Reading TABARMAR KASHI 1&2 complete by SAFIYYA HUGUMA Chapter 71 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kaf zamanin nan saidai tsakanin rabo don Allah karki sake magana makamancin haka akanta, inda kinsan me ta yiwa rayuwarmu mu duka da baki fadi haka ba" sanyi jikin hilma yayi, bata kuma sake cewa komai ba taja bakinta tayi shuru.

Washegari jikinta babu qwari ta tashi, amma a
daddafe ta shirya masa sassaugan breakfast ta koma daki ta kwanta. Sanda ya gama shirinsa na zuwa gidan maji,saboda a ranar nadeeya zasu wuce qatar da mijinta,ya bude breakfast din,sai baici komai ba ya hada ruwan tea ya sha ya fice,duk da zuciyarsa tanata otsa masa da son ganinta.

Itama bata jima ba bacci ya dauketa, koda ta tashi farkawa garfe dava na saura, mamakin kalar baccin da tayi ya kamata,ta shiga toilet ta wanke bakinta ta dawo tayi nata breakfast din tayi sallar azahar,duka sai wata kasalar ta sake rufeta, ko awa daya bata rufa ba wani baccin ya sake daukarta.

Stil ba ita ta tashi ba sai shida saura,a gurguje tayi la'asar tana istigfari,ta kalli agogo taba rayawa a ranta sauran mintuna kadan jirginsu nadeeya ya tashi.
Taso qwarai tayi ma nadeeya din rakiya, saboda ita din ganwar miji ce ta gari qwarai da gaske, wadda samun irinta a wannan lokacin sai an tona.

Samun kanta tavi da kunna wayarta da tun jiva
da zata kwanta ta kasheta,batason ma ta barta a kunne don ta tabbatar za'a yita kiranta ne ana daga mata hankali, yadda kuma taga yanayin toufeeq din kuma tayi imanin babu wani maganar ya barta fita a yau din.

Kamar jira akeyi kira kuwa ya shigo, nadeeya dince, muryarta can qasa ta daga

"Jikinne maami?"

"Alhamdulillah sister nadeeya da sauqi ai,ya taro?"
Raunana muryar nadeeya din tayi sosai

"Taro ya tashi maami, zamu wuce,ki yafemin...
." Sai kuka

ya qwacewa nadeeyar. Sosai zuciyar säahar ta raunana, itama muryarta na rawa amma lallashinta takeyi,daga gefe taji shigowar muryarsa

"Kiyi kuka ki sakata kuka? wanne irin shirme ne wannan?" Sai kuma taji wayar ta katse.

Kanta ta saka a gefan gado,sai kuka sosai ya
I gwace mata,kukan da take tasan bawai na nadeeya kadaj bane,wani raunin zuciya kawai takeji cikin girjinta,can deep inside her sabaninsu da toufeeq yana kassarata amma kuma taqi bawa zuciyarta amanna akan hakanne.

Ta jima a haka kafin tayi controlling kanta,ta miqe tana ninke abun sallarta, saita tsaya kalion kanta gaba madubi.

"Anya zata iya jurewa?" Ta tambayi kanta. Sai ta koma da baya ta zauna. A hankali ta fara tuna asalin faruwar matsalaryawan kiransa da yarinyar da batasan ko wacece ba takeyi,tun tana kau da kai har ta magantu.
Dariya sosai ya dinga yi kafin yayi mata bayani

"Ni ban santa ba, infact ma ban taba daga kiranta ba bare naji muryarta,ina dake bani da buqatar kowacce diya mace a duniya,so ki kwantar da hankalinki, a yanzun bana ganesu gaba daya". Hankalinta ya kwanta a lokacin, tunda tayi imanin baya magana biyu kamar yadda qarya ba dabi'arsa bace.

Ranar da ya rage saura kwana biyu bikin nadeeya,tana ta zagaye zagayen yadda zata gaya masa zasu tafi gobe, zasu kwana har sai an kammala biki, tunda tasan bayaso,bayan ya shigo sun gama welcoming nashi ya wuce wanka,ta bishi ta fidda masa pyjama din da zai sanya cikin sabbin pyjamas din data siya masa da kudinta. Tana zaune saman sofa kira ya dinga shigowa wayarsa,tun bata tsargu ba har ta tsargu, sai tasa hannu ta dauki wayar

"Soulmate" shine abinda taji an fada. Kalmar ta daketa sosai iya duka,amma sai tayi controlling kanta ta maida wayar ta ajjiye.

Daure da towel ya fito a gugunsa, jilkinsa sharkaf da lema data jige gargasa da sumar qirjinsa. Tana gaba madubi,ya risketa ya kama qugunta ya hade da nasa,ya dora kansa saman kafadarta yana kallon fuskarta ta dikin madubi

"Inason baby girl me irin fuskar nan sosai, yaushe zaki harama?" Sai taga kamar gatse yakeyi mata,don haka ta zame jikinta tana cewa

"Ni da haihuwa ba yanzu ba" sak yayi yana duban fuskarta sai kuma ya basar yaci gaba da qoqarin shirya kansa. Rashin tankawarsa sai zuciyarta ta
yunquro,shaidan ya dinga raya mata kamar akwai abinda ya taka shi yasa bai damu ba don tace haihuwa ba yanzu ba. Fita tayi tabar masa dakin, kafin ma yazo kwanciya ita ta gama shirya yara suna dakinsu tazo ta shirya itama tayi kwanciyarta.

Mutum ne shi bai matugar bawa dan adam uzuri qwarai da gaske don haka koda ya sameta a kwance sai shima ya shirya yabi bayanta.

Sanda va fara aike mata da sagonni sai ta tankwabe saqonsa,daga qarshe ma ta miqe tana sauka daga kan gadon, mafi munin abinda shi kuma yafi tsana kenan kaf rayuwarshi

"Mun zama second hand fa,a bari amarya tazo,gobe idan Allah ya kaimu zamu wuce gidan maji,sai kafijin dadin sakewarka da yin waya da soulmate din taka® shuru yayi ya zuba mata ido yana kallonta,duk maganganun da takeyi kuma taqi bari su hada idanu,sai kawai ya miqe ya dauki abinda zai dauka ya canza daki.

A daren ya dinga qoqarin cooling down kansa da kansa,har zuwa wayewar gari yana shirin fita sai gata, ta sake shaida masa zasu wuce fa gidan maji

"Ba da vawuna ba" abinda ya fadi mata kenan ya fice.
Yana office maji ta kirashi, ta kuma bashi umarnin ya dauko mata sãahar din da yara ya kawo mata su.
Bai tambayi ba'asi bai kuma musanta mata ba,ya katse duk abinda yakeyi ya koma gida ya daukosu kamar yadda maji ta fadi, saidai abinda ya fara daga mata hankali da taji yana waya,salon wayar da bata gamsu ba,saidai kuma bata gane da mace ne ko da namiji yake wayar ba.

"Zamu tafi" tace dashi tana dubansa sanda ya saukesun,jikinta yana danyin sanyi. Maganganun da ya gaya matan sune suka tsaya mata a rai matuqa

Ajiyar zuciya ta sauke tana jin ranta duka babu
dadi

"Astagfirullah" ta fada qasa qasa, tana hango rashin kyautatawar muraran. Knocking din baaba ramatu taji,sai ta bata izinin shigowa

"Sau uku ina kewayowa amma banji mitsinki ba,gashi dare yayi kuma ba'a dafa komai ba duk da tagwaye basa nan" dan murmushi ta saji,tana jin dadin kulawar da baaba ramatu ke basu

"Yanzu zan fito baaba, tare zamu sbiga kitchen din, a cire nama a freezer danye a zuba masa ruwan zafi"

"To shikenan, saikin fito" tace da ita. Gefan sofa ta koma ta zauna,ta jawo hula ta sakawa kanta,sannan ta miqe tsam tayi kitchen.

Duk da dare ya soma kawo kai, amma haka ta zage a nutse ta shirya masa dinner sassauqa amma ta musamman tare da taimakon baaba ramatu.

Har ta gama bataji shigowarsa ba, itama hakan
yayi mata dai dai, ta kammale komai ta barwa baba ramatu gyaran wajen.

Sai data gamsasa gidan da dukka nau'in turarukan da tasan yana so sannan ta wuce bedroom dinsa. Kintsashi shima tayi,bai wani hargitse ba duk da kwana biyu kenan Bata nan ta sanyayashi da turaren da ta tanadeshi ne kawai saboda bedroom dinsa sannan ta wuce nata dakin.

Kayan jikinta ta cire ta fada toilet, ta zuba man wanke gashi sosai ta wanke sumarta sannan tayi wanka ta fito.

Tanata sage sage tana gogarin busar da kanta a
gaban madubi tana kuma duba agogo, qarfe tara saura na dare, cikin ranta tana mamakin me ya tsayar dashi har kawo wannan lokacin bai qaraso gida ba.

Har ta ajiye Drayer din zata fara taje kanta taji an turo gofar da sauri lokaci guda ana kiran sunanta.

A nutse ta waiwaya,asad ne da as'ad sai kuma fadeela biye dasu. Kamar yadda suka saba, kowa rige rigen isowa gareta yakeyi, murmushi ya qwace mata tana dubansu. A rayuwarta kaf tanason wannan moment din,tana jin babu wata uwa data kaita a duniya.
Murmushin ta yayi dai dai da kallon bakin qofar dakin da tayi.


Zafafabiyar

"HUGUMA*

•TABARMAR KASHI_*

Book 02 Page 76


Yana tsaye bakin gofar dakin sanye da trouser da shirt charcoal color da yayi matuqar haska fatarsa.
Idanunsa a tsaye carr a kanta,yadda sumar kanta ta bazu a sassan fuskarta da farar lalalusar fatar jikinta sai ya zama kamar wani ado ne a gareta, fuskarta tayi fayau tayi kyau sosal.

Shi ya fara dauke idanunsa,ya juya a hankali da zummar barin gurin, zuciyarta sai ta karye

"Sannu da zuwa" ta fada da karyayyar muryarta,bai amsa ba yaci gaba da takawa yana barin wajen.

Sosai zuciyarta ta sake karyewa,banda yaran dake mararin ganinta ba zata iya ci gaba da tsaiwa bata bishi ba. Duk irin tsauri da zafin zuciyarsa zata iya cewa bata taba ganin fushi haka da I don't care manner haka a tattare dashi ba. A daddafe ta zauna ta biyewa shirmensu da hirarrakinsu,sannan ta samu ta tattarawa baaba ramatu sunata cewa

"Gobe zamu koma maii tace a hada mana kayanmu"

"Allah ya kaimu" tace da as'ad yafi kowa dokin komawar.

Cikin nutsuwa ta bude gaba daya closet dinta, idanunta akan kayanta daya bayan daya. Tsaida kallonta tayi akan was kaya,murmushi ya kubce mata, tana iya tuna ranar data sanya masa kayan, cak ya dagata sama ya juyata sosai,babu inda baiyi kissing a jikinta ba kafin labari ya sha banbam.

Tsaf ta shirya cikin kayan, ta tsaya sosai gaba madubi ta yiwa gashinta wani irin gyara me tafiya da hankali,sannan ta fesheshi da sassanyan hair mist.

Kayan abincin ta kwashe ta mayar sassansa, bata sameshi a falo ba, tayi imanin yana cikin toilet yana wanka,abinda bai taba faruwa a tsakaninsu ba kenan.
Kusan ko yaushe wankansu tare sukeyi,koda tayi nata wankan idan ya dawo sal ya batashi,wani irin mutum ne da tara vaara basa hanashi baje kolin soyayyarsa, baya tsufa da soyayva hakanan idanu basa hanashi nunawa matarsa qauna da kulawa. Ta godewa Allah da va bata maji a matsayin suruka,mace me fahimta wadda al'adarta tasha banban data bahaushe, tayi imanin banda hakan da tuni ta fara ganun canjin fuska saboda kukawa gauna da tattali da yake nuna mata. Tana da kawaici qwarai da gaske, a kullum bata gajiya da sake iadda masa girman amanarta dake wuyansa.

Kafin ya fito ta gama kai kawonta tsakanin sassanta da na yaran,ta tabbatar ta sallamesu, kiwa yayi shirin kwanciya dukbda weekend ne goben sannan ta wuce sashen nasa.

A nutse ta bude bedroom dinsa, har yanzu still yana toilet, saboda tana iya jin qarar saukar ruwa. Zare hijabin jikinta tayi ta aje saman sofa. Dakin takebi da kallo _r a nutse,ko na kwana daya ta masa daga dakin sai taji tayi kewarsa,tana mamakin vadda ameesha ta iva rabuwa da toufeeq,yana da shiga rai ya kuma hada dukkan wasu. qualities na miji na gari. Matsawa gaban dressing table dinsa tayi tana gyara turarukan da ya zube akai,gefe kuma qaramar jakar ce me kyau dauke da tambarin company din da yayi siyayyar. Daya daga cikin kwalaben ta daga, favourite turarenta ne, siyo mata yayi kenan?, ta tambayi kanta,duk da yana fushi da ita amma hakan bai sanya ya manta ko ya wofantar da duk abinda ya shafeta ba

"Shi din na musamman ne" zuciyarta ta gaya mata hakan
"Good men still exist one of them is mine" ta fada a fili hadi da lumshe idonta tana rungume turaren a qirjinta.
Baivi zaton ganinta ba sanda ya bude gofar amma maganar da ta furta gasa gada ta shiga kunnensa,can gasan zuciyarsa wani abu me sanyi ya saukar masa, baqin gashinta me qyalli idanunsa suka fara sauka a kai sannan a hankali suka sauka zuwa gadon bayanta da fiye da rabinsa yake a bude fara tas din fatarta ta dace da launin bagar rigar jikinta.

Ta cikin madubin take satar kallonsa,tsayyayen jikin dake gine da wasu muraddun muscles, tashin farko taji kewarsa ta cikata. Wani irin mutum ne shi mai
•r tsayawa a zuciya a kowacce tarayya zakayi dashi.

Cikin sa'a ya lura da satar kallonsa da takeyi ta gasan ido duk da ta fara fusgar hankalinsa amma sai ya dauke idanunsa daga kanta 'yan miskilancin suka motsa.

Qaramin towel ya saka yana goge ruwan sumarsa data jikinsa,sumar kansa mai santsi da laushi duk ta cakude,yaja stool ya zauna gaban dressing table din daura da ita har yanzun kuma bai dubi sashenta ba.

lya maqura haqurinta ya gaza,ta ajjiye kwalbar
turaren hannunta, ta taka a hankali ta zagaya bayansa.

Qaramin towel din hannun nasa ta rige da kyau,suka hada ido ta cikin madubin, saita dage masa dukka girarta biyun. Bugawa zuciyarsa ta danyi yana jin wani abu yana bin sassan jikinsa,ya lumshe kyawawan idanunsa yana sakar mata towel din salin alin, ita kuma ta zare towel din a hankali ta dorashi saman sumar tasa.

Cikin wani irin salo ta soma nutsa yatsun hannunta cikin sumar tasa,a hankali ta soma yamutsata cikin wani irin yanayi da ya tilasta masa rufe idanunsa ruf yana jin duk wani motsi na zara zaran yatsun nata har cikin kwanyarsa.

"i feel bad for making you sad am sorry for making you loose your temper, sorry for being rude and hurting you with my words,i promise not to repeat it ever" idanunsa 5° ya lumshe yana jin zagin kalamanta. Tana da baiwar iya kalami mai sanyaya zuciya da cire duk wani fushi da bacin rai duk da shi dama bawai har vanzun vana fushi da ita bane,a'ah,he want to teach her lesson.

Ci gaba tayi da yamusa gashin nasa tana kuma tayar da kowacce tsiga ta jikinsa. Ganin yayi shuru bai amsata ba sai ta dan bubbuga qafa a shagwabe

"Kace wani abu pleaaaaaaaassssseee.i can go to any extent to make it up to you,am sorry from the bottom of my heart,please better half..... forgive me manaaaa,)
miss your sweet voice, your hug and your smile,sorry for hurting you" still har yanzu ya kasa bude idanunsa,duk da zuciyarsa kamar zata fito daga qirjinsa yakeji wani wata irin soyayya me motsa zukata,tare da tsananin shauginta da yakeji, muryarta kadai na neman rikitashi. A nutse ya bude idanun nasa ya watsasu a kanta

"Ba wani, baki sona,bakin sadaukarwa da wata ni ba?"
Kuka ta sake ta sake masa tana bubbuga qafafunta a gasa tamkar qaramar yarinya, abinda ya bawa boobs dinta damar motsawa qwarai yadda zata samu damar jan hankalinsa sosai.

Burinta ya cika,don gaba daya kasa motsawa yayi daga inda yake zaunen, sosai take masa shagwaba tana tsaye daga gabansa,shi kuma ya lalace a kallonta yana jin yadda zuciyarsa ke bugawa da sauri da sauri.

A nutse ya miqe yana gyara zaman towel dinsa a qugunsa,sannu a hankali yake takowa a nutse saiji tayi ya sakata cikin jikinsa,ya rungumeta tsam ta baya.

Kusan lokaci guda kowannensu ya saki ajiyar zuciva ya dora tattausan tafin hannunsa saman ruwan cikinta ya fara yawo da su yana shafa fatar saman cikin wani yanayi yana ratsashi.

Hannu daya ya saka yayi gefe da gashinta sake fake va barbazu a bayan nata. Cikin wani irin yanayi dake nuna zallar shaugi da yadda qauna ke kassafa jiki jini da bargo ya dora labbansa saman wuyanta, abinda ya sanyata daukewar wuta sama numfashinta na wasu daqiqu kafin ya dawo dai dai

"No matter what happens you will always remain my biggest priority" ya furta mata da wani sirrintaccen sauti da ita kadai ta isa ta jishi.

) "No bodv above mistake,you are a wife material na sani, sometimes i look at you and i wonder How i got to be so damn Lucky" sosai kanta ya fasu,sai fa dinga jin duk duniya babu macen data dace da miii irinta"

"I will make up for all the days i ruined baby" itama ta maida masa cikin yanayi na rad'a hadi da sakar masa dumin numfashin bakinta.

Zafafabiyar

TABARMAR K'ASHI


HUGUMA

BOOK 02
PAGE 77 END


Wani numfashi ya aje mata da ya ratsata har cikin kunnenta,sai ya sake mannata sosai da jikinsa ya mayar mata shima cikin rada

" melt when you call me baby"

"And i like when you call me yours" ganqameta yay cikin jikinsa kamar zai maidata su hade su zama abu guda

"You are mine and only mine, all rights reserved" ido ta lumshe zuciyarta na dandana zaqin kalamansa,tanaji kamar ta sanya hannu ta fiddo zuciyar tata ta miqa masa

"Mohhhh" ta kirashi da wani sirrintaccen suna da ita daya ke kiransa da shi a irin wanann yanayin

"SAHR" ya amsa mata shima ilkinsa na amsa sagon da take aika masa dashi a fakaice ta sautin murvarta da tsaiwarta cikin jikinsa

"I really want to kiss you,and not just on the lips"

kaman an fusgeshi da lantarki yaji, sai ya sake qangameta da kyau kafin ya saketa, yaja baya sosai yana bude hannuwansa gaba daya kamar wanda yake jira ayi hugging nasa sanann yace

"Kiss me moonbeam,kiss me iya yadda kikeso, I don't care if it's 5minutes or a whole night,i am always ready to cheer you up,no matter the time place or situation"
•cikin wani irin taku me janye hankali ta garaso gabansa,ta Sanya hannunta ta rige gefe da gefan fuskarsa,sanann tayi dage don ta samu isa ga bakinsa saboda ya fita tsaho

"No...wait" ya fadi da sauri, hannunta ya riqe da kyau ya dagata ya dorata saman qafafunsa, ta tsaya sosai a kansu,ya tallafo qugunta ta baya yadda ba zata fadi ba tsaiwar kuma zatayi mata dadi

"Thank you" ta fada tana hade fuskokinsu guri guda.
Yadda take sauke masa salon kisses kala kala ya
sake narkar da zuciyarsa cikin gaunarta,tun suna a tsaye a hankali har tsaiwar ta gagaresu suka zube saman gado.

"I Know you want me but I want you to tell me" ya fada numfashin yana fusgarsa, ko ina na jikinsa yana rawa

"I want you,i need you...." ta fada itama lafuzzan suna rarrabe mata saboda bugun da zuciyarta keyi da qarfi sosai. Daga nan ya kasa ci gaba da bata dama,ya fara maida mata zazzafan martani, wanda shi yayi jagorancin kaisu wata duniva me nisa wadda daga shi sai ita suke iya fahimtarta.

Tsahon rabin awa kafin komai ya daidaita,jinsa shuru baice komai ba sai saukar numfashinsa me dumi a fatar ilkinta ya sanyata motsawa,da sauri yace

"Shshshis..... don't move,when i am holding you,the whole world makes sense" sake gyara mata kwanciya yayi sosai a jikinsa,dumin jikkunansu yana ratsa kowannensu

"Ki qaramin lokaci,inason wanann yanayin,i prefer silent conversation,ones our bodies speak and our hearts listen" birkota kanta da kanta tayi fa juyo tana fuskantarsa,saita shige cikin jikin nasa sosai ta kwantar da kan nata a qirjinsa tana lumshe ido hade da murmushi. Wannan ya bata damar jin qamshinsa sosai,ta zuqi numfashi tanajin dadin qamshin kamar yau ta fara ji.

Yatsantsa daya ta saka tana wasa da gargasar qirjinsa

"Mohhh" ta sake kiransa a nutse

"Am all ears"

"Am jealous" wani qaramin kyakkyawan miskilin murmushi ne ya qwace masa

"Yes i know"

"Ehhnnn?" Ta fadi tana buqatar qarin bayani, zamewa yayi a hankali yana boye fuskarsa tsakiyar qirjinta

"Am sorry NUGGET,na fada ne kawai saboda nayi tsokana,saboda kada ki tafi, but bazan sake cewa zan kawo wata ba gidan nan, banyi alqawarin bazanyi ba, amma banayi da sha'awa bana kuma fata har abada"

"I can't bare to loose you"

"Zamu zama a tare har abada" kalmominsa sun wanke mata rai fes sai ta sake narkewa a ilkinsa. Migewa yayi da hanzari

"Gate up nugget" ya furta yana qogarin dagata tana dariya qasa gasa hadi da sake narke masa.


******Washegari**


Tana farkawa hayaniyarsu da kakacinsu ne ya isketa har kan gadonta, muryar toufeeq asad da as'ad sai fadeela. Kai ta girgiza a hankali tana sakin murmushi, qarfi da yaji sun maida abby din nasu magananne wani lokaci ita dinma ko da ta gudu ta barsu sai sun zagulo ta Wayarta ta daga ta kalla tana murmushi, babu arziqin da ya wuce wannan a rayuwa,samun lafiyayyen family me cike da farinciki da qaunar juna,ga arizigi da wadatar rayuwa.

"Ikon Allah" ya furta a hankali, saboda kwanan wata yana nunawa yau hajiya qarama ta cika kwanaki arba'in da rasuwa. Wayarta ta ajjiye tana sauka daga gadon tana ji a ranta ya kamata suyi mata sadaka na kwanan arba'in din.

Toilet ta wuce kai tsaye don ta tabbatar gidanta a gyare yake fes sannan breakfast ma ya kammala, abinda kawai zatayi gyaran bedrooms dinsu. Cikin mintuna qalilan ta gyare bedrooms din nasu. Wani kyakkyawan zama sukeyi wanda zaka samu Muhammad toufeeg jarma kamar bashi ba cikin gidansa. Yana iya zagewa su gyara duk part din da suka kwana a ciki fadeela na tayashi.
Säahar takan jima tana mamaki har wataran yace

"Komai isa dukiya da taqamarka a wajen matarka
holoqo ne kai, sannan komai izzarka da jin ka isa kai din ba kowa bane idan bakayi koyi da fiyayyen halitta ba,yace mafi alkhairinku shine mafi alkhairinku ga iyalinsa,shin bazan so na kasance mafi alkhairi ba nima don ranar gobe na shiga jerin sahun mutanen da prophet Muhammad S A W zaiyi alfahari dasu ba?" A ranar har qwalla sai da tayi.

Kwata kwata idan ka kwantanta rayuwar ADAN da
TOUFEEQ misalin rayuwar matacce ne da rayayye. Takan rasa da wanne irin kalmomi zata godewa Allah da bata shi da yayi.

Tana shiryawa bayan ta fito daga wankan tana tuna jinyar hajiya qarama, har ta mutu bakinta yanason fadin wasu maganganu amma kuma Allah bai bata iko ba,saboda ba'a ji ba'a kuma gane abinda take fada, saidai duk sanda taga wani abu da ya shafi dr ko toufeeq tayita kallonsa tana hawaye, idan taga su asad kuwa tayita son kama hannuwansu kenan.

"Allah yasa muyi kaykkyawan qarshe" säahar ta fadi tana warware sabuwar lafayarta 'yar borno me tsananin kyau da tsada.

Haka kawai yau tayi sha'awar yi masa kwallivarta da safe,tsaf ta nade jikinta da ita,ta kuma lullube gashinta me tsaho da santsi wanda ta zubo dashi gaba ya rufe rabin goshinta ta zagaya dashi vabi ta bavan kunnenta ta kuma daureshi da babban ribbon.

Best perfumes nashi ta yayyafawa jikinta sannan ta dauki wayarta ta fito.

Idanunta na akan wayarta, bata lura da shi ba saida sukayi clashing. Dukkansu sukaja baya suna kallon juna, babu abinda yazo zukatansu sai rayuwarsu a MT JARMA GLOBAL COMPANY.

Baya yaja ya harde hannayensa a qirjinsa yana mata wani azababben kallo from head to toe,ba abinda yake masa yawo a kai sai sanda take irin dressing din nan,ganinta na farko da ya farayi a mt jarma a matsayin president dinsa.

"Wanne irin mutum ne kai mara kirki mara iya mu'amala? wanda baisan kima da martabar dan adam ba? me yasa dukkan zancanka kudi? me yasa kake hangen kudi sune gaba da komai?" Ta fada tana tsuke fuska tamkar a lokacin abun yake faruwa. Takowa yayi a hankali yana sauke dogayen yatsun qafarsa saman
Tallausan carfet din hallway din. Gabanta ya iso ya sulale yana sauke dukka gwiwoyinsa a gasa hadi da hade tafukan hannayensa guri daya ya kawosu saitin bakinsa

"Am sorry mr president, am arrogant, ki yafemin" kai ta dauke gefe

"Nooo, you are fired" dariya ta qwace masa ya mige da sauri ya dagata cak yana dariya

"Baki isa ki koreni ba, zan karba kora daga kowanne guri a fadin dunivar nan amma banda daga nan wajen" ya fadi yana nuna saitin zuciyarta da yatsarsa. Dariya itama sosai ta qwace mata tana sake rigeshi

"Nasha wahala qwarai da gaske don duk sanda kikazo da shigar laffayar nan haka kawai sai naji zuciyata tana zafi, kuma gashi kullum ina sake qoqarin tabbatarwa kaina komai bai hadamu ba,coz na tsorata da na kasa jin haushi da tsanarki a zuciyata kamar yadda nakeji ta sauran dukka mata at once....... shigar na masifar yi miki kyau da qara miki kwarjini,zaki iya tuna ranar da na kori jamal?" Kai ta gyada don ta tuna
"Kamashi nayi yana hirar kyan da kikeyi da laffaya,sannan kina boye dirinki ne a ciki, ranar kwana nayi da zazzabi, kamar zan mutu haka naji, but ban gane so bane, rabon dai sai na sha wahala kafin na sameki" murmushi ta saki tana jin dadin labarin, uwa uba kuma tana a jikinsa ne yana takawa da ita zuwa parlor

"For the first time na hadu da macen da kudi kyau ko matsayi basa gabanta,na hadu da mace me sadaukarwa irin sadaukarwar nan me tsada sadaukarwar da za'a yi maka ita a boye ba tare daka sani ba,ta warware min tunani na na dukka mata mayun kudi ne,zasu iyayin komai saboda kudi,ta dauki dukiyarta tayimin hidimar da kudi bai isa ya biyata ko ya siyeta ba.....sanda kikacemin zakiyi aure ne ba zaki dawo kici gaba da kula da fadeela ba.....kinsan saura kadan zucivata ta fashe? sanda kikace kin amince zaki aureni kinsan yaya naji?" Kai ta girgiza,sai ya kada kai kawai yana murmushi, don baisan yadda zaiyi mata bayani ba

"Baki da wayo da gaske na yarda, baki taba tunanin me yasa naqi yarda muyi yarjejeniya cikin aurenmu ba?"

"Gayamin please, don ka yaudareni da gaske fa abby"

dariyar da ita daya ke samun irinta ya saki
"Ban aurenki don mu rabu ba,koda banason mace bazan aureta don mu rabu ba,hakanan malamai sun tabbatar duk auren da aka daurashi bisa wani sharadi ki yarjejeniya to wannan auren BATACCE NE"

"You are the real definition of deciever"

"Na yarda indai a kanki ne"

"Abby......yara fa, saukeni" ta fada da

Please Login or Register in order to submit comment