Reading TABARMAR KASHI 1&2 complete by SAFIYYA HUGUMA Chapter 66 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

batajin zata sassauta miata. duk randa ta tashi miga hukuntata,sai ta san ya yarinyar tayi dana sanin saninta a rayuwa,sai ta saryata ta zama izina ga kowacce diya mace dare shirin sake shiga rayuwar toufeeq din,ciki harda uwar data haifesa

_uhmm, kifi na ganinka me jar koma_

"Ki gara haquri duka saura kwanaki biyar mu wuce gaba daya har da ita fadeelan,zan saka a yau din a duba mana ticket da zai maidamu gida lokaci daya" sai data hadiye wani abu a gasan ranta sannan ta dauke dubanta ta mayar ga yayanta

"Yaaya, vanzu lalacewata yakai toufeeq ya wuce ba tare da ya gaidani ba?, hakan ba 'yar manuniya bace ga matarsa tayimin duk wani diban albarka da taga dama?" Dan dubanta kadan maji tayi, sai ta mige a nutse ta fice tabar musu dakin. Cikin ranta takejin indai toufeeq din bai gaidata ba bai kyauta ba da gaske, koba komai ganwar uba uwa ce komai lalacewarta ita da Dr din duka ba wanda ya lura da hakan. Reception ta wuce tana fidda wayarta ta kirashi tace ya sameta a can.

Ba jimawa ya taddata, ta nuna masa guri ya zauna

"Moha ban zaci samun dabi'ar raina na gaba daga gareka ba,ko meye a tsakanina da fauziyya ba huruminku bane wannan wani abu ne dava shafemu,me yasa baka gaida fauziyya ba?" Qas yayi da kansa, ya rasa wacce amsa zaya bata, ya sani ba Dr ba,ko ita da yayi imanin tasan halinta ciki da waje sai ta girgiza idan taji abinda hajiya qaraman ta aikatawa jininta gudar jikarta, yanzun kuma bayason yacewa kowa komai,so yake su isa gida ya gabatar da komai da hujja


"Bazan iya gaidata bane maji, kiyimin afuwa" ya furta a hankali vana daga idanunsa zuwa kan majin. Kafeshi tayi da kallo tana mamakin yadda tashi guda kamanninsa da launin idanunsa suka sauya, idan ma idanunta sun gane mata dai dai harda kwanciyar hawaye a qasansu.


Zafafabiyar

"HUGUMA*

_TABARMAR KASHI*

Book 02 Page 63


"Me yasa Mohammed?" Ta jefa masa tambayar a mamakance tana karanto tsantsar duhun bacin ran dake qasan zuciyarsa, tana son karanto zuciyarsa kai tsaye, inn karatun da cikakkiyar uwar da tasan abinda takey, takewa yaron cikinta komai girmansa. Dauke dubansa yay ya maida gete ransa yana soyewa

"Zakiji maji a gaba, kiyimin afwa" shuru dukkansu sukayi shi da ita,jilkinta ya bata tabbas akwar wani gagarumin abu da ya faru,duk da ba'a shaidar dan yau amma ita din tayi amanna da Muhammad din d'ari bisa d'ari

"Shikenan,Allah ya rufa asiri" ta fada a sanyaye

"Ameen" ya amsa. Har ya miqe tace

"Ka dauki matarka ku wuce zan saki dakin dana Kama din tunda babu amfani, ruwanka ka taimaki likitocin Kan taimakon da sukayi muku don ku samu ganin diyoyinku, ruwanka kuma ka wargaza aikinsu" sai a sannan yaji kunya ta kamashi,yasa hannu ya shafi lallausar sumar kansa yana murmushi cike da jin kunya

"Allah ya saka da alkhairi ya qara girma". Kai kawai ta girgiza bayan wucewarsa, har ranta tana jin wani farinciki yana saukar mata,nutsuwa tana gauraye rayuwarta,ta tuna da darensu na jiya ita da Dr jarma din, komai nashi dare zuciyarta ya koma sabo. Yadda a ajiyan ya dinga bayyana mata bazai taba samun wata mace da zata maye masa gurbinta ba Itama tayr imanin hakanne a tata zuciyar, kawai tana ja masa aji ne saboda ya sake sanin muhimmancinta, tabbas, dan adam abun toro ne, kuma sharrinsa abun neman tsar ne.

_ya ubangiji dukkan wanda zai nufemu da sharri cutatarwa ko quntatawa ga rayuwa da farincikinmu,ya rabbus samawati ka shagaltar dashi da damuwoyinsa,kayi mana tsakani da shi tsayin nisan tazarar da bata da yaka don hasken fuskar annabi muhammad S A W.

*******
Qwarya qwaryar honeymoon suka gudanar a
Germany din tsakanin toufeeq da saahar. Wata irin narkakkiyar soyayya ce me matugar tsayawa a ral ke huda zuciyar kowannensu. Wani irin so me matuqar qarfi da tasirin karya kowanne qarfi kafiya zati da turjiya na zuciya. Karon farko saahar din ta koma masa tamkar wata raqumi da akala,gaba daya ya sauke mata tunaninta,ya goge haddar kanta tasss!!' ,ya tsiyayar mata da man kai babu wani abu da yayi saura cikin zuciya ruhi da gangar jilkinta sai MUHAMMAD TAUFEEQ din.

Gwarzon namijin da cikin lokaci qalilan ya tabbatar mata da karin maganar nan ta hausawa da suke cewa MAZA SUNA SUKA TARA Kuma KOMAI LALACEWAR AL' UMMA AKWAI NA GARI. Yayi nasarar cisge kowanne mummunan tunani a ranta damuwa da bad memories dake damunta,ya maye gurbinsu da wata zazzatar qauna soyayya da zallar kulawa. Irin nau'in kulawar da ta sanya ta dinga hango tsananin wauta da sokonci da take kallon abinda adam ke mata a baya da sunan KULAWA,sam sam babu hadi tsakaninta da wanna kulawar ta ainihi da toufeeq yake nuna mata. Sassanyar soyayya me tafiya da imanin diya mace, duk kuwa da cewa bashi da damar shiga gonarsa yayi ban ruwa,amma a hakan daga ita har shi cikin wani irin aminci suke.

Baisan lya adadin sau nawa bakinsa ya furta godiya ga ubangiji ba,wato inda Ubangly bai cire ameesha daga rayuwarsa ba haka zai tabbata cikin quncin kurkuku da sunan AURE?,haka zai dawwama cikin mayaudariyar soyayyarta wadda bata da ma'ana ko gardi ko kadan?,cikin kwanakin KHADIJATU SAAHAR ta zame masa ALJANNARSA TA DUNIYA kamar yadda taci alwashi. Komai nata a nutse yake da want inn tsari me tsayawa a zuciyar namiji,tana da want irin Kula da takatsantsan a komai nata da sanya farincikinsa a gaban nata. Sun hadu sun kulle sun dinke sun zama cikakken abu guda.

_RAMIN KARYA kurarre ne_*


karfe uku na rana jirginsu ya sauka a filin sauka da tashin jiragen sama na mallam aminu kano dake garin kano. Jirgin da yayo dakon iyalin DR MAHMUD JARMA da kuma surukansa. Toufeeq da sahar,dr din da kansa
• da sarautar mata maji, afifa da hayatee dinta sajjad, sal kuma sister nadeeya da shalelensu fadeela, daga gefe kuma hajya qarama ce dake ankare da takun kowa,cikin ranta da zuciyarta kuma tana jin duk wannan scenes din ya qare tun a Germany,dukkansu sun gama cin gaajiyar soyayyarsu, a yanzu lokaci ne da kowa zai girbe hukuncin data tanadar masa.

Duk da haka babu abinda ta tsana irin idanunta su sauka akan maji da Dr, ko kuma säahar da toufeeq,basu ba hatta nadeeya ta sakawa ranta wannan karon ba zata sassauta mata ba,ita kanta afifa saita fita daga da'irar danginsu tunda ta silar saahar ta shiga family din.

lauranin masoyan guda biyu,zaka rantse da Allah saboda hutunsu da jin dadinsu yasa aka shirya tafiya garmany, daga toufeeq din har saahar sunyi wani irin kyau sunyi fresh cikin sati biyun da suka qara akan kwanakin da suka shirya tahowar. Saahar ya hade mata da yanayin cikinta wanda ya samu cikakkiyar kulawa da tabbacin zamansa dai dai bisa mahaifarta, ya kuma sake zuba mata wani irin kyau kamar 'yar sarkin aljannu.

Toufeeq kuwa zai iya cewa kafff! Tsahon rayuwarsa bai taba samun nutsuwa makamancin wannan a rayuwarsa ba,nutsuwa ta ainihi tun daga gangar jiki zuwa ruhi.

Ko da soyayya bata burgeka kana kallonsu zasu baka sha'awa ta kowacce fuska,sai nan nan yakeyi da sahar din tamkar sarauniyar matan duniya, o yaya ta motsa sar ya tambayeta

"Me kikeso ne moonbeam?" A sannan dumin jikinsa kadai take bugata,amma tana jin kunya da nauyin nuna masa,ta tsinci kanta a wani yanay na tsananin son kasancewa dashi. Sanda ta fahimci hakan hankalinta ya tashi,ba da wanda zata iya maganar dashi sai bestie dinta.

Dariya afifa tayi sosai kamar zata kifa akan dan matashin cikinta,har sai da saahar da zuciyarta yanzu yanzu zakaga tazo kusa tace da ita

"'Ki yarfani yadda kikaso,dama aini na kawo kaina ko?"

Rigo hannunta afifa tayi tana qoqarin saita kanta

"Ki yafemin Bestie, Allah bazan ya riqe dariyata bane, nasan wannan yanayin zar yiwa moha dadi qwaral,ashe akwai wanann lokacin zaizo?"

"Ban sani ba,sakeni"

"Zauna kiji" ta fada tana daidaita dariyarta,sannan ta zauna tana fuskantar saahar din.

"Akwai yanayi irin wanann dake iya samun mace me ciki dama, saboda qaruwar hormones dake jikinta, amma karki damu,tunda kwanakin da zaki wake ki koma mu'amalarku yayi,ba wani matsala, kibar toufeed yaci karensa kawai babu babbaka,nayi imanin zai sake haukace miki ne kawai, saboda a yanzun jikinki na sakin sinadaran da suke sake maida mace cikakkiya qwarai,kada ki damu,zan fahimtar da hayatee,ya daukawa yaa toufeeq hutu a kowanne branches na Kamfaninsa dake kowacce qasa har sal ya gama biyan bashin dake kansa" dariya wannan karon bestie din nata ta bata, sal kawai ta dungure mata kai,amma qasan ranta kunyar aritan takeji,itama ta fahimci haka sai tace

"No boundaries between us bestie, komal nawa ya shafeki, kamar yadda komai naki ya shafeni".

"Tunanin me kikeyi moonbeam?" Ya tambayeta yana dan Jan hancinta,kanta yana kwance akafadarsa

"'Ba komai" muryarsa ya sassauta yana yin qasa da muryarsa

"Na gane komai fa, kuma zan biya duka basussuka,ina
• tsoron qetare ryaka ne maji tace nayi wani abu da ba dai dai ba ta daukemin Kai,shi yasa nayi kawaici na qara wadan nan kwanakin akai, amma definitely am craving for you" sunne fuskarta kawai tayi ta rasa amsar bashi.

Madubi hajya mansura ta dauka tana sake kallon fuskarta da kyau, kamar yadda labiba ta kasa zaune ta Kasa tsaye,duk bayan mintuna saita duba make-up din Tuskarta. Dukkaninsu ita da mahaitiyar tata sun shirya tarbar uba da dansa, bayan cikakken shiri da kuma tabbacin da suka samu daga bakin sabon boka na musamman da mansura ta canza saboda gain bayan hajiya qarama. A yau din kacokam ta sauka gidan toufeeq don tarbar mijinta, labiba kuma ta tarbi touteeq ta Kuma ci gaba da zama a gidan tana farautar zuciyarsa kamar yadda tayi imanin hajya qaraman na cusa haseena cikin lamuransa ta qarfi da yaji don samun shiga a wajensa. Taci alwashin wannan Karon babu gudu babu ja da baya, kanta tsaye zatayi fito na fito da hajiya qaraman,ta kuma gama shirya duk wata hujja akan hajiya garaman koda zata nemi kawo mata wargi ko ta Kawowa shirinta tarnaqi. Manya manyan hujjoji ne da ake tanada saboda rana irin wanann,manyan hujjojin da kake ajjiyewa saboda tarwatsa maqiyi kuma abokin adawa a duk sanda yakejin zai tsallake lyaka da kuma gonarka.

Karo na uku hajiya mansura ta sake leqawa da
Kanta farfajiyar gidan ta window din sashen Dr jarma wanda bazai iya tuna yaushe rabonsa da shi ba. Da kanta ta sanya akayi masa gyara na musamman saboda zamanta a nan dinne kadai zai iya bata damar aiwatar da burinsu hankali kwance.

Duk da ta fara qaguwa da jiran isowarsu amma zuciyarta fes take saboda albishir din data samu daga mutumin da take Kira da malam.

"Akwai nasara a goben guda d'aya,akwai faduwa da asara guda biyu" bayanan da yayi mata kenan, bayan ya sake bata tabbacin hajya qarama na daya daga cikin faduwa da asara guda daya cikin biyun da ya lissata

"Nike da nasara!, tabbas nike da nasara!!" Abinda ta maimaitawa kanta kenan,saboda tako ina idan ta juya tunanita nasarar take hangowa kanta,cikakken shirt ta yiwa kanta da take da yaqinin babu faduwar!!, nasarar dal!...

-tofa jama'a, maji ma gani wai an binne tsohuwa da ranta,maga wake da nasarar,wake da asarar da kuma faduwa_

Zafafabiyar

"HUGUMA*


*_TABARMAR KASHI_*

Book 02 Page 64

Dukkansu suka mige sanda sukaj| qarar bude gate din gidan tare da qarara shigowar ayarin motocinsu su
MT JARMA. Kallo sosal hajiya mansura ta mayar kan labiba

"Wannan karon babu sauqi babu sassauci,babu kuma daga qata,fatatawa ce ta gaske,yaqin sunquru za'a yi tsakaninmu da duk wanda zai hana mana cikar burinmu,ni dake kowa yayi amtani da damarsa ya samawa zuciyarsa abinda takeso" kai labiba ta jinjina cike da gamsuwa

"In sha Allah mama" tare suka fara takawa suna fita zuwa harabar ajjiye motoci na gidan, don zuwa yanzun sunsan duka motocin sun isa can.

Lissatinsu ya basu dal dal, sanda suka isa din duka suna qoqarin fitowa daga motocin, banda toufeeq, da säahar dake zaune cikin tasu motar kamar basu shirya fitowar ba,ya tsareta da fararen idanunsa yana Kalionta bayan ya dauke kallonsa daga duk jama' ar dake farfajiyar gurin, kama daga ma'aikatan gidan da haseena dake riqe da hannun hajiya qarama dake qogarin fitowa da mota,har labiba da ke isowa gurin.


"SAHR…...bana buqatar.....

"Shshshsh" tace dashi tana dora yatsantsa kan labbansa fararen idanunta masu wani irin haske ta zubesu a cikin nasa

"Kada kace komai,duk wadan nan tarkace nima bana bugatarsu,for now ya kamata su nisanci rayuwar mijina ko? idan ba haka ba zasuy nadaman cusa kansu ga rayuwarka,am new version of saahar, ba tsohon version din da suka sani bane" a hankali ya kama yatsanta dake kan labbansa ya tura bakinsa yadan tsotse kadan. Da sauri ta fuse hannun tsigar jikinta na tashi tana masa nuni da fadeela dake zaune gaban motar, kafadunsa duka biyun ya daga sannan ya rausayar da idanunsa ya maidasu waje shi da ita duka suna ci gaba da kallon wajen.

Cikin takun kissa da jan hankali hajiya mansura ke takowa zuwa gurin har ta iso bakin motar dr jarma

"'Barka isowa,marhaban da......." Qafewa kalaman bakinta sukayi suka tsaya mata a wuyanta,su basu fita ba su basu koma ba,wani irin abu ya tsarga mata wanda ya haifar da tsatstsafowar gumi daga kowacce kafa ta jikinta sakamakon ganin maji da tay na fitowa a motar mazauni daya da Dr din. Duk wata walwala tata ta janye kaff!. Bata taba zaman kishi da maji ba, amma tayi imani zaman kishi da matar bazai taba yi ma kowacce macce dadi ba,duk wadda kuma tayi gangancin aikata hakan tabbas zata iya kwasar kashinta a hannu.


Da boka da malam cakude da tuggu da makirci amma tsahon shekarun da tayi da Dr din basuyi nasarar cire maji dari bisa dari daga zuciyarsa ba,ta wahala ta wannan fannin da tsantsar baqin kishi, wanda ta dinga ji inda tare suka rayu da maji babu abinda zai hana zuciyarta bugawa fes.

Murmushi hajiya qarama ta saukewa fuskar hajya mansura,ta tabbatar a yau boom na farko da zai fara tayar mata da kan mansura batun maida auren mijinta ne da tsohuwar matarsa da tayr imanin mansura din bata sani ba,kuma tasan itace mutum ta farko da zata fara aje zarginta a kanta,to ko hakan ma yayi mata,wannan zai qara mata tsoronta cikin zuciyarta hadi da shakkarta,zai kuma sake dasa mata cewa ita din ta isa da yayanta kuma kome tace ya aikata zaiyi din,duk da lamuran sun fara sauyawa.

Murmushin da ta gani a fuskar fauziyya shi ya sanyata hanzarin maida nata murmushin saman tata fuskar itama,ta sani murmushin fauziyya irin wannan ga abokin takun saqa ba alkhairi bane,sai ta sake matsawa tana yi masa maraba,fiye da rabin hankalinta nakan maji.

Ko sau daya majin bata dubeta ba,saboda bata qaunar kishin dake ranta ya motsa a kanta,abu daya ta sani,ranta yana baci da yadda Mahmud din ya buge da auren mansura. Tasan mansura farin sani tunda tana daya daga cikin qawayen da fauziyya ke tara mata suna keta alfarmarta har cikin gidanta a wancan lokacin.


Ta gefansu ta wuce abinta tana migawa nadeeya
Jakar hannunta,sannan suka wuce zuwa sashensu.

Idanun Dr yana kan maj,yayin da idanun mansura yake kan Dr,har zuwa sanda maji tayi nisa ya maido hankalinsa ga mansura. Fuska ta bata sosai baqinciki yana ciciyar zuciyarta,babu ta yadda zata yarda ta bari matar nan taci gaba da zama a qasar nan,idan ba haka ba kuwa tayi imanin tata ta kusa qarewa.

Juyawa tayi abinta saboda bacin rai,sai yasa hannu ya kamota

"Yaki mana,ya zaki tafi?" Ya fada a tausashe. Dole yabi a sannu, saboda yasan a yau din Allah ne kadai yasan kalan tashin hankalin da za'a yi a gidan idan taji maida aurensu, amma hakan ya zama dole ya shelanta kowa ya sani saboda fidda zargi da kuma sake shaidar zamantowarsu miji ga mata din ga family dinsa.

"To me yayi saura kuma?"

"Muje" kawai yace da ita. Gaba tayi tana qoqarin hadiye fushinta, tanason taci ribar yau din,ta kuma kwashe dukka nasarorin da malamin tsubbun ya gaya mata, tasan tushi kuma ko tashin hankali bazat sanya ta tsira da komal ba indar Mahmud ne.

"Ki koma suna cikin motar, ki tarbeshi ki nuna damuwa da kulawarki a kansa" hajiya qarama tace da haseena wadda ke shirin shiga sashenta. Bata cewa uwar komai ba ta juya din da sassarta, ya qaguwa tayi da son ganin toufeeq din, tunda ya tafi ko sau daya bataji muryarsa ba bare ay zancan ganinsa.

Tana dab da isa ta hangi labiba a tsaye a gurin,wani bacin rai ya taso mata,itafa ba labiba da suke takara tare ba,hatta da saahar din ta tsaneta.

Ya gama karantar takun kowa a cikinsu, sai ya janye idanunsa cikin ransa yana raya kowacce zataci qaniyarta. A nutse ya bude motar ya sanyo qafafunsa waje. Cak kowacce ta tsaya daga inda take, kwarjininsa cikar haiba da kamalarsa yana dukan fuska da zuciyar kowaccensu.

Hannu ya miga ma saahar dake zaune cikin motar, idanu suka hada ya sakar mata murmushin nan nasa me tsada,sai ta mayar masa da martani, ta miga masa nata hannun tana jin qaimi cikin zuicyarta,wani sashen na zuciyarta yana sake cika sosai da kishinsa.
Tamkar wata da zara haka suka fito, sunyi want irin mugun kyau da matching da junansu, koda maqiyr idan ya gansu a lokacin sal sun burgeshi.

Daga labiba har meenal kowacce sai data hadiye wani yawu mai tauri, a take dukka wani qwarin gwiwar da labiba ta debo ta tsiyaye ta kuma tarwatse a gurin, kallon sãahar kawai na farko taji ta raina kanta gaba daya,tako ina bata isa ta gwada kanta da ita ba, koda silin yatsanta guda daya tasan bata kamo ba,sãahar din tayi wata muguwar gogewar da ko ke diya mace sai ta burgeki bare d'a namiji,duk da wanna kuma idanuwanta sun gaza daukewa daga kallonsu.

Yawun bakin meenal gaba daya ya dauke da wani irin mahaukacin kishin saahar, tabbas inda ace akwai bindiga yanxun a hannunta babu abinda zai hanata harbawa saitin zuciyar saahar, tako ina ita dimma tasan zati da cikar haiba nutsuwa da kamalar säahar ta zarta tata,saidai kuma bata jin ko kadan wannan Karan zatay giving up, ba zata sassauta ba wajen farautar toufeeq har sai taga abinda ya turewa buzu nadinsa,don haka ta tattara dukkan qwarin gwiwarta tayi taku biyu zuwa inda suke takawa,cikin fari da ido, lanqwasa harshe da yauqi tace

"'Barka da dawowa yaa mohanmu.....

"'Wayy!" Säahar ta datsin maganar da meenal ta debo tana lanqwashewa, abinda ya maida dukkan hankalin toufeeq kanta

"Yaya? me ya faru?" Cikin wata muguwar shagwaba data shigeshi gaba daya cikin jini da julya tace

"Qafafuna,na gaji,nidai ka daukeni"

"Angama" ya furta yana nannade hannun tsadadden yadin jikinsa. A tausashe sannan a hankali ya tsugunna yasa hannunsa ya dagata cak ya fara takawa da ita zuwa sashensa idanunsa cikin nata yana tambayarta

"Are u comfortable?" Kai ta jinjina masa sannan a sace ta dubi sashen da su labiba sukayi mutuwar tsaye,cikin sa'a suka hada idanu,ta aje musu wani kallo na baku isa ba sannan ta maida kanta saman qirjinsa ta kwantar a shagwabe.

Dariya labiba ta qyaqyace da ita sanda taga haseena da tayi mugun shaqa,ta kuma gaza boye shaqar da tayi din ta hanyar binsu da kallo, duk da cewa sun bacewa ganinta

"Ashe dai duka burga ce,ashe dai ba'a isa din ba,ashe duk kwana da tashin da akeyi gida daya duka suna ne,ah wai" labiban ta furta tana tura dauninta gaban goshi,duk kuwa da cewa ita dinma ta shaqi bacin rai har kusan fiye dana haseena.

A mugun fusace haseena din ta waiwayo
'Ke, ki saurara malama, koda giwa ta fadi tafi qarfin wawa, ni ba sa'arki bace,don nafi qarfinki har abada" sosai labiba ta sanya dariya harda shewa

"Mu gani a qasa mana,wai inji kare ana biki a gidansu yace mu gani a qasa,ashe duk wani cika baki da fankamar uwar taki na banza ne, tunda ta gaza mallaka miki mutum daya tal a rayuwarki,wannan ma ya isheku hasara da kaico, bayan kaicon da a wunin yau kafin faduwar rana yake shirin samunku, ku shirya zuwarma gagarumar FALLASA wadda zata cimma rayuwarku" daga wannan sai ta juya tana taku d'ai d'ai, cikin ranta tana jin FALLASAR da zata auku a yau din, tamkar mabudin nasara ne a garesu.

_to maji ma gani wai an binne tsohuwa da ranta_

A bisa bigire daya suke takawa,saidai kowacce zuciyarta cike take da alwashi da kuma mugun tanadi ga ‘yar uwarta,wani irin kallo a sace wanda bakuna basu furta komai ba sai fatan cikan burika, a haka har suka iso mararrabar sassan guda biyu,dr jarma yay gaba. Daga Mansura har fauziyyar kowaccensu tsawa tayi "Ina miki barka da isowa qasarki ta gado,ina miki barka da isowa bigiren da zaki fahimci bakin rijiya ba wajen wasan makaho bane,ina kuma yi miki jaje da kalar qaddarar da yau din tazo miki da shi, ina miki fatan samun juriya a bisa hakan" sai da gaban hajiya qarama. yadan fadi, amma kuma tayi gaggawar ture wannan daga ranta da tunaninta,don kuwa a kaf tarihinta bata taba yarda kalaman barazana sun tsoratata daga bakin abokin adawa ba. Jifanta tayi da murmushi duk da zuciyarta na cike da kokwanton yadda mansura ke magana kanta tsaye cike da qwarin gwiwa

"Ke ya kamata ki riqe wadan nan kalaman kiyi bitarsu da kyau,domin a yau kadai zaki fahimci ni fauziyya nike sanyawa a auro a kuma saka sannan ayi kome a duk sanda naso hakan, baya ga wanna kuma..…... Tarantin
nan da kike shirin taka gefansa, kina gab da gain asarar da bazaki iya qidanya adadinta ba" murmushin ta jefa mata Itama

"Ni dake shege ka fasa"

"Dan halak sai kallo" sai kowannensu ya juya yana nufar sashensa, saida dukkansu zukatansu cike suke da fargabar yagewar zaninsa a tsakiyar kasuwa,saboda gaba dayansu sunsan sunyi birniya me zurfi da kowa a cikinsu yasan da mummunar ajiyar dan uwansa,amma cikar da zukatansu sukayi da daukan fansa da samun cikar burin diyoyinsu ya sanya suke jin komai zasu iyayi, komai ta fanjama fanjam.


*_turqashi, kuzo kuyi kallon dinkin gadar zare zai tsinke_*


Da hanau gwara mannau inji hausawa * ,ku yimin uzuri,jiya dama ta bayar,yau kuma sal a hankali, na gode qwarai_*



Zafafabiyar
"HUGUMA*


*TABARMAR KASHI_*

Book 02 Page 65


Zucivarta kamar zata fado take takawa zuwa bedroom din Dr jarma din. Hankalinta na tashi idan duk second daya da zai shude idan tayi tunanin ko dai fauziyya ta sanya Dr jarma ya dawo da shifa dakint? tunda dai kalamanta hakan suke nunawa yana shirin faruwa. Kai ta girgiza, indai hakanne har abada ba ) zata taba yadda ta zauna da shifa ba, ba zata taba aminta wata mace ta shigo mata gidanta ba gidan data ciwa burika masu yawa,take kuma sanya ran ita daya ce macen da zata yiwa dr jarma takaba ta kuma karba tumunin takabar ita daya.


Fuskarsa cike da nishadi yake cire kayan jikinsa da zummar yin wanka,jya walwalar dake saman fuskarsa ya sake dasa mata matsananciyar fargaba "'Drya akayi na ganku tare da maji ne?, dama tare kukayi tafiyar?" Waiwayawa yayi ya dubeta yadda ta cake tana masa tambayar wadda tafi kama da titsiye. Kansa ya dan kawar yasan akwai dan rashin kyautatawa da yayi mata,a galla ya shaida mata koda ta waya ne zai maida aurensa

"'Me kikeson ii mansura?"

"Ka maida matarka ne?" Sake maida dubansa yayi a kanta

"Me kike ci na baka na zuba?, ki barni na watsa ruwa mana, ba tun muna can kika gayan kin shirya mana liyafa tare ba?" Kai ta jinjina masa kawai

• "Okay, bari na watsa ruwa na fito, saikiyi gogarin shaidawa kowa ya fito akan lokaci aci abincin tare. hakan dama va kamata lokaci lokaci a dinga yi, saboda vana kawo hadin kai da garin fahimtar juna" bata iya amsa masa ba har ya wuce zuwa bandakin,sai ta furzar da iska daga bakinta,ta dunqule hannunta ta daki dava tafin hannun nata, ta koma ta zauna ta kirayi daya daga cikin masu aikinta tace ta sake shaidawa kowa,amma sashen toufeeg a shaida musu ta waya. Ajiye wayar tayi gaba daya tana jin nutsuwa tana yin qaura daga gangar jikinta,duk yadda taso bawa kanta qwarin gwiwa da kwantarwa da kanta hankali abun ya faskara, sai ta bude wavarta ta hau shirya komai cikin shirin ko ta kwana koda
bugatar hakan zata taso.

Tun a hallway ya din bedrooms dinsu ya fara rage
mata kayan [ikinta,yana tsaye daga bayanta yayin data dogara dukkan wani garfi nata a jikinsa,cikin wani irin slow motion suke takawa shida ita,sadarwar skin to skin din dake a tsakaninsu tana rura wutar dake zukatansu gaba daya. Ta dauka yana isa qofar bedroom dinsa zal bude, sai taga bai tsaya ba har dai dava isa gaban full length mirror din dake bangon garshe na hallway din. Tar surarta da tashi suka bayyana a jikin madubin,

Please Login or Register in order to submit comment