Reading KARFE A WUTA Chapter 2 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register








??*?ARFE A WUTA*??

MALLAKAR AISHA ADAM (AYSHERCOOL)

MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION

*BRIGHT PENS SECOND BATCH*

https://whatsapp.com/channel/0029VaPywxs8kyyIhWtuvh3g

Arewabooks ayshercool7724
Watpad ayshercool7724

2

A ?alla sun kai ?arti uku majiya ?arfi, suka ri?e shi, amma sai ?o?arin watsar da su yake yi, ga wani irin gurnani yana yi, kamar mahaukacin zaki.

Da ?yar suka ha?u suka kai shi ?asa, suka daddane shi yana cigaba da ?o?arin watsar da su ya tashi.

?aya daga cikinsu da yanayin kamanninsa ya bayyana, ?arara shaye-shaye ya huda shi, saboda yadda la??ansa suke ba?i ?irin, ga wani irin ?aton tabo a gefen fuskarsa.
A hankali yake ?an dukan bayansa cikin sigar rarrashi yana fa?in "Easy maza, easy, mun san ka na cikin damuwa da ra?a?i, amma hakan ba mafita bane ba, ka yi ha?uri muna tare da kai ?ari bisa ?ari iya wuya" ya cigaba da maganar yana rarrashin sa.

A hankali jikinsa ya saki, ya daina gurnanin da yake yi, ya lumshe idanunsa, ya rufe su, tamkar mai bacci. Sai da suka tabattar ya yi relaxing, sannan suka ?aga shi.

Major ne tsaye a gaban mudubi, yana ?ara kintsa jikinsa kamar wani matashi, ba dattijo ba, uwargidan sa na gefensa tana taimaka masa yana shiryawa, Ba tare da ya kalle ta ba ya ce "Arfa kuwa ta tafi aikin?".

Ta yamutsa fuska ta ce "Ta ga dama ta tafi"

Ya jinjina kai ya ce "Punishment ?in da na yi mata jiya, shi ya hana ta zo ta gaishe ni yau kenan,'? zan gamu da ita ne idan ta dawo".

"Dan girman Allah major ka ?yale sabgar yarinyar nan, sai ka ce itaka?ai ce ?a a gidan nan, komai ita su duk sauran ba ?a?a bane ba, da ba ka damu da lamarinsu ba?" Kallon da yayi mata ne ya sanya ta yin shiru, tare da sunkuyar da kai, bai sake ce mata komai ba, ya ?auki mukullin motarsa ya fice.

Cike da takaici ta sauka daga benen, ta fito main falon gidan tana mita.

"Yaya ya dai? Meyafaru ne?" Duk da ba ta kasance mai sakarwa abokan zamanta fuska ba, amma haka kurum ta tsinci kanta da gaya mata abun da ya faru saboda takaici.

"Major ne mana, gaba ?aya ya tattara hankalinsa a kan yarinyar nan, kamar itaka?ai ce ?a a cikin gidan nan, jiya kwana na ne, amma a barandarsa ya ?are kwanan jiya, wai yana gadinta, abubuwan nan sun fara isata"

?ayar ta ta?e baki ta ce "Ai ni na gaji, na zuba ido su ?arata, abun da ba jiya aka fara ba, ba yau ba".

Anty, wadda take ta uku, da take karyawa, duk da ba da ita suke ba ta ce "Amma dai an yi abun kunya, kishi zan ce ko ba?in ciki da ?ar cikinku"

A fusace Uwargidan major, da ake cewa Mama ta ce "Asiya, da ni ki ke ko wa?"

Anty ta ce "Duk wanda ya tsargu, sai menene dan ya nuna mata kulawa ta musamman, duk kulawar da yake bawa sauran yaran bai isa ba? ?a?a nawa ne a gidan nan, kowanne ya na bashi kulawa dai-dai da bu?atarsa ne, amma da yake kishi ya zame muku bala'i, mussaman ma ke, da kowa ma yi ki ke, kin fi mu da?ewa da shi, amma haryanzu ba ki san halinsa ba"

Mama ta ce "Ba zan yi musayar yawu da ke ba ?anwar bayana, dan ba ki isa ba, da wanda ya ajiye ki zan yi".

Anty ta ce "Idan ma ?ar cikinki ce, matsayinmu ?aya matan major, kuma ni gaskiya nake fa?a" haka suka cigaba da ?an fa?ace-fa?acen su na kishi.

Nabila kuwa da wasu lokutan a kan yi mata la?abi da Arfat, tana zaune a katafaren office, itaka?ai sai aikin danna waya take yi, cikin nisha?i kamar babu wani abu da yake damunta.

Knocking ?in ?ofar office ?in aka yi, ta bayar da izinin a shigo.

Nabila suka gaisa da matar ta ce "Nabila ko?"

Nabila ta jinjina kai ta ce "Eh"

"Ki zo Barrister yana kiranki"

"Wane barrister?"

Matar ta ce "Director. Dama ina son in yi miki magana. Kin ga wurin nan babbar organization ce, da muke dealing da mutane daban-daban, especially manyan mutane. Yana da kyau ki jajirce director baya son ragwanci ko harkar ko in kula da aiki, sai ku samu sa?ani"

Nabila ta yi murmushi ta ce "Na gane, na kuma fahimta na gode sosai" matar ta jinjina kai ta fita.

Nabila ma tashi ta yi, ta fita ta tafi office ?in da ake nemanta.

Ta tarar da shi da wani babban mutum a zaune a office ?in sa, ta gaishe su cikin girmamawa sannan ta kalli Director ta ce "Sir gani"

Ya kashingi?a ya ?are mata kallo sannan ya ce "Nabila, what is actually wrong with you ne?"

Cikin mamaki ta ce "Ni kuma? Me na yi sir?"

Ya gyara zamansa ya ce "Anya ke ki ke son zama lawyer ko choice ?in major ne? Tun da ki ka zo wurin nan you don't care, sai dai ki zauna ki danna waya, ki yi ciye-ciye, sai kwalliya. Bama kya shiga cikin ma'aikatan ki ga yadda ake aiki, balle mu ga gogewarki, mu faa tura ki trials, dama zuba miki ido na yi amma na ga baki san zuru ba" Nabila ta yi shiru ta sunkuyar da kanta ?asa.

"Ina bu?atar ganin canji a tare da ke, idan ba haka ba na fara kai ?arar ki wurin Major, yanzu muna da client da yake son yin apeal, a kan wata shari'a da wasu mutane suka kai ?ararsa. Ki je na saka ki a team ?in su barrister Habib, ki je ku tattauna yadda za ayi handling case ?in. Effort ?inki shi zai sanya na baki manyan cases to help your career"

Ta risunar da kai ta ce "Ok sir" ta juya ta fara tafiya, sai dai mutumin da tarar a office ?in, ya bi bayanta da kallo yadda ?ugunta ke juyawa, cikin skirt ?in kayan jikinta.

Office ?in Barrister Habib ta je, aka sanar da ita suna ?akin sirri, dan haka kai tsaye can ta wuce.

Ta tura ?ofar ta yi sallama, suka amsa mata, ta nemi wuri ta zauna.

Barrister Habib ya ce "Kin ga damar zuwa kenan?" Wani irin kallo ta yi masa, amma ba ta ce komai ba, su kuma suka cigaba da abun da suke yi.

Shari'a ce a kan wani attajirin mutumin ya kar?e gonakin wasu ?an ?auye, ya basu diyya ya fara ginin kamfanin sarrafa shinkafa, sai dai suka yi ?ararsa diyyar da ya biya su, ta sa?awa yarjejeniyar da suka yi da shi, dan sam bai kai darajar gonakinsu ba. Ganin ba su da galihu, ya sanya bai damu da ?arar da suka kai shi ba, sai da aka yanke hukuncin ya biya su, sannan ya ce zai yi apeal.

Mamaki ya cika Nabila, irin ma?udan ku?in da ya biya law firm ?in su, a bashi lawyoyi su kare shi, ya isa ya ?arawa mutanen nan, ya biya su ha??o?in su.

Nabila dai ta yi zuru da ido, tana kallon yadda ake harha?a hujjoji na halal da na haram, domin mutumin yayi nasara a kotu.

Ba?in ciki da takaici suka isheta, sunan ?auyen da abun ya faru kawai ya isa ka gane cewar masu ?aramin ?arfi ne. Dan galibi mutanen karaka da Allah suka dogara, da harkar noma suka dogara.

Tashi ta yi tsaye ta ce "Excuse me please, na fara jin yunwa lokacin cin abincina yayi"

Duka lawyoyin da shi kansa client ?in suka ?ago suka kalleta.

Habib ya ce "Ana tsaka da aikin?"

Ta basar ta ce"Am sorry, am having a chronic ulcer, za a iya samun matsala, idan na cigaba da zama" daga haka ta ?auki jakarta ta fice, tana mitar ba zata zauna a ?ulla wannan sharrin da ita ba, ranar lahira ta shiga uku.

Ta koma office ?in ta, ta yi alwala tayi sallar azahar, ta je ta samu Director ta sanar masa da tana da uzuri ta na son ta tafi, yayi mata iznin hakan.

A hanya ta tsayar da mai napep, suka ?auki sumayya, sannan suka tafi.

Ta kalli Sumayya ta ce "Sumy, meyafaru ne? Na ga kina wani ?ata rai"

Sumayya ta yi tsaki ta ce "Haushin kaina nake ji, da na karanci aikin jarida Arfa"

Cikin mamaki ta ce "Amma meyasa, na ga shi ne za?inki?"

"Wallahi duk ya fita daga kaina, hira aka yi da honorable Indabo, wai an yi borehole a ?ananan Hukumomin da yake wakilta, an raba kayan makaranta ga ?alibai. An kai bencina makarantun firamare da na islamiyyu. Last week aka ce na je na tattauna da al'umman local government ?in, na je ni ban ga ayyukan da aka yi ba, na tattauna da mutanen ?ananan hukumomin, sun ce ba ayi musu ba. Na kai recording ?in, aka saka, wai lawisa ba ta tantance shirin ba, ba ta sani ba aka saka, kin ga cin mutuncin da aka yi mini, wai zan lalata musu business wai sai na je na samo mutanen da zan yi hira da su, su ce eh an yi ayyukan su yi godiya alhalin ba ayi ba. Na zama ma?aryaciya kenan me zan ce wa Allah? Wai har da idan ban yi wasa ba, sai honorable ya saka an ?aure ni"

Nabila ta ce "Ikon Allah, ashe duk kanwar ja ce sumy, yo nima hakan take ai, wani tasonon Alhaji ne ya zo yayi kirim a kan kujera kamar damin doya, ya biya uban ku?i wai za a kare shi, ya cuci talakawa ko kunya bai ji ba, kuma director ya sakani a team ?in lauyoyin, ni dai ba zan yi ba wallahi, sai dai ya yi ta gaya wa Abban. Haka kurum a cuci mutane ka je ka cewa Allah me?"

"Wallahi Nabila, ba ki ji zuciyata ba, yanzu sai dai na je na tara ma?wabta na yi hirar ?arya da su, a zo a sake sakawa, kuma wai sai na rubuta takardar ban ha?uri, ki ji fa"

Nabila ta ce "Tir?ashi, wai ya ?aure ki, to ya ?aure ki shi ma ya hau da ?aurin Allah " Haka suka cigaba da tattaunawa, har suka isa in da sumayya za ta sauka.

***

Cikin tsananin tashin hankali, yake magana, kallo ?aya zaka yi masa ka san hankalinsa a matu?ar tashe yake.

Ya daki teburi ya ce "Kwamishina, dole fa ku nemo yaron nan, dole ku mayar da hankali a nemo shi a duk in da yake a ?asar nan"

Mutumin da yake zaune cikin kakin ?an sanda ya ce "Honorable, ka kwantar da hankalinka, aikinmu baya bu?atar garaje da gaggawa, sai mun bi a sannu"

"Haba Cp, wane irin bi a sannu? Rayuwata na cikin hatsari, yayi i?irarin kashe ni, dole fa a nemo yaron nan, ko be kashe ni ba, idan ya bu?e bakinsa yayi wata magana a kaina kashina fa ya riga ya gama bushewa, na san fa waye yaron nan ciki da bai"

Cp ya gyara zamansa ya ce "Amma honorable, wace irin yadda ko ala?a ce tsakanin ka da yaron nan, da har ya sanka haka, zamansa a gari yake barazana a gareka"

Tsaki mutumin yayi ya ce "Kai har ka tambayi ala?ar da ke tsakanin ?an siyasa, da tantirin ?an daba, ?an iska? Ku nemo shi dillalin wiwi ne, da hard drugs. Da kun ganshi ma kawai a harbe shi, kuma a tuhumi controllern gidan yari, a kan dalilin sakinsa, bayan ko shari'a ba ayi masa ba tsawon lokaci"

?an sandan ya jinjina kai ya ce "Shi controller ya ce court order ya kar?a"

"Ni dai ka yi mini wannan taimakon a nemo shi da gaggawa, dan yana cikin garin nan, tun da ga ayyukan ta'addanci yana ta yi yadda ya ga dama".

CP ya ce "In sha Allah, ka kwantar da hankalinka za ayi duk mai yiwuwa, zan nemi za?a?urai daga cikin mutanenmu, da suke dealing da criminal cases, very soon zai zo hannu, DSP Nasir na san zai yi abun da ya dace in sha Allah"

"Yauwwa to shikenan, ko dai sanarwa za ku yi, ace duk in da aka gano shi a kamo shi, an sake shi ba bisa ?a'ida ba"

Da sauri ya ce "No ai ba haka aikin tsaro yake ba, ai wannan abun kunya ne ga hukumominmu, yanzu sanin in da yake shi ne babban target ?inmu, dan yaron yana da wayo sosai, na bibiyi record ?in sa, sai an yi taka tsantsan sosai wurin kama shi, sai an yi amfani da dabarun aiki, hatsabibi ne sosai"

"To ayi ?o?arin hakan dan Allah".

***
Gudu-gudu sauri-sauri ta ?arasa gida, saboda azababben fitsarin da ya cika mata mararta, tana zuwa ?aki ta watsar da komai a kan gadonta, ta shiga ban?aki.
Sai da ta gama fitsarin, ta ji iska na shigarta, tayi wanka ta fito, ta tattare kayan da ta watsar, ta samu riga ta shan iska ta saka, ta shafa turare ta fita.

Kitchen ta shiga dan zuba abinci, ta ci karo da fate-faten wake a cikin food flask ?in ta. A ?ule ta ja uban tsaki, ta fito babban falo kamar ta fashe da kuka, ta hau ?walawa mai aikinsu kira.

"Baba magajiya!"

Daga can wani sashen ta amsa da "Na'am, Arfa gani nan"

"Na ga faten wake yau?"

"Eh, umarnin Hajiya babba ne, ita ta ce ayi faten wake".

Cikin ?aga murya arfa ta ce "Amma dai an san ba na ci ko? Kin dafa mini wani abun ne?"

Magajiya ta ce "Wallahi har na ?aukko doya na fara frayewa, na ?an dafa miki, na soya miki miya, aka kuma sakani aiki".

Nabila cikin kwakwazo take masifa "Saboda tsabar an tsane ni, so ake na mutu a huta, in je aiki in dawo a kasa ajiye mini abinci, sai a dafa abun da ba na so"

"Ke Nabila meye haka ne, hajiya ce ta bayar da umarnin hakan, ki shiga kitchen ki dafa wani abun mana" Nabila ta kalli Yaya Sauda ta ce "In je in dawo yanzu, sannan in shiga kitchen in hau girki, bari in je in sha faten waken, duk abun da ya same ni, ku kuka kasheni, ai kun san likita ya hana ni cin wake"

"To ki je ki ci ?in mana, idan kin mutun sai ne? Banda gulma amma ai ki na cin ?osai da shinkafa da wake, ko duk su ba waken bane ba"

Kamar ?ar goye, Nabila ta din ga zirarar da hawaye ta na bala'i.

"Kar Allah ya sa ki ci abun da aka dafa, kya mutu da yunwa agola ?ar wahala".

Cikin tsananin fusata Nabila ta ce "Tun da dai ba shegiya ba ce ni da ubana, ai da sau?i"

Cikin son kunna Nabila, Sauda ta ce "Meye marabarki da mara uban?"

Baba magajiya da ke tsaye ta ce "A'a Sauda, dan Allah kar ayi haka, ke fa babbace"

Sauda ta ?aga mata hannu tare da cewa "Babu ruwanki, ki wuce ki ?arasawa mama aikinta. Ke kuma ki tsaya ki cigaba da hauka, banda samun wuri ina na ta?a ganin agola da mi?e ?afa".

"Ai gara ni, agolar ce, kuma iya wuya ni ?ar gari ce, ba ba?uwar haure ba, jikar yarabawa. Kuma ni ba dan albarkacin ubana ba, wallahi da na da?e da barin gidan nan, gara na je na kama gida na yi zaman kaina, iyaka ace ina zaman kaina, ba ?an iskan da zai takura mini"

Sauda ta tsaya ta ce "To ki je ki kama ki yi zaman kan naki mana, ke dama banda Abba a tsaye yake a kanki, ai ?ar zaman kantan za ayi, kuma ?ar gagara".

Nabila ta bu?e baki za ta yi magana, suka ji gyaran muryar Abba, daga saman bene. Tuni idon Nabila yayi jawur, saboda kuka da ?acin rai.

Ya ce "Magajiya" cikin sauri ta ce "Na'am ranka ya da?e"

"A gabanki kina tsaye yaran nan suke fa?a? Ki ka kasa tsawatar musu?"

Ta risuna ta ce "Tuba nake ayi mini afuwa".

Sauda ta ce "Wallahi Ab...." Ya dakatar da ita ya ce "Ban tambaye ki ba, kukan me ki ke yi ke kuma?" Yayi maganar yana kallon Nabila.

"Faten wake aka yi, ba a dafa mini komai ba, kuma yunwa nake ji"

Ya ce "Wannan abun kawai shi ne abun kuka kuma? Ke a rayuwarki ba zaki ta?a girma ba kenan?" Tayi shiru tana sheshshe?ar kuka, kukan da yake jin sa har zuciyarsa.

"Magajiya, ko aikin wa ki ke yi, ki ajiye ki sama mata abun da za ta ci, ba biyanki nake dan a farantawa wani a ?atawa wani ba, duk ?a?ana nawa ne, babu banbanci a tsakaninsu"

Ta risuna ta ce "In sha Allah Alhaji, za a kiyaye"

"Ke kuma, ki cigaba da fa?a da yayyenki, zaki ga yadda zan yi da ke. Kuma na gode da furunciki Arfa, zaki yi zaman kanki ko? Tun ina raye ki ke wannan i?rarin, ranar da na mutu ban san me zaki aikata ba, kin kyauta" bai tsaya jiran me za ta ce ba, ya wuce ya koma ?akinsa.

Sauda ta yi wa Nabila gwalo, Nabila ta ce "Ai ke yakamata na yi wa gwalo, ni na yi nasara, tun da an ce a ajiye aikin babarki ayi nawa, banza ?atuwar kwabo" Nabila ta wuce ?akin su, tana tunanin ko dan wannan tijarar, ya isa tayi fatan tayi aure ta bar gidan nan.

***
?an siririn matashi ne dogo, wankan tarwa?a, sanye da kakin ?an sanda, da ?an hanzari yake bin wata doguwar baranda, wadda ta sa da shi da wata ?ofa.

Ya bu?e ya shiga da sallama, ya sarawa wanda ya tarar a cikin ofishin, wanda da gani babu tambaya, ka san babba ne sosai a cikin rundunar jami'an tsaro, duba da yanayin ranks ?in da ke ma?ale a kafa?ar uniform ?in sa, da kuma ha?uwa da tsaruwar office ?in na sa.

Ya ?ame tare da sarawa mai office ?in, ya yi masa alama da ya zauna.

Ya zauna tare da sake gaida wanda ya tarar a office ?in, da uniform ?in sa ke ?auke da sunan ACP Solomon wada.

ACP wada ya kalli matashin ya yi murmushi ya ce "CSP Nasir Yusuf"

Nasir ya waro ido ya ce "Wane ni Yalla?ai, Dsp ?in dai"

"Au Csp ?in ne ba ka so? Ba abun mamaki ba ne ba, ka ji gobe kai ne Cp na garin nan, kai koma IG gaba ?aya"

Nasir yayi murmushi yana sunkuyar da kai.

"?wazon mutum babu in da ba ya kai shi, kuma kar ka yi mamakin ?wazonka ya kai ka in da ba ka zata ba. Yanzu ba karatunka da kuma ?wazon ne ya kawo ka matakin da ka ke yanzu ba?"

Ya jinjina kai ya ce "Haka ne ranka ya da?e".

Acp Wada ya ce "Good, wani aikin za'a sake baka, wanda mu ke bu?atar sa da gaggawa, direct order ce daga Cp,ya kuma ce a jinjina maka aikin office ?in ka yana kyau"

Nasir ya tattara hankalinsa ya ce "Ok sir, na gode sosai"

Solomon wada ya ce "Nasir, idan ka mayar da hankali yadda ake so, ka gudanar da aikin nan, za ka samu cigaba a aiki sosai da sosai"

Cikin girmamawa ya sake cewa "I will do my best in sha Allah".

"Good" ya ?aukko wani file ya ajiye masa, sannan ya ce "Kwanakin baya, akwai wani ?an daba, da ya addabi garin nan, kai ?an garin nan ne za ka fi ni sani, wai shi Aminu ana yi masa la?abi da viper.
Shekarun da suka gabata yana tsare, sakamakon laifin da ya aikata, kafin kwatsam mu samu sanarwar cewa an sake shi. So bayan sakin nasa, akwai kokwanto a cikin sakin da aka yi masa ba bisa ?a'ida ba ne ba, duk da controllern gidan yari ya ce order aka bashi ya sake shi, bayan fitowarsa ya cigaba da aikata miyagun laifuka a ?oye, na sayar da miyagun ?wayoyi tare da ?yan?ysar sabbin ?an daba, da suka hana jama'a zaman lafiya a garin nan, wanda ya?i da wannan a ?ar?ashin kulawar office ?in ka yake, a zone ?in. Abun da muke so da kai shi ne, Aminu ya shigo hannu, ko ta halin ?a?a."

Nasir ya ?an yi shiru sannan ya ce "Ok sir, tabbas cases na dillancin ?wayoyi da harkar daba, yana ?ara ta'azzara, amma laifin me yayi aka kai shi kurkuku? Kuma ya aka yi, aka sake shi ba bisa ?a'ida ba?"

"Wannan ba huruminka bane ba, duk ba shi ne a gabanmu ba, kamo yaron shi ne abun da muka saka a gaba, wannan abun da ya shafi shari'a ne, ?arnar da yake aikatawa ta yi yawa. Kuma a zone ?in ka yaransa suka fi yawa, dan haka ka je ka yi iya ?o?arin ka a kai. Yabawa da nustuwarka, da jajircewar ka ya sanya muka baka aikin nan, ina nan ina saurarenka, ba a bu?atar ?ata lokaci. Ka je ka duba file ?in a tsanake, akwai sauran informations da za su taimaka maka wurin kama yaron, da duk wani record na criminal acts ?in sa yana ciki. Nan da gobe in Allah ya kaimu zaka dawo mini da file ?in. ba na bu?atar kuma ka yi wani abu sama da haka, kar ka ?etare iyakar da na gindaya maka".

"Ok sir, i will do mai best in sha Allah" ya ?auki file ?in, tare da sake sara masa ya fita.

?angaren Nabila kuwa, al'amuranta ba a samu sauyi ba, dan duk shari'ar da ba ta yi mata ba, ba za ta mayar da hankali a kai ba.
Director kuma ya bar ta ne, saboda mutuncin mahaifinta Major Yusuf da yake gani, mutum ne na gari kuma akwai tarin alkhairai da ya yi masa, shiyasa ya ?yale Nabilatake cin karenta babu babbaka.

Nabila gaba ?aya wasu lokutan sai ta ji tana danasanin karantar ?angaren shari'a, yadda wasu abubuwan suke gudanawa sam ba sa yi mata da?i.

Hausawa suka ce sai hali ya zo ?aya ake abota, ?angaren ?awarta sumayya ma haka, kusan ?alubale ?aya suke fuskanta, dan har gara ma Nabila tana da alfarma a wurin na ta aikin, Sumayya kuwa na ta babu sani babu sabo.

Yau ganin motar Abba a gida bayan ta dawo daga aiki, ya sanya ta fuskanci yana gidan, dan haka da ta zuba abincinta, sai ta hau saman benensa.

A falonsa ta tarar da shi da Yaya Nasir, suna magana, da alama magana ce mai muhimmanci suke yi, sai dai yayi shirin fita.

"Abba sannu da gida" "Yauwwa" ya amsa a ta?aice.

Sai dai ta na zama ya tashi ya yi wa Nasir sallama, ya fita ya bar falon.

Nasir ya galla mata harara.

A shagwa?e ta ce "Dsp me na yi ne? Kwana biyu duk Abba ya canza mini, kai ma kuma kana hararata"

"Ba dole ya canza miki ba, duk kin gallabi kowa a gida, bayan na dawo daga kaduna ake gaya mini wai kin je biki kin yi dare, ?arshe a haraba ki ka kwana yayi punishing ?in ki, ba ki zo kin bashi ha?uri ba. Law firm ?in ku director ya kawo masa ?ara, daga danna waya sai kwalliya ki ka iya, ba kya son aiki, yayi ta bashi ha?uri ya ce a kula da ke a koya miki aiki, ko ba a biya ki ba, shi zai din ga biyanki salaryn. Kwatsam jin kunnensa ya ji ki na cewa ba dan shi ba, zaman kanki zaki yi, kin san kwana nawa ya ?auka ba ya bacci saboda wannan maganar da ki ka yi? Duk cikinmu babu wanda Abba yake lelensa kamar ke, amma sai ba shi kunya ki ke ko ta ina?"

Cikin sanyin jiki, da tashin hankali ta ce "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, ban zaci ran Abba zai ?aci har haka ba, to kuma ba ka bashi ha?uri a madadina ba? Yaya sauda ce fa take ce mini agola, ni kuma ba na son na gaya masa. Ba na son fushin Abba, dan Allah ka tayani ba shi ha?uri. Maganganun Sauda ne suka ?ata mini rai, na yi dana sanin abun da na fa?a, amma dan Allah Yaya Nasir ka bashi ha?uri"

Ya girgiza kai ya ce "No ni ba ruwana"

Kuka ta saka masa tana cewa "Wallahi ba zan ci abinci ba, sai yanzu na ji maganar da na yi, ta yi nauyi ban san abba zai ji ba"

"Kin ga ya isa, kar ki saka ciwonki ya tashi na shiga uku, ya mayar da fushin da yake yi da ke kaina" ai kamar ya sake tinzirata, ta cigaba da sheshshe?ar kuka.

Cikin tsawa ya ce "Ke wai dan ubanki meye haka? Am i your mate, ba magana nake yi miki ba?" Sai da ta razana, amma hakan bai saka ta daina kukan ba.

Ya zuba mata ido, Nabila tun asalinta tun tana yarinya take fama da taurin kai na tsiya, yanzu ko dukanta zai yi, ba za ta daina kukan da take yi ba, balle ma yanzu ba wannan dan ta girmi duka. Har mamakinta yake yi, ?atuwar budurwa ta kammala degree, kusan

Please Login or Register in order to submit comment