Reading TABARMAR KASHI 1&2 complete by SAFIYYA HUGUMA Chapter 19 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Ta fahimci Aafiya takai qololuwar fushi,kuma bata da sauran zabi illa ta gaya mata abinda take da buqatar ji din

"Zauna sai muyi magana a nutse"

"Bazan zauna ba har saikin gayan komai,yaushe kika fara wannan allurar,keda ko bari baki taba yiba tsahon shekara biyu da aurenki,muna nan munata addu'ar ganin qwanki a duniya?"

"Satin farko na aurena" sosai maganar ta daki Aafiya,har sai data dan ja baya kadan,to amma tana buqatar samun cikakken qarin bayani daga bakin saahar din don ta samu makama

"Satin farko kuma?,shi adam din ya sani ko munafuntarsa kike?" Gyara zama tayi tana jin tambayoyin Aafiya sunkai mata ko ina,ta gaji da jera mata tambayoyin da taketa faman yi

"Kin fiya takura da zaqule zaqule,xama mukayi mukayi shawara muka yanke hakan ni dashi,duka duka saura watanni kadan watannin da muka diba su cika na dainayin allurar gaba daya,so please don Allah banason kowa yaji zancan nan,tunda dai mun kusa kammalawa".

Tashin hankali sosai ya shigi Aafiya,ita da tayi karatun lafiya tasan illar da hakan zai iya haifarwa da saahar,ta sani.....saahar ta saya ne kawai,ba zancan tare da adam sukayi shawarar aikata hakan,tunda duk mahaluqin daya kwana ya tashi yasan saahar din mada mugun son yara kamar me,tana iya yin komai saboda yara,tana kuma iya barin komai saboda yara,naturally ma akan ce dukka wani ko wata auta suna da son yara,to na saahar har ya wuce misali,abun kamar cikin jininta ne,ada maama ta dauka iya na quruciya ne,saidai har girmanta har zuwa aurenta abun yana nan tare da ita,to ta yaya koda dukka jikinta kunne ne zata amince saahar zatayi planning bisa radin kanta?.

To amma koma meye a yanzun tashin hankali ba nata bane,idan illa take gudarwa saahar kome meye zuwa yanzu allurar ta dade dayi mata,fada tashin hankali da masifa ta tabbatar ba zasuyi tasirin komai ba,ta sauke ajiyar zuciya bayan dabara ta fado mata,ta dawo a hankali jiki a sanyaye ta zauna daga gefan saahar,ta kamo dukka hannuwanta ta sanya a nata

"Idan wani ya fahimceku bestie wani bazai fahimceku ba,idan wani bai zagi adam ba wani zai zageshi,don me kina da buqatar irin wannan allurar kinsan zan iya yi miki amma baki nemana nayi miki asirinku a rufe basai sun fallasa sirrinku ba?" Sosai maganar ta bawa saahar mamaki a yadda tasan hali da dabi'ar Aafiyan tata,ta kafeta da idanu,wani sashe na zuciyarta ta gaza gasgata zancan afiyan,wani bangaren kuma na gasgatata,tunda ita din kaifi daya ce,bata qarya don a sota,hakanan duk yadda magana takai ga rashin yi maka dadi zata gayamaka ita muddin dai gaskiya ce.

Hannuwanta ta kamo cikin son gamsar da saahar din tayi yadda takeso

"Wannan din sirrinku ne,kuma sai amintaccenku ya kamata ya sani,tashi nayi miki" ta qarashe maganar tana sakin hannayen saahar din,ta soma zuqe ruwan allurar cikin syringe tana mita

"Shekara biyu amma bestie ace kina da wani sirri da kike boyemin,duk yadda muke dake,na sake yarda adam ya shiga tsakaninmu" sai zuwa sannan tadan saki murmushi,idan da sabo ta saba jin wannan tababar da suke akan juna,aafiya na qorafi akan adam koda yaushe,kamar yadda adam ke qorafi akan aafiya,batasan yadda zata hada kawunansu su fuskanci juna ba.

"Next month idan kin tashi zuwa ki sameni a asibiti,don banason maama ta gani ta tambayi ba'asin yin allurar"

"Wai meye ya sanyaki saukowa haka da wuri bestie?" Saahar ta jefawa aafiya tambayar da tun dazun take cin zuciyarta,ta kuma shiga cikin kokwanto

"Saboda inason abinda bestie na takeso,kinason adam,kinason duk abinda yakeso,ni kuma inason bestie na,kuma dole na tayata son duk abinda takeso muddin da gasken ina sonta"ta amsa mata kai tsaye idanunta cikin qwayar idanun saahar.

Janye idanunta tayi daga na Aafiyan tana son gamsar da kanta da gasken aafiya take,don ita din kaifi daya ce,dadi ko wuya basa sakata canza ra'ayinta.

Tana jin kamar kada ta tafi tabar gidan saboda tsananin sabo da kuma soyayyar dake tsakaninta da familyn ta,amma dole qarfe uku da rabi ta yiwa maama sallama

"Da wuri haka bestie?" Aafiya ta tambayeta sanda ta isketa tsaye a falo bayan shigarta kitchen kenan ta hada musu banana smoothie

"Munyi da adam zai sameni gidan momee da yammar nan,daga can saimu wuce gida" tabe baki Aafiyan tayi

"Ya kamata,muje na taka miki"

"To bani smoothie din na shanye mana kafin na tafi,kinsan akwai amana tsakanina dashi"

"Na zaci ai sauri bazai barki kisha ba" qaramin murmushi kawai saahar din ta saki,batasan me yasa duk Wani abu daya shafi adam ba aafiya bata maraba dashi,zuwanta daya tsahon shekara biyun nan gidansu adam din,ta kuma yimata rakiya da qyar,bayan sun fito kuma tayi shuru cikin mota kamar wadda ruwa ya shanye

"Yadai bestie?"

"Mamar adam din nan sam bata yimin ba,wai yaushe ta fara sonki ne bestie?" Aafiyan ta jefawa saahar dake driving tambaya.

Dan qaramin bakinta ta bude cikin alamun mamaki sannan ta bushe da dariya,ta san halin Aafiya ba kowanne mutum bane yake mata a karon farko

"Ni banga aibun momee ba,bata da matsala,tana daukata kamar wata qawarta,bata taba takuramin ba,hasalima bata iya boyen duk wata damuwarta,so kuma ni dama bata taba nunamin qiyayya ba"

"K'nnnnn,haka ne" Aafiya ta fada a taqaice tana jawo wasu takardu dake ajjiye gaban motar sahar din ta tara dubawa,shuru ya ratsa motar kafin ta sake dago kai

"Waye zai bude joint account kuma?"

"Adam ne ya karbosu,bai gayan na waye ba yace na ajjiye masa kawai" saita gyada kai ta maida takardun da ba'a kai ga cikewa ba inda ta daukosu,ta gyara zamanta tana dauko wata hirar daban.

Har bakin mota Aafiya ta rakota,saahar tanata mita

"Wallahi wallahi kin bani mamaki,ban taba zaton aure zai nesantamu ba,tsahon shekara biyu cur amma zan iya irga zuwanki gidana da yatsun hannuna?,wanne laifi mukayi miki?,tun adam na min qorafi har ya koma gorantamin kan cewa baki damu dani ba,ni daya na damu dake,ko yaa zain da yake namiji ya fiki zuwa gida na fa" qaramin murmushi Aafiya ta sake

"Ke kuma sai kika yarda da zancan adam?,ki rabu dashi so yake ya hadamu,aiki bestie kema kin sani,amma na miki alqawarin zuwa in sha Allah ending next month" hannu kawai saahar ta sanya tana rufe qofar motarta

"Kice kawai baki shirya zuwa ba,basai kin fitomin ta haka ba"

"Seriouse,Allah da gaske nake miki" ta fada tana dariya bayan taja ta bata hanya,tana nan tsaye har saahar dake galla mata harara ta mirror din motar ta fice daga gidan,Aafiya ta saki ajiyar zuciya sannan ta juya a hankali tana komawa cikin gidan.

Minti ashirin kacal suka kaita unguwar sharada. Saboda ta danyi gudu ba laifi,bataso taje ta samu adam ya isa yana jiranta.

A farfajiyar gidan ta tsaida motarta ta kasheta ta fito,ta fara takawa cikin nutsuwa da takuntan nan zuwa cikin gidan tana gyara laffayarta.

Gab da zata qarasa qofar da zata sadata da ainihin falon gidan mata biyu suka fito,daya a gaba daya a baya,sai tadanja da baya ta tsaya don basu damar wucewa.


FURAR DANKO
Billyn Abdul

-ZAFIN KAI
Mamuhgee

-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma

-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo

Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400

Pay at👇

1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim
Sai katura shedar biyanka anan👇

09032345899

Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇
09033181070

VIP🔥💯
Zafin kai 3k
Furar danko 3k
Tabarmar kashi 3k
Bakon munafuki 3k

*Al'ummar NIJER ku kira wannan number don yin naku pyment din*

+22799643131

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*

*THANKS FOR CHOOSING US*🥰

Zafafa🫶🔥


: *H U G U M A*

*_TABARMAR ƘASHI_*💔
https://arewabooks.com/u/huguma

Page 37

Ta farkon macace da aqalla ta doshi shekara hamsin da biyar,saidai a ido ba zakace haka ba,saboda yanayin yadda take,kallo daya zakayi mata ka fuskanci gogaggiyar macace wadda tasan kan rayuwa sosai,idanunta fes suke,akwai wayewa mai tsanani a tattare da ita,gajeriya ce mai gogaggiyar baqar fata,tana da manyan idanuwa da dogon hanci,wannan ya qawata mata fuska sosai,ta bayan nata kuwa doguwa ce,wannan itace momee din adam,wadda suke kama sosai ta fuska.

"Kina hanya ashe?,har na fidda rai?" Ta fada cikin madaukakiyar fara'a,cikin kunya da kara irin wadda kowacce diya keji ga surukarta saahar tadan duqar dakai

"Ina hanya momee.....barka da yamma,ina wuni?" Ta gaida baquwar dake tare da momee din wadda ta kafeta da idanu cikin wani irin kallo na qurilla,har saahar din na jinsa har cikin jininta.

Da sauri ta murmusa cikin nuna kulawa

"Lafiya lou,kina lafiya?" Ta amsa da hausarta data dan baci kadan,da alama su momee din sun fita qwarewa nesa ba kusa ba

"Lafiya lau alhmdlh"

"Ki shiga ciki bari na rakata na dawo" momee ta fada suna juyawa da baquwar

"Ina mamakin yadda adam ya samu kyakkyawar yarinya haka,kyanta na bani tsoro k......" Saahar ta jiyo muryar baquwar,wadda bata qarasa jin abinda take fadi din ba,katsewa tayi ko nisan data fara yi mata ne bata sani ba,ta sanya kai cikin parlor din momee din,wanda a yanzun ya zama abun sha'awa cike da kayan alatu.

'yar budurwar da ake kira da raihanatu ta amsa sallamar saahar din cikin mayalwacin murmushi da kuma tarin kirki da girmamawar da takewa saahar,ta qaraso da sauri tana karbar ledar hannunta hannu bibbiyu har kamar zata kai qasa tana cewa

"Sannu da zuwa anty" cikin fara'a Sahar din itama ta maida mata

"Sannu raiha sarkin aiki,ya gida ya aiki?"

"Alhamdulillah anty,bari na kawo miki ruwa" ta yiwa ledar guri a wajen,ta juya da sauri ta doshi kitchen dinsu dake manne da parlor din,saahar ta bita da kallo.

Yarinyar diya ce ga qanwar momee,momee din ta dauko riqonta,itake mata komai,kamar yadda yarinyar itama itace komai na gidan,yarinyar nada wani irin hankali kirki da kuma nutsuwa,bata da surutu sam,hakanan bata da shiga shirgin da ba nata ba.

Cikin mintin da bai gaza daya ba raiha ta gabatar ma da saahar drinks masu sanyi hade da ruwa,tana murmushi tace

"Mun cinye abincin rana anty,bamu gama kuma na dare ba kiyi haquri" murmushi ya subuce mata

"Ni ba baquwa bace raihana,kada ki damu" ta girgiza kai tana murmushi itama,har cikin zuciyarta tana jin qaunar anty saahar din,saboda sauqin kai kirkinta kyauta da kuma kyautatawarta,matsayinta dana mahaifinta,kyawunta ko iliminta sam bai sanya mata girman kai ba ko jin ita din wata bace,uwa uba kuma yadda ta dauki momee din a matsayinta na surukarta.

Bata taba komai a ciki ba,don ta fito gida a qoshe,har zuwa sanda momee ta dawo parlon ta zauna tana cewa

"Sannu da zuwa,har na cire rai ai" a kunyace saahar ta saki murmushi,tadan sunkui da kai tana murza zoben hannunta

"Ina sane momee,ga saqon nan" sosai ta washe baki cikin fara'a,ta miqe tsam ta dauko ledar da kanta tana budawa.

Manyan kaji ne broilers da suka qanqare saboda dadewa cikin freezer,cikin ma'aikata gidansu ta sanya wata cikinsu ta ciro mata

"Allah dai yayi miki albarka,ai baqi nayi,duka naman gidan ya qare,gashi ni kuma banason girki babu nama ko kadan" saita qwalawa raiha kira,cikin minti daya ta iso gurin,harara ta jefa mata

"Kina abu kamar kazar da qwai ya fashewa a ciki,dauki wannan naman,ki cire wani daga ciki kiyimin farfesu"

"Tom momee" ta amsa a ladance,ta sukunya ta dauki ledar ta wuce kitchen din.

Kamar ko yaushe hira sosai momee ke janta da ita,harda abinda saahar ke ganin bai shafeta ba,to amma tana baiwa momee din uzurin banbacin al'ada da yare dake tsakaninsu,sannan kuma irin wayewarta daban da wayewar sauran surukai data sani.

Mafi yawa saidai ta amsa da eh ko a'ah,ko kuma tayi murmushi wani lokacin,tun tana zuba idon ganin adam har aka kirayi sallar magariba,a sannan raiha tayi mata jagora zuwa dakinta,duk da momee din tayi mata tayin shiga nata dakin tayi sallar amma sai tace a'ah,don ba zata iya sakewa ba.

Sai a sannan ta samu sukunin kiran adam din,amma harta qaraci ringing dinta bai daga ba,ta haqura ta ajjiye wayar zuciyarta na gaya mata yana sallah ne hala.

Tana idarwa ta sake gwada kirannasa,cikin sa'a ta shiga,ta bada dukkan hankalinta ga wayar tana jira ya daga.

Dab da zata tsinke ya daga din,muryarsa can qasa yayi sallama,ta amsa masa cikin kulawa

"Nayita jiranka dear.....kuma baka shigo ba" dan gyaran murya yayi kadan

"Ban samu na fita din bama,throughout yau ina gida" hankalinta ya sake kaiwa ga muryarsa

"Lafiya kake?"

"Me kika gani?"

"Muryanka was so cool.....kaman jikinka ba qwari"

"Yeah.....bacci nayi ban tashi ba har yamma,shi ya kashemin jiki"

"Alright,na taho kenan?"

"No,ai nayi alqawari,zan shigo saimu dawo tare"

"Okay"

"I missed you" ya fada cikin tsananin kulawa, murmushi ya subuce mata

"I missed you too,saika qaraso" daga haka sukayi sallama ta ajjiye wayar taci gaba da lazuminta,lokaci lokaci tunani yana waftar hankalinta ya kaishi ga wani abu na daban,bata bar dakin ba har sai datayi sallar isha'i.

A falo ta samu momee,ta baje dabgen kajin tana kaiwa ciki,tayi d'ai d'ai saman kujera kamar ita daya ta rage a duniyar.

Raihana ta qwala kira har kusan sau uku a jere

"Maza hadawa diyata abinci taci" ta amsa a aladabce,ba jima ta dawo da babban tray ta ajjiye gabanta

"Zauna mana muci" saahar ta yiwa yarinyar tayi,saita girgiza kai,tamkar taga hararar da momee din ke watsa mata ta gefan ido

"Zanci nawa yanzu anty,wannan naki ne".

Batayi nisa dacin abincin ba ta qoshi,dama ita tun tale tale bata cikin sahun mutanen da abinci ya dama,tana rufe warmers din adam na shigowa.

Hannayensa zube a aljihun wandonsa,cikin wasu shirt da trouser yake sanye,shi din gwanin wanka ne,akwai iya daukan ado me jan hankali,idanunsa a kanta,haka yake mata irin wannan kallon ko gaban waye.

Kallo daya tayi masa ta dauke kanta daga sashensa,yayi mata kyau amma jikinsa babu kuzari kamar yadda taji dazu a waya,sai daya iso cikin Parlor din sannan yayi sallama yana laluben wajen zama,saahar din ta miqe tsam da tray din bayan tayi masa sannu da zuwa ta nufi kitchen dasu,duk da yadda momee ke cewa ta zauna raiha tazo ta kwashe.

A kitchen din ta sameta ta gama cin abincin tana wanke plates din,da hanzari ta karba kwanukan tana mata sannu, murmushi saahar din tayi ganin yadda ta tarbeta kamar wadda tayi wani aiki me yawa

"Aike za'a yiwa sannu"sai kawai taja kujerar plastic ta zauna tana bin yadda raiha ke gudanar da aikin nata cikin nutsuwa,batabar kitchen din ba har sai da adam ya leqo yayi mata magana.

Sunyi gaba shida momee din,ta tsaya tana tattara jakarta data gani a bude,ta danyi mamaki,don tasan a zuge tabar jakar,to amma sai wata zuciyar ta bata may be ta manta ne,a buden ta barta,tunda babu wani baqo cikin gidan bare parlor din bare ta zargi wani abun.

"C'mon momee,please kibar maganar nan" muryar adam kenan dake fita a kasalance idanunsa nakan saahar dake fitowa,waiwayowa momee din tayi kafin ta maida dubanta ga adam

"Okay,amma kayi tunani akai ka gani,think twice kafin yanke hukunci"

"Nasan abinda nakeyi fa" ya amsa mata kai tsaye yana dosar motar saahar da key din ke hannunsa,ya buda mazaunin mai zaman banza yana jira isowarta.

Sai data yiwa momee saida safe,ta rakata da addu'o'i kamar zata rusuna mata har qofar motar,saahar din ta shige a kunyace kan yadda momee din ke mata,sannan ya zagaya shima ya shiga seat dinsa,ya tayar da motar suka fice a gidan.

Shuru ne ya ratsa motar,tunanin saahar ya dauketa ya wulwula da ita can baya,wasu watanni masu dan dama da suka shude cikin rayuwar aurenta da adam,koda cikin tarin mafarkai,bata taba tsammanin zatayi mafarki guda daya da zai nuna mata nan gaba momee zata sota ba,zata amsheta hannun bibbiyu a matsayin suruka ba,sai gashi a yanzun......cikin wani hali da yafi kama da juyin juyi momee ta amsheta har fiye ma da yadda take nunawa adam qauna da kulawa,duk da kasancewarsa tilon d'a a gareta.

Saukar hannun adam saman nata hannun ya fargar da ita,ta waiwayo ta zube masa kyawawan idanunta da suka tilasta masa lumshe nasa idanun

"Yaadai?,akwai matsala ne?" Tattausan murmushi ta sakar masa tana girgiza kai

"Babu" sai yaja hannun nata zuwa bakinsa a tausashe yayi kissing bayan hannun,wani abu ya sauka a zuciyarta,ko yaushe adam baya gajiya da ita,hakanan baya gajiya da bayyana zallar soyayyarsa a gareta.

********Misalin qarfe shida ne na yamma,dai dai lokacin babu abinda gidan yake fitarwa sai daddadan qamshin turaren wuta daya wadaci kowanne lungu da saqo na gidan,sai sauran burbushin qamshin daddadan abincinta da tuni ya gama zama ready saman dining table.

Saahar din irin matan nan ne da suka kai sunan mata ta kowanne fanni na rayuwa,suka kai qololuwa gurin iya zamantakewar gidan aure,suka kuma qware tare da ci gaba da neman sani cikin kowacce rana ta ubangiji ga dukkan macen data amsa sunanta,ta kuma qware gami da sanin dukka hanyoyin kyautatama miji,tare da zama tauraruwarsa.

Tun daga abinda ya shafi kyan sura,gayu dake cakude da ilimi da kuma tsantsar tsafta,kawaici haquri da iya mu'amala,uwa uba iya girki da kuma gyaran kai kowanne lokaci lungu da saqo,ta yadda zata dace da muradin adam,tasan yadda zata hadawa kanta nau'in dukkan wani abu da zai daga martabarta da darajarta na diya mace awajen miji.

Idan ka shigo gidan ka sameta kaga yadda take tafiyar da gidanta cikin tsari da nutsuwa ba tare da ta buqaci me aiki ba zakiyi matuqar mamaki,duk da tarin gata da dukiyar da mahaifinta keda ita,amma wannan sam bai sanya ta dauki kanta takai wani bigire ba,tana ganin cewa cinyewar rayuwar mace a gidan aurenta shine ta bautatawa mijinta,tayi hidima cikin gidanta da dukka jikinta da hannuwanta.

Kamar yanxun data kammala komai,tana sanye da wata gown ta wani farin material me santsi qal dashi,ta daure sassalkan gashinta cikin farin ribbom daya dace da rigar jikinta,jikinta na fidda wani sihirtaccen qamshi da babu lallai ka iya tantance ainihin turaren da tayi amfani dashi kai tsaye,qamshine mai tafi da zuciya da tsayawa arai,tana qaunar qamshi har batasan iyaka ba,zata iya saka ko nawa ne ta siyi turare muddin qamshinsa ya dace da tsarinta.

Tana shirin zama ta tuna bata hada ruwan wankan adam din ba,saita aje wayar hannunta,ta juya cikin tafiyarta me kama da na me tausayin qasa ta wuce dakinsa sannan ta zarce toilet dinsa.

Daga ciki ta jiyo qarar sautin wayarta,ta goge hannunta jikin rowels din dake rataye a bandakin cikin tsari,wanda da kanta ta zabarwa kanta tsarin duka toilets dinsu,take kuma kula dasu kamar ba muhallin qazanta ba saboda yadda suke samun kulawa.

Special tone ta sanya masa,don haka kafin ta qaraso ta fahimci wanda yake kiran, murmushi ya subuce mata,ta juya qwayar idanunta sannan ta daga wayar ta kara a kunnenta

"Amincin Allah ya tabbata a gareka"

"Tare dake mace daya tamkar da dubu.....nazo wuce wani fish park ne naga suna gashin kifi,kina da buqata ne?" Take taji yawunta ya tsinke,ta tuna wanda taci shekaran jiya kamar ta tsinke harshenta,tunda take bata tana craving na kifi irin wannan karon ba

"Na gode qwarai da gaske dear,ina buqata idan har zan samu"

"Kin samu ma matar aljanna,kinfi gaba haka,kinfi qarfin ki nema abu ki rasa" ya fada a tausashe,sautin murmushinsa yana isa kunnuwanta,idanunta ta juya dadi yana dada ratsata,idan tace duk duniya babu miji kamar nata to ba shakka batayi kuskure ba,batajin a wannan lokacin akwai miji kamar nata,ko yaushe soyayyarsa a gareta sabuwa ce,kulawar data tabbatar mata da yawa sun rasata,wasu kuma suna kewarta,batasan dame zata amsa masa ba,saidai farincikin da takeji wanda a kullum baya gajiya da sanyata a cikinsa,a haka ya barta da waya a hannu tanata smiling,kafin daga bisani ta zame wayar daga kunnenta,ta koma ta zauna saman kujerar ta zauna,sannan taja wani english novel tana dubawa qafarta daya saman daya tana jiran qarasowarsa.

FURAR DANKO
Billyn Abdul

-ZAFIN KAI
Mamuhgee

-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma

-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo

Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400

Pay at👇

1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim
Sai katura shedar biyanka anan👇

09032345899

Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇
09033181070

VIP🔥💯
Zafin kai 3k
Furar danko 3k
Tabarmar kashi 3k
Bakon munafuki 3k

*Al'ummar NIJER ku kira wannan number don yin naku pyment din*

+22799643131

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*

*THANKS FOR CHOOSING US*🥰

Zafafa🫶🔥


*H U G U M A*

*_TABARMAR ƘASHI_*💔
Page 38


Horn dinsa kadai ya isar mata da saqon dawowarsa,ta ajjiye littafin a gefanta ta miqe a nutse tana takawa zuwa farfajiyar gidan.

A tsakiya suka hade, yasa dukka hannayensa biyu ya tarbeta,ya dagata sama cak yana dariya

"Na jima banga macen da bata da nauyi kamarki ba" dubansa tayi sosai da dukka idanunta,saiya lumshe idanunsa yana jinjina mata kai

"Ka jima kuma?,akwai wata ne bayan ni?" Idanunsa dukka ya ware yana dubanta gami da girgiza kai

"Babu,har abada kuma ba za'a samu ba,idan mutane na cewa kada ki yarda da mijinki muddin zaice miki bayanke babu qari,banda adam a ciki,ki rubuta ki ajjiye,ina miki magana ne kan qanne na da nake dasu wanda momee ta riqesu kafin daga baya ta aurar dasu tun a ghana" murmushi ta saki tana saqalo wuyansa

"Nima nafison na zauna a haka,don banason ka daina daukata" ta fada tana langabe kai.

Dariya ya saki yana duban idanunta

"Kina tunanin akwai qibar da zatayi sanadin da zan daina daukan matata masoyiyata?,babu ita,muje ciki na baki kifinki" daga haka ya taka da ita zuwa ciki suna hira qasa qasa.

Tun hankalinsa baikai kan yadda take cin kifin hannu baka hannu qwarya ba har ya ankara,ya tsaya da abinda yakeyi yana kallonta,sai ya kama hannunta da take qoqarin kaiwa baki ya riqe yana dubanta cikin kokwanto,suka hada idanu saita sakar masa murmushi

"Please dear,don Allah ka barni na qarasa mana"

"Yaushe kika zama hadamammiya ne?" Wuyanta ta langabe tana kallonsa

"Nima ban sani ba,kawai dai na wayi gari inason kifi fiye da komai" hannun ya sakar mata,sannan ya koma da baya ya zauna yana fuskantarta,yanayin fuskarsa yana dan canzawa kadan bada wani alamu me yawa ba

"Tun yaushe?" Ya jefa mata tambayar,wanda ita tuni taci gaba da cin kifinta,ta daga kai suka hada ido

"Dearrrr.....ka bari na gama tukunna,ban qoshi ba Allah" shuru ya danyi yana ci gaba da kallonta,kafin ya miqe yana zare kayan jikinsa saboda wanka

Please Login or Register in order to submit comment