Reading TABARMAR KASHI 1&2 complete by SAFIYYA HUGUMA Chapter 62 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da mahaifansa,sai gashi abun mamaki a gaban idanunta mommy qarama din ke cewa a saki mahaifiyarta?,me maji tayi mata?, ita da duka duka ko awa hudu basuyi da haduwa ba a yau din.

A nutse ya maida dubansa ga fauziyya dake ci gaba da aikin kuka kamar wata qanqanuwar yarinya,zuciyarta ja sake cika da mamakin yadda a yau yaya Mahmud din yayi funfurus da kukanta,abinda a baya baya taba iya jurewa kukanta koda na minti daya ne

"Fauziyya,yanzu ke bakijin kunya a gaban yarinya ki dinga fadin a saki uwarta?" Tambayar ta sake gigita tunanin hajiya garama,ta yungura zata tashi don ta kalli yayan nata da kyau, amma yadda kanta ya sara ya hanata aikata hakan,sai daga kanta tayi tana daga kwance ta kalleshi

"Yaaya, matsayina baikai ka saki shifa ba saboda ji?" Kai ya girgiza

"Komai ana yinsa ne saboda dalili, banga dalilin da zai saka na saki shifa ba, abinda nayi mata a shekarun baya ma kadai ba tare da qwaqwqwarar hujja ba har yanzu ina nadamarsa"

"Ba zaka iya sakinta ba yaaya?"

"Fauziyya ki kwanta kisha magani,ki daina maganar sakin maji a gabana banaso,karon farko da zan nema abu nima daga gurinki kenan" ta qarasa maganar yana danna wayarsa yayi kiran nadeeya.

Idanun nadeeya saman fuskar maji data hade yatsun hannunta guri guda,har yanzu tana jiran amsar tambayar data yiwa majin.

"Maji,don Allah ki gayamin,me kika yiwa hajiya qarama haka a rayuwarki?" Maji ta daga kanta a nutse tana duban nadeeya

"Idan nace miki ban sani ba zaki yarda dani?" Kai nadeeya ta gyada

"Na yarda maji, saboda tunda kike damu baki taba yi mana qarya ba,koda qaryar wasa kuwa maji" nadeeya ta furta cikin gamsuwa tare da yarda da kowanne furuci da yake fita daga bakin maji din.

_K'alubale a gareku iyaye,babu abinda yake matuqar ruguza rayuwa,ya sauke maka dukkan wani kwarjini da kima taka irin K'ARYA, duk wata matsala da muke fama da ita a yanzun ta fara ne daga gidajen aure,matsalar shugabanni na gari, matsi da wahalar rayuwa, daya daga cikin jigon matsalar itace K'ARYA,muna wani kuskure na yiwa yara qaryar "idan naje guri kaza zan siyo maka mota,ungo (bayan babu abinda zaki bashi)yiwa wata ko wani garya idan kuna hira bayan ke kanki kinsan qaryar ne,ko yiwa mahaifinsu qarya don ki kubuta daga wani laifi da kika aikata masa,wallahi irin wadan nan qananun abubuwan da muke rainawa su yara sukafi dauka tare da qoqarin kwatantawa,kafin kace meye wanann sai a wayi gari yaro ya zama shahararren maqaryaci, tun yana qarami yana ganin ba komai bace, zuwa sanda zai girma sai ya zama gagara badau a fagen qarya,qarya masifa ce,qarya masifa ce,tana iya sanyawa a tsani mutum,kamar yadda gaskiya ke siyawa mutum soyayyar jama'a,iyaye mu kula,mu raini 'ya'yanmu a cikakkun masu gaskiya da fadinta da aiki da ita,mu nuna musu ita kadaice hanya mafi dorewa da sanya rayuwa tayi dadi nan duniya da ranar gobe, Allah ya bamu dacewa,ya bamu ikon tarbiyyantar da su bisa tafarkin addinin musulunci_.

K'arar wayarta ta katse tunanin da kowannensu ya shiga,ta daga wayar Dr jarma din sannan ta ajjiye tana fadin

"Gani nan zuwa abba" saita waiwaya ga maji

"Abba na kirana,sai da safe maji" murmushi tayi

"Ki kwanta kiyi baccinki, bance kuma ki tanka mata da maganar ba,kici gaba da addu'a da tsare kanki" abinda maji ta gaya mata kenan,wanda har ta isa dakinsu tana juya maganganun a ranta.

Nadeeya din na fita ta shirya kanta tayi kwanciyarta saman sofa bed tare da qudundunewa a duvet,lokacin da ya shigo kwarjini tayi masa,ya kasa cewa komai da ita,ya sani ya mata laifi a rayuwarta me girman gaske, da ya tashi dawowa da ita kuma zucivarsa
ta kasa daurewa ya tsaya lallabata,ya biyo ta ganin
kakanta suka tilastata suka maida aurensu,ya sani dole
ya lallabata ya gama wanke laifinsa fes sannan su dora
daga inda suka tsaya,don cikin zuciyarsa yana jin kamar
yanzu ya fara son shifa din.
Yana zaune daga saman gadon, qafafunsa a
miqe yayin da ya jingina bayansa da fuskar gadon. Duvet
ya jawo ya rufe qafafun nasa zuwa qugunsa, idanunsa
nakan wayarsa da yake rage saqonni na mutane, sannan
fiye da rabin hankalinsa yana kanta sanda take gaban
madubi tana shafe skin dinta da mai tare da gyara jikinta
da turarukanta tausasa. Dagowar qarshe da yayi ya kasa
dauke idanuwansa daga kanta,sai ya sauke wayar daga
cinyarsa ya miga mata hannuwansa yana daga
zaunen, murya can qasa yace da ita

"Come closer" wani abu ne ya saukar mata a take, irin
abun nan da ba'a rasa kowacce diya mace dashi,jan aji tare da jan rai, iya kallonsa a gareta ya saukar mata da
wata kasala da yanayi a jikinta,wani abu me qarfi yana
buda zuciyarta ta qarfin gaske,sai ta fara takowa cikin
jan aji da yanga fiye da yadda ainihin tafiyarta ta halitta take,wanda ita kanta batasan hakan na faruwa da ita a
daidai lokacin ba.

Kasa jura yayi,ji yayi kamar ba zata iso ba,sai
kawai va vaye duvet din ya sauko gaba daya daga kan
gadon ya tako ya risketa a hanya. Hannayensa ya sanya ya zagaye bayanta dasu tare da matsowa da ita dab dashi a zafafe, fuskokinsu sukayi kusa da juna sosai, ta yadda kowa na iya ganin fuskar dan uwansa fes. Kallon kallo suka fara yi a junansu tamkar yau suka fara ganin fuskokin juna. Daga kan kyakkyawan girarta zuwa dogon hancinta me dan tudu da ya zauna sosai akan tsararriyar fuskar dake da shinfidadden kyau,ya zarto a hankali zuwa zaman lips dinta dake hasken lip gloss data dan shafa masa. Tsigar jikinsa yaji ta tashi,ya miqa yatsantsa saman lips din nata a hankali yana kewayeshi da su

"You're super hot!" Ya furta a hankali kamar me rada

"Kinsan kiss guda daya yana burning around 6colories a jikin dan adam?, do you want to workout with me?" Yayi tambayar yana dage mata dukka girarsa guda biyun?.

Wani siririn murmushi ne ya kubce mata ba tare data sani ba,murmushin da ya qara mata kyau, kyan daya sake ingizashi,ba tare da ya jira ta bashi damar da yaso samu tun farko ba ya hade bakinsu guri guda,ya dora lallausan lebansa saman nata ya fara yadda yaso dashi.

Wani irin abu ya shiga aikawa jikinta,kowacce gaba tata ta amsa,ta kasa kowanne motsi tana jin yadda yake sarrafa bakinta zuwa lips dinta cikin qwarewa kamar ya samu sweet,tsahon wasu mintuna kafin ya janye a hankali yana maida numfashi. Kasa hada ido tayi dashi tana jin nauyinsa yana saukar mata, hannuwansa yasa ya kamo fuskar tata a tausashe da sautin da koda kana cikin dakin babu lallai ka iya jin me yake fadi

"Kinsan meye?" Kai ta girgiza masa a hankali

"A da banason abu me zagi sam sam,but when i tasted
your lips,sai na zama addicted to sweet, because your lips are the yummiest thing in the world" kunya ce ta kamata matuga da gaske, kalamansa suna da wani irin girma da ko yaushe ya furta su sai ta jita kamar a wata duniya ta daban take, kalamai ne da ba gama gari ba qwaqwalwarta da zuciyarta basu tana amsar kalamai masu tsada da girma irinsu ba tsahon rayuwarta, ta rasa inda zata boye kanta sai kawai ta cusa fuskarta tsakiyar qirjinsa tana boyeta. Murmushi ya saki yana dora hannunsa saman tattausar sumarta

"Good!, duk sanda na nema gurin fakewa nima i will bury my face in your boo.....

.." Saurin miqewa tayi daga
jikinsa,tasan yanzun sai sake mata zancan da zai kusa sanyata narkewa a wajen. Ko taku guda bai bari ta qara ba ya dagata cak ya nufi gadon da ita yana cewa

"Muie na karanta miki wani abu" adan tsorace tace

"Am still bleeding" bai kulata ba sai daya direta saman gadon,fuskarsa dauke da sirrintaccen murmushin nan da ita daya take samunsa yace da ita softly

"So?,all i want is to feel you close to me,tell you my story and at the end watch you fall asleep in my arms,ba wani can gurin zan je ba" ya furta yana zare rigar jikinsa,sai kuma yayi mata rumfa da qirjinsa. Kunya ta sanyata mirginawa,sai yasa hannunsa ya birkitota bayan ya kashe hasken dakin daga nan inda yake ta hanyar switch din dake kusa dasu. Bayanta ya koma ya kwanta tare jawota cikin jikinsa

"Sanyi sanyi nakeji kadan kadan,let's cuddle so i can steal your body heat" kafin tayi wani motsi sai ta jishi yana cusa kanta ta cikin oversized shirt din data saka,kafin tayi wani yunquri tuni ya shige cikin rigar,ya zagaya hannunsa ta saman plate tummy dinta ya sake janyota sosai kamar me shirin tsaga jikin nata su narke su zama abu daya.

Sanda dumin jikkunansu suka gauraya waje daya sai wata ajiyar zuciya ta subucewa kowannensu lokaci guda

"I know the real KHADIJA SΓ„AHAR,but har yanzu bakisan waye MUHAMMAD TAUFEEQ na gaske ba,i will tell you duk da baki buqata ba,zan gaya miki ne to clear all the doubt and negative think" kunya taji da abinda ya fada,ya akayi yasan tana masa wani bahagon kallo?. Bai fira ta bawa kanta amsa ba ya fara magana da nutsatsiyar muryarsa.

"Kinsan waye mahaifina, qanwata da mamana,na taso hannun mommy qarama fauziyya tun ban gama mallakar hankalin kaina ba har na zama mutum, a lokacin na dan fuskanci rigonmu a hannunta akwai qalubale da matsaloli, amma duka mun shanye na kuma kula da nadeeya fiye da yadda nake bawa kaina kulawa har muka kawo yanzu. Na girma wani mutum na daban bawai ina yabon kaina ba,dukiyar mahaifina bata a cikin lissafina,komai ina lissafin yadda zan mallaki nawa ne na kaina,sai kuma na fuskanci wani abu. Fauziyya bata qaunar na mori komai daga mahaifina,ko yaushe tana cewa da ni da shi 'ka tashi ka nemi naka na kanka' sannan tana cewa da dr 'ka barshi ya nemi na kansa yasan zafin nema', a haka na gina rayuwata, kusan komai nafi sha'awar na yiwa kaina".

Duk yadda naso boye kaina daga mutane su fahimci ni din waye hakan bai yiwu ba, daukan kamanni da mukeyi da abban da kuma ganina cikin was lamuran nasa ya sanya yake wahala na shiga guri ba'a san wayeni ba. Cikin hakan abban ya bada gagarumin taimako ga wata organization ta marayu da iyayen marayu, a nan gurin ne naga AMEESHA.

Tana cikin layin wadanda zasu karbi taimako da
suke cikin matsanancin hali na rashin muhalli da
abinci,acikin masu karbar tallafin duka ta fisu quruciya
da qananun shekaru,abinda ya fara jan hankalina kenan a kanta. Komai ina qoqarin yinsa akan tsari, don haka a sannan ban tunkareta ba kai tsaye,sai da aka tashi taron nabi address da komai nasu na isa gidansu. Na tsaya na tabbatar da halin da suke ciki din kafin na gabatar da kaina a wajenta.

Murmushi naga tayi bayan na gama mata bayani

"Na ganka a wajen taro, ba kaine d'an Dr mahmud jarma ba?" A zahiri banzo da nufin gaya mata waye ni ba,to amma kuma bazan iyayi mata qarya ba,don haka na amsa mata da "eh nine"


Zafafabiyar
πŸ”₯πŸ”₯πŸ”₯πŸ”₯πŸ”₯πŸ”₯

*HUGUMA*

*_TABARMAR KASHI_*

Book 02 Page 55



Tom


Bai taba dauka fada mata hakan zai zama babbar matsala a tsakaninsu ba,ya sanya tausayinta da na mahaifiyarta shine gaba da komai, tausayinta ya sanya masa soyayyarsa a ransa, musamman da ya fuskanci mahaifiyarta dake kwance tana fama da jinya mutuniyar kirki ce qwarai. Irin mutanen nan da sam rayuwa bata damesu ba,basu da wani buri me zurfi a cikinta. Kusan tafi kowa farinciki da wanzuwar taoufeeq cikin rayuwar d'iyarta, bawai saboda dukiya ko kuma wani abu daya mallaka ba, a'ah tsantsar nutsuwa hankali da hangen nesa da ta hanga muraran tattare dashi,dukiyar mahaifinsa ko wadatarsu bata sanya masa girman kai ko jin cewa shi din wani bane,tayi imani ameesha din zatayi aure hannun da za'a datajtata, za'a mutuntata,inda koda bata raye ba zatayi kukan maraici ba.

To ita rayuwa a duk yadda kaga Allah ya ajiye bawa,tofa yafi cancanta da wannan matsayinne, saboda shine Allamul ghuyub wato (masanin gaibu). AMEESHA na daya daga cikin matan da zuciyarsu ke cike da dimbin burika na rayuwa saboda kyawun fuskar da Allah ya azurtasu dashi. To amma me? yanayin talauci da matsi na rayuwa da kuma yanayin environment da suke ciki dukkan alamu sun nuna babu inda wadannan burika nata zasu shura,saidai duk da hakan akwai was baqin halaye da idan kayi tsinkaye zaka iya fahimta a tattare da ita.

Yadda ameesha din bata da saurayi duk da kyau da take dashi da kuma yadda matasan unguwar ke sonta ya gara kafa ameesha a zuciyar toufeeq,a nasa tunanin tsananin kamun kai ne da kuma darajta kai,abinda bai sani ba shine,ita din ta raina ajin dukkan mazan da suke zuwa mata da kalmar soyayya,tana ganin tafi qarfin ajinsu,ko a ranar da taje karban tallafin sai da mahaifiyarta tayi da ayar sannan taje din, da kuma tsananin rabon haduwarsu da toufeeq.

Shigowar toufeeq cikin rayuwarta sai ya sanya ta fara jin kanta yana budewa,idanunta suka fara budewa,ta fara shanshanowa tare da hango cikar wadan nan burikan da talauci ya yiwa dukan mutuwa suka kwanta magashiyyan,sai ta fara farfado dasu, musamman da ya kasance toufeeq din me sakakken hannu ne, mutum ne me tarin kyauta. Cikin lokaci qalilan tafi qarfin sutura da cima,ta samu tsadajjiyar wayar hannu wadda tayi sanadin haduwarta da 'yammata irinta da suka dauki rayuwar duniya da fadi,'ya'yan da sai da taimakon Allah da huwacewarsa ake samun abicin da za'a ci cikin gidajen iyayensu,amma idan sukayi wanka suka riqe wayoyinsu zakayi tsananin 'ya'yan wani commissioner dinne. lya wayar hannunsu kawai tafi jarin ubansu kauri.

To bare kuma ameesh da a sannan abinci a gidansu baya yankewa, toufeeq ya fahimci yanayin rayuwar da suke ciki, ya kuma dauki nauyin komai hatta da jiyyar mahaifiyarta. Mutuniyar kirki ko yaushe addu'a take Allah vasa ameesha ta kasance tasa ce ta har abada,ko yaushe fada takewa ameesha ta riqeshi hannu bibbiyu.

To koda umma batace mata ta riqeshin ba itama ba zata soma sakinsa ba,ina taga ta sakin toufeeq din?, mutumin da ya fara matso mata da burikanta kusa kusa da ita ya kuma fara cika mata su?. Ai bata ma gama sanin waye toufeeg din a zahirance ba sai bayan haduwarta da hadaddun qawayen data maye gurbin rayuwarta dasu,ta sake sanin waye mahaifin toufeeq, a nan suka hure mata kunne akan ta qara yawan buqatunta tana sake samun abubuwan rayuwa masu tarin yawana jikinsa,su saka sanya ta fara raina hidimar da yake mata,saboda suna gaya mata

"A arzigin ubansa,wannan hidimar da yakeyi miki tayi matuqar yin kadan" yana mata kwarjini sosai,tana kuma kunyar ta tambaya kanta tsaye,sai ta fara shigo da qarairayi tana karbar kudade a hannunsa. Bai taba hanata ba,duk da sannu a hankali ya fara fahimtar wasu kudaden da take karba setup ne kawai,yana yi matan, saboda kawai a lokacin bugatunta basa hawa kansa,kuma basufi qarfin samunsa ba.

Sanda ya gabatar da zancan aurensa ga Dr jarma hankalin hajiya garama yayi mugun tashi,ko kusa ko alama bata taba tsammanin zaiyi zancan aure a lokacin ba, babban abinda ya Sanya take sake ingiza Dr jarma akan yabar toufeeq ya nema na kansa kada ya sangarce ya shagala da dukiyar sa ba,ba komai bane sai don taja lokaci zuwa sanda HASEENA zata sake tasawa,ta zama mutum, kuma a nata lissafin sanda haseena zata gama nata karatun zuwa lokacin ya zama wani me fada aji,yayi irin kudin da take buqata daga mijin diyarta, tunda toufeeg din yana da wani irin nasibi da albarkar hannu.

Kiransa tayi tayi masa fada sosai bayan ta gama binciken wace ameesha?,diyar wacece?. Fadan da tayi masa ta bullo masa ta bayan gida ne

"A matsayin da mahaifinka yake dashi, da baiwar da Allah yayi maka,ai abun kunya ne ace kaje ka nemo aure a wannan gidan"

"Arzigin kaykkyawar nasaba shine arziqi bana dukiya ba,so ni banga abun damuwa ba mommy, please cool down" ya fada da I don't care manner dinsa.

Duk hanyar da zatabi don ta ruguza abun bai yiwu ba saboda rabo da Allah ya tsaga a tsakani,tana ji tana gani akayi auren, saidai kuma ta barwa ranta lallai saita ruguza abun ko ba dade ko ba jima, don ba zata bari ma haseena ta zauna da kowacce mace da sunan kishiya ba.

Tun lokacin shagalin bikin ameeshan ta fidda tsarukan biki na kere sa'a da kuma kashe kudade,yayi wasu wasu kuma yace bashi da kudi bazai iya ba.
Maganar data sosa ran ameesha, zugar tawagar qawaye kuma suka sake azata akai suna fadin

"Anya zaki qulla abun arziqi da mutumin nan?, ki dubi dukiya irin ta mahaifinsa amma ya dinga ambatar babu?, ina babu taga gurbin zama a family dinsu ma gaba daya?.

Washegarin ranar da Ameesha ta tare bayan sunyi first night dinsu,tana langabe a jikinsa saboda hannu da tasha a hannunsa tace dashi

"Mota nakeso a matsayin tukuicina na first night" gyara zamansa yayi

"A yanzun bani da kudin siyan wata sabuwar motar, motocina guda biyu,duk sanda kk fara fita kidauki guda daya aro kafin na samu sukunin siya miki". Tashi tayi ta zauna sosai tana kallonsa

"Nikam mamaki yake kamani idan kana cewa
BABU.kasan me wannan kalmar ke nufi? duk tarin dukiyar da Allah ya mallaka muku kai da mahaifinka?" Murmushi yayi ya girgiza kai, zuciyarsa na girgiza sosai da yadda ta iya buda baki kanta tsaye ta fadi abinda ya fahimci ya jima a zuiciyarta,yau ta amayar dashi da alama ta gaji da boyonsa
"Bana lissafi da abinda ba gumina bane ya tarashi ba,sanann ban isa nayi rabon gadon mutumin dake rayuwa lafiya lau cikin iyalinsa ba,duk abinda naga ya kamaci nayi miki zanyi miki gwargwadon wadatata ba wadatar mahaifina ba,nayi miki alqawarin ko sau daya ba zakiyi kukan rashin ci sha ko suttura ko kuma kudin da zaki biya bugatunki ba tare da almubazzaranci ba".

Hakan da ya fadi baiyi mata sam,tun a satin ta fara fushi dashi akan ya gaza siya mata mota,bata kuma sake bari ya tabata ba,har sai bayan wata guda da ya kawo mata motar har farfajiyar gidan. Ba kunya ba tsoron Allah ta ware,ta dinga murna tana waya da qawayenta tana labarta musu zuwan motar,ranar kyautatawa sabuwa tare da wani sakin jiki na musamman, tun a sannan jikinsa ya fara sanyi, tunani kala daban daban ya shiga kai kawo a ransa.

Watansu uku kacal ta soma ciwo wanda aka tabbatar musu da shigar ciki na watanni biyu, abinda bai taba kawowa ba,don kuka ameesha ta dinga yi,da yabi ba'asi babu kunya tace dashi

"Nifa ban shirya haihuwa yanzu ba,haba.....kamar wata akuya,aure wata uku kawai? ,bana tunani cikin friends dina da akayi aurenmu tare akwai wadda ke da ciki, sai kuma ni?duka duka ma sau nawa mukayi tarayya?, uku ne fa kawai" Kansa kawai ya kawar ransa yana baci zuciyarsa na masa suya Sosai,dazun kafin su fito ya raba rigima tsakaninta da hajiya qarama,ci mata mutunci tayi sosai abinda ya hanashi daukan mataki rashin lafiyarta,gashi yanzun ta sake dasa masa wani bacin ran

"Me kikeso yanzu kice?" Ita kanta kafin ta furta sai dataji shakka,saboda tasan halinsa sarai,idan ransa ya baci ko va baude bashi da dadin sha' ani,ciki ciki tace

"Kawai, kawai aje a zubar dashi, a sakamin implants,kamar nan da next two years sai a cire kafin na samu ciki na haihu aqalla munyi 4 to 3yrs" wani wawan birki yaja tsakiyar titi,saura kadan ya daki motar dake gabansu

"Ni inaso, kuma ina gaunarsa ko da dan qadangare zaki haifa,sannan ina miki rantsuwa da ubangijin da ya busamin numfashi, duk ranar da kika sake yimin magana makamanciyar wannan sai kin gane ni toufeeq asalin tataccen mara mutunci ne" daga haka bai qara ba ya tashi motar ya figeta da mugun gudu,har tana yin gaba kamar zata daki gaban motar.

Har suka isa gida bai sake kallon koda koda gefen da take ba,duk da kikan da taketa yi har da sheshsheqa.
Suna isa gidan ya fita a motar abinsa ya barta. Cikin watanni uku kacal tayi masa abubuwa masu tarin yawa,abu daya zuwa biyu yasa yake shanye komai,darajar so da zuciyarsa ke mata zalla mara algus kuma fisabilillahi, sai kuma mahaifiyarta da a kullum yaje gaidata ko yayi mata aike take bashi tausayi,bakinta baya gajiya da gode masa da sanya masa albarka tare da bashi amanar ameesha,don a koda yaushe takance bata dauke tsammani da mutuwar ta ba.

Yadda ya watsar da ita itama data gama kukan baqinciki kan yadda cikin zai kawo mata cikas akan sabuwar rayuwar morewa da more arziqin mazajen da suka aura da cikin zai kawo mata, taga baibi ta kanta ba kwana daya biyu har zata nema sulhu sai ta fasa,zugar qawaye da tarin shawarwari batakai marasa kan gado sukayi mata caaa a saman kai,sai itama ta watsar dashi taci gaba da rayuwarta.
Shawara daya ce tasu da bata zauna mata a kai ba,na tayi amfani da qwayar zubda ciki ta cire cikin kawai. Ita kanta tasan aikata hakan babban ganganci ne da kuma kuskure me tarin yawa a gareta,tunda tafi kowa sanin waye toufeeg din.



Zafafabiyar
πŸ”₯πŸ”₯πŸ”₯πŸ”₯πŸ”₯πŸ”₯

"HUGUMA*


β€’_TABARMAR KASHI_*

Book 02Page 56


Koda suka iso gidanma cikin motar yayi tafiyarsa ya barta bai kuma sake bi takan al 'amuranta ba,ya ajiyeta gefe saboda yadda tayi mugun bata masa rai saidai bai fasa sauke duk wani nauyi da haqgin ta ba, da kuma sauran bugatu da yasan mace me juna biyu zata iya buqata.

Fushi itama ta dauka sosai dashi, hukuncin data yanke na farko na qaurace masa a shimfida, abinda ta manta dama duka duka ina abun yake? sau nawa ta bayar da kai?.

Randa hakan ta fara faruwa migewa yayi ya zauna sosai ya kuma kunna fitilar dakin, idanunsa a kanta sanda take tattare kanta gefe guda cikin fushi

"Me kike nufi?"

"Kai tsaye bazan iya bane, tunda nima ba wai ina samun abinda duk zuciya takeso daga gareka bane"

"Okay" kawai vace da ita. Tun daga ranar shima ya ajiyeta a side ya shiga sabgar gabansa. Tun tana daukar abun da saugi tana kumbure kumburenta har ta fahimci duk inda ta dosa shi ya wuce nan, tilas ta fara neman hanyoyin shiri. Shirin nasu babu jimawa sai kuma Allah ya saukar masa da wani ibtila'i a cikin kasuwancinsa. Asara ya dinga samu daya bayan daya,kafin kace meye wannan?, komai nasa ya tafi sai abinda ba'a rasa ba. To duk sanda vanayi irin wannan ya faru dole a samu sauyin rayuwa abubuwan da aka saba yi a baya dole a sassauta wasu ma sugi samuwa don dai a samu a tsira da abinda yayi saura,a kumayi qogari da tanadin mai da rayuwa kan bigirenta na asali.

Sam ameesha tace batasan zancan ba, kawai dai yayi niyyar wulaganta ta ne da tozartata, kamar yadda mata da yawa ba kasafai suke iya fuskantar irin wannan yanayi ba idan ubangiji ya jarabci mazaje da shigarsa ba (akwai mugayen mazaje asalan,wadanda ba'a san samunsu ba saidai rashinsu, mazajen da basusan su yalwatawa iyali ba,suna da arziqi amma matansu saidai suji labari ko su gani a iya jikinsu su kadai, irin wadan nan koda ibtila'i irin wannan ya fada musu,ba kasafai ake zargin mace da kau da kai da rashin nuna tausayi a kansu ba,muddin namiji tsayayye ne wanda yake hidimtawa iyali da wahalta musu kaman toufeeq a labarin nan, to butulci na garshe da zaki masa shine ki nuna baki damu da shigarsa matsala ba,sanann baki zama matar rufin asiri ba, Allah yasa mu dace)..

A wanann lokacin da yake fafutukar gain yayi maintaining rayuwarsa tare da goqarin cike gibi da guraben da da wanann babbar gaddarar ta fada masa,daga gefe kuma ameesha na zuba nata lalatar kala kala. Ko sau daya bai taba yunqurin kaita qara ba,saboda tausayin mahaifiyarta da ko yaushe adduarta Allah ya qaddara dogon zama a tsakaninsu, mutu ka raba.

Cikinta yana da wata hudu kacal ta matsanta masa sai ya saketa, tace sam ba zata iya zama dashi ba,ta gaji da zama cikin talauci bayan mahaifinsa shahararren mai kudi ne, muguntar kai ko kuma girman kaine yake damunsa?, Da bazai shiga dukiyar mahaifinsa ya amfana da ita ba?,itama ta samu damar cika duka burikanta da muradan rayuwarta?.

Maganganun data fada a lokacin masu tsauri ne sosai da suka sosa masa zuciya. Daga daren har wayewar garin bata barshi ya runtsa ba, haka ya dauki takarda ya rubuta mata saki guda daya. Har zai fita ya dawo ya yanka mata zazzafan warning

"Koda wasa wani abu ya samu cikina,na rantse da ubangijin sammai da qassai sai nayi miki daurin da koda dukka qasarnan gatanki ne basu isa su karbeki ba".

Al'amarin ba qaramin farantawa haiiya garama yayi ba

"Ai duk mutumin daka ganshi a waje nan ne yafi dacewa da shi shi yasa Allah ya barshi a nan, ai duk inda talaka yake matsiyaci ne(ita ta manta tushenta),ni dama tunda naga idonta Muhammad nasan ba son Allah da ma'aiki takeyi maka ba,dukiyarka take so".

Baice

Please Login or Register in order to submit comment