Reading TABARMAR KASHI 1&2 complete by SAFIYYA HUGUMA Chapter 46 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya faru ne saboda nacin da fadeelan ta dinga yi mata

"Please anty N mu zauna kawai a nan,nan din yafi dadi, kuma sai nafi sanin abby ya dawo,daxun yayimin alqawarin kawomin cookies" kumatunta ta kama taja tana murmushi

"Bakin kwadayi,shi yasa kike qara kumatu" hirar da suke ne ta tsaya cak, fara'ar fuskarta kuma tayi gaura duka lokaci guda. A nutse ta tashi daga durquson da tayi tana duban fuskar IG celebrity MEENAL YA'AQOUB AJI,wadda ta shahara da dora mabanbanta hotuna da fuskokin MT JARMA da Instagram basa gajiya da recommending mata ita tamkar ta buqaci haka daga garesu. Ta bangaren MEENAL itama sanda take takowa nata idanun suna kan fuskar säahar din, wani irin abu me girma yana zarta mata tun daga tsakiyar kanta har zuwa tafin qafarta. Jikinta dukka ya fara fidda gumi tana jin wani rudani yana shigarta. Addu'a takeyi qasan ranta. Ya Allah ya sanya ba wannan bace matar yaa moha, Allah ya taqaita wahalarta ya sanya ba ita bace,muddin hakan ta kasance tasan babu ta inda zatakai labari wajen hada kyanta da take taqama dashi dana sãahar din.

Duba daya tal ta yiwa meenal din ta dauke idanunta daga kanta,saboda cikin qasa da minti daya sautin muryarta ya tabbatar mata itace haseenar hajiya qarama. Yadda ta debeta ta watsar itama ya bata amsar cewa ita dince, itace matar da tasha gaban burinta takeson kawowa cikar burinta barazana,wannan tunanin ya sanya ta sake tsuke fuska itama

"Ukhtie....abby dinki yana ciki?" Ta tambaya don gudun karya tsarinsa, kamar yadda a dazun ya gargadeta kan bayason irin wannan zuwan

"Ya fita" fadeelan ta amsa mata a taqaice don ba wani sabo ko shaquwa bane me yawa a tsakaninsu,don meenal din na hannun mahaifinta tun tana da shekara goma sha biyar, kawai lokaci lokaci ne take zuwa musu hutu,tunda kuma ta shiga university ma bata sake zuwa ba sai yanzu data kammala

"Okay" meenal din ta fada, cikin satar kallon sahar ta samu waje ta zauna, ta kuma dora qafa daya saman daya ta fidda tsadajiyar wayarta ta fara dannawa.
Tamkar batasan Allah yayi ruwanta a gurin ba sukaci gaba da hirarsu da fadeela, nadeeya duka yau din bata nan, don haka sai su biyu. Har zuwa lokacin sallar azahar yayi ta janye fadeela suka wuce dakinta suka bada farali, sannan suka fice daga sashen don komawa sashensu,saboda yau tana da sha'awar yi musu abincin dare abinda tunda ta dawo gidan batayi ba.

Bayan sãahar din meenal tabi da kallo, tana da izza fiye da tata tana kuma da miskilanci da jin kai da yafi nata yawa yanzun ta ina zata fara quntata mata? ta wanne bangaren ya kamata ta fara ajiyewa rayuwarta bacin rai?, sai kawai ta gyara kwanciyarta cikin qayatattun kujerun falon tayi kwanciyarta hankali kwance,ta dauki. waya ta turawa hajiya qarama tex don kada tayita bulayin nemanta cikin gidan.



_tambayoyin dani kaina bansan amsarsu ba,saidai lokaci zai bayyana mana komai

"HUGUMA*

"TABARMAR KASHI'

Book 02 Page 23


*****Tsaye take cikin kitchen din tana qoqarin rufe lunch bag din fadeela dake dauke da tarkacen kavan beak dinta na makaranta. Sanye take da wata lafiyayyar tattausar abaya sagar dubai, da aka sagata da zare da kuma yadi me tsananin kyau da tsada. Maroon color ce wadda aka yiwa ado da bagi da kuma zaiba a jiki. Daga ciki kuma wani lallausan cotton lace ne maras nauyi wanda aka yiwa dinkin riga me dogon hannu da straight skirt. Daurin kanta ya zauna das sakamakon yadda ta yiwa gashin kanta gammo daga baya ta kuma daura dankwalinta ya zauna mata dass da samfurin daurin dankwalin nan da ake kira zahra buhari. Wani irin tattausan gamshi take fitarwa,wanda ya zame mata al'ada ya kuma kama suturunta da kyau. Turaren wuta na kaya me asalin tsada wanda take samu takanas daga masu abun wato garin mahaifinta BORNO. Wani irin sassanyan kyau tayi a safiyar kyau me ratsa idanu da shiga zuciya,ba tun yau ba shigar laffaya na daya daga cikin shigar dake matuqar qara mata kyau da matuqar da kwarjini, takan koma kamar balarabiya tare da fita a ainihin yarenta na SHUWA-ARAB.

Dai dai lokacin da dukka motocinsa da suke fita zuwa kamfani suka gama komai, fitowarta kadai suke jira, harda toufeeq din dake zaune cikin motar. Sanye yake da wasu kurtas charcoal color da suka dace da farar fatarsa,hankalinsa duka suna kan system din dake cinyarsa yana shigar da wasu bayanai akan meeting din da sukayi a daren jiya shida board members na sabon kamfaninsa da zai fara aiki wata me kamawa, dai dai lokacin da yake sanya ran ya kammala da kamfanin MT JARMA. Ta cikin eye glasses dinsa ya daga agogon hannunsa daya kwanta luf cikin gargasar data zama tamkar rumfa wa fatarsa vana duba lokaci. A galla sunyi zaman jiran mintuna goma kenan zuwa sha biyar,baya cikin tsarinsa bata lokaci da saba lokacin zuwa aiki,gashi tana son zama silar haka a ranar farko. Qaramin tsaki yaja yana ajiye system din, sannan ya buda gofar side dinsa a hankali yana zura gafafunsa waje. Da sauri elyas ya matso,sai ya daga masa hannu,ya fahimci me yake nufi don haka ya koma da baya yaci gaba da tsaiwa a gurbinsa.

Har ya sako daya qafar ya hangi tahowarsu,fuskokinsu gaba daya cike da wani irin walwala da annuri ita da fadeelan, tana riqe da lunch box din fadeelan,ta kuma rataya school bag din nata still a daya kafadar, daya hannun kuma na riqe da hannun yarinyar. Sak suka fito a 'YA da UWA,wani abu ya taba zuciyarsa ya kuma tuno masa shekarun baya,a lokacin da yake da shekaru kwatankwacin na fadeelan,lokaci da maji ke riqe hannuwansa kamar haka ta kaishi makaranta sannan ta wuce gurin nata aikin. Anutse ya zare idanunsa daga kansu,ya maida qafafunsa cikin motar tare da jan murfin motar. Karo na biyu idanunsa suka sake sauka a kansu. Dai dai sanda ta zame hannunta daga na fadeela tana gyara yafen lafayar jikin nata,zara zaran yatsunta da aka sakawa lalle a jiya suka bayyana hakan sai ya tuna masa da wani lokaci can baya, ranar farko data mige cikin taron ma'aikata kamfani don ta gabatar da nata aikin. A ranar dukkan wanda ya kalla cikin mazan dake hall din idanunsa vana kanta, daya bayan daya ya dinga bin fuskokinsu da kallo ba tare da sun sani ba,haushi da takaicin da ya sanya yace ta hada file din kenan zai duba a gida ko office ba tare data garasa cinye mintuna goman da suka rage ba.

A yau ma sal ya samu kansa da sauke dubansa saman fuskokin guards din nasa dake tsaye suna dakon fitowarta. Daya bayan daya yake nazartarsu,sai ya janye idonsa yana furzar da iska daga bakinsa. Kusan mutum biyar a cikinsu idan idanunsa sun gaya masa dai dai kamar ita yaga suna kalla. Jamal daya daga cikinsu ya hanga yana gyara tsaiwarsa tare da gyara zaman glasses dinsa. Haka kawai yaji wani abu me nauyi yana sauka a hankali saman qirjinsa. Jamal na daya daga cikin mazan da Allah ya jarabta da son mata,mutum ne me yawan kule kule, abinda ya sanya tasu sam batazo daya da toufeeq ba. Kusan sau biyu yana dakatar dashi kafin ya samu ya maida hankalinsa ya kuma dai daita kamar yadda tsarin duka yaransa suke.

"Madam…madam" muryar adama daya daga cikin
masu aikin dake aiki a sassan hajiya qarama ta ziyarci kunnenta. Cak ta tsaya tadan juya kadan har adama ta

qaraso
"Abincin makarantar fadeela ne......inji hajiya qarama" ta fadi a ladabce. Sosai ta kalli qawatacciyar lunch bag din dake rige a hannun adama, mamaki yana sauka a ranta.

Yaushe har aka canza tsarin baiwa fadeela abincin makaranta?, lallai da gaske matar nan take, qaramin murmushi ya subucewa fuskarta wanda ya sake qara bayyana kyanta

"Ki gaya mata ummarta ta riga ta tanadar mata komai" ta furta tana daga mata lunch bag din hannunta. Kalla adama tayi saita juya tana komawa ciki. Saita juya tana ci gaba da tafiya tare da jan siririn tsaki, tsanar matar yana samun gurbi cikin zuciyarta.

Idonsa ya dauke daga kanta yana lumshesu,yadda ta juya tsukakken bakinta da yasha Marron lipstick yana wulgawa ta cikin idanunsa,ya rasa me yasa tsiwa take mata dadi,idan tayi tsiwar kuma sai ta sake maidata kamar wata qaramar yarinya.

Tun kafin ta garaso tayi noticing motar da yake ciki,don haka sai ta tsaya daga motar da aka kebe saboda kai fadeela makaranta da kuma sauran uzurorinta, budewa fadeela gaba tayi,ita kuma ta shiga seat din baya.

Jibril ne ya duga vana rufe motar sannan ya zagayo yana gogarin tashinta

"Madam tace zamu fara sauke fadeela a makaranta sannan mu wuce" jibril ya fada cikin girmamawa. Mamaki ya kamashi, me kenan?, bayan yarinyar nada driver?,so a lokacin bashi da lokaci dogon surutu,don haka ya gyada masa kai kawai,motocin suka fara tashi a nutse suna ficewa daga gidan.

Sanda security na gidan ya kammala rufe qofar bavan fitarsu a sannan hajiya garama ta garaso farfajiyar gidan a birkice, cikin matsanancin fushi take bin shatin tayoyin motar da kallo

"Uban waye yace ki dawomin da abincin saboda ta fadi haka? me yasa baki tsaidasu ba kin kuma shaidamin kafin fitarsu daga gidan?"

"'Kiyi haquri hajiya,ban zaci...." Kyakkyawan mari ta sauke a fuskar adama tana wani irin huci,wanda hakan da tayi dai dai yake da haushin kaza huce kan dami. Har ta buda baki zatace wani abu sai kuma ta fasa,saboda koma meye yanzu zata fada din bashi da amfani, saboda komai ya riga ya ruguje, amma tabbas ba zata taba bari komai ya tafi a banza ta ruwan sanyi haka ba. Tana takawa cikin qida take gava mata

"Ki cewa bala va shirya nan da awa daya zai kaini
makarantar su ukhtie " bata tsaya jiran amsa ba tayi
gaba cikin tsananin fushi.

A kan idanunsa yana ganin sanda ra budewa
fadeela gofa ta rataya mata jaka da lunch bag dinta,ta
tsugunna tayi kissing dinta ta kuma rada mata wata
magana dashi kansa baisan me tace mata ba,fadeelan ta
doso motarsu,ganin haka ya sanyashi bude murfin motar
tun kafin ta garaso. Murmushi fal saman fuskar
yarinyar, saboda hirar da sukayi da säahar din cikin
motar, tana jaddada mata daga yau itace zata dinga
kawota tana kuma maidata gida. Kidding goshinta yayi
sai tace

"Yau abby ka rakoni makaranta, inajin dadi sosai "
hannunta da a yanzu suka zama masu kauri ba kamar a
baya ba ya kama yana murmushi ya jinjina kai, sai ya
sanya hannunsa saman kanta ya shafi kan

"'Barakallahu fiik, ayi karatu da yawa" hannu ta daga
masa tana masa bye bye, idonsa ya sauka akan motar
fadeelan, säahar ta koma ta zauna cikin motar,har
fadeela ta juya ya kirata

"Angel" sai ta dawo da sassarfa,ya danyi shuru yana juya
maganar a ransa,bayason ya fadi ta dauki maganar da wata manufa daban,haka kawai cikin zuciyarsa yakejin bai dace su zauna mota guda daga ita sai driver ba,yayi gogarin hana kansa gain baiken hakan amma ya kasa,idanunsa nata sake dawo masa da irin kallon da ya gani daga idanunsu jamal a dazu

"'Kije ki gayawa autynki ta dawo wannan motar".
Shuru tayi tana duban fuskar fadeela sanda take gaya mata saqon toufeeq din, kafin takai ga yin komai fadeelan ta dauki handbag dinta tayi gaba da sauri tana cewa

"Nima bari na tayaki aunty" bata da sauran zabi illa bude murfin motar da tayi ta fita a hankali tabi bayanta.

A nutse ta zauna elyas ya maida murfin ya rufe, qamshinta ya mamaye motar,ta gyara zamanta sosai tana maida dubanta ga bakin qofa sannan tace

"Good morning" a taqaice, saidai ko uffan bataji yace ba.

Ranta ya baci sosai, ba abinda a yanzun yake takura mata irin wannan gaisuwar data zame mata qadangaren bakin tulu,idan tayi ya amsa mata da qyar,idan kuma bata yin ba tana tsoron abinda ya furta zai aikata mata.

"'Good morning" ta sake fada adan qufule, idanma bata maimaita ba tasan tsaf zaice bata gaidashi ba. Dukka gaisuwan nata yaji sarai, amma yadda ta juya baya tana fuskantar gofar sannan ta gaidashi kamar dole ya bashi haushi, yadan dauke idanunsa daga kan system din ya aza mata su

"Wani ne yace dole saikin gaidani?, ki riqe kayarki bana so daga yau,don ba qanfar gaisuwa nakeyi ba,na saka miki dokarta ne saboda na saitaki kan abinda ya dace" daga haka ya maida dubansa ga allon system din. A yau din karon farko taji jikinta ya sanyaya da yadda yayi mata magana,babu wannan fadan Sam cikin muryarsa sai wani irin softness har cikin ranta taji abun bai kamata ba,don haka ta gyara zamanta da kyau tana dan fuskantarsa

"Barka da asuba" fa furta itama da sanyin muryarta.
Tsigar jikinsa ne yaji ta zuba,ya daga idonsa a nutse sai suka hada ido,kowannensu ya janye dubansa da sauri

"Barkanki"


"An tashi lpy"

"Alhamdulillah" ya fada ba tare da ya sake dubanta ba, daga haka ta rasa abinda zata sake fade, saita ja bakinta tayi shuru tana maida dubanta ga hanyoyin da suke ratsawa da gudu.


"HUGUMA*


• TABARMAR KASHI

Book 02 Page 24

Har suka isa company din babu wanda ya sake cewa da dan uwansa komai. Jibril nayi parking a parking lot na company din ya kashe motar sannan yayi magana ba tare da ya waiwayo ba

"Akwai employees da suka shirya welcoming naku,da tayaku murnar aurenku,suna entrance na main building" system din ya sauke daga saman cinyarsa yana ajiiveta gefe daya,idanunsa akan jibril

"'Waye ya sanar musu da hakan?" Ya jefa masa tambayar da salon tambayarsa din nan me cike da dakewa. Cikin dan daburcewa jibril din yace

"Yallabai sajjad ne" dauke dubansa yayi daga kan jibril,ya gama gano abinda sajjad din ya shirya, sai kawai ya bada umarnin bude gofofin motar.

Kusan dukka manyan ma'aikatan company dinne suka jeru sahu biyu hagu da dama, kowanne dauke yake da gift a hannunsa,wasu flowers wasu boxes,mafi akasari sunyi hakanne saboda säahar din, don babu wanda baii cadin mu'amalarsa da ita ba,basu sake tantance muhimmancinta ba sai bayan tafiyarta,yanzun kuwa data dawo musu a karo na biyu sai hakan yayi musu dadi gwarai.

Ta tsakiyarsu suka fara takeaway a nutse,duk wanda zasu gifata sai ya ranqwafa cikin girmamawa. Mr hamza shine mutum na biyu a sahun, sunzo dab dashi ya ranqwafa idanunsa akan fuskarta

"Sir, congratulations, congratulations sir" ya fada da dan murmushi saman fuskarsa,sannan ya miqa flower din ga sãahar.

Baisan ya akayi ba,yadai tsinciki kansa da sanya hannu ya karba flower din daga hannunsa ya miqawa elyas tare da yi masa inkiya, sannan a hankali ya sanya hannunsa ya lalubi hannunta, ba zato ba tsammani sai jin tafin hannunta yayi ya manne da lallausan tafin hannunsa guri daya,ta waiwayo da hanzari tana dubansa idanunta kuma suka fada cikin zagayayyun fararen idanunsa. Zame hannunta taso yi cikin hikima da dabara amma ya matseshi tsam cikin nata,saboda ya fuskanci idanun mr hamza na kan hannayen nasu

"All eyes are on us" ya fada qasa qasa,a hankali itama tayi noticing hakan, musamman daga idanun mata da yawa da dama can ba huldarsu take shiga cikin company din ba, da masu goqarin shiga gonarta amma tayi musu iyaka irinsu saima.

A gaggauce suka dinga wucewa,hakan ta bishi saboda hannunsu na cikin na juna. Bai sakar mata hannu ba har suka isa bakin elevator.

Zame hannunsa yayi a nutse,abinda sãahar keta qoqarin yi kenan,ba tare da ya dubeta ba kuma ba tare da yace da kowa komai ba ya danna button ta bude.
Baya yaja kadan tare da yi mata nuna da hannu akan ta shiga. Cikin nutsuwa tabi ta gefansa,har kafadarta na gogar hannunsa saboda yadda ya tsaya yayi bake bake a bakin elevator din,wannan ya sake bawa turarenta damar bugun fuskarsa,ya damqe hannunsa da kyau kamar wanda ya boye wani abu. Waiwayawa yayi baya,kallo daya ya yiwa su elyas taga sun janye baya,ya taka da sassanyan takunsan nan ga shiga ya rufe dasu suka fara haurawa. Shuru elevator din yayi sai qamshin jikkunansu daya cikata. Yana tsaye daga gabanta dai dai bakin gofa,wannan ne ya bata damar gare masa kallo da kyau,duk kuwa da yadda taso dauke kanta,amma halin zuciva, sai taji a karon farko tana son yin hakan. Tun daga kan lallausar nannadaddiyar sumarsa,murdadden hannunsa dake boye a aljihunsa, daya hannun nasa dake rige da waga qawatacciyar briefcase dinsa zuwa bayansa da takalman dake gafarsa wanda suketa daukan idanu. Tana gama satar kallon dai dai sanda elevator din ta iso dasu floor din da suka nufa wato gini na garshe na kamfanin. Ya danns button din sannan ya taka yana shirin fita

"Ki ringa kame ganinki,karki manta ni dan iska ne me yiwa mata fyade, muddin kika cika kallona zan iya dauka cewa ranki ya biya ne da ni, komai kuma zai iya faruwa".

Idanu ta fiddo waje cikin mamakin maganarsa,sai tasa hannunta guda daya ta dafe kanta haushin kanta yana kamata,meye ma ya kaita tsaiwa ta kalli wannan mutumin idan ba jawowa kai matsala ba ta fahimci shi kullum baiso a zauna lafiya,batasan meye tayi masa ba,wai shi kunyar furta kalmar fyade ma baya jinta sam?. Gani tayi idan ta barshi ba shakka ya sha da ita, saita tako itama tana biye dashi sanda yake scanning key din a jikin qofar

"Wai shin me ma zan kalla hala? wannan kodaddiyar fatar ko kuma wanna gashin mara kyan gani?" Ta furta tana nuna singalilin hannunsa dake riqe da handle din gofar. A karon farko dariya taso qwace masa amma ya rage kaifinta ta hanyar murmushin gefan bakiya kalli hannun nasa data nuna sai ya sanya daya hannun yana shafarsa


"U'uzubi kalimatillahit taammati minsharri ma khalaga, da gasken dai qaremin kallo kikeyi, banda haka ta ya kika san da zaman gargasata iyee?" Ya jefa mata tambayar data sanyata fara raba idanu amma ta basar

"Bayan gashina mara kyan gani sai kuma meye kika gano?,oya tell me" ya fada yana murza handle din tare da tura gofar baya ta bude.

"Eheenn, ina jinki da meye da meye?" Ya kuma jefa mata tambayar yana matsota idanuwansa akan lips dinta da suke haifar masa da wani irin abu a jikinsa wanda yake sanya tsigar jikinsa zubawa,a duk sanda yaga lips din sai ya tuna da santsi da kuma laushinsu. Ba zato ba tsammani taii va cafketa ya kuma finciketa zuwa office din ya maida murfin da qafarsa guda daya. Jefata yayi jikin bango yana bin bayanta
"Saifa kin gayamin, kada naje wadan nan marasa kunvar idanun naki sun ganemin sirri na" yadda ya matseta da bango ya sanyata jin kamar iskar dake wajen tayi mata kadan,ta tabbatar ko da wasa ta motsa ba shakkan qirjinta shine abu na farko da zai fara gogar jikinsa.

Qangame jilkinta tayi guri daya tana rufe idanunta sanda taga ya taho da hannunsa saitin fuskarta, ta gama taga ya taho da hannunsa saitin fuskarta,ta gama saddagarwa may be maruka zata sha,sai taji yatsunsa guda biyu saman lips dinta suna zagayasu.
Tsigar jikinta ne ya zuba lokaci daya taji kamar wayar wuta ta jata

"'Waye ya baki izinin shafa wannan abun?" Kusan daukewa numfashinta vayi, saboda a saman fuskarta yayi maganar muryarsa can gasa kamar me shirin rad'a mata, hucin furucin bakinsa dake cakude da mint scent ya daki fuskarta. Bata gama kokawa da wanna ba ta tsinci lausasan lebunansa masu dan tudu a saman nata siraran labban, ta gama fahimtar abinda yake shirin yi mata, saita tattara dukka qarfinta ta sanya hannunta saman girjinsa ta turashi baya tana gocewa gefe cikin bacin rai.

Idanunsa da wani abu ya sirka a cikinsu ya daga yana dubanta

"Duka wannan baya cikin sharudanmu,koma meye zanyi ko zan sakawa fuskata ba damuwarka bane, na kula kawai da fadeela,i will do my very best, that's all" ta fada muryarta tana rawa. Kafin yace komai yaji qofar na bada alama na shigowar wani,don haka ya juya da dan hanzari kai tsaye ya wuce cikin office dinsa.

Saima ce rungume da files, gaba daya fuskarta zuwa zuciyarta babu wani sukuni ko annuri, ido suka hada da säahar, sai säahar din ta dauke kai tana gyara rufin lafayarta sannan ta durfafi office din itama kai tsaye,cikin ranta tana jin kamar ta zura da gudu tabar office din, a karo na biyu ta sake dawowa aiki da wannan mutumin da bashi da kirki ko kada,ko yaya zata kasance musu?.

A nutse ta buda ta shiga da murtukakkiyar fuskarta,har hanzu office din yana nan kamar yadda ta sanshi,saima sake qawatashi da akayi da gyare gyare.
Guri ta samu ta tsaya tana harde hannuwanta a girji, bugun zuciyarta har yanzu bai daidaita ba. Bashi a office din,amma taji qarar ruwa daga toilet, sai ta zabi taci gaba da tsaiwa kawai.

A galla mintuna kusan goma sha biyar ya shafe kafin ya fito,kallo daya ta masa ta dauke kanta, gaba daya fuskarsa ta sauya,ya koma real MT JARMA dinsa data sani,kamar ba shine yanzu yanzu yaso matseta yayi mata mugunta ba,ya jade fuskarnan da kyau,abinda ya sake qara masa kwarjini kenan

"Have a seat" ya fada yana jan tashi kujerar baya tare da shirin zama a kai,har yanzu bai kalleta ba.

Batason suia magana da vawa,don haka ta garaso ta zauna din, ya buda wani file dake gabansa ya ciro wata takarda ya ajiye saman file din

"As my new P.A,aikinki zai zama a qarqashina ne, zai kuma zamana kan umarnina,na baki access da duk wani kira mo email da ya shafi office dina, sauran abinda zakiyimin idan ta kama zan sanar miki, koda ya fita daga tsarin aikin PA"


•_HAJIYA QARAMA_*


Ita da masu aikinta biyu suka isa makarantar, kai tsaye har zuwa office din shugabar makarantar.

"Abincin jikata ne FADEELA Muhammad jarma" dubanta headmistress din tayi

"Cute angel,ko ba ita ba?" Ta fadeta da sunan da yawanci ake kiranta dashi a makarantar. Murmushi hajiya garama ta saki tana gyada kai "Eh ita fa"

"'Amma dazu mamarta ta kawota da kanta,kuma da abincinta tazo kamar yadda aka saba" kai hajiya qarama ta jinjina,tana jin dacin kiran sãahar da sunan mahaifiyar fadeela

"Ba itace mamarta ba,matar ubanta ce,nanny dinta kuma ada" ta qasan glass matar ta dubeta

"Eh amma ita muka sani a yanzu,don ko last week da za'a shiga sabon session itace tazo tayi updating data na fadeela,da sunanta muka cike komai,so ko yanzun ba zamu iya karbar abinci daga hannunki mu bata ba,sannan koda daukarta ma a yanzu ita ke da alhakin hakan,idan fana da uzuri kuma zata kiramu da kanta ta bamu shaida akan wanda ta turo din".

"Turqashi!" Ta furta tana dukan hannun kujerar da take zaune a kai ba tare da tasan ta aikata hakan ba

"Madam kinsan da waye kike magana kuwa? hajiya fauziyya ce ni fa qanwa ga Dr mahmud JARMA, uwa ga MT JARMA, sannan kaka ga fadeela,kinaso ki gayamin matsayin matar uba ya wuce na kaka?" Ita kanta matar mamaki sai daya darsa mata a rai, saboda bataga meye abun tashin hankali ko bacin rai ga gin karbar abinci ba,amma duk da haka ta basar ta girgiza kai

"Ko kadan kuma wannan ai family issue ne ma hajiya,abinda na sani dai kawai, duk wanda aka sanyashi cikin data na dalibi shine zaici gaba da juyawa da kulawa da komai nashi,dama kusan ita fadeelan ce kadai bata da wannan record da muke dauka a duk shekara,so wannan karon kuma ta samu,haqginmu ne mu kula da lafivar dalibi da tsaronsa, ki koma da abincin hajiya idan kuka sasanta a gida sai kuzo asan sunan wanda za'a cike dashi, ko kiyi kiranta muji hakan daga bakinta".
Tsantsar bacin ran da take ciki ya hanata sake cewa komai sai kawai ta miqe tana fita dava office din, adama na biye da ita da lunch bag din. Sai data kusa minti ashirin a tsaye jikin motar tana juya abun a ranta, ita yarinyar zata dinga shigewa rayuwa haka? lallai zata nuna mata kurenta,amma kafin sannan bari taje ga mataki na gaba.

"Gida zamu koma hajiya?" Driver dinta ya tambayeta,saita girgiza kai

"Gidan yaaya zaka kaini"

•_DR MAHMUD JARMA RESIDENT_


Yana duge gaban garamar luggage dinsa, daya daga cikinsu wadda duk sanda tafiya ta kamashi yake amfani da ita. Yana tsaka da zugewa hajiya mansura ta shigo dakin dauke sa tray data shiryo masa kayan abinci a ciki.

Idanunta a kansa har ta garaso ta ajiye,ta koma gefan gado ta zauna

"Kwanaki uku kenan inatason yin magana da kai, amma sai nake ga kamar baka da lokacin kanka a 'yan kwanakin nan" ba tare da ya dago ya dubeta ba va iiniina kansa

"'Inata shire shiryen yin tafiya ne kuma a galla tafiyar zata dan iya daukana lokaci wala'alla me dan dama kafin na dawo,duk da bana fatan hakan" ya bata amsa yana tsaida luggage din bayan ya gama rufeta. Sosai take kallonsa,cikin kwanakin gaba daya kamar ma cikin nutsuwarsa yake ba,to amma ita abinda yake gabanta a yanzu yafi tasa a damuwar a

Please Login or Register in order to submit comment