Reading TABARMAR KASHI 1&2 complete by SAFIYYA HUGUMA Chapter 33 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

data sako kaya masu muhimmanci a mazaunin tsaraba wa mahaifinta. Baki galala da kallo hajiya mansura ta bita dashi, cikin ranta tana jin wani irin kishi yana kamata,a fakaice kamar anaso ne ayi wining a kanta,bayan tarin nasarorin da akaci a kanta,har yanzu wannan matar...
..wannan
mutum dayar ta gagara cimmata yadda ya kamata,tsakaninsu kar rasan kar ne, amma har yanzu qudurinta bai isa ga inda taso ya qarasa ba,MUTUM DAYA TAK! Ita ta samu dukka wasu damarmaki da taso ace ita ta samesu,duk da tayi musu nisan zangon da suke da imanin kasantuwarta a cikinsu abune mai wahalar yiwuwa,wannan ya rage garfi da kaifin wasu damarmakin nata ainun WACECE?!


AMSARKU TANA GABA_.


Juya cokali kawai takeyi cikin abincin da hajiya mansura ta gabatar mata,tana kuma amsa tambayoyin dr jarma. Gaba daya hankalinta bai waien, Allah Allah kawai takevi a tashi daga zaman cin abincin da akace an shirya da sunanta don tayata murnar dawowa,cikin ranta tana fata da addu'ar kada Allah yasa dr din yace ta zauna tare da su.

Yana tsame hannunsa itama ta tsame nata tana gogewa da tissue,haiiya mansura ta kalli plate din nata

"Ya haka kuma?,banga kinci komai ba"

"alhamdulillah ‚naci abinci a jirgi"

"Abincin jirgi wani abinci ne? ki zauna ki garasa ci, yanzu zan yiwa su taiba magana su sake gyara miki dakinki" tana gama maganar nadeeya na miqewa,ta goya jakarta tana duban dr jarma

"Abba zan wuce gidan yaa toufeeq,fadeela tun ina hanya tasa ake kirana"


"Alright,ki mintsinemin kumatunta ja'ira,tunda tayi sabuwar nanny ta rabu da zuwarmin, kullum kuma nayi kiranta cikin bani labarinta take,ki gaya mata nayi mata garin salary akan abinda ake biyanta,ina mata godiya da kyau da kyau,don da alama tasan aikinta sosai" murmushi nadeeya tayi,tana jin dadin yadda Dr bai hanata tafiya ba,sanann kuma ita kanta tana jin sãahar har ranta,duk da basu dade da sanin juna ba,amma tana jin tamkar ta dade da saninta.

Sai da taga sun dau hanyar barin gidan ta sauke ajiyar zuciya,koda ta yiwa dr alqawarin zasu zo suyi kwanaki da fadeelan,batajin zata iya wuce kwana daya ko biyu.

Guri hajiya mansura ta samu ta zauna bayan fitar nadeeya

"'Dr inason magana da kai" kansa ya cire daga wayarsa da yake dannawa,daya hannun nasa kuma yana sakace da toothpick

"Nikam nace ba,bai kamata ace kana raye ba amma dukka yaran da Allah ya baka basa rayuwa tare da kai,ka tattarasu ka barsu a wani guri na daban,ni kaina da nake matsayin uwa a waiensu sam babu wata shaquwa a tsakaninmu" a nutse ya ajjiye tsinken sakacen yana dubanta

"Tohhhh...

...yau kuma wajen qarama dinne
ya koma wani guri na daban?,kin manta suna rayuwa ne garqashin gidan da toufeeg ya gina da kansa? nadeeya da ita tafi sabawa,a hannunta ta garasa girmanta, taoufeeq dinma kusan hakane,sannan shi namiji ne wanda banda gaddara da a yanzun yana qarqashin kulawar matarsa ne,so a ciki bansan meye matsalarki ba" ya qarashe maganar yana kafeta da idanu.

Ajiyar zuciya ta sauke,dama tayi zaton hakan daga gurinsa,yadda qarama ta tattare yaran gaba daya ta maidasu qarqashin mulkinta ita kadai yana mugun ci mata tuwo a qwarya,wanann dalilin ya sanya ta tattara labiba ta miga mata ko hakan zai sanya a samu wani sauyi,amma dai jiya i yau babu wani abu da ya canza

"Shikenan" abinda ta fada kenam cikin suyar zuciya ta miqe tana tattare gurin,zuciyarta kamar zata fito ta qirjinta. Binta shi kuma yaci gaba dayi da kallo,yana mamakin yadda har zata iya gaya masa wannan maganar akan qarama,ko ta mance cewa ta silarta ta sanshi?,ta silarta ta zama abinda take a yanzu take kuma amsa sunan da take amsawa na matarsa.

Dukka wannan shi ba damuwarsa bane,abu daya ya sani,duk abinda zai takura yaran ya sakasu cikin qunci zuciyarsa ko qangani bata so,muddin dai wannan abun bai kaucewa hanyar addini da al'ada ba,can qasan rai da zuciyarsa yasha kasa runtsawa cikin dare,he have feeling of guilt akan TOUFEEQ da NADEEYA,saidai har yanzu kwanyarsa ta kasa gaya masa meye ainihin tagamaimen laifin?,idan ya matsa da bincikar kansa kuma sai matsanancin ciwon kai ya saukar masa.

_uhmmmmm hmmmmm_

Turus ta tsaya cikin mamakin ganin cewa ba wani mummunan abu bane ya sameta sanadiyyar ihunta data jiyo tun daga toilet din dakinta. Suna rungume da juna ne ita da nadeeya kamar wadanda suka bace tsahon shekaru sal yau suke ganin junansu.
Nadeeyan ta daga fadeela tayi juyi tayi juyi da ita har babu adadi sai kawai sãahar din ta saki murmushi ta juya ta koma ta garasa abinda takeyi,saboda taga basa ganin kowa sai kansu,masu aikin gidan nata wucewa da kayan nadeeya din zuwa cikin dakinta


"Ya zaki tafi?,ki tsaya mana mu gaisa" muryar
nadeeya ta ratsa kunnensa sãahar dake
yunqurin komawa ciki. Waiwayowa tayi tana
murmushi

"Ai naga baku gama ba" ta fadi tana duban
nadeeva da take sake ganin wasu kamanni
saman fuskarta,tana ji a jikinta kamar ta santa
a wani guri daban kafin wannan lokacin.
Karamar dariya nadeeya ta saki tana
takowa zuwa inda säahar ke tsaye

"Indai nida ukhtie ne wallahi bakiga komai ba"
saita buda hannuwanta tayi hugging säahar
kadan tana murmushi yadda larabawa ke
marabtar 'yan uwansu

"'Fatan na sameku lafiya" ta fada tana janye
jikinta,fuskarta cike da fara'a


"Alhamdulillah"

"Tambaya ta farko,don Allah me uktie takeci ta fara kumatu?" Dariyar da sãahar bata shirya ba ta subuce mata,yadda nadeeya tayi tambayar tana riqe habarta da yatsarta,da alama da gaske abun yana bata mamaki,ko ba'a gayawa sãahar ba alamu sun nuna mata nadeeya mutum ce me barkwanci da faran faran da yawan surutu

"Ki nutsu ki huta,zaki ganewa idanunki" baaba ramatu ta bayar da amsar tana dariya

"En lallai to nima ko dole aci dani, bari na garasa" nadeeya ta fada tana daukar garamar suitcase din data rigo suka wuce ciki tare,saahar ta koma kitchen,fadeela tabi bayan nadeeya.

66

*HUGUMA*

* TABARMAR KASHI_*

DON MARTABAR MANZAN ALLAH ME
FITARWA KIYI HAKURI KIBAR MANA
KAYANMU

To kusan yinin ranar fadeela na tare da nadeeya,har sai da sãahar tayi mata dan biki

"An samu sister nadeeya an manta da ni ko?"
Dariya tayi,ta taho da gudu ta rungume sãahar din ta baya tana fadin

"A'an Aunty,sorry".

Duk da säahar din na dan basu guri tana Kame kanta a dakinta,amma duk da haka nadeeyan bata qyaleta ba,komai saita sanyota a ciki,kota biyota dakin ta fiddota,da dare ma sai gata da dalleliyar kaftan abaya ta mata me kyau da sulbi 'yar saudiyya

"Ga tsarabarki aunty nanny" sosai kyautar ta burgeta,ta kuma yaba tare da yi mata godiya.

Cikin sati guda kacal da dawowar nadeeya sukayi wani irin sabawa da sãahar,sabon da ita kanta sãahar batasan lokacin da ya faru ba,kafin cikar sati biyu sai suka zama tamkar wasu 'yan uwa. Abubuwa da yawa na kula da fadeela tare suke yinsa,idan tayi wani abun,wani abun nadeeya ce zata karba.
Wani irin qaunar sãahar nadeeya takeji har cikin ranta,bata sani ba,ko don bata taso da
'yar uwa sa'arta kamar sãahar din bane? to amma kuma akwai LABIBA da HASEENA,SU din kusan zata iva cewa sun dan rayu tare,to saidai ko kadan bataii abinda takeji game da sãahar ba,ko don ita din tana da wasu dabi'u
da kuma halaye tare da wasu qualities da bata
taba ganinsu daga gurin su biyun da suke
kamar sune dolenta ba?.

Zuwan nadeeva sai ya sanya itama ta dan
sake,takan fita zuwa gida tayi wasu awanni ta
dawo,a nan ne afifa ke tsokanarta,wai nadeeya
nason qwace mata faada,tayi maganar tana
dariya. Afifa tasan labarin nadeeya kaf daha
bakin säaharduk da basu taba ganin juna ba.
Murmushi kawai säahar ta saki

"Bestie,da alama har yau bakisan matsayinki a
guri na ba" hararar wasa ta jefa mata

"Na sani mana,tunda gashi har yau kingi
amsar mahmud yadda ya dace" zancan da ya
sanyata miqewa kenan,ta lalubi mayafinta tana
maida rolling din kanta


"An ambato maqiyin naki ko?"

"No,kawai inason na biya a wankemin kaina sannan na wuce gida,yau na yiwa fadeela algawari zan dafa mata burabusko ita da nadeeya....tashi don Allah ki kaini,saiki saukeni a gida" gyara kwanciyarta afifa tay!

"Bazan iya ba,ki dauki motar ki kawai ki dinga amfani da ita"

"Kin manta ni din nanny ce?" Ta fada tana murmushi,don zuwa yanzun ita dadin sunan ma takeji,hakanan rayuwar da takeyi din tana bata wani irin nutsuwa,ta kauce daga idanun maza kwata kwata,gidan ya zame mata kamar wata mafaka

"Kina sauri ne kawai ki gudu kada ku hadu da abba" murmushi tayi tana maida agogon hannunta

"Duka koma meye zakice bazan musa ba,tashi don Allah kafin ya dawo mu hadu" hakanan afifa ta mige,ta dauko abaya ta dora saman kayan jikinta tanata mita,ta dauki key din motar tabi bayan sãahar din.

A kitchen ta tadda maama,tayi mata sallama,sai ta waiwayo tana dubanta

"Zo nan sãahar" ta kirata tana tsame hannunta daga ruwan da take wanke alayyahu,ta yiwa baaba rabi sign saita fita a kitchen din,ta barsu su uku

"Zauna" tace da ita bayan ta jawo kujeru guda biyu dake kitchen din ta zauna a daya.

Cikin mutuwar jiki kamar wadda aka yiwa tayin zama bisa garwashin wuta ta zauna

"Wannan rayuwar ba ita nake da muradin ganin kinayi ba,nafi bugatar ganinki a dakin mijinki kamar kowacce mace,kije ki sauya tunani ki kuma canza shawara" iya abinda tace kenan da ita.

Duk da kalmomin da tayi amfani dasu ba masu yawa bane amma nauyinsu ya cika mizani taf,jiki a salube ta mige ta sake iaddada mata sallamar sannan ta fito.

Tuni har afifa ta tayar da motar ta kuma barta a kunne saita shige seat din gaba ta maida murfin ta rufe,afifan tadan juya kadan ta kalleta,saita dauke kai ba tare da tace mata komai ba ta motsa motar zuwa gaba,ta saki hon kadan,baaba habu ya taso ya bude musu yana musu fatan sauka lafiya.

Suna gogarin fita a layin motar Dr mamman girema na shigowa,ya kuma gansu,don haka yasa driver dinsa yin slow da motar har suka hade a tsakiya,ya sauke Glass din motar yana duban afifa da idanunsa dake saye da gilashin garawa ido qarfin gani

"Sannu da dawowa abba"

"Yauwa sannu,ku dawo ciki,inason ganinku" hantar cikin sãahar ce ta kada,don bata manta da awa gudan da suka share dashi a waya ba wancan satin,yau din sai da tayi kamar ba zatazo gida ba,so amma zuciyartat a damu dason ganin maamanta,wannan dalilin ya sanyata fitowa.

A gofar gate afifa ta faka motarta kalli sãahar da gaba daya takejin wani rugugin tashin hankali yana sauko mata

"'Muie ko?"

"'Na shiga uku afifa,wallahi zancan mahmud ne" wani duba afifan tayi mata

"'To ai yayi kyau" da kallo tabi afifan,ganin yadda tayi hankalinta kwance bata ma wan damu ba,ga furta sunan Allah da qarfi tana runtse idonta da sauraron bugun da zuciyarta takeyi,ta bude murfin motar tabi bayan afifan.

Tuni har ya isa falonsa yana cire hularsa ya ajiye yana zare agogon hannunsa. Kamar kaiin da aka watsawa ruwa suka samu guri qasan carfet suka zauna,yanayin fuskarsa shine ya fadar musu da gaba tun baikai ga cewa komai ba,a yadda yake da sauqin kai da kuma haba haba da iyalansa,dole yanayinsa a yau ya sanyasu a fargaba.

Sosai ya zauna saman sofa yana maida bayansa ya jinginar da kujera yana dubansu daya bayan daya

"Aishatu" yayi kiran afifa da ainihin sunanta,kai tadan daga kadan sannan ta amsa

"Na'am abba"

"Me kike jira har yanzu baki gabatar min da mijin aure ba?" Shuru ta danyi tana dawurwura,saita rasa me zatace da abban. A halin yanzu tana da samari da a qalla sun kusa mutum hudu,kuma dukkansu da aure suke sonta,saidai babu wanda ta maida hankalinta a kansa

"Na sani nasan komai,saboda haka kije na baki wata uku ki karancesu ki fitar da wanda kikeso a cikinsu"

"' In sha Allah abba" dauke dubansa yayi ya mayar kan sãahar,a jikinta taji irin duban da yayi mata,wasu daga cikin maganganunsa kuma suka dawo mata

"Na miki alfarma na kuma daga miki qafa saboda banason na matsanta miki,na kashe miki gishirwar yin aikin duk da sam aikin bai dave dake ba,amma na barki kinje kinvi saboda babu haramci sai tarin lada a cikinsa..
... okaci yayi da zaki tsaya ki fuskanci
wanda yake sonki da gaskiya.

"Ummee,a ina maganarmu ta kwana? ya muke ciki?" Yayi mata tambayar da a waienta tamkar gatse ce.

"Abba‚bamu gama fahimtar juna ba" gafarsa daya ya dora kan daya

"Ta yaya zaki fahimci juna bayan akwai nisan tazara a tsakaninku?,to ni na gama nawa,na gama fuskantarsa,hatta bincike nayi a kansa,babu wata matsala tattare da shi,abinda kawai ya rage shine ke ki fuskanceshi,don haka daga yau yana da lasisin zuwa gurinki zance a duk lokacin da ya buqaci baka,sannan damar fuskantarsa da kike da ita wata daya ne kacal,daga lokacin duk abinda naga ya dace zan iya yankewa" sanda ya sauka a zancan yayi daidai da jin tsargawar gumi me dumi daga kowanne sashe na jikinta,sai take jinta kamar ba'a zaune take dai dai ba,batu fa abba yakeyi na aure a karo na biyu cikin rayuwarta,bayan ko shekara hudu cikakku batayi ba daga fita daga siradin data afka ba,tayi zaton saita debe shekara koma ma babu wanda yayi mata sha awar yin aure bare akai ga batun yi mata tayinsa

"Ku tashi kuje,Allah yayi muku albarka,banason kuma kowacce takai magariba a waje ba tare data nufi inda ta dosa ba"

"To abba" afifa ta samu damar fadi,yayin da sãahar keta qoqarin ganin ta mige ta fita a falon ba tare da an samu matsala ta fadi qasa
ba.

"Kaini nasarawa kawai,na fasa wankin kan" abinda sãahar ta fadi kenan tana kwantar da kanta jikin kujerar tana jin toro da fargabar hukuncin da abban zai iya yankewa a wata gudan daya deba mata

"Aure fa kenan,aure da mahmud,ta karba sadakinsa.ta amsa sunan matarsa,har ta hada shimfida dash.

"A'uzu bi kalimatillahit tammati min sharri ma khalag" taji bakinta yana furtawa bayan runtse idanunta da tayi. Kadan afifa ta waiwayo ya dubeta,sai ta mayar kan titi,a irin wannan yanayin ba kasafai ta fiya son yiwa sãahar din magana ba,don haka batace komai ba har sai da suka iso katafaren gate din gidan,tana shirin fita afifa tace da ita "Take care of yourself.... kada kie ki zurafafa tunani,kinsan dai kina da ciwon kai" kai kawai ta gyadawa afifan,ba tare dat waiwayo ba ta wuce kai tsaye zuwa qaramar qofar dake manne da gate din daha gefe ta fara knocking da wani irin sanyi da mutuwar jiki kamar wadda aka yiwa mugun duka.

Allah ya taimaketa sanda ta shigo gidan nadeeva tana tare da fadeela,ta jiyo kakacinsu a dakin nadeeyan,kamar ma game suke bugawa ita da ita,sai ta sulale ta wuce dakinta ba tare data bari sun ankara da dawowarta ba,don a yanzun kadaici kawai take bugata,batason hayaniya ko doguwar hira.

Kwance kawai tayi tana saqa da warwara,ba tabbatuwar aure a kanta ba,'ah....ambatar kalmar kadai tana sanyata fargaba da razani,wai ta yaya zata iya hada muhalli da wani d'a namiji kuma wai a kirata matarsa? iya wannan tunanin kadai juya mata kwanya yakeyi tare da gara sanyata a wata dimuwa da kuma damuwa.

Gab da magariba ta shiga wanka,ta fito ta shirya cikin wata lallausar riga me hade da wandonta,ta sanya hijab tayi sallar magariba,taci gaba da zama saman abun sallar,tana jin motsi da gilmawar nadeeya da fadeela,wani lokaci harda baaba ramatu.
Tasan ba lallai su san ta dawo ba,saboda duk wani qwan lantarki me haske ta kasheshi,sai dim light kawai.

Har nadeeya ta gota dakin ¡ilkinta ya bata kamar akwai mutum,saboda kana iya jin gamshin turaren sãahar me sanyi da baya buya yana ratsa qofar zuwa hallway din.
Komawa tayi da baya ta murda qofar,sai ta bude,ta sanya kai cikin mamaki bakinta dauke da sallama,sãahar dake shirin tayar da sallar isha'i ta dakata tana amsawa

"Antvn fadee,har yaushe kika dawo haka?,muna can muna jajenki,i called you several times amma ban sameki ba? mutuniyar tana can tana dakon dawowarkita kasa zaune ta kasa tsaye tun dazun‚bakinta da labari" dan lumshe ido tayi cikin murmushi

"Nafi awa da dawowa,na shigo ne banjin dadi shi yasa na kebe"

"Ya salam! me ya sameki?" Nadeeya tayi maganar sautin muryarta na nuna tsantsar kulawa damuwa da qauna

"It's not something serious,i felt relieved"

"Really?" Kai ta gyada tana murmushi,saboda ta hangi wani irin damuwa da kulawa da ita shigen na afifa

"Bazan gayawa faadee dinki ba,if not ta zama itace patient din,please zakiyi joining dinmu muyi dinner?" Kai tadan yada gefe

"Banajin yunwa,amma zanyi qoqari ko ban fito dinner ba,zamu hadu kafin animan"

"Is okay,Allah yasa kaffara ne'ta fadi cikin mutuwar jiki ta juya ta fice tana jawa sãahar qofar. Ajiyar Zuciya ta sauke me qarfi,tana mamakin yadda suka damu da ita da al'amuranta a lokaci guda haka.

Sai wajen Tara na dare,dai dai lokacin kwanciya baccin fadeela sannan ta shirya ta fita don tayi mata shirin bacci,aikin kulawar ya rage mata sosai tunda ko yaushe nadeeya na kula mata da ita koda bata a kusa. Qaramin hijab ta zura ta fito a dakin.

Kasancewar qofar dakin bata kammala rufewa ba tun bata gama shiga ba ta fahimci video call sukeyi,duka ita da fadeelan na samon gado sunyi rub da ciki,sun sanya system din nadeeya din a gaba suna faman surutu.
*HUGUMA*

*_TABARMAR KASHI_*

67

"'yauwa maji....gata nan" nadeeya ta fada
tana murmushi idanunta akan fuskar sãahar.
Tsarguwa kawai tayi,tasan hirarta akeyi
kenan batasan itakam wanne irin gauna
nadeeya da fadeela ke mata ba da basa gajiya
da ambatonta ba a duk wurin da suka zauna
ba

"Marhaban da ita‚ta qaraso mu gaisa" wata
nutsatsiyar murya dake dauke da accent na
arabic ya fidda amon maganar.

Bata da wani zabi,tunda taji abinda ta
fada,uwa uba sunan maji ba bago bane a kunnuwanta,suna ne da a galla tana jinsa daga bakin nadeeya da fadeela yafi sau uku a rana.
A nutse ta taka zuwa gefan gadon,nadeeya ta zauna sosai tana juyar mata da fuskar system
din zuwa tata fuskar

"Ma sha Allah, intee jameela" murmushi sãahar ta danyi,tana dan sadda da kanta daga kallon tata kyakkyawar fuskar,fuskar da shekaru suka fara bayyana samanta,amma kuma bisa dukkan alamu kyakkyawar kulawa da ingatacciyar rayuwar da take ciki bai bar tsufa ya bayyana ba. Wani irin kyau me daukan hankali wanda dukka kamanninta sune tsaf bisa fuskar nadeeya a yanzu

"Ki dayra,wesh wella famille?" Ta tambayeta da tantagaryar labarancin larabawan Algeria
"Maii namu larabcin fa ba irin naku bane"
nadeeya tayi magana da shagwabar da sãahar
bata taba gani tayi ba

"Ya salam, ina mantawa ne,kina lafiya? ya kuma iyalinki?" Murmushi ta sake

"Alhamdulillah, da fatan kina lafiya"

"Alhamdulillah, Allah yayi albarka,naji dadin ganinki,na san sunanki da kyau,amma bansan fuskarki ba" maii ta fadi mayalwacin murmushin dake dauke da nutsuwarta ta halitta na fita a fuskarta. Har qasan zuciyarta tana jin dadin yadda idanunta ke iya hango sauyi daga jikartata,fadeela rayuwarta ce,tana mata wani irin so da zata iya cewa soyayyar da takewa toufeeq da nadeeya ce tayi tsuntsuwa ta koma kanta,fadeela ita daya ce makamin data tabbatar a yanzun dukkan maqiyinta dake Nigeria zai iya amfani dashi ya cutatar da ita,cutarwar kuma ta risketa kai tsaye har gasarta Algeria. Cikin dabara ta sulale ta wuce wardrobe din fadeela tana fidda mata kayan bacci,saidai hakan bai hanata jin wasu hirarrakin nasu sama sama,duk da bata dora hankalinta a kai ba.

Tana fita daga closet din taji an daneta an riqeta qam qam,kafin tace komai muryar fadeela ta ratsata
"Albishir dinki aunty nanny" dariya taso kubce mata,saboda yadda tayi hausar ma kanaji kasan ba iya karin maganar tayi ba,saita zura hannu ta kamota ta dawo da ita gabanta

"Wannan hausa taki....to ba laifi goro"

"Ni bana cin goro,amma dai..
.. ki tayani

murna,am very happy today,
next week abby zai dawo" sai ta qyalgyale da dariya tana nuna zallar murnarta. Da kyau sãahar ta kama hannuwan fadeela cikin nata tana tayata murmushin,duk da hakanan taji zuciyarta ta harba ba tare da wani dalili ba

"Am so happy nima fadee,congratulations" rungume sãahar din tayi,itama sai ta buda hannayenta ta sanyata sosai a jikinta tana tayata murnar.

*******Cikin kwanakin gaba daya shire shiryen dawowarsa akeyi cikin gidan,nadeeya gaba daya ta kasa zama,ita da fadeelan batasan waye yafi wani murna da zumudi ba,itadai 'yar kallo ce,amma kusan kullum sai an fita shopping na dawowar abbyn fadeela.
Tun tana janye jiki har nadeeya ta sakata tsundum a harkar,tunda ta fahimci sãahar din ta iya mota ta hanata sukuni,duk inda zasu saita marairaice mata akan tayi drive nasu
Zuwa gurin,hakanan ba yadda ta iya take karba su tafi.

Sai a sannan ra fahimci siyayyar da suke fita sukeyi,a nata gurin tsabar son yawo ne irin na nadeeya,qananun kayayyakin amfani dake sashensa ake canzawa,abinda taji hajiya qarama na cewa nadeeyan tayi magana da company suzo su sauya masa komai kamar yadda aka saba,amma son yawo dai yasa tace da kanta zata siyo komai. Duk da ko sau daya bata taba takawa sassan sa ba,amma bataga wani abu daya baci ko ya lalace da za'a sauyashi ba. Kamar nadeeya tasan me take tunani, ranar suna tafe cikin ShopRite tana zaban wasu turarukan daki na ruwa masi shegen tsada,ta dan ja tsaki kadan ta waiwayo tana duban sãahar dake amsa wayar afifa
"Aunty N,don Allah tayani zaben turarukan nan mana,yaa toufeeq akwai shi da taste a zabi inason kome na siyo ya zama unique" zare wayar taki daga kunnenta tana duban nadeeya,duk lokacin data ambaci sunan
TOUFEEQ sai taji gabanta ya fadi,ranta kuma ya baci
"Basu isa bane haka sis nadeeya?" Ido tadan fidda
"Da saura,indai yaa ya dawo daga tafiya muddin ya wuce one month yakai two to sai an canza masa irin wadan nan kayayvakin" batace komai ba sukayi sallama da afifa,ta tako gurin zuciyarta na tuna mata maganganun da sukayi da afifa yanzu akan mahmud. Ta fuskanci ta garfi da yaji mahmud din yakeson kafa kanshi a gidansu tare da maida kansa dan gida,to amma zata gani indai ana siyan so a dole.
Sosai ta nutsu ta zaba wasu kalolin, wadanda ita kanta nadeeya sai data yaba

"Wow,gaskiya u are the best selector" murmushi ya qwacewa saahar din,saita koma gefe tana jiran su kammala.

Tana ganin yadda suka koma zaben kayan da zasu saka ranar da abby din zai dawo, nadeeyan tayi tayi tazo ta zaba itama,saita girgiza musu kai alamun a'ah,fadeela ta marairaice kamar zata saki kuka,ta rige hannunta kam

"'Please anty N"ta fada itama kamar yadda taji nadeeya ta koma ce mata

"Okay,kije ki zabarmin fadee na,koma meye i will accept it" da haka ta samu ta barta,bayan sun kammala kuwa sai gasu da leda wai duka kayanta ne na tarar abby

"Wai wai,sis nadee, thank you, amma kayan is too much gaskiya" murmushi ta sake

"'Wallahi Allah ko?" Ta fada tana duban sãahar

"Ina jinki ne kamar wadda muka fito ciki daya da ita,banajin banbanci tsakaninki da yaa toufeeq "

ambatar sunan ya sake sanyata lumshe idanu sannan kuma ta budesu, Allah ya sani bata qaunar jin sunan sam,saidai don babu yadda zatayi,shi daya ne tal ambaton sunansa yake sanyata jin faduwar gaba.

A falonsu na biyu ta barsu baaba ramatu tana tayasu duba siyayyar ta shige dakinta ta watsa ruwa,sannan ta wuce kitchen don ta samar musu da abinda zasuci,saboda fafur sukaqi girkin zuwaira,sal ya zamana ita ke musu girki su hudun,nadeeya fadeela ita sai baaba ramatu. Ta sauya musu abinci sosai,daga girke girken fararen fara zuwa abinciccikan hausawa da abincin yaran maamanta wato buzaye,sai na yaren abbanta wato shuwa,duk da har yanzun bata tantance yarensu ba su din, amma kana kallonsu kasan babu ta inda suka hada Jini da HAUSA banda yaren dake bakinsu,a ido kuma sai ka rantse zo na kasheka da hausan basu sani ba. Ita dinma mutane da yawa kallon da suke mata kenan.

Tun a ranar suka gama tsara bin guard airport su taho da abbyn fadeelan, harda sunanta suka jefa a ciki, murmushi tayi can qasan zuciyarta tace "Saboda gayyar sodi" amma a zahiri batace dasu dai komai ba,ita haka kawai take jin dama me gidan da suketa zumudin dawowar tasa zaiyi zamansa a can,cikin gidan yaci gaba da kasancewa iya yasu yasu mata.

********Ana gobe zai dawo nadeeya ta hanata sakat,duk da yana da cook dinsa permanent da yake masa girke girke tare da tanadar dukkan abinda yakeso,qwararren cook daya qware waien sarrafa nau'ikan abinci,cook din da ake biya da kudade masu nauyi,samfurin albashin wani ma'aikacin na wata guda…...amma duk da haka nadeeya sai data shirya nata dafe dafen

"Yaa moha ya jima baici abinci na ba,zan bashi mamaki wannan karon,zaiji canjin taste" yadda nadeeya keta sanyata a abubuwa tana zugewa yasa a wannan gabar don kada taji babu dadi ta karba ragamar yin fried rice.

Saidai kuma a daddafe ta gama hada kayan bugata ta ajiye,saboda wani ciwon kai da ya saukar mata lokaci guda,sauqin abun taji suna maganar evening flight ne,sai tasa a ranta zuwa goben xata warware in sha Allah. Ba wanda ta gayawa a cikinsu don kada su sanya damuwarsu a kanta,ta kawowa walwala da farincikin da suke ciki naqasu,sai ta wuce daki kawai ta kwanta abinta.

Washegari ta kammala komai akan lokaci,duk da har lokacin tana dannewa ne kawai amma bata dawo dai dai ba,tana gamawa ko wanka bata iyayi ba ta koma gado ta nade tana sauke numfashin,sauqin abu

Please Login or Register in order to submit comment