi wanka ta barshi a haka don ko Draver bata samu ta saka ta busar da shi ba ya tarwatse iskar dake dan kadawa cikin dakin na mata wasa dashi daga hannun hagunta zuwa dama. Idanunsa a kanta har ta zura garamin hijabi wa jikinta yayi qarfin halin dauke idanun nasa ya biyo bayan fadeela.

"Anty N,tun dazun nake nemanki sister nadeeya ta hanani shigowa,wai baki da lafiya?" Ta fadi cikin kulawa.

Dan qaramin murmushin da bata shiryawa saki ba shi ta saka, ta saka hannu ta shafi gefen fuskar yarinyar,she was so caring

"am getting better fadee na,so karki damu" Idanunsa a kansu har ya qaraso ya zauna saman sofa bed ta yadda zai iya fuskantarsu. Ledar hannunsa ya ajiye ya fidda magungunan ciki sannan ya dubi fadeela

"Jeki kawomin cup be careful"

"No ta barshi" sahar ta fadi zata miqe, hannu yasa ya maidata, suka hada ido ta kauda kai,sai ya miqe

"'Karki rufe qofar before na dawo please" ya fadi da sigar lallashi. Bata ce masa komai ba sai sake kau da kanta tayi,ya gaji da saurarenta ya juya yana fita a dakin.

Lokacin da ya dawo fadeela na zaune d'are d'are saman cinyarta tana mata surutu, idanu yadan fidda sannan yasa hannu a nutse ya sauketa daga kan cinyar tata

"Noo my angel,anty N bata da lafiya,kinyi mata nauyi da yawa"

"Ayyah,sorry anty" ta fada tana kallon säahar, kai ta girgiza mata tana shafa kan yarinyar,a yanzu duk wani tunani nata ya tattara kan yadda zata samawa yarinyar lafiya,yanzun shine abinda kadai ya rage mata tayi, tana jin daga wannan ta kammala zamanta cikin gidan.

Tablet din farko va miga mata yana kafeta da idanunsan nan da suke gara mata wani nauyi,sai kuma haushinsa da takeji can qasan zuciyarta

"Take it please" ya fada qasa gasa yana sake watsa masa idanun nasa, hannu tasa ta dauka a tsakiyar tattausan tafin hannunsa sannan ta karbi ruwan da ya zuba a cup. Daya bayan daya ya dinga bata tana sha har ta gama,ta ajjiye cup din sanda fadeela take kallonta

"Ya akayi fadee?"

"Am starving" ta fada qasa qasa daidai sanda yake kwashe magungunan ya dora sanan dressing table, dawowa yayi gabanta ya kama hannuwanta ya rige cikin lallashi

"Fadeela" yayi kiranta

"Yau ba girki, oya ki yiwa zuwaira ko nadeeya magana,su baki wani abun kici,she's sick kin gani ai ko?" Kai ta jinjina, sai ya fiddo wayarsa yayi kiran nadeeya.

Mintuna kadan ta shigo, suna hada ido da sãahar din taji wani nauyi ya saukar mata,gani takeyi kamar ma kowa zai gane abinda ya faru, kamar an rubuta abunne a gaban goshinta haka takeji a jikinta

"Sannu anty N" kai kawai ta gyada mata tana lumshe ido nadeeyan bata zafafa ta garaso kusa dashi.

Bata ji abinda yace da ita ba,yau an magana dasa
gasanne suka motsa, ita dai taji ta kama fadeela sun fita a dakin. Ta cikin rufaffun idanunta taga hasken dakin ya ragu,a hankali taji an maida qofar an rufe, ta tsammaci tare suka fita saita gyara kwanciyarta cikin duvet. Saidai ko minti daya ba'a rufa ba sassanyan qamshinsa ya mamayeta,kafin ta gara tuna komai ta jishi a cikin duvet din. Wani wawan juyi tayi da nufin tashi, tashin bai samu ba,sai ma kyakkyawan masauki da yayi mata cikin jikinsa, lallausar fatarsa me wani irin gamshi da dumi ta manne a nata jikin,hucin numfashinsa da ya sauka daga wuyanta
zuwa gefen kunnenta ya sanya ta jin wani irin abu na
mata yawo cikin jikinta

"Karki wahalar da kanki, don ba zaki iya qwacewa
ba, dukkanmu bacci mukeji ni da ke, so mu rage baccin koda na one hour ne you will feel better idan muka tashi, and baccinki it will be more comfortable idan tare mukayi,karki wani yunqurin yin komai, just relax please"ya garasa fadin please din yana cooling voice dinsa sosai cikin yanayi na salon shagwaba. Ido kawai ta rufe tana jin yadda bugun zuciyoyinsu ke sauri ita
dashi,hawaye ya cika idanunta tana jin zafi cikin ranta. Ya yaudareta,ya karya alqawarin dake tsakaninsu,yayi
abinda ransa yakeso, dama jikinta ne yake bashi
sha'awa?,hakan kuma bai isheshi ba yanzu ya dawo ya tilasta mata yin bacci dashi. Ta tabbatar yadda ya fada ne, no way da zata iya qwatar kanta, amma kuma bakinta tana ganin zai iya qwatarta

"Bamuyi aure da kai don mu dinga wannan abun ba, ka karya yarjejeniya kaci amana" garamin murmushi ya subuce masa,a yanzun son tsiwar nan tata yakeyi,ya fuskanci da tayi masa shuru gwara tayi masa tsiwar,yana enjoying sosai,sai yasa hannunsa ya birkitota,ya sanya tafin hannunsa ya tallafe kansa bayan ya dogare gwiwar hannunsa saman gadon, qwayar idanunsa ya narka cikin tata yana mata wani mayataccen kallo

"You are saying na karya alqawari, naci amana,i break the rules,dama munyi alqawari da ke? yaushe mukayi yarjejeniya?, uhmmm madam suna ina? ‚nunamin su" Baki ta saki tana kallonsa tsakanin idanunsa guda biyu,wata qwallar ta sake cika mata idanu. Sai yanzu ta tuna basuyi a rubuce ba,yace baya bugata ta rige kayanta to rami yayi mata a sannan?, ko dama ya shirya faruwar hakanne? yanzu bata da wata huija kenan koda bavan ta gama aikinta akan fadeela ta nemi takardar sakinta?.

"Kinzo kulawa da fadeela amma baki yarda ki kula da daddynta ba ko dan gangani?" Ya fada yana langabe mata kai, wanda shi kansa baisan lokacin da hakan take faruwa ba. Ta karanci abubuwa na neman saba saiti, gaba daya kamar ba da MT JARMA take magana bama, sai taji kanta bazai iya dauka ba

"I need space please ka sakeni ka fitarmin daga daki" wata wawiyar rungumar yayi mata yana saka kanshi tsakanin boobs dinta da har yanzu yakeji basu isheshi ba

"Ki huta hakanan please magani kika sha" yadda yaketa morewa albarkatun girjinta yana masifar gona mata rai,cikin rawar muryar dake nuna kowanne lokaci kuka zai iya qwace mata tace

"baka da bugatar bazawara in all ways,so me zakayi da ilkin da ba'a san darajarsa ba?" Bai gara barinta tace komai ba sai tsintar bakinta tayi cikin nasa ya hade bakunansu gam,ya hanata sake cewa komai, sai wani zazzafan mouth to mouth kiss da yake sauke mata wanda cikin mintuna yaso sake birkitashi, da qyar ya zare bakinsa yana jin dumin hawayenta suna taba fuskarsa

"Idan kinason zaman lafiya kiyi baccinki kawai" ya fada yana aza mata nauyin girjinsa idanunta kawai taja ta rufe gam, bata sake cewa komai ba, saidai tuni ta yanke hukuncin abinda zata aikata. Ba jimawa bacci yazo yayi gaba da ita, ya gyara mata kwanciya cikin jikinsa yakai lips dinsa yayi kissing goshinta,kamar zai cinyeta da idanunsa wani irin murmushi na fita akan fuskarsa

"Rigimammiya ta" ya fada softly yana jin zuciyarsa kamar wadda aka canzawa muhalli.

Afwan,yau na baku shi a rarrabe kuma page d'ai
d'ai,ayimin uzuri na wuni a asibiti ne. Amma gobe komai zai zama normal in sha Allah, Na gode da kasancewa tare dani.

*HUGUMA*

_TABARMAR KASHI*

Book 02 Page 34

Yamamci lis ta farka, ta samu baya dakin,sai abinci data tarar, toilet ta shiga tayi alwala ta dawo tayi sallar la'asar, kamar ba zata taba abincin ba amma wata irin azababbiyar yunwa takeji, rabonta da abinci tun toasted bread da taci da milk tea. Tana bude abincin tasan nadeeya cs ta girka,ta diba kadan taci ta maida ta rufe.

Taji dadin jikinta sosai, hakanan taji ta gaji da zaman dakin, tana zura slippers dinta aka turo gofar.

Toufeea jarma ne,cikin sassanyan yanayinsa,yana sanye da shirt da trouser dukkansu baqaqe,shigar data sake gara masa kwarjini qwarai, ta kuma fidda ainihin zallar kyansa,idanunsan nan masu kaifi a yau sun koma masu laushi, saidai cike suke da tasirin was abubuwa masu tarin yawa. Qarasa shigowa yayi cikin dakin qamshinsa yana mamaye ko ina,ta dauke kanta tana jin haushin yadda tabar qofar a bude har yaketa samun
damar shigo mata kai tsaye. Hannunsa goye a qirjinsa ya
garasa ya jingina da dressing table,da lallausar muryarsa
din nan yace

"How are you feeling?" Ta qasan idanunta ta gasa masa harara. kamar ba zata amsa masa ba sai kuma tayi magana ciki ciki kamar wadda aka viwa dole
"'Da sauqi"

"Ma sha Allah Alhamdulillah" ya furta a nutse

"Su sajjad suna parlor suna jira" ya fada yana dubanta
still, don tunda ya shigo ko sau daya bai dauke idanunsa daga kanta ba. Da sauri ta daga kai suka hada ido,sai kuma ta basar, tana jin zumudin ganin afifa har cikin ranta, ta garasa sanya slippers dinta ta mige tana takawa.
Har ta gotashi taji an riqe hannunta a tausashe, da dan mamaki a fuskarta ta juyo suka hada ido ta watsar da kallon nata gefe

"Tsayani mana" y fadi yana sakar mata hannun. Dole ta dakata har ya cimmata suka jera,tare suka ratsa hallway din har suka isa falon. Idanun afifa akanta, murnarta itama ya gaza boyuwa. Rungume juna sukayi suka zube saman kujera tana gaida sajjad

Lokacin da yake ce maya ya jiki? Allah ya sawwaqe sai da taji kamar gasa ta tsage ta shige, tadan saci kallon toufeeq shima ita yake kalla. Ya fahimci kallon da take masa,sai ya tabe baki ya kuma watsa hannayensa alamun ba ruwansa baisan komai ba,a kunyace ta ja afifa suka shiga kitchen tana nemana abinda zata basu.

Karon farko data fara baqi kenan, afifa da ta lura tana ta wani bove dariya ita ta tayata suka shirya komai cikin tray, tana shirin dauka toufeeq din ya shigo. Har saman fuskarsa taga yaji dadi, yasa hannuwansa ya tallafe nata hannayen dake dauke da farantin yana mata wani irin kallo

"Jeki huta, thank you" banda tana gudun jiwa kanta ciwo da tuni ta zare hannunta daga qasan tray din, amma dole ta jira ya karba sannan ta zame nata hannuwan a hankali.

Koda ya fita ta laluba kitchen din ba afifa ba dalilinta, ta tako ta fito sai ta cimmata tsaye a tsakanin hallway dinsu

"Ke nake nema ai"

"Tuni na yiwa kaina qiyamullaili na fito..... Kai azaba,irin wanna kallo haka kamar babu gobe?, bestie kamar zaku cinye junanku?, kuyi haquri ku ragewa 'ya'yanku fuskar da zasu kalla taku mana karku cinye kanku tun yanzu su su rasa abin kalla...

" Batasan ta dimawa afifa
dundu ba sai data gantsare tana fadin

"Wayyo hayatee,zata wujijiga maka baby" surrender sãahar tayi daga bakin qofar dakin tana riqe da handle tana duban afifa dafe da bakinta

"Bestie,ke yanzu har kina zancan daukar ciki?" Harara ta watsa mata

"Yo me za'a jira?, daga ni har mijina dukkanmu jarumai ne kuma munason junanmu, ribar auren soyayya kuwa ai haihuwa,ki zauna ke kam,nan da wata takwas zaki rakani labour room in sha Allah" dariya ta kubcewa sahar,abinda ta jima batayi ba, ta maida gofar ta garaso dakin tana neman gurin zama kusa da afifa

"Sannu da qogari bestie na yarda har yanzu da sauranki a hankali"

"Allah am serious, kedai ba kin zauna ba?, da alama ma sai yau aka bare gyadar" ido sahar ta fidda tana dubanta sosai

"Inji wanne munafukin?"

"Ba wani munafuki, ina ta kiran wayarki ne naji baki dauka ba,da na nemi nadeeya tacemin yau tun safe baki da lafiya, kina can kina bacci ke da oga,yanzun suka fito ita da fadeela, nasan halin bestie na da taurin kai da tsanar maza,nasan ba abinda zai kaiki bacci tare da MT JARMA haka siddan,saidai idan ya miki qarfa qarfa ne,idan kuwa hakane to ya burgeni wallahi, Allah yasa yayi miki ciki ma yau din ko jiyan, bansan actual ranar ba" ta fada tana ayaqyata dariya abinta, sai kuma ta sassauto ganin fuskar säahar din ba walwala, kamar ma hawaye ne cikin idonta. Kama hannun nata tayi

"Me kuma ya faru bestie?"

"Amanata vaci bestie,ni bance masa ina da bugatar auratayya ba,yasan auren meye mukayi amma sai ya yaudareni yaci amanata?" Saura kadan dariya ta sake qwacewa afifa,amma ta tabbatar idan tayi dariya gayyar zata watse ne

"Hana bestie, kamar bakiyi karatun addini ba?,haduwata da hayatee yasa na sake sanin waye taoufeeq sarai, may be ma fiye da ke tunda ke baki maida kanki ba,na miki imani da Allah jinki yayi kawai da kunne, amma dai baiyi niyyar aikata miki komai ba, kawai an samu akasi ne,wanda dama ba yadda za'a yi kina halalinsa ya zauna yana kallonki, saboda me?,bayan Allah ya bashi damar yayi komai ba komai?" Hannunta ta qwace daga na afifa, saboda ta karanci ba wani goyon baya zata bata ba,zata zartar da abunta ba tare data nemi shawara daga wajenta ba

"Kiyimin bayanin ciwon fadeela sosai,inason naji yadda yake fiye da bayanin da kika taba yimin, hankalina yana tashi, inason na kawo garshen ciwon a tare da ita,ina zargin matar nan zargi me qarfi,na tsaneta bestie haka kawai zuciyata ta wayi gari bata gaunarta sam sam" gyara zama afifa tayi

"Gaskiya ba'a yimin tarba me kyau ba,masu juna biyu ai sai da abun kwadayi,abani abu na saka a bakina sai naji dadin yi miki bayanin" harararta tayi tana migewa

"Zakiyi bayani ne da kyau,me bestie na takeso?"
Idanunta ta juya

"Me zan zaba ma?, kitchen din bestie din nawa kamar ba na matar aure ba,ba wasu ajiyayyun snacks ba komai,ko girki banga alama ba,ina dukka fikirarki ta girke girke?"

"Zaman nazo ma kenan" ta bata amsa tana harararta
sannan ta juya ta fice. Mintuna kadan ta dawo mata da
abinda ya samu ta ajiye mata bayan ta gama ta tattara hanakalinta ta fara yiwa säahar din bayani

"EPILEPSY Ciwo ne na kwakwalwa da ke iva shafar kowacce halitta me rai hatta dabbobi ma suna yin ta
Kin San ita kwakwalwa da nerves su ke controlling jikin
gaba daya suna anfani da electric signals ne wajen aika sakonni a sassan jikin Dan Adam.
Misali ko Abu ka kalla ko kaji sauti nerves din da ke cikin
idanun ka da kunne su zasu sarrafa wnn abun da ka gani
ko ka ji su Maida shi kwatankwacin electric current su
aika ma kwakwalwa ita Kuma ta tantace maka kaza ne ka gani ko ka ji"

"Haka zalika idan kwakwalwa na so misali ka daga
hannun ka zata Yi relaying sakon ne ta hanyar aika
electric signals ne ta nerves zuwa hannun sai ka daga
shi kawai,wnn shi ake kira voluntary movement, xaka iya yin shi duk sadda kake so kana da control on kayi ko Kar Kar kayi Amma kamar bugun zuciya kyafta Ido,
movements na kayan ciki wajen sarrafa abinci da sauran motsi da sassan Jimi ke Yi Wanda baka iya controlling shine involuntary movement dukan movements din nn akwai sassan kwakwalwa da ake da alhakin Yin su Guiyoyin kwakwalwa, NOTE akwai jijiyoyi kala kala a jikin mutum kamar na jini,na kwakwalwa,na ba jiki kariya daga cututtuka da sauran su suna da sunayen su na turanci, Amma dai bahaushe duka jijiya yake Kiran su).
Abun da yake faruwa a epilepsy shine ita kwakwalwar kwatsam zata saki wadannan electric signals din ne lokaci daya sai ta Kuma kasa controlling dinsu shi yasa
Zaki ga sun fadi kusan ko Ina na jikinsu Yana motsawa uncontrollably a Hakan was har fitsari ko bahaya Yana kufce masu
Yadda electric signal din ke faruwa lokacin attack din is similar to kamar wutar lantarki na spark ne abun da yake faruwa kenan a cikin kwakwalwar
Attack din Yana faruwa ne kusan kamar a stages 4

1) na farko ana Kiran shi aural stage wato kamar warning sign ne cewa anytime ka fara Jin wadannan alamun xaka iya samun attack Kuma kowa da yadda yake ji wasu zasu rika Jin cowon Kai,ko su rika gain was abubuwa,ko su rka Jin wava Kara ko harshen su ya rika Jin wani dandano ko jikin su ba dadi kowa dai da irin abun da yake ji sai mutum yayi preparing ya samu waje ya kwanta saboda gudun samun raunuka

Sai stage na biyu shi ake kira Tonic clonic stage shine actual convulsions din Zaki ga mutum ya fadi Yana jujiga Yana zubar da miyau da fitsari da sauran su dai actual seizure din

Stage na 3 shine post ictal stage kamar recovery k nn bayan seizure ya tsaya zasu zama confused suna ganin Jiri da cowon jiki snn bacci Mai nauyi zai dauke su.

Stage na hudu Kuma na farawa ne bayan sun Farka daga wannan baccin was da yawa basu iya tuna ma sunyi Amma zasu tashi da cowon jiki da raunuka na faduwa ko ciccije Baki da harshe da sukayi lokacin sezure din har zuwa lokacin da zasu warware gaba daya.

Epilepsy kala kala ne. Akwai Wanda muka sani
Wanda mutum zai fadi yayi ta jijiga shi ake kira generalized epilepsy,akwai Wanda Kuma iya sashe daya na jikin shi ke jijigar Kila fuska ko hannun ko kafa,wani
Kuma Zaki ga zuru zai Yi ya kura ma wuri daya Ido kamar yy hooking anywhere dai ya danganta da sashen kwakwalwar da ke da, matsala tunda ita kanta kwakwalwar akwai sashe sashe da ke controlling kowane fanni na jiki.

Akwai aune aune da ake yi a gane sashen kwakwalwar da ke da matsala da Kuma abubuwa da suka haddasa seizure din

Akwai hoton kwakwalwa kamar su CT scan,MRI,
Akwai awon dake duba electric signal din(EEG). Ana Kuma auna jini a duba ko akwai infection kamar sankarau (meningitis) tetanus,rabies da sauran infection dai da ke iya taba kwakwalwa.

Ana Kuma auna jini a San adadin wasu sinadaral kamar calcium,zine, phosphates,vitamin D,B da Kuma parathyroid hormone da karancinsu a jiki ko Kuma yswansu idan ya wuce misali yake haddasa seizure din, Akasin shekarun baya da ake tunanin seizure shafar aljanu ce ynz an gano cewa ciwo ne na kwakwalwa da zaa iya controlling din shi da magunguna ko surgery.

Akwai kalolin maganin da ake sha ko ayi allura da dama da ake kira anticonvulsants da ake anfani da su Kuma da ake nasarar controlling din ciwon da su.
Wadanda aka samu gano kamar tumor, ko scar ko fannin kwakwalwar da ke da matsala akanyi surgery a Yanke sashen da ke da matsalar ana Kuma dacewa musamman idan kwararru ne masu kayan aiki na zamani su kayi.

Amma surgery na iya zuwa da complications misali bayan anyi ya kasance mutum Bai iya anfani da wani bangare na jikin shi ko ya samu paralysis gaba daya. Yawanci epilepsy na Yara Yana farawa ne dg zafin zazzabi Zaki ga da sun fara fever jikin su ya dau zafi sosai zasu fara convulsing da yawansu sukan warke daga lokacin da suka Kai 5-7yrs haka. Duk da akwai wasu dalilan sake haifar da ita, kamar mummunar faduwa ko buguwa a kai.

Masu epilepsy na fama da tsangwama daga wajen mutane Wanda rashin sanin ainahin ciwon ke kawowa.

Akwai side effects na magunguna da suke affecting learning da behavioral abilities na musamman yaran, so wannan shine cikakken bayanin".
"HUGUMA”

*_TABARMAR KASHI

Book 02 Page 35

Shuru sãahar tayi tana gyada kai, idanunta dauke da qwalla,tausayin masu ciwon yana ratsata

"Surgery shine best hanya nake tunani da fadeela zata rabu da ciwonta,saboda kamar nata ciwon hakan ya nuna a yadda naji daga bakin nadeeya,hajiya qarama ta gara iza wutar ba za'a tabata ba,ba za'a yi mata aiki ba....yanzu kuwa lokaci yayi,ko tanaso ko bataso" sãahar ta fada with confidence.

"Bestie,please nan da sati daya ki bincika min best asibiti a kowacce qasa yake da zasu iya yiwa fadeela aiki, zanji da komai,ko sajjad banaso ya sani sai an gama" kai afifa ta mirgina

"Anya bestie?,bakya gudun faruwar komai?" Kai ta girgiza

"'Na yarda da Allah, kuma nayi imanin bazai tozarta ni ba,kyakkyawar niyya sa tsarkin zuciya shine a gaba da komai" ta qarasa fada tana daukar wayarta, ta bude calendar na period dinta don ta duba kwana nawa ya rage, saboda ciwo da taji mararta tana mata kadan kadan. Qatoton circle ta gani tare da manyan rubutun
OVULATION DAY,sai ta sauke wayar tana dan yatsina fuska

"'Kina experiencing wani pain ne?" Kunyar afifa kadan tadan kamata,saita kau da kai tana girgizawa
"Na sha magani" murmushi afifan tayi, qasan ranta tana jin dadi da hakan ta faru, tana kuma sake ganin kima da martabar toufeeg, don wanna abun da yayi a wajenta ya tabbatar mata yasan abinda yakeyi,kuma shi ba shashasha bane,hakanan ya tabbatar mata cikakken namili ne da tunaninsa ya saba da na diya mace.

********Kamar ko yaushe,qarfe takwas saura minti biyar ta kammala shirinta,har ta fiddo mayafi zata yafa ta tuna da hijaban da ya aiko nadeeya ta kawo mata guda goma sha biyar a jiya. Tun ranar da su afifa suka tafi tunda ta rakasu bata koma sashen nata ba,tayi zamanta a sassansu,kwanaki biyu yau kenan ko fuskarta bata sake bari ya gani ba,ko hijaban ma sai nadeeya taga ta shigo mata dasu

"'Inji yaa moha, ki fara using nasu on Monday" tayi maganar tana hadiye dariya. Da kallo ta bita,nadeeya da afifa sun hade kai,sai suyita mata magana suna boye dariya,sun maidata kamar wata 'yar tsanar wasansu,amma taci alwashi itama duk ranar data kamasu ba zasuji da dadi ba.

Qaramin tsaki ta ja, batasan meye nufinsa da yin hakan ba,zama tayi ta zazzagesu,ta kuma cire color din da zai shiga da atamfar jikinta,ta qarasa gaban madubi ta saka tana daure igiyar kai data hannun hijabin. Lokacin fadeela ta shigo wadda ta barta ne tana qarasa yin breakfast a dining.

"Anty na gama"

"That's good girl,oya let's go" ta fada tana goya school bag din fadeelan a bayanta kamar yadda suka saba.

Tun daga nesa taga parking space din da yake cin motocin nasa wayam ba kowa, ba kamar yadda suka saba ba,a safiya irin wannan gurin zaka sameshi jere da motocinsa da kuma su jibril suna tsaye suna jiran garasowarsu. Yau din shi daya ta hanga,tsaye jikin BMW dinsa fara sol, wadda a wancan satin ta iso,sai daukan idanu takeyi tana tabbatarwa da me kallonta tsadar da take da ita.

Yau din sassaugar shiga ce, amma yadda kayan suka karbeshi sun maidashi wani so hot,ya koma balarabe sosai amma mara yawaitar haske sosai, cikin taupe color button up shirt yake da slim fit trouser medium gray, gafarsa wani tsadadden sneakers ne da ya kwanta sosai a lafiyayyar qafarsa da take qal kamar baya taka qasa. Wayarsa na hannunsa yana dannawa,tamkar hajiya qarama dake tsaye gabansa tana fuskantarsa ita da haseena baya jin abinda ma suke fadi,yayin da haseenan dake rungume da hannayenta ta zuba mishi idanu,sirrin tasirin kyan dake fita tattare da kamilar fuskarsa me yawan kwarjini suna sanyata jin kamar ta rungumeshi a yanxu haka,tana jin kamar ta bude idanu ta ganta ta zama mallakinsa matarsa, kishinsa na sake hauhawa cikin zuciyarta, tana ji a ranta zata iya vin komai zata iya rasa komai muddin shima ta rasashi, ciki kuwa harda rai da rayuwarta.

Kai säahar ke gogarin daukewa bayan idanunta sun gama qarewa kowa kallo a cikinsu,wani abu taji na neman tsaya mata a wuya,tsaiwar meenal tayi mugun yin kusa da toufeeq din, ta tabbatar da zaiyi wani wawan motsin tsaf zai iya taba jikinta, qoqarin gayawa kanta takeyi

"Ba huruminki bane,meye naki?" Amma ga mamakinta zuciyar taqi karba,kai ta sake kawarwa tana fadin
"Wataqila tana tuna cewa dukkansu musulmai ne masu amfani da yaren hausa, bai kamata kuma a samu

Please Login or Register in order to submit comment