Reading KARFE A WUTA Chapter 76 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da ni a wuri daban, tsawon wannan lokacin" wani lafiyayyen mari Indabo ya ?auke Abdul da shi, ya dafe kuncinsa ya ja da baya.

"Abdul yasar, yaushe ka yi girman da zaka yankewa kanka hukunci ba tare da sanina ba? Yanzu duk dambarwar da ake yi yarinyar nan na tare da kai? Audio da yake yawo aka ce muryar babarta ne, da gaske kenan zuwa ka yi ka ?auke ta, saboda mahaukaci ne kai, sai ka je da kanka, ba ma turawa ka yi a ?aukko maka ita ba, lallai ta tabbata baka da hankali dabba ne kai, wallahi ba zaka lalata mini siyasa ba duk wannan wahalar da nayi ta tashi a banza ba"

"Daddy, dan Allah ka fahimce ni".

"Shut up my friend, ubanka zan fahimta ka je ka kawo mini yarinyar duk in da ka kaita, kafin na casaka wallahi ba zan bari ka tona mini asiri ba, saboda hauka da wautarka ba, fice ka bani wuri kan na tattaka ka"

Abdul ya tsuke fuska sai hura hanci yake yi, ya fice, sam bai ji cewa ko indabo zai jajjaga shi, zai kai masa Ramma ba, ko ya yarda ta tsaya a gaban kotu ba, sai dai ayi duk wadda za ayi.

***
Bayan farfa?owar Viper daga baccin da allura nan ta saka shi, ya din ga mamaki, wace irin allura ce haka, bai takura da kansa da dogon tunani ba, sai dai yadda ya din ga jin ina ma, ya yi wa Abdul mummunar illa, kan ya baro asibitin, sai kuma wata zuciyar ta tuna masa, ba shi ne yayi masa laifi ba. Wata zuciyar kuma ta ce kai ma ba matarka ce tayi musu laifi ba, suka kasheta.

Ya tashi ciwon cikin da sau?i, ya yi alwala ya rama sallolin sa, da daddare ya zauna yana jiran kiran wayar Nabila da daddare, dan ya san ba zata iya zuciya ba, sai ta kira shi ta ji ya jikinsa, amma shiru ba ta kira ba, har cikin dare idan ya juya, sai ya duba wayarsa ko ta kira bai sani ba, amma babu kiranta, shi ma kuma ya kasa kiranta.

Abba kuwa godiya ya din ga yi wa Allah, da likitoci suka tabattar masa da ba wani abun tashin hankali ne ya samu Nabila ba, ta bugu ne a ka, kuma babu internal injury, sai hannunta da ta samu gocewar ?ashi shi kawai za a gyara.

Mama ta hau masifa, ta ce "Ba dai ita yar gata ba, an ?auki mota an bata ba, Allah ka?ai ya san tu?in gangancin da take yi, ko dan ma tayi burga a titi, gashi ta tayar da mutane tsaye"

Abba ya ce "bata tayar da kowa tsaye ba, babu wanda na yi wa dole ya zo ya zauna mini da ita, a da ma baku yi ba sai yanzu? Kuma tu?in da take yi, ai masaniyar doka ce ita ma, ba wani tu?i da take yi na ganganci, jarabta ce kawai Allah ya kawo, kuma ya ta?aita, Magajiya zata yi mini jinyarta, zuwa a sallameta, ban ce dole ayi mini ba" mama ta ja bakinta tayi shiru, jin abun da ya ce.

Ya cigaba da kallon Nabila, cikin tsananin tausayawa, kwanan nan abubuwa sai samunta suke yi, daga wannan sai wannan.

***

Nasir ne zaune a gaban Indabo, fuska babu walwala Indabo ya ce "Naga alamar aikin nan baka ?auke shi da muhimmanci ba, idan har ba zaka iya ba, zan saka a canza mini kai, nayi abun da nake ganin shi ya dace".

"Ina mai baka ha?uri, amma komai ya kusa zuwa ?arshe"

"Idan ma baka kawo shi ba, ni zan kawo".

***
Hafsa ce zaune a gaban baba ta ce "Baba"

Ya ce "Na'am ?ar baba"

"Baba na san ai kai ba zaka ?aryata ni ba ko?"

"Eh mana yaya zan yi na ?aryata ki ma?"

Hafsa ta gyara zamanta ta ce "Ai dai ka san na warke yanzu, bana yawo, ba na shan komai, kuma na warke ai dai ko?"

Ya ce "Alhamdilillah kam, duk na sani hafsat"

"To yadda naga jauhar yau Allah ya nuna mini annabi haka, ta saka ni?ab, da irin tafiyarta, da irin idonta, amma sai da na ganeta, na so na bi ta, yaya saifu ya kira ni, na nemeta na rasa"

Baba ya ajiye cokalin sa, ya ce "Anya kuwa warkewar nan hafsa? Yaya za ayi ki ga wanda ya riga ya mutu, kuma ta cikin ni?ab ?in ki ka iya gane ita ce?"

"Haba Baba, ka san dai yadda nake da jauhar, amma ko ina ga fatalwarta ce, amma dai da ko da ta zo mini a fatalwa, sai ta tsaya mu gaisa, bai kamata ta nuna kamar ba ta sanni ba, ina ga haryanzu haushina take ji, saboda na auri Alhaji mu'azzam yakamata ai ta yafe mini, ba ta ga irin wahalar da na sha ba, ai ko gaisawa sai ta tsaya mu yi. Ka ce na din ga yi mata addu'a, ina yi mata fa, amma duk ba ta ga wannan ba, ta share ni, ban san ya aka yi waliyiyyarka ta koyi wannan halin ba baba" tayi maganar tana kuka iya ?arfin ta.

Ya share hawayen da yake shirin gangaro masa, ya ce "Bata kyauta miki ba, zan yi mata fa?a, amma ina ga zamu koma Asibiti ganin likita".

Hafsa ta ce "Baba da hankalina fa, ba hauka nake yi ba, ina sane da duk abun da nake yi fa" Mama ce ta shigo ?akin ta ce "Ke mahaukaciya, tashi ki fita ki bashi wuri, ya gama cin abinci dan Allah, kin saka shi a gaba da sakarci"

Hafsa ta ce "Ni ba mahaukaciya ba ce ba, cutar damuwa nayi ba hauka ba"

Baba ya ce "Na sha garga?inki a kan kiranta da mahaukaciyar nan, wannan salon ki sake tunzurata ne ai"

"A'a dama ai a tunzuren take" Hafsa ta tashi rai a ?ace, ta fita tsakar gida tana kiran Anty.

"Hafsa wane irin kira ne wannan? Menene?"

"Kin ga maman su surayya tana ce mini mahaukaciya ko? Ni fa ba mahaukaciya ba ce ba"

A fusace Anty ta nufi ?akin Baba ta ce "Wallahi kar ki sake kiran ya ta da mahaukaciya, idan ba haka ba duk abun da nayi miki ke ki ka saya"

"Mecece idan ba mahaukaciya ba, ba dai auren cin amana ba, da son abun duniya ba, ta ha?u da babarta a makirci a matsayin kishiya ai, ga hauka ga ba auren, sai an yi magana ace depression ne, yarinya ta zama yar ?waya ta haukace"

"Eh bakomai, tun da har ta yi auren ai, ta shiga ta fito, da babbar budurwa ai gara ?aramar bazawara, da kike maganar zama yar ?waya, naki ?an uban menene ba ya sha? Ko kina tunanin bamu san komai ba"

Hafsa ta koma gefe tana kuka, saboda ta tsani taji an kirata da mahaukaciya, kuma haryanzu idan ta tuna jauhar, da cin amanar da aka yi mata sai ta ?ara shiga damuwa, tayi ta kuka, ta san hakkin jauhar ne ya sanya ta tsinci kanta a wannan mawuyacin halin da take ciki.

Baba yana jin su, ya fito a zuciyarsa yana Addu'ar, Allah ya sa jauhar da mahaifiyarta suna tare a aljanna. Ya fice ya bar musu gidan.

Walid yana ta lalla?a Viper, ya ci abinci ya sha magani, gaba ?aya jin sa yake yi wani iri babu da?i, ya kar?i kofin shayi yana sha a hankali.

?an mama ya kunna radion wayarsa, liti ya hau mitar ya cika musu kunne, ya ce "Dan Allah oga liti kayi ha?uri, labarin wasanni zan ji"

"Ai sai ka yi"

Tashar su Sumayya ya kai, a dai-dai lokacin da murtala yake sanar da hatsarin da Nabila ta samu a jiya, bayan kammala program da suka yi ta tafi, suna barar a sakata a cikin addu'a.

Buredin da viper ya ha?iya ne, ya tsaya masa a ma?ogwaro, tamkar ya ha?iyi dutse.

Liti ya fizge wayar hannun ?an mama ya ce "Ban gane hatsari ba, ji ya ma fa taje Asibiti duba Viper, har yaushe ta yi hatsari kuma?"

Walid ya ce "Babu kusa babu nesa ga Allah, amma dai dole mu san halin da take ciki"

Liti ya ce "Ta? yarinyar nan tana shan azaba, dudu yaushe ta kusa mutuwa a gobara, yanzu kuma hatsari?"

Viper ya din ga murza kofin hannunsa, gumi yana tsatstsafo masa, amma bai tofa uffan ba.

?an mama ya tashi ya ce "Bari nayi maza nayi wanka, na je unguwar su na jiyo, wane asibitin take? Ko kuma na je asibitin da ta kwanta lokacin da tayi gobara, yadda ake ciki dai zan kira ku"

"Saura kuma ka kira mu ka yi mana wannan ga?ancin naka, kayi mana wauta, ka tsaya ka nutsu, kuma saura ka ce baka da caji a waya"

?an mama yayi murmushi ya ce "Ni na isa, in sha Allah ba za ayi haka ba"

Walid ya ce "Viper ka ?arasa ci, in sha Allah babu wani abu, tun da ba su ce ta mutu ba, an ce dai ta ji raunuka ne kawai" shi dai bai ce komai ba, ya ajiye kofin shayin.

***
Yanayin yadda Abdul ya shigo, sai da ramma ta ?an tsorata, maye yake yi sosai.

Ta tashi ta nufi in da yake, ta ce "Abdul giya ko? Baka ce mini ka daina shan giya ba?"

Yayi shiru yana ta numfarfashi.

"Kai dai ba zaka ta?a gyara rayuwarka ba, idan ka yi kamar zaka nutsu, sai ka ?ara fan?arewa, kayi ta yi mini al?awari baka cikawa".

Ya kama hannunta ya rirri?e, ya ?aga jajayen idanunsa da ?yar ya kalleta ya ce "Rahama"

"Meye?"

"Dan Allah karki rabu da ni, ban san me zai iya faruwa a gaba ba, ina sonki, ina sonki....Ai zaki yafe mini ko rahama" yayi maganar cikin maye yana kallonta.

Ta kwantar da kansa a kan cinyarta, tana shafa sumarsa a hankali ta ce "Kana so na amma ka je ka sha giya, kafi bawa soyayya muhimmanci a kan tsoron Allah ko?"

Ya girgiza kai alamar a'a.

"Ga lokacin Sallah yayi, amma babu damar ka yi saboda kana maye, idan ka mutu a haka fa, zan yafe maka ne kawai, ranar da ka mayar da ni gaban mahaifiyata ka nemi afuwarta"

"Idan nayi hakan, zaki yafe mini, mu cigaba da zama tare?" Tayi shiru ba ta ce komai ba.

"Wallahi rahama, komai zai faru sai dai ya faru, idan aka yi ?o?arin raba ni da ke, zan ?auke ki ne na yi gaba da ke, muje mu cigaba da rayuwarmu tare"

Ta ce "Mhmm Abdul yasar rigima, kayi shiru ka daina wannan surutun ka samu ta sake ka, kayi salla ba na son ka mutu kana rashin ji, wasu lokutan dai kayi ta abu kamar mutumin kirki, amma zunubanka da kake tafakawa ne, sun wuce misali"

"Rahama"

"Abdul yasar"

"Wallahi ba zan yadda a rabani da ke ba, ina sonki sosai"

"To likita, amma na ce kayi shiru ai"

Ya ce "To na yi" da haka ya din ga sauke numfashi, yana bacci.

****
?arfe biyu da rabi na dare, Viper yana cikin asibitin da Nabila take, sawu duk ya ?auke, yan dubiya babu kowa, daga majinyata, sai marasa lafiya da ma'aikatan da za su kwana.

Ya jinjina ?ofar ?akin da Nabila take, ya tura a hankali, bai ji an yi magana ba, ya sake turawa ya ga duhu, an kashe fitilar ?akin, ya shiga ya rufe ?ofar, ya kunna fitilar wayarsa ya haska, baba magajiya na ?asa kan carfet tana bacci.
Ya haske Nabila tana kan gado, ita ma baccin take yi, ana ?ara mata jini.

Ya taka a hankali, ya je gaban gadonta ya dur?usa, an na?e mata hannu ?aya da bandeji wanda ta samu gocewar ?ashin.

Hular kanta ta zame, tun daga farkon goshinta, a cike yake da gashi mai santsi, kasancewar ba gwanar yin kitso bace, gashin nata a tsefe yake.

Ya kai hannunsa goshinta, in da aka rufe da plasta, da alama rauni ne a wurin, ya dawo ya ri?e hannunta ya ce "Get well soon, Allah ya baki lafiya"

"Viper" ta furta a hankali kamar mai ra?a.

"Angry bird"

"Ya jikinka?"

Ya ce "Na ji sau?i"

"Yanzu ma na san ba zaka kira ni a waya, ka yi mini sannu ba, ka tsane ni"

Ya girgiza kai ya ce "Ban tsane ki ba Abla, ina so ki rayu ne, in cigaba da ganin fuskar jauhar a cikin taki"

"Viper"

"Mmm"

"Zan cika maka al?awarin ka in sha Allah, duk wuya duk rintsi, zan tsaya maka sai ka yi 'yanci, duk girman barazanar da zasu yi mini, zan tabattar da an yi maka adalci da kai da matarka"

"Allah ya baki iko"

Ta sake cewa "Viper"

"Mmm Abla"

"Dan Allah kar ka tafi daga mafarkina yanzu, na san idan na tashi, ba zan iya zuwa asibiti na dubaka ba"

Yayi shiru bai kuma ce mata komai ba, ta ?ara ri?e hannunsa, da yafi nata girma sosai.
Jikinta ne ya ?ara saki, ta cigaba da bacci, tana yi tana surutai, a hankali har ta yi shiru. Ya sake haskata da fitilar sa, irin innocent face ?in jauhar ta bayyana a fuskar Nabila. A hankali ya zare hannunsa daga nata, ya yin?ura ya tashi ya fita daga ?akin.

Washegari da safe, sai tunanin mafarkin da tayi jiya take yi, tana tunanin gaske ne, ko kuma kawai mafarki ne?.

Da safe ana ta zuwa dubata, wajen ?arfe sha ?aya Nasir ya zo, lokacin babu kowa kasancewar ranar aiki ce, sai baba magajiya. Suka gaisa, ya aiki baba magajiya ya rage saura daga shi sai Nabila a ?akin.

Ya zauna daf da ita a kan gadon, yana kallonta ya ce "Sannu ya jikin?"

Ta amsa da "Jiki Alhamdilillah, da sau?i, zuwa gobe in Allah ya kaimu nake so na tafi ma, i have a lot to do"

Ya ce "Well, tambayarki zan yi, kuma bana bu?atar ki yi mini ?arya, saboda zargina ya tabatta gaskiya ne a kanki"

"Wane zargin?"

"Nabila kin san in da Viper yake, kina ha?uwa da shi!"

Ta kalleshi ta ?ura masa ido amma bata yi magana ba.

"Ina magana kina kallona, na samu rahoton an ganshi a A.I hospital, naje bamu sameshi ba, amma naga signing ?in ki, kin je asibitin me ki ka je yi?"

"Ni ganin likita naje, ka daina zargina tun da baka da wata hujja, mai asibitin aka tura ni wurinsa follow up, saboda lokacin da aka sallame ni, bai zo ba"

"?arya ki ke yi Nabila"

"Ni ba ?arya nake yi ba, ka fara samo tabattaciyar hujja, kafin ka ?aryata ni"

Ya jinjina kai ya ce "Zamu gani ai, bayan duk wannan abubuwan hujja ki ke so na kawo miki? Shikenan zamu gani, amma ki sani aikinki ba zai baki kariya ba, muddin aka kama ki da laifi, sunanki yar ta'adda kema, mai ?oye mai laifi"

"Abun kunya ne ga hukumar yan sanda ace sun gagara kama mutum ?aya, da yake iya yawonsa a cikin gari, sai ma a din ga bibiyar wanda bai ji ba, bai gani ba, ana yi masa baranaza" tsananin fusatar da yayi, ya sanya kawai ya tashi ya bar ta a ?akin.

Ta dafe ?irjinta, saboda yadda yake tsananin bugawa, ta yanke a ranta dole tayi gaggawar fara shari'ar Viper, kafin ta kammala ta ramma.

Ya fita babu jimawa, baba magajiya ta dawo, ta kar?i aron wayarta, ta shiga ban?aki, ta kira wayar Walid, Allah ya taimaketa ya ?aga.

Ya ce "Barrister ashe tsausayi ne ya faru haka, ya jiki?"

"Jiki da sau?i, meyake faruwa ne? Yayana ya ce mini ya samu labarin Viper ya je asibiti, ina yake ina fatan babu wata matsala?"

"Eh, Yana nan cikin ?oshin lafiya mun koma gida ma, ha?uwa yayi da ?an Indabo a matsayin likitan da ya duba shi, shi ne ya sanarwa security"

Ta ce "Haba dai? Likitan da ya duba shi kuma? Garin yaya dole mu ?ara taka tsantsan amma ba abun da ya faru?"

Walid ya ce "Babu abun da ya faru, mun bar Asibitin ma, muna gida"

"Dole na ha?u da shi, nan kusa Allah ya ?ara afuwa" ta katse wayar ?irjinta na cigaba da bugawa.

***
Indabo yana ta sanya ran ya ga ta ina Abdul zai ?ullo, ya kasa zaune ya kasa tsaye, saboda matsalolin da suke kunno kai, ya rasa wanne yakamata ma ya fara ?o?arin kawarwa.

Kwanaki biyu kenan, ko ya nemi Abdul a waya, baya samunsa. Kuma bai sake zuwa gida ba, hakan ya ?ona wa Indabo rai fiye da kima.

Viper bai sake neman Nabila ba, ko a waya, dama bata saka rai ba, dan ta san bata gabansa, idan ta tashi, Walid take kira ta tambaye shi ya jikin Viper, tana ta neman hanyar da zata bi, ta samu ta ganshi, dan sosai Nasir yake sanya mata ido yanzu, ya hanata sakat duk motsinta a kan idonsa, kasancewar motarta tayi damage, an kaita garrage wurin gyara, hatta wurin aiki shi yake kaita, da farko ya so ya Abba ya hanata fitar ma, amma ta din ga kuka, taba nuna wa Abba cewa akwai shari'oin da suke bu?atar ta yi attending.

Bayan ya ajiyeta a wurin aiki a?alla yayi mintuna talatin a tsaye, ko da zata fito, sai da ya samu ?aya daga cikin security na wurin, ya lambar wayarsa, ya ce masa idan ya ga fitar Nabila ya kira shi ya gaya masa, ya kawo alheri yayi masa sannan ya tafi.

Nabila kuwa a office ta iske barrister Habib, ya shirya tsaf zai fita, ta shiga da sallama.

Ya amsa mata ya ce "Sannu Nabila, ya hannun?"

"Hannu Alhamdilillah, fita zaka yi ne?"

Ya ce "Eh, zan je shari'a ne"

Ta ce "Mu fita tare, magana nake son mu yi da kai" ya ce "To shikenan babu laifi" suka fita suka shiga motarsa suka fice.

Kamar mai aljanu, suna tafe a hanya, ta ce "Ya ajiyeta, tayi mantuwa, office zata koma, ya ce zai kaita ta ce masa a'a, ta fice ta hau napep.

Viper ya bu?e ?ofar gidan zai fita, ya ganta a tsaye tana shirin shiga, ta saka hannu ta ?age ni?abinta, suka yi ido hu?u ya ?an tsura mata ido, ta fa?a sosai.

Ta ce "Ya jiki, ka warware?"

"Mmm"

"Zuwa nayi mu ?arasa tattaunawa, ka fara yi mini bayanin shaidun da kake da su a hannu, zan fara gudanar da shari'ar ka, zan cigaba da yi tare da ta ramma, kafin su halaka ni, accident ?in nan, da nayi, takani aka so yi da mota, garin na kauce musu, nayi accident" ya tsura mata ido, tare da ha?iye wani abu a wuyansa.



(Alhamdilillah ala kulli halin, ina godiya sosai da sosai addu'oin da ku ka yi mini, bisa ga rashin lafiya da nayi, Ubangiji Allah ya bar zumunci na gode ?warai)

Ayshercool
08081012143
???500 ne via 0009450228
Aisha Adam jaiz bank sai shaidar biya ta 08081012143
Wanda za su jira document 1K ne.

90009343
'Yan Nijar ku turo katin airtel na 300fcfa

Arewabooks ayshercool7724


Viper ya tsaya ?yam yana kallon Alhaji mu'azzam da ya mi?o masa hannu.

A rikice Nabila ta ce "Amm eh, ai na ma warware na ji sau?i, ka shiga, ka jira ni a office ?ina, yanzu zan dawo"

Viper ya kalli Nabila ya ce "Koma ciki" sai ta tsaya tana rarraba ido, tana kallonsa tana kallon Alhaji mu'azzam wada.

Wani irin kallo Viper ya yi mata, da ya tilasta mata barin wurin, tana waiwayawa.

Viper ya saka hannunsa a hannun Alhaji mu'azzam, ya sauke facemask ?in sa yana kallon cikin idonsa.

"Dama ana ganinka, ka yi wa hukuma wuyar kamawa? Ya aka yi na ganka tare da yarinyar da nake so, kuma nake fatan na aura?"

Viper ya tsananta ri?on da ya yi wa hannun Alhaji mu'azzam ya ce "Ka gaya mata wani abu ne?"

"Kamar me fa?"

"Ka san abun da nake nufi" yayi maganar yana ?ara tsare shi da ido.

Alhaji mu'azzam ya ce "Kana tsoron wani abu ne?"

"Ba maganar tsoro bane ne ko akasin haka, garga?i ne nake yi maka, idan baka furta ba kar ka fara, nike da alhakin kai ?arshen wannan lamarin, idan ka yi wani yin?uri da zai kawo tangar?a ga abun da nake tsarawa, ka san abun da zan iya aikatawa".

Alhaji mu'azzam ya yi murmushi ya ce "Da fari jauhar, na bar maka ita, a wannan karon kuma Nabila, kar ka zama mai......

"Jauhar ta wa ce, haka zalika Nabila, muddin zan cigaba da ganin fuskar jauhar a cikin ta Nabila ta haramta a gareka, ba kai ba kowane mahaluki ma" ya fizge hannunsa daga na Alhaji mu'azzam ya mayar da facemask ?in sa ya bar wurin.

Nabila kuwa kai komo ga din ga yi a office ?in ta, cike da fargaba da tsoro.

Kankarofi ya turo ?ofar office ?in Nabila ya shigo, ta tsaya tana kallonsa yayi mata murmushi ya ?arasa ya ce "Madam ya na ganki a tsaye ne?"

Murmushin ?arfin hali ta yi ta ce "Bisimillah zauna mana"

Ya zauna ya ce "Ashe tsautsayi ne ya kuma afkuwa haka, ya ?arfin jikin?"

Ta ce "Jiki da sau?i Alhamdilillah"

"Amma dai babu wani mummunan rauni ko?"

Ta ce "Eh, gocewar ?ashi na samu a hannuna, amma Alhamdilillah da sau?i"

"To Alhamdilillah, na ji da?i ?warai, ya shari'a kuma?"

Tayi murmushi ta ce "Mu na ta fama, sai fatan Ubangiji Allah ya iya mana"

"Allah ya yi jagora, kin ga kamata yayi ace har gida na je dubiya, daga nan na mi?a bu?ata ta ga Abba, ayi komai a kan lokaci, kin ga babban mutum ne ni, amma soyayya ta saka sai wahalar da ni ki ke yi, kina sakani sintiri, sai dai na yi ta biyoki office"

Ta ?an shagwa?e fuska ta ce "Wahalar da kai kuma?"

Ya kwantar da murya ya ce "Eh mana, ko ba ayi na ne, ya sanya ake ta bani wahala"

"Matanka fa biyu, ni gaskiya...

"Ba kya son mai mata ko?" Ta jinjina masa kai alamar eh.

"To meyasa?"

"Wahala ake sha, kuma nan da nan ake sakin wadda ta zo daga baya, impact ni fa tashin hankali ne ba na so, gidanmu ma uku ne, ina ganin tashin hankalin da ake yi"

Yayi dariya ya ce "Barrister, dabarar mutum ba ta sanyawa ya kaucewa ?addararsa. Da dabara da wayon mutum na sanyawa ya kaucewa ?addara, da wata?ila haryanzu fatima tana raye da ni ta aura"

"Wacece hakan?"

"No kar ki damu, kawai dai misali nake yi miki, wata yarinya ce da na ta?a ?allafa raina a kan aurenta, Allah bai yi ba"

"Baka aureta ba, sai ka auri mata biyu, yanzu da sai ka yi ta uku da ita ni ta hu?u?"

Sosai ta bashi dariya, saboda yarinyata da kishinta da suka gaza ?uya.

"Karki damu, labarin ne akwai sar?a?iya, idan ya zo ?arshe zan baki. Amma matana ba matsala bane. Uwargidana tana Abuja, amaryata kuma na kano, ke kuma sai in da ki ke so zaki zauna"
No?e kafa?a tayi, tana ?an tura baki, har ya gama yi mata hirar, bai yi mata magana akan Viper ba, duk da ta so ta tambaye shi ko ya san shi, amma ta ja bakinta tayi shiru, dan da Viper yakamata su tattauna wannan maganar.

****

Naja'atu Bunkure ce zaune a office ?in Abdul yasar, ya hakimce a kan kujera yana saurarenta.

"Abdul, yarinyar nan fa dole ka fito da ita, even for your own safety, idan fa aka wanke mutumin nan, akwai cakwakiya, bamu san ya shari'ar nan zata kasance ba, taurin kan nan da kake yi, babbar barazana ce gareka da mahaifinka Shari'a sa?anin hankali ce"

Abdul ya ce "Ba wata barazana, ai ba yau ki ka saba goge laifi ba komai girmansa, wannan karon ma ki yi wani abu"

"Nayi iya yi na, da kai da mahaifinka ne kuka ?ata komai, Abdul idan lamarin nan ya kwa?e fa, zaku shiga matsala mussaman ma kai. Kuma an gaya maka shaida kawai zata bayar a kotu shikenan ba wani abu ba"

Abdul ya yi murmushi ya ce "Naja'atu Bunkure, na sanki fa, na kuma san waye mahaifina, na san abun da zaku iya na san wanda ba zaku iya ba. Idan aka kuma cutar da yarinyar nan a karo na biyu, ba zan yafewa kaina ba, ke da kanki kin san kura tayi lafiya, duk da a duk lokacin da zan shiga Asibiti ina ajiye duk wani iskanci a gefe, in shiga a nutse, amma ke kin san yanzu na nutsu sosai da sosai, albarkacin rayuwa tare da rahama"

Naja ta tafa hannu ta ce "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, Abdul kidnapping fa kenan, bayan fya?e ka saceta kana rayuwa da ita, wani laifin fa kake aikatawa a kan wani"

"Babu wani laifi da nake aikatawa, da na barta to da tabbas kun yi mata wata illar, barinta a wurina shi ne zata zauna safe"

"Shikenan, zamu ?auki duk wani mataki da hukuncin da muke ganin ya dace"

Ya ?age kafa?a alamar ko a jikinsa.

***
Indabo kuwa gaba ?aya ya kasa zaune ya kasa tsaye, ya rasa abun da yake yi masa da?i, tun yana ?irga adadin shigarsa ban?aki, har ya sare lissafi ya ?wace masa.
Gudawar tsoro da fargaba kawai yake yi, tun bayan da Viper

Please Login or Register in order to submit comment