Reading TABARMAR KASHI 1&2 complete by SAFIYYA HUGUMA Chapter 31 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

jujjuya mazuban dukka plain fararen mazubi ne, abun sai ya daure mata kai,ta dinga juyasu daga gaba zuwa baya har batasan adadi ba,kanta ya daure sosai,gefe guda na zuciyarta kuma ya cika wa wasi wasi da fargaba. Motsin shigowar fadeela ya sanyata ajiye bottle din,ta daga kai tana dubanta,hannunta riqe da wata babbar sweet,cikin sakalci da salo na shagwaba ta zauna gefanta
"Uncle dina ne ya kawomin,yace gobe shima zaibi abby na,munyi waya da abby ta wayarshi, yace a barmin tab dina a bude zai dinga kirana kullum ta google meet muyi video call" cikin dauriya ta saki murmushi
"In sha Allahu" ta fada tana tattare kayan magungunan,ta maidasu cikin ledar,ta sake kadema fadeela gadonta ta saisaita sanyin ac din dakin da kuma hasken,ta rakata toilet tayi brush suka dawo tare. Sai data tabbatar tay bacci sannan ta zauna gefanta tana kallon doguwar fuskarta,abubuwa da yawa data taras a gidan suna dawo mata kanta,tun daga shigowarta gidan kawo yanzu,haka kawai jikinta yake bata akwai wani qalubale,akwai wani abu tattare da rayuwar yarinyar,ina mahaifiyarta?,don daga baaba ramatu har hajiya qarama tasan sunyi girman da ba zasu haifi kamar fadeela ba,to amma tana da mahaifi,shi din me yasa bazai zauna kusa da yarinyarshi ba? ko don babban lalurar daka iya zamewa naqasu ga rayuwar mutum?. Da wannan tunanin ta tashi daga gurin ta fita a dakin bayan ta tofeta da addu'a ta shafeta da ita,ta rufe dakin ta shige nata ba tare da tabi takan magungunan da hajiya qarama ta bata ba,haka kawai ranta da jikinta taji basu aminta data dauka ta bawa yarinyar ba. Zuwa lokacin wutar dake bada haske a hallway din ta sauya launi,alamun dake nuna lokacin baccin yayi kenan.
Sai da tayi sallar shafa'i da wutiri sannan ta zare wayarta a charge,ta zauna sosal saman gadon ta shafe jikinta da addu'o'i sannan ta kunna wayarta tana duba time. Taso shigowa da wuri ta kira kowa amma lokaci ya qwace mata sanadiyyar shigowar hajiya qarama,yanzun kam dare yayi ba zata iya kiran kowa ba a cikinsu.
Wayar na gama daidaituwa saqon
mahmud ya shigo har guda uku a jere,yau kam dai ta duba,saqon fatan alkhairi ne tare da nuna zallar kewarta da zaiyi,afifa ta gaya masa ta samu aiki amma ba'a kano ba. Ko data gama karantawar batayi reply ba ta soma kiran afifa,bugu biyu ta daga
"Nanny bestie,me ya faru da wayarki tun dazun switched off?,ko gidan basa bari a daga waya ne?" Ta garashe maganar cikin shaqiyanci da zolaya
"Ban sani ba,mu hadu a WhatsApp" daga haka ta gintse kiran,ta sani ai tunda ta zabi wannan aikin ta shiga uku gurin afifa,qilan sai tayi kamar zata zautata da tsokanarta.


*HUGUMA*

*_TABARMAR KASHI_*

Page 62

Bata sake tsokanar tata ba bayan sun hau online,suka gaisa saidai ta tambayeta ya vanayin alkin
"There's is something terrible a cikinsa" ta amsa mata har zucivarta tana in akwai wani abu
"'Kaman yaya?" Afifa ta tambayeta cikin fargabar kada ta sake fadawa wata cutarwar kwatankwacin na baya. A nutse ta gaya mata komai,ba jimawa voicenote me yawa. Ajiyar zuciya ta sauke bayan ta gama saurara,dukka maganganun afifa akan hanya suke,kuma taji dadin yadda ta qwarara mata gwiwa

"But afifa how she can survive without medication?"

"Yes,her illness needs treatment,idan ba haka ba abun zaiyita worsening ne,so that zanyi prescribing miki wasu magunguna,su zata dinga sha zasu taimaka mata in sha Allah,but kafin sannan ki samo history na ciwon nata,yanayin yadda yake mata idan ya tashi da kuma asalinsa,ki ajiye wadancan,tunda babu sahihanci a cikinsu". Sosai suka tattauna da afifan,sai taji dadin shawarwarin data bata game da yadda zata kula da fadeela din,shawarwarin da afifan ta bata saita tsinci kusakurai da yawa game da yadda ake kula da yarinyar.

Basu rabu ba sai can dare,don daya ma ta kusa,ta sauka ta daura alwala ta gabatar da sallar dare kamar yadda ta saba,ta miga bugatunta wa ubangiji idanunta cike fal da hawaye. Wannan din wani sirrin rayuwarta ne da babu wanda ya sani sai afifa. Data kammala fita tayi ta dubo fadeela,ta sake gyara mata kwanciya da rufa gaba daya sannan ta jawo gofar dakin ta fice,a ranta tana jin rashin kamatar barinta ta dinga kwana ita daya alhalin tana da irin wannan lalurar,anytime zata iya far mata.

*WASHEGAR I*

Komai na gidan ta fuskanci cikin tsarin yahudanci zata iya cewa yake tafiya,safiya a garesu tamkar dare ne,don ba da wuri suke tashi ba sam,fadeela ce kawai za'a yiwa abincin tafiya makaranta,a kuma shiryata ta wuce. Kowa rayuwarsa yakeyi,saidai idan an hadu a gaisa,kowa yayi aikinsa kuma ya kama gabansa,sai idan wani aikin ya sake hadaku.

Tun bayan data shirya fadeela driver ya dauketa saita shiga dakin yrinyar,da kanta ta yiwa dakin gyara,ta fidda duk wani sharp objects da zai iya cutar da ita idan ciwonta ya tashi,ta gyara komai ta sanyashi a muhallin da koda faduwa tazo mata ba zata cutu ba
Teddy's manya tayi list cikin abubuwan da fadeelan ke bugata,tanason aje mata agurare mabanbanta ya zama ko ina dakin bai cika da wani abu me tsini ko tauri ba,tashin ciwon unexpected abu ne,tanason tayi abinda zai zame mata first aid koda ba wani a kusa da ita.
Tana tsaka da aikin me gyaran dakin ta shigo,sai kawai ta sallameta,da kanta ta shiga walking closet dinta,cike yake da kaya masu kyau da tsada na alfarma,saidai alamu sun nuna akwai kayan da ba'a sanya mata su,ko ba'a damu da saka mata su din bane oho ta gyarata fes ta sake jera komai. Bata fita a dakin ba sai garfe daya,sai sukayi clashing da baaba ramatu.

Baya ta jaye mata cikin girmamawa,fuskarta da fara'a tace

"Naji shurun yayi yawa nace bari na dubaki" murmushi tayi

"Ina ciki ina aikin gyaran dakin fadeela"
"'''ah,ina mabaruka?"

"Ni na sallameta,akwai gyaran da na yiwa dakin ne"

"To madalla,sannu da qoqari" baaba ramatu ta fada,har cikin ranta tana jin cewa yanzun fadeela ta samu nanny din da zaiyi wuya korarta,tun daga jiya zuwa yau taga tarin banbamce banbamcen da sauran masu kula da itan da tayi a baya.

Cikin sati guda kacal ta gama fahimtar
dukkan wasu tsare tsare na gidan,sannan
itama ta gama tsarawa kanta yadda zata rayu
da kowa. Cikin sati guda din nan kacal suny!
wani mugun sabo da fadeelan,yarinyar tana da
wani irin shiga rai da kuma masifaffen wayo
dake da alaqa da kaifi basirarta a makaranta.
Sannu sannu dukkan wasu ayyuka da sauran
ma'aikatan gidan kewa yarinyar,kama daga
abincinta,gyara dakinta,hada kayan wankinta
a bayar zuwa laundry room duka ta qiya
kowa yayi mata,dukka sun koma wuyan
sãahar. Wani irin girma take bata,tana jinta a
ranta ta zarta mata kowa a gidan,kafin tayi
wata guda sai ya zamana sun koma tamkar
ya da uwa,hatta da dakinta idan zata koma
sai bayan yarinyar tayi bacci,data farka ta
sauko a gadonta komai asuba zataji ana
mata knocking,indai taji wannan bugun tasan
fadeela ce,tare xasu qarasa kwanan,ayi shirin
makaranta. Ayyukan makaranta kuwa shima
ya koma aikin sāaharlesson dinta da ake mata
still dai shima taqi malamin,a nan ne fadeela
ta lura kamar akwai rauni wajen karatun
addininta,da kanta ta zauna ta tsara yadda
zata fara koya mata,duk da ason ranta yarinyar
ta shiga islamiyya,to amma batasan yadda
zata tunkari masu gidan da maganar ba.

A nata bangaren ayyukan fadeela gaba daya nishadi suka sanyata,sun debe mata kewar yara sosai,sun kuma nesantata da dukkan wani namiji kamar yadda take da muradi,tana jinta kamar a killace,babu idanun kowa a kanta,ta samu cikakkiyar nutsuwa da gamsuwa cikin gidan,hajiya qarama da takejin kamar zata zame mata matsala ko akwai wani illa tare da ita,saita fuskanci ba wani damuwa tayi da sassan ba,saita share kwanaki ma bata shigo ba,sai idan fadeela taje mata. To amma,shin da gaske fadeelan jikarta ce?,idan jikarta ce ta yaya mu'amala irin wannan zata wanzu tsakanin jika da kaaka?,tanason sanin labarinsu,tana son sanin ainihin wacece hajiya garama a wajen fadeela,to amma ita din bata cikin sahun mutanen da suke shiga lamuran da sukayi yaqinin basu shafi rayuwarsu ba.
*****K'arfe biyar da wasu yan mintuna na yammacin ranar ne,dai dai sanda madaidaiciyar motar me kyau ke shigowa cikin gidan,wanda da shigowarta da isowar masu aikin gidan duka duka bazaiyi minti biyu ba,cikin gaggawa kowanne ya iso,saboda sanin mamallakiyar motar,kowa yana gudun tsira da mutuncinsa.

Bude murfin motar tayi,sannan ta qwalawa daya daga cikinsu kira,matsowa tayi da gaggawa,bakinta dake tauna chewing gum ta motsa

"Daukarmin hand bag dita"

"Tom" ta fada tana buda daya side din da jakar take ta dauka ta riqe

"Kai jama'a,mutum ba uban kowa ba sai shegen ji da kai da izzar banza" tayi gorafi gasa qasa,saidai ya fidda sautin gunaguni
"Me kike cewa?" Labiba ta tambaya taba juyowa,murmushi tadan saki a rikice

"Bab.....babu komai,cewa nayi maraba da dawowa" bata sake cewa komai ba ta fita a motartabar musu aikin kashewa da rufeta hadi da rigo mata key din. Cikin jin kai take takawa,sanye da wani skinny jeans da yabi jikinta sosai ya lafe, kamar a jikin nata aka dinkashi,manyan mazaunanta da suke da wani irin dan banzan tsini sun fita sosai,saidai kuma shafaffen qirjinta dake boye a t shirt din jikinta ya kawo cikas waien cikar adon da akesonyi da bayyana abinda akeson a bayyana din. Kitson attache ne a kanta daya zuba har gadon baya,ya bullo da qasan gantalelallen mayafin data yane kanta dashi wanda iyakarsa wuyanta.
Har ta doshi sassan hajiya qarama suka shaida mata ta fita, amma ba nisa tayi ba,saita sauya akalarta ta wuce sassan fadeela,tanason ta saba da yarinyar,to amma matsalar ita batasan yadda zata shawo kanta su shaqu ba.

Dai dai lokacin da sãahar ke zaune a madaidaicin falonsu na biyu,suna zaune qasan carfet ita da fadeelan, ita tana cin abinci sãahar din na monitoring dinta,a daya bangaren tana duba homeworks din da aka basu ranar a makaranta.

Sanye take da brown din chiffon gown budaddiya sosai,sai kanta data yafawa vail na plain chiffon din shima brown da bai garasa na jikin rigar haske ba, kyakkyawar fuskarta tayi fresh,tes take fatarta na nan da glowing dinta,babu digon ko tabo ballantana qurji,pink lips dinta sai shegin lips balm sukeyi,zara zara yatsunta take sanyawa tana buda book din page by page tana ganin performance din fadeelan a homeworks dinta na baya.

Sau biyu tana buda baki da niyyar yin magana tana dora mata yatsa akan lips tace

"Shshshsh" tasan tanason yin Santi ne akan abincin da takeci, wanda säahar dince yau ta dafa. A karo na uku data hanata saita langabar da kai
"Please aunty ki barni nace wani abu mana" yadda tayi maganar yayi masifar baiwa sãahar dariya,saita rufe littafin tana murmushi idanunta akan fadeela

"Say it fadee"

"Wallahi anty ban tabacin abinci me dadin wannan ba,kamar daga aljanna aka kawosa" ba shiri dariya sosai ta kubcewa saahar,saita miga hannu ta dauki pillow ta saka mata daga gefanta
"'Bari na tareki kada santi yasa ki fadi" dariya itama ta saki sukaci gaba da yi tare

"Please aunty nanny,zaki ci gaba da dafamin abinci?,harda wanda zanje school dashi don
Allah,nasan abincina sai yafi na kowa dadi" idanu ta lumshe tana gyada kai,a yadda takejin fadeela kamar jininta babu hidimar da bazata ivayi mata ba
"Alright,amma idan satin nan ya wuce baki gama haddace suratul a'alah ba,to zan daina,kin yarda?"
"'Na yarda aunty,nayi algawarin jibi zan gama" ido ta ya fidda tana dubanta da mamaki
"Really?" Kai ta jijiga mata alamun da gaske take.
"Hi fadeela" muryar labiba dake tsaye a kansu ta ratsa kunnuwansu,dukkaninsu babu wanda yasan da shigowarta bare wanzuwarta a gurin.

Daga kansu sukayi kusan lokaci guda suka
dubeta,dai dai lokacin idanunsu suka gauraya
da juna ita da sãahar.
Dan ja baya kadan tayi cikin yanayin dake
nuna qaramar razana
"Ya salam" ta furta can gasan ranta,tana
hadiye wani abu me tauri a maqoshinta,a
ina aka samo wannan cikin gidan?" Ta yiwa
kanta tambayar da batasan amsarta ba,zataso
ta jefa tambayar ga baquwar fuskar,amma
idanunta zuwa fuskarta suna fidda wani irin
kwarini.
Sãahar ce ta fara janye idanun nata daga
kanta,ranta yana dan baci da yadda ta riskesu
gatsau kai tsaye tayi musu kuma tsaye a
ka,saita maida idanunta ga duba littafin
hannun nata ba tare data sake dagowa ta
dubeta ba,saidai a jikinta tana jin kamar tasan
fuskar,kamar ta taba ganinta a wani waje.

Tana jinta ta isa gaban fadeela ta zauna
tana ta janta da surutu,lokaci lokaci idanunta
suna satar kallon sãahar,wadda bata sake
duban sashenta ba,koda ace suna da dabi ar
yahudawa,a qalla tunda musulmi ne su tay!
musu sallama sanda ta riskesu
"Na gama anty" fadeela ta fada bayan ta ajiye
gorar ruwan hannunta
"Good bari na dauko miki hijab,qur ani zamu
fara yi" saita kife littafin ta mige zuwa dakin
fadeelan. Kallo labiba ta bita dashi hankalinta yana tashi, ko ita da take mace ta tabbatar
ta kuma yaqini hakanan ta sallama wannan
din ta cika mace wani abu me cakude da
kishi da tashin hankalin wanzuwarta a gidan
yazo yayi mata tsaye,sai ta maida dubanta ga
fadeela dake qoqarin dauke plate din da taga gama cin abincin tana tattare inda ta bata da
tissue,abinda bata taba gani yarinyar tayi ba "Wacece wannan uktie?" Duban labiban kawai
tayi,da yake itama miskilar kanta ce,kafin tace
komai baaba ramatu ta shigo falon,hannunta
dauke da humidifier da tasan sãahar na
yawan ajjiyeta a gurin saboda tsananin son
qamshinta,waccan ta lalace ta sauyo musu
wata,tana respecting duk wasu buqatu na
sãahar din,don zata iya cewa tsahon zamanta
a gidan,bata taba jin dadin zama da wani
mutum a gidan ba kamarta
"'Barka da dawowa" baaba ramatu ta fadi tana
duban labiba
"Yaushe akayi baquwa a gidan nan?" Ta jefa mata tambayar ba tare data amsa marabar ta
ba
"Ba baquwa bace,kawai ita ke kula da fadeela
yanzun" a take fuskar labiban ta washe,ta saki
garamar dariya.

"A'ah ramatu,kice nanny ce kawai,basai kin
wahalar da harshenki ba" tayi furucin dukka
a kunnen säahar data qaraso gurin hannunta
dauke da gogaggen hijabin fadeela,cikin
wadanda ta dinko mata da kudinta,saboda
tazo ta risketa bata da jiba ko daya,sai wani
fingilalle V shape na uniform dinta.
Hada idanu sukayi da labiban,sai sauran
maganar ta magale mata a magoshi,ta mige
daga zaman da tayi tana fadin
"Zan jira mommy a sassanta, fadeela enjoy
your new nanny" saita dan daafa kan
fadeelan ta soma takawa tana barin falon.
Ran baaba ramatu ba dadi ta ajjiye
humidifier din,tasan halin kowa a gidan,don
kusan kowa a gabanta yayi girmansa, ta samu
guri ta zauna lokacin da sãahar ke sanyawa
fadeela hijab din nata,daga can qasan
zuciyarta tana fassara kallon da kalaman labiba. Ta fahimci ma'anarsu fes,to amma abinda ya bata mamaki daga haduwar farko ko maganar farko babu a tsakaninsu me ya haifar da wannan matsanancin kishin cikin qwayar idanunta?
"Wannan itace labiba, kuma za'a iya cewa ita din ganwa ce ga mahaifin fadeela,wato
'yar matar babansa ce,tana da wasu halaye marasa kyau wani lokacin,sai kinyi haquri da ita" a nutse ta daga kai ta kalli baaba ramatu,saita saki kyakkyawar murmushin nan nata da ba kasafai take yinsa ba,ta taka tana debo litattafansu
"Karki damu baaba ramatu,haquri da ita bai zama dole ba,tunda bani da case da ita" jinjina kai baaba ramatu tayi,tasan sarai tana da kawaici da kuma sanyin hali,hakanan bata da kwaramniya ko hayaniya,amma labiban fa?,tayi imanin koda bata shiga gonarta ba ita zata shiga tata,saidai fatan Allah ya kiyaye.


*HUGUMA*

*_TABARMAR KASHI_**

Page 63

Sasai wuyanta ke cike da wani qatoton abu,sashen hajiya qaraman taso wucewa amma saita kasa,ta samu kujera ta zauna a nan farfajiyar gidan tana jan numfashi tana fesarwa,ba abinda ke gilma mata cikin idanunta sai kyakkyawar surarta,kamewarta da uban kwarjin da zai hana ta takata yadda taso. Ta yaya zaman wannan cikin gidan zai yiwu?,kuma a matsayin me kula da halittar da toufeeq yafiso duk duniya fiye da komai da kowa?,ta yaya zata bari su dinga gwama numfashi tare dashi?,anya idanun hajiya garama ba rufewa yayi ba kuwa harta amshi wannan surar a mazaunin nanny?.

Qafa daya kan daya tana kadata makeken gate din gidan dake da rassa biyu daya daga cikin reshen(enter) wato shigowa ya bude,ta zubawa gun idanu tana fatan hajiya qarama dince ta dawo. Ita dince kuwa,bata iya haqurin jumurin tsaiwar motar bama ta miqe ta bi bayan motar har zuwa parking lot na gidan,dai dai sanda motar ke tsaiwa,tasa hannu ya bude seat din baya wanda tasan a nan hajiya qarama din ke zama driver yana tuqata,ta shiga ta zauna idanunta akan hajiyan dake amsa waya da dukka hankalinta
"Nooo. karki damu MY BABY,duka duka watannin guda nawa ne? ki kwantar da hankalinki ki kammala karatunki,na miki algawarin duk lokacin da nazo bikin yayeku dake din zan taho,na miki wannan algawarin" girjin labiba ne ya buga,a duk sanda taji tana waya da BABY din,sai ta samu fargaba irin wannan,sunan da ita kanta me sunan ba qaramin barazana bane ga kunnuwanta da rayuwarta

"Alright.....kada ki damu da wannan,ki maida hankali kiyi karatu sosai ki fita da result din da yafi qarfin raini... okay,bye,i love you" saita katse wayar murmushi me kama da dariya kwance akan fuskarta,soyayyarta tana sake ratsata,burinta a kanta yana sake hauhawa,lokaci kawai take jira,kuma mutuwa ce kadai zata shiga tsakaninta da cikar wannan burin nata
"'Ya akayi labiba?" Ta waiwaya gareta bayan ta saka wayar a jakarta, numfashi ta ja ta hadiye yawu
"Mommy, nazo na samu andauki wata me kama da aljanu wai a mazaunin nanny"
"Shine me?" Tavi tambayar hankalinta kwance

HA
"Mummy bakiga irin kyau da halittarta bane?,bakya tsoron ta rudi yaa toufeeq da kyan nata?" Qaramar dariya hajiya qarama ta saki
"Toufeeq..
. toufeeq dai? ke bakisan halinsa
bane halan har yanzu?,kin taba ganin idanunsa bisa fuskar wata mace da zummar so ko sha'awa?,bare har yaji tayi masa? inama yake toufeeg din?" Shuru labiba tayi tana juya maganar mommy din. Tabbas ko ita din iya tsahon rayuwarta zata iya irga sau nawa ya daga kai ya kalleta,kallon da mafi yawan lokuta yana mata shine don hukuntata idan tavi wani abu daya saba da nasa ra'ayin,sai taji wannan case din kamar ya mutu ne
"Mommy haseena zata dawo ne?" Sai data buda murfin motar ta saka qafarta waje sannan ta amsa mata Ад
"Ba yanzu ba" ta fara qoqarin fita sai kuma ta dakata,shuru tayi kamar me nazarin wani abu,sanann ta fara magana da labiban a hankali
"Toufeeq allura ce cikin ruwa,me rabo ka dauka,so ki dinga sassautawa kanki wasu abubuwan kinji daughter" daga hakan ta saka gafafunta waje ta fita a motar tabar labiba a ciki.
Shuru tayi gumi na dan tsatstsafowa daga goshinta,mommy din tayi magana cikin kwantar da murya da kuma nuna kulawa,to amma kalaman dake qunshe cikin maganarta....sunyi mata wani iri,me rabo ka dauka?,allurar cikin ruwa?,duka me hakan yake nufi?. Shuru ta sakeyi tanason lallai saita fahimtar da kanta,amma ta gaza gano komai,tunda tace dawowar HASEENA ba yanzu ba,ta toshe duk wani kafa ta tunaninta,dole ta jawo qafafunta ta fita a motar don ta bawa driver din damar rufe motar,saidai a ranta tana jin ya kamata ta kira

hajiyarta ta gaya mata ko ita din zata gano abinda ta gaza ganowa.
Da daren ranar suna saman gadon fadeelan,bayan ta tabbatar ta bata magungunan da afifa ta rubuta ita kuma ta fita da kanta ta siyo. Ta shiryata cikin kayan bacci,kan fadeela na kwance saman cinyarta,gashinta me tsaho da santsi irin na saahar din ya baje saman gafafun sãahar din,ta nace wai sai sãahar din tayi mata kitso.
Itama ba iya kitson tayi ba sai kalba,don haka kalbar taketa qoqarin kitsawa amma tana warewa, kunnuwanta suna kan fadeelan daketa complain din rashin kiranta da Abby din nata baiyi ba. Kusan duk wayar da zaiyi matan tana gurin baaba ramatu,a can suke wayarsu su gama
"Abby yayi busy ne tabbas,amma ayi masa uzuri kinji,ki daina complain da yawa fadee,he cares about you fadee,you have to appreciate his efforts kinji" ta fadi ne don kawai kwantar mata da hankali tare da nuna mata muhimmanci haquri da kau da kai. Kai ta gyada a sanyaye,bata sake cewa komai ba.
Kamar jira kuwa akeyi tayi shurun sai tab din ta fara gara, zamewa tayi da gudu ta dira a gadon ta nufeta,ta iya karatu sosai,don haka ta karanta sunan me kiran
"Aunty,budemin google meet dina,abby ne a nutse ta sauka a gadon,ta dauko mata headphone da fold up stand,ta fara bata headphone din ta saka a kunnenta,sannan ta ware fold up din ta dora mata tab din a ciki don taji dadin amsa wayar,ta koma daga bayan camera din ta saita mata Google meet din.
Cikin qawatacce kuma tsararren balcony din nasa yake a zaune,wanda aka rabashi sassa biyu lounge and eating area qawace yake da wasu irin stone tiles da kuma couch masu tsananin laushi hade da table din dake da kujerunsa guda hudu,sai swing bench daga can gefe guda daya dake mahadin furniture din. Da wasu irin fitilu aka yiwa gurin ado,hakanan aka wadatashi da potted plants a kowanne sago da kuma qasan gurin,tsirran dake iva garawa gurin kyau iska me dadi da kuma qamshin furannin dake magale dasu.
Pajamas ne a jikinsa,farare tas tas dasu,rigar me gajeran hannu ce qwarai,v shape neck dake iya baka damar hango lallausar gargasar dake kwance lambam a girjinsa,hakanan gajartar hannun rigar yasa kake iya ganin dantsensa dake da wasu irin muscles,daga can gasa zuwa tsintsiyar hannun kuma gargasa ce itama me santsi baga sidik.
Wandon jikinsa iyakarsa gwiwa,yayi crossing gafafunsa yana jiran kiran da ya yiwa halittar mafi soyuwa a gareshi ya shiga,hannun damansa coffee dinsa yake sipping kadan kadan. Duka duka bai cika awa guda da dawowa daga office ba,ya sake maida kansa busy qwarai da gaske da tunanin hakan shi zai zame masa abokin debe dukka wata damuwa da kewa.

Miskilin murmushi ne ya subuce a labbansa sanda innocent face din fadeela dake zaune tsakiyar gado da hargitsatsen gashinta ta bayyana
"Assalamualaikum abby" sallamar tata ta ratsashi qwarai,ta kuma dace sosai da muryarta
'Waalaikumus salam,daddy's angel ta girma da gaske,an iya sallama da kyau‚barakallahu fiik"
"Abby,aunty nanny ce ta koyamin" sai ya jinjina kai yana murmushi
"Tace min tafi lada akan ace hello"
"'Da gaske ne" ya amsa mata yana gyara zamansa,ya buda baki zaice wani abu,saidai kafin yace komai din ta rigashi,ta barke da bashi labarin aunty nanny,abubuwan da take koyamata,abubuwan data hanata yi da wadanda ta gyara mata,karatunta da sauransu. Shuruuu kawai yayi yana bin bakinta da kallo tare da sauraren bayananta,yana tsintar abubuwa masu yawa game da labarin nanny din da take bashi,a hankali ya samu kansa da furta
"Alhamdulillah" a gasan zuciyarsa,tana sake gaya masa abubuwan da suke gudanarwa nutsuwa na sake saukar masa game da hannun da diyar tasa ta fada a wannan karon,abinda yake ta taraddadi kenan,sai ya gara sakewa sosai ya bata dukka hankalinsa yana sauraronta,cikin ransa yana jin mai yiwuwa Allah ne ya dubeshi ya share masa damuwarsa ya hada sanyin idaniyar tasa da nanny ta gari
"Kanason ka ganta? daddy na nuna maka ita?" Tayi gasa gasa da muryarta harda dan sunkuyowa screen din wayar alamun quima,tana maganar kuma tana satar kallon säahar dake tsaye bakin mudubi tana
taje kanta tare da gogarin hadeshi cikin
ribbon,fadeelan ce ta watsa mata kan a dasu garin cewa lallai saita koyi kitso itama a kanta.
Yadda tavi maganar da sunkuya da yin qasa qasa da murya ya bashi dariya,ya daga hannu yana shirin dakatar da ita,amma
inaaa... bata tsaya jin ta bakinsa ta juyar da screen din zuwa sashen da sãahar din ke tsaye tana daure gashinta da ya zuba har bayanta.
"aunty na juyo miki da camera kizo ku gaisa da abby na..." Wani muguwar faduwa gaban sãahar din yayi,tamkar wadda aka dasa taci gaba da baiwa camera din baya ba tare data juyo ba,ba abinda take tunawa sai kayan jikinta,inda Allah ya taimaketa doguwar rigace sakakkiya a jikinta,amma duk da hakan tasan tudun mazaunanta da kuma gashinta dake sake a baya yana lilo bazai kasa ganuwa ba,lallai ta yarda quruciya na damun fadeela sosai, banda haka ba wanda zaiyi irin abinda tayi.

Da sauri ya janye idanunsa daga kallon abinda baiyi niyyar gani ba,ya dunqule hannunsa sosai yana fadin
"Angel,move the camera,basai mun gaisa ba" kasancewar akwai headphone a jiki ya sanya ita daya take jin abinda yake fada,saita kyabe fuska tana fadin
"Anty na dauke camera din,yace basai kun gaisa bama" ido ya zubawa fadeelan sosai yana kallonta,can qasan magoshinsa yana qogarin harhada abinda zai fada mata,saboda ta sanyashi kallon abinda bai shiryawa ganin ba,dole ya mata bayani cikin hikima yadda zata fahimta,don ya fahimci ita kanta matar batasan zata juyar mata da camera ba. Zama yayi sosai yana fuskantarta,ya maida fuskarsa serious da zummar mata bayani da kyau,kada wataran ta sakashi ganin abinda baiyi niyya ba

"Fadeela"

"Abby"

"Kina iina?"

"En daddy"

"Daga yau idan na kiraki,idan bance ki bawa wani waya ba kada ki sake yin hakan kinji?" Kai ta gyada a sanyaye

"Kome zaka yima mutum saida izninsa,kinga yanzun ba hijab ko dankwali a jikinta,kuma ba kyau aga mutum a haka,kin saka mata camera,kinga ba zataji dadi ba ko?" Kai ta sake gyadawa da alamu jikinta ya mutu

"Good girl,idan mun gama waya ki bata haquri"

"In sha Allah" sai murmushi ya sake subuce masa,in sha Allah din kamar a bakinta aka radata,bai taba jin ta fadi ba,kamar wata babba,amma yanzun data fada sai yaji wani sanyi a ransa

"Khairan in sha Allah" ya fada a ransa yana jin hope

Please Login or Register in order to submit comment