Reading TABARMAR KASHI 1&2 complete by SAFIYYA HUGUMA Chapter 57 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

va bayvana baro baro saman fuskarsa ya zubawa maji ido, majin da lokaci guda tunaninta ya juye, tsananin kidima da rudewa da jin yadda fauziyya ta juyar da abin kanta lokaci guda ya gigitata

"Shifa?,kece shifa da kanki?, bazan musa zancan fauziyya ba,saboda gashi na gani da idanuna" sai ya watsa mata takardun hannunsa saman fuskarta

"Sati uku cur na fuskanci ana dauke takardun kadarorina,sama da qasa na dinga nemansu daya bayan daya ina rasawa,sai gasu guda shidan cif a dakinki, ashe kin shirya kasheni ne ki mallaki abinda na tara ko?" Wani irin kukan baginciki ne ya balle mata

"Wallahi wallahi bani na daukar maka ba bansan dasu ba" ta fada tana jin ranta yana daci,sharrin kisa da sata duka lokaci guda?.

"Idan bake bace nine kenan nakaisu dakin
naki?,bayanke ki gayamin wanda yake shiga dakina"

"Babu" ta amsa masa kai tsaye,saboda tasan babu din shine amsar

"Gwara da baki wahalar da shari'a ba,kije na sawwaqe miki na gaji da yadda gidana yaqi zama lafiya sanadiyyarki,na sakeki saki daya"

"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, allahumma aiirni fi musibati, wa'akhlifni khairan minha" ta furta da madaukakin sauti dake gauraye da sautin kuka, idanunta suna sauka akan fuskokin nadeeya da toufeeq wadanda suke tsaye daga bakin qofa suna kallonta, daga shi har nadeeya din idanunsu cike yake da hawaye,sai taga uban yaja hannuwansu ya fice dasu ya barsu daga ita sai fauziyya.

Dariya sosai ta fara qyaqyatawa wanda hakan ya tabbatar mata itace ta sauyawa takardun guri daga dakin Mahmud din zuwa nata dakin

"Idan asiri baici ba,ai ita kissa bata da magani" ta furta kai tsaye

"Fauziyya" maji dake hawaye ta kirayi sunanta

"Alfarmar sayyadina rasulillahi S A W,yadda kika birkitamin rayuwar aure na,kika hanamin jin dadin gidan mijina,ina rogar ubangijin sammai da gassai ya hana miki jin dadin aure har gaban abada" daga haka batà qara ba ta wuce dakinta.

A daren taso tabar gidan,saidai kuma abubuwa biyu suka hanata,na farko tunanin yadda zata hada kudin ticket din da zai maidata Algeria,sauqinta daya babban yayanta yayi mata visa ba dadewa ta shekara biyar, kuma shekara biyu kacal taci a ciki,abu na biyu kuma tana tsaka da hada kayanta jini ya balle mata, koda ta isa bandaki sai ta iske bari ne tayi,barin dan tayin cikin da jini ne zalla,ko ubansa baisan dashi ba, dole ta haqura ta kwana tana bigin kanta da jinin barin da take zubarwa,cikin taimako da dafawar Allah zuwa asubah ya tsagaita.

Kafin gari ya waye ta gama shirya komai nata dana yaran,a daki suka iskota ta kamasu ta shiryasu tsaf tana shirvasun toufeeg yace

"Jiya abba baiyi bacci ba maji,kije ki bashi magani"

"Zaiyi toufeeq" abinda ta iya ce masa kenan.
Ga kaya ga murdawar mara ga yara haka ta ratso
falon gidan zata fice a gidan

"Ina zakijemin da yara?" Ta tsinci muryar mahmud
JARMA yana fadi. Kafin ta waiwayo ya iso gabanta,yasa hannu ya zame hannun toufeeq da nadeeya

"Ba dasu kika zo ba ina ke ina tafiyar mana da zuri'a?"
Fauziyya dake tsaye a gefe ta fada, ranta fes duniya yau sabuwa a gareta. Gaban fauziyya ya isa da yaran

"Na mallaka miki su halak malak"

"Na gode yaaya,na tabbatar ko ranar qiyama ummee zatayi alfahari da kulawar da ka bani" tayi maganar tana goge hawayen munafurci. Cikin dakiya da zallar jarumta maji ta tako gaban yaran, ta dora hannuwanta duka biyun saman kawunansu ta furta

"U'izukuma bi kalimatillahit tammat min kulli shaidanin hammah wamin kulli ainin lammah" ta maimaita sau uku sannan tace

"Ya ubangijin sama da gasa,ina neman alfarma daga gareka cikin karamci da adalcinka tare da isar ga bugatar wanda aka zalunta,wannan addu'ar da nayi musu koda ta zama ta qarshe, koda nisan dake tsakanin uwa da ‘ya'vanta ya wanzu a tsakaninmu kasa addu'ar tayita bibivarsu har garshen rayuwarsu,na damqa amanarsu a hannunka ya mijibancin al'amarin bayinsa" daga haka ta miqe,ta kuma kalli idanun fauziyya

"Zan sake miki addu'a a Karo na biyu kafin na wuce, yadda kika shiga tsakanina da farincikina,ina roqon
Allah ya gimtse naki farincikin a sanda baki taba zata ko kawowa ba, addu'ar da nayi miki rannan,da wadda nayi miki yanzu kadai sun wadatar, ba zan sake kai qararki gaban Allah ba,sai kuma jiran sakamako".

Bata tabajin furucin da ya shiga jikinta yayi mugun kassarata ba irin wannan,amma sam batason majin taga kamar ta karaya,wadan nan addu'o'i biyu suka kasa barin ranta,suka kuma sanyata qudurar anivar kassara duk wani abun da zai zamewa maji farinciki a rayuwarta daga nan har zuwa garshen numfashi,wannan ne kuma ya sanya FADEELA a target na hajiya garama tun ba'a san da wanzuwar mahaifiyarta a duniya ba bare ita kanta.

*HUGUMA*


*_TABARMAR KASHI_*

Book 02 Page 44

Karon farko ta isa gidan aminiyar dake gaunarta dason qawancensu,ta shiga baqinciki da tashin hankali itama tayita roqon maji ta zauna dasu tace a'ah, tabar nigeria kenan har abada daga lokaci irin wannan, alfarma daya take nema tayi mata magana a landline phone dinsu da yayanta ya siya mata ticket na komawa

"Allah ya sawwage ace har saikin nemi yanuwanki" a aljihunta ta siya mata ticket din, kwana biyu kacal maji ta qara ta koma Algeria,wanda tunda tabar nigeria bata gara waiwayarta ba sai a wannan lokacin.
Kawa ga maji ita taci gaba da bibiyar al 'amarin su toufeeq kafin fauziyya ta ganota ta hanata shigowa gidan da ganinsu gaba daya. Cikin ikon Allah ta shiga neman mai aiki saboda a lokacin ta soma bungasa kasuwancinta da tafiye tafiye,ta kuma qulla aure tsakanin yayanta da daya daga cikin qawayenta,auren da sukayi yarjejeniya tsakaninta da qawarta ta.

tata. Ruqayya qawar maji ita tayi wuf ta aika da baaba ramatu,saboda yadda da amintar da tayi da ita,ta kuma tabbatar zata bawa yaran dukkan wata kulawa tare da kula da lamarinsu. A hankali baaba ramatu ta fuskanci yadda fauziyya ta kawar da hankalin yaran gaba daya daga ganin kima da jin maganar kowa,duk abinda ta shimfida ya zauna daram. Da farko maji na kiransu,idan aka kwana bivu bata kira ba zasu nemi babansu ya kira musu ita suyi magana sannu sannu sai gashi gaba daya daga yaran har babansun sun soma mantawa da wata mai suna MAJI sam cikin gidan,duk wata kewa da qulafucinta da sukeyi ta sanya anzareshi tsaf daga ransu,sai abinda tace sai abinda takeso.

Tun ba'a ie ko ina ba ta raba auren maryam qawarta da dr jarma,ta sake kutun kutun ta aura masa murja itama bayan wasu shekaru ta raba auren da salon kissa da kuma asiri. Cikin shakarun sai data aura masa mata hudu tana sanyawa yana sakinsu, mace ta garshe da ta aura masa mansura. Mansura itace babbar aminiya cikin gawaventa, kuma ta kashe aurenta ne don kawai tazo fauziyya ta aura mata Dr jarma,ta fito daga gidan baban labiba ta baro yara hudu labiba auta ta biyar,can qasan zuciyar mansura itama danqare fal da buri da nata qudurin na mallakar Dr jarma da uban dukiyar da ya fara tarawa a dare daya.

Mafarin rashin gaunar da toufeeq yake yiwa mansura din ya samo asali ne da zuwansa gidan wata rana,a lokacin duka duka shekararsa sha biyar ya samu tana yiwa Dr jarma barbaden magani, wanda kusan maganin nata ne data fauziyya,yawanci mansura ita ke sabuntawa fauziyya aikinta,saboda komai yana tafiya mata dai dai,rayuwa tana mata yadda takeso,bata bugatar Dr jarma ya koma Mahmud dinsa, ta tabbatar inda har yanzu maji na cikin rayuwarsa babu lallai takai matsayin da take kai yanzu a rayuwarta.

Komai yana iskar maji ta hanyar ruqayya,co sau daya bata taba sassautawa wajen yiwa yaranta addu'a ba,tasha hana idanunta bacci saboda sallah,ta sha hana cikinta abinci saboda azumi, duka tana yine saboda nemawa yaranta kariya,a kullum idan ta kwanta babu abinda ke mata yawo a kunne sai kukan nadeeya dana toufeeq, wani irin kuka me karyar da zuciyar me imani suna kiran sunanta,kukansu na qarshe da taji bata kuma sake ji ba saidai tayi hasashe.

Shekararta biyar da rabuwa da DR JARMA sannan tayi wani auren,saidai auren duka duka shekara biyar mijin ya rasu, bata kuma sake sha'awar sake wani auren ba,ko wancan matsantawa ce ta yayanta guda daya daya rage, shekara biyu kadai da yin auren kuma ya rasu.

Sau biyar hajiya qarama na yin aure bayan aurenta na fari da ya'aqoub, amma auren baya wani lasting sal ta fahimci ba don komai suke aurenta ba sai don abinda ta tara,saita sallami mutum tunda yawanci auren dauki sandarka ne. Allah ya jarabceta da sha'awar auren amma haka ta tattara ta haqura saboda tsoron kada abinda ta Jima tana yaqi akan tarashi ya salwanta. A karo na shidda ne taga DR GIREMA(mahaifin säahar), a lokacin suna abota sosai da Dr jarma kafin rayuwa ta cilla kowa wani sashe na daban. Ta mutu sosai akan dan mutanen borno shuwa arab na asali dake da kyau na burgewa,irin kyan da take ganin yayi dai dai da nata kyan. Ta soma shiga da fita akan a jawo mata hankalinsa,cikin ikon Allah duk inda take tunanin nasara babu ita,a hankali ta fahimci matarsa tsayayya ce,ta tsayawa kanta da mijinta da addu'o'in tsari,sannan gwanace kuma qwararriyar mace wadda ta amsa sunanta wajen iya kula da miji tare da dasa soyayyarta me zafi a zuciyarsa,don duk inda ka zauna dashi zama ya danyi tsaho sai yayi maka zancan AMINATOUnsa. Tayi barnar kudi akan dr girema kamar ba gobe amma kusan a banza za'a ce,don babu wani ci gaba ko nasara data samu,tana ji tana gani haka ta haqura da shi, don ta fahimci kallon ganwa kawai yakeyi mata, daga gaisuwa kuma babu abinda yake qara shiga tsakaninsu.

Abinda maji ta mallaka daga gadon iyayenta da tumunin takabarta data samu shi ya shiga kasuwanci dashi babu kama hannun yaro. Family dinsu babban family ne kuma sananne da suke da mutane masu tarin muqamai kala daban daban,wannan yasa bata wani sha wahala ba kasuwancinta ya samu karbuwa daga gurin matan manyan qasar ta Algeria, a hankali kuma sai ya fadada zuwa qasashen qetare maqwabta,harma da
Nigeria din kanta, amma bata taba yarda ta saka qafarta Nigeria ba saidai aike, duk da cewa Zuciyarta da gangar jikinta ko da yaushe tana kan yaranta,tana kuma bibiye da dukkan wata nasara ko faduwa tasu.

Taso zuwa auren toufeeq na farko amma hajiya qarama ta aike mata da saqon basa gayyatarta. A sanda sagon ya isketa tana asibiti bata da lafiya,saita saki murmushi kawai tana girgiza kai. Ta sani tabbas addu'a babu abinda ya kaita kaif,ta jima ta fahimtar wata muguwar shakkarta da tsoronta ya shigi hajiya qarama,gamuwarsu kuma shine abu na qarshe da bataso. Ciwonta shi ya hanata zuwa bawai barazanar banza da wofi ta hajiy qarama ba,ta barwa ranta akwai lokaci na gaba,akwai kuma dama ta gaba,don tana ji a jikinta dama lokaci yayi da zata tabbatarwa da fauziyya yaranta data bar mata,ta bar mata su raino ne kawai,ta gama yanzun kuma zata karbi ajiyarta.

Sanda taji matar toufeeq ta haihu sai taji kowacce soyayya tata ta tattara akan FADEELA, tun tana jaririyarta har kawo shekarun da take kai a yanzu,sai taji tamkar itace ta yiwa nadeeya qanwa. Wata iriyar soyayya ce da bata boyuwa sam sam,wannan ya sanya hajiya qarama karkade makaman yaqinta data binne,ta kuma tabbatarwa kanta lokaci yayi da zata dawwamar da hajiya qarama cikin toro firgici da kuma zulumi

_wannan kenan_*

_sauran warwarar lamuran suna nan a gaba kadan zakuji komai filla filla_*

"sauran duka abinda fauziyya ta aikatawa rayuwata data su moha wanda idanu basa iya gani ita daya ta sani,sai kuma ubangijin sama da qasa,wanda idan yaso bayyana komai zai bayyana shi ba tare da wani jinkiri ba,wannan itace fauziyya,wanann itace hajiya qarama, kina tunanin akwai yanayin da zaizo wanda zai sanya na manta wacece ita?,na baki goyon baya dari bisa dari ki fita da fadeela,ba'asan abinda Allah ya hukunta ba,zama ba shine mafita ba tunda har akwai chance na yiwuwar warkewarta" gaba daya jikin säahar ya gama yin sanyi,duk gwiwarta ta mutu,cikin ranta tsoron Allah yana sake kamata,ashe ire irensu adam da momee suna da yawa a duniya? ‚ashe har yanzu mutane basa ji a jikinsu bisa yarda da imanin akwai ranar sakamako?,a yanzun bata ko shakka ko kokwanto,hajiya qarama zata iya aikata komai ma,sannan qarfinta ya karkata dari bisa dari akan sanya hannunta da ta'azzarar ciwon fadeela,ta sake imanin akwai wata boyayyar manufa tata data sanya take matsa qaimi akan duk wanda yace zaiyi maganar a yiwa fadeela aiki,ita ta cusa toro da fargabar surgery na fadeela a zuciyar mahaifinta,hakan na nufin shi dinma yana kan wani TARKO nata ne kenan ba tare da ya sani ba?. A karon farko wani tausayinsa ya sauka ya lullube zuciyarta, idanunta da suketa zub da qwalla
suka saka tara sabon hawaye tana jin radadinsu dikin
idanunta,da gasken gaske maji taga rayuwa,ta hadiyi
abinda ba kowacce maca ce zata iya hadiyarsa ba
"Ki ajjiyemin account number dinki, zan saka miki duk iya
adadin abinda zaku kashe da wanda zaku buqata,wacceqasa ce?"

"Germany ne maji,bonn, amma don Allah mai, inason nayi wannan aikin da kudina ne, ko da duk abinda nake dashi zai qare, ina kwadayin ladan" kai ta gyada

"Bansan wanne lokaci zaya daukeni kafin na samu visa
din can ba,tunda ban taba shiga ba,amma zanyi iyakar
bakin goqari na,ina matuqar alfahari da wanzuwarki cikin ahalina khadijatu,banzan kuma da kalar bakin da zan miki godiya ba".

Hirarsu da maji a ranar ta maqale mata a wuya,ta yini
tana juya abinda suka tattauna da ita. Yau gaba daya sai ta kasa fita a sashen,saidai duk wani motsi idan akayi cikin gidan yana kan kunnenta,sai ta dinga jin taron data baiwa fadeela a baya ma kamar yayi kadan, kamar hajiya qarama zata iya yin wani motsi don ta cutar da fadeela,don haka a idanunta da kunnuwanta motarsu ta shigo gidan,cikin motar toufeeq jarma wanda a yanzun ya zamana vadda suke fita tare tare suke dawowa.

Labulen ta sauke tana sakin ajiyar zuciya sanda ta tabbatar sune tanason taje ta tari fadeelan amman kuma tasan suna tare ne da toufeeq. Har yanzu wani matsanancin kunya ce take lullubeta idan ta tuna abubuwan da suka faru a dazun,wuni tayi abin yana dawo mata tana mamakin kanta na vadda ya sanyata ta saki layi haka lokaci daya, sai ta juya a nutse ta koma kitchen din,ranar farko da zata girka wani cikakken abinci a ciki.

Yadda jilkinta vake a sanyaye yau tasan ba lallai ta gama abinci da wuri don haka tun bata dora ba ta fara yiwa fadeela pancakes da smoothie ta ajiye mata,sai fura data dama daban Incase ko batason smoothie din.

Tana aikin yayyanka vegetables amma hankalinta yana cikin gidan. Tana jin lokacin da suka bude gofar suka shigo,fadeela ta rada mata kira da kyau. Tanason ta amsa amma idan ta tuna da toufeeq na gurin sai ta kasa. Har zuwa sanda fadeela ta kalleshi

"Abby,ko anty N na wajen baaba ramatu?" Kafada ya maqale yana murmushi tare da dan tabe baki

"Muje na rakaki ki gani" ya fadi can qasan ransa yana jin zumudin ganinta.

Sallamar yarinyar cikin kitchen din ya sanyata sakin abinda takeyi tana amsawa ba tare data juyo ba

"Anty,yau bakiyi welcoming dina ba" fadeelan ta fada tana togewa daga bakin qofar gami da qin qarasowa ciki.

Qaramin murmushi ya saki yana jin farinciki na saukar masa a zuciyar ,kamar fadeela tasan muradinsa a yanzun na kallon qwayar idanun säahar din,wanda ya tabbatar ko zai narke a banza ba zata bari ya gani ba.
Gyara tsaiwarsa yayi sosai yana sake zube idanunsa a kanta,tana sanye da high tummy skirt na yadin chiffon wanda aka yiwa qananun tattara ainun,hakan ya santa qugunta fita das a jikina,ya kuma fitar da shape dinta.
Rigar jikinta ta plain chiffon din ce wadda ta dace da skirt din jikinta, gashinta na nannade a boye cikin dankwalin kayan. Idanunsa ya lumshe yana fitar da iska tun daga hunhunsa,hancinsa na dawo masa da sassanyan qamshin gashinta wanda yake jinsa kamar yanzun yake nutsa kansa cikin sumar sa. Tana takowa idanunsa nakan lips dinta,baya gajiya dasu sam, akwai sirri me yawa da wani irin softness samansu

"'Faddee rigima" ta furta a hankali, abinda ya bawa lips din nata damar motsawa da juyawa a hankali, wannan ya sanyashi sake fidda wata iska me nauyi ta hancinsa.

Duqawa tayi tana karbar lunch bag da school bag din
fadeelan

"Sannu da zuwa" ta fadi ba tare data dubi sashen da
yake ba. Banza yayi da ita kamar baiji ba

"Sannu da zuwa" ta sake fada still da yanayin dazu,sai a sannan ya saki hannayensa yana dan waiwayawa,kamar me neman da wanda take magana

"Da wa kike?" Yayi mata tambayar da ta sanyata daga
kanta zuwa gareshi cikin mamaki, don dai ita bataga
kowa a kitchen din ba saishi da ita sai kuma fadeela

"My angel, karba kayanki ki qarasa dasu daki,oya" ya fadi yana duban fadeelan. Bata musa ba ta miga hannu ta karba komai nata da sãahar din ta cire, ta kuma fella da gudu ta fice ta barsu a tsaye.


Da kallo säahar tab fadeela duk data qule, gabanta na
faduwa kadan kadan,tana tsoron kada ya zamana wata muguntar ya sake hada mata,har yanzu bata warke daga mikin jiya ba. Bata gama tunanin ba kuwa tattausan gamshinsa ya ya soma ratsata qofofin hancinsa,ta daga idanunta ta kalleshi, karon farko da yaga karaya da tsoro a cikinsu. Taku ta fara yi da baya yana biye da ita,cikin zafin nama ya sanya hannu ya rigo qugunta ya tsaidasu cak shi da ita tsakiyar kitchen din yana jifanta da wani shu'umin kallo da narkakkun idanunsa
*HUGUMA*

*_TABARMAR KASHI*

Book 02Page 45

"Na dawo daga office a gajiye, ina jin yunwa,inaso nayi wanka,amma duk baki lura ba, sai kawai ki bini da wata sannu da zuwanki me kama da bada umarni umarni?" Ya qarashe maganar yana lashe lips dinsa,hankalinsa na fusga akan nata lips din zuwa qirjinta da yaketa son rudar masa da tunani, rigar jikinta din doguwace sakakkiya,amma duk da haka akwai wata tattara a qirjinta data sake yiwa halittunta mazauni da kyau. Sake fincikota yayi sosai zuwa cikin jikinsa yana ci gaba da ifanta da wani narkakken kallo cikin qwayar idonsa

"You know what?" Ya fada yana hadiye yawu,ba tare da ya jira amsarta ba ya bata amsa yana sake jawota cikin jikinsa da kyau

"I swear i straight up forget my name for a second duk
sanda na kalli wadannan qwayar idanun" ya qarasa fada yana sanya yatsarsa tare da yi mata yawo dasu softly saman idanun nata, abinda ya tilasta mata lumshesu, tana jin tsigar jikinta na neman fara tashi

"Hold me so close for some minutes your breath already become my oxygen" ya fada yana kama hannuwanta ya kuma sanyata ta zagaye bayansa da su,sannan ya kama fuskarta a tausashe ya rige suna musayar numfashi me dumi dake fita daga hancin kowannensu.

Qafafunta ne suka fara rawa, ta fara gogarin zamewa,bai hanata ba ya barta ta janye,saidai bai barta ta matsa duka daga jikinsa ba ya rige hannunta

"Wannan shine kalan gaisuwar da nakeso bayan na dawo a office,zan shiga nayi wanka, kafin na fito please i want something to eat....am starving" tuntuni ta juya masa baya,a haka ta gyada masa kai tana addu'ar ya fita a kitchen din, tana tunanin zai fitanne tunda ya gama abinda ya kawoshi saita tsinci muryarsa cikin karyar da murva a shagwabe

"Please,my lips are so lonely one kiss please" har cikin bargonta taji tasirin muryar tasa. Qarasa rudata yayi,har spoon din hannunta na faduwa qasa,ya tsugunna ya dauka yana miga mata

"Matsiyaciya" ya fadi yana sakin wani tattausan murmushi hadi da soma takawa a nutse yana fita a kitchen din.

Bayan ta tabbatar ya fita din sai data samu guri ta zauna saboda ta daidaita bugun zuciyarta,idonta ta lumshe tana mamakin yadda yake yawan sanyata faduwar gaba da rudewa, abinda a baya Sam ba dabi'arta bane?.

Komai ta zubawa fadeelan har furar ma tace tanaso, sanann ta dawo ta shirya masa nasa saman wani kyakkyawan tray bisa tsari,sai taji kaman ta aikata fadeelan takai masa,amma kuma tunda ya fuskanci ya zama dan garari me neman dalili galilan ya moreta son ranshi,sai ta haqura ta zura hijabinta ta dauki tray din ta wuce dakin nasa tabar fadeela na kallo a parlor.

A nutse ta bude bedroom din ta shiga gamshin da yake fitarwa da sanyi suka buso mata,first night dinta da tayi da ranar Allah shi ya fara dawo mata fes a kai,ta dauke kai daga kan bed din ta soma takawa da gaggawa,tanason ajiye masa ta fice kafin yakai ga fitowa daga toilet din da take jiyo qarar ruwa. Har ta kusa isa qofar fita ya bude qofar bandakin ya fito

"Wait mana" ya furta yana dubanta, kamar ta zura da gudu haka taja ta tsaya sannan ta waiwayo da nufin ta samu gurin zama. Kadan ya rage bata fadi ba saboda tsabar rudewa,murdadden jikin nan nasa dake dauke da curarrun muscle ya bayyana muraran, gargasar dake lullube da jikinsa da damatsensa da suke fadin yadda mamallakinsu ke yawan daga qarfe, ba komai a jikinsa sai wani gajeran towel da ko cinyarsa bai gama rufewa ba don tabbas idan yace zaya zauna ne to kana iya hangen jikinsa sosai.

"Come and serve me masallaci zaki shiga ne haka na ganki da hijabi?" Ya fada cikin gatse, don ba haka yaso ganinta ba,yaso ya morewa kallonta ne sosai. Bata tankasa ba ta dawo gaban tray din

"Stop madam,ki cire wanann hijab din kada kiyimin gazanta" magana ce fal bakinta takeson maida masa, amma kuma tana tsoron kada allura ya tono garma,abisa dole ta hadiye ta zare hijabin yadda ya bugata ta fara saving nasa pancake

"Furar is enough" ya fada yana duba wayarsa da ya samu da tarin miscalls

Gida biyu hankalinsa ya rabu,rabi yana kan wayarsa rabi kuma tana ta fusgar hankalin nasa,so samu ace yanzun tana jikinsa yana shan duminta bai taba tunanin akwai ranar da wata mace zata dinga wasa da hankalinsa haka ba.

A nutse ta mige ta isa gareshi, dai dai sanda ya daga kiran dava shigo wayar tasa, miqa masa cup din tayi,ya miga hannu da zummar karba, kawai sai ya hade hannuwansu guri daya ya kuma jawota a tausashe yayi mata masauki saman cinvarsa tare da manneta da qirjinsa ya riqeta tsam. Ko motsi hanata yayi,cikin tattausar muryarsa din nan da yau tayi kusanci sosai da kunnenta taii ya ambaci sunan maji yana kuma gaidata.

A galla ya kusa minti talatin suna magana da majin,ita kuma tana zaune zaman cinyarsa,wata muguwar kunya na dawainiya da ita,duk sanda ta motsa zai zake maidata jikinsa va manneta gam, har ya kammala wayar sukayi sallama,ya aje wayar gefansa sannan ya tattara hankalinsa a kanta. Tallafo hannayensu dake riqe da cup din yayi ya matso dashi saitin bakinsa,sannan ya kamo daya hannun nata ya aza saman cokalin dake cikin furar, murvarsa gasa gasa cakude da alamun damuwa yace

"Oya...feed me please" ya furta kamar wanda ke tsoron wani ya jishi. Shi ya taimakawa hannun nata ta hanyar rigeshi, yana tayashi debowa tare kaiwa bakinsa. Wani irin shiru ya ratsa tsakaninsu,ba wanda ke cewa komai a tsakaninsu,sai jikkunansu dake hade,dumin fatar cinyarsa da towel din bai gama rufewa ba tana ratsa

saahar tare da haifar mata da wani irin vanayi a cikin jikinta. Shima baice komai ba har suka gama,sai ya sanya daya hannun ya sake dafe tafukan hannayenta yana kallon cikin idanunta tare da sauke wata ajiyar zuciya me nauyin gaske

"Na gode, Allah yayi miki albarka" har ciki tsakiyar ranta tali dadin addu'ar, batasan cewa shi ya fita jin dadin samun wannan kulawar ba, duk da sai daya tilastata kusan ya samar da ita

"Ameen" ta furta can gasan ranta amma kuma labbanta sun motsa

"Amma....kin saka an dakeni kuma an hanani kuka?" Ya fada yana langabe kai cikin wata shagwababbiyar murya data sanyata daga kai ba shiri, idanunsu kuwa suka hade guri daya,sai ya dage mata gira abinda ya sanyata saurin mai da kanta qasa

"Yes maji tace zakuyi tafiya tana neman alfarmata na barki ki tafi, batason kuma doguwar tambaya ita tasan inda zakin keda angel" ya qarasa fadi cikin yanayi na nazari.

"'Nima ina sake neman alfarma tare da rogon kauda duk wata tambaya daga ranka shakka ko kokwanto, khairan in sha Allah" har cikin bargonsa sautinta ya ratsashi, karon farko data masa magana da irin wannan salon, hashi kuma kusancin dake tsakaninsu ya bashi damar jin tone dinta tarrr

"Oh my god,repeat please,sake fadi" fuska ta tsuke,ta kuma shammaceshi ta mige da zafin nama,saidai ya rigata ta hanyar cafko hannunta

"Waye yace ki tashi?, haka kawai kin ciremin towel,oya mayarmin da abuna" sulalewa kawai tayi a wajen ta tsugunna tana curewa guri guda,ko kallonsa a haka ba zata iya sake yi ba bare ta gyara masa munafukin towel din daya dauro. Magiya ta hau

Please Login or Register in order to submit comment