Reading TABARMAR KASHI 1&2 complete by SAFIYYA HUGUMA Chapter 37 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

taba jin rayuwa tayi mata dadi ba kamar wannan lokacin,saahar ce komai nata,yadda take kula da ita a gida haka a nan,harna sama da gidan,saboda a nan din a sake take fiye da can da take ganin bata da wani hurumi da can din. Batun ciwo kuwa tun randa aka kawota babushi ya tafi,gefa guda kuma kullum sai sunyi waya da nadeeya da kuma dr Jarma,wanda ya dauke nadeeyan ya maidata gidansa,yace itama ta zauna a can na wani lokaci.

*****Duk yadda yakai ga son ya dauke kai ya bar musu fadeelan yaga iya gudun ruwansu amma ya gaza. A yau yana tsaka da aiki ya kashe system din ya mige gafafunsa saman table din hadi da relaxing bayansa jikin couch din da yake kai yana lumshe idanunsa,jiya ya kira nadeeya yayi mata titsiye,ta kuma tabbatar masa fadeelan tana can. Yaso qwarai ya tattara ya zuba musu idanu,to amma zuciyarsa ta kasa dauka,gidan gaba daya shuru,babu kowa,dr din ya dauke nadeeya kamar yadda ya dauke fadeela.

Miqewa ya sakeyi yana kaiwa bakin corridor din dab da wasu flowers dake fidda sanyi me qamshi,ransa yana zafi sosai game da yarinyar. A baya yana lallaba rayuwarsa,yana yinta hankali kwance ba tare da wata baquwar fuska ta kutso musu ba.
Amma daga bayyanarta cikin watanni kacal tana neman ta zame musu qarfen gafa

"Idan kabar mata fadeela tayi winning a kanka" daga can tsakiyar zuciyarsa ake gaya masa,kamar an zaburar dashi ya dawo da baya ya dauki wayarsa yayi kiran number dr jarma.

Bugu biyu ya daga ya koma ya zauna sosai yana gaidashi cikin girmamawa. Kadaran kadaham ya amsa masa,cikin kamewar nan tasa yace

"Abba idan babu damuwa zan qarasa na dauki fadeela, kusan hutunsu nex week zai qare,ya kamata ta dawo ta shirya a nutsr kafin lokacin" gyara zamansa dr jarma yayi

"Eh to ai babu laifi.
..ummm... babu laifi,amma
idan kaje ka tano harda yarinyar khadijatu me kula da ita din kenan" hannunsa ya dunqule guri daya yana shigar da tafin hannunsa ciki

"Okay abba" ya fadi yana jin kamar dr jarma din yayi masa wata mummunar bushara

"Ka dauki saiiad kuma ku tafi tare" dr jarma ya gara fada,saboda yanason ya samu me masa monitoring abubuwa "In sha Allah" ya fada sanann ya gimtse wayar.

Iska me zafi ya furzar daga bakinsa zuciyarsa na sake soyewa da bacin rai da kuma damuwa,dr yana girmamawa al'amuranta da yawa,ya bata wani matsayi me girma,ya bata kuma yarda dari bisa dari

"Ya Allah, ya rabb,kada ka sanya yarinyar nan ta zame mana sharri cikii rayuwarmu,dukka abinda ya qulla ya Allah ga wargazashi" ya samu kansa da furtawa.

Lokaci ya duba yaga akwai sauran lokaci da zai isheshi yaje ya dawo,sai ya fada toilet ba tare da ya kira sajjad ba,nufinsa idan ya gama shiryawa sai ya kirashi,idan yace baya cikin gidan shikenan sai yayi tafiyarsa,ya tabbatar aikin Sanya Ido zaije yayi,shi kuwa sam sam bazai iya wani tsaiwa lallabata ko neman alfarma daga gareta ba.

Tsaf ya shirya cikin kamala da wani ajiyayyen kyau da kwarininsa cikin wani lallausan vadin boyel me garancin kauri,fari ne qal kamar yadda kake iya hango fara tas din singlet dinsa daga ciki,rufaffen takalmi ya saka charcoal color na kamfanin Stuart Weizmann me asalin kvau da tsada. Kansa sai dake dauke sassalkar sumar daya gada daga bangare biyu,dr girema asalin shuwa dan qasar borno,da kuma maji balarabiyar
Algeria ta kwanta luf saman kansa tana sheqi da fidda tattausan qamshi. Lafiyayyar fatarsa yake daurawa agogo,dai dai lokacin sajjad ya tura gofar ya shigo sanye da wata abaya ta maza,da alama yana cikin gidan yana hutawa,idanunsa akan TOUFEEQ da yayi wani mugun kyau

"Yanzu nake shirin kiranka ka fito zaka yimin
rakiya"

"Amma dai my man.....
.Wannan kwalliyar
zance zakaje?" Ya jefa masa tambayar cikin shakku. Kyawawan fararen idanunsa ya dago ya watsa masa,bayan ya dakata daga sanya agogon,wani abu yayi masa tsaye a wuya,kamar zaiyi magana sai ya maida bakinsa ya rufe yaci gaba da daura agogonsa,don yiwa sajjad magana ma bata bakine,kome zai fada bazai fasa jansa da magana ba,kuma gobe sai ya qara. Shi kuma a yadda yanzun yakejin zuciyarsa ko doguwar magana bayason yi. Gaban dressing table dinsa ya qarasa,ya dauki turarukansa ya fara feshe jikinsa daga wuyansa zuwa qirji,sannan ya sauya wani ya feshe sauran sassan jikinsa dashi,ya ciri key din mota guda daya daga inda yake ajiyesu yayi gaba yana fadin

"Kada ka wuce minti uku,ina parking lot" ya garasa fita ba tare daya waiwayoshi ba.
Qaramar dariya sajjad ya saki yana dan buga qafansa, already yasan da fitar,tuni Dr ya sanar masa,amma baisan da wurwuri haka zasuje ba

"Ko second daya ka bani sai fa na rakaka" yayi zancan shi daya,sai ya juya ya fita daga dakin.bava iin zai canza komai a jikinsa,don dakin,baya jin zai canza komal a jikinsa,don haka takalmi kawai ya sanya ya biyo bayanshi.
*HUGUMA*

* TABARMAR KASHI_*

Book 02 Page 04

Sosai take zaune gaban dr girema gafafunta a tanqwashe kamar zata maidasu cikinta,ko cikakken motso batayi tun zamanta a wajen

"Sati guda suka rage miki,har yanzu bazan hanaki damarki ba,ki bawa Mahmud dama,ko kuma ki gabatar da wanda kikeso ban hanaki ba,bance lallai sai mahmud ba,shikenan maganar,kina iya tafiya" kamar qafafunta ba zasu iya daukar gangar jikinta ba haka ta miqe tana hada hanya,tun jiya kanta yake mata ciwo kadan kadan tunda taji abban nata yana nemanta,ta sani dama tatsuniyar gizo ba zata wuce ta qoqi ba. Sannu sannu takai kanta daki,Allah yasa yau din afifa ta dauki fadeela sun fita yawonsu,itama meson fita guraren shan iska ne kaman afifa,sai biyu ta hadu sukayi tafiyarsu suka barta.

Ba irin saqe saqen da zuciyarta
batayi mata ba a sanda take kwance saman gadon,tana hasaso yadda yau za'a daura mata igiyar wani,wanda dukka wani nauyi nasa da haqgin aure zai rataya a wuyanta,duk wata kebantacciyar mu alama ta maaurata zata hadasu?, Saita runtse idanunta gabanta na tsananta faduwa. Bata shiryawa wannan al'amarin ba sam cikin rayuwarta,ta sake mallakawa wani namiji zuciyarta da gangar jikinta?,wani abu ne me wahala da ko cikin mafarki batason ganinsa bare a zahiri. Kuka takeson yi amma a yau din zuciyarta gaba daya ta ida qeqashewa,sai faman zafi da radadi da zuciyar keyi.

Baaba rabi ce ta shigo dauke da wayarta data wuce ta bari a falo

"Alhaji yana kiranki" tana daga kwancen ba tare data cire kanta daga cikin duvet ba ta miga hannu ta karba wayar ta kara a kunnenta

"Kina ina?" Dr girema ya tambayeta

"Ina dakina"

"To yayi,ki duba nan veranda dake baya kina da bago" wayar ta saki ta sulale cikin duvet din. Wai me yasa mahmud bazai haqura ya sakar mata mara tayi fitsari ba? yafison suvi zama mara alfanu?,zaman da ba zai qaru da ita da komai ba?,tabbas yau zata sake jaddada masa da babbar murya,don bata shirya wani rayuwar aure da kowa ba,dole idan abba yaga ya janye kuma bata kawo kowa ba ya haqura ya ayaleta. Da wannan qudurin ta sauko daga saman gadon cikin bacin rai,Adire boubou ce a jikinta,saita yafa mayafinta zalla saman kanta ba tare data nema babban mayafi ba ta zura takalmanta ta fice.

Tun bata qarasa ba jikinta taji yana bata ba mahmud bane,to amma idan ba mahmud bane waye zaizo har cikin gidansu nemanta?,tanason ganin fuskarsa amma babu dama saboda ya bada baya,sai lallausan gamshinsa daya karade ilahirin gurin har ya bazu zuwa wasu sass na gidan,da kuma cikakkiyar baqar sumarsa dake kashe ido, kasancewar bai sanya hula ba.

Tsaye tayi daga bayansa nesa kadan dashi,yaji alamun takun tafiyarta,tsaiwarta ta sanyashi waiwayowa,lokaci guda idanunsu suka gauraya cikin na juna. Baya ta dania da sauri saboda juyowar da yayi sai taga kamar ya cika wajen,kamar kuma ya sake rage tazarar dake tsakaninsu ne. Ta lumshe idanunta tana jin faduwar da gabanta yayi wanda har yanzu bugun zuciyarta bai koma dai dai ba,yayin da tasa zuciyar yaji ta danyi shacking saboda yadda lallausar sumar kanta ta fito sosai saboda janyewar da siririn mayafin kanta yayi ya koma rabin kanta,sajen dake kwance gefen kunnuwanta shima ya fito sosai,sai bagin gashin ya zama ado ga kyakkyawar farar fuskarta. Kwashe idanunsa daga kanta ya maida gefe yana jan qaramin tsaki wani bacin rai vana sake taso masa. Tayi nufin juyawa ta barshi a nan,sai taga idan tayi hakan zaiyi tsammanin tsoronsa ko shakkarsa takeyi don haka ta gyara tsaiwarta tana harde hannuwanta a girjinta,abinda ya baiwa tudun girjinta damar fita sosai ba tare da tasan hakan zata faru ba

"Lafiya kake nema na?" Tayi masa tambayar kanta tsaye da siriryar muryartan nan dake cike da tsiwa. Lokacin daya waiwayo ya kalleta sai da taji dukka wani qarfi da qafafunta ke dauke dashi yana raguwa,tsakiyar idanunta yake kalla sannan yace

"Da zaki taimaki kanki da kin nemo mayafin arziqi kin suturta jikinki,duk da naga alama bakisan darajar jikin naki ba" ya qarashe maganar yana sake dauke dubansa daga kanta.

Maganar tayi mugun sokarta,saita samu kanta da sauke dubanta ga jikinta,tunda dai tasan boubou ce a jikinta da take sakakkiyar da sai an saka mata irinta uku ma a ciki ko biyu bata matsesu ba.

"Subhanallah " ta fada can gasa muryarta da dukka ilahirin jikinta suna rawa,cikin hanzari ta saki hannayenta,wannan ne ya bawa rigar damar komawa ta sake kamar yadda take.
Qafafunta taji kamar suna neman kayar da ita,Allah yasa tana kusa da kujerun da aka aje a wajen domin hutawa,da hanzari ta nema daya ta zauna a kai,duk da yadda zuciyarta ta cika da burin takawa ta fice a gurin,to amma yadda qafafun sukayi sanyi tasan ba zasu bata hadin kai ba.

Waiwayo ya sakeyi karo na uku,saiya tako sosai ya garaso gabanta,iska ta fara debo qamshinsa dake da wani irin scent na musamman tana watsawa tsakiyar hancinta har zuwa kwanyarta. Ya rage tazarar dake tsakaninsu sosai,ya duqa yana dubanta da kyau

"Bari na baki amsarki da farko,ba lafiya bace tasa nake nemanki ba,saboda kalen dangi kin daukarwa mutane yarinya kin riqe kamar ke kika haifeta,ki fiddomin yarinyata,sanann.
..daga naira daya har
zuwa cikar burinki na kudin da kikeson mallaka ki gayamin,zan biyaki ki koma kici gaba da aikatau dinki,badon son raina ba,sal don saboda cika umarnin Dr jarma" maida idanunta tayi ta runtse da kyau,ya zageta iya yadda ransa yakeso,bayan bata aikata masa komai ba,idan ta barshi bata mayar masa ba lallai yaci nasara a kanta,to amma yayi mata wani irin kwarjini a yau wanda bai taba yi mata irinsa ba,sai ta miqe cikin dabara tana dubansa kai tsaye

"Sannu garuna,jinin mansa Musa, you are too proud mr jarma na sake maimaitawa,daga million daya har million dari idan zaka bani bazan koma aiki babazan koma ba nace bazan koma ba ana dole? yarinya kuma ka fini sanin yadda tazo gidan nan,so no need na tsaya maka bayani..
...sannan wannan jikin
da kake magana a kai, inason gaya maka idan ka saba bin matan turawa da sauran yarika na qasashe daban daban inda kake zuwa da sunan kasuwanci....to wannan ilkin da idanunka da baka yiwa shamaki suka sauka a kai,ka gaya musu yafi qarfinka har abada,har gaba da abada din,saidai kallon daga nesa" ta garasa fada tanason hana kanta sakin kukan da yake danqare a zuciyarta. Juyawa tayi zata tafi,saidai kafin tayi wani motsi yasha gabanta.
Zuciyarta ta tsinke da ganin yadda yayi dab da ita,iskar bakinsa da hancinsa dake cakude da wani kalar qamshi tana sauka akan fuskarta kai tsaye saboda qarancin kusancin dake a tsakaninsu,fararen idanun nan nasa sun kada zuwa launin ruwan goro goro

"Dan iska ne ni tatacce wanda yake bin mata daga qabilu da qasashe daban daban,amma kinsan wani abu?…....dukka virgin nake ballewa sabbi dal a leda,bana amfani da second hand ko zawarawa" a hautsine ta daga kanta tana dubansa,juriyarta tana katsewa, qyallin hawaye na ragaita cikin fararen idanunta. Bakinta ya bame bam,ta rasa wacce amsa zata bashi,cikin hakan muryar sajjad da fadeela ta soma dososu hakan kuma bai sanya shi ya matsa ba,sai itace ta zame ta zauna a gurin tana qoqarin boye ruwan hawaventa kada yaga zubarsa.

Tana jin alamun sun iso gurin,bata Ko iya waiwaya wa ta hada ido dasu ba ta mige ta fice a gurin gudu gudu sauri sauri,sajjad ya bita da kallo,sanann ya dawo da dubansa kan toufeeq dake rungume da fadeela cikin kallon tuhuma

"Me kayi mata haka?"

"Let's go" kawai ya fada yana dauke da fadeela a kafadarsa wadda keta masa surutu. Sai da taga sun shiga mota suna shirin fita a gidan sai kuma ta marairaice

"'Ina zamu abby?"

"Gida,gidan ba dadi fadeela, hutun ya isa haka ko?" Kai ta gyada a hankali, itama tayi missing nasa,to amma tanason zama da sãahar fiye da komai

"Amma ba tare da anty N zamu tafi ba? naga ko sallama bamuvi ba"

"Zata taho daga baya" ya amsa mata a taqaice,don a yanayin da yake ciki baya bugatar dogon zance. Maganganun data gaya masa sunfi komai tsaya masa a rai,shi zata kalla ta yiwa qazafin neman mata?,shi Muhammad toufeeq?, wanda ko yatsar mace da gangan bai taba rigewa ba,bai taba sanin kowacce mace ba a duniya sai matarsa ta sunnah,ita dinma duk duka lokutane gayyadaddu da zai iya lissafasu. Idanunsa dake masa zugi ya mayar ya kulle yana sauraron radadin kalamanta a tsakiyar zuciyar tasa.

Karon farko a rayuwarta da kalmar
BAZAWARA ta taba gona mata rai,tayi kuka tayi kuka sosai,kukan kuma ya hade mata da wa'adinta da takeci a gidan. Shigowar afifa biyu tana neman inda fadeela ta shiga,amma saahar din tayi banza kamae bata ji ba,tana qudundune a bargo,ta tabbatar idan tayi magana afifa zata fahimci kuka takeyi,wannan ciwon kuma na yau batason rabashi da kowa,a barta ita kadai tayi jinyar kanta da kanta,itadai ta sani a yadda yazo din nan,bazai bar gidan ba sai ya dauki diyarsa.

A shigowa ta uku kuwa taii afifa na fadi yanzu maama ta gaya mata abban fadeelan ya
Aiko a bawa maama haquri ya wuce da afifa zata qarasa hutunta a gida,idan dr ya dawo a gaya masa. Tsaki taja qasan ranta

"Badai shi ba,saidai sajjad,shi zai bada sagon" ta gayawa kanta. Maganganunsa sun mata munin da takejin ba zata iya yafe masa ba,duk da ta gaya masa masu zafin gaske,amma shi va jawo koma meye ta fada,don menene zai aibata mata jikinta? maganar ta zafafeta da yawa,don ko sanda ta miqe don yin sallar magariba sai data tsaya gaban mirror ta sake qarewa kanta kallo,ta kuma sake maimaita yanayin tsaiwar da tayin a dazun da har tasa ya fadi hakan

"Allah ya sakamin" ta fada qasa qasa tana wucewa bandaki.

Kwanakin haka ta dinga kwana tana tashi da zafi da ciwon kalamansa,wadanda ta rubutasu tas suka zauna cikin kwanyarta.
Maama da dr girema sun dauka kawai kewar fadeela ce,afifa ta gama karantar akwai wani abu,saidai har lokacin sãahar din bata fito ta gaya mata me ya hadasu ba,saboda tana in haushin yawan yin wayar data tsiro dashi a kwanakin da wani da batasan waye ba. Bata nutsu ba bare suyi ma magana don haka ta zuba mata ido tana jiran sanda zata nutsu ta fidda komai daga ranta.

********kwanaki uku da dauko fadeela,da safe yana shirin fita ya kaita gurin dr raheema tayi mata checkup,daga can ya biya da ita daya daga cikin guraren wasa na yara wai don ta warware sosal ta koma kamar da,yanason ta manta da sãahar da abinda ya danganceta.

Ta wani bangaren kuma tunanin daya kwana dashi a daren jiya ne har yanxu bai sakeshi ba. Yaya akayi maji tasa yarinyar nan har irin haka,harma take yabonta da kuma shawartarsa ya dawo sa ita? wai wanne irin abune da ita da har take iya mamayar zuciyar kowa daya danganceshi?,mutane masu kima da daraja a rayuwarsa? kamar amfani da tsafi?

"Astagfirullah" ya fada yana gama saka links din hannunsa,dai dai lokacin da akayi masa knocking.

Muryan Joshua ne,amintaccen yaron dake masa shara yake kula da tsaftar lungu da saqo na sassan bedrooms dinsa. Daga bakin qofar ya gaidashi ya sanar masa cewa BOSS ne ya shigo. Ajjiye abinda yakeyi a gaggauce ya buda qofar ya fito yana mamakin zuwan Dr iarma din a daidai wannan lokacin.

A tsaye ya sameshi, fadeela na lafe a jikinsa

"Barka da warhaka abba,bismillah ka zauna" cikin nuna girmamawa yake maganar. Wani kallo Dr jarma ya bishi dashi

"Ai bansan na haifo dan da yafi qarfin na gaya masa magana yaji ba sai yanzu" furucin da ya sanya dukka masu akin nasa dake falon yin sum sum suka fice a gurin,sun tabbatar yau boss da fada yazo akan ogan nasu

"Abba…”
"
"Dakata Muhammadu,inason na gaya maka,ka dauki yarinyar nan tun muna shaida juna ni dakai ka maidata inda ka daukota,ni dana kaita ni zan daukota da kaina,bayan ka kaita kuma ka nema alfarmar dawowar sãahar
taci gaba da kulawa da ita muddin lafiyarta kakeso,dukka rashin kirkin da kaje kayi
sajjad ya gaya min,idan ka koma din ka sake maimaita abinda ka aikata" sai ya zare fadeela
da zazzabi ya fara saukar mata yana fita a
falon.

Baisan zazzabi ya rufe yarinyar ba sai da sukazo fita,kai tsaye ya wuce asibitin da ita yasa jibril ya kira dr anwar yana gaya masa suna hanya. Sanda ya gama dubata drip yace zai saka mata,saboda tayi zazzabin a kurkusa kuma for now jikinta babu qwari. Yana daga

gefenta yanajin zuciyarsa kamar zata narke sanda Dr Anwar ke gaya masa har yanxu akwai damuwa tattare da Fadeelan.

“No more option,dukka zabi ya qare,dole ya sake maida kansa gidan ya nema alfarma ta dawo?”Statement din da zuciyarsa ta bashi kenan na karshe wanda shi kanshi yasan shine ya rage masa.

“_WOHOHO,WAYE ZAI SAUKE NE?😂,MUJE ZUWA_*

*HUGUMA*


*_TABARMAR KASHI_*


Book 02 Page 05

********Tunda suka taho a hanya yake mata hira cikin nutsuwa tare da son janye hankalinta,dukka a qoqarinsa na ganin ya kafa kansa cikin zuciyarta yadda ya kamata.
Kaf tsahon hirar da yake mata tun daga thairaphy beaty saloon din har yanzu da suke gab da shiga unguwar su bata amsa masa sau hudu ba. Ta cika tayi fam,tasan tabbas afifa ta gayawa mahmud inda taje. Tun jiya sukayi zata rakata ta wanke kanta,ayi mata gyaran fuska a kuma saka mata jan lalle iya yatsun qafa dana hannu,tayita jiran afifan bata dawo ba,daga qarshe sukayi waya tace tana da patient data kusa haihuwa,so saidai taje,ta sameta acan saita daukota su dawo tare. Maimakon taga afifa sai taga mahmud,hakanan don babu yadda zatayi ta shiga motar,saboda idanu sunyi yawa a kanta sanda take fitowa,dole ta shiga din ya rufe ya jasu,ranshi fari qal,yana jin dadin yadda a yau ta aminta ta yarda ya dawo da ita gida.

Zata iya cewa tsahon rayuwarta,tun Karin ma aurenta na farko yaushe ne ta shiga motar wani d'a namiji ba banda yayunta maza,don haka ko a yanzun jinta take a takure qwarai.

Taso ya ajjiyeta daga gofar gida amma sai ya giya

"Wannan ladan dole na garasashi" ya fadi yana murmushi,da kansa ya buda mata qofar ta fito ya mayar ya rufe

"Yanzu sai yaushe kenan ranki ya dade?"

"Zan duba" kawai tace dashi tana yin gaba.
Kansa ya girgiza,shi sam abinda takeyi bai dameta ba,yasan with time zata daina komai idan ta shiga gidansa,ya soma amfani da kyautatawarsa a kanta wajen kafa kansa.

"Madam,oga muhyiddeen yace ki sameshi a dakin baqi idan kin shigo" cewar jamilu yana dan rusunawa. Duban jamilun tayi,kamar zatayi magana sai kuma kawai ta sauya akalarta zuwa can din,wataqila vana wani aiki ne da yasa ya kebe a can,tunda time to time yana yin hakan,sai ya baro gidansa vazo nan yayi aikinsa a nutse,saboda su khalipha basa barinsa.

Har zata daga curtains din masu kauri da girma sai ta dakata,saboda wani bagon qamshi da ya shiga hancinta,cikin iiki da zuciyarta takejin kamar tasan qamshin,amma ta kasa banbancewa. Ta kauda tunanin ta sanya hannu ta budesu.

Shine yake fuskantar gofa,wannan yasa tana budewar dashi suka fara hada idanu,kwantattun sexy eyes dinsa da yau suke cikin wani irin nutsuwa wadda damuwa kadan ta cakuda dasu. A tare dukkansu suka janye idanun nasu,kowa yana jin zafin dan uwansa a qasan ransa. Itakam sãahar sai da taja siririn tsaki qasan ranta,cikin zuciyarta tana tunanin me kuma yazo yi a gidan nasu?,saboda ita dai ta riga ta yiwa kowanne zuwa nasa gidansu fassara da zuwan da baida alkhairi.

"Yauwa kin dawo?,qaraso ciki kinyi bago" ya muhyiddeen ya fada. Cikin nutsuwa take takowa da wani irin rashin sakewa da batasan meye dalilinsa ba,saidai tanajin kamar ido ne a kanta. Tabbas batayi qarya ba,can gasa gasa toufeeq yake qare mata kallo,yanason ya gano meye ne tafi kowa dashi har Dr da maii suke iya magana da bada umarni a kanta? saidai idanunsa basu gano masa komai ba face zara zaran yatsun gafafunta da suka sha jan lalle da yayi radau,suka fito fes gwanin sha'awa.
Daga bisani dole ya zare idanun nasa yana sakin tsakin da baisan anji ba ko ba'a ji ba.

Yaa muhyiddeen din ta gaisar,can qasan ranta tana juya ta yadda zata gaida toufeea din don batajin zata iya gaidashi sam sam.
Kallon da yaa muhyi yayi mata yasa don babu yadda zatayi ta waiwaya sashensa ba tare data dubeshi ba tace

"'Barka da yamma"

"'Barka" ya furta da gasaitacciyar muryarsa,idanunsa nakan wayarsa da yake qoqarin sanyata a flight mode.
"Sun kawo drinks sun wuce,kiyi serving nasa,idan kin gama ki jirayeni wajen maama" yawu ta hadiye sannan ta gyada kaitana qyashin yadda zata yiwa wannan mutumin hidima,wanda baisan mutunci da darajar kowa ba. Dole ta zamo ta sauko qasa daga saman lallausan sofa din,dai dai sanda ta fara serving din nasa yaa muhyi ya juya ya fice daga falon.

Mutum ne shi mai kaifin karantar mode din mutum,koda bakayi magana da bakinka ba,yana da saurin fahimtar yanayinka koda ta cikin qwayar idanu ne. Tsaf ya fahimci akan dole take zuba masa komai,saboda mugunta kuma sai daya cika kome taf har bakin cup,ta mige ta koma kan kujerar tayi zamanta ba tare da tavi masa tayin sha ba.

Ya fahimci Allah Allah take ya fadi uzurinsa ya tafi,hakane kam a zuciyarta,don ji takeyi kamar ta zura da gudu tabar dakin. Yana sane shi kuma yaqi cewa komai,yanata danna wayarsa ba tare da yace ta tafas ba,yavin da ita kuma keta murza yatsuntsa da sukasha lalle,ranta yanata quna,hancinta yanata zugo mata qamshinsa yana watsa wani irin abu ilahirin jikinta ta kowanne sashe. Kamar ta yayyaba masa magana kan yadda ya barta a zaune haka taji,saidai ta kanne ta cije,don batason yaci gaba da sanin abinda yake bata mata rai.

Sai daya mula don kansa,yanata tauna yadda yau a karon farko zai furtawa wata diya mace kalmar ban haquri,bayan maji dinsa da hajiya qarama. Sai daya sauke gafafunsa dake harde ya gyara zamansa yana zuba mata narkakkun idanunsa. Ba abinda yake hangowa saman fuskarta sai tsiwa fal,shi kansa bai san me yasa duk sanda zai dubeta ba yakejin kallon kamar ya bambanta da sauran kallon da yakewa kowa.
Kalmar haqurin tana masa maqaqi a wuya,musamman idan ya tuna da kalmar data jefeshi dashi shima. To amma sajjad ya gaya masa tun a hanya,mai nema baya fushi,kuma zaiyi komai ne for the sake of fadeela,indai da gaske yana son diyar tasa.

"I hope zaki manta da komaiina neman alfarmar ki dawo kici gaba da zama da angel" yayi maganar da wani irin softness.

har yanzu izzarsa tana nan cikin maganganunsa.

Nata idanun ta zube masa tana gyara zamanta

"Ba komai kudi ke iya bayarwa,kamar yadda ba komai ne darajarsa take hawa mizani daya dana kudi ba. Komai ya wuce a gurina saboda fadeela da nadeeya,but am sorry.....bazan iya dawowa gidanka ba,infact ma am getting married in the next month" abinda ta fada kenan ta miqe tsam tana daukar hand bag dinta.

Wani rudu ne ya shigeshi,a hankali yaji zuciyarsa ta motsa da wani irin qarfi ta matse guri daya

"Aure zatayi?" Ya tambayi kansa,kamar ba yanzun nan kunnuwansa suka jiye masa abinda tace ba

"Idan tayi aure ta tafi,yaya makomar rayuwar fadeela?" Muhimmiyar tambayar data tilasta masa furta abinda ko a mafarki bai taba zaton zai furta ga kowacce diva mace a doron duniya ba

"Will you marry me?". Wannan kalmar idan ta kirata da saukar ajali lokacin mutuwar fuju'a a kunnuwanta to batayi kuskure ba. Kalmar data ji girmanta ya wuce girman dutsen dala a kanta. Kunnuwanta suka bada wani shuuu,sai ta kasa daga qafafunta daga gurin,kamar an dasata

"Will you marry me?" Ya sake maimaita maimaitawa a karo na biyu. Wannan karon wata faduwar gaba da sautinta yakai har ga kunnuwanta taji,numfashinta yadan so ya fara fita da sauri amma saita yi qogarin saitashi. A nutse ta waiwayo tana dubansa kai tsaye

"Absolutely no" ta zare idanun nata daga kansa tana qoqarin ci gaba da tafiya. Saidai taku biyu kacal tayi ya cimmata,ta fahimci hakanne ta hanyar qamshin turarensa da ya mamayeta,taja baya da sauri tana rabewa gefe,saboda yadda yayi

Please Login or Register in order to submit comment