Reading KARFE A WUTA Chapter 83 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

?yar jami'an tsaro suka kawo masa ?auki, suka tarwatsa matasan, suka ?auke shi a galabaice, dan ba su zaci yana raye ba, suka kai shi Asibiti.

*****
"My Abdul" ta yi maganar tana murmushi, cikin hanzari ya ?ago, dan bai zaci daga bakin ramma maganar ta fito ba.

"Meyafaru ne? Gaba ?aya na ganka a cikin tashin hankali?"

"Rahama abubuwa sun ?ara caku?e mini, barin ?asar nan zamu yi"

Cikin mamaki ta ce "Mu bar ?asar nan, mu je ina?"

"Rahama abubuwa ba zasu tafi yadda na tsara ba, zamu bar Nigeria"

"Ban gane ba, uwata fa?"

Abdul ya ce "Zan saka a kawo miki ita, yanzu visa za ayi miki, amma sai na fara barin garin nan da ke"

"Abdul, ni fa gani nake wannan guje-gujen, duk ba zasu kaimu ba, kayi ha?uri ka yi abun da mahaifinka ya bu?ata mana"

Ya kalleta ya ce "Na kai ki kotu ki gaya wa duniya, ni ne nayi miki fya?e? Ba wannan ne ya dame ni ba, abun da zai biyo bayan shaidar da zaki bayar shi ne abun jin, dan haka ki nutsu kiyi abun da na ce kawai"

Murmushi ta yi masa da ita ka?ai ta san ma'anarsa, ta wuce shi ta tafi kitchen.

****
Daga Naja'atu har Indabo fuskokinsu ?auke da damuwa, Bunkure tayi ?wafa ta ce "Gaba ?aya hankalina a tashe yake, lallai gaskiyar hausawa, ?an hakin da ka raina, shi ne yake tsole maka ido, yarinyar nan dai ta dage sai ta ga bayana, idan asirina ya tonu, ban san wane irin kallo zan yi wa al'umma ba. Abdul duk shi ya janyo wannan abun.

P.A ya ce "Duk ku kwantar da hankalinku, babu wani abu da zai faru, kamar yadda ka yi umarni, dattijon nan zai shiga silent, yanzu uwar yarinyar ta rage, ita muke binciken in da take, kuma ita ma zamu ganota in sha Allah, Abdul ma muna daf da gano, wurin da ya ?oye yarinyar nan"

Indabo ya girgiza kai ya ce "Ban san in da Abdul ya koyi wannan ba?in taurin kan ba, magana ta fito fili, an ce a binciki ministocin da muka ?ulla har?allar ku?a?en nan da su, na san kuma dole sai sunana ya fito, wai ya kwashe ku?in nan, ya yi wa yan ?auye ayyukan raya ?asa, na rasa uban abun da ya samu a jikin yarinyar talaka mara galihu, ya nace mata take abun da ta ga dama har haka"

Bunkure ta sauke numfashi ta ce "P.A ya batun barrister Nabila?"

"Kamar yadda na gaya muku, sponsiring ?in ta ake yi, na gwada sakawa a kamo mini ita, amma hakan ya gagara akwai jami'an da suke bin ta, wanda ba san suwaye ba, kuma da alama ita kanta ba ta san suna bin ta ba"

Indabo ya ce "Kar ku ja da nisa, kankarofi ne, babbar bu?atar sa ya ga ya kai ni ?asa, ya rama abun da nayi masa, kuma yayi ka?an".

*****
Nabila na zaune a ?akinta, tunanin ma ta rasa wanne yakamata ta yi, kawai ta ga Nasir ya shigo ?akin, ba ta ko motsa ba, balle ya sanya ran za ta kula shi.

"Nabila"

Ta ?aga ido ta kalleshi. "Da gaske ke ki ka nemi a hana kama Aminu Viper"

"Eh" ta fa?a a nutse.

"Nawa aikin ki ke burin ?atawa kenan, me nayi miki haka ne?"

Ta kalleshi ta ce "Ba kai nake fatan ?atawa aiki ba, duk wani mara gaskiya sai na ?ata masa aiki. Gaba ?aya ka canza i miss my old DSP, the only person that understand me" tayi maganar tana tashi ta bar shi a ?akin.

Tana office ?in ta, tana son zuwa duba jikin malam garba, tana son zuwa wurin 'yan sanda, tana son ganin Viper, ga kuma maganar Abba da ta tsaye mata, da ya ce taje ta nemi ubanta, ta bar masa gida.
Kenan Abba ya goyi bayan ?an sa, shi ma a wannan karon ya nuna mata, gurbin ido ba ido bane ba.

Turo ?ofar office ?in aka yi, ta tashi zaune sosai daga kashingi?ar da tayi, tana tunanin ina ta ta?a ganin ba?on nata.

Ya samu wuri ya zauna, suka gaisa, ya ce "Baki gane ni ba ko?"

Ta jinjina kai ta ce "Gaskiya dai"

"Haka ne, magana na zo mu yi da ke mai muhimmanci"

Nabila ta ce "Ok, ina jinka"

"Sa?o ne daga wurin distinguish Ma'aruf Indabo, na zo mu yi magana mu fuskanci juna da ke"

Nabila ta yamutsa fuska tana kallonsa.

"Muna yi miki tayin ki fanshi kanki da kanki ne, kan abun da ba a so ya afku"

"?an yi sauri, ina da wurin zuwa"

P.A ya ce "Maganar da na zo da ita, ta fi abun da zaki je yi muhimmanci, muna son ki janye shari'ar nan ta batun fya?e nan, case ne tsakanin ki da Bunkure, kuma ko yanzu kin cika burinki a kanta, akwai ma?udan ku?a?e muddin ki ka aikata abun da na ce"

Nabila ta ce "Malam na yi maka kama da shashasha ne? Da Bunkure nake case ?ina, meye nasa a ciki? Bibiyar rayuwata da ya saka aka din ga yi, da ?o?arin kashe ni, duk bai ishe ku ba, shi ne zaka zo mini da maganar bunkure? Wallahi idan kaga na bar case ?in nan, to an hukunta ainihin mai laifin ne, kuma muddin wani abu ya same ni, kai ko mutuwa nayi, ina da manya manyan hujjoji a kan sa, da suke a hannun wakilai ne, akwai wanda za su ?ora, in sha Allah sai na bayar da misali a Nigeria, an fara hukunta masu ri?e da madafun iko, da iyalansu, ba wai doka a kan talaka kawai ba, everyone is equal before the law"

"Haka ki ka ce?"

"Hala kurma ne kai?"

Ya ce "To bari mu gani, yaro bai san wuta ba sai ya taka"

"Na santa farin sani, tun da na ?aukko ?ARFEN CIKIN WUTA, da ya gagari hannaye da yawa"

P.A ya kalleta ya ce "Me ki ke nufi?"

"Zaka fahimta nan ba da jimawa ba"

Yana fita tayi tsaki, ta ?auki jakarta ta fita, a nan ta bar motarta, ta hau abun hawa ta tafi gidan Viper.

Yana tsakar gida, daga shi sai ?an mama a gidan, suna hira.

Sun da?e suna kallon juna, sannan ta ?arasa ciki, ta samu wuri ta zauna ba tare da ta ce masa uffan ba.

Ya samu abu ya zauna, ya ce "Ya ake ciki, meye labari?"

"Ko ka neme ni, kwana biyu ina cikin damuwa da tashin hankali, amma ko a jikinka"

Ya tsuke fuska ya ce "Menene?"

"Vi"

Ya Kalle ta, tare da ?age girarsa ?aya.

"Ka dubi girman zatin Allah, ka tausaya mini, ina ga ciwon zuciya na daf da kamani, kowa ya ja da baya ya juya mini baya, Abba ya yayyaga hotunan nan ya watsa mini, ya ce naje na nemi ubana na bar masa gida, daga shi har yan gidanmu, babu wanda yake kula ni. Gashi a tsakiyar program sumayya ta hau yi mini tambaya a kanka, yanzu ta ko ina mutane sai attacking ?ina suke yi a media, saboda case ?inka, client ?ina malam garba wai ya yanke jiki ya fa?i na je na duba shi, na tarar wai ya samu stroke, yanzu P.A ?in Indabo ya bar office ?ina da tashi barazanar, kuma haryanzu ka ?i gaya mini dalilin da ya sanya Indabo yake bibiyata. Na rasa ya zan yi me zan yi ne? Kamar na gaza, ba wanda zan je na samu duk na gaya wa damuwata, dan Allah Viper ka gaya mini wacece ta jikin hoton nan, ina jin kamar ina da ala?a da ita, tun da ni dai na san ba ni bace ba, dan Allah idan akwai wani abu da ka sani ka gaya mini, atleast na rage wata damuwar".

"Na gaya miki ban san komai ba, 'yan gidanku zaki tambaya"

"Na gaya maka ba zasu gaya mini komai ba, so kake sai na mutu ban san babana ba, idan kana da yadda zaka yi ka taimake ni dan Allah, ko hakan ne alfarmar da ya rage da zaka yi mini a rayuwa" tayi maganar tana ha?a hannayenta biyu cikin sigar magiya.

"Ana kiranki a waya"

"Ni ba ta waya nake yi ba, ka taimaka mini dan Allah"

"Ki ?aga wayarki " yayi maganar yana kallon ta.

Ta ?aukko wayar, ta ga lambar barrister Habib ce, ta ?aga wayar ta ce "Hello"

"Na duba office ba kya nan, Allah ya yi wa malam garba rasuwa yanzun nan" mi?ewa ta yi tsaye, ta saki wayar, ta tashi za ta nufi hanyar fita, jikinta yana rawa.

Cikin zafin nama, Viper ya tashi ya ri?e ta, gaba ?aya ta gigice, ta ce "Sun kashe shi, wallahi kashe shi aka yi"

Ya ce "Waye? Waye ya kashe shi?"

"Malam garba, wayyo Allahna, meyasa na kar?i shari'arsa, na janyo ya rasa raywarsa a banza, bani da sa'a wayyo Allah zuciyata" wata irin mi?a tayi, kamar zata zare, ta fara kokowar ?wace wa daga hannun Viper, tana kallon hanyar waje.

Ya ?ara ri?eta ya ce "Abla, tsaya ki ji, ki nutsu"

Magana take son yi, amma numfashinta ya din ga sama yana ?asa, hannunta da ya ri?e, ya din ga jin bugun zuciyar ta da sauri-sauri.

Ya ciro wani abu a jikinsa, ya saka mata a gefen wuyanta, gaba ?aya jikinta ya saki.

Ya kalli ?an mama ya ce "Ka kira mutanen nan a waya, su aiko da mota, a kaita Asibiti"

?an mama yayi saroro ya ce "A ina ta ajiye motar tata?" Viper ya ?ura masa ido, ya ce "Au, ammm wasu mutanen?"

"A tunaninka duk abun da ka ke yi ban sani bane? Zaka kira su ko ni na kira su?" ?an mama yayi wi?i-wi?i da ido, cikin tsoro da mamaki".

"Am talking to you, and you are looking at me" ba shiri ?an mama ya ciro waya yana kallon Viper.

****
"Abdul yau ka addabe ni, kamar nayi maka dukan tsiya haka nake ji"

"Sorry baby, kin san kullum ke ta musamman ce, i so much love the natural you".

Ramma ta ce "Wallahi ka isheni, duk ka dame ni"

"Wallahi wani mafarki nayi da bai yi mini da?i ba, ya bani tsoro".

Ramma ta ce "Maganin wanda baya addu'a"

"Wallahi ina yi, har karatun Alqur'ani nake sakawa fa"

Ta ce "To Allah ya bada lada, yanzu ka bani wuri na je nayi wanka, zan yi salla".

Ya tashi zaune ya ce "Mu je, daga nan sai ki ?an dafa mana wani abun, yunwa nake ji"

Yayi maganar yana ?agota, daga kwancen da take.

A tsakiyar gado suka din ga ciye-ciye da shi da ramma, suna yi yana tsokanarta, tana gaya masa ba?ar magana yana dariya.

Tamkar ya mayar da ramma cikin sa haka yake ji, kuma ya kasa ?oye mata hakan, suka kwanta ya gama damunta, bacci ya kwasheta.

Juyi ta yi zata gyara kwanciyarta, ta ga Abdul a zaune, ya saka wayarsa a gaba, ya ?ora hannu a ka, yana wani irin kuka tamkar ?an ?aramin yaro.


Ayshercool
08081012143
???500 ne via 0009450228
Aisha Adam jaiz bank sai shaidar biya ta 08081012143
Wanda za su jira document 1K ne.

90009343
'Yan Nijar ku turo katin airtel na 300fcfa


https://whatsapp.com/channel/0029Va9QtrY4dTnBYG1hST2VHADARIN

*BRIGHT PENS SECOND BATCH*

Ku kasance da littatafan bright pens, second batch.
*?ARFE A WUTA (AYSHERCOOL)*
*MUTALLAB (NIMCYLUV)*
HADARIN GABAS (NAZEEFA NASHE)*
*ZAYTOON (ZEE KUMURYA)*


Tashi ramma tayi, ta ce "Abdul, wai menene meyafaru ne?" Yayi mata shiru ya cigaba da kuka.

"Dan Allah kayi magana mana, ko mutuwa aka yi muku?"

Yayi mata shiru bai yi magana ba, ta kai hannu zata ?auki wayar, amma ya janye wayar ya kashe.

Kawai ya yin?ura, ya ?auki mukullin motarsa, ramma ta mi?e ta ri?e shi ta ce "Ina zaka je ne?"

"Fita zan yi"

"A wannan yanayin da ka ke? Idan wani abu ya sameka fa, dan Allah koma menene kayi ha?uri, zuwa Allah ya kaimu gobe, dan Allah ka ha?ura da fitar nan" jifa yayi da mukullin, ya koma ya zauna ya cigaba da kuka.

Ta zauna a kusa da shi, cikin damuwa ta cire masa hannunsa da ya rufe idanunsa ta ce "Abdul, kalleni menene wai?"

Ya sake sunkuyar da kai, kamar ita ce baya son ha?a ido da ita. A hankali ya kwanta a jikinta kamar ?aramin yaro, ta rungume shi sosai, tana shafa kansa ta ce "Koma menen kayi ta nanata Innalillahi wa Innalillahi raji'un, zaka samu sassauci in sha Allah" wata irin ajiyar zuciya ya din ga yi, wanda sai da ya bata tsoro.

"Rahama" ya kira sunanta da kyar a galabaice.

"Dan Allah ko na fuskanci hukunci, kar ki manta da ni, na san koma menene zuwa ki gama karatunki, zan fito"

"Tom" ta fa?a a sanyaye, dan wasu lokutan har tausayi yake bata, gaba ?aya Abdul ya saduda, duk wannan iskancin da rashin mutunci ba ya yin su.

"Rahama kin ce mini kina da yaya da ?ani ko? Har su ina son in ?auki nauyin su"

Ramma ta ce "Ba na gaya maka yayana ya mutu ba, sai ?anina sani"

"Da gaske ki ke fya?e aka yi masa ya mutu?"
Ta ce "Oho ina na sani, ba ka ce mini ba a yi wa maza ba, ni kamar haka na so na ji an ce, wai za a samo masa aiki, yaje Abuja aka yi masa, amma mama ba ta ta?a zama ta gaya mini yadda abun ya faru ba, ko tunawa ba ta son yi, idan ta tuno da shi tayi ta kuka"

Yayi ajiyar zuciya ya ce "Ban san me zai faru ba, amma dan Allah duk tsanani kar ki rabu da ni, ki zama mai yi mini uzuri da tausaya mini dan Allah, Allah ma baya kama wani da laifin wani"

Ramma ta ce "Da bana yi maka uzuri, da bana tunanin zamanmu zai zo i yanzu, ka daina wannan kukan dan Allah kunya kake bani" tayi maganar da sigar tsokana.

Ya ?an?ameta ya cigaba da sheshshe?ar kuka.

"To ?an jariri, ya isa haka, cikin dare kawai mutum ya tashi yana kuka, ko ka je ka yi alwala kayi salla".

"Ba zan iya ba, ba zan yi karatun sallar dai-dai ba"

"Kaga amfanin ibada ko, idan bawa ya tuna da Allah, lokacin da yake cikin yalwa, Ubangiji yana tuna wa da shi lokacin da yake cikin ?unci, ka cigaba da addu'a, Allah ya yaye maka damuwar ka doctor Abdul yasar" yayi lamo kamar kyanwa a jikinta, ba tare da ya kuma magana ba.

****
A hankali Nabila tayi juyi, tana ?o?arin gyara kwanciyarta kawai ta ga Viper a zaune a kan kujera, yana danna waya. Ta ?ura masa ido tana kallon sa.

"Wannan kallon haramun ne, ki daina yi mini wannan kallon" yayi maganar ba tare da ya kalleta ba. Ko ?ifta ido ba ta yi, ta cigaba da kallonsa.

Ya waiwayo sosai yana fuskantar ta, ya ce "Ya aka yi ne? Ya jikin?"

Ta ?aga hannunta, ta kalli drip ?in da yake shiga, ta ce "Vi"

"Mmm"

"Ina ne nan?"

"Wurin sayar da mutane" yayi maganar yana cigaba da danna wayar.

Ta lumshe idanunta ta bu?e, ta ce "Kamar bacci nake yi, kuma kamar a zahiri ne, dan Allah da gaske malam garba ya mutu?"

Viper ya ce "Eh, ya mutu"

Ta girgiza kai, tana kuka daga kwance ta ce "Ai shikenan, ya mutu bai sha?i iskar 'yanci ba, ban cika masa al?awarin da nayi masa ba, da yaya zan kalli iyalinsa? Kullum da shi nake kwana nake tashi a zuciyata, ya mutu da mummunan tabo a zuciyarsa da rayuwarsa, ban cika masa al?awarin da nayi masa ba, na gaza na kasa" tai maganar tana fashewa da matsanancin kuka.

"Ke, wai baki da tawakalli ne? Shikenan ke ba zaki mayar da lamarinki ga Allah ba? Wani ya ce ke ki ka kashe shi ne?"

?ara sautin kukan ta yi, ta ce "Ya ka ji da aka kashe matarka, ya zuciyarka tayi da aka ?ala maka laifin kisanta? Haka iyalan malam garba suke ji, da wannan ?acin da ba?in cikin ya mutu, kuma ni ban yadda da wani stroke ne ya kama shi ba, wani abun suka yi masa" Viper ya janyo kujerarsa gaban gadon sosai, ya matsa daf da ita, ya ce "Ki yi ha?uri" ta kalli cikin idonsa ta ce "Kai yakamata na bawa ha?uri nayi al?awarin saka kotu ta wanke malam garba, a gurfanar da ainihin wanda yayi laifin, amma ya rasa rayuwarsa ina kan ?adamin aikin, na fara tsorata kamar ba zan iya ba Vi"

Ya girgiza kai ya ce "Zamu cigaba da ?o?ari, ba zamu gaza ba, ba zamu sare ba, zamu yi nasara in sha Allah, idan kina cewa kin karaya, nima karaya nake yi" ta ja wata irin ajiyar zuciya ta kalli rigar jikinsa.

"Vi"

"Mmm"

"Me kake ?oye mini ne? Ba irin wannan rigar ka yaga lokacin kana Asibiti ba, mai tambarin dragon ?in nan ba?"

"Ki daina saka ido, kina ?irga mini kaya, son rigar nake yi" hararsa tayi ta ce "Am not kid"

"You are" yayi maganar very serious.

Wani ne ya shigo ?akin Nabila, yana shigowa ya ce "Viperrr" ya kira sunan yana jan sunan, tare da dun?ule hannunsa, ya mi?awa Viper, Viper ya dun?ule nasa suka ha?a.

Ya ce "Ya madam, ta tashi? Barrister ya ?arfin jiki?"

"Ba sau?i" ta fa?a tana tura baki.

Duka suka kalleta, ya ce "Subhanallah, ba sau?i fa, garin yaya meyafaru?"

Ta nuna Viper, ta ce "Baya son na warke, bai iya jinya ba sam" dariya ya yi ya ce "Maza gumbar dutse, ina Viper zai iya jinya dama, ki manta da shi, zaki samu sau?i in sha Allah, meyake damunki yanzu?"

Ta girgiza kai ta ce "Babu komai, ?irjina ne yake nauyi kawai"

"To ki cire damuwa daga ranki, zai daina in sha Allah"

Ta ce "Ok sir, na gode sosai" yayi rubuce-rubuce a file ?in hannunsa ya fita.

"Vi"

"Mmm"

"Wai ina ne nan? Kuma waye wannan ?in?"

"Asibiti da likita"

Nabila ta ce "Ai na san asibitin ne, ina son tafiya ne, zan je na ga malam garba"

Viper ya kalleta ya ce "Kina da abun gaya wa iyalinsa ne?" Jiki a sanyaye ta girgiza masa kai.

"To sai ki daina maganar zuwa"

"To ina son na gaya wa yan gidanmu ina Asibiti, kar a neme ni"

"Wa zaki kira? Wanda ya ce ki bar masa gida ki je ki nemi babanki, ko kuma yayanki da yake yi miki bita da ?ulli? Ko kuma sauran yan gidan da suke yi miki kallon yar hana ruwa gudu? Ba wanda ya damu da ke, mutum ?aya ne, kuma a halin yanzu an gur?ata masa tunani, na ta?a tsintar kaina a cikin wannan halin. Mata guba ne mai masifar dafi da saurin kashe wanda suka hara. Annabi Sallallahu alaihi Wasallam yayi gaskiya, da ya ce Bai bar wata fitina a bayansa da take cutar da maza ba a bayansa sai mata, banda haka me zai sanya mace ta raba ?a da uba?" Yayi maganar jijiyoyin kansa na kumbura, idanunsa suka yi ja, suka ciccika da hawaye, tuna mahaifinsa da ya yi.

"Ni ba guba bace ba, idan ka yi wa dukkan mata ka kira mu da guba, baka yi mana adalci ba, yakamata ko albarkacin jauhar mu ci, ka din ga kallon wasunmu ne gur?atattu, kamar yadda kuma a jinsinku yake da akwai gur?atattu"

Yayi shiru tare da sunkuyar da kai, saboda sake soso masa wurin da yake yi masa ?ai?ayi.

****
Indabo yana zauna yana karyawa, tare da matarsa, kawai Abdul ya fa?o tsakiyar wurin da suke cin abincin.

"Meye haka Abdul, baka iya sallama ba baka iya gaisuwa ba"

Indabo ya ce "Ko giyar ka je ka sha, ka yi shaye-shaye ne?"

"Na daina shan giya da miyagun ?wayoyi, tun bayan da rahama ta shigo rayuwata, ta haskar ba?ar bayahudiyar rayuwar da kuka tarbiyyantar da ni a kai, kodayeke gara ma ni shan giya ne da neman mata kawai, but am so much disappointed on you, nayi dana sanin kasancewar ka mahaifina. Dama a tsatson talakawa na taso, talakawa futuk sai ya fiye mini wannan mummunar rayuwa da iftila'in kasancewar ka mahaifina"

"Abdul, uban naka ka ke gaya wa haka? Duk iya ?o?arin da yayi na ?arar da rayuwarsa wurin ganin ya gina ku, ka zo gabansa kana gaya masa wannan maganar?"

"Mummy! Wace irin gina rayuwarmu, gangar jikin da aka gina da zunzurutun haramun da jinin mutane? Haba mummy da alama mafitarki kawai ki ka nema, ya sanya ki ka auri Daddy, wallahi mu 'ya'yanki baki yi mana adalci ba, kuma a yau ba sai gobe ba, zan bar ?asar nan, na nesanta kaina da ku, tun kafin asirinka ya tonu a idon duniya abun da ka yi ya shafe ni, gara in kalli duniya a hukunta ni da laifin fya?e da nayi, da a hukunta ni da mummunan laifin da ka aikata, ga waya nan ka kar?a ka saurari sa?onka"

Yayi maganar yana mi?a masa wayarsa, Indabo ya saka hannu ya kar?a, yana dubawa.

Wani audio ya fara bu?ewa, sai dai jin muryar wanda yayi message ?in kawai, ya rikita masa lissafi, ya fara gumi hannunsa ya hau rawa.

"Wanna sa?on ba naka bane ba, na mahaifinka ne. Duk da ina da access na yadda zan same shi, amma yafi dacewa na tura masa sa?on ta hannunka, sai yafi kar?ar sa da muhimmanci. Lokaci yayi da zamu daina buga wasan 'yar ?uya da kai indabo, zamu yi wasa na ?e?e da ?e?e, saboda ina daf da barin ramina da nake ?oye, na cigaba da addabar rayuwar ka ta kowane hali. Idan ka muzgunawa Nabila, tamkar jauhar ka ta?a mini, ta?a jauhar kuwa ta?a zuciyata ne kai tsaye. Dan zan yi wasa irin wanda ka ke so ayi.
Ka so ta zama tarkon da zaka yi amfani da shi ka kamani, shi kuma Allah ba azzalumin sarki bane ba. ?anka ya yi wa rahama fya?e ?anwar Nura, da ka lalatawa rayuwa ka kashe, ka ?orawa wani daban, kuma ka bishi ka saka an kashe shi. Abun da baka sani ba shi ne, ina da cikakkiyar shaidar mummunar ?abi'ar da ka ke aikatawa, ta lalata rayuwar matasa da sunan sama musu aikin yi.
Sannan ni na saka aka kama ?anka Jafar, a Mexico in da ya gudu neman mafaka bayan yayi kisan kai, haka zalika yanzu ma da saka hannuna a mayar da shi amurka.
Yanzu haka miyagun ?wayoyi da hodar iblis ?in da aka loda maka a jirgin ruwa, za ayi safararsu ta ruwa, za a kama su a ga?ar tekun italy. Kamar yadda nayi maka aike na farko, ina tare da Simon kuma shi ya bani wannan sa?on naka".

Jiki na rawa ya bu?e videon, shi ne a cikin videon, yana ta kokowa da Nura guduma, wasu irin ?arti majiya ?arfin gaske, suka ri?e Nura, yana kururuwa yana ?o?arin ?watar kansa, amma abu ya gagara, kuma ba iya fuskar Indabo ba ce a videon, har da wasu daga cikin manya a ?asa.

Da ?yar Indabo ya iya ?aga ido, ya kalli Abdul, ya ha?iye wani irin abu mai yaji da ?aci, ya kasa magana. Abdul kuma ya ?ure shi da ido, yana jiran ya ji mai indabon zai ce.

Mahaifiyar Abdul tayi shiru, suka yi tsuru-tsuru.

"Na tabattar ba sharri aka yi maka ba, kai ne a jikin videon nan, naga baka bu?e sauran audios ?in ba, amma ya tabattar da cewa, mutum goma ne suke da videon, muddin ka cigaba da takura musu, sai sun sake shi a duniya, kuma sai an ?auki mummunan mataki a kanka, babban takaicina me zan cewa rahama, yarinyar da nake nema ta yafe mini, ashe akwai babban aiki a gabana jawur, kai kayi silar mutuwar ?an uwanta, tayaya mahaifiyarta zata yafe mini ta bari na cigaba da rayuwa da ita?"

"Abdul ka cigaba da rayuwa da wa? Tona wa mahaifinka asiri zaka yi? Satin bikinka ya kama kana nufin zaka yi aure kuma ka ajiye karuwa?"

"Rahama ba karuwa ba ce, aurenta nake yi, kuma yau zan tattara na bar garin nan da ita, da wannan abun kunyar da ka aikata"

Indabo ya ce "Aurenta ka ke yi kamar yaya?"

SOME MONTHS BACK.

Abdul ne ya shigo, ya tarar da rahama a raku?e, a jikin gado, idanu duk sun kumbura saboda kuka.

"Wai ba zaki raba kanki da wannan kukan ba? Aikuwa kina tare da wahala, dan kuwa yanzu ki ka fara, tashi ga abinci"

Ta ?ago ta kalleshi ta ce "Ba na ci, ka ?yale ni na mutu, ai tun farko cewa kayi zaka kashe ni, menene na ajiye ni kana tozarta rayuwata, saboda kawai ina 'yar talaka? Talauci ne ya saka na fita aikatau, da burin yin karatu, mahaifiyata ba zata iya ?aukar ?awainiyata ba, ban da haka killace ni zata yi a tare da ita, ba zata bari ma ka ganni ba balle ka keta mini haddi" ta yi kneel down ta ce "Dan girman Allah ka kasheni na huta"

"Ke naji, kin cika mini kunne da koke-koke, zan mayar da ke"

Ta girgiza kai ta ce "Ko ka mayar da ni, ba zan yi daraja ba, abar ?yama zan zama, kawai ka kashe ni, ka kaiwa mama

Please Login or Register in order to submit comment