Reading TABARMAR KASHI 1&2 complete by SAFIYYA HUGUMA Chapter 65 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta fada tana ciro wayarta don ta sanya a sake samar musu wani
dakin wannan din kamar wata dama ce a wajenta da
wajen sãahar dinma gaba daya,zata sake waana Dr
jarma da kyau,itama kuma sãahar din zata samu
cikakken hutu,zasu kuma sake fahimtar juna tsakaninsu ta sake samun damar da zata shirya kyakkyawar alaqa tsakaninta da toufeeq din.

Tunda yaji maji ta fadi haka ya kasa sukuni,yayita
goqarin kallon qwayar idanun säahar din don yayi mata alama amma bata ko kalleshi ba. Cikin jikinta tasan za'a rina hakan indai toufeeq dinne da yake jin kansa kamar tuzurun da yayi aure kwanan nan, to amma ita kanta tana da bugatar hutun ko don su tsira da abinda take dauke dashi din karo na uku a rayuwarta shi kuma karo na biyu.

Har akayi la'asar bai samu wanna damar ba, duka ya shiga damuwa walwalarsa ta ragu,sajjad na ankare dashi,yaji komai daga bakin afifa,ba abinda ya rage masa illa dariyar da yaketa boyewa,har suka idar da sallah,ya gama azkar dinsa, haqurinsa ha gaza,ya cire wayarsa ya tura mata gajeran tex

"please ki gayawa maji fa, bazan iya ba,Allah bazan jure ba"

Wayar na hannun afifa,sun gama waya kenan da maama data duba jikin fadeela da na sãahar din gaba daya, Murmushi afifa ta saki tana miga mata wayar. Sai data kalli fuskar afifa din sannan ta karba wayar ta karanta saqon,tana kaiwa qarshe ta daga kanta ta kalli afifan suka hada ido, saita watsa mata harara, dariya ce sosai ta qwacewa afifa

"Meye zaki nade tabarmar kunya da hauka a kaina? munafukai,kun gama gulmar baku son juna Allah ya toni asirinku shine zaku wani dinga dojewa,ni kinga tafiyata gwara naje naji dumin hayatee daga nan na duba fadeela ko ta tashi" ta fadi tana rolling mayafinta doguwar rigarta a kanta.

Fitar afifa ya maida dakin shuru, maji ta shiga wajen fadeela,Dr ya fita tun dazun, nadeeya kuma na saman abun sallah tana sallah. Gyara zaman wayar tayi a hannunta tana tunanin amsar da zata bashi, ita kanta tasan akwai rikici, har ta shiga gurin tura saqo aka tura gofar dakin aka shigo.

Muhammad toufeeq ne, hannunsa daya cikin aljihun wandon lallausan yadinsa, idanunsa carrr a kanta,yayi wani sanyi da laushi da yasa zuciyar saahar cika da mamaki,kawai don maji tace zata wuce da ita shi ya hautsina shi haka? wanne irin so ne haka?.

A nutse ya iso gaban gadon, kai tsaye ya yiwa kansa guri a gefan gadon shima kusa da ita, kafadunsu har suna gogar juna. Da sauri ta dubeshi tana masa nuni da nadeeya dake zaman tahiya zata sallame, sai ya daga mata gira murya can gasa

"And so what?" Ya fadi gaba gadi abinsa, hannunta ya lalubo ya rige cikin nasa

"Maji so take kawai ta horani yadda take hora Abba, dazu sailad vake gavamin va maida aurensu.lalurar fadeela yasa bamu sani ba" wani lafiyayyen murmushi dake qarawa fuskarta kyau ne ya kubce mata,bayan samun nasara a alkin fadeela wanzuwar cikin jikinta wannan shine labari na uku da yayi masifar sanya farinciki a zuciyarta. Kaman zaice wani abu sai ya waiwaya sashen da nadeeya ke zaune

"Tashi ki bawa mutane guri munafuka" ya fadi vana dan fidda fararen idanunsa waje. Batasan ya akayi ya fahimci ta sallame sallarta ba, sosai taso jin gulma shi yasa tayi kaman zaman tahiya takeyi, tanason taga wanna salon boyayyar soyayyar tanason taga salon soyayyar yayanta Classy anty N da muskilin yayanta yaa moha, ta tabbatar wanna kalar soyayyar zata kasance ta musamman,sai gashi ya baro jirginta. Hakanan ta miqe tana ninke abun sallar tana satar kallonsu har ta fita a dakin.

Dariya ce sosai ta kama nadeeyan,afifa dake fitowa daga dakin fadeela sukayi kacibus

"Lafiya sister nadeeya?"

"Anty afifa,wadancan mutanen,wai dama suna so suke kaiwa kasuwa?" Baki afifa ta tabe tana dariya

"Ko ba bestie ba, gulmammu, kowa ciwon dake ransa kadai ya sanyashi jin babu wani da zai sake burgeshi, basusan ita zuciya ba'a ci mata alwashi ba"

"Zo kiga don Allah" nadeeya ta fada tana yafito afifa.
Hannuwanta afifa ya daga tana dariya

"Wallahi bazan iya leqensu ba karna ganowa kaina abinda yafi qarfina" dariya suka sanya su duka suka wuce dakin fadeela tunda zaman dakin säahar din yafi garfinsu.


Zafafabiyar
"HUGUMA*


• TABARMAR KASHI_*


Book 02 Page 61


Shuru ne ya ratsa dakin, nauyi kallon da yake mata ya yiwa idanu da gangar jikinta, saita zame idanunta zata sunkuyar da kanta qasa.

"Mom twins" ya furta a hankali yana jin farinciki yana ratsashi. Qaramin murmushi ta saki a kunyace tana maida kanta gefe,sai yasa hannu ya juyo fuskar tata

"Ki gayawa maji ba zaki ba.......am telling you akwai matsala, komai zai iya faruwa kika bita" fararen idanunta ta daga ta kalleshi tana dan bata fuska

"Maji din? i can't* sosal ya sake zubawa fuskarta ido,sai tadan ja da baya kadan tana sake dubansa

"What do you want from me?" Ta samu kanta da furtawa ta yadda labbanta kawar ya iya kalla ya fahimci me tace

"I want to wakeup to you every morning and fall asleep to you every night ban shirya bin tsarin maji ba,please help me, tell her zaki iya warkewa koda muna tare" ya qarashe maganar yana sake matso da fuskokinsu kusa dana juna,har tana iya jin fitar numfashinsa sosai.

Idanunta ta lumshe tana jan ajiyar zuciya

"Bazan iya gaya mata ba" ta fada a shagwabe, har sai da tsigar jikinsa ta zuba

"'Zan gaya mata ni, zance mata ni dake duka bama so"

I "No please"

"'Whay?" Ya tambayeta still idanunsa suna cikin nata suna wani irin narkewa da gaunarta

"Inajin kunya"

"Ni kuma bana ji" wani garamin kukan shagwaba da
batasan daga ina yazo ba ta shiga sauke masa, take ta soma kunnashi,jikinsa duka ya amsa. Hannu yasa ya jawota ta fada jikinsa, sautin qaramin shagwabben kukan nata yana sauka a wuyansa yana ratsa tattausan gashin fuskarsa yana taba kunnensa kadan kadan

"If you kiss my neck, am not responsible for what
happens next" yayi maganar kamar yana rada mata a kunne. Da sauri ta janye fuskarta daga gareshi, amma sai yayi caraf ya rigota yana ritsata da narkakken kallonsa

"| crave you emotionally and physically do you even
realize how amazing you are to me?" Kasa bashi amsa
tayi, saboda kalamansa suna mugun kashe mata jiki tare da dasa wata sassanyar soyayyarsa mai matugar garfi a jininta

"Am sorry" ya sake cewa,yadda yayi maganar ya sakata daga kai ta kalleshi

"Sorry for what?"

"For loving you too much" dukka hannayenta ta bude ta zagaye bayansa dasu,ta kuma kwantar da kanta a girjinta, sosai take iya jin bugun zuciyarsa cikin kunnuwanta,da muryarta mai laushi da wani irin nutsuwa tace mishi

"Kalamanka suna da zagi kamar zuma,All very sweet,i'll never get enough of you,i want to spend the rest of our lives together, baka qetare iyaka bai feel the same way and i can prove it to you in sha Allah" ta qarashe maganar tana cusa kanta a tsakiyar qirjinsa saboda nauvinsa da takeji.

Kamar me jin bacci haka ya dinga lumshe ido saboda zagin da kalamanta sukayi masa

"You're the only person who makes me smile constantly" ya furta yana qoqarin daga fuskar ta daga qirjinsa,a sannan yaji ba abinda yake buqata irin ya dandana lips din da suka furta masa wadan nan kalaman masu zaqi

"Your lips on mine tell me better than your words" ta fahimci kiss yana daya daga cikin weakness dinsa,kuma babu abinda zai hana maji tafiya da ita,don haka ta bashi cikakken hadin kai tare da maida masa martani me kyau.

Basusan me vake faruwa sai muryar maji da sukaji tana fadin

"Subhanallahi" shi ya fara zare fuskarsa daga tata tare da rigeta da kyau don kada ta firgita. Basuga maji din ba sai gofar data maida ta rufe da sauri tare suka dauke idonsu daga kan qofar suka mayar fuskokin juna. Tuni kunya ta lullube sãahar,ta kebe baki zata masa complain, ya dora yatsansa saman lips dinsa da sukayi jaa

"Shshshsh" vace da ita saita maida maganar da tayi niyyar yi din, abinda ya bashi daman gyara mata gashinta da ya hargitse. Yanayi yana kallon cute face dinta,ba magana a tsakaninsu sai bugun zukatansu kawai, kowa na tuna tarayyarsa tare da dan uwansa.
Yana gyara mata yafen mayafinta nadeeya ta tura gofar ta shigo,ya juya ya watsa mata wani kallo saita koma ta lafe tana cewa

"Maji ce ta aikoni,wai anty N ta fito"

"Bacemin daga gun" ya fada adan zafafe, sai ta juya ta fice tana gunshe dariya. Tunda taga maji ta fito tana
maimaita salati tasan tayi gamo ne.

Ba jimawa wayarsa tayi qara,daya duba yaga maji ce dole ya daga

"Okay to,in sha Allah" yace yana ajiye wayar,sai ya miqe yana zube hannayensa a aljihunsa yana dubanta,sai kuma ya miga mata hannun nasa, ba musu ta dora nata hannun saman nashi ya rige da kyau ya tasheta tsaye.

Duk inda suka gifta sai idanu yakai kansu tsakanin turawan dake kai kawo cikin asibitin, sai daya kaita gurin fadeela sukayi sallama sannan suka wuce gurin ajiyar motoci na asibitin inda taxi ke jiransu. Da kansa ya bude mata back seat kusa da maji,ya mayar ya rufe ya matsa baya yana folding hannunsa a qirji. Duk duniva banda maji ba wanda zai yadda yayi masa hakan,yana tsaye yana kallonsu har motar ta tashi suka fice a asibitin, ya bita da kallo yana jin kamar wani sashe na iikinsa ne aka tafi dashi

"Mr man" ya tsinci muryar sajjad daga bayansa, koda ya waiwayo sai ya dinke fuskarsa tsaf saboda yasan tabbas tsiya sajjad din zaiyi masa

"Muje ka rakani wani guri" yace da saijad din,sai yayi gaba yana biye dashi shima dai dariyar yake boyewa.
Kafin su isa already ma'aikatan hotel din sun gama shirya dakin. Sanda Dr jarma yaga maji na maida luggage dinta dakin sai ya kalleta

"Kada ki fara shifa indai baso kike muyi abun kunya a gaban surukarki ba" kallon shakulaton bangaro ta watsa masa

"Ai ba damuwa"

"Haka kika ce?" Ya tambayeta,sai bata amsa masa ba kawai tayi gaba abinta.

Tunda maji ta shigo dakin sam sãahar ta kasa sakewa,kunyar yadda ta gansu dazu ne keta dawainiya da ita.ko hada ido da ita ta kasa. Itama majin ta fahimci hakan ta kuma tabbatar idan tace tare zasu kwana zata kwana ne a takure,sai ta aika nadeeya toilet tace ta hada mata ruwan dumi ta shiga tayi wanka.

Shigar nadeeya toilet din sai ya zamana saura su bivu.a tausashe maii din ta kira sunanta.ta amsa ba tare data lya daga kanta ta dubeta ba

"Ki saki jikinki dani ba abun kunya kikayi ba,mijinki ne kuma lada zaki samu, saidai abu daya nakeso, ki kula da kyau saboda mu tsira da wadan nan bayin Allahn,nasan me yiwuwa ne moha bame haquri bane a take takensa dana gani, that's why na daukoki,kina cika kwanaki goman da likita ya fada zan maida masa ke, karki biye masa azo ayi aikin dana sani" kai ta gyada a mugun kunyace, dai dai sanda nadeeya din ta fito tace ta gama, ta miga mata babban towel ta zauna shirya musu abincin da aka kawo musu daga restaurant a hotel din.

Tare da maji din sukaci abincin dare,Dr mahmud na dakin hajiya garama yana fama da koke kokenta da a yau yakejin kamar yayi mata dukan tsiya,yana mamakin yadda ya dinga dauke wadan nan abubuwan nata tsahon shekarun, bai kuma taba ji ya gajiya ba sai yanzu?.

Maji tanata kaffa kaffa da sãahar din, sai data tabbatar taci abinci da kyau,ta kuma tambayeta bata bugatar komai sannan tayi musu sallama ta fito.

A qofar dakin sukayi kacibus da dr jarma,sukabi juna da kallo,sai ta kauda kanta tana mamaki, da gaske zaije ya taho da ita din kenan?, tana jin sanda ya saki ajiyar zuciya tare da wani qaramin murmushi ya juya ya rufa mata baya.

Sai da suka dan taba hira da nadeeya kan yadda fadeela ke sake warwarewa da farincikin da yarinyar ke nunawa duk sanda aka gaya mata ta daina irin faduwar nan da takeyi

"Kinsan daxun me tace?" Kai säahar ta girgiza tana murmushi

"Bansan waye nafiso tsakanin anty N da abby dina ba" murmushi ya kubcewa säahar, Allah ne kadai yasan me ya ajjiye tsakaninta da fadeela tun bata wani santa ba amma Allah ya jarabceta da tausayin yarinyar, kafin daga bisani a hankali ya koma gauna, gauna tamkar ta d'a da uwa

Sai sha daya saura na dare sannan suka kwanta
kowa saman gadonshi. Dakin ya dauki shuru,sai dim light da nadeeya ta sanya musu,a hankali sai kwanyarta ta tafi tunani, ta maida idanunta ta lumshe. Ba abinda ke mata kai kawo sai fuskar toufeeq a mabanbantan gurare, tun daga farkon haduwarsu har zuwa yau cikin Saarland university hospital.

Doguwar ajiyar zuciya ta saki, tana gyara
kwanciyarta da taji sam batayi mata dadi ba,saidai duk da gyara kwanciyar da tayi hakan bai sanya taji dadin makwancin nata ba

"'Wai kewarsa nake?" Ta tambayi kanta cike da dimbin mamaki

"'Yes you missed him" wani sashe na zuciyarta ya bata amsa. Idonta ta sake lumshewa tana hasaso taushi dumi da kuma sassanyan qamshin dake fita ko yaushe a jikinsa

"Da gaske ni munafukar kaina da kaina ce" ta fadawa kanta da kanta qaramin murmushi yana subuce mata
Ashe duk yadda taje avoiding nasa a baya duk sanda yayi nufin rungume ta,ashe da gaske da yace tana pretending pretending din takeyi

"Ya Allah" ta fada gasan ranta tana runtse idonta. Sansa ta bude idanun nata ta danna wayarta don duba lokaci.

Har sha biyu saura na dare, ta sake maida idonta ta kulle ranta yana jagulewa gaba daya,wani matsanancin kewarsa tana ratsata har zuciyarta na quntata sosai. A karo na biyu ta sake bude idanunta, hakan yayi dai dai da hasken da wayarta tayi,ta miga hannu ta jawo wayar tana dubawa.

Sunan nan nasa ne da nadeeya tayi mata saving a wayarta ya bayyana. Tayi dan Jim,sai kuma taji ta cika da zumudin ganin abinda sagon ya qunsa,ta bude a nutse ta duba

_how are you?_ yace a taqaice, ta sauka qasa a hankali ta maida masa amsa a taqaice itama,ranta yana mata babu dadi, saboda ta saka ran jin kalamansa masu dadi da sukafi haka dadi a zuciyarta,saita tarar da gajeran
sago

_am fine_ ta amsa tana maida idanunta ta lumshe, qasa da second biyar taji alamun shigowar wani sagon

_are you sure?_ tabe baki tayi kaman zata saki kuka,saita maida masa still a taqaice

_"yeah i said am fine"_. Wannan karon ko idanun bai bari ta rufe ba ya maido mata amsa

_tell me the truth_

"Haka kawai zuciyarta tayi rauni, idanunta suka cika sosai da qwalla, kewarsa takeji ba dan kadan ba,a gaggauce ta maida masa itama

_i miss you okay?‚i miss you so much, and it's killing me_

Qaramin murmushi ya saki vana sauke gafafunsa dake saman qaramin glass table din dake gabansa,tsam ya miqe tsaye yana zura wayarsa cikin aljihun ya wuce can cikin daki ya jawo luggage dinsa ya soma cire wasu kayan yana fidda na jikinsa.

Minti daya biyu uku har minti goma tana jiran taj§ amsa daga gareshi amma shuru kakeji,ta rufe idanunta ta kuma bude har batasan iya adadi ba, qwallar da take

•I rigewa sai gata tana saukowa,me yasa ta zura jiki haka ta fallasa masa sirrin zuciyarta?. Sanda ya cika mintuna talatin sai ta gaza daurewa,ta sake daukan wayar ta rubuta wani sagon a tagaice

_hey,why are you not replying?_ tana turawa ta saki ajiyar zuciya tana dora wayar saitin fuskarta. Minti daya tak wayar ta qara haske

_am sorry. Am here front of your room, come outside and see me_ miqewa tayi ta zauna ba tare data zata ba tana raba ido, saita maida idanunta bakin qofar tana tantama. Taba qofar kadan taji anyi, mamaki sosai ya cikata,ta zamo a hankali daga saman gadon ta zura slippers ta nufi qofar dakin,ta murza key din ta cireshi daga jikin qofar, kafin ta bude har ya murda handle din qofar ya turota,sai taja da baya tana dubansa ta hasken waje daya ratso dakin mamaki yana kasheta.


Zafafa biyar

"HUGUMA*


_TABARMAR KASHI_*

Book 02 Page 62

Murmushin nan nasa dake gara masa kyau ya kasheta dashi,sannan ya dora yatsansa saman lips dinsa

"Kina mamaki ne?,zan iya binki ko ina kika tafi, no matter how far it is" ya qarasa fada yana ratsawa ta gefanta zai. wuce. Har yazo tsakiya ya tambayeta

"Maji tana ciki ne?" Kai ta gyada masa tana boye darivarta gasa gasa, baice komai ba sai ya fidda wayarsa daga aljihunsa ya kunna torch ya haska daya gadon da garamin haske. Waiwayawa yayi ya jefeta da wani salon harara me dauke da wani nau'in kallo

"Inda maji dince, zan roqi alfarma ne kawai wajen abba,nasan shi zai fahimceni" yayi maganar yana isa makunnin fitilar dakin ya kunna,yasan abu guda kenan
dake tayar da nadeeya daga bacci komai nisan da tayi.

Take kuwa haske ya gauraye dakin dai dai da sanda ta motsa tana mitstsika ido

"'Anty N,tashi kik....." Magale mata maganar tayi ganin mutum a tsaye tsakiyar dakin, duk da ya bata baya amma ta fahimci toufeeq dinne, saboda yanayin tsaiwarsa daban take

"Tattara kayanki ki koma dakin wancan matar garama ki kwanta" ya fadi ba tare da ya waiwayo ya dubeta ba.

Salin alin ta sauko daga gadon bayan ta lalubi garamin hijabinta ta zura,ta saka slippers dinta tana rungume da duvet da wayoyinta tazo ta rabasu zata wuce

"Saura naji kina bada labarin nazo" ya fada a dake yana wani shan gamshi

"Ba'a bakina ba yaa moha" ta fada tana qara wuta. Tana jiyo sanda ya maida qofar ya kulle, murmushi kawai ta saki,gaba daya yaa moha din ya sauya, da alama dukkansu soyayyar data tashi kamasu batayi musu da saugi ba.

Yana gama rufe gofar ya juya ya kashe wutan dakin sannan va sanya hannunsa ya dagata cak, bai sauketa ko ina ba sai tsakiyar gadon nata. Idanu ta fidda sanda taji yana qoqarin duvet

"Amma...

"Shshsh....a nan zan kwana"

"Maji fa?"

"'Itama tana gurin mijinta, infact ma bani da gurin kwana sai inda matata take........sleep please" ya fadi yana zuge zip na gaban rigarsa gaba daya har gasa ya ballesa,sannan ya sanya hannu ya zame sleeping dress din jikinta ta wuya ya saukar da ita har zuwa cinyoyinta,ya sanya qafarsa a tausashe ya qarasa zameta har zuwa gafafunta,sannan ya hade fatar jikinsu guri daya,suka samu good skin to skin contact.

A tare suka saukar da ajiyar zuciya,wata irin nutsuwa taii ta saukar mata lokaci guda hadi da kasala da wata tsumammiyar gajiya da batasan da ita a jikinta ba

"Good night moonbeam-may your rest be complètely
peaceful" sai ya karanta addu'o'i ya shafe musu jikinsu
shi da ita.

_sai muce asuba ta gari MT jarma angon Sãahar_


******Akan lokaci sukayi sallar asuba duk da nauyin
baccin da suka samu,sukayi jam'i shi da ita ya jasu sallar da daddadar murvarsa data sake sanya mata nutsuwa. A gajarce sukayi addu'o'i duka ta dauka yana sauri ne ya wuce kada gari yayi haske maji ta iskoshi,saidai suna gamawa tana shirin maida kanta saman pillow ya isketa

"Gari yafa waye"

"I know" ya amsa mata a taqaice

"Amma, kada maji ta sameka fa a nan?"

"Haka nakeso"" sai ya jawota cikin jikinsa kawai ya
hardeta tsakiyar qafafunsa,bai sake bata damar yin wata magana ba har bacci ya sake awon gaba dasu.

Maji tana gama shafa addu'o'inta ta miqe,dr
jarma da a yau soyayya tayi aikinta,yayi galaba akan mail tarihi ya kuma maimaita kansa bayan tsahon shakaru kusan talatin,ya daga kansa yana jin zuciyarsa fess ta shayar dashi wani tafki daya manta rabonsa da samun makamancinsa,duk da tanata kumbure kumbure tana kuma basarwa amma sam bai dameshi ba,ya sani magana ta riga ta qare a tsakaninsu,aikin da yayi saura ba me yawa bane yanzun a gabansa

"Ina zaki fita da safe haka?"

"Zan tavar dasu nadeeya kada su kwanta suyita bacci basu tashi sunyi sallah ba" murmushi kawai ya saka ya maida kansa saman pillow yana cewa

"Da kin dawo kawai kinyi kwanciyarki, don nasan toufeeq bai taba makara sallar asuba ba na tabbatar sun tashi sunvi" a mamakance ta juyo tana kallon dr dake kwance

"Toufeeq kuma?, toufeeq din da yake a daya hotel din, me ya kawoshi nan kuma?"

"Matarsa kika dauko masa shi yasa ya biyoku,da da baki dauko masa matarsa ba kin ganshi ne?" Cikin hanzari ta zura slippers dinta tana salati gasa gasa toronta Allah toronta kada ya warware aikin likitan nan azo a zamu sabani. Caraf Dr jarma ya rigota

"Dawo ki zauna, ba inda zakie kina zaton kin fishi son cikin nan?,na tabbata yasan abinda yakeyi, ba abinda zai sameshi, kwanta ki huta hakanan" ya gwada mata garfi ya maidota kan gadon,tilas ba yadda zatayi haka ta koma ta kwanta tana qwafa amma qasan ranta.

"Qarfin hali" taji Dr ya fada. Tasan sarai da ita yake amma sai tayi kamar bata jishi ba.

Duk ta rude saboda kunya da tunanin sa wanne ido zata kalli su maji? amma shi sai taga hankalinsa a kwance yake,hasalima ko a jikinsa,yayi zamansa saman stool daure da towel yana waya da jibril ya shiga wani

• shago ya siyo masa kaya ya bayar a reception a kawo masa. Ya gama wayarsa yayi wankansa,ya dawo ya shirya hankali kwance a gabanta,sai nata idanun taja ta kulle har ya gama.

Ji tayi yana bude qofar dakin,sai ta zabura ta zauna tana dubansa a marairaice, shima ita din yake kalla. Fasa budewa yayi ya dawo da baya a hankali yana
cewa

"Ki daina razana hakanan, ki rufamin asiri gurin maji, kinga dai banyi komai ba,dan kadan ma nace adanji tausayina a sanmin amma ba'a bani ba, kada zaburar nan ta haifar da wani abu kisa maji ta hukuntani". Narke masa sosai tayi tana sauke masa kukan shagwaba. Zubewa yayi a gabanta gaba daya ya tsugunna saman gafafunsa ya kamo zara zaran yatsunta yana kallon qwayar idanunta

"This shagwaba.....bani da jarumtar shanyeta fa ba tare da na biya tukuicinta ba, ki taimaka ki sassauta min" sosai ya bata kunya, gashi ya tsareta da ido, ta dan kauda kanta gefe tana fadin

"'Amma....ta yaya zan iya zuwa na gaida maji don Allah"

"Zo na rakaki" ya furta yana game tafukan hannayensu guri guda.

Yadda säahar ke sissingewa tana jin kunya da nauyin maji haka suka bar majin itama da kunya da nauyinsu. Wato namiji dai komai qanqanta ko girmansa duka halinnan dai guda daya ne. Ta gefan ido take kallon
Dr jarma, ya wani sake yana hira da toufeeq din sosai, farinciki ne zallah saman fuskarsa da zai nunawa mutum me shekaru da zurfin hangen nesa lallai a yau din va cimma burinsa. Shan tea din kawai take amma kunya ta cikata tsakanin Dr jarma din da toufeeq dan dikinta da sahar surukarta batasan wanda tafi jin kunya ba. Jefi jefi take jan sahar da hira wadda itama kunyar ta hanata tabuka komai,a haka hajiya qarama ta tura gofar da dama ba rufeta akayi sosai ba ta shigo.

Kamar zuciyarta zatayi tsalle ta fito haka taji,ga maji ga mahmud again ga kuma toufeeg, toufeeq din da sannu sannu take kallo yana komawa qarqashin iko da mulkin maji din ta ruwan sanyi,sai ta girgiza kai,wannan babbar asara ce da tabewa a gareta, ba zata taba yarda wannan abu da ya fara afkuwa yaci gaba da wanzuwa a haka ba.

Tana wani shan qamshi ta shigo dakin, ta samu waje ta zauna Dr mahmud na tambayar ta fito

“Eh, ai naga ba kasafai kuka fiyawa tunawa da kun aje mutum a dakin ba" dire cup din hannunta maji tayi ba tare data dubi sashenta. Ta shirya sauya taku don haka ta hadiye wani abu da ya tsaya mata a wuya tace

"Barka da safiya matar yaaya" wani kallo maji ta ajewa hajiya garama, a hankali ta sakarwa hajiya qarama din murmushi, a kallo daya tak ta fahimci inda maganar ta dosa

"Barkanki fauziyya* ta smisa mata a taqsics taria barys dubanta daga kanta.

Duk yadda toufeed yasi controlling carisa gaidata don ya sake binneta ya pra isovar fariar da /5 gayawa duniya wace ita, da fiddata a rayanarsa fitsrea ta har abada da kuma sarin hukuncin da yay imani sal yali kowanne hukunci yi mata cio a rayura sai ya kasa.
Tsar ya mique abinsa, yanata cocarin had ye bein fan dake taso masa a duk sadda ya kalli fuskar ha, ja garama, baya ga amneesha itace mutum ta biyu a durija da tayi masa abinda zai koma ga manaliccinsa da tabonsa.

"Zuwa nayi na gaya maka inason na koma gida,zan yank. ticket zuw anjima in sha Allah" hajya carama ta fada tana hadiye wani abu me daci da ya tsaya mata a wuya,ciwo kan ciwo,duka kan duka,yadda toufeed yayi watsin ruwan tsarki da ita ta karanci hakan. Tayi laluben duniya ta gano wanne laifi ta aika masa data cancandl yayi mata wannian rashin arzigin a matsayinta na wra kuma uwar goyo a gareshi?. Abu daya zuciyarta keta nanata mata,sãahar ce kawai ta shiga tsakaninsu, ita ta avatar da kornai,shi yasa

Please Login or Register in order to submit comment