Reading KARFE A WUTA Chapter 1 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

??*???ARFE A WUTA??*??

MALLAKAR AISHA ADAM (AYSHERCOOL)

MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION

*BRIGHT PENS SECOND BATCH*

Writer of
Gaba da gabanta
?anwar maza
Cutarwa
Ru?in ?uruciya

Follow the COOL HAUSA CHANNEL channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaPywxs8kyyIhWtuvh3g

*BISIMILLAHIRAHMANIRAHIM*

*Labarin ?arfe a wuta, ?ir?irarran labari ne, idan yayi kamanceceniya da rayuwar wani ko wata, arashi ne.*

Ban lamunci a juya mini littafi, ta kowace irin siga ba, sai da izinina?







Page 1







Tsit ?aton falon yayi, ba ka jin sautin komai, sai ?arar gudun AC.
Sai mutanen falon da suke tsaye sun yi cirko-cirko, kamar masu jiran wani sakamako.

Wata matashiyar budurwa ce, dur?ushe a kan gwiwoyinta, fuskarta ?auke da wani yanayi na tsantsar damuwa, da tashin hankali, fuskarta tayi sharkaf da hawaye.

"Yanzu sakamakona kenan a wurinki? Irin wannan sakamakon shi na cancanta daga gare ki ko?"

Cikin ?ulewa wata babbar mace ta ce "Dama wani sakamako ka ke saka ran samu daga tsintaccaiyar mage? Ai ba za ta ta?a mage ba, abun da na din ga ankarar da kai kenan, tun a shekarun baya, amma ka kasa ankarewa, yanzu ta nuna maka ita ?ar kunama ce"

Budurwar ta yakice gumin da yake tsatstsafo mata, ba tare da nadamar abubuwan da suke gudana ba a ?asan ranta, a zahiri ta ce "Ba mummunan sakamako bane ba, abun da ka tarbiyantar da ni a kai ne, gaskiya ita nake tsaye a kai, bani da niyyar cutar da kowa a gidan nan, kowa aikinsa yake yi, yakamata ayi mini adalci, ba a goyi bayansa a nuna ni ce nake kan ?arya ba, a bari nima na yi nawa aikin"

Cikin tsawa ?aya matar ta ce "Har wata gaskiya ce da ke.....

Dattijon ya ?aga mata hannu ya ce "Ya isa haka, tashi ki je, ba na ko son ganinki, ki je ki yi abun da ki ke ganin ya dace da ke".

Cikin rauni da tashin hankali ta ce "Abba, ba ka son ganina ka ce?"

"Eh mana, idan har ki na gudun ?acin raina da fushina, dole ki ba wa ?an uwanki duk wani cikakken ha?in kai, domin gudanar da aikinsa yadda yakamata"

Cikin matsanancin tashin hankali ta ce "Amma Abba ni kuma menene makomata...? Yakamata a ji ta bakina Abba"
Bai tsaya sauraron mai za ta ce ba, yayi gaba zai bar falon. Cikin matsanancin tashin hankali, ta ri?e ?afarsa ta na fashewa da kuka.

"Haba Abbana, me yayi mini saura a duniya, idan har zan rayu ka na fushi da ni, ka yi ha?uri zan yi abun da ka ce in sha Allah" tuni hawaye ya cigaba da wanke mata fuska, tsantsar nadama da damuwa suka mamayeta, ta din ga kuka da sheshshe?a kamar ta shi?e, amma ya fizge ?afarsa ya yi gaba.

Yana barin falon, tamkar mutanen falon za su cinyeta ?anya, haka suka yo kanta sa surutu, kowa da abun da yake fa?a.

Tashi ta yi tsaye, ta goge hawayenta, cikin ko in kula, ita ma ta bi wata hanyar ta bar musu falon, cikin sigar kwa ci kanku.

?akinta, ta shiga ta bu?e drower, ta fito da wasu takardu ta zube su a kan gado, ta kunna system ?in ta da take caji a gefen gadon, lokaci guda kuma ta ?auki wayarta tana dannawa.

Jin motsin mutum a bayanta, ya sanya ta waiwaya da sauri.

A tsaye ta ganshi bakin ?ofa, fuskarsa babu walwala balle annuri.

Mayar da hankali ta yi, za ta cigaba da danna wayarta, ya tako zuwa gabanta, ya tsaya ya ?are mata kallo sannan ya ce "Kin shirya aikata abun da aka umarce ki ko kuwa?"

Cikin hanzari ta tari numfashin sa ta ce "Ban ce shirya ba, kuma ba zan shirya ba, daga nan har gaban abada, ka fita ka rabu da ni".

Cikin matu?ar mamaki yake bin ta da kallo, "Yanzu duk kukan da ki ka yi, ?arya ki ke yi kenan?"

A hasale ta ce "Ina ruwanka, idan ma kukan ?arya ne ko na gaske, ka yi aikinka in yi nawa, kar ka sake yin?urin shigar mini aiki, idan ba haka ba komai yana iya faruwa, wallahi ba zan fasa abun da na yi niyya ba, idan kuma ka cigaba da takura mini, zan baka mamaki"

Hannu ya saka, ya ?agota daga kan gadon ya ce "Menene zai faru, wani irin mamaki zaki bani? Me zai faru nake son ki gaya mini. Kina da hankali kuwa? Kin san doka amma kina taka ta yadda ki ke so? Da me ki ke ta?ama ne haka?"

"Doka ko? Ni iya takata na yi, kai kuma cin zarafinta ka ke ?o?arin yi, ka ?yale ni babu ruwanka da ni, ka yi naka aikin na yi nawa duk wanda yayi galaba shikenan. Idan ka ga dama ka je ka sake gayawa Abba abun da duk yayi maka a kaina, wallahi babu gudu babu ja da baya, ban fara dan ina saka ran dainawa ba, ba tare da na yi nasara ba" hanka?ata yayi kan gadon, yana wani irin huci, zuciyarsa na yi masa zafi, yayi wata irin ?wafa yana bin ta da kallo. Cikin hanzari ya fice ya bar mata ?akin, saboda idan ya cigaba da tsayuwa, zai iya yi mata abun da ba shikenan ba. Ta yin?ura ta tashi zaune tana haki, tana kallon ?ofar da ya fita.

****
Tsaye take a gefen wani gini, tana ?arewa harabar kotun ido. Yadda aka cika harabar da manya da ?ananan motoci ne, ya sake tabattar mata da manyan shari'oi za a gudanar a yau.

Ta din ga kallon agogon hannunta, tana kallon gate shigowa harabar kotun.

Motar gidan yari ce ta shigo, aka yi parking ?in ta, sai dai tsayuwar motar babu da?ewa wata dan?areriyar motar, ta shigo harabar kotun.

A ?alla an kai mintuna goma da parking ?in motar, sannan aka bu?e bayan motar, wata mata ta fito, sanye cikin coat.

Mutanen da ke harabar wurin, suka nufeta, wasu suka kar?i jakarta, ana ta yi mata fadanci, cikin girmamawa.

"Ya Allah kai ne Allah, kai ne buwayi gagara misali, Ubangiji da babu wani kafinsa, kuma babu wani a bayansa. Allah na san mutanen nan sun fi ?arfina ta ko ina, amma kaine abun dogaro na, na san ba za ka bani kunya ba. Allah sun fi ?arfina ka fi mini ?arfinsu. Allah ka yi mini kunfayakununka a kan shari'ar nan, hasken gaskiya ya shafe duhun ?arya, duk da ina da masu goya mini baya, amma Allah goyon bayanka nake bu?ata" ta jima a tsaye tana karanto addu'a, tare da yi wa Allah kirari.

A hankali ta furta "What a hectic trial, Ubangiji ka iya mini" cikin nutsuwa, ta fara taka takalminta mai tudu, ta nufi shiga cikin kotun, da takunta mai kama da na ?asaita, shigarta ta lawyoyi tayi matu?ar yi mata kyau, tana tunkarar ?ofar shiga, zuciyarta na tsananta bugawa,tana fatan Allah ya shiga lamarin ta.

****

?ofar famfo kano state.

?arfe goma saura mintuna goma na dare, tu?i yake yi cikin sauri, saboda yadda fasinjar da ya ?aukko take azalzalar sa. Duk saurin da yake yi, mita take yi masa, a kan ya ?ara gudu.

Yanayin kwalliyar da ta yi, cikin ba?in material, fuskarta ta sha make-up, zai tabattar maka daga wurin biki take.

Ta kalli agogon hannunta, kamar ta fashe da kuka ta ce "Mai napep, ka yi wa girman Allah ka yi sauri"

Ya ce "Wai dan Allah hajiya yaya ki ke so na yi ne? Haba babata duk saurin da nake yi, ki yi ha?uri mana mu tafi a sannu".

A ?ule ta ce "Ban gane babarka ba, wani irin wula?anci ne wata babarka, na yi maka kama da tsohuwa ne?"

Yayi murmushi ya ce "A'a, ai ku mata duk in da ku ke iyaye ne... Katse shi ta yi ta hanyar cewa "kuma sai aka ce na haifi kamar ka? Ai sai a bari na haifa tukuna, a yanzu na haifi kamar ka, ai tawa ta ?are a duniya. Ko yayarka ka ce mini ka cuce ni, balle babarka. Ni dai ka ?ara sauri, yau na san kashina ya bushe, sai an yagalgalani da masifa a gida yau. Aikin banza, ?awayen amarya ?an wahala, mun gama wannan wahalar a ?auke ta a mota an kai ta gidanta, mu muna fama a titi. Mu ma Allah ya kawo lokaci, ace ga miji ga mota"

Ya waiwaya ya kalleta yana murmushi, a fusace ta ce "Lafiya malam?"

"A'a Allah ya baki ha?uri".

Kafin su ?arasa in da zata sauka, ta ciro masa ku?insa, su na zuwa in da za ta sauka, ta mi?a masa, ta sauka tayi cikin layinsu da gudu a kan takalminta mai shegen tsini, ko wahalar gudun ba ta ji.

Mayafinta da jakarta a hannu, ta tura gate ?in ta shiga ta na haki.

Wani matashin saurayi, yana tsaye a harabar gidan hannunsa ri?e da waya, ya kalleta ya ce "Daga ina ki ke?"

"Biki" ta bashi amsa kai tsaye.

"Za ki ci ubanki kuwa, Major yana nan ido biyu, tun ?arfe takwas ya dawo yake tambaya ko kin dawo, gashi kin kashe waya ke ga ?wararriya"

Cikin ta yayi wata ?ara saboda tsoro "Allahumma inni as'aluka afuwa wal afiya, yau na ka?e" ta ?arasa maganar tana nufar cikin gidan.

Cikin san?a ta shiga falon, sai dai tana shiga, ta fara tozali da dattijon zaune a kan kujera 3 seater, ya sanya ?ofar shigowa falon a gaba, da gani babu tambaya ta san ita yake jira.

Tsayawa tayi ?yam da takalmanta a hannu, da jaka da mayafi, kamar ta juya da gudu ta koma.

"Daga ina?" Yayi mata magana cikin dakakkiyar muryarsa.

Cikin rawar murya ta ce "Abba, wurin biki"

"To juya ki koma in da ki ka fito"

"Ai an tashi" tayi maganar kamar ta fasa ihu, dan tuhumar Abba babu da?i.

"Dama haka mu ka yi da ke? Ki fita ki je ki yi zamanki? Ki dawo mini gida bayan goma, sai ka ce ki na zaman kanki?, koma ki kwana a in da aka yi bikin"

"Dan Allah Abb.."

"Get out, kar ki kuskura ki yi mini magiya. Duk gidan nan babu mai bani ciwon kan da ki ke bani Arfa, koma in da ki ka fito ba ki da wurin kwana a cikin gidan nan yau" da gudu ta juya ta fita saboda tsorata da ta yi.

Ta koma harabar gidan, a ?asan zuciyarta ta ce "Na shiga uku, ni ake kora kamar wata karya, yanzu idan gidan mijina ne, ba sai dai ya gama bala'in in shige ?aki na bar shi ba..

Ba ta gama tsinkewa da lamarin ba, sai da major ya kulle babbar ?ofar shiga cikin gidan.

Ta zube kayanta, ta tafi famfon harabar gidan, ta dinga wanke fuskarta, ta wanke kwalliyar fuskar gaba ?aya, ta koma ta zauna jiran tsammani ko Allah zai saka Abba ya bu?e mata ?ofa.

Samarin gidan suka fara fitowa daga BQ, suna shimfi?a a harabar gidan, za su yi kwanciyar zafi. Sai wula?anci suke yi mata, suna yi mata Allah ya ?ara, suna kyararta, kamar wadda ta aikata wani gagarumin abun kunya.

Ganin ba ta da mafita, ta laluba ta samo tabarma ta shimfi?a, ta yi kwanciyarta dan a gajiye take sosai.

Tsakar dare, ta yi juyi, ta ji babu kowa a kan gadon sai ita ka?ai, mamaki ya kamata, ta kalli agogon wayarta, biyu da rabi na dare.
Tasowa ta yi ta fito nemansa, sai dai ga mamakinta, ta tarar da shi a ventilation ?in saman bene, ya zauna a kan kujera ya saka harabar gidan a gaba, hannunsa ri?e da ?an ?aramin Alqur'ani yana karantawa.

"Lafiya dai?" Tayi maganar cikin mamaki.

Ya waiwaya ya kalleta ya ce "Lafiya ?alau"

"Amma me ka ke yi a wurin nan, a wannan uban daren? Na zata tuni ka kwanta, na fito na duba falo baka nan"

Cikin ko in kula ya ce "Kar ki damu, ki je ki yi kwanciyar ki, Arfat ke punishment"

Cikin takaici matar ta ce "To ta na punishment, sai kuma kai ka zo nan ka zauna, ka hana idonka bacci?"

Yayi murmushi ya ce "Ko na kwanta ba zan iya rintsawa ba, ki yi kwanciyar ki kawai" tamkar ta yi tsaki, haka ta wuce shi ta ?yale shi, tama tunanin yaushe ?arshen wannan lamarin zai zo?.

Haka ya kwana a zaune, yana gadin harabar gidan, duk wanda yayi juyi cikin mazan nan, yana kallon shi.

Yana ganin yadda Arfa ke ta juyi, sauro ya dame ta, sai da ya ji tamkar ya sauka ya samu abu ya rufe ta, amma ya ?yale ta.

Asubar fari, ya yi alwala, ya sauka ?asa domin tafiya masallaci.

Samarin na jin takunsa, suka din ga tashi, idan ba haka ba, ya tashi mutum da carbi.

Ya na zuwa in da take kwance tana bacci, ya tsula mata carbi a ?afafuwanta.

A razane ta tashi tana rarraba ido.

Bai ce mata uffan ba, ya yi gaba ya fice.

Tana ganin ya fita, ta tattara komatsanta, ta shiga cikin gidan, sai soshe-soshe take yi, saboda uban sauron da ya cije ta.

Cikin ?akinta ta shiga, ta watsar da jakarta da sauran kayan a kan gadonta, ta jona wayarta a caji.

Ta tu?e kayanta daga ita sai underwear. Wata matashiyar budurwa da a?alla za ta ?an girmewa Arfa ta fito daga ban?aki, ta kalle ta, ta ce "Arfa, ke kuwa a ina ki ka kwana? Har sha ?ayan dare ba ki dawo ba" banza tayi mata, ta taho fuuu ta kusa bangajeta, ta shiga ban?aki. Ta girgiza kai kawai ta shimfi?a sallaya.

Da ?yar ta yi sallar asuba, sai soshe-soshe take yi, tana idarwa ta ?ingire ta hau bacci a wurin.

Sosai take baccinta, dan ta gaji sosai, ga baccin jiya sam bai yi mata da?i ba.

"Nabila!Nabila!!"

Tsaki tayi tare da jan "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, menene, wannan wane irin kira ne dan Allah?"

"Abba ne ya ce, ace miki yana fatan kin ajiye aiki ne, da ki ka kwanta kina bacci haryanzu ba ki fita ba"da sauri ta bu?e idonta, gaba ?aya ta manta yau Monday.

Kamar korarriya ta tashi, ta afka ban?aki, a gurguje ta wanke bakinta, tayi wanka, ta fito ta shafa mayuka, da turaruka ta shirya cikin uniform.

Ta sa?a coat ?in ta a kafa?a, ta ?auki jakarta ta goyo, ta sanya takalminta, tayi waje tana kunna wayarta.

Ta shiga kitchen, ta bu?e fridge ta ?ebi lemuka ta zuba a jakartab, da abun da ta ajiye da wanda ba ta ajiye ba, duk ta kwasa ta zuba, ta zuge jakar ta fito falo.

A falon suka yi karo da wata matashiyar mata, matar ta kalli Nabila ta ce "Ma'aikaciya ko mahaukaciya, kalleki kamar korarriya Nabila, zaki fita aiki amma ki ka kwanta ki na kwasar bacci abinki".

Nabila ta ce "Anty, the whole barrister ki ke cewa mahaukaciya?"

"Yo banda shirme, kalleki kamar an hanka?oki, ke wannan wane nutsatstsen ne ma zai ce ki tsaya masa shari'a?"

Nabila ta ce "I will fill a lawsuit against you, what you did is deformation of character, the whole barrister Anty ki ka zaga"

"Wuce ki tafi kafin na make ki ni? Idan suka kore ki daga wurin aikin, ai kya nutsu" Nabila ta sake kwasa da gudu a kan takalmanta kamar ba budurwa ba.

Mai aikinsu ta tarar a famfon harabar gidan, tana wanke-wanke.

"Shalelen Abbanta, yau kamar kin makara"

?aga mata hannu kawai Nabila ta yi, kowa ya ganta sai yayi magana, ta kalli hanyar benen Abba, kamar ta je ta gaishe shi, amma ta fasa ta san yadda ta makaran nan, sai ya zaunar da ita yayi mata fa?a, ga laifin jiya ga na yau, kuma ta san sai ya ha?a har da na waccan shekarar yayi mata, dan haka tayi wuf ta fice waje.

Duk irin vibration ?in da wayarta take yi, ba ta ?aga ba sai da ta zauna a cikin adaidaita sahu, sannan ta ?aga kai wayar kunnenta.

"Wai Nabila wani irin wula?anci ne, nake ta kiranki ki ka ?i ?agawa?"

Nabila ta ce "Ke ban son tijara, kin wuce aiki ne?"

A fusace mai maganar ta ce "Ban sani ba"

Nabila ta yi dariya ta ce "Sorry masoyiyya, ki fito titi gani nan" tafiyar mintuna sha biyar suka yi, suka iske wata matashiyar budurwar a titi, sanye cikin doguwar rigar abaya, ta kama adaidaita sahun ta shiga tana hararar Nabila.

"Sorry sumy, kar ki fashe dan Allah"

"Wallahi kin fusata ni Nabila"

"Shiyasa na ce ki yi ha?uri ai, ya gidan ya su mama?"

Sumayya ta ce "Suna lafiya ?alau, meyasamu fuskarki? Na ga kamar ?uraje"

Nabila ta rausayar da kai ta ce "Ke bari, the whole me, jiya Abba ya saka na kwana a haraba, sauron nan na cikin flowers suka yi idi a kaina"

Sumayya ta waro ido ta ce "Wai da gaske?"

"Zan yi miki ?arya ne? Wallahi dattijon nan ya ce wai na koma in da na fito ya rufe ?ofa. Aikuwa na din ga tsinewa amaryar nan, na baro ta a gidanta cikin nisha?i da farinciki, ni kuma na afka tashin hankali, kamar ni degree holder, Abba ya rufewa gida. Yanzu dan Allah da a gidan mijina ne, da ba sai dai yayi masifar ya gama ba, babu wanda ya ji ya gani? Ai Abba ya tozarta ni jiya. Sai so ake a ga fuska a tuhume ni, ko ayi mini rashin mutunci a gidan nan, kin san gidanmu Allah ya wadata mu da munafukai, ni kuwa na ha?e rai"

Sumayya ta ce "Allah ya ?ara, ke uwar gwaninta, har da kai amarya, banda uban anko da ki ka yi mata. Ina mai tabattar miki ke da ganinta ta tako gidanku, sai wani ikon Allah"

Nabila ta ?an yi shiru ta ce "Ku ma fa haka ne, kin san wani abu, ba hassada nake yi wa amira ta yi aure ba, amma kalli na fita kyau fa, na fita komai amma amira ta shige daga ciki, ohh ni Nabila, duk kyan nan da dirin nan yadda ki ka san na je na haye kan high table ?in nan ayi da ni ranar dinner. Ba ma wannan ba duk wannan gayun da kwalliyar ban yi saurayi a bikin nan ba"

Sumayya ta ce "Ki je ki ?orawa ranki jarabar son aure, ki ?i focusing a kan career ki, ni ko a jikina na san lokaci ne, kuma tun da ba yawon iskanci nake ba, duk wadda ta yi mini gorin aure sai na ci ubanta, shekarun namu nawa ne duka da za a addaba mana"

Nabila ta yi ajiyar zuciya ta ce "Ba haka ba ne Sumayya, we have a different backgrounds, ke kin san me nake nufi, wallahi ?anci nake so Sumayya, ko ta halin ?a?a"

Sumayya ta ce "Kar neman ?anci ya kai ki ga halaka, duk ina samarin naki ne to?ba wanda zaki tsayar?"

Nabila ta yi tsaki ta ce "Bar matsiyata, daga ?an wahala sai ?an iska. Sai dai duk wanda ya zo hannuna sai na ci rabona ayi baran-baran. Na daina wahalar son mutum, daga ?arshe yayi breaking heart ?ina, ya ci bulus. And also haryanzu ban samu spec ?i na ba kin dai gane"

Sumayya ta ce "Au ke yanzu har wane za?e-za?e ki ke yi?"

Nabila ta ce "To ana raba mai rai da motsi ne? Iya wuya akwai abun da zuciya take so, kuma ni na fi son namiji mai kumari sosai. Irin wanda zaki ganshi ingarman namiji mai cikar zati. Beside fuskar namiji ba gemu, ai sunansa sumayya, ni kuma daga dattijai, sai marasa gemu, sai kuma ?an wahala, ni matashi nake so, ba kuma yaro ba"

Sumayya ta ce "Au sunana ne ma abun kwatancen iya shegenki ko, to ki je dan kanki. Mai napep zan sauka a nan, za ta baka ku?in"

Nabila ta ce "Ke uban waye ya ce miki ina da ku?i?" Tuni Sumayya ta sauka, ta bar Nabila.

Nabila ta yi ?wafa ta ce "Zamu ha?u ne, zaki ga wula?anci".

***
A hankali yake bu?e jajayen idanunsa, a lokaci guda kuma yana lumshe su, tamkar mai shirin yin bacci. Sai mirgina kansa yake yi, yana sake lumshe manyan idanunsa da suka koma jajaye matu?a.

Tamkar an jefo shi, haka ya fa?o ?akin, yana rarraba ido.

A hankali ya ?aga kai ya kalli wanda ya shigo ?in, ya mayar da kansa ?asa ya sunkuyar.

"Allah ya taimaki oga..." Bai amsa ba kawai ya bu?e tafin hannunsa ya mi?a masa.

Wata ba?ar leda ya ciro, ya ?ora masa a hannun, sannan ya ce "Sai dai Oga ba a samu da yawa ba, ?ar ka?an ce, cinnaku sun yi wa kasuwar ?awanya, shiga da fitar kaya na bayar da wahala, da ?yar na samu wannan wurin wani ?an inyamura, ina ga wuri zan canza, saboda kamar ana son yi mini cune".

Bai ce masa uffan ba, ya kwance ledar, ya fito da kwalin wata allura pack guda, mai ?auke da ampoule na allura guda goma.

Sirinji lamba biyar ya ?auka, ya din ga fasa alluran yana zu?a, sai da ya cika sirinjin, sannan ya mi?e hannunsa.

Ya ?aga kansa ya kalli matashin da ya kawo masa allurar, bai ce masa komai ba, matashin ya bar ?akin.

Ya mayar da idonsa kan hannunsa, ya yana kallon jijiyoyin da suka kwanta ?o?ar a ?ar?ashin fatarsa, suka yi ru?u-ru?u, manya da ?anana.

Ya dubi guda ?aya, ya huda ta da sirinjin hannunsa, ya fara bawa kansa allurar sannu a hankali. Sai da ya zuba ta duka, sannan ya yi jifa da sirinjin, ya sunkuyar da kansa ya na jiran Sakamakon hukuncin da ya ?auka.

Sai dai kusan mintuna goma sha biyar, bai ji abun da yake so ba, sai wani irin nauyi da kansa ya ?ara, idonsa ya din ga yi masa yaji, ya rintse idanunsa amma bai ji alamar abun da yake so ba.
Abu kamar wasa kansa ya din ga wani irin sarawa, ?irjinsa yana zafi. Ya dafe kansa da hannunsa bibbiyu yana jujjuyawa tare da rufe idanunsa.

Ihu ya fara yi iya ?arfin sa yana ta?ar?rewa, yana girgiza kansa, saboda yadda yake jin kansa tamkar zai yi bindiga.

Da gudu suka shiga ?akin, suka fara ?o?arin danne shi, amma ya yi ihu ya watsar da su baki ?aya ya cigaba da kururuwa.

Ayshercool.
08081012143


Please Login or Register in order to submit comment