Reading TABARMAR KASHI 1&2 complete by SAFIYYA HUGUMA Chapter 70 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

soyayyarsa,sai ta motsa bakinta a hankali itama

"Dukkan wadannan kalmomi naka masu tarin tsada da daraja ne"

"Kamar vadda kike da tsada da darajar da bansan
adadinta ba a idanuna, bude idanunki mu kalli tsarabar
da kika kawomin a tare" ya fadi yana miga hannunsa
cikin takatsantsan da kulawa ya soma bude fuskokin
varan
"Yes!, ma sha Allah, Allah banyi wahalar banza ba" ya fadi
kansa tsaye yana ma mantawa dasu sajjad dake dakin.
Da sauri saahar ta rufe bakinta saboda kunya,sai sajjad
din ya tattara towel din ahlam yana cewa
"Oya let's go, muje ki garasa bata ko cikin mota ne" ai da
gudun tsiya afifan ta rungume diyarta suna ficewa kada
ayi barin zance a gabanta
"Ai da kunyi zamanku" toufeeq ya fadiwa sajjad cikin
gatse sai sajjad din ya gyalgyale da dariya baiko waiwayo
ba
"Bestienkin nan da sajjad original 'yan sanya ido ne" yayi
maganar sanda ya Sanya hannu yana gogarin daukar
babyn ya zauna a gurin
"Ko yaushe gana fadi min muna basu mamaki, basu taba
tsammanin soyayya zatayi mana mummunan kamu har
haka ba"

"Sai gashi tayi mana kamu me kyau harda result" ya furta yana sake bude fuskar dayan baby din, suna nannade cikin wasu lausasan shawl farare gal masu ratsin blue a jiki

Har wani lumshe ido yakeyi sanda yake kallon fuskar varan

"Na yarda ni din jarumi ne, duka vara na ahalina suke daukowa,kiyi haquri ina miki fatan nasara a gaba" kukan shagwaba ta sakar masa, sai ya saki dariya sosai kaman ba MUHAMMAD TAUFEEQ JARMA ba

"Eh, next time ina expecting baby girls twins, zan tayaki addu'ar samun masu kama dake, don nima ina kwadayin* nayita kallon kyakkyawar fuskar nan ta cika kowacce kusurwa ta gida na" sai ya sunkuya a tausashe yayi
U kissing dinsu su duka sannan ya juya kunnuwansu yayi musu khuduba “Muhammad da Mahmud" ya fadi yana kallonta. Farinciki ne sosar ya ratsata, tabbas taji dadin wannan zabin nasa,dama tun asali sunaye ne masu asali

"Allah ya raya dr girema da dr jarma" ta furta a hankali Ameen,let me hug you please ko zan samu sassaucin abinda nakeli na farinciki a zuciyata" ba musu ta bude masa hannayenta,yayi mata kyakkyawar runguma yana sauke ajiyar zuciya idanunsa akan yaran.

Awanni shida kacal aka rubuta mata sallama cikin aminci da goshin lafiya. Tunda yaji maji na zancan tafiya da ita ta kula da ita ya kasa ya tsare. Koda aka rubuta sallamar sai daya kwashesu ya kaisu motarsa sannan ya gaya musu batun sallamar, kafin maji ta ankara tuni motarsa ta dauki hanyar gidansa, don ko kadan bazai iva jumurin rashinsu a kusa ba. Yanzunne yakejin kansa a cikakken magidanci,wanda ya hada dukkan wata falala da farinciki na rayuwa.

Hakanan maji ta gama salatinta ta haqura

"Muhammad ya maidani kakarsa Allah da gaske" haka tayiya mita tana fada. Nadeeya na gefe tana dariya

"Maji, shifa yaa moha har yanzun farin shiga ne,sai yanzu yasan meye dadin family ki bar masa matarsa da yaransa"

"Allah baiko isa ba, dole na gyara diyata, idan yaso su garata,amma dai yara shima yasan bashi kadai ke dasu ba"

"Ah lallai maji akwai kallo kenan,nan gaba kwashesu zakiyi"

"Zasu haifa wasu in sha Allah" ta fadi, don har ga Allah a son ranta ma su koma gidanta da zama.

Wani irin alheri albarka da farinjini yaran sukazo dashi,yadda gidan yake cika kullum saika dauka suna akeyi kullum. Saahar sai yanzu ta sake amanna da gasken gaske 'ya'ya rahama ne,da gaske haihuwa wata falala da baiwa ce daga ubangiji,wani irin budi da alkhairi ita kanta take gani tako ina. Gadan gadan ake shirya I katafaren suna, duk wani taro na biki da basuyi ba toufeeg ya shirya fansheshi a ranar sunan,ya tsara walima ta musamman shi da abokansa, haka bangaren mata da zasuyi nasu cikin yalwatacciyar harabar gidan.

Zafafabiyar
"HUGUMA*

*_TABARMAR KASHI*

Book 02 Page 73

Qarfe takwas na dare ta fito daga wanka,wanka
ne sosai na jego akeyi mata da dalbejiya,jego takeyi na gaske wanda aka sani a qasar hausa,qanwar maama da maji suka tsaya kan hakan, tuwo kunun gyada wankan darbejiya da gasashen nama bata wasa dashi.

Yaran duka na nannade cikin was kayan babies masu taushi da daukan idanu 'yan qasan turkey,gaba daya ubansu ya maidasu kamar shi, kullum shigar fararen kayan babies suke,komai nasu fari qal sai ratsin blue wani lokaci.

Afifa da nadeeya ne cikin bedroom din
nata, fararen hannuwan nan nata da gafarta sunsha jan lallen suna har bayan hannunta,wani irin dan ubansun lalle kamar ka daye shi daga fatarta, kanta ma yasha gyara na musamman sai gyallin da gamshi yake fiddawa,ta cika ta sake yin dam ta zama 'yar duma duma,don da gasken gaske take gyaran kanta.
Tana gogarin shirya kanta nadeeya tace

"Kada na manta na shiga uku,yaa moha ya kira yace ki sameshi a sassansa, kada ki manta ki tafi masa da
Asad(Muhammad) da as'ad(Mahmud)" amsa mata tayi
da to,sannan ta waiwaya a nutse ta fara gyara jikinta.
Cikin minti talatin kacal ta fito cikin lallausan
material baby pink color da kalae sea blue a jikinsa,tayi
sassanyan kyan nan nata da ya cakude da kyan jego,tayi fresh sosai, jikinta sai qamshin turarenta yake fitarwa.
Baki afifa ta saki tana kallonta sanda ta dauki
asad da as'ad
"Anya kuwa? ,kada fa kije ki ballowa kanki ruwa" ta fadi tana dubanta.

"Ruwa wanne iri?" Gyara zamanta afifa tayi

"To don Allah kina jego inake ina buga irin wannan kwalliyar?" Harara säahar ta sakar mata

"Kefa kin cika sharri, har yanzu bakisan an girma ba? ina kikaga nayi kwalliya a nan?" Tabo nadeeya daketa danne danne a wayaa afifa tayi

"Sister nadiya tayani gani, don Allah ko ke bata dauki idanunki ba bare me gida?" Kame kanta nadeeya tayi tana danne dariyarta

"Anty afifa,na rabaki da shiga sha'anin yaa mohaa da ,anty N,wallahi lamarin yafi qarfina, kame kaina nakeyi kafin naji ya moha ya kirani da munafuka" saita mayar da kanta kan wayar ta tana murmushi qasa qasa
"Kanku akeii" säahar ta fada tana rungume yaran ta fice. dasu

"Su sãahar dadi miji" afifa ta fadi cikin dan daga muryar duk dai cikin salon tsokana.

A tausashe tayi sallama sassan nasa. Ya daga kansa daga zaunen da yake, sai ya ajjiye duk abinda yakeyi cikin lallausan murmushinsa ya taso yana takowa zuwa gareta idanunshi a kansu. Sanye da wasu pyjama ruwan sararin samaniya. Har ya qarasa gareta idanunsa suna karakaina a kanta,yana jin wata qaunar ahalin nasa tana gewayeshi.

Hannu ya miga ya shafi gefan fuskarta cikin murmushi idanunsa cikin nata,sai ya miqa hannu yana karbar asad

"Barka da zuwa giwa ta" ya furta cike da wani irin launin soyyaya da ya haifar da murmushi me qayatarwa saman fuskarta

"Barka kadai aljanna ta" itama ta maida masa tana juya qwayar idanunta a kansa. A nutse ya juya yana shiga ciki vana fadin

"Bari nayi hanzarin matsawa, those beautiful eyes..
Sai bai garasa ba ya saki murmushin da sai da ya bata dariya.

Da d'aya da d'aya ya kwantar da asad da as'ad,a nutse ya waiwayo yana kallonta, har yanzu wannan murmushin bai bace a fuskarsa ba. Hannunsa ya sanya ya riqe nata hannun yana murzawa da vatsuntsa a hankali, idanunsa na biye da kowanne zane na jan lallen hannunta da yayi masifar daukar hankalinsa

"This henna..." Shuru ya sakeyi yana cije lip's dinsa. Sai kuma ya daga kansa yana kallonta

"It's been a long day,i need one of those tight hug"
zame hannuwanta tayi, taja baya a nutse, ta buda masa dukkan hannuwanta. A hankali ya sake matsowa gabanta,ya buda shima masa hannayen ya cusasu ta bayanta ya shige jikinta sosai yana kwantar da kansa saman kafadarta ita kuma ta maida hannuwan nata ta lullubeshi tsam. Duk da bata iya ratsashi ba amma wani irin nutsuwa yakeji tana saukar masa,yayi imani da gaske ne babu abinda yakai mace ta gari bayar da nutsuwa da kwanciyar hankalin mazaje.

"Your touch and your kisses are my weakness" ya furta dai dai saitin kunnenta, abinda ya sanya tsigar jikinta tashi. Ta sani yayi missing kiss ne,saboda tasan yana daya daga cikin abinda yakeso yake kuma rage masa zafi. Dan ja baya tayi kadan,abinda ya basu damar ganin fuskar juna sosai

"Please stop being cute,it makes me want cuddle with you forever" ya garasa fada yana cije lip's dinsa. Hannu tasa ta dan ja kumatunsa tana murmushi

"I can't taste my lips, could you do it for me?" Rigota yayi sosai cikin jikinsa vana murmushi

"Thanks for this beautiful opportunity" bai sake qara koda second biyu ba ya hade bakunansu waje daya.
Hungrily yake kissing nata in and out na bakinta,yanaji cikin jikinsa yayi kewarta sosai. Duk yadda yaji vanason ya wuce ga'ida amma dole ya yiwa kansa birki saboda yasan yanayin da take ciki,ya maida jikinsa ga bango yana maida numfashi, kusan minti biyar sannan ya budesu a hankali. Hannu ya miga mata

"Zo ki gani" ya fada da dakusashiyar murya. A nutse ta tako ta iso gareshi,sai yaja hannunta a nutse suka zauna saman lallausan carfet din dake zagaye da tsakiyar dakin.

Wata kyakkyawar jaka ya jawo ya bude,ya fara ciro abubuwan da suke ciki.

Set ne na gold dan kunne sarga da abun hannu da zobe, muqullin sabuwar dalleliyar mota qirar BMW,sai wasu takardu dake buge da sunanta a sama. Duka ya tattara ya miga mata

"'Bansan da wanne abu zan saka miki ba,bansan meye zan mallaka miki da zai tabbatar da godiyata da jin dadina akan abubuwan da kika yiwa rayuwata ba, inda ana bayar da aljanna tun a duniya lallai da na jima da mallaka miki ita,na baki wannan ne don na nuna kadan daga cikin jin dadin abinda kikayimin,bawai don na biyaki ba" gasa tayi da kanta tana jin wani sassanyan abu yana ratsata tana duban takardun dake gabanta. A duniya babu abinda yafi tsarkin zuciya dadi a lokacin da adam yake dukkan qoqarinsa don gain ya rabata da abinda ta mallaka da guminta qwanjinta da dukka nemanta.....sai-gashi Allah ya aiko mata da wanda ya sadaukar mata da dukiyarsa saboda farincikinta, cikin girmamawa da ) mutuntawa. Adam ya kwashe takardun filayenta sai gashi yau an mallaka mata estate guda, ta mallakawa adam bangles dinta don tsantsar sadaukarwa da soyayya da zuciyar daya.....ya ha'inceta akan hakan,sai gashi yau ta mallaki sarga bangle's da zobba da tasan cewa kudinsu ya ninka abinda ta sadaukarwa da adam.
Adam yaso tattare kudadenta ya gudu,sai gashi ta mallaki motar da ta ninka ninkin baninkin abinda ta tara din,me zata cewa ubangiji banda addu'ar qwarai?, tabi toufeeq tsananin biyayya kamar yadda d'a zaibi uwarsa?.

Hawayen da take zubarwa yaja hankalinsa,ya jawota jikinsa sosai vana shafa bayanta a hankali

"Kada kice komai,all i want is to stay with me forever" gangameshi tayi tana matse ragowar hawayen idanunta tana jin wata qauna me zafi tana Huda qirjinta,a duniya a yanzu batajin akwai wata rayuwa tata da zata iya yiwuwa babu toufeeq.


Zafafabiyar
*HUGU MA*

_TABARMAR KASHI_*

Book 02 Page 74


*_BAYAN SHEKARU UKU_*


A nutse take takawa cikin mansion house din mallakin DR MAHMUD JARMA wanda ko ina kai kawo ne
na jama'a,kaikawon da duba daya zai tabbatar maka da hidima akeyi, hidima irin ta biki.

A nutse MAAMIN SÄAHAR ke takawa cikin dogom corridor din dake qunshe da kebantattun dakin baccin maji,gurin da amintattunta kadai ke ratsashi, kamar saahar nadeeya da afifa da a yanzun ta zama kamar diyar cikinta.

Dakakkiyar shadda 'yar mali ce a jikinta Onion color da yarfin baqi da kima off white, dinkin tea boubou wadda yayi matuqar tafiya da tsari da qirar jikinta.
MRS MUHAMMAD TOUFEEQ JARMA, KHADIJA MUHAMMAD GIREMA, babbar mace hakima da Allah ya huwacewa baiwa masu tarin yawa. Tana sabe da
Mahmud as'ad dake sanye da wata suit ta yara me azabar kyau da daukan idanu,kyakkyawan fine boy wanda kamanninsa ke sake bayyana da babansa shi da dan uwar tagwaitakarsa,kamar toufeeq yayi kaki ya ajiye,bacci yakeyi lakadan a kafadarta,duk da yadda yaketa doki da zakwadin tafiya dinner din SISTER NADEEYA kamar yadda suma suka tashi suna kiranta.
Wani irin sabo sukayi qwarai da ita,suna daukarta babbar abokiyarsu da suke mugun sakewa da ita.

Cikin shekara ukun kacal khadija Muhammad girema ta sauya gaba daya,ta zama wata hakimar mace da idan ka kalleta sai ka sake son ka sake dubanta a karo na biyu,iya 'ya'ya mata kawai kishin kyau da ajin da take dashi sukeyi.

Wannan ya sanya Muhammad toufeeq kishinta sosai da son killaceta hadi da kaffa kaffa da ita,domin ita din rayuwarsa ce kuma mahadin ruhinsa.

Daya daga cikin gofofin ta murda ta bude ta shiga bakinta dauke da sallama. Qamshi da sanyin na 'urar sanyaya daki ne abu na farko da zai fara buso maka. Maji wadda ke a zaune saman carfet din dakin ta amsa. Tana sanye da wata light army green super Holland ta ainihi,fararen hannayenta da qafafunta sun sha jan lalle, ainihin qabilarta da dangantakarta da jinin labarabawa ya fita zammm,gashinta da har yanzu bai surka da furfura ba ya fito ta qasan dankwalin atamfarta.

'A'ah yayar amarya baki tafi ba dama?" Maji ta tambayeta tana miqa hannu zata karbi as'ad. Bata jin nauyin yaran ko kadan,duk da cewa jikin kakansu sukayo

Dr jarma,suna da qiba madaidaiciya da cikar zati

"Ban tafi ba maji,na dai tsaya naga tafiyar kowa"

* "Kedai sannunki, Allah ubangiji yayi miki albarka"

"Ameen ya Allah maji" ta amsa a sanyaye tana qogarin
fidda murmushi.

Sai data gyara zaman as'ad a jikin maji sannan ta mige ta gyara wuyan rigarta,ta miqa hannu tana daukan mayafinta mahadin kayan jikinta ta yafa

"Zamu wuce maji"

"Ke da waye zaku tafi?"

"Yusuf ne zai kaini a motata"

"To Allah ya tsare saikun dawo". Ta amsa da amin tana juyawa maji din kuma ta bita da kallo.

Har takai bakin gofa maji ta kirata,sai ta dawo ta samu gabanta ta zauna

"'Amma me yake damunki maami?" Shuru tayi tambayar maji tana taba zuciyarta,a sanyaye tace

"Ba komai" shuru itama majin ta danvi, ta sani dole ko tsakanin harshe da haqori ma ana sabawa bare miji da mata. To amma tsahon shekarun aurensun nan, ko sau daya daga ita har toufeeq din babu wanda ya taba kawo mata qarar dan uwansa, batason ta cika zurafaf tambaya don tasan a yadda halaye da dab'un sãahar din suke na zurfin ciki ba zata gaya mata komai ba,bata dai jin dadin yadda take gain damuwa saman fuskarta, tun daga shekaran jiya da suka taho biki gidan kawo yau

"Shikenan, Allah ya rufa asiri, amma ki rage sanyawa ranki damuwa ko don abinda yake jikinki" daga kai säahar tayi da sauri tana duban maji kamar me neman garin bayani.

Maji din tasan hakan zata faru saita dauke kai, alamu sun nuna mata sãahar din batasan da zaman cikin ba,shi yasa tayi mata jirwaye mai kama da wanka.

"Tashi kije, Allah ya tsare, ko ba'a tashi ba ki sanya yusuf din ya dawo dake kinsan halin Muhammad"

"'In sha Allah" ta fada tana migewa. Gidan duk an yoye an tafi dinner din nadeeya da mijinta Nader,a hankali maganar maji take dawo mata a kai

"Abinda yake jikina kuma?,maji na nufin wani cikinne dani?" Ta yiwa kanta tambayar dai dai sanda ta iso gaban motarta. Yusuf dan qanwar maji ne da sukazo biki daga Algeria, matashin saurayi ne da duka duka bai wuce shekara goma sha tara ba,amma yana da hankali sosai kirki da kuma son jama'a. Yana matugar son asad da as'ad,duk sanda yazo Nigeria baya rabo da yaran.

Hannunta ta sanya ta shafi cikin nata tana mamakin ace juna biyu ne da ita, kuma har ana iya gani amma ita bata ankara ba?. Shuru ta sakeyi tana wani tunani, kwanakin nan tana danjin motsi a mararta,amma saboda ba cikin nutsuwarta take sosai ba bata ma baiwa ranta komai ba.

"Yaaya another half zaiji?" Ta yiwa kanta tambayar,sal kuma wani abu ya ratsa zuciyarta. Wanne toufeeq din?, toufeeq din da suke tafka rigima yau kusan sati guda kenan?, ko zuwanta bikinma ta taho ne da yawun maii kawai.

Kanta ta kwantar tana dubam fuskar
wayarta,tunda suka taho din ko sau daya bai nemeta ko ya kirata ba,yaransa ma a wayar fadeela suke gaisawa kamar baya qasar, bayan kuma yana nan

"Qila ma yana can suna waya da Hamdiyya" zuciyarta ta raya mata. Ido ta runtse tana jin zafin iya tuna hakan da tayi,cikin ranta tana kiran sunayen Allah hadi da tuna maganganun da ya furta mata ranar da zata taho
"Kije abinki, ban hanaki ba, kome kikayi dai daine,tunda kin gama da zuciyata,kin kuma san soyayyar da nake miki,amma wallahi na gama yarda mace tayi amfani da soyayyar da nake mata ta wahalar da rayuwata, akwai masu sona dake da yawan gaske, zan qara aure na ne, kema kiyi abinda duk kikeso" hawaye ya sauko mata tasa gefan mayafinta ta daukeshi, ashe duk abinda akewa rigimar ma yana tare da ita su duka basu sani ba.


Sanda suka isa guri ya dauki harama sosai, tace yusuf ya riqe key din motar zata kirashi idan ta tashi tafiya,saita wuce ciki. Batasan ya akayi ba tana shiga MC ya kama sunanta lokacin da aka kira ango da amarya,kwata kwata batayi niyyar hawa wajen ba,amma saboda ba yadda zatayi ta mige ta bude jakarta ta fidda rafas guda biyu na dubu daddaya sabbi qal a mige suna daukan idanu.

Liqi sosai takewa nadeeya da nadir,me ya cika gurin da kambamata da kiran sunanta saboda ganin yadda take barin kudi,farinciki da qaunar säahar ya sake lullube nadiya. Cikin sabgar bikin tun daga kamawarta har zuwa yau da za'a gargare säahar din ita ta zame mata uwa kuma babbar yaaya.

Riqota taji anyi ta baya,ta waiwaya kadan sai taga fadeela

"Abby yana motarki yana kiranki" mamaki yadan kamata ta kauda wannan ta migawa fadeela sauran kudin tace ta liga musu,ta soma sauka daga step din a nutse, idanuwa suka sake yawa a kanta MC ya fara kwarara sagon godiya wanda har ya fita daga hall din bai daina zubata ba.

Dukka hannayensa biyu ya saka yana dafe steering motar yana lumshe idanunsa hadi da furzar da iska me zafi a bakinsa. Har cikin tsakiyar zuciyarsa yakejin suya da zafin yadda bakin wani qato ke kiran sunan säahar din yana maimaitawa kamar shi va rada mata sunan, sosai yakejin zafi a zuciyarsa,yana cewa ya hanata zuwa gurin dinner din?, bama ta nadeeya ba, kowacce dinner idan ba tare suke ba, saboda shi kadai yasan abinda yake gani, Allah ya mata ajiyar wani irin kyau me sanyi da daukan hankali,irin kyan dake iya zamewa fitina ga mazaje idan ba'a hadu da mace mai kamun kai da miji mai kula ba. Shi kansa kullum ta Allah ya sake ganinta yake kamar wata sabuwa a idanunsa.

Hana jan qofar ta bude, saita sake budeta sosai tana matsawa gaba zata shiga. Fes ya bude idanunsa da suka canza launi a kanta vana kallonta

"Kata'i" ya samu kansa da furtawa,wani bacin rai yana sake lullubeshi saboda mahaukacin kyan da tayi,abu daya ya hana zuciyarsa gazawa,shigarta ta boye halittun jikinta sosai,saidai yau din tayi masa mahaukacin kyan da sai daya dauki mintuna yana dubanta kafin ya janye idonsa ya maida gaban motar yana jin kamar ya fashe da kukan takaici. Me yasa ya biye mata sukayi fada har ta samu damar yin tafiye tafiyenta ita kadai?.

Fuskarta ta hade tsam kafin ta shiga motar bakinta dauke da sallama,har yanzu tana jin zafin cewa zai qara auren da yace zaiyi. Maida murfin tayi ta rufe,bai waiwayo ba vace

"Waye ya baki izinin zuwa nan?"

"Maji ce" ta amsa masa kai tsaye tana jin zuciyarta tana mata zafi itama

"Mugullin motar ma itace tace ki bawa wani gardin ya kawoki?" Waiwayawa tayi da hanzari

"Yusuf dinne gardi?" Ta jefa masa tambayar tana ) dubansa, shima juyowa yayi yana dubanta

"(dan ba gardi bane mene?" Abinda ta gani a idonsa ya sanyata janye dubanta daga kansa ba tare da tace komai ba

"Soyayyarki da nake miki ce ta Sanya kika fara rainani ko?" Yayi mata tambayar da zafi zafinsa yana jiran amsarta.

"Wannan kwallivar da kika fita da ita wani gazami yana kiran sunanki ta mic shima duka maji dince tace kiyi?" Ya sake jefa mata tambayar. Gaba daya taji ta diririce da tarin tambayoyinsa, ta rasa wacce amsar zata bashi,sai kawai ta fashe masa da kuka

"Ba aurenka zakayi ba?, kaje kayi,nima ka barni nayi rayuwata,dama ai ba sona kakeyi ba"

"Ni dake waye baison wani? 3yrs amma ana zancan haihuwa kina dojewa,kije ki zauna abunki zan dauko wadda zata yita haifamin yara, kuma zakisan da gaske nake" daga haka ya tayar da motar ya fusgeta cikin bacin rai suka haura kwalta. Sai da yayi dai dai akan titi sannan ya sassauta gudun saboda yadda kukanta vake kassara jiki da zuciyarsa,amma ko akan fuska yaqi ya nuna hakan,bayaso ya bata wata qofa da zata gane lagonsa.

Har taci kukanta ta godewa Allah basu isa gida ba,bata fahimci yawo kadai suka dinga yi saman titi ba sai bayan da taga sun qara goma a hanyar kafin su dauki hanyar gida.

Sanda suka isa gidan ita ta fara fita a motar,sai bayan mintuna kusan goma ya rufe motar ya wuce ciki shima.

Dakinta ta wuce abinta,ta fidda kayan jikinta ta fada wanka tana ajiyar zuciyar kuka. Karo na farko data fara kuka hankalinsa bai tashi ba bai kuma saurareta ba,abinda yayi matuqar sanyaya mata jiki kenan.

Koda ta gama wankan tsaye tayi gaban madubin bandakin daure da towel tana kallon kanta, idanunta ta sauke akan cikinta,kamar yasan shi take kalla wani motsi mai garfi ya ratsa ta qasan mararta. Hannu ta saka ta dafe marar tana furta

"'Subhana man khalaqal Janeen fil arham" wani hawaye yana cika mata idanu.

Karkiyi missing last page

Zafafabiyar
"HUGUMA”


•TABARMAR KASHI_*


Book 02 Page 75

Tasbihi ta dinga yi ga ubangiji cikin ranta,komai na rayuwa yana da iyaka,hakanan duk abinda bawa yaga bai samu ba lokacinsa ne baiyi ba.

Cikin mutuwar iiki ta shirya ta haye gado, idanunta a rufe zuciyarta har yanzu babu dadi. Sunayen Allah ta dinga ambata a hankali, har wani bacci me nauyi yayi awon gaba da ita:

Tunda suka shiga gidan ya wuce sassansa ya kasa nutsuwa cikin ransa,duk shirinsa zuwa kwanciyarsa kukanta ke masa amsa kuwwa a kunnensa, saidai duk da haka baiso ta gane lagonsa, da haka ya dake ya gama shirinsa.

Har va kwanta ya dinga juyi,sam bacci ya gauracewa idanunsa, kusan minti arba'in yana a haka.
Migewa yayi ya kunna wutar dakin ya sanya slippers dinsa ya dauki wayarsa ya fito.

A nutse ya isa sassanta hancinsa na shagar wannan daddadan gamshin da yake mugun tasiri, qamshin da bai taba jin makamancin sa a wani waje ba sai a sassanta sai kuma jikinta,qamshi ne na musamman da gurinta kawai yakejin irinsa

Shuru har ya isa gofar bedroom dinta, cikin jikinsa ya dinga jin kewar yaransa, da yanzun suna zaune a nan yana fama da rigimaru da fadace fadacensu.

Dim light ne kawai a dakin, ya saki gofar ya taka
zuwa ciki. Daga gaban gadon ya tsaya,ya sanya hannu ya kunna side drawer lamp sai ya rage haskenta kadan ya jawo stool ya zauna gaban gadon.

Fes fuskarta ta bayyana cikin dan garamin hasken fitilar, innocent face din nan da yaga zallar kishinsa muraran a kwance a samanta, tuna hakan kadai ya sanya murmushi ya subuce masa,sai ya miga hannu ya shafi gefan fuskarta yana jin tausayinta kadan kadan yana ratsashi, ko yaushe qara kyau takeyi,sam shekarunta basa wani nunawa, idan kaga sa'ad da as'ad ba zaka ce itace ta haifesu ba sam.

Ya kusa awa guda zaune a wajen kafin ya miqe, a nutse ya gyara mata duvet dinta ya mayar mata da lallausan gashin ta baya ya kashe fitilar bayan yayi kissing dinta ya fito. Yana matuqar son kasancewa cikin ilkinta a daren da ya fara busa wani yanayi na sanyi sanyi,amma kuma yana son ya zama taayayyen namiji,wanda so baya rufe masa idanu ya hanashi aiwatar da abinda ya dace.

Yana shirin komawa ya kwanta kiran maji ya shigo masa waya,ya zauna sosai sannan ya daga wayar

"Tare kuka fita da maami?" Kansa yadan shafa, säahar na vawan sakashi sauka a layi a cikin idanun maji

"Eh muna gida"

"Allah ya tashemu lafiya" ta fada a taqaice, don idan da sabo ta riga ta saba,musamman da ya zamana wannan zuwan da tayi din shi ba haka yaso ba,yafiso kullum tazo ne ta koma.

"Zakuci ganiyarku tunda kuka bar yaran nan sun dawo din kenan" ta fadi a hankali.

Hilma (wata cousin dinta)ta tabe baki

"Wai nikam maji ko kishi yaronki bakyayi?, duka yarinyar nan ta gama juya masa tunani? ba zuwa ne na farko ba,duk zuwan da nakeyi abinda na karanta kamar yarinyar nan ta gama dashi, ya zama kamar wani bita zai zai, ya sanya ayiya ajiye miki yara suna yawo, ya maidata kamar alihunsa ke kina zaune?" Wayar ta saka tana duban hilma baki bude

"Kinsan akan waye kike magana? to säahar ko kamata nayi tana zubawa moha maganin mallaka a abinci saidai na tayata juyawa,saboda nayi imanin ba mallakar da zata cutar da shi zatayi masa ba,babu suruka irin tawa

Please Login or Register in order to submit comment