Reading TABARMAR KASHI 1&2 complete by SAFIYYA HUGUMA Chapter 58 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

masa

"Tashi kije" ya fada yana danne dariyar dake qasan ransa,da gaske yarinyar ta horu yadda ya kamata,inda dane da tuni yasha tsiwa da musu sau babu adadi. Koda ta fita waiwayawa tayi ta ballawa dakin harara tana jan awafa sannan tayi gaba

_niko nace a banza,ihu bayan hari kenan,idan yarinya ta isa tayi a gabansa mana 😂😂
"HUGUMA*


* TABARMAR KASHI *

Book 02Page 46

_assalamu alaikum,barkanmu da dare,jiya an samu typing error,zakuga na sana matsiyaciya a maimakon matsoraciya,ina fatan kun fahimci kuskuren dake gurin,na gode_

Tun daga ranar data fuskanci ina ya sanya gaba take rufe dakinta da wuri su kwanta ita da fadeela,idan yazo ya gani saidai ya koma ranshi babu dadiyaso ya sake wasata da kyau ya kuma more kafin lokacin tafiyar kamar yadda maji ta gaya masa. Amma a kwanaki itace take shirya musu breakfast tayi musu abincin da zasuci idan sun dawo,ta kuma hada lafiyayyen dinner. Sai a lokacin ya vadda da zancan hausawa da sukance a rashin uwa akanyi uwar daki, tabbas a rashin samun girkinta yake yaba abincin Jacob, bai taba tunanin akwai wani da yakai
Jacob iya girki ba sai gashi ya samu wadda ta fishi nesa ba kusa ba.

Hankali kwance säahar keyin shirin tafiyarta,shiru da meenal da hajiyan sukayi da al' amuransu jikin säahar ya bata tabbas ba a banza ba,saidai ita kanta cikin satin baccinta ragagge ne, don addu'ar neman nasara tuquru takeyl.

Qarfe biyu na dare yana zaune cikin dakin nasa yana sarrafa CCTV camera din dake cikin dakin nata,duk da ta haramta kwanansu tare amma hakan bai haramta masa ganinta ba ta hanyar CCTV camera din, abinda ya zame masa kamar ibada,a kullum idan ya dawo daga aíki ya kammala komai sai ya zauna yayi bitar wuninta na ranar a cikin dakin,saidai daukar kadan yake samu,duk da cewa yawanci zazzafar dauka ce dake yawan dagula lissafinsa,don a nan ne yake samun damar ganinta sosai, abubuwan da bata iya barinsa ya kalla yadda ya kamata a nan yake samun dama.

Kwanakin data dauka tana sallar daren duka yana sane da su,ko a yanzun da tafiyarsu ta kama jibi ne yana bibiye da komai,amma har yanzu baici karo da inda tayi maganar tafiyar ko wani abu daya danganceshi ba.

Ajiyar zuciya ya sauke,ya tabbatar gobe zai tafka mata tsiya ne,bazai iya bari tayi tafiya me nisa haka ba ba tare da sunyi kyakkyawar gaisuwa ba,sai ya maida daukar ya rufe ya koma duba history na jiya da daukan da camera din ta yiwa sashen hajiya qarama. Bude video din yayi yana sake nazari,hajiya mansura ce ita da hajiya qaraman,kowacce fuskarsa cikin bacin rai,kuma magana suke da juna cikin fushi, saidai har yanzu ya kasa tantance me suke gayawa junansu saboda sunyi nisa da ma'ajiyar camera din tsaron. Ya jima yana duban fuskokinsu su biyun,yadda suke a haka a hakan ake nuna masa su cikin mafarkinsa,ya dade sosai yana sake bibiyar wasu motsinta na baya dake ajjiye sannan ya kashe yana sauke ajiyar zuciya

"Akwai gagarumin abu a qasa" ya furta a hankali, gaba daya zuciyarsa da gangar jikinsa suna bashi akwai babban al' amarin dake tunkaroshi, saidar ya rasa meya wannan?.


*********Washegari tun bayan sallar isha'i da sukaci abincin dare ya kafa ya tsare a falon, wanda kusan wannan ba al'adarsa bace yafi zama a balcony dinsa study room ko cikin dakinsa,kasancewar shi din mutum ne maras son hayaniya ko a shiga al' amarinsa. Fadeela na lafe a jikinsa tana ta masa hira,yayin da nashi idanun kekan säahar duk wani shiga da fita da taketa yi tana sake kammala musu kayansu na tafiyar da zasuyi a gobe saman idanunsa ne. Tun a yanzun ya dinga jin wata kewa tana ratsashi.

Bai tashi a gurin ba har fadeela tayi bacci a jikinsa,sai ya gyara mata kwanciya yana canza tasha zuwa News channel.

Sai data tabbatar komai ya kammala,ta canza kayan bacci fadeela kawai zata dauka su kwanta sai ta zura hilabinta ta sanya slippers dinta ta fito falon don dauke fadeelan su kwanta.

Takunta ya sanyashi waiwayawa,kallo daya tak yayi mata ya dauke dubansa daga kanta zuciyarsa tana harbawa,cikin baby hijab din jikinta fuskarta tavi wani mugun kyau,tattausar rigar baccinta me gajeran hannu ta fidda qirarta ta coca-cola shape, duk da idanunsa baya kanta amma idanun zuciyarsa yana tattare da ita,ya kuma qididdige takunta har ta iso gareshi,ta kuma duqa zata dauki fadeelan

"¡dan kin kwantar da ita ki kawomin coffee daki"

"Tom" tace da shi ba tare data kawo komai cikin ranta ba, don zuwa lokacin ta fannin abinci bata ayashi ta data ta bashi. Ba abinda take tunawa a duk sanda ya bugaci abinci sai yadda yayi missing mahaifiyarsa a shekarun da yake da buqatar kulawarta,hajiya qarama ta shiga tsakaninsu,ta tarwatsa soyayyar da Allah ya ginata,sannan ita din bata zauna ta basu irin kulawar da uwa ke bawa danta ba.

Kasancewar sai ta tsaya ta dafa ya dan ja lokaci wannan ya bashi damar gama nasa shirin baccin.
Yana zaune saman gado rabin gafafunsa lullube da duvet ta shigo dakin da sallama. Bata lura ds kallon da yake binta da shi ba,saboda ta qagu ta gama dashi taje ta kwanta ta samu isashen baccin da zata farka tsakiyar dare tayi addu'a ta musamman saboda samun dacewa da nasara.

"Migo min" ya fada a nutse yana lumshe ido, sassanyan qamshinta yana hautsina tunaninsa tare da qara masa kwadayinta.

Hannunsa cikin nata kamar yadd ya saba mata duk sanda zata bashi wani abun sha ya riqeta tsam. Duk zafin coffee din haka ya dinga kurbarsa da zafi zafi saboda wata wuta ce ke ruruwa cikin ruhinsa da zuciya,dama kowanne sashe na gangar jikinsa.

Kurba hudu kacal ya gama dashi,ya zare cup din da daya hannun yayi wurgi dashi cikin zafinsa, saboda ji da yakeyi cikin jikinsa yakai maqura. Gaba dayanta ya fincikota jikinsa,ta samu kyakkyawan masauki tsakanin girjinsa da tsakiyar qafafunsa,yayi mata wata zazzafar runguma yana laluben bakinta da nasa bakin dake dauke da dumin coffee.

Kyarma jikinta ya fara yi ganin yadda gaba daya yake a gigice yadan dakata kadan yana duban idanuntà da jirkitattun idanunsa tamkar wanda yasha abun maye

"Baki d imani wallahi, kin sani sarai yadda na jigata a kwanakin nan, amma kin dauke kanki kamar baki sani ba,har yanzu baki sona ne?, ko irin dan kadan din nan ki soni mana don Allah" ya furta kamar zai shide saboda yadda qamshinta da dumin jikinta ke sake birkitashi,ga abubuwan dake tone masa ido yau din suma cikin yancinsu suke, don rigar baccin ne kawai a jikinta


"farewell mee..." Kasa garasawa yayi saboda
muryarsa gaba daya ta sarqe, sai ya lalubi bakinta ya fara aike mata da wani zazzafan kiss kamar zai cinye bakin, saidal kuma cikin taushi da laushi.

Duk yadda take zaton jikinta zaiqi karbar abun sai zancan yasha banban,a duk wani saqo da ya aiketa masa sai ta samu jikinta ya karbeshi da kyau har fiye da yadda ya kamata. Yaqi ta dinga yi da zuciyarta saidai itama zuciyar tako ina lugiguita yakeyi cikin salo da qwarewa,duk da haka saboda qi fadi bata fasa yunqurin tureshi ba.

Cak ya dakata da abinda yakeyi, sanann a zafafe ya kama hannuwanta yayi musu kyakkyawan rigo yana kallon tsakiyar qwayar idanunta fuskarsa a dinke tsaf. Bai shirya ba wata qaramar dariya ta kufce masa yana sake ci gaba da kallon idanunta da suka sauya launi, tabbacio ko ta ina itama sagon yana isar mata

"Malama you are just pretending fa,amma tun daga zuciya gangar jiki dama ko ina na jikin sun nuna suna karban saqo,so stop please,let's enjoy our selves"

kunya ce ta sanvata tattarashi ta tureshi da sauran garfin da ya rage mata, baiyi musu ba ya fada gefe,sai yayi rigingine idanunsa a lumshe yana sakin boyayyen murmushi

"Okay,baki buqata ko?‚am sorry you can go" ya fada yana jan duvet ya lulluba har kansa. Minti daya biyu sannan yaji ta motsa tana shirin sauka,ya birkitota da sauri ya aza mata nauyinsa yana dariya

"Ki daina pretending din nan,ki fada kanki tsaye, kina bugatar mijinki simple and easy" bai bata damar yin magana ba ya hade bakinsu guri guda.

Bata sake turje masa ba,saidai cikin ranta ta cika da mamakin yadda komai yake kai mata inda bata zata ba. Da wannan damar shima yayi amfani ya kwance mata lissafinta tasss fiye da wancan ranar, shima dai daga

baya kukan kunya ta saki,ya biye mata yana bata haquri dariya kuma na cinsa,yayi mata kyakkyawan masauki a faffadan qirjinsa ta boye fuskarta da kyau tana kula

"Kiyi haquri,tsautsayi ne ko? ‚kuma baya wuce ranarsa" ta fahimci gatse yake mata,saita tattarashi ta ture tana sauka a gadon ta nufi qofa bayan ta lalubi rigarta da ayar. Baiko motsa ba saima gyara kwanciyarsa da yayi yana dariya qasa qasa,ya fuskanci idan ba sauketa yaci gaba da yi daga kan layi ba ba zai taba sauke mata zafin kanta a nan kusa ba

"Idan aka shiga turaka ba'a fita sai da asuba koma da safe" dole ta dakata, kamar zata saki kuka ta dawo da baya ta zauna bakin sofa bed. Kusan minti sha biyar tana zaune,har ya miqe ya shiga toilet yayi wanka ya fito.

Gajeran wando ya sanya wani cotton fari qal,ya shammaceta ya isa gabanta. Hannu ya sanya ya lakuce dogon hancinta

"Indai kikaci gaba da wannan abun bayan kun dawo daga tafiya tabbas aure zan gara" daga haka bai jira komai ba ya sunkuceta ya wuce gado da ita. Tas ya tube rigar data sanya ya kuma matseta cikin jikinsa yana lullubesu da duvet tare da sakin wata sassanyar ajiyar zuciya. A duk sanda ya samu wani mu' amala tsakaninsa da ita yanajin duniyarsa kamar ta banbanta datà kowanne dan adam,wata mahaukaciyar soyayyarta da kullum yake goqarin ya saisaita kansa da ita kada ya wuce gona da iri qara ninkuwa takeyi cikin ransa. Yayi imanin batasan me yakeji tattare da ita bane,da duka ta sauke abinda takeji din akansa. Can qasan maqoshi tsakiyar kunnuwanta ya furta a hankali

"| always sleep better with you by my side,gobe da sauran kwanakin bansan ta yadda zanyi bacci me dadi har haka ba,to be honest,at this point in my life, i just need one women to love me hard, and never leave me alone" ya furta da alama har cikin zuciyarsa abinda ke ciki din kenan. Kashe mata jiki kawai yayi gaba daya,saita lumshe ido kawai ba tare data sake motsawa ko tace komai ba.

Da asuba ma bai ayaleta ba,kiran sallar farko taji ya sake cewa

"I want to water the plants" bata sake tunani na biyu ba ya sake wurgata wata duniyar,yayi alqawarin sai ya bar mata abun tunawa tun daga tafiyarta har dawowarta,muddin baiyi hakan ba ya tabbata looser,bai kuma amsa sunansa na Muhammad toufeeq ba,yaci alwashin goge mata haddarta fes da duk wani daagiya tata da qi fadinta.

****Qarfe tara na safiyar ranar suna a filin sauka
da tashin jiragen sama na mallam aminu kano.
Yana rige da hannun fadeela,fuskarsa da safiyar yau din ke cike da annuri cikin shigar farin yadi na maza me taushi wanda yake da shara shara har kana iya hangen fara qal din vest din jikinsa,ginannen jikinsa dake a tsaye qyam ya zauna cikin dinkin ya kuma dace dashi.

Sassanyan kyansa me cakude da kwarini ne shimfide akan fuskarsa,zubin halitta da kyansa kuma yana ci gaba da fusgar hankalin duk wata diya mace.
Sãahar na tsaye a gefe cikin doguwar riga sakakkiya sosai wadda ta yiwa rolling da mayafin da ya sauka har mazaunanta ya rufesu sosai,shiga ta biyar kenan da tayi a safiyar kafin ya danne zuciyarsa ya haqura aka taho a hakan.

Haka kawai yau din ta samun kanta da satar kallonsa,kyakkyawan murmushin sa da wani irin aji cikin maganarsa da aikinsa. Karo na barkatai idanunta ya sauka akan fuskar 'yammatan dake facing dinsu,ta sake samu idanunsu a kansa dukka su biyun. Janye dubanta tayi daga kansu tana jin wani abu yana tsaye mata a wuya. Sake maida kallonta tayi kansa a sace,sai takejin babu dadi cikin ranta, tunda suka fito cikakkiyar magana bata hadasu ba,yayi ma kamae baya ta tata, dukka attention dinsa na kan fadeela.

Zaman gaba daya taji baiyi mata ba,kallon da matan dake gurin suke masa taji ya fara hawa kanta,duk da wani sashe na zuciyarta nason qaryata hakan, amma tabbas tasan she's not comfortable. Ajiyar zuciya ta sauke sanda lokaci da zasu wuce zuwa ciki yayi. Sai a sannan ya waiwayo suka hada ido,sai ta janye idanun nata gefe tana tura baki gaba wanda ita kanta batasan tayi ba,a qasan ranta tana cewa

"Dan rainin hankali sai yanzu yasan ina wajen" shi da fadeelan suka qaraso gurin,ya miga hannu a tausashe ya rigo nata hannun yayi kissing sannan ya dage hannun sama alamun yanason miqar da ita. Kamar ba zata tashin ba, amma idanun mutum biyun nan da sukafi kowa baci a gurin ta fahimci yana kansu,sai ta samu confidence sosai na miqewar, tana kuma miqewar ta fada jikinsa tayi hugging nasa tightly.


Zafafa biyar
🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥
🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥

*HUGUMA*


*_TABARMAR KASHI *

Book 02Page 47

To dama shi din me neman kuka ne aja jefeshi da kashin awaki inji hausawa lea, maida hannuwansa yayi ya rufeta ruf

"Na baki amanar kanki da kanki, kiji tsoron Allah ki kulamin da kanki,Allah ya sani na barku kuyi tafiya ne a bisa harshen maji, saboda duk duniya babu alfarmar da zata roga na kasa yi mata, ki kularmin da amanar kanki da kanki,i love you and am gonna miss you" wadan nan sune kalaman da suka yiwa säahar abokan zama har cikin jirgi. Yana tsaye bai matsa a gurin ba har jirginsu ya tashi,ya kuma nausa dasu qasar Germany ba tare da Muhammad toufeeq jarma yasan abinda zasuje yi can ba.

_tofa, Allah ya kiyaye tsautsayi da asara,muje zuwa
dai,munata gangarewa_ 😃


*_GERMANY_*


HOMBURG


Zweibrücken Airport_


K'arfe biyu agogon qasar Germany jirginsu ya
sauka a Zweibrücken airport dake homburg, bisa
jagoranci da kulawar asibitin wanda sajjad ya hadasu da dukkan wanda ya dace da zai musu jagora akan komai kafin isowarsa da ya shirya yi ba tare da ya gayawa sãahar din ba suka sauka a leaonardo hotel dake kusa da Saarland university hospital main campus, inda anan ne suka suka shirya ganin prof Dr med Klaus fassbender wanda shine shugaban department na neurology and epileptology na jami'ar gaba daya.

Miss Sophia da mr Stephan sai da suka tabbatar da komai yayi settling, hatta da layin wata na kira suka bata sannan suka ce su huta, sai zuwa gobe ne appointment dinsu da Dr Klaus.

Ta window din dakin hotel dinsu akwai kyakkyawan view na garin Saarland,ta fidda kayansu tana ajjiyewa a inda ya kamata, ita kuwa fadee na daga can tana kallon garin tana zuba mata surutu har ta gama,gamawarta nata yayi dai dai da isowar ma'aikatan restaurant na hotel din da lunch dinsu.

Karba tayi tayi godiya ta rufe qofar tare da kiran fadeela tazo taci. Kusan duk wani motsi na fadeelan na kan idanunta,zuciyarta nata karyewa,sai a yanzun takejin kamar tayi wauta data taho gari ya gari ita daya da yarinyar mutane, zuciyarta a raunane tana duban yarinyar,Allah shine masanin gaibu, zata tashi ko kuma komai zai sake rikicewa ne?,ko kuma ita zata zamo sila na garuwar ciwon nata?. Da sauri ta kawar da wannn tunanin ta hanyar kiran sunan Allah, ta sauko ta jawo abincin suka fara ci tare.

Ko da suka kammala layin ta saka a wayarta,afifa ce mutum ta farko data fara kira sannan maama dinta,sai kuma mahaifinta Dr girema

"Baki kiramin abby na ba" fadeela ta fada tana karyar da kai. Dan murmushi ta saki tana juya wayar a hanunta,fadeela nason sakata yin abinda batayi niyya ba, amma tausayin yarinyar takeji, kowanne motsi na yarinyar tausayi yake bata,ta kuma kawota qasar da babu kowa nata sai ita,itace uwa da ubanta,to amma bata da tabbacin tana da number nasa a wayarta,don haka ta fara kiran nadeeya.

Kiran nadeeya din shi ya dauke hankali fadeelan daga kiran abby din,suka dinga hira kafin daga bisani sãahar ta karba wayar

"Nadeeya ki turawa fadee number abby" dariya nadeeyan ta saki a boye

"Fadee ko ummin faddee, aunty N kada dai ace har kin fara missing yaa moha?"

"Kinga sister nadeeya,kin fara rainani ko?"

"Tuba nake aunty N,waye ni da raina matar babban yaaya,so kike yayi tamaula da ni?, already na miki saving number din nasa a wayarki saboda rana me kama da wannan" sai kiran ya yanke. Wayar kawai ta sauke tana kalla,sai kuma murmushi ya subuce mata, yaushe har nadeeya din tayi saving number bata sani ba? ,sal ta fara binciken contact nata, amma ku suna me kama da nashi babu,daga qarshe tayi finding out suna guda daya da iya saninta dai ba ita tayi saving number din ba FOREVER. A bisa dole ta saki dariyar da batayi niyya ba,ko yaushe ya zama forever din oho?. Tana shirin editing ta canza suna taji fadeela na kiranta tazo ta kunna mata tv,dole ta ajjiye wayar ta fita gurinta.

Washegari miss Sophia da mr Stephan ne suka sake dawowa, already ta shirya saboda tasan da zuwan nasu. Tun daga yadda suka samu asibitin ta tabbatar afifa ta zaba musu gurin da yafi dacewa. Sun gana da Dr Klaus ya kuma yiwa säahar dukkan tambayoyin da suka dace,ya shirya komai ya kuma bada gwaje gwajen da za'a fara yi mata kafin a fara zancan surgery.

Cikin kwanaki hudun duka basu wani zauna ba,ta bada hankalinta dari bisa dari akan aikin fadeelan da zirga zirgar asibitin, don ma wasu abubuwan da yawa basu zasuyi ba daga asibitin ne. Kwana take saman abun sallah tana addu'a,sunyi waya da maji tun randa suka iso da daddare, kuma daga ita har afifa suna samun update na yanayin da ake ciki, dukansu kuma neman visa ta shigowa Germany sukeyi kafin ranar aikin,saidai dukansu basu gaya mata ba.

Cikin kwana biyar kacal komai ya kammala, Dr Klaus kuma ya tabbatar mata part na brain din fadeelan dake bada matsalan seizure din nata za'a iya removing nasa,so ta cancanci surgery, amma kafin nan zasu bata treatment na sati biyu, zasu rigeta a asibitin. Kukan farinciki ne ya qwace mata, bakinta ya kasa gajiya da addu'a da fatan samun nasara a gareta da fadeelan baki daya. A ranar suka bata daki da komai da komai, su zasu dauki nauyin kula da ita,basa buqatar majinyaci,akwai qararrun ma'aikatansu da zasu bata duk wata kulawa data dace. Tayita roqon alfarma su barta gurinta amma suka bata haquri kan haka tsarinsu yake,dole a ranar ita kadai ta koma hotel, saidai sam bacci yaqi zuwar mata,kewar fadeelan takeyi sosai,sai tayi alwala ta hau abun sallah kawai ta tsaya gaban ubangiji.


******Bai taba kawowa zata dauki wadan nan kwanakin ba tare data nemeshi ba,cikin kwanakin gaba daya karsashi da komai nasa ya ragu,yana jin kamar yayi missing wani part na jikinsa, komai yana yinsa ne kawai cikin qarfin hali da juriya,bai taba kawowa cewa ta kama zuciya da rayuwarsa har haka ba sai a wannan lokacin

"Wanann wanne irin abu ne?" Ya tambayi kansa da kansa a wani dare da bacci ya qauracewa idanunsa. A nutse ya miqe ya sauka daga saman gadon nasa,yana sanye da wasu silk pyjama bagaqe da suka fitar da zallar kyansa cikin hasken dakin da bashi da yawa,yana bugatar wani abu da zai debe masa kewarta,yana jinsa kamar mara lafiya, kowanne sashe na jikinsa yana bugatarta. Slippers dinsa ya zura,ya miqa hannu zai dauki wayarsa dake kan bedside drawer sai wanilabu yaja hankalinsa. A nutse ya miqa hannu cikin wani glass bowl dan garami ya dauko wani abu. Dan kunnenta ne,dan kunnen da ya fadi a wancan ranar cikin elevator,a wancan lokacin da yake matuqar jin zafi da haushinta, zafin da ya tabbatar yana jinsa ne a sannan saboda yadda zuciyarsa ta kasa jin qinta a ransa kamar vadda yakejin na sauran mata,yana tsoron faruwar wani abu tunda har zuciyarsa ta kasa jin wannan emotion din a kanta sai wani feeling na daban. Wannan abun dai da yake gudun faruwarsa sai gashi a yanzu ya tsinci kansa dumu dumu a cikinsa, dumu dumu din da ko gefenta bai taba isa ba sai a wannan lokaci, mummunan kamu na soyayya me wahalar cirewa a rai, soyayyar da ya fuskanci tamkar tanason jefashi zuwa ga son maso wani. Yana shaugi da burin ganin martani me zafi daga kan fuskarta,duk da ya sanya zuciyarta tayi laushi yadda ya kamata, amma mizanin soyayyarsa a zuciyarta yana hasashen kamar bai kai ba,yana tsoro da fargabar sake, afkawa wani ramin da baisan iyakacin zarfinsa ba a kanta. A kullum ya tuna kulawa da tattalin da ya bawa ameesha da sakamakon da ya samu daga baya sai gwiwarsa ta karye akan lamarin soyayya. Kissing na earring din yayi, sannan yasa hannu ya jawo drawer din ya zura,baikai ga rufewa ba dairy dinta daya dauko yaja hankalinsa.

Qasan ransa ya gayawa kansa ya samu abun debe kewa,sai ya fiddoshi yana budewa,ya sake bude page din farko ya maimaita rubutub rannan, sai ya zare slipper din da ya sanya ya maida jikinsa kan gadon ya zauna sosai vana sake bude next page.

Kai tsaye a kuma tsanake ya fara bin rubutun dake shinfide cikin tsari da kuma qwarewa, tun daga farkon haduwarta da ADAM,a nan ya dinga gaza jure wasu abubuwan ya dinga jin wani abu me kama da zallar kishi yana tabashi saidai zuwa sanda zai kammala karanta labarin zuciyarsa da ma gangar jikinsa sunyi tubus

_Thats me,hurt in private, heal in silence,we fall, we learn we rise_

_My dear heart,one day you will heal to such an extent that you will smile as if it was never broken in sha Allah_


“In sha Allah" din shima ya maimaita a bayyane yana rufe bangon qarshe na littafin,fararen zagayayyu idanun nan nasa sun canza launi, kwanyarsa ta cika da abubuwa masu tarin yawa,ya mots lips dinsa a hankali

"We are all hurting and healing in silence, tabbas we go through one similar condition, i have made many errors in my life,but loving you is definitely the thing i have done right!" Ya furtawa kansa da kansa yana lumshe nasa idanun,tashi madubin rayuwar na haska masa,cikin jiki da zuciyarsa wani irin gamammen aminci da kanta yana gauraye jinin jikinsa, da gaske! Allah yaso wanke musu kowanne bacin rai da suka shiga,shi yasa ya jarrabesu a mabanbantan gurare da kuma mabanbantan mutane. Hikimarsa!, Ya hadasu zaman tare na har abada a sannan shine zasu Fi fahimtar muhimmancin funansu

"Exactly!" Ya fada yana bude idanun nasa. He really missed her,yana jin kamar zai zauce da son ganinta, me yasa tun tuni bai karanta diary din ba? ‚sai yanzu da tayi nesa dashi.

Saman gadon ya zauna sosai yana duba number dinta, saidai duka kiran da zaiyi matan a kashe layin,ya sani dama ba samunta zaiyi ba,kawai idanunsa sun rufe ne da son jin muryarta.

"A ina zai samu number dinta?" Itace tambayar dake masa yawo akai. Har zai kira nadeeya ya tambayeta sai kuma ya fasa gudun raini. Maji ya tuna, don haka ya maida akalar kiran nasa gareta, KARON FARKO da wani qulli ya warware daga tsakiyar kansa ba tare da ya sani ba. A dai dai lokacin kuma hajiya qarama tayi wata mummunar firgita cikin baccinta,ta kuma miqe ta zauna sosai saman gadonta a gigice tana dube dube.

Fadeela ta gani cikin asibiti, asibitin ya cika da yan uwa da abokan arzigi wai ana tayata murna ta warke daga ciwonta,yarinyar tana ganinta ta karbi wuga daga hannun säahar dake yanka mata fruit tayo kanta da gudu, tana tsaka da gudun ta farka a mafarkin.
Jikinta sharkaf da gumi ta sauka daga gadon,ko ina na jikinta rawa yakeyi tanason ta fassarawa kanta da kanta mafarkin. Kai tsaye ta isa drawer din data killace magungunan da take sauyawa fadeelan dasu,ta fiddosu gaba daya ta fito falonta dasu.

Zaman dirshan tayi saman carfet ta zazzagesu,ta kuma hau irgasu daya bayan daya tsaf har ta gama

"Turqashi" ta fada a bayyane tana goge gumin fuskarta.

Yau kwana d'ai d'ai har kwana sittin bata samu damar bawa fadeela maganin ba

"Ko warkewar ne ma a gaske ai sai tayi, tunda na zauna yarinya qarama tana son firgitani da kawomin tsaiko akan aiki na" ta fada a fili kamar wadda ke magana da wani.

Tattara magungunan tayi ta maida cikin leda tana rayawa a ranta yanzun nan komai duhun dare sai ta isa dakin fadeela ta aiwatar da shirinta.

Daxu daxu ta dawo daga Cotonou order din wasu atamfofi,bata da masaniyar ma fadeelan basa gidan yadda ta saba ba,sai kawai ta sauka a sashenta tana huce gajiya.

Mayafi ta yafa,ta kuma taka a hankali ta fita a sashen nata. Farfajiyar gidan tsit take,babu kowa sai hasken fitilu da kuma kukan

Please Login or Register in order to submit comment