Reading KARFE A WUTA Chapter 69 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

a waya ba, idan ma an kama ni, ko ma menene ya same ni, ba ruwanka ko?" Tari ta fara yi, saboda haya?i, sakar mata hannu ya yi, tayi sauri ta ?auke kwalin sigarin da ashanar, ta tura a jakarta.

Satchet ?in maganin da ya le?o a gefen aljihunsa, shi ma ta ?auke, tana mita "Wallahi Allah ya hore maka taurin kai, wannan shaye-shayen ne ba zaka daina ba ko?" Ya ?ura mata ido, saboda jin tana ?amshin turaren florie irin na 'yar madara.

"Ina magana kana kallona, baka tausayin lafiyarka, yanzu duk ?o?arin jauhar a kanka ya tashi a banza, yawaita yi mata addu'a, istigfari da mayar da hankali a kan addu'a, shi zai rage maka damuwa, amma baka ji, kullum cikin haya?i, da shan miyagun ?wayoyi"

"Fa?a fa ki ke yi mini"

"Au kar na yi maka? Ka daina mana da na yi maka mana, wannan abubuwan da kake yi ba shi yake nuna halaccinka a gareta ba, ka daina abun da ka ke yi, ka zama mutumin kirki, shi ne cikar halaccinka a gareta"

Kawar da kansa gefe yayi a hankali ya ce "Angry bird"

"Ni ce bird ?in? Wallahi ni ba tsuntsuwa ba ce ba, da ba ka neme ni ba, ni gani ai na zo, ba a kama ni ba fa"

"Dama na san ba za a kama kin ba ai"

"Haba ya aka yi ka sani?"

"Bani wayarki" ta ciro wayarta ta mi?a masa.

Ya ciro tasa ya danna, sannan ya saka a kunnensa.

Muryar P.A ta fito ranga?au a waya ya ce "Hello"

Viper ya yi shiru, bai ce komai ba.

Ya sake cewa "Hello", still bai yi magana ba.

"Waye ne ya ?oye lamba yake kirana, idan ba za ayi magana ba, zan kashe, waye?"

"Mai zamani ne" waro ido P.A yayi ya ce "Wane mai zamanin?"

"Zuwa yanzu, na san sa?ona ya iske shi, ya shirya, zan bayyana a lokacin da bai yi tsammanina ba, kuma ya daina wahalar da kansa a kan lallai sai an kamani, ko da an kama ni, nafi ?arfinsa, ya kuma jirani aikena na biyu" ya katse wayar yana ajiyar zuciya.

"Kai, Oga kana burgeni, ka din ga acting kamar a film ?in indiya hausa, wai dan Allah, a ina ka ko yi wannan halin naka?"

Ya jefa mata wayarta jikinta.

"Amma wait, wai ne ka ke yi a wayata ne baka gaya mini?"

"Yaushe zaki fara shari'ata?"

Nabila ta ce "Shari'arka akwai sar?a?iya boss, sonake na gama da ta ramma gobe in Allah ya kaimu zamu koma kotu." Ya jinjina mata kai.

"To zaka fara bani ku?in aiki ai, ka ?an ragen wani abu, na din ga zuba mai, tun da na je fa aka nuna mini file ?in ka, nake ta up and down, ina tattara abun da zan tattara. In sha Allah zan zama sanadin daina zubar hawayenka"

"Dama kuka nake?"

"A'a murna ka ke yi"

Ya girgiza kai ya ce "Ko matata da muna tare, ta da?e kafin ta iya kallona ta yi mini magana, balle ta yi mini ba?ar magana, amma ke kin mayar da ni kamar wani sa'anki, har hantarata ki ke yi"

"Ni ?in ce na rainaka? Ni na isa wacece ni? Amma dan Allah sweetheart meyasa ka kusa kashe ni ranar farko da na zo wurinka?"

Ya ?ago ya kalleta ya yi shiru.

"Ka amsa mini dan Allah"

"A lokacin ai kamar mahaukaci nake shiyasa"

Ta girgiza kai ta ce "A'a, wani abu na din ga gani a idonka, da na rasa menene? Dan Allah meyasa?"

"Ke ban sani ba, tashi ki bar wurin nan"

Ta no?e masa kafa?a tana kallon idonsa, abun da ya tsana. Yayi tsaki ya kawar da kansa gefe.

Turare ta ?aukko a jakarta, ta toshe hancinta, ta fesa a wurin. Ba shiri ya waiwayo yana kallon hannunta.

"Gashi yanzu na saka ka waiwayo ai, gashi saya maka na yi" ya kar?i turaren, ya din ga juya shi a hannunsa yana kallo.

Ta na ?o?arin ?aga wayar da ake yi mata, ta ga hawaye na ?iga a hannunsa.

Sai jikinta yayi sanyi gaba ?aya. "Haba mai babban suna, a yanzu fa kuka ba naka bane ba, wanda ka yi ya isa, mu cigaba da addu'a da ?o?arin tattara shaidun da zamu shiga kotu da su, dan Allah ka daina bana jin da?i.

"Da jauhar na raye, da yanzu na san ta kammala law school, maybe ta haifi yaronmu na biyu ko uku, ina da tarin burika a kanta, na kyautata rayuwar ta, ta ji da?i ta huta, saboda wahalar da ta sha a rayuwarta, amma wauta ta da rashin hankali, ya sanya ta mutu ta bar ni a duniyar. Lokacin da duniya ta yi watsi da ni, ake yi mini kallon mara amfani, ta rungume ni, ta kar?i ?addararta, ta kula da ni, a lokacin da nake ?o?arin kyatata ratuwarta na fara bata kulawa, lokacin da na fara gano haske yana tunkaro rayuwarmu, ashe yayi daidai da lokacin da zan yi girbin ya mummunar hanyar da na za?awa rayuwata, na rasata" yayi maganar yana ?o?arin mayar da hawayen sa, amma suka cigaba da zuba, kamar an kunna famfo.

"Viper, ka yi ha?uri, Allah ya ambaci masu ha?uri a wurare daban-daban a al?ur'ani, tare da yi musu bushara. Viper Allah ya fi kowa so da kishin bawansa, wata?ila mutuwar jauhar a wannan lokacin shi ne mafi alkhairin ta, a duk bu?e ido muka yi muka ganmu a duniya, dan haka ba zamu tsarawa Allah yadda muke son kasancewa ba a duniya.
Ba kowa Allah ya tsarawa jin da?i a duniyar nan ba, ai dama ita duniyar kurkukun mumini ce, aljannar kafiri. Wani ga jin da?in yana cikinsa a zahiri, amma a ba?ini rayuwar kawai suke yi mara ma'ana.
Yanzu tsohon ubangidanka ga duniyar ya samu, yana jin da?in amma nauyin zunubin da yake aikatawa ba zai ta?a barinsa ya rayu cikin kwanciyar hankali ba. Ba sai mutum ya samu wadata dan ya sha wuyar rayuwa, shi ne tabbacin Allah yana son sa ba, duk tsananin rayuwa da ka ke ciki, idan har ya barka da imaninka, kuma ka yi kyakywan ?arshe, wallahi ya fiye wa ?an Adam duk wani abun more rayuwa.
In dai ana samun aljanna a biyayyar iyaye, da biyayyar aure in sha Allah Jauhar ta samu" ya jinjina kai yana cigaba da zubar da hawaye.

Ta bashi handkerchief ?in ta, ta ce "Share hawayen haka, kaga ni ma ka saka ni kuka, bana iya jure in ga mutum a cikin damuwa ko yana kuka, alhalin ba zan iya yaye masa damuwar sa ba.
Yanzu ni kaina, duk abubuwan da nan da nake yi, ?arfin hali nake yi, zuciyata akwai wani ciwo da yake addabata, ina kuka iya yi na wasu lokutan, sai dai babu yadda na iya, da abun da ?addara ta zana mini" tayi maganar ita ma tana kuka.

Ya ?ago ya kalleta, ya motsa baki, yana son ya fa?i wani abu.


Ayshercool
08081012143
???500 ne via 0009450228
Aisha Adam jaiz bank sai shaidar biya ta 08081012143
Wanda za su jira document 1K ne.

90009343
'Yan Nijar ku turo katin airtel na 300fcfa

Arewabooks ayshercool7724



Cikin hanzari Viper ya tashi ya tsaye, yana cewa "Kina ina ne? Meyake faruwa?" Sai dai still shiru ba ta ce komai ba.

Su Walid ma duk suka mi?e tsaye, suna kallonsa.

Walid ya ce "Yaya meyafaru Viper?"

"Ki yi mini magana, kina ina meyake faruwa ne?"

Liti ya ce "Mai zamani menene wai?"

"Yarinyar nan tana cikin matsala"

"Subhanallah, to tana ina ne yanzu?" liti yayi maganar yana kallon sa.

"Safiya ce yanzu, ko tana gida, ko hanya ko wurin aiki. Babu yadda za a yi ace a gida ne wani abu ya same ta ta kira ni, da hanya ne kuma da tuni an kai mata ?auki, ko dai an ?auketa ne ko kuma tana wurin aiki, wuta na ji ta ce"

Hanyar fita Viper ya nufa, Walid ya ri?e shi ya ce "Ina zaka fita ka je? Ba kai yakamata ka fita ba, liti ko ?an mama, ?an maman ma dai, ka san wurin aikinta ai in da kuka ?aukkota?"

Ya ce "Eh oga Walid"

"Je ka gano mana menene yake faruwa"

Ya ce "To bari na canza kaya"

Viper ya cigaba da bin layin Nabila yana kira, amma shiru ba ta ?agawa.

Nabila kuwa tuni ta fice daga hayyacinta, ba ta sake sanin in da kanta yake ba.

Masinja ne da shigowarsa kenan, ya ga wurin ya turnu?e da haya?i, ya shiga dudduba daga ina haya?in yake fitowa.
Cikin tsananin tashin hankali, ya nufi ?ofar office ?in Nabila, ya din ga bubbuga ?ofar, amma ya ji ta a rufe gam, ya girgiza ya girgiza amma a rufe, ya fito ya nufi wurin masu gadi, ya na sanar da su wuta.

Suka tashi gaba ?aya suka rankaya a guje, ?aya daga cikin su ya ce "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, Nabila fa ta shigo aiki, tana ciki jama'a ku taimaka".

Nan da nan wuri ya cika da mutane, ana ta ?o?arin a ?alle ?ofar a cirota, a daidai lokacin barrister Habib ya ?araso cikin tashin hankali, kasancewar an kira shi a waya an sanar masa.

Da kyar aka ?alle ?ofar, wani irin huci mai ?auke da haya?i ya buso waje suka ja da baya, wani matashi ne ya kutsa kai, ya na nemanta, ya hangota a yashe a cikin office ?in ga jakarta da system ?in ta, da wayarta a wurin.

Wutar ta mutu ba ta cigaba da ci ba, iya wadda ta kama ce ta haddasa haya?i, da huci mai zafi.

A kafa?arsa ya sa?o Nabila, yana fitowa barrister Habib ya kar?i wayar da system ?in, yayi waje da ita. A motar barrister Habib aka saka ta, suka nufi asibiti.

Barrister Kabir ma hankalin sa yayi mummunan tashi, ya din ga kiran waya, Habib ya ce masa sun tafi da ita Asibiti.

Gaba ?aya hankalin ma'aikatan wurin ya tashi, dan duk jin kan Nabila da gayunta akwai girmama mutane, ga yawan kyauta da take yi musu.

Viper ya kasa zaune ya kasa tsaye, Liti da Walid ne suke ta rarrashin sa, amma ya kasa nutsuwa, sai cewa yake tafiya zai yi ya gano halin da take ciki, suka din ga kiran wayar ?an mama, amma bai ?aga ba.

Viper ya ce "Walid, ba zan lamunci a wannan karon wannan ita ma ta rasa ranta ba, dole fa na gano halin da take ciki"

Walid ya ce "Mun sani, amma ka fara bari mu ji daga bakin ?an mama"

Suna tsaka da maganar ya kira waya, Viper ya fizge wayar daga hannun liti, ya ?aga ya ce "Kai ana ta kiranka ka ?i ?agawa, yaya aka yi ka sameta?"

"Wuta ce ta kama fa a ofishin ta, lokacin da na je an bu?e ?ofar an fito da ita, za a tafi asibiti"

"Dalla ba wannan na tambayeka ba, tana ina yanzu a wane hali take ciki?"

"Eh, sun tafi kaita Asibiti, na bi bayansu a adaidaita sahu, an kaita wani ?aki an hana kowa shiga, haryanzu dai ina asibitin, likitocin dai ba su ce komai ba, amma dai kamar fa ba ta da rai"

Ashar Viper yayi masa, ya ce "Yaya aka yi ma wuta ta kama a iya ofishin ta kawai? Me hakan yake nufi? Likitoci sun ce ta mutun ne?"

?an mama ya ce "A'a ni nake tunanin hakan, bata motsi ko numfashi a yadda naga an sakata a mota wallahi da ?yar idan ba mutuwa za ta yi ba"

Liti ya ce "?an mama ko ?an shegiya, gaba ?aya yaron nan ga?o ne, ya za ayi ka gaya masa wannan maganar?"

Walid ya kar?i wayar daga hannun Viper, ya saka a kunnensa ya ce "?an mama kana ji na?"

"Eh oga Walid"

"Duk abun da ka ke ciki, ka din ga sanar da mu"

"To oga walid in sha Allah"

"Jikinta wutar ta ta?a ta ne?"

"A'a, ba ta ?one ba, haya?i ne ya yi mata illa, wutar ma ba ta kama sosai ba"

"To shikenan, muna saurarenka"

Walid ya kalli idon Viper, yadda ya bayyanar da matsanancin tashin hankali.

"Viper, ka kwantar da hankalinka dan Allah komai zai zo da sau?i, in sha Allah ba zata mutu ba, sai ta cika maka burinka"

Jiki a sanyaye ya ce "Walid yanzu shikenan duk wanda ya ra?e ni, rayuwarsa sai ta shiga hatsari, idan ita ma ta rasa ranta fa, jikina yana bani set up ne abun nan"

Liti ya ce "Kar ka zargi kanka, dama can wannan ba ta ji, kuma haryanzu ai bata fara shari'ar ka ba, balle ace saboda kai ne"

Walid ya ce "Ya isa haka liti, kai abu ba ya wucewa a wurinka"

"Yaushe zai wuce, tun da ta munafurce ni, ta saka aka kamani"

***
Abba kuwa Allah ne ya tsare bai yanke jiki ya fa?i na, bayan sanar masa da cewar, gobara ta kama a ofishin Nabila tana Asibiti.

Haka Nasir ma, cikin gigita da tashin hankali, ya nufi Asibitin da aka ce an kai Nabila.

Likitoci sun hana kowa ya shiga, an cire mata kaya an saka mata wata gown, ana duba jikinta ko da in da ta ?one, amma babu, sai dai ga zuciyarta na bugawa, amma babu numfashi, idan tayi kamar zata yi numfashi, sai tayi ta tari, haya?i na fita ta hancinta da bakinta, sai tayi ?if.

Gaba ?aya Abba a rikice ya ?araso asibitin, cikin matsanancin tashin hankali Abba ya ?arasa asibitin, zuwansa babu da?ewa Nasir ma ya ?araso, Abba ya nemi a bar shi ya ganta, amma aka ce ba a shiga likitoci na aiki tukuna.

Abba ya ce " 'ya ta ce, ko me za ayi mata ayi a gabana, idan ma ta mutu ne a bari na ganta, ai ni musulmi ne na kuma yadda da ?addara mai kyau ko mara kyau" suna ?o?arin lalla?a shi ya ha?ura kar ya shiga, ya burkice musu, babu shiri aka bashi damar shiga wurinta.

A kwance ya tarar da ita, ana ta allurai, ya ?arasa gaban gadon ta ya zuba mata ido, dama ya lafiyar kura balle ta yi hauka, an sha wahalar ciwonta na asma sosai da sosai, sai da ta girma ta ?an samu sassauci, tayi gado mai wahala, dan mahaifiyarta ce mai ?auke da ciwon ta gada.

Ya kalleta a kan gado, sai ya ga ta koma masa kamannin mahaifiyarta sosai da sosai, lokacin da take gadon asibiti ta ri?e hannunsa a halin rashin lafiya.

Ya ri?e hannun Nabila, ya ga alamar akwai rai a jikinta, amma a galabaice take, ya da?e yana yi mata addu'a, sannan ya tashi ya fita waje.

Barrister Kabir kuwa tuni suka yi reporting wurin Jami'an tsaro, aka zo aka fara bincike a kan musababbin tashin wutar, abun bai tsaya iya nan ba, sai da aka tattare masu gadin wurin, aka tafi da su wurin 'yan sanda domin fuskantar tuhuma.

Sumayya ma tun kan ta ?araso asibitin take uban kuka, saboda yadda aka gaya mata faruwar abun, ta riga ta fitar da rai Nabila tana raye.

Sai da Nabila ta shafe awa biyu, likitoci na procedure daban-daban a kanta, aka samu numfashinta ya dawo, sai dai a wahale take yin sa, aka fito da ita daga emergency, aka mayar da ita wani ?akin.

****

Bunkure ta daki tebur ta ce "Tana raye kenan?"

Mutumin gabanta ya ce "Eh ranki ya da?e, an samu nasarar fitar da ita daga wurin, amma na samu tabbacin tana raye, bata mutu ba sai dai tana cikin mawuyacin hali"

"Babu ruwana da mawuyacin hali, wannan wane irin aiki ne? Yaya za ayi ni ga yadda muka yi da ku, amma abun da ku ka yi daban?"

"Ba daga mu bane ba ranki ya da?e, wallahi aiki an yi shi yadda yakamata, agajin gaggawa aka kai mata shiyasa"

Ta numfasa ta ce "Shikenan, zaka iya tafiya, a asibitin zan saka a ?arasata".

***
Hankalin Viper bai dawo jikinsa ba, sai da ?an mama ya dawo, ya tabattar masa da a kan idonsa aka fito da ita, tana raye, kuma ba ta ?one ba, ko ?warzane babu a jikinta.

Nannauyar ajiyar zuciya Viper ya sauke, yana fatan Allah ya sa hakan, ya kuma bata lafiya.

Hatta 'yan gidan su Nabila, sai da suka tausayawa halin da take ciki, duk da ba shiri suke yi da ita ba, baba magajiya kuwa kuka ta ?ora hannu a ka ta din ga yi, ba ta san iya tashin hankalin da zata shiga ba, idan aka ce ba Nabila.

Sumayya na gefen Nabilan, ta ri?e hannunta tana ta matsar hawaye, tari ne ya kuma turnu?e ta, kawai ta yin?ura zata tashi zaune, duk suka nufo kanta, Sumayya ta ri?eta tana kiran sunanta.

"Viper wuta, wani ya kulle ni ta waje, ku taimaka mini, Viper wuta" gaba ?aya sai suka yi sak, suka zuba mata ido.

Abba ya ce "Waye kuma Viper?"

Cikin matsananciyar tuhuma Nasir yake bin ta da kallo, da yake ta surutai cikin fita hayyaci.

Barrister Habib ma sak yayi, Sumayya ta ce "Abba sunan wani ?an daba ne, da take bincike a kan sa, maybe tana ?adamin aiki a kansa ne abun ya faru"

Abba ya ce "Na rasa irin Arfa, wata?ila ma a dalilin wannan kwashe-kwashen nata, aka yi yin?urin cutar da ita.

Barrister Habib ya ce "Bana tunanin haka sir, maybe ?addara ce kawai, ai tana yawan zancen ?an daban nan ne, ta ce Yayanta shi ne incharge na nemansa tana fatan ta taimaka masa"

Nasir duk da ido yake bin su da kallo, yanayin yadda take surutan, kamar akwai sabo da kuma sha?uwa a tsakanin su.

A hankali sumayya ta ce "Masoyiyya"

"Na'am sumy"

"Na'am"

"Wuta aka saka mini a office ?ina, da ta tashi, na tafi da gudu na bu?e ?ofa na ji an rufe ni ta waje"

Abba ya ce "A'a Arfa, Allah ne dai ya ?addara tashin wutar, kar ki zargi kowa"

Nabila ta ce "Abba, ni fa na bu?e office ?in da kaina, na bar key a jiki ta waje na shiga, da wutar ta tashi na je na bu?e, na ji an mur?a key ?in sau biyu"

Abba ya ce "Ki na cikin hayyacinki, kin farka gaba ?aya?" Ta jinjina masa kai.

Ya ce "Alhamdilillah" nan aka din ga jera mata sannu, duk da tana ta haki a hakan ma.

***
Ramma ce a tsaye, ta shirya cikin doguwar rigar abaya, ta ?ora mayafin a kanta, Abdul ya bata facemask ya ce "Saka wannan" ta kar?a ta saka, ya ce "Wow, kin yi kyau sosai beb" ta yi murmushi tare da gyara mayafinta.

Ya ri?e hannunta, har cikin motarsa, da hannu ?aya yake tu?i, hannunsa ?aya kuma ya ri?e nata, loka-lokaci sai ya sumbaci hannunta, yana jin wani irin so da shau?inta yana ratsa ilahirin jikinsa.

"Ni ka daina shafa mini yawu a hannu"

"Haba Rahama, yawun ?auna ne fa" yayi maganar yana satar kallonta.

Ta jingina da seat ?in motar, ta numfasa ta ce "Yaushe ne bikinka, ko an yi ne?"

Ya ce "A'a, ya za ai, ayi ba ki sani ba? Wai bata ?arasa karatu ba, da an so ayi ne idan ta dawo shikenan ta tare, babanta ya ce a bari ta gama, saura 2months"

Ramma ta ce "Allah sarki, ni nawa karatun ko oho, na zama karuwa"

"Haba rahama, dan Allah ki daina wannan maganar, ina da kyakykyawan tanadi a kan rayuwar ki da iliminki, na san na cutar da ke, amma zan gyara laifina in sha Allah" tayi masa shiru tana kallon titi.

Dare ne sosai, duk sahu ya ?auke.

Ya zuba mata ido, a lokacin da take shan ice cream ?in gabanta, ya tuna yadda yake ta fama da mahaifinsa, ya tsunduma tunanin ya zai yi ya sanar da shi batun ramma? Dan sai dai ayi wadda za ayi a kan ramma, amma bai ji duk iya bala'in da za ayi zai rabu da ita ba, ta kalleshi ta ce "Ka sha mana" yayi murmushi ya jinjina mata kai, mama ya cigaba da jujjuya cokalin.

Hakan ya sanya ta fuskanci a cikin damuwa yake, ta ?ebo icecream ?in ta kai bakinsa, ya ?aga ido ya kalleta, ya bu?e bakinsa ya kar?a.

Ya ce "Kin yafe mini dukan da nayi miki, kin daina fushi da ni?" Ta jinjina masa kai alamar eh.

"To ?aya laifin fa?"

"Ban yafe wannan ba" ta bashi amsa kai tsaye.

"Tun da ki ka yafe wannan, wancan ma zaki yafe mini in sha Allah" ta yi shiru tana kallonsa.

Sai da ta gama ciye-ciyenta son ranta, sannan ya ce ta raka shi asibitin abokinsa, zai duba wasu marasa lafiya.

A zuciyarsa yake zargin kamar wani cikin ne da ramma, amma bai tabattar ba, kuma bai ambata ba, balle ta tashi hankalinta, muddin kuma ya ce zai gwada za ta gane, kuma ta daina yarda da shi, dan ce mata yai, yayi mata allurar planing, ba zata sake ?aukar ciki ba sai allurar ta sake ta.

Wa?anda ya yi wa tiyata a asibitin ya duba, sun fito take tambayarsa "Nan ne asibitinka?"

Ya ce "A'a, Asibitina na can wajen gari, na kan je wasu asibitocin da aka bu?ace ni, na gabatar da aiki, zan kai ki namun ma ki gani"

Ramma ta ce "Naka dai"

"A'a namu dai, idan komai ya daidaita, ai bikinmu za ayi, na nuna wa duniya ke, komai ya wuce"

Ta ce "Ta? kwa?o"

Babu tsammani yayi karo da wata matashiyar budurwa, hannunta ri?e da ledar Pharmacy.

"Ke ba kya gani ne?"

"Ban gane bana gani ba, kawai ka zo ka tsaya a hanya, kana rangwa?a, da alama kai jin da?i ne ya kawo ka asibitin ba mara lafiya ne da kai ba" Ramma ji tayi kamar ta san muryar.

A fusace ya yin?ura zai yi masifa, ramma ta ce "Dan Allah ki yi ha?uri, mun tsare hanya kam, Allah ya ?ara afuwa ga mara lafiyan"

Sumayya ta amsa da "Amin" ta harare shi ta wuce.

"Dan Allah ka din ga rage fa?a, har marasa lafiyar ma, fa?a ka ke yi musu, haba kai kuwa" ?wafa yayi suka tafi.

***
Sosai Viper yake son kiran wayar Nabila, amma babu hali, dan ?an mama ya tabattar masa da ya ga an fito da wayarta, da jakarta da system ?in ta, wani mutum ya kar?a, amma alamu sun nuna a wurin yake aiki shi ma.

Viper bai san waye ya kar?i wayar da system ?in ba, akwai ayyukansa a cikin system ?in ta, da suke bu?atar sirri sosai da sosai.

Nasir ya kar?i system ?in Nabila da wayoyinta a hannun barrister Habib, sai dai ya kasa bu?ewa, dan bai san menene password ?in ta ba, har su walida ya tambaya ko sun sani, suka ce ba su sani ba.
?aramar wayarta kawai ya iya bu?ewa, sunan confidential ya fara nema, yayi sa'a ya samo lambar, sai dai ya duba lambar da aka yi saving a kan sunan, ya tarar da suna babu lamba, ya duba ya duba, amma ya rasa samun lambar, ya din ga kwafar lambobin wayar, yana dubawa a Truecaller ?in sa, amma babu wani suspicious abu da ya samu.

Yanzu tantamar da yake yi a kan Nabila, ya wuce zargi, akwai abun da take aikatawa na rashin gaskiya, ya ?allafa ransa sai ya gano, waye wannan mutumin da ya gansu tare sau biyu.
A kunne ya bar wayoyin, sai dai yadda aka din ga kira babu ?a??autawa, tun yana ?agawa yana saka ran, zai samu wani abu na information, harya ha?ura ya daina ?agawa.

Nabila ta farga da rashin wayoyinta, ta tambayi a bata wayoyinta, aka ce mata suna wurin Nasir, ta jira ya zo Asibitin ta ce ya kawo mata wayoyinta ya ce ba zai bayar ba.

Cikin mamaki ta ce "Amma meysa na san za a neme ni a wayar?"

Ya ce "Kina fama da kanki, uban me zaki yi da wata waya?"

Sumayya ta ce "Ke ma dai arfa, uban meye a wayar ne, ki hutawa kanki ki gama farfa?owa" kallon Nasir take yi, tana nazarin irin kallon da yake yi mata, ta fara fatan Allah ya sa ba wani abun ya gano a wayar ba.

Abba ne ya shigo, suka gaggaisa, ya din ga tsokanar Sumayya tare da Nabila, ko wurin aiki Sumayya ba ta zuwa, tana li?e a asibiti da Arfa, Sai da Nabila ta magantu a kan wurin aikin sumayya amma ta basar da ita.

?wan?wasa ?ofar ?akin aka yi, sannan aka bu?e.

Jmau'an tsaro ne da bindigogi suka fara shigowa, gaba ?aya suka yi ?uri da ido, suna kallonsu.

Alhaji wada m karofi ne ya shigo, suka gaisa da Abba, Nasir ma ya gaishe shi.

Nabila ta ce masa "Lafiya, wannan kama ni za su yi?"

Yayi murmushi ya ce "Saboda ke ce Sarkin laifi ba, yaya jiki ashe haka wannan iftila'in ya faru?"

"To ai na ganka da yan sanda me na yi?"

Yayi mata shiru, suka ?arasa gaisawa da Abba suka gaisa, Sumayya ta ce "Ina kwana?"

"Lafiya ?alau T ladan, ya gidan radio?"

"Yana nan sir"

Nabila ta ce "Dama kin san shi?"

Sumayya ta girgiza kai.

Ya ce "Eh ba lallai ta sanni, amma ita muryarta sananniya ce ai, kuma kina bani labarinta ai, ko ba sumayya T ladan ba ce?"

Sumayya ta

Please Login or Register in order to submit comment