Reading TABARMAR KASHI 1&2 complete by SAFIYYA HUGUMA Chapter 40 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da zaizo ya rusa tsarinta ba dai dai da qiftawar idanu, bata taba kawowa wata mace zata shiga rayuwar toufeeq ba baya ga hassenarta wadda aka fi sani da MEENAL YA'AQOUB AJI,saugin abun har yanxu ta tabbatar meenal din bata san da zancan ba,don ko jiya sunyi waya kuma lafiya lau suka gama sukayi sallama.

Sautin qarar wayarta ya tabbatar
mata da shigowar kira wayarta,ko da ta duba taga sunan baby na kamar yadda tayi saving number meenal haseena sai da gabanta ya fadi,ta zauna sosai tana daga wayar da hanzari,don jikinta ya bata ta faru ta qare.

Yadda ta zata din kuwa haka ne,kukan meenal haseena kawai ya tabbatar mata da zarginta,cikin hargagi da daga murya da muryarta da tayi sirantaka da yawa har take bada wani irin amo da ba kowa yakewa dadi ba

"Momy? kina ina akaci amanata?, kina raye kuwa momy?"

"Ina raye baby meenal,ki kwantar da hankalinki,ba wani abu bane babba"

"Ta yaya zakice ba babban abu bane,bayan next week zaiyi aure? zai auri wata bani ba,bayan kinyimin algawarin bazai sake auren kowacce diva mace ba bayan ni?,yanzu duk zaman da nayi shekara da shekaru ina jiransa ya tashi a banza?,duk wani buri na da naci a kansa ya zama mafarki?"

"Haseena!"

"Momy!!! ba abinda zakicemin,na dauka ina da uwar dana wuce nayi kuka na zubda hawaye na? ta isa ta sharemin kowanne kuka nawa ashe kuskure nayi!"

"Meenal ki saurareni mana,kin manta wacece fauziyya?,kin manta waye toufeeq a wajena?,ubansa ma ya yake a gurina barshi?" Maganar ce ta sanya meenal din yin shuru,saidai har yanxu bata fasa kukan da takeyi ba

"Wallahi momy idan har ban auri yaa toufeeq ba mutuwa zanyi"

"Indai kinga baki aureshin ba saidai idan bana raye,ke ko bana raye saikin aureshi,shine mijinki" hajiya qarama ta maimaita da confidence,tana ajjiye wannan alwashin har tsakiyar zuciyarta

"Wani ma yayi rawa bare dan makadi?,bani da qwai a duniyar nan fa sai ke,ke kadai na mallaka kuma duk duniya babu wanda nakeso kwatankwacin yadda nake sonki,idan ban sama miki farinciki da jin dadin rayuwa madawwami ba me nayi kenan?,koda tsiya koda arzigi saikin mallaki muradin ranki,ki rubuta wannan ki ajjiye,alqawari ne dauka"

"Ki tabbatar kin cikashi momy,saboda komai zai iya faruwa,inason na auri yaa toufeeq a watannin da muka riga muka tsara tun farko,bazan iya jurewa rashinsa na tsahon wani lokaci ba,bazan iya jurewa ganinsa da wata mace ba bayan ni"

"Ki kwantar da hankalinki ki kammala exams dinki,sati biyu fa kacal ya rage,a satin bikin ma zan miki booking ticket,ko Dr jarma banason ya sani,saidai kawai suga isowarki"

"Thank you momy”

"Naji,amma haka zamu rabu kina wannan kukan don kawai ki hanani sukuni?"

"Na daina"

"Kin tabbatar?"

"Kinsan idan na fadi abu bana canzawa ai"

"'Yayi kyau,ki huta da kyau" . Wani qaimi taji yana shigarta tare da karsashin son ganin ta gudanar da komai,don haka ta sake migewa tana qarasa hada kayanta,tare da duba jirgin garfe nawa zata bi.

********Tun daga saukarta farkon layin zuwa shigowarta cikin gidan hankalinta ya soma tashi,ta sake tabbatarwa eh lallai aure MT JARMA zaiyi,irin auren kuma dake nuna cikin wadata da tarin arzigi za'a yishi,ba irin aurensa na baya ba. Abinda ta lura dashi cikin nutsuwa da zurfafa dubanta akan kowa,kamar kowa fuskarsa dauke take da annuri da farincikin auren,komai na gidan an canzashi an sake masa fasali da tsari, hatta da uniform na ma'aikatan gidan kuwa. A ranar kasa zaune tayi ta kuma kasa tsaye,hatta da fadeela da nadeeya bata samu ganinsu ba a ranar,don ba'a basu zama ba,yaa moha zai dawo musu da masoyiyarsu,a wannan karon da a sunan nanny ba,a sunan MATARSA ta sunnah.

Tanason ta fita don fara aiwatar da wasu abubuwa,amma baqin da aka fara yi a gidan da abokan kasuwancinta da suketa zuwa ganin kaya sun hanata motsawa,komai kawai yinsa takeyi ba cikin nutsuwarta ba,tana da bugatar zuwa ta sabunta tsonon aikinta,don dama an jima ana gargadinta akan hakan, bata fuskanci da gaske bane sai da taga kwabarta tana shirin yin ruwa. Komai a quntace take yinsa cikin yage da tsabar duniyanci wajen iya boye damuwa da tashin hankali ta kuma bi sahun 'yan murna da Allah ya sanya alkhairi.

*_KALLON KALLO *
👀👀👀
*HUGUMA*


* _TABARMAR KASHI*

Book 02 Page 10

*_KALLON KALLO_*👀👀

Hantsi ne wanda yazo mata a birkice,irin birkicewar da bata taba hasasota ba. Tun safiyar data tashi take jinta sukuku,amma ta danganta hakan da fitar da taketa son yi jama'a na tsaidata,saidai ta yanke a ranta gobe komai matsi taje din,don da zafi zafi ake dukan qarfe. A safiyar a daki tasa aka ajjiye mata breakfast dinta ta tsakura ta ajjiye,saboda kullum damuwa ce ke narkewa a zuciyarta,yadda taga dan uwanta Mahmud jarma ya dauki lamarin auren nan sai yake sake sakata cikin tashin hankali. Kamata yayi ace dukka wadan nan shire shiryen da zumudin akan auren toufeeq ne da meenal
'yaruwarsa,ba wai akan wata nanny ba. Da wannan baqinciki ta kwana ta tashi,da gyar ta samu wajen sha daya da rabi ta shiga wanka,ta fito ta shirya kamar kullum cikin shigar alfahari da fariya na wani dandaqegen lace,ta cika jikinta da turare,ta fito don ganin meye kuma yake gudana cikin gidan gaba daya,wanda kusan wannan din al'adarta ce,komai na gidan idanunta suna kai tana biye dashi saidai idan bata qasar tayi tafiya.

Tana takawa ne cikin jin izza tare da yadda take samun komai yadda takeso,idan ka cire yadda al'amuran a yanzu suketa son yi mata gardama,wanda ta tabbatar sako sako da dauke mata hankali da neman kudi sukayi shine musabbabiyyar faruwar hakan.
Zuciyarta a cike fal da qunar yadda gidan yake kasancewa kullum cikin hada hada da kai kawo jama'a,duka a shirin fara gudanar da bikin da batasan da meye yafi saura ba?,tana tsoron ma a qare dukka shagalin akan wannan auren data sanyawa suna MATACCE,azo bikin shalelenta abubuwa sugi armashi saboda komai an gudanar dashi a wannan.

Dai dai sanda take isowar farfajiyar gidan,biyu daga cikin security din gidan na qoqarin bude qofar gidan,sai ta tsaya cak tana jiran ganin su waye?

Wasu laflyayyun range rovers ne guda uku,biyu daga ciki ta sansu farin sani,mallakin toufeeq ne. Tunda ya siyesu suke ajjiye bai hau su ba,to amma ya akayi yau aka fiddasu daga gidan?,ina akaje dasu bata da masaniya?.
Waiwayawa tayi tana gogarin kiran daya daga cikin me kula da motocin gidan,saidai kowacce kalma dake bakinta ta qafe tas!,cikin sakannin da basu haura biyar ba yawun bakinta ya dauke,wani abu me nauyi da girma ya daki kanta,abinda ya sanya mata dawo da dubanta zuwa gabanta a hankali kamar me ciwon wuya.

Cikin wata lafiyayyar abayar take blue black. lya adon jiki kadai ya isa ya gaya maka daga wanne gabila da kuma kalar nau'in ahalinta

"alhamdulillah,alhamdulillah,a'uzu bi kalimatillahit taammati minsharri ma khalaqa,Allahumma anzil ni munzalan mubarakan wa'anta khairul munzaleen" addu'o'in data furtasu dukka a bayyane kuma daki daki,cikin nutsuwa ta haqiga,addu'o'i masu qarfi da tsananin tsari.

Wata mummunar faduwa gaban hajiya qarama yayi,ta runtse idanu da kyau tana kuma budesu,suka sauka fes akanta SHIFA
CE,maji,matar yayanta Mahmud,bayan shudewar shekaru talatin da wani abu,sai yau gata a gabanta,sun hade cikin gida daya,sun hade cikin gidan toufeeq,toufeeq din da tace ta sanya a ranta ita ta haifarwa saidai ta haifi wasu a gaba shi da nadeeya,toufeeq din da tace itace dashi har abada...
...kai alwashin
da taci suna da yawa,wasu lokaci yayi mata halacci ya bata damar cikasu,wasu kuwa har yanzu walagigi takeyi sun kasa cika kamar yadda taso.

Murmushin da ta gani saman fuskar shifa bayan isowarta dab da ita,ita da fararen danginta wanda koda baka tambaya ba zakasan cewa yes,larabawan Algeria ne shi ya sake dugunzuma hankalinta,murmushi?, murmushi fa a fuskar shifa,shin ko yawan shekaru da tsahon lokaci yasa ta manta wace ita a wajenta? ‚bata tunanin zata bari taga koda haqorinta muddin ta tuna ita din fauziyya ce

"Assalamualaikum hajja fauziyya" maji ta kawar mata da dukka wata tantama daga ranta. Ko wacce gaba ta jikinta sai data cika saboda tasirin sallama,amma kuma nuna hakan a tattare da ita babbar faduwa ce,don haka itama ta saki nata murmushin,murmushin da ko kadan bai shiga fuskar maji ba bare ya ratsa zuciyarta,tasan wace fauziyya,kuma bata tunanin shekaru zasu canza halinta

"Wa'alaikummus salam,baqi ne haka damu? marhaban bikum" wani murmushin maji ta saki har sai da farare tas din hagoranta da toufeeq ya gado suka bayyana,wanda shekaru bai ragesu da komai ba. Waiwayawa bayanta tayi kadan ta kalli 'yan uwanta da suka yo gaba,suka bar sauran suna fidda luggage dinsu

"'Baqi? baqi,nidai nafi gaban baquwa,saboda daukan ciki wata tara,naquda ta kwana biyu cur babu sassauci a gasar da babu uwa ko uba,haihuwa zuwa raino har na tsahon shekara shida....kin tuna,su kuma dukka wadan nan da kika gani,bari nayi miki taqaitaccen bayani duk da idanunki na shaida sun gama gaya miki,wadan nan sun zarta baqi,ahali ne kuma halastattun dangi ga d'ana
Muhammad toufeeq,d'a na halali ga mahmud umar jarma….mun shigo cikin gidan d'ana da
sunan Allah tare da dukkan amincinsa,zamu zauna adadin yadda Allah ya deba mana,amincin Allah a gareki" ta furta tana miga mata hannu. Tamkar an shukata haka hajiya qarama taji,tsahon shekaru yau matar da take kalla a matsayin matsala yau ta sake waiwayarta,ta yarfa mata maganganu a gaban masu aiki da dukka hadiman gidan da sukayi tsaye suna mamakin jin bayanan maji. Tunda suke basu taba ganin gilmawar wata mace da sunan mahaifiya ce ga sir toufeeq ba,kowa yana kallon hajiya qarama ne a matsayin uwar kowa,hatta da Dr jarma. Ganin ta gagara bata hannun sai ita ta kamo nata hannun ta hade guri guda a sukayi musabahar,ta sake sakar mata murmushi tana cewa

"Kada ki manta,har yanzu a mazaunin qanwata kike,saboda haka daga zamana zuwa fitata hukuncina zai iya hawa kan kowa,ciki harda ke a mazaunina na uwa ga dan da ake qarqashinsa yake bada ci da sha da suttura harda mafaka ga kowa,saina tabbatar da wanzuwar matar alkhairi a gareshi wadda zata kula da rayuwarsa sanann na sake barwa Allah shi amana,kamar yadda nayi tsahon rayuwarsa ta baya, alqawarin kuma Allah gaskiya ne,ya kulamin da su fiye da yadda zato yayi tsammani" sai ta zame hannun nata daga na hajiya qaraman,kai tsaye ta cusa kanta zuwa cikin gidan ba tare data nema jagoranci daga kowa ba.

Wata iska me nauyi da zafi ta zuqa ta kuma fesar,me yake shirin faruwa?

"Kada ki damu, kwanaki bakwai kawai zatayi idan ta dade ta koma inda ta fito,ta barki da yaran da take taqamar a kansu,ki kuma sake mantar dasu suna da wata uwa a duniya wai ita shifa har abada" wannan saqar da zuciyarta tayi mata ita ta kawo sassauci cikin ranta,sai ta juya cikin gida tabi bayan su maji din. Dole ne kamar kullum tayi amfani da kissa da kyau

Cikin hararrami ta dinga bada umarnin kwashe kayansu maji zuwa dakunan da sajjad ya shirya musu,tun a ranar hajiya qarama taga wani irin banbanci muraran,wato shi tuwo dai ba'a taba canza masa suna,daga nadeeya har fadeela babu wanda ya yarda ya saki maji koda kuwa na minti daya ne,suna maqale da ita,bayan sun gama koke koken su,don koda wasa basu taba sanya ran zuwanta ba,nadeeyan rabonta da gain majin tun kafin ta tafi makaranta karatu,yanzu haka shekara kusan shida kenan dr jarma saidai ya bata haquri yace ba yanxu ba,shi ko toufeeq sai ya dauki zancan da gaske saiya shashantar dashi har kayanta ta taba hadawa da yace mata gobe ko jibi zai siya mata ticket tabi jirgi
Zuwa Algeria,amma ranar data kirashi yana airport ma zai tashi zuwa dubai haka taci kukanta ta haqura.

A yau din da taga majin sai takejin kamar duk duniya bata da sauran wata bugata,taci kukanta qwarai,amma yadda maji din ke kwantar mata da hankali tare da jaddada mata ta yiwa yaa moha uzuri sai ta samu relief. Duk wani shiga da fita na hajiya qaraman idanun maji na biye da ita,saidai kawai tayi murmushi ta girgiza kai,koda nadeeya ta tambayeta takance

"B komai nadeeya, Allah yayi muku albarka,ya tsaremin ku"

Tun kafin ya iso gidan labarin zuwanta ya riskeshi daga bakin nadeeya da kuma fadeela data rasa inda zata sanya ranta saboda murna,yau gata ga maji. Yana toilet cikin bathtub amma zuciyarsa na wani irin daka,yana jin doki da son haduwa da mahaifiyar da tayi silar kawoshi duniya,wadda rabonsa da ita shekara gome kenan cif,amma wani irin abu me kama da toro da shakkarta yana tasowa hadi da danne wancan dokin da yake ji. A qalla ya kusa kashe awa guda kafin ya garasa wankan ya fito,ya daur towel a qugunsa yasa qarami yana sharce ruwan dake kwance cikin gargasarsa data yiwa murdadden jikinsa ado.

Cikin wani sassauqan yadi mara nauyi ya shirya,duk da ba wani zaman ado yayi ba amma kyansa ya fito ainun,rashin walwalarsa ta qaru a 'yan kwanakin saboda damuwar da dr da sailad sukeson jafeshi a cewarsa. Kamar yau din,bashi da niyyar fita amma hakanan ya fita bayan sajjad ya gama ce masa dangin amarya zasu zo su sake ajjiye wasu kayayyaki.
Wani takaici yazo masa wuya ya tsaya masa.don me za'a dinga masa shige da fice a sashe?,bayan shi ya fadi cewa bayason dukka wadan nan abubuwan amma anqi sauraronsa.
Hasalima shi sashensa ba gurin shigar kowa bane,wannan ya sanya dai dai da masu aiki kebantattu gareshi, su daya sai sajjad ke shiga masa guri. Baisan me yasa sajjad din be gyara spare part din dake gidan ba suje suyi koma meye a can,key din ya jefa masa ya tattara ya fita ko breakfast dinsa da Jacob ya hada bai tsaya yayi ba.

Flip flops slippers masu taushi ya saka,wadanda suka bayyana sirrin fara tas din doguwar qafarsa,ya jefa wayarsa a aljihu yana fitowa. A falon suka hade da Jacob wanda yake sanye da afron

"Welcome sir,the food is ready" a ga'ida ya zauna din yaci,to amma haka kawai yakejin bashi da nutsuwar hakan

"Not now i will be back" daga haka ya Sanya kansa yana fita daga sashen nasa cikin takun nan nasa na nutsuwa da kamewa.

Lokacin da muryarsa ta bada sautin sallama maji na zaune fadeela na saman gafafunta kamar zata koma cikinta,fadeela na tare dasu nawwara,houria hessa,minafah ,maysam,banaan,amjad,taraneem,tayma da saneem,kusan su sha biyar 'yan mata kamar nadeeva akazo dasu,sai manya masu dan shekaru kusan saannin maji,wasu kuma basu qarasa shekarunta ba suma sun kusa su takwas. Dukansu suna taya nadeeya shirya gifts da kayayyakin bikukuwan al'adar al'ummar gasar Algeria da maji ta shirya gabatarwa. Sarqoqi ne na wuya hannu da gafa na alfarma,dukkansu na gold,coins na gold da kuma wasu irin velvet gown tare,pakistani bride gown masu azabar kyau da tsada,wanda aka samar daga zare mafi tsada da kuma daraja,tare da wasu duwatsu masu tsada.
Ga trousseau package dake dauke da dukka nau'in jewellery na gold da zatayi amfani dasu throughout bikin gaba daya. Kudi sosai marasa misali maii ta kashe, kamar yadda tayi gayya sosai ba tare da jin kudin jirgi ba,duk da kusan kowa shi ya yiwa kansa kudin jirgi,banda
'yammatan da tace suna wuyanta,family ne da sukayi suna a qasar,saboda sun hada komai malanta da kuma dukiya. Dakuna manya manya guda biyu masu girman gaske a wadace ya ishesu,aka zuba musu kuma dukka nau'in abinda zasu bugata bisa jagorancin baaba ramatu data kasa zaune ta kasa tsaye,takaicinta ya cika zuciyar hajiya garama,saidai babu damar yin magana ko wani motsi kada abinda ke lullube a zukata ya bayyana.

Kusan babu wadda idanunta bai sauka a kansa ba cikin 'yammatan,zukatansu suka fara raurawa.wasu suka samu nasarar kau da kawunansu,wasu suka kasa,tamkar babu tsala tsalan mazan larabawa a Algeria.

Kallon kallon suka yiwa juna shi da maji din,kowa a cikinsu zuciya na motsawa da wani irin yanayi,kewa da soyayyar d'a da mahaifi ta fara aikinta. Duk yadda maji taso daurewa saida qwalla ta cika idanunta,amma tayi namijin goqarin hanasu zubowa duk da basu koma ba. Ta tafi tabar moha din nata dan qanqani a gabanta da qananun shekaru,sai gashi yau ya bayyana a gabanta a matsayin magidanci harda d'iya. Nadeeya ce ta janye 'yanmatan suka fice bayan sun gama gaidashi,sunata daburtawa su sa nadeeya,ita bata qware a larabci ba,su kuma hausar tasu duka kame kame,kai tsaye ma idan kace basu iya ba bakayi kuskure ba.

*HUGUMA*


* TABARMAR KASHI_*

Book 02 Page 11

Wani irin mugun sanyi dukka qafatunsa sukayi,cikin nutsuwa yake takowa gabanta bayan ya sake jaddada sallamarsa kansa a qas,yana jinsa a matsayin wani gagarumin me laifi. Qoqarin zubewa yake a gabanta amma sai ta miga masa dukka hannayenta,baiyi jinkiri ba ya sanya nasa hannuwan a ciki,tayi masa mazauni a gefanta fuskarta dauke da murmushi me hade da hawaye

"Kar kace komai,basai ka nemi gafarata ba,na riga nayi maka dukkan uzuri har a gaban
Allah,na yafe maka kai da dukkan zuri'arka"

majin ta fada tana dauke hawayen fuskarta lokacin da yake zaune a gabanta kansa a qasa har yanzu ya gaza cirashi,yana jin kan nashi yayi masa wani irin nauyi,kunya da nauyinta suna cikashi. Dai dai lokacin hajiya qarama ta hadiyi yawu da gyartaja da baya a hankali ta koma inda ta fito, zuciyarta na wani irin gonewa

"Bani labarin yadda rayuwa ta kasance" ta fada tana sakin murmushi,abinda ya sanyashi daga kansa,ya sauke idanunsa cikin na mahaifiyarsa,wani siririn murmushi ya sauka saman miskilar fuskarsa.

**********K'arfe biyu da rabi na ranar juma'a,babban masallacin juma ar dake iya daukar dubban jama'ar musulmai a wannan ranar a cushe yake da garin baqi daga qasashe daban daban da kuma garuruwan dake QASATA Nigeria domin halartar shaida daurin auren MUHAMMAD TAUFEEQ JARMA da amaryarsa KHADIJA MUHAMMAD
GIREMA,bayan gama daura auren AFIFA
AHMAD da MUHAMMAD SAJJAD a asalin garin mahaifinta da dr mamman yace lallai aje tushenta ayi don karramasu.

Duk yadda takeso taii cikin ranta da jikinta cewa yau din ba wata rana bace ta daban da dukka sauran ranakunta na rayuwa ba,yau din sunanta amarya a karo na biyu dukka taron al'ummar dake gidan da masallacin sunzo ne don su shaida ta zama matar MT JARMA hakan ya faskara,tana gayawa kanta akasin hakan zuciyarta na jaddada mata qarya take fadi,a haka ta dinga jin rauni,raunin da yakai ga zubar hawaye a idanunta masu yawa da zafi.

* MUHAMMAD TOUFEEO RESIDENT *

Kai kawo takeyi cikin dakinta,wanda a qalla ta kusa awanni biyu cur tana yinsa ba tare data zauna ko kuma ta huta ba.
Tashin hankalin da take ciki ya zarta duk yadda hankali zai iya dauka,ya kuma shafe tunanin me tunani. Asara mafi muni tare da faduwa muraran take gani a gabanta,a dai dai lokacin da tafi bugatarsa a dai dai lokacin da mummunar labarin shudewarsa ta sameta?,batasan haka zata faru da ita,batasan haka zata kasance ba,da babu shakka ba zata bashi baya har na tsahon shekarun nan ba.
A nata ganin da hangen bugatarta ta biya,ya kuma tabbatar mata da cewa qulli me dan karen garfi da warwarewarsa ba'a nan kusa ba,nasara biyan bugata da cikar muradi suna ta zuwar mata fiye da yadda tayi zata,hakan ya sake bata qaimin bazama cikin duniya,taci gaba da rayuwarta ta kuma karbeta a yadda tazo mata tana moreta yadda ya kamata.

Knocking qofarta a kayi,a mugun fusace take,don haka har ta buda baki zata tambaya cikin zafi,sai kuma ta tuna,a yanzu gidan yana cikin yanayin da bai kamata ta bari aga alamun matsala ko wata damuwa a tattare da ita ba,wanann yasa ta furzar da iska sannan tayo tattaki ta bude qofar.

Hajiya mansura ce,ita da hajiya qaraman sukayiwa juna kallon kallo,duk mutumin da ya sansu a shekarun baya,a yanzu idan yaga kallon da sukewa juna zai garyata hakan,duba daya kacal zaka yi musu ka tabbatar da abubuwa masu yawa dake qunshe a zukatansu. Abubuwa biyu itama ke neman zame mata barazana,labiba dake neman zauce mata saboda auren toufeeq,ga kuma saukar shifa a nigeria,labari mafi muni ga kunnuwanta. Abune da bata taba kawoshi ga ranta ba,saboda tana da tabbaci daga gurin masu bata tabbaci.
..ita da Nigerian
har abada,tamkar yadda jinjiri yake barin cikin mahaifiyarsa. Ita kadai tasan abinda take gani take kuma karanta daga gurin Dr jarma,bai cancanci shifa ta shigo Nigeria ba ma sam a irin wannan lokacin

"Amarya na dab da shigowa cikin gidan nan,ya kamata a ajiye zafin rashi ko ayi abinda ya dace" sarai ta fahimci mansurar magana take danqara mata,amma sai ta sake mata wani murmushi,saboda ta tabbatar tana wasa ne kawai da wuta me tsananin ruruwa da azabar turiri cikin rashin sani,tayi imani bata gama sanin ita din wacece ba,da tabbas! batayi wasa da ita har haka ba,saidai kuma zata dandana kalarta ta ainihi, wala'alla a nan gaba kome irin sunanta ta gani da gudu zata gusa daga wajen

"Karki wani damu,dama ni nafi cancanta da karbar matar toufeeg" hajiya qarama ta amsawa mansura. Ciki ta juya tana duban suturar jikinta. Girman kanta ne ya motsa,taji tafi gaban fita haka,don haka ta bude makekiyar closet dinta ta fara laluben suturar alfarma.

llahirin jikinta lullube yake da wata irin
suttura da aka yiwa dinki na mussamman da lafiyayyen yadin silki me tsananin tsada da daukar hankali,sannan akabi adon doguwar rigar silk din da wata rigar me zubin alkyabba ta baqin yadin velvet me adon zaren da aka tsomashi cikin ruwan gold. Tun daga nesan nesa da ita hancinka yana iya jiye maka kwantaccen qamshi me tafiya da tunani da takeyi,ba abinda ke fita daga jikinta sai wani irin haske da walwali ke kashe idanu. Babu abinda ake iya gani a jikinta,sakamakon yanayin shigartata daya rufe ko ina nata ruf,rufewar data bata damar yin kuka me yawan gaske ta qasan hular rigar da aka
Tullubeta da ita. Ba abinda ke mata yawo a tsakiyar kanta sai nasihar Dr girema,maama yaa muhyi yaa Saifullahi da yaa zaid,da kuma shaqigan 'yan uwa sannan masoya irinsu anty farheen anty samreen.

Can cikin jikinta take jin wani yanayi me kashe zuciya, maganganun da sukayi mata sun shiga jikinta sun kashe duk wani karsashi da rashin damuwa da auren,sun dora mata nauyi me yawa, kalaman da suka furta a gareta,banda tana da aminci da afifa zata ce tabbas ta gaya musu manufarta a auren.

Ido ta lumshe tana jin wata
matsananciyar fargaba lokacin dajerin gwanon lafiyayyun motocin dasuka daukota suka fara cusa kai cikin gidan,a baya qaddara ta sanya ta shigo gidan a sunan nanny,a yanzu a karo na biyu qaddarar ta sake dawo da ita d sunan matar aure kuma matar me gidan,abinda ko kadan bata taba tunanin faruwarsa ba.

Wani irin yanayi taji yana bin sassan jikinta lokacin da hannunta ya game da na hajiya qarama da ta karbeta daga hannun yakura yayar Dr girema,zuciyarta ta motsu lokaci guda. Haka kawai takeiin matar kwata kwata bata kwanta mata ba ko kadan. Saidai har suka doshi sassan da ita kanta sãahar batasan wanne bane saboda kanta na lullube tana iya tsintar muryarta fes tana sake marabtar danginta

"Maji tace a wuce da ita sashenta ta huta,ita
'yar gida ce a gurinta basai an bata wahala ba,kuma ko yaushe zasu kasance tare" sagon da baaba ramatu ta matso ta shaidawa hajiya garama kenan qasa qasa. Kai ta jinjina,a gasan ranta zuciyarta tana bata tabbas akwai dalilin da yasa shifa ta aikata hakan,amma koma meye har yanzu sauran akaloli suna hannunta,kuma ita zata ci daga da yin nasar kamar yadda tayi a baya.

Tunda ta tsoma gafarta a sashen jikinta da hancinta ta TABBATAR mata wani guri ne daya banbanta da kowanne sashe na gidan,guri ne me tsari da koda idanunta suna a lullube amma hakan bai hanata ganin lallausan carfet dan gasar turkey da qafafunta ke nutsewa a ciki ba. Qamshin da wajen ke fiddawa kawai ya isa ya saukarwa da zuciya tare da ruhi salaama,uwa uba dukka hayaniyar gidan sam sam babu ita a nan,bisa alama ma sun baro mutanen dake dauke da hayaniyar a can baya,sai wani irin shuru da sautin muryoyin da basu wuce biyar zuwa shida ba dake magana da sauti mara hayaniya.

Bata gushe ba tana biye da hajiya qarama dake ci gaba da cusa Kai zuwa hallway din da dakunan baccin sashen suke a jere,wanda aka sake narka kudi aka masa mugun gyara na fitar hayyaci,duk kuwa sa cewa babu abinda ya sameshi, amma a yanzun an masa gyaran da zai dace da rayuwar maaurata.

Zuciyarta dake qirjinta takejin kamar ana hurawa wuta saboda ruwan kudin da taga toufeeq din ya barnatarwa gurin,bayan ta samu dukkan bayanai da huijoji masu qarfi daje bayyana mata cewa ba auren soyayya yayi ba,auren sadaukarwa ne ga diyarsa fadeela,a qalla tafi shekara goma batasha maganin hawan jininta ba,amma a yau batajin zata iya kwana ba tare da tasha din ba.

Wasi wasi yaso cika zuciyarta taf,tunda suke mata aiki tsahon shekarun basu taba kawo mata labarin da ba haka yake ba,amma a yau ta shiga tantama,yadda taga komai ya canza,tayi imanin muddin babu son ron taoufeeq

Please Login or Register in order to submit comment