Reading TABARMAR KASHI 1&2 complete by SAFIYYA HUGUMA Chapter 52 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

hakan daga garesu ba"

Kamar wanda aka yiwa wahayi da tahowarta,ya cira kansa a hankali idanunsa suka sauka a kanta

"Ya salam,ya Allah" ya furta a fili qasa qasa. Idanu ya kafeta da shi yanason banbamce shigar mayafin data hijabin

"Ba abinda ya buya" wata zuciyar ta gaya masa,wannan kyan yana nan a muhallinsa d gurbinsa,cikakkiyar halittar da a yanzu yasan ainihin cikarta da zatinta sai yake ganin tamkar kiwa na iya ganinta ta cikin hijabin nata,boobs din da yake qoqarin ganin sun buya sai idanunsa ke nuna masa su muraran,wani abu ne nauyi yaji ya sauka aqirjinsa ya sauke hannunsa yana yarfar dashi sannan ya ratsa ta tsakanin hajiya qaraman da meenal ya nufesu.

A hanya sukayi kacibus, kowa idanunsa cikin na dan uwansa,fadeela ta wuce gaba abinta ta tafi gaida hajiya qarama,wadda a yanzu sai zata fita school suke haduwa,sabanin lokutan baya da duk safiya sai an kai mata ita kafin ta wuce makarantar.

"Babu ta yadda za'a iya boyesu ne?" Yayi mata tambayar yana riqe qwayar idanunta cikin nasa,wanda taketa shirin gocewa hakan. Cikin rashin fahimta da dan hadewar fuska tace

"Me?" Idanunsa ya sauke akan qirjinta, da sauri takai dubanta kai,sai tasa hannu tana daga hijabinta ta saitin gurin hadi da ja baya tana kuma sake hade rai

"Ummmm?" Ya sake fada da sigar tambaya.

"Bana so" ta fadi cikin jin haushi,taku biyu yayi gabanta yana qare hade tsakaninsu

"Nine dai bana so, banason kowa ya kallesu Allah zan iya hadiye zuciyata, they're mine" A mamakance ta kalleshi tana zare ido, tanason tace wani abu ma ta kasa, bai kuma bata dama ba,sai ya sake matsawa gabanta,a hankali yasa hannunsa ya jawo hijabin saman habarta wai ko hakan zai rage mannuwarsa a jikinta yana sake kallon girjin nata

"Damn it!" Ya fada gasa gasa,sai ya zura hannu ya karba lunch bag din fadeela,ya sake saka hannu ya zare school bag din nata sannan ya juya ya fara tafiya. Juyowarsa ta sanya hajiya qarama dauke kai daga kallonsu wani abu yana bugun zuciyarta was canje canje take gani a tsakaninsu wanda batasan meye silar afkuwar sa ba.

Meenal kuwa kuka takeson saki hajiyan na mata nuni da kada ta sake tayu,haka ta dinga hadiyeshi tana ji kamar tana hadiyar zuciyarta,zuciyar tata kamar zata fashe.

"Barka da safiya" sahar tace da hajiya qarama,sai da tayi namijin qoqarin dai daita kanta sannan ta jefa mata wani kallo

"Barkanki dai,ya ayyuka?" Yadda ta kira ayyukan ya yiwa säahar kama da gatse, sai tayi kamar bata jita ba, tayi gaba dai dai lokacin da ya bude mata seat din gaba. Sai data kalleshi cikin mamaki ya dage mata dukka girarsa biyun,bata ce komai ba ta shige ya tattara mata hijabinta ya rufe mata motar.

"If you are not ready to go ki koma ciki" yace d meenal da takaici va sanyata tsaiwa a gurin, tabota hajiya qarama tayi sai ta taka ta bude murfin motar ta shige. Sahar na kallonta ta cikin madubi, haka kawai yau din taji kanta ya fashe, gyara zamanta tayi tana kauda kanta gefe.

"Set your belt" ya furta a nutse yana gyara zamansa.
Kasa jira yayi ya miqa hannunsa da nufin jawo belt din ya daura mata,wanann ya bawa hannnun nasa damar shafar qirjinta. Daga shi har ita ba wanda jikinsa bai amsa ba,haushi ya kamata,tana tsammanin zai janye,sai taji ya garasa kwantar da fin rabin jikinsa a kanta. Da sauri ta daga kanta ga hajiya qarama dake tsaye saitin window din nasu,idanunta fes a kansu tana gain komai,ta dauke kan nata da sauri ta maida gareshi, tanason magana ma amma ya matseta sosai jikin seat din, yanata kokawar sanya belt din amma har yanzu baikai ga sakawa ba.

Bugun zuciyarta ya fara qaruwa saboda gaba daya kusan a fakaice rungumeta yayi, saita sanya hannunta tana son tureshi, saidai kafin takai ga aikata hakan ya saka belt din da wani irin hanzari,ya kuma kama dukka hannuwan nata ya rige cikin nasa va sauke mata tattausan kiss saman lips dinta abinda ya sanya hajiya garama rufe idanunta da sauri ba tare data shirya ba

"Kwana biyu,kwana biyu ko?"' Ya fada qasa qasa, tasan me yakeson fadi ,yanason sakayawa ne saboda meenal dake cikin motar. Da sauri sukaji an bude murfin motar kuma a wani irin fusace,bata iya tsaiwa ba ta kwasa tayi cikin gidan da mugun gudu, abinda ya yanke tsaiwar hajiya qarama a gurin,tabi bayan meenal din cikin sassarfa.

Tashi yayi ya koma mazaunin driver yana sakin murmushi
"Ko kishin kanki baki dashi? a gaban idonki na bawa wata lift?" Ya fada with softness yana shirin kunna motar
"Kishi? god forbid" kadan ya waiwaya ya kalleta, kaman zaiyi magana sai ya fasa murmushi ya sake kubce masa
"Alright,zamu gani, amma dai yanzun ai na taimakeki da korar miki ita,ko banza kya shaqi numfashi me kyau" kasa amsa masa tayi saboda gaba daya ya yamutsa ta a fakaice,kuma batason taci gaba da amsa masa fadeela ta fahimci wani abun. Kawai dai abu daya ya bata mamaki driving da yakeyi yau da kansa abinda bata taba gani ba, sai daya fita sauran motocin suka taso suka rufa musu baya,biyun kuma sukayi gaban tasu.
A yau din bayan sun isa company,su biyu kadai suka wuce zuwa ciki. Dukka ma'aikatan kowa goqarin gaidashi yakeyi cikin girmamawa,abinda yadan basu mamaki shine yadda yake amsa gaisuwar tasu a yau kadan kadan, musamman ma'aikata mazan. Hatta cikin elevator su kadai ta dauka har zuwa building dinsu. Baya yaja yana kallonta,fa fahimci abinda yake nufi tayi gaba kenan, dauke kai tayi gami da noqewa kamar bata fahimci abinda yake nufi ba. A nutse ya tako ya garaso kusa da ita,ya sanya hannunsa ya rigo nata hannun yana hade tafukan hannayensu guri daya. Cikin sauri ta daga kanta ta kalleshi,ta kuma fara yunqurin zare hannunta daga nashi. Jifanta yayi da wani irin kallo sannan ya girgiza mata kansa alamun a'ah,bai sake saurararta ba ya jata a tausashe suka fita daga elevator din.
Kusan duk inda suka gifta sai idanun jama'a sun bisu da kallo,wani irin mugun matching sukayi a safiyar tare da wani sassanyan kyau dake cakude da annuri saman fuskar kowannensu. Wanna kallon da ya lura ana binsu da shi ya sake jagula masa lissafi,sau uku yana canza mata side,from left to right, from right to left.
Cikin kamalarsa yayi sallama cikin lobby na office din nasa, mazaunin saima kenan. Da kuxarinta ta dago tana amsawa, harda gyara zamanta, saidai kuma kafin takai ga garasa amsa sallamar komai ya magale mata a wuya,da qyar ta tattaro kalmomin
"Good morning sir"
"Morning" ya amsa mata yana wucewa kai tsaye ga office dinsa,har a lokacin kuma bai sake mata hannu ba "Sir,kowa kai yake jira,dukka suna hall din" saima tayi qarfin halin fada tana jin wani abu me daci saman harshenita. Sai a wanna karon ya waiwayo,kallo yayi mata irin wanda ya saba yiwa kowa, amma sai taji wani dadi a ranta,saboda takan jima bata samu wannan damar ba
"Monday ne dama?" Ya tambayeta cikin kokwanto. Sai data hado wani murmushi saman fuskarta sannan ta gyada masa kai tana lumshe idanu
"Yes sir" tana gama fada jibril yayi knocking ya nemi izini sannan ya shigo
"Sir, kowa yana jiranka"
"Okay" ya amsa yana gyada kai

"HUGUMA*


• TABARMAR KASHI*

Book 02 Page 36


A nutse da wani irin sanyi ya maida dubansa gareta,wani sashe daban take duba bashi ba. Har gasan ransa yaji bazai iya tafiya ya barta cikin office din ba, kamar bai gaji da kallonta ba
"Madam" ya kirayeta da wani irin amon sauti me laushi da sanyi. Tsigar jikinta tadan zuba saboda canzawar sautinsa a yau din, amma sai ta fuske kamar bata jishi ba.

Ya matsu ya Kalli qwayoyin idanunta,yanason yabar mata wani saqo me nauyi da narka zuciya,kamar yadda ya sani, sauran mata ma suka sani, idanunsa nada wani irin mugun tasiri da maganadisu me qarfi dake narka zuciyar mata da yawa,ya kuma tafi da tunaninsu. Uwa uba yana matuqar qaunar idanunta, tun a shekaran jiya daya qure musu dukkan kallo harda wanda ya wuce qa'ida ma idan akwai,kallon cikin idanunta na tuna masa yanayin da suka shiga gaba daya shi da ita a wancan ranar,yadda komai ya canza cikin lokaci qanqani. A ranar ya fara tabbatar da kyawun qwayar idanun nata.

Hannunta ya saki kawai sai ya rigo qugunta, sai gata
tsaye a gabansa suna fuskantar juna. Kanta kawai ta
sunkuyar ta hanashi kallon fuskarta bare akai ga idanunnata, abinda ya hanata kowanne yunquri na qwatar kan ta shine Karantar da tayi saima tana wajen

"Da mutane fa a gurin nan" ta fada qasa qasa wai don
kada saima din taji, saidai abinda bata sani ba,yadda tayi
cooling voice dinta ya sanya yaji tsigar jikinsa gaba daya
ta tashi,yadan ja wani numfashi hade da sheshsheqa

"| know, just i want to look into your eyes......please" jin
abinda ya fada ya sanyata maida idanun nata ta kulle
gam, tana nufin ba zata bashi wannan damar ba,har cikin zuciyarta abinda tayi niyya kenan, indai idanunta yakeson kalla zai bushe a wajen saima ce kawai ta zalunceta data ci gaba da zama a gurin, tana pretending kamar bata ganinsu,ita kuma tayi imanin dukka hankalinta yana kansu,banda ita da tuni ta tureshi daga riqetan da yayi.

Zanen fuskarta ya shiga kallo daki daki, tun daga
kyakkyawan eye brows dinta,miqaqqen hancinta mar
tsaho da tudu, shape din idanunta da kuma eye lashes
dinta masu tsaho ya dire zuwa kyawawan lips dinta da
suke yawna fuzgarsa,duk yadda yaso ya daure ya kasa

"Your lips look so lonely, would they like to meet mine?" Babu shiri ta bude fararen idanun nata tarr bisa fuskarsa da suka cika da tsoron kada ya aikata din. Qaramin murmushi ya subuce masa. Fuskarta ya kama ya hade fuskokinsu guri guda, abinda ya Sanya saima ba shiri cikin rawar hannu ta kwashe takardun da bata gama tabbatar da ingancinsu ba ta bude qofa ta fice

"Am dying to have my lips on yours one chance please!"

Duka garfinta ts tattaro ta turashi tana yin baya,numfashi take maidawa hadi da sanya hannunta daya tana gyara zaman hijabinta

"Why all these ne wai?, why?" Ta tambayeshi cikin zafin rai, zuciyarta na gaya mata shi kuma jikinta kadai yakeso, sha'awar ta kawai yakeyi, bashi da aiki sai burin son taba jikinta?.

Da baya da baya yaja ya jingina jikinsa da bango yana rufe idanunsa, tuni kowacce jijiya ta jikinsa ta amsa

"You stole my heart" ya fada can qasan
maqoshinsa,labbansa kadai sune suka motsa. Itadimma lallabawa tayi ta zauna zaman kujerun dake gurin, tsahon wasu mintuna shuru ba wanda yace da kowa komai,yayi ta maza yana qoqarin binne komai a ransa ya mige ya tsaya saman qafafunsa ya fara takawa

"Let's go" ya fada a taqaice, sai ya kasa ci gaba da tafiya sanda ya isa bakin qofa,ya tsaya har ta qaraso. Lalubar hannunta ya sakeyi ya hade da nasa,ta ja zata fincike yace

"'Kina cirewa ban yafe ba" laqwas taji zuciya ds gangar jikinta tavi, bata da wani sauran zabi sai ci gaba da binsa da tayi.

Kamar ya koma haka yaji lokacin da suka isa hall din, bai dauka zaman meeting din da mutane da yawa ba haka idanu sukayi caa a kansa shi da ita dukka suka mige suna masa barka da zuwa. Da ka ya amsa yana jin nutsuwarsa na raguwa. A nutse y jawo hannunta ya jawo kujerar da aka tanada saboda zaman CEO ya matso da ita gabanta,ya zaunar da ita a kai sannan ya koma bava ya tsaya yana dafe da kujerar, tamkar yaron gidan da uban gidan nasa.

A schedule na meeting din one hour ne meeting ne, amma cikin mintuna talatin ya sallamesu. Yadda suka shigo yanzunma haka suka koma office din yana riqe da hannunta,wannan shi ne ya zama muhimmin topic na tattaunawa a cikin company din a ranar.

Tunda suka dawo duk bavan minti dava zuwa biyu sai ya daga kai ya kalleta. A duk sanda ya kalletan kuwa sai wani abu mai qarfi ya fusgeshi tattare da ita. Wasu lokutan har sai ya tsaida abinda yakeyi ya zuba mata idanu yana kallonta cikin wani irin nutsuwa da wank lamari me matugar qarfi kaifi da kuma zurfi cikin zuciyarsa.
Bata fahimci komai ba, kawai ta fuskanci yau din yana ta sanyata zurga zurgar dauko wancan ajjiye wannan.
Yayi amfani gwarai da wannan damar wajen samun damar morewa kallonta ta yadda ranshi yakeso.

A karo na barkatai ya sanyata dauko masa wani book cikin tsararriyar book shelf dake gefen table dinsa,saidai akwai tazara tsakaninsa da ita. Sanda ta miqe don isa gurin sai ya daga kansa gami da ajiye biron dake hannunsa,a hankali yake sake qarewa tafiyarta kallo, komai nata unique ne, bai taba cin karo da mutum me uniqueness irin nata ba.

Ta maida hankalinta sosai tana duba masa littafin da
ya aiketa ta dauko din,ba kuma wai don zaiyi karatu bane,a'ah,kawai yanason yaga wannan kyakkyawan takun nata. Yadda take tura baki da bata rai saboda bataga book din ba ya sanyashi sakin murmushi yana jin wata gajiya da kasala suna bin sassan jikinsa,wanda shi kansa yasan ma'anar hakan a tattare dashi. Ya miqe a nutse yana sanya hannayensa a aljihun wandonsa, har ya isa gareta bata sani ba. Daga bayanta ta tsaya, dab da ita,tazarar data rage a tsakaninsu duka baifi taku daya rak ba.

Muryarsa ya sassauta sosai ya kuma rage tsahonsa yana son daidaita kanshi da ita ya dawo da kansa saitin kafadarta,cikin laushin murya tamkar wanda yake a buge yace

"Am so tired,can you give me a hug pleasssssse" cak ta dakata daga abinda takeyi tsigar jikinta tana tashi,yadda yayi maganar saitin kunnenta ta shigeta sosai,sam sam bata tsammaci tsaiwarsa a wajen ba,saita qame a tsayen, bata juyo ba bata kuma ci gaba da neman littafin ba. Ragowar taku dayan da ya rage shi ya qarasa, cikin sanyi da tashi ya zura hannuwansa ta saman cikinta.va kuma jawota a mugun slow ya manneta da jikinsa. Kamar wadda aka yiwa allura ta zabura tana juyowa da sauri da nufin kufcewa,saidai kuma babu damar kuncewar saboda yayi mata zobe gaba da hannunsa. Kai tsaye idanunsu suka jone guri daya,ya lumshe nasa idanun tare da budesu lokaci daya yana sakin wani lafiyayyen siririn murmushi da ya sanyata kasa jurewa kallonsa saboda wani tsalle da zuciyarta tayi ta kuma ce mata

"He was elegant" kanta takeson kawarwa amma ya hanata wannan damar,ya kama fuskarta ya riqe da kyau yana mata wani duba dake dauke da tarin ma'anoni masu wuyar fassarawa,wanda yakejin tamkar bakinsa bazai iya fadinsu ba

"Hold me please hold me so close, that your breath become my oxygen" ya fadi numfashinsa na fita da sauri da sauri saboda yadda ya kwadaitu da labbanta. Bai iya controlling kansa ba kuwa sai daya dangane da bakin nata kaman dazun,ya shiga sauke mata hot kisses ya hanata katabus da dukka wani yungurinta na qwatar kanta. Har tsahon wani lokaci kafin ta samu nasarar tureshi, taja baya tana kallon idanunsa da nata idanun da hawaye ya cikasu taf yana gab da gangarowa. Bai wani damu da kalar kallon da take masa ba, yafi damuwa da yadda bata qaunar ya rabi jikinta,wanda a yanzun yakejin cikin zuciyarsa bazai iya wani dogon zamani ba tare da ya rabeta ba,ji yake kamar wani magnetic ne a tsakaninsu. Murmushi ya sauke mata da idanunsa da suka sakeyin wani irin laushi

"Your eyes driving me insane madan ki daina kallona haka" ya furta yana gyara zaman sumar kansa da yatsunsa

"Only you can give me that feeling" ya furta a nutse idanunsa har yanzu cikin nata idanun da bata iya gani sosai saboda qwallar cikinsu.

Ba tare da kowannensu ya sakeyin komai ba sukaji an tura qofar office din, sautin takalma masu tsinin dunduniya ya soma tashi kafin daga bisani muryarta ta bayyana cikin sallama.

Har cikin jinin jikinsa sai da yaji wani abu ya tsarga,lokaci daya gabanin yakai ga juyowa dukka wata walwala da nishadi da ya samu a yanzu suka fara narkewa. Säahar ke fuskantar qofa,don haka da ita idanunsu ya fara jonewa.

Fara tas din mata, wanda har haskenta yaso zarce haske na dabi'a,tana da wani irin kyau shimfidadde akan fuskarta,saidai kuma a gangar jiki, irin matan nan ne da basu da hips kwata kwata,duk kuwa da cewa ita din ba wai siririya bace amma rashin hips din nata bayyananne ne ga duk wanda yasan tsarin halitta a gurin mace. A shape gown ce a jikinta ta wata shadda 'var mali komai na jikinta cike yake da ado da gawa

"Sãahar, nanny N ko?, i see" ta furta tana jifan sahar da wani irin kallo, zallar kyawun da bata tsammaci samunta a tattare da ita ba yana bugar son bugar da ita,tako ina tana hangen wasu qualities kai tsaye daga gareta ta cikin hijab dinta kai tsaye, kyan suffa ciki da waje wanda cikin qasa da minti biyu wani azababben kishinta daya ninka wanda take ji a kanta kafin ta ganta ido da ido va lullubeta.

Farat daya kwanyar säahar tayi mata recalling muryar, take kuma ta fahimci wacece, idanunta ta maida kan toufeeq wanda tashi daya kamanninsa suka canza da wani irin bacin rai da zallar tsana

"Barka da warhaka uban 'yata" ta fada tana rangaji tare da jifansa da wani irin shu'umin kallo da tasan yanaso ada

"Kar ka damu yanxu am single, naje na dawo kuma dukka don saboda kai" zare idanunta sãahar tayi daga kansu,tanaji a ranta bata da bugatar sauraren kowa a cikinsu,bata son jin komai daga bakinsu, don ba matsalarta bane, kowa yaji da matsalarsa, kuma kowa ya rige damuwarsa don haka ta fara takowa da nufin ta isa ga gurbinta na dazu ta dauki takalminta da hand bag dinta.

Cikin jikinsa yaji tahowarta, zuciyarsa kuma ta gama gaya masa abinda zatayin, ficewa zatayi ta barshi da ameesha,fuskar da ya jima da shafe babinta cikin rayuwarsa. Rabuwa yayi da ita har ta garaso dab dashi, bata taba tsammanin yana ganinta ba,sai kawai ji tayi ya tattarata cikin jikinsa yayi mata wata kyakkyawar runguma. Mamaki ya hanata motsawa, sai kuma yadda kunnuwanta suka jiye mata adadin qarfin bugun zuciyarsa da ya qaru matuqa, ala dole tayi luf tana jin bugun sosai cikin kunnuwanta,abinda zai shaida maka lallai yana cikin fushi

"'Baki yarda da gargadin dana yi miki ba?" Duk da zuciyarta ta qone sosai da kalar rungumar da ya yiwa sãahar din wanda ita daya tasan gardinta da dadinta, da
kuma sirrin dake tattare da wannan ingarman girjin nasa
data jima tana kewa,ta kuma gaza samun
kwatankwacinsa acan inda take harin

"Babu me rabani da kai sai Allah moha..... you are mine
forever" cikin nutsuwa ya dauke kallonsa daga
kanta,yasa hannu daya ya jawowa sãahar kujera ya
zaunar da ita a kai

"'Huta a nan" ya fada cikin kulawar da sai da Ameesha
taji kamar numfashinta zaiyi skipping na wasu daqiqu.
Tasan toufeeg ciki da bai fiye da kowa,soyayyarsa
kulawarsa da tsantsar iya ririta mace wani abune da ta
gama lalube daga gurin kaffff mazan data hadu dasu
bata samu wanda yake da koda rabin rabinsa baya
tattara abubuwa masu yawan da sai an tara maza dari
ba'a samu qwaya daya rak irinsa ba.

Wayar da ake kiran security kawai ya danna ya koma
ya tsaya kusa da sãahar kamar wanda yake bata kariya

"Inason ka bani dama mu fahimei juna, nayi maka kuma
bayani mu yafewa juna na dawo na kula da 'yata" runtse
ido yayi,ju yayi kaman ta soka masa wuqa a qahon
zuciyarsa,har bayason ta furta fadeela diyarta ce.

Bazai iya bata yawun bakinsa ma a kanta ba sai yaja waya yayi kira zuwa wajen saima

"Come in" ya fada a kausashe yana ajjiye wayar saima da security uku suka shigo, mata biyu namiji daya
Migewa yayi sosai iyakar tsahonsa yana dubansu,hatta säahar satar kallonsa take ta qasan ido,yadda lokaci daya ya koma Muhammad toufeeq jarma din data sani farkon haduwarta dashi, kaman ba shine yanzun nan ya gama karyar da wuya da murya a gareta ba

"Who allowed that women to enter?" Kallon kallo aka fara a tsakaninsu,kowa yana tsoron magana yana kuma tsoron gaddarar yau ta fada kansa ta kora daga aiki, duk da cewa tunda ya dawo din ko ma'aikaci dava bai kora ba.

"We are sorry sir, don Allah, bamusan bakason ta shigo ba" daya daga cikin matan tayi qarfin halin fada zuciya a karye

"Take her outside, and daga yau,idan na sake ganin gilmawar fuskarta cikin kamfanin nan ku tabbatar kun rasa aikinku" yana kaiwa garshe suka cafketa su biyun,don kuwa ba zata jaza musu asara ba,don kaf fadin kano dama Nigeria basajin akwai company da zasu samu me dadin aiki da kuma albashi me tsoka wanda yayi kamanceceniya da kamfanin MT JARMA.

"Ni ka wulaganta haka?" Abinda ta iya fadi kenan saboda tuni suka garasa yin waje da ita. Sai a sannan ya waiwayo ga saima ,wadda kallon idanunsa kadai ya sanyata taji kamar zata saki fitsari a wandonta

"You are fired" ya fada kansa tsaye. Ya jima yanason rabuwa da zaman yarinyar cikin office dinsa,amma ya rasa da wanne irin laifi zai kamata,sai yanzun da wannan dalilin yazo.

"Nan din ba Bar bane ko club da zaki dinga barin mata anyhow suna shigo min,bayan kin sani tare muke aiki da iyalina a ciki" yayi mata bayanin yana juya baya ba tare dava dubeta ba. Kuka ne ya hanata cewa komai, kawai saita juva da gudu gudu ta fice saboda ta gama tozarta tako ina a gaban idanun matar da take bala'in jin zafinta da tsananin kishinta,wanda ita sam saiman bata cikin damuwarta a rayuwa.

"HUGUMA*


"_TABARMAR KASHI_*®

Book 02 Page 37

Yana jin qarar rufe gofar saima ya tako zuwa gaban saahar din, saman qafafunsa ya tsugunna vana dubanta da wannan zafin da har yanzu baibar saman fuskarsa da kuma zuciyarsa ba. Kauda idanunta tayi daga kansa tana jin wata shakkarsa tana shigarta,scene din da ya gabatar yanzu a nan ya sake tabbatar mata har yanzu TOUFEEQ JARMA shine dai,a gareta ne kawai ya sauya.

Yatsunsa ya sanya ya dawo da fuskarta saitin tata fuskar, sai ta sake kau da kai,ya sake maido fuskar tata ta sake kawarwa,a karo na uku ya sake juyo da ita a zafafe sannan yace

"Idan kika sake juyamin qeya sai na miki hukuncin da na fahimci shi kikafi jin toro,idan baki wasa ba saidai a kawo wheel chair a daukeki, kada ki manta ina da sofas masu taushi a resting room" izzarta ce ta motsa,ya akayi ta bari ya karanci ta tsorata da abinda yayi mata?. So take ta gaggaya masa magana, amma ta sani daga qarshe yamutsatan da batason yayi shi zai aikata mata

"Na kusa kawo qarshen komai" ta fada qasan ranta a fili kuma tana hade rai

"Wayonki da tsiwarki dukka yau na rainasu, saboda baki kishina saiki bar duk wata karya da godiya su dinga tunkarar mijinki gaba gadi ko 'yar shakkarki basa ji saboda sunsan lusara ce MATAR TOUFEEQ?" Da gayya ya kira mata lusarar saboda ta motsa wani abu dake danqare a zuciyarta,yaci nasara kuwa,don take bacin rai ya bayyana

"Ko ba komai ya kamata su dinga jin shakkar tunkarata
haka kai tsaye saboda KE"

"'Ina ruwana da abinda ya shafi rayuwarka?,rayuwarka
daban tawa daban,ka taba ganin anyi kishin abinda ba'a so?, ba'a kuma damu da shi ba?" Ta fada itama gaba gadi. Murmushi ya saki karon farko shima zuciyarsa a yau ta dandana dacin kalmar RASHIN SO da kuma QIYAYYA. Kai ya girgiza

"Tashi mu tafi gida" ya furta yans miqewa tare da ja baya ba tare saya sake bi ta kanta ba. Ranta a quntace itama ta tashi tana jin haushin maganar da ya gaya mata, bataso yabar zancan iya haka ba,sai gashi yayi kamar komai bai faru ba.

Baice mata ci kanki ba a mota har suka dauko fadeela suka wuce gida yana jinsu sunata sabgarsu,bai ce musu komai ba kuma bai hanasu ba. Yau din sun koma da wuri, yana zaune a motar yana kallonsu har suka qule a sassansu fadeelan, kai ya jinjina

"Zanyi maganinki" ya fadi qasa qasa, kafin ya kashe motar,ya barwa jibril key din a jiki ya fito yana cewa

"Kada kayi nisa,zamu sake fita kaman nan da one hour"

"Okay sir" ya fada cikin girmamawa.

Falon wayam,har yanzu Jacob bai dawo ba, hakanan har yanzu bashi da tsayayyen gurin cin abinci. Bai tsaya dogon nazari ba ya wuce bedroom dinsa,don yana matuqar bugatar ganin Dr jarma a yau din,don a gobe yace masa zaiyi tafiya,morning flight zaibi, dukbda dai har yanzu bai gaya masa inda zashi ba, kusan kuma basu saba hakan dashi ba, shima bai matsa da tambaya ba, kasancewarsa mutum ba me bun qwaqwafi ba yasan idan ya dace yaji tabbas zai gaya masa. Ya fara zare kayansa, idanunsa suna bisa gadon Duk lokacin da ya kalli gadon babu abinda yake tuna masa sai wancan moment din, wani abu guda daya da

Please Login or Register in order to submit comment