Reading TABARMAR KASHI 1&2 complete by SAFIYYA HUGUMA Chapter 60 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

irinwannan nutsuwar da kike fada?"

"Eh kika sani ko babies din namu tare sukeson isowa" afifa ta fada tana murmushin tsokana. Dan tsuke fuska tayi tana harararta


Zafafa biyar
🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥
🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥
"HUGUMA*


•_ TABARMAR KASHI_


Book 02 Page 50

"An gaya miki kowana ayu ne irinki?, besides mani ba auren zama nayi ba wannan shine last aikina da zanyi na gama zama a wajen" dariya sosai afifa ta saki harda kama ciki, sanann kuma daga bisani ta samu guri ta zauna. Dariyar ta qular da sãahar

"Waye kikema dariya haka?"

"Astagfirullah,da wanda ya tsargu nake" ta fadi tana fuskewa. Bata taba gain wauta zalla irinta sãahar din ba,da gasken gaske autar ce ta gaske, duk yawan buda sagonnin toufeeq da yadda fuskarta kan saki a duk sanda ta gama karanta sagon afifan na karance da shi daga jiya zuwa yau din,amma duka wanna ta tattara ta ture, itakam zataso taga ya wanna drama zata kaya.

_muma zamu so mu gani ni da jama'ar zafafa_😃

Sai säahar din bata sake cewa komai ba don vau
din bata jin kowanne wasa da afifan zata yi mata zaiyi tasiri, amma hakanan maganar baby din data fada saita tsaya mata a rai. Ta yaya zata samu wani baby?, bayan ko kafin ta taho tayi period, kuma zuwa next week take sanya ran zuwan next period dinta,sannan ko a yanzun tana jin cramps a mararta, amma idan ya tabbata fa baby dinne? ta yiwa kanta da kanta tambayar,sai kawai ta samu kanta da subucewar murmushi a fuskarta wanda ita kanta batasan dalilinsa ba.

Kurba uku kacal ta yiwa tea din taji ya cika mata ciki fal, qamshin madarar dana Lipton din ciki yana son hautsina mata ciki,sai ta ajjiye tana duban afifa dake cin abincinta tuquru kan jiki kan qarfi. Kaman zatace wani abu sai kuma ta janye idanunta, tuni afifan ta ganta, murmushi ta saki

"Bestie wannan dan naki acici ne Allah"

Sai da dukkansu suka jira afifan na kusan minti
ashirin ta gama lodin abincinta sannan suka fita farfajiyar hotel din,inda taxi din da zata garasa dasu asibitin su ukun take jiransu.

Ko a hanya ma shuru ne nata,tayi nisa a duniyar
tunanin me ranar ta vau zata haifar musu? farinciki ko
akasin haka?, abinda ke qara sanyaya mata gwiwa daya ne,dukkan sakamakon da zai biyo baya ITACE SILA ALKHAIRI KO AKASINSA.

Da gudu fadeela ta sauko daga saman gadon ta
rungumeta tana kiran sunanta

"I missed you anty N" sosai sãahar ta rigeta hawaye
nason zuba a idanunta amma tana danneshi, ta tsugunna a hankali ta rungume fadeelan cikin jikinta hawayen na zartowa. Har an aske area din da za'a yi mata surgery din. Tsanar hajiya garama ta sake cika a zuciyarta sanda fadeelan ke fadin

"Abby bazaizo na ganshi ba?" Banda gudun sharrinta, ta yaya za'a yiwa fadeela aiki irin wannan toufeeq baya gurin? baima sani ba?.

"'Zaizo in sha Allah my fadee, kada ki damu"

"Yaushe anty?" Ta sake tambayarta tana rungume a jikinta

"Yau in sha Allah" taji afifa ta fada tana riqe hannun fadeelan a tausashe. Ajiyar zuciya säahar din ta saki, har a ranta taji dadin yadda afifan ta kubutar da ita, don batason viwa fadeelan qarya.

Migewa tayi ta aza fadeela din saman cinyarta tana jin labaran da take bata na nurses din dake kula da ita,da sauran abubuwan da ke wakana a asibitin duk sanda ta tafi gida.

Awarsu guda nurses biyu suka shigo dakin nasu,cike da kulawa da sanin darajar mara lafiya suka shaida musu zasu shirya fadeela za'a shiga da ita theater room din. Dukkansu dai jikinsu yayi sanyi, banda ita abinka da yaro da kuma quruciya, tana ta yiwa säahar hira ita kuma tana qoqarin boye hawayenta. Har suka kammala shiryata hannunta yana cikin na sãahar, ba ita ta sake mata hannu ba har sai data isa gofar theater room din. A hankali ta zame hannunta cikin nata, amma idanunta cikin na fadeelan. Duk yadda taso dakewa ta kasa, muryarta na rawa tace

"Allah yasa ayi lafiya a gama lafiya fadee na,in sha
Allah,in sha Allah from this day kin rabu da wannan lalurar rabuwa ta har abada. Murmushi kawai fadeela tayi mata,idanunta gyar bisa fuskar säahar din har suka maida gofofin suka rufe suka daina ganin juna.
Afifa ce ta matso tana dora hannunta akan kafadar saahar din

"Wannan damuwa ta isa hakanan-karkije ki yiwa kanki illa fa, damuwa a irin situation dinki bata kamaceki ba,an viwa mutane bila'adadin surgery din nan,kuma alhamdulillah they're healthy and safe,suna rayuwarsu vanzu kaman kowa,ya riga ya zama tarihi ma,samu guri ki zauna" sai taja hannunta suka zauna saman kujerun dake shirye a gurin.

Sannu a hankali sakanni suka juye zuwa mintuna, mintuna suka juye zuwa awanni, awa ba daya ba har biyu shiru,zuwa lokacin sai ta dinga jin kamar hankalinta nason barin jikinta, da gyar ta iya daurewa aka cinye awanni uku cur.

Tuni duk wani fata nata ya yanke, confidence dinta ya soma zagwanyewa tsoro da firgici, ta waiwaya ta dubi afifa data dawo daga cin abinci, abincin da babu yadda batayi da sãahar din tazo suci ba amma tace ba zata iya motsawa ko nan da can ba

"Bestie lafiya kuwa? 3hours fa" dan murmushi ta sakar mata na kwantar da hankali

"Ba komai in sha Allah, suna aikinsu ne" kasa zama tayi,sai ta mige ta koma dakinsu ta daura alwala,sannan ta dawo gurinta,ta bude qur'anin cikin wayarta ta fara karantawa gasan ranta ko hakan zai taimaka mata ta samu nutsuwa komai qangantarta.

Sannu sannu sai gashi an sake shafe wata awa
dayan har da rabi, adadin awanni hudu da rabi kenan,zuwa lokacin karatun kawai takeyi, amma gefen lafayarta gaba daya ya jiqe da hawaye, idanunta kuma sun tasa sunyi jajur, kamar yadda fuskarta ta hada jaa musamamn wajen hancinta zuwa habarta, abinka da farar fata. Duk iya hilatar da afifa zatayi tayi matan amma kuma bata samu nasara ba dole ta zuba mata ido ta shiga tayata da addu'ar itama cikin zuciyarta.

Sajjad ne ya shigo gurin, ya tsaya daga baya ya yiwa afifa alamar tazo da hannu,dukka tana kallonsu,amma hankalinta baya kansu, har zuwa sanda afifan taie sukavi magana qasa qasa sannan ta sake dawowa wajenta,shi kuma ya juya ya fice a hankali.

›Wasu mintuna arba'in dinne suka zo suka wuce duka akan idanunta dake a rarrabe tsakanin qur'aninta da gofar theater room din.

A hankali gofar ta bude, abinda ya kusa tsayar da bugun numfashinta saboda wata qaqgarfar faduwar gaba. Ko ina a jikinta rawa yakeyi sanda likitan ya bayyana a gofar dakin. Zumbur ta mige har wayar hannunta na subucewa ta fadi a gasa, dukkan idanunta a kansa tanason zuwa ta riskeshi taji daga bakinsa amma tsananin tsoron abinda zataji daga gareshi ya hanata aikata hakan.

Lokaci daya kuma gabanta ya sake faduwa fiye da na dazu sakamakon tsintar muryar da bata taba zaton ji ba. Da wani irin sauri ta juya tana kallon qofar farko ta shigowa gurin.

Sajjad ne gefansa kuma toufeeq, nadeeya na biye dasu. Sanye yake cikin wasu lafiyayyun suit da aka saqa da asalin zare me daraja na vicuna giviut fabric.

Kalar suit din data dace da kwantacciyar fatarsa da hutu da kulawa suka ratsata. Idanunta ta sauke kan fuskarsa,abinda ta hanga wani irin shimfidadden bacin rai tare da cushewar fuska,ainihin kamanninsa na cikakken miskili kuma fusataccen MT JARMA take gani muraran, hakanan cikin sassarfa yake takowa fiye da sajjad da nadeeya. Kamar ya sani ko yaji a jikinsa tana kallonsa. Nasa idanun va zube a kanta sanda idanunsu suka sarqe cikin na juna sai taji gafafunta sun fara rawa, bugun zuciyarta ya garu ainun, mararta ta daure tamau yana sake kusantota tana jin kamar ana juyata daga hagu zuwa dama, daga gaba zuwa baya. Sai ta fara gani dishi dishi lokacin da mararta tayi wani mugun murdawa dai dai lokacin kuma da likitan ke magana da harshen jamusanci

"Wo sind Fadeelas Verwandte? Folgen Sie mir ins Büro, es gibt etwas sehr Wichtiges, das ich Ihnen sagen mochte (ina 'yan uwan fadeela?,akwai bayani me matuqar muhimmanci da zanyi muku". Idanunta ta dauke daga kansa tana mayarwa kan likitan dake nufar office dinsa da sauri sauri. Ganinta yana sake zama dishi dishi toufeed na kusantota idanunsa a kanta,lokaci guda kuma taji wani abu me dumi yana ratsa jikinta sannan ya zarto zuwa qafafunta ta cikin lafayar jikinta,sannan ya taba takalminta ya kuma fara sauka a farin marbles din dake shinfide a gurin.

Idanunta takai kai,wani irin abu ya daki
kwanyarta,jini ne, irin jinin da ta taba gani kenan sau biyu a rayuwarta,zamanin rayuwarta a gidan adam,zamanin da take mararin haihuwa da samun iri, yau ga na uku na fita daga jikinta wanda shi kuma wanna bata da tabbacin jinin meye?. Ruf idanunta suka gama fullubewa, tayi baya gaba daya zata zube a wajen,saidai tsananin zafin naman da toufeeq yayi ya hana hakan faruwa.

Cikin zallar tashin hankali ya tarota ta fada a jikinsa. Tuni afifa ta taso kanta, itama nadeeya ta garaso da sassarfa, shi da su kowa na kiran sunanta da garfi hankali tashe, toufeeq din yana jijiga kafadunta,saidai ko alamar motsi batayi ba. Hankalinsa a matugar tashe yake duban jinin dake zuba daga jikinta,sai ya dauketa cak kawai ya wuce office din likitan da gaggawa.

Suna shiga likitan dake rataye lab coat dinsa ya waiwayo,zuwa lokacin tuni ya shimfideta saman gadon dake dakin,cikin rudani ya juye harshen jamusancin shima yana cewa

"'Der Arzt hat ihr schnell das Leben gerettet, ich weiß nicht, was mit ihr passiert ist (Dr ka ceto rayuwarta da hanzari bansan me ya sameta ba)" da gaggawa ya danna wani abu sai ga nurses har biyu sun shigo, ya kalli toufeeq

"Sir, geben Sie uns einen Arbeitsplatz?(sir ko zaka bamu guri muyi aiki?)" Kai toufeeq ya girgiza,yana tsaye qyam a gabanta hannunsa cikin nata,yana jin wani tashin hankali na ratsashi

"Ich kann nicht rausgehen und ihr vor meinen Augen irgendetwas antun(bazan iya fita ba,kuyi mata komai a gabana)". Yadda suka karanceshin sunsan ba zaya fita din ba,abu daya yayi dole ya sake mata hannu don ya basu damar gabatar da aikinsu,ya koma baya kadan hannunsa zube a aljihun suit dinsa, idanunsa da suka sauya launi saboda tsananin tashin hankali qur a kanta tamkar an gaya masa yana janye idanun zai rasata.

Cikin lokaci gangani suka farfado xa ita daga suman da tayi sukayi goqarin tsaida jinin. Bai tsaya ba amma ya ragu,ganin hakan ya sanya likitan ya kunna na'urar scanning ya fahimci ne yakeson yi,sai ya matso gabansa

"Fass es nicht an, lass die Frau es ihrer Tochter antun, ich kann es nicht ertragen, das zu sehen(kada ka tabata,ka bari mace 'yaruwarta tayi mata,bazan jure ganin haka ba)" likitan nada fahimta sosai da kuma saugin kai ya saki murmushi kawai ya matsa baya yana-sakarwa daya nurse din na'urar,har yanzu murmushi yakeyi sannan yace

"Du liebst sie anscheinend sehr, deshalb bist du so eifersuchtig auf sie(kana son ta da yawa da alama, shi yasa kake wannan kishin)" Kansa ya jijiga da qarfi don ya tabbatar masa da girman hakan cikin zuciyarsa

"extreme Liebe(matsanancin so)" ya amsa masa a taqaice.

Idanun likitan nakan allon computer din sanda take scanning din yana kuma yiwa toufeeq din bayani

"Kaine mahaifin fadeela?" Kai ya sake jinjina masa,sal ya waiwayo a nutse ya kalleshi, sannan ya saki murmushi, haka kawai yaji toufeeq yayi masa,ya miga masa hannu yana murmushin

"'Ina tayaka murna,munyi aiki successful irin wanda bamu taba yin kamarsa ba,munyi nasarar cire sashen dake sakata jijiga in sha Allah daga yau zata rayu kamar kowanne mutum, amma zaku kula sosai da qa'idoji da kuma zuwa dubata har ta kammala warkewa duk da dai mun fahimci kamar any amfani da wasu magunguna a kanta da sukaso fadada ciwon ya taba wani sashen daban na qwaqwalwarta,wanda inda hakan ta faru ba zata taba warkewa ba, saidai taci gaba da rayuwa akan magani har qarshen rayuwarta,to sai kukayi dabarar tsaida maganin, abinda yayi nasarar hana afkuwar hakan,kuka kuma yi dabarar kawota akan lokaci akayi mata aikin,Glückwunsch(congratulations)". Wani irin abu me sanyi ne ya sauka saman zuciyarsa tamkar ana sanya sassanyan ruwa ana wanke masa zuciyarsa. Cikin sanyin da mutuwar jiki ya migawa likitan hannu shima

"danke Doktor(na gode dr)". Maida dubansa yayi ga saahar dake numfashi a hankali saboda allurar baccin da yayi mata bayan farfadowarta

"Wanne irin nau'in so zai gwadawa rayuwarta ne?" Ya
tambayi kansa da kansa,shi kansa baisan iya adadin sonda yake mata ba,ga wasu dalilai da suka qara rura wutar qaunarta me tsanani a ransa,shi kam bai sani ba baisanta yadda zai sarrafa wannan soyayya da qaunar da yakej) cikin qirjinsa ba.

"Setzen Sie sich, Herr (zauna yallabai)" likitan ya fada
yana dubansa, koda suka bashi seat din gaban gadontaya maidashi hannunsa cikin nata vana sake kula da dukwani motsinta

"'Zamu bata daki itama,zuwa nan da awa sha biyu zamu tattara bavananta zamu sanar maka" likitan va fadi yana sake nazarin scanning din.



Zafafabiyar
🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥
🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥

"HUGUMA

• TABARMAR KASHI*
Book 02 Page 51



Lokacin da aka fito da ita tana bacci. Afifa so tayi ta rude, toufeeq din ya riga yasan situation din da afifan ke ciki, don haka ya yiwa sajjad din alama na ya jata yabar gurin da ita.


*********Sannu a hankali ta dinga bude idanunta da taji sun dan mata nauyi ga kuma hasken da ya cikasu. Yana zaune a gabanta hannunsa cikin nata,ko motsi baya yi da idanunsa bare hannun nasa dake dame da nata.

A nutse ya miga hannunsa zuwa saman goshinta don tabbatar da farkawarta. Dumin hannunsa dake saman goshin nata ya sakata dauke idanunta daga kan maji dake zaune gefe daya saman kujera ta dawo dashi kansa. Sarqewa idanunsun sukayi cikin na juna,ta dan zuba masa ido tanason tabbatar da shi dinne?, har yanzu akwai fushin nan saman fuskarsa ko kuma yayi qaura?.

Hawaye ne suka fara tsatstsafowa idanunta,idonsa ya lumshe sannan ya bude yana girgiza mata kai alamar a'ah dai dai lokacin maji ta dawo da dubanta kansu,ta matso a nutse tana fadin

"Ta farka ne?"

"Eh" ya amsawa maii din. Qogarin zame hannunta daga nashi takeyi saboda gain maji a wajen, amma saidai bashi da niyyar motsawa daga wajen ma bare ya bari ta zame hannun nata.

"Sannu d'iyata" maji ta fada cikin kulawa. Kai ta gyada mata sannan ta motsa bakinta a hankali

"Yauwa" ta amsa mata,dai dai lokacin likitan ya shigo, bayansa afifa ne ita da sajjad. Dukkansu kayan data gani a jikinsu a daxun yanzu basu bane ba,da alama ta dauki wasu awanni kenan tana bacci ba tare da tasan abinda yake faruwa ba.

Sannu suka yiwa likitan, afifa ta matso tayi mata sannu sannan suka juya dukka suna fita saboda bawa likitan damar dubata, banda toufeeq da ya gara matse hannunsa cikin nata.

Wannan karon cikin harshen turanci likitan yake masa bayani

"'Ina mai baka haguri, ta samu bari na ciki dan sati hudu"

"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, Allahumma ajirni fi musibati, wa'akhlifni khairan minha" ya furta yana runtse idanunsa.

Har cikin saman kansa ya dinga jin wani abu, sai ya kasa ci gaba da tsaiwar,ya koma a hankali ya zauna saman kujerar yana ci gaba da rige hannunta,kana ya sauke idanunsa a kanta.

Tunda likitan ya fadi maganar taji kamar an sauke mata dutse mai nauyi a girjinta
"Anya tana rabon ganin qwanta a duniya?" Tambayar data yiwa kanta kenan,tana jin numfashinta kamar yana mata wahalar shaqa.

"Akwai abinda yadan raunata qarfin mahaifarta,don haka tana da dan rauni,wanda cikakken motsi ko zirga zirga me yawa,ko kuma razana suna iya kawo mata miscarriage" idanunsa ya mayar kan likitan,yana jin zuciyarsa na quna

"Yanzu sai yaushe zata iya sake conceiving?" Maganar ta sanya likitan dagowa ya dubeshi tare da sakin qaramin murmushi

"Kada ka damu yallabai, indai za'a kula da ita yadda ya kamata, maida wani babyn bazai zama abu me wahala ba"

Magunguna ya rubuta cikin file din sannan ya ajiye yana qara masa was bayanai sannan ya juya ya fita. Ya barshi cikin wani irin yanayi,ya dinga ji kamar laifinsa ne, kamar shi yayi sakacin da cikin ya fita,amma bai sani ba ba shakka inda yasan akwai ajiyarsa tattare da ita ko sama da gasa zasu hade bazai bari tayi tafiyar ba. Shi daya yasan yadda Allah ya jarabceshi da son tara zuri'a,musamman a yanzun a yadda yake,Allah yayi masa dukkan wata ni'ima da sutura ta rayuwa.

Idanunsa ya dauke daga kan likitan a nutse ya maida saman fuskarta dake a runtse wani abu me masifar garfi yana sake fusgarsa a kanta. Duk da idamunta a kulle suke, duk da a gadon asibiti take amma hakan bai hana bayyanar kyan siffarta ba.

Sosai ya zubawa gefan idonta ido yana son tantance hawaye takeyi?,ya gani kuwa dai dai?. Yatsansa ya sanya ya dangwali hawayen,ya tabbatar sune, abinda ya sanyashi tashi cak daga kujerar da yake zaune a kai ya koma gefan gadon saitin kanta.

Cikin taushi ya daga kanta ya dora saman cinvarsa, sannan ya sanya tattausan tafin hannunsa ya fara dauke mata hawayen. Saukar hannun nasa saman fuskarta ya sanya ta dakata da kukan saboda yadda ta jita kwance saman jikinsa. Sai da ya gama tas sanann ya sunkuya da kansa saman fuskarta,sai ya zamana kamar yayi mata rumfa. Cikin muryarsa me taushi da kuma wani irin deepness yace

"Kema kina bugatar sa ko?" Yayi mata tambayar da sai da taji kamar zata nutse a gurin. Sake sassauta muryarsa yayi

"me yasa ya tafi a irin wannan lokaci? ya tafi ya barmu da kewa me yawa ni da mommy dinsa,we missed him a lot, but karki damu,kiyi goqari ki warke da wuri, nay algawarin zanyi replacing wani very soon in sha Allah" kasa jurewa tayi duk da idanunta suna a bude ne, saita mirgina kanta daya sashen tana sake lumshe idanunta.

Tsaye tayi daga bakin qofar ICU din, inda aka
kwantar da fadeela,wadda a qalla zata iya kaiwa gobe ko jibi tana bacci saboda allurar baccin da sukayi mata,suka saka mata na'urar ventilator saboda ta taimaka mata wajen yin bacci da kyau.

Duk lokacin data kalli fadeelan sai taji zuciyarta ta
tsinke sosai, tsoron Allah yana sake kamata,tare da
tabbatar da cewa lallai dan adam ba'a bakin komai yakeba. Haka kawai cikin jikinta takejin zargin hajiya qarama me garfi akan ciwon fadeela,har yanzu kunnuwanta suna iya jiye mata fadan da take a dazu cikin wayar jarma bayan ya kirata don ya gaya mata ta aikawa mansura a kira company din nan suyi gyaran sashensa irin wanda sukeyi duk shekara, daga nan ya shaida mata suna Germany tare da sãahar da fadeela harma da toufeeq da nadeeva an yiwa fadeela aiki.

Saura qiris ta zame ta fadi saman marbles na
kitchen din da take tsaye a ciki a sannan, don sai data
dafa me aikinta sannan ta samu guri ta zauna zuciyarta na wani irin rawa kamar zata tsinke daga qirjinta

"Yaaya? yanzu har rashin muhimmanci na yakai kowa da kowa ya tafi gurin aikin ciwon fadeela amma banda
ni? bayan nice nafi cancanta da naje?"

"Nima daga qasar da naje na samu visa na wuto, bansan me yake faruwa ba"

"Amma yaaya ina cikin gidan nan, har yaushe aka yanke. shawarar yin hakan ba tare da na sani ba?"

"Wannan kuma ki jira danki yazo sai yayi miki bayani, don hukuncin surukarki ne,ita ta tsara hakan, ban sani ba ko da saninsa ne koma meve dai anvi aikin successfully inji likita, farfadowarta kadai muke jira"

"Turgashi!" Ta fadi cikin matsanancin tashin hankali

"Ita har waye yaaya da zatayi kutse a rayuwarmu? har ta isa tayi hukunci cikin rayuwar 'yarmu?, to wallahi ka shaida mata ta kuka da kanta, muddin daya daga cikin matsalolin da akan iya gamuwa da su sanadin surgery din nan ya samu fadeela to la shakka sai nayi shari'a da ita,sai na daureta wallahi, akwai visa ta ta garmany dana taba yi, batayi expire ba,ina nan tafe nan da kwanaki uku in sha Allah" ya zuwa yanzu haka kawai Dr mahmud yakeji ya fara qosawa da damuwa da matsalolin fauziyya

"Sai kin iso. kawai vace da ita vaja jan garamin tsaki.
Hayaniyar da tayi masa cikin waya yaji tana bata ransa, ya waiwava va dubi maji dake zaune a gefansa cikin mota.

Ko a fuska bata nuna taji komai ba, duk kuwa da yasan
bata yadda za'a yi tace bata ji din ba saboda handsfree ya saka,amma yadda ta nuna din sai ya garyata maka hakan. Ajiyar zuciya kawai ya saki,shi kadai yasan irin rudanin da yake ciki, tunda me afkuwa ta afku suka baro.

Algeria ko sau daya bai gara ganin murmushinta ba.
Sallamar Dr mahmud jarma din ta sanyata
motsawa kadan,ta kuma amsa ba tare data juyo ba.
Gefanta ya garaso ya aza hannunsa daura da nata,sai kawai ta cire nata hannun ta fara takawa tana barin gurin.

Kamar ya kirata sai kuma ya fasa, gudun kada ayi
abun kunya gaban surukai,ya maida kansa ga fadeelan
vana ci gaba da yi mata addu'a,don shi kansa yayi
matuqar damuwa, kasancewarta tilon jika a gurinsa.

******* Kusan minti guda cif yayi yana kallonta daga nesa zuciyarsa tana narkewa. Kwata kwata bata zauna ta samu cikakken hutun da likita ya bugata ba daga gareta, tunda har taji zata iya migewa taqi zama,sai zirga zirga da takeyi tsakanin ICU din zuwa dakin da aka bata, tsahon kwanakin ukun duka ta tashi hankalinta,ta dorawa kanta laifin komai da komai har da rashin farkawar fadeela akan lokaci.

A hankali taji an rungumeta ta baya, sannan cikin
taushi ya sanya hannunsa va hannuwansa saman ruwan cikinta ya sake jawota cikin jikinsa sosai. Kansa ya dora saman kafadarsa,cin taushi ya soma mata magana a kunne me kama da rada

"Damuwarki tana ciremin kowanne karsashi daga raina"

hannunsa ya sanya ya juyo da ita suna fuskantar juna,ya miga yatsansa yana dauke ruwan hawayen dake layi saman kuncinta

"Karki sake kuka we'll figure this out together, she will be fine in sha Allah,don't blame your self" qas tayi da
fuskarta wasu sabbin hawayen na saukowa,sai kawai ya bude girinsa ya sanyata a ciki,ya kuma rungumeta tsam yana shafa bayanta a hankali idanunsa kan fuskar fadeela da ta dan kumbura kamanninta suka dan jirkita kadan.

"Toufeeg" yaji an kira sunansa daga bayansa. Dukkansukoda basu waiwaya ba sunsan me muryar. Motsawa säahar tayi kadan da nufin janye jikinta

"Don't move" ya furta can gasan magoshinsa, idanunsa a lumshe yana ci gaba da shafa bayanta. Bata sake motsawar ba kamar yadda ya buqata,hakanan bai juya ba shi dinma, har zuwa sanda ta iso gabansu

Hajiya qarama ce, cikin shigar nan tata da ko yaushe take nuna tsananin alfaharin da take dashi,izza da kuma nuna isa

Toufeeq.…...au lallabata kakeyi ma?,na tsammaci zanzo na samu kana hukuntata da mafi tsananin hukunci? yarinyar da take shirin yi maka sanadin rasa tilon 'yarta saboda shegen shishshigi da rawar gafarta? ko an gaya mata mu bamusan hanyar germany din bane da zata kwaso gafafunta ta kawo mana yarinya uwa duniya? gashi har yanzu bata farka ba? waye ya sani ma ko cinikin qodarta kota qwaqwalwar tata tayi mana"

"Stop" ya furta cikin gautsi da bacin rai,yana jin kamar ya juya ya wanke mata fuska da mari,saidai a yanayin da ake ciki yanzu bayason yace mata komai,lokaci kawai yake jira. Sai a sannan ya bude idonsa kan fuskar sãahar wadda ta daga kanta daga qirjinsa tana duban awayar idanunsa cikin damuwa da razanin kalaman hajiya qaramar.

Hannunsa ya dora saman kanta kamar qaramar varinya

"Banason wannan tsoron, banason wannan firgitar,tun yanzu nakeson ki ajiyeta, da irin wannan abun naki kikayi mana asarar baby". Wata nutsuwa taji tana saukar mata da kalamansa dake nuna ko daya zancan annamimiyar matar baiyi tasiri a ransa ba.

"Asarar wanne babyn bayan fadeela?" Tayi masa
tambayar adan rude. Kai tsaye ya waiwaya,karon farko
tunda ta iso ya dubi qwayar idonta kai tsaye

"She had miscarriage, cikina dake jikinta ya bare"
mummunar faduwar gabanta yayi wanda sai data jishi
har tsakiyar kanta,me yake shirin faruwa tana toshe wata barakar wata barakar tana kunno kai? yanzu har tayi saken da wata macen da ba meenal dinta ba zata dauki cikin toufeeq?. Kafin ta sake cewa wani abu ya dauke idonsa daga gurinta

"Ko zaki matsa daga nan gurin, saboda basa bugatar
hayaniya da tarin tarkacen mutane" dubansa tayi a
mamakance a karo na biyu, Ita toufeeq yake kira da tarin tarkace?, koda yake tayi masa uzuri yana cikin dimuwar rashin farkawar fadeela,to amma kuma idanunta suna nuna mata canzawar mu'amala tsakaninsa da yariyar, yaushe hakan ta kasance? indai hakanne kenan aikinta ya sake linkuwa?,kenan wani dogon zangon zata ci muddin hakan ya tabbata kafin cikar muradinta?.

Shuru ne va ratsa gurin bayan ta juya ta bar gurin
cikin wasi wasi. Ci gaba yayi da boyeta a qirjinsa, saboda weakness din da yake hanga tattare da ita bayason ganinsa, she's strong enough,tayi abinda dukka dangin fadeela suka gaza yi mata,bai kamata ta karaya haka ba.

"Subhanal malikil guddus" taji ya furta yana sakinta daga jikinsa. Daga kanta tayi da sauri ta kalleshi,sai kuma ta maida dubanta ga

Please Login or Register in order to submit comment