Reading TABARMAR KASHI 1&2 complete by SAFIYYA HUGUMA Chapter 56 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yana maganar ne a gaban fauziyya,idan yana irin wannan maganar tashi take ta basu guri, saidai ga dukkan me hankali a lokacin idan ya kalleta zai fahimci yadda zuciyarta ke suya a gasan qirjinta. Shifa kam takanyi murmushi ne kawai

"Nisful hayaat,ban baka wani abu nawa wai don ka maidamin koda kwatankwacinsa ba bare ninkinsa,da kai da kaya duka mallakar wuya ne" kai yake girgizawa

"Na sani,amma kada ki manta,komai naki ya qare,fili biyu ne kawai ya rage miki da gida guda daya"

"'Kaci halak malak fa"tace dashi tana murmushi.

Dukka wadannan algawura da alwashi sun tashi a
banza daga lokacin da fauziyya ta yiwa zuciyarta saqa
da mugun zare

"Mu biyu kacal nahaifiyarmu ta haifa,bazan taba bari wata mace da ta sameshi daga sama ta fini cin
moriyarsa ba" fauziyya ta fada sanda take tsaye a gaban madubi tana gayawa kanta da kanta.

Dukka wadannan alqawura da burika a sannu
suka bi ruwa suka kuma shafe daga tunani da kwanyar
mahmud. Lokacin da ya kamata ace rayuwa ta koma musu dai dai maji da kusan ita taci wahalar komai sai ta
koma 'yar kallo daga gefe,wasu abubuwan saidai taji
daga fauziyya cikin waqe da habaici. A yanzu ta zama
tamkar uwarsa,da ita yake shawara,kuma duk abinda
tace ya zauna kenan. Kamfanin da suka bashi aiki sun
hada masa da kyautar gida da mota kamar yadda ya
shaidawa maji zasu bashin kafin tabbatuwar
al'amarin,saidai koda suka bayar din a bakin fauziyya ta
fara ji,ranar suna hira cikin falonta tana daga daki, ta fito
zata wankewa nadeeya jikinta fauziyyan tace

"Maji, kinji abin arziqi ko?, kamfani sun bawa yaaya gida da mota,zamu tashi daga nan in sha Allahu,ki tayashi murna" wani abune ya tsaya nata a wuya,al'amurinsu ya zama abun tsoro, saboda tako ina babu lamari na hankali a ciki,wai ita matarsa mafi kusanci da shi,a yau ta zama

'yar kallo,labarin da za'a ji a bakinsa yau ita takeji a bakin wani

"Allah ya sanya alkhairi" kawai tace dasu tana ficewa abinta. Har taje ta dawo suna zaune a gurin, tana gyarawa nadeeyar jikinta sai gashi ya shigo. Sau daya tak ta kalleshi ta kauda kanta,saboda zuwa yanzu ta sallamashi,abu daya ne yake bata nutsuwar ruhi addu'ar da takeyi,ta rame sosai a lokacin saboda tsananin damuwar da take ciki da abubuwan da take ga suna faruwa,gidanta a yanzun bata jin nata ne sam.

Akwai alamun jikinsa ya sanyaya kadan sai ya tako ciki
"Wai ke me yake damunki? ‚gaba daya kin canza hali?" Ya fada yana kallonta,qasan ransa yana jin damuwa ne tarin yawa,amma kuma wani sashe na zuciyarsa najin ba komai bane muddin fauziyya tana cikin farinciki da walwala

"Me yake damunki nace?,kin sake sabbin baqaqen halaye shifa" abun yayi mata ciwo sosai,wato itace ma ta sake sabbin halaye baqaqe

"Ba komai" ta bashi ams tana daga nadeeya don saka mata riga

"Ai shikenan,sai kije kiyita yi tunda haka kika zaba" ya. bata amsa yanason fita a dakin amma kuma sai ya kasa fitar,ya samu guri ya zauna,har ta gama shirya yarinyar ta kwantar da ita,ta gyarawa toufeeq shima tasa kwanciyar,saboda tun lokacin da abun ya soma faruwa ya raba daki da ita,itama bata sake nemansa ba,tunda taje sau daya yayi mata korar kare

"Don Allah idan ka gama ka fita zan rufe qofata" ta fada da sassanyan muryarta

"Korata ma kike shifa?" Yadda ya tambayeta a yau din da tausasawa sai ya sanya hawaye sauka daga idanunta,daga nan kuma ta fashe masa da kuka sosai harda shashsheda.

Kasa rarrashinta yayi yadda suka saba a baya,yana zaune ya zuba mata ido yana jin zuciyarsa tana gonewa,a cikin ruhinsa yana jin shifa bata cancanci haka ba,amma kuma bazai taba iya daina abinda yakeyi ba,shifa tayi masa abinda uwa mahaifiya cs kawai zata yi hakan wa d'anta. Sai data ci ta cinye don kanta sannan ya qaraso gareta. Miji da mata sai Allah, a nan ya samu hadin kanta,abinda shi kansa ya jima bai nemeta dashi-ba. Bayan komai ya kammala cikin hikima da kwantar da kai ta soma masa magana akan matsalar da suke fuskanta su dukansu

*HUGUMA*


* TABARMAR KASHI_*

Book 02 Page 42

"Nifa bakiyimin komai ba kibar ma maganar don Allah, banason bacin ran fauziyya gaskiya,a kan ranta ya baci komai ma zan iya aikatawa,yar uwata ce bani da kamarta,farincikinta shine nawa, zama lafiya da ita shine zama lafiya da ni" shuru tayi tana juya maganar a ranta,tabbas akwai qamshin gaskiya akan abinda zuciyarta keta raya mata. Tun faruwar wannan mu' amalar tsakaninta dashi sai aka dan samu sassauci kadan,ya daina fushin da ya dauka gadan gadan da ita,yaci gaba da bata kufin cefane shima, amma kuma har yanzu abubuwa da yawa bata canza zani ba, fauziyya taci gaba da juya akalar gidan tamkar yadda mahaifiya ke juya akalar gidan danta. Hatta da abinci a yanzun suna cin duk abinda fauziyya ta zabi a girka ne. A haka aka yiwa mahmud albashin farko,sun kuma hada masa da wani kudi da suke bawa sabon ma'aikacinsu,don haka a sannan ya shirya tashinsu daga gidan, zuwa babban gidan da Kamfani ya bashi.

Batasan hawa ba batasan sauka ba,sai siyayya da taga suna ta fita ita dashi. Ko sau daya bata nuna tasan abinda yake gudana ba,idan ma fauziyyan tayi ne saboda ta quntata mata ko ta bata haushi, saidai qasan ranta bacin rai ne danqar irin wanda fauziyya ke burin ganin ta cusa mata,ko a fuska a lokacin wani irin ramewa majin tayi,saboda dukka wani kwanciyar hankali da • nutsuwar gidan miji ta rasata, dukkan hankalin mahmud ya karkata ga buqatunta da faranta mata,kai idan kaga yadda abun yake zaka dauka kishiya ce fauziyya a wajenta,kishiyar ma irin wadda tayi dukkan me yiwuwa wajen raba tsakanin miji da abokiyar zamanta.

Da wani dare mahmud ya aika toufeeq ya kirayi shifa din, a lokacin tana zaune saman abun sallah,don yanzu babu abinda yake bata nutsuwar ruhi da sanyin zuciya sai sallah da azkar. Ta iso ta riskesu a falo sunata sabgoginsu,fauziyyan ta wani murje a lokacin saboda tarin supplement da take dirkawa kanta na qarin qiba da kuma qara haske,wanda har sun wuce qa'ida,hips da boobs dukka sun fito sosai.

Guri ta samu ta zauna a nutse tace

"Gani" dubanta mahmud yayi,a idanunsa yaga ramewa da kuma canzawar da tayi, qasan zuciyarsa yana jin wani iri babu dadi, saidai baki ya gaza furta komai, hakanan wani abu yana tasowa yana danne dan qaramin tausayin da yakejin yana masa tasiri.

"Nidai bansan me yake damunki ba, gaba daya kin tsangwami kanki?,lokacin da ya kamata ki tsaya mu fuskanci rayuwa, Allah amshi addu'ar da kiketa yi mana" wani kallo tayi masa sai ta kauda kanta,batason tace komai saboda bata son fauziyya ko kadan taga alamun karaya a tattare da ita,ta tabbatar abinda taketa son gani kenan,saboda yadda ta matsa qaimi kawai ya isa bayar da amsa ga maji

"Nan da kwanaki uku zamu koma sabon gida,a baya na miki alqawarin sabbin kayan furniture da komai da komai,to yanzu yanayi ya sanya ba zasu samu ba,saboda nauyi da ya gara yimin yawa,an siya bawai ba'a siya ba, amma kayan furniture za'a sakawa fauziyya tunda itace garama, kuma ba mai zama bace, idan ta samu miji aurar da ita zanyi,kayan kitchen kuma na ajjiye mata su kada auren ya taso bani da komai a lokacin, idan Allah ya hore miki nan gaba sai a canza miki wasu,zan saka azo a kwashe wadan nan ayi musu gyara" qas tayi da kanta,har cikin zuciyarta takejin wani irin bacin rai,bawai na furniture din da yace za'a yiwa kwaskwarima ba,a'ah…...na yadda kullum kwanan duniya yake qara qasqantar da martabarta a idanun fauziyya yake kuma sake wulagantata. Ta tabbatar idanun fauziyya a kanta suke taga action dinta,don haka ta daga fuskarta da murmushi

"Banda abinka ai basai ka tsaya yimin bayani ba, Allah ya hore ya bada yadda za'a yi‚ba komai" har ransa yaji dadi duk da cikin jikinsa yakejin bai kyauta ba, sai ya jawo wata leda

"Gashi ganwarki tace ki fara dauka"

"A'ah ta dauka ba wani abu;idan ta gama zaba moha ya kawomin" ta fada tana miqewa

"Laaa maji ai ba wani abun bane,komai iri daya aka siyo, bambancin kala ne kawai" fauziyya ta fadi,wadda bata son maiin ta wuce ba tare data sake ganin wannan ba. Sabbin atamfofi ya siya musu masu tsada da zasu dinka na tarewa a sabon gida,waiwayawa maji tayi ta kalleta

"Bani da zabin kala fauziyya,ko kin manta likkafani da kala qwaya daya yazo?, kuma shine tufafinki kuma tufafina na qarshe?" Turus tayi tana bin maji da kallo,tasan cewa magana ce ta gaya mata a fakaice,sai bata sake cewa komai ba har ta wuce zuwa dakinta.

Saman abun sallarta ta koma ta zauna tana nazarin abun zuciyarta na soyewa,ta gaji da zubda hawayenta,zuwa yanzu zuciyarta ta fara soyewa,sai taci gaba da ambaton sunan Allah sannu a hankali har ta samu sassauci.

Cikin wannan yanayin suka koma sabon
gidan,wanda duk yaga dakin fauziyyan zai dauka shine dakin maji,ya zuba mata komai sabo,hakanan kayan yara ma suna gurinta da komai nasu

"'Itace uwarsu ai ita zata kula dasu" abinda Mahmud ya fada kenan. Maji ta jishi kawai, amma ta barwa ranta koda zata sallamawa fauziyya komai banda yaranta da ita daya ta raini cikinsu ta kuma haife abinta. Tsayayyar macace da ita kanta fauziyyan tasan cewa nasararta dukka akan yayanta take,amma majin ta shallake hankalinta,duk yadda taso a maida mata maji kamar mahmud don taci duniyarta da tsinke ta gaza samun hakan. Hakanan yaran, kusan tunda suka koma gidan majin ta sake janye yaranta jikinta da kyau,ta kuma sakasu cikin dukkan wasu addu'o'i na tsari na sha da shafawa.

Kwatsam Allah ya fiddawa fauziyya miji,a ranar har kukan farinciki maji tayi cikin daki, saboda tana ganin Allah ya kawo mata qarshen baqinciki da damuwarta. Da farko fauziyya taso taqi auren YA'AQOUB AJI, saboda yana da mata,sannan arziqinsa baikai yadda ta tsarawa mijin da takeson aura b,amma daga bisani yaci galaba a kanta bayan itama yaci galabar fidda matarsa daga gidan tun kafin takai ga shiga gidan.

Mahaukatan kudi mahmud ya kashe wa auren fauziyya,duk abinda ta nuna tace tana so shi zai saya mata,a lokacin hatta hidimar yara data gida data makarantarsu sai data tabu,ya tsaida wasu abubuwan da yawa saboda ya cika muradin fauziyya yayi mata aure kece raini. Sam maji bata damu ba,saboda tasan aski ya riga yazo gaban goshi,akayi biki aka tattarata aka migata gidanta.

A washegari sai da maji tayi azumin godiya ga
Allah,a ranar gidanta ya fara zamar mata gidanta,hatta da iskar gidan sai da ta jita daban da wadda ta saba shaqa. Cikin lokaci kadan abubuwa suka fara komawa saiti,saidai hausawa sukance ba'a taba bari a kwashe duka,haka yake,don duk da da tayi nasarar daidaita al'amura masu tarin yawa,amma har yanzu fauziyya na baki da zuciyar mahmud,a qalla a rana sai yayi zancanta ya kusa sau goma,kira kuwa sai da maji ta gaji tayi masa magana

"Kai yayanta ne kuma namiji, bai kamata ace kana vawan kiranta haka ba saboda tsira da mutuncinka, ina laifi a rana sau daya?" Shine aka samu sassauci ta fannin kira, amma banda haka babu abinda ya canza zani.


* BAYAN SHEKARA BIYU_*

Ana murna bago ya tafi ashe bago yana bayan gari,shekarar fauziyya biyu da aurenta da diyarta daya
HASEENA MEENAL arziqin Mahmud ya fara dawowa yadda ya kamata. A take shaidan yayi mata kururuwa,taji sam zaman gidan YA'AQOUB bai dace da ita ba, hakan kamar ta tauyi rayuwarta ne,ta kuma barwa wata dan uwanta tana cin arziqin da daga ita har mahaifiyarta basu cishi ba,duk da babu abinda Mahmud ya rageta. dashi,komai ya samu tana ciki kuma taba da kaso a ciki.

Dare daya ta shiga ta fita da yawan gidan malamanta ta tilastawa ya'aqoub ya rubuta mata takardar saki uku a jare,don bata tunanin har abada zata dawo,don yanzu ba wannan ravuwar bane a gabanta. Manya manyan zawaran dake tashe a media ake damawa dasu ta fannin kasuwanci su suke rudarta, rayuwar 'yanci da business,fita qasashen qetare a duk sanda suka so,gidan kansu da manyan motocin hawa da sutturu na alfarma vanzu sune babban burinta, sai kuma diyarta meenal wadda Allah ya jarabta da mugun sonta,irin soyayyar da bata taba yiwa wata halitta irinta ba.
Tanason ta tara mata dukiyar da ba zata taba sanin meye talauci ba har garshen tata rayuwar.

Ranar data isa gidan Mahmud da takardar shaidar saki a ranar baiwar Allah shifa na cikin farinciki,karon farko tun bayan karayar arziqinsa ya sake siyan mota,a lokacin yace ta dinga hawa tana hidimar gida,kai yara makaranta da daukosu,da sauran abinda ba'a rasa ba,idan ta kama kuma shima zai karba ya hau ya fita sabgoginsa,kafin ya samu damar siya mata tata.
Sallamar fauziyya kadai a gidan janye da meenal da faggon kaya ya sanya maji cikin matsanancin faduwar gaba,tana fadin cewa sakinta yayi maji ta samu ta daddafa kuiera ta zauna a kai cikin zucivarta tana ian

"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" yadda takeji cikin ranta da jikinta a sannan tamkar ita aka saka ba fauziyya ba.

Zaman dai bai sauya zani ba,saima canza salo da fauziyyan tayi, cikin salon wata hikima da iya taku take tatsar kudi daga hannun Mahmud, adadin kudin da ko ita maji wadda ita tasha wahalar kusan komai kawo yanzu bata samesu ba daga jikinsa. Tunda majin ta qyalla idanu ta fuskanci mugun shiru fauziyya ta yi, wanda ya ninka na baya,saboda ayanzun ta samu makiran qawaye gwanaye iya bin malaman tsubbu, sai ta hana kanta sakat da addu'a ba dare ba rana,wanann ya sakawa majin qarfin zuciya da ruhi,duk wani kalar iskanci da fauziyya tayi mata awancan zaman wanna karon ko daya bata dauka ba,wanann ya kawo gagarumin sabani tsakaninta da mahmud, saboda muddin kanason kaga tashin hankalinsa ka taba fauziyya da 'yar lelenta meenal.
Yarinyar Allah ya zuba mata rashin ji na tsiya,zuwansu ba dadewa amma ta fashe duk wani kayan ado da alatu na falon gidan.

Lokaci galilan kuma ta fiddo dabi' ar tara mata qawaye a gidan,sabbin qawaye irinta,wadanda suka bawa duniya amana da dukkan qauna,suka kuma riqeta da kyau,wasu 'yammata ne wasu kuma zawarawa ne kamarta,cikinsu kuma akwai MANSURA wadda tafi kowa zagewa tare da rawar kai.

Da farko falonta ake zuwa a baje,fauziyya ta shiga kitchen cikin taqamarta da jin izza harda yin gayyata ta bare duk abinda takeso tayi musu abincin wadata da alfarma,su bata ko ina a kuma fice abata guri a barta da aiki. Idanunta maji ta rufe, cikin tsayayyar nan tata da dakewa randa suka cika sati guda suna mata tayi musu tasss daga fauziyyan har qawayen,kai fauziyya ta jinjina

"Zakiyi nadama" kamar yadda ta furta kuwa daren ranar majin bata samu cikakken bacci ba,saboda mugun tashin hankalin data haddasa tsakaninta da mahmud,ya gaggaya mata maganganu masu zafi da gori wanda tunda sukayi aure bai taba gaya mata irinsu ba. Ta kwana tana kuka tana kuma gayawa Allah,da safe kuma tayi qoqarin ta tashi kamar komai bai faru ba, abu daya ta sani, ko zasu dawwama suna rikici da Mahmud, ba zata. dauki wasu bagin halayen cin fuska na fauziyya ba,ba ita kadai bama,ace har gawayenta suna da power din shiga mata kitchen suyi yadda sukeso?, bazai yiwu ba, inda ita daya ce zata iya kau da kai, saboda kau da kai da haquri ta sani su kadai ne suka kawota warhaka gidan.

Ba'a jima da gama wannan ba tana zaune da wani yammaci tana gyarawa su toufeeq farce fauziyya ta shigo,tanata baza qamshi hade da taunar chewing gum, tunda taji hayaniyar tarkacen qawayenta na banza marasa da'a ta hada kan yaranta cikin falonta suka zauna a nan

"Key zaki bani" a nutse ta daga kai ta kalleta

"Key na me fa?"

"Na motar yaya na,zan fita unguwa,wani ma yayi rawa bare dan makadi, a bani na mori arziqin dan uwana ko kuma rai ya baci" bacin rai ne ya tasowa maji,yadda take mata magana a tsaitsaye saman kanta,sai ya maida dubanta ga aikin da takeyi

"Bazan bayar ba,rai kuma ya dade bai baci ba,idan kuma kina da qarfin qwata saiki danne ni ki karba"
"Abu me sauqi, kamar qofar dakin naki baqona ne" ta furta tana takawa zuwa hanyar bedroom dinta. Tsam maji ta mige ta kuma daka mata tsawa

"Ke fauziyya!, dakata,kikayi kuskuren shigamin daki wallahi saikin gane sakarya ce ke,ina da kaidi da kuma tuggun da yafi naki ninkin baninkin,saidai kawai banbanci na dake ni din ba jahila bace,nasan sakamakon dake iya biyo bayan aiwatar da sharri tuggu da kuma makirci" tsaiwa tai tana duban idanun maji,ta rasa meye a tattare da matar da har yanzu ta kasa juyuwa a gareta kamar yadda take juya yayanta? ita kadai ce yanzu matsalarta
*HUGUMA*


*_TABARMAR KASHI *

Book 02 Page 43

"Zaki bayar ko sai nasa an karbarmin?" Murmushin takaici maii ta sauke

"Har abada ba zaki taba cin galaba a kaina ba fauziyya,yadda baki taba karbar abu a hannuna gaba gadi ba saidai kisa a karbarmiki, har abada a haka zaki qare, ni maji bazan taba sallamamiki komai nawa hannu da hannu ba,saidai kisa na gaba dake din ya karbar miki,zoki wuce ki fitamin a daki" maji ta fada cikin zafinta,abubuwan da fauziyya ke mata tana kau da kai tana tarasu cikin haquri irin nata yau suna taso mata. Ganin ta tsaya zata bata mata lokaci sai kawai tasa hannu ta fincikota baya ta watsata waje ta maida gofar falonta ta rufe.

A sanyaye ta koma gasan carfet ta
zauna,gabanta na tsananta faduwa,batayi dana sanin abinda ta yiwa fauziyya ba,amma yau tabbas ba shakka tasan abinda zai biyo baya a gidan bame dadi bane, wannan ya sanya ta tattara ta gama yanke musu farcen da wuri,ta hadasu sukayi sallar magariba duk da nadeeya dama shi kansa toufeeq din basukai wannan munzalin ba amma ta soma horas da su,saboda haka kawai cikin jikinta takejin ba zatayi dogon zama dasu ba,ta basu abincin dare sukaci ta kaisu dakinsu ta kunna musu cartoon a tv din dake dakinsu tace idan sun gama kalla suyi bacci,sannan ta dawo ta zauna a falo.

Ko minti talatin ba'a cika ba taji shigowarsa gidan,ta runtse idanunta saboda yadda gabanta ke duka tana kiran sunayen Allah tare da jan addu'o'in

"Allahummakhfinihim bima shi' ita,inna kafainakal mustahzi'een,ya rabbi innalqaumas tad'afuni, wa khadu yaqtulunany fala tushmit biyal'a'ada'a wala taj'alni ma'al gaumizzalimin" a hankali ta dinga maimaitasu qasan ranta idanunta a runtse har zuwa sanda taji ya bankado gofar.

Tana bude idanunta ya fada cikin nasa,a hankali yaji wani abu ya dakeshi, kaifin bala'i da masifar da yakeji suna tafasa cikin ransa sai yaji suna raguwa. Ci gaba tayi da kafeshi da idanu,yayin da fauziyya da idanunta sukayi luhu luhu na kuka wadda ke tsaye a bayansa tace

"Muje yaya" ganin ya tsaya bai shiga ba bai fita ba.

"Sannu da zuwa" maji ta furta a sanyaye, baice mata komai ba sai hannu da ya miqa mata

"Bani key din motata" idanu suka hada da fauziyya,saita saki murmushi,batace komai ba ta miqe tsam,ta shiga dakinta ta fito dashi ta miqa masa. Juyawa yayi ya miqawa fauziyya

"Ki riqe a hannunki ki dinga hawa,duk lokacin da ni nake da buqata na dinga amsa daga hannun naki,jeki" sanyaya gwiwar fauziyya din tayi, ba haka taso ba,so tayi yayi mata irin cin mutuncin da ya saba yi mata a gabanta,ya wulaqantata ya fifita darajarta akan tata. Juya key din tayi a hannunta sannan ta juya ta fice shi kuma yazo zai wuce cikin dakin nasa ba tare da ya sake bi takan maji ba.

Kasa motsawa tayi tana zaune a gurin har ya gama abinda zaiyi ya fito,ya buqaci abinci ta zuba masa,yayi kiran shalelen tasa tazo suci abinci yadda suka saba tace ai ta fita dana mota. Maji na zaune tana nazarin rayuwa,me gobensu zata haifar ita da mahmud da irin wannan makauniyar rayuwar dake wakana a tsakaninsu. A daren bayan sun gama shirin kwanciya ta sameshi cikin kwantar da kai take tambayarsa abinda vake damunsa tare da shawarar yayi gogari ya daidata gidansa

"'Ni ba abinda yake damuna, hankalina yana tashi idan fauziyya bata cikin walwala, raina yan baci idan nata ran ya baci saboda ba abinda nake tunawa sai amanarta da mahaifiyata ta barmin" yadda yake maganar kadai ya sake tabbatarwa da maji lallai abub yayi girma ya wuce duk inda ake zato,daga wannan lokacin ta sanya idanu kan fauziyya fiye da baya,babu jimawa kuma ta fahimci irin aikin asirin da takeyi akan yayan nata kuma miji ga maji din.

Randa ta karanci hakan ta samu fauziyyan na zuba wasu abubuwa cikin abincin Mahmud din maji tayi ram da hannunta tana kallonta

"Kin ganowa kanki ranar barinki gidan nan sakarmin hannuna" ta fada kanta tsaye bacin rai ya hana maji magana, wacce iriyar baqar masifa ce haka?,duka duka shekarunsu dava da fauziyya har yanzu babu wanda ya rufa shekara arba'in, gaba daya ba zasu wuce talatin da bivar ba amma ta zama wata bagar masifa?.

"Kinyi asara wallahi,sannan bana danasanin barina gidan nan saboda nayi imani duk sanda hakan ta faru cikin qaddarata yake,ke baki isa ki zanamin gaddarata ba".

Tun daga wannan ranar fauziyyan ta dauki damara,saboda ta sani maji din nada wani irin kariva da take hana asiri cimmata nan da nan, kuma tasan hakan baya rasa nasaba da yawan addu'a da azumin nafila da bata rabo dashi.

* MAMAYA *

Tun daga wancan lokacin da ta kama fauziyyan take kaf kaf da abincinsu su duka cikin gidan, don tayi imani ba abinda fauziyyan ba zata iya aikatawa ba.
Ranar da ta zama baqar rana a gareta, ranar data shiga tarihin rayuwarta,ranar da ba zata taba mancewa da ita ba,ranar kuma data zama mafarin zanen dukkan qaddarorin da suka wanzu a rayuwarta dana iyalinta.

A wani yammaci liqis wanda kadan ya rage magariba ta kunno kai,ta gama abincin dare cikin galabaita saboda yadda qamshin girkin yake damunta yana hautsina mata kayan ciki, yanayi ne dakan faru da ita a duk lokacin da take da qaramin ciki,ko a yanxun tana tsammanin cikinne saidai haka kawai ta kasa gwadawa bare ta tabbatar, saboda yanayin da take ciki wanda zaiyi wuya ta samu nutsuwa ta kwana uku cikin gidan fauziyya bata sakata a masifa ba,abinda yake dakushe kaifin abun wanda a yanzu sukanyi sati daya har zuwa biyu lafiya lafiya shine addu'ar data tashi tsaye tana yi, ba dare ba rana. Tana kammala abincin ta fita a kitchen din tana fatan samun wata iskar da babu qamshin abincin a ciki kota samu ta dawo dai dai,ta kama hannun nadeeya ta saka toufeeq a gaba suka wuce, zuciyarta na tuna mata da kalaman da fauziyya ta gaya mata kwanaki uku da suka wuce,wadanda suka sanya maji din dauketa da mari, abinda bata taba yi mata ba kenan.

"Badai yara ba? sai na rabaki dasu rabuwa ta har abada,saina tabbatar miki da cewa ni fauziyya ni kika haifawa su". Ta jira abinda zai biyo baya akan marin da tayi mata amma har yanzu bataga alaman Mahmud ma yasan da abun ba,hakan bawai ya bata kwanciyar hankali bane, a'ah, ta sani tabbas akwai abinda zai biyo baya.

"Abba ya dawo maji,muna masa sannu da zuwa bai amsa ba" toufeeq ya fadi mata,saita kalleshi da mamaki,don bataji shigowarta ba bai kuma nemeta ba,qilan yau an birkitashi ne kamar yadda ake masa duk sanda akaga dama. Batabi takan zancan toufeeq ba,sai ta zauna tana jira ta koma dai dai sannan ta iskeshi.

Motsin da ta danji a kitchen ya sanyata yunqurawa babu shiri saboda tunawa da tayi ta baro abincinsu ta cewa da toufeeq "Ina zuwa ku zauna". Tun kafin ta garasa ta hangi fauziyya a ciki gabanta ya fadi ta kirayi sunan Allah tana qarasawa da gaggawa. Shigarta yayi dai dai da ware wani abu baqi cikin kwalba da fauziyya tayi tana shirin antayawa a cooler din abincin Mahmud. Caraf tayi da hannun fauziyya tana kallonta

"Me kike shirin aikatawa maqiyar Allah da manzansa" maimakon ta amsa mata yadda suka saba sai kawai taga ta saki kwalbar,maji tadan ja baya tana duban kwalbar data fadi qasa ta fashe,wani irin wari wari yana fita daga ciki, shi ba warin fiya fiya ba shi ba na maganin bera ba, kafin ta gama wannan nazarin fauziyyan ta zame hannunta ta kama hannun majin ta rige tsam kamar me shirin hanata tabawa,sai kuma taji ta kwazara ihu tana kiran sunansa

"Yaaya!, innalillahi wa inna ilaihi raji'un yaaya kazo ka gani* tunanin maji ne ya juye, ta kasa fahimtar abinda fauziyyan ke shirin alkatawa. Cikin qasa da second talatin ya iso qofar kitchen din, hannunsa riqe da wasu takardu,wani irin lafiyayyen fushi na kwance kan fuskarsa

"Yaaya,kaga abinda na kamata tana shirin zuba maka,yaaya dama kasheka takeson yi,bata qaunarka" fauziyya dake wani irin rawar jiki ta fada hawaye na wanke mata fuska.

Wani tashin hankali ne

Please Login or Register in order to submit comment