Reading KARFE A WUTA Chapter 40 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

poly.

Dodo harkar sha da fataucin miyagun ?wayoyi yake yi, babban distributor ne, har garuruwa yake rarrabawa kaya.
Bai damu da harkar daba ba, sai wannan sana'ar, Abbu bai ta?a tuhumar ya aka yi Al'amin ya koma makaranta ba, wace sana'ar ya fara duk bai tuhume shi ba.

Dodo yana da manyan yara da matasa, ciki har da sa'an Al'amin mai suna Walid. Sai dai Walid ya tsani Al'amin ganin yana neman ?wace masa fada a wurin dodo babban sarki.

Ko aike babu wanda ya isa ya aiki Al'amin, dodo ne kawai yake sa shi ko ya hana shi, haka zai zauna a cikin su, su yi ta shaye-shaye suna ?u??ula kayan maye, amma ba ruwansa da su, ko sigari bai ta?a gwada sha ba.

Idan yayi dare a yawonsa, sai ya tafi gidan dodo, yayi kwanansa, dodo har safarar makamai yake yi, babban criminal sosai da sosai.

Komai Aminullahi, komai Aminullahi, lokaci lokaci, ya kan tuntu?i Al'amin, ko zai iya yafe wa madaki, amma ya ce har abada, har sai ya rama abun da yayi masa ya kan yi murmushi ya ce "Aminullahi kenan, in dai zaka zauna a haka, ba ka shirya ?aukar fansa ba, ?arfe dole sai da ?an uwansa ?arfe, roba ba ta tasiri a kan ?arfe" baya gane mai dodo yake nufi, dan haka sai dai ya bi shi da to
Al'amin ya ce masa dan Allah ya samo masa sana'a, ko wace iri ce zai din ga yi. Dodo ya ce masa zai duba.

Duk abun da Al'amin zai yi, dodo bai yadda yaransa su yi masa wani abu na horo ko cutarwa ba, hatta kaya idan Al'amin ya cire, sai ya ce Walid ya wanke masa, wanda kan zuwan Al'amin shi ne na gaban goshi.

Sannu a hankali, ya fara aiken Al'amin kai kayan shaye-shaye wasu wuraren, cikin dare idan motar kaya ta isao, haka zai ?auke shi, su tafi su kar?o kaya.

Wataran ya aike shi, hukumar hana sha da fataucin, suka kama shi, aka din ga tuhumar Al'amin, ya ?i fa?an wanda ya aike shi da kayan, sai da aka kwana biyu ana nemansa, hankalin dodo ya tashi, aka bincika aka gano masa shi a hannun hukuma.

Ya je ya kar?o Al'amin, sannan ya ce "A bashi kayan da aka ?wace ayi musu ku?i zai saya, idan suna da wasu ma a ha?a masa ya saya. Kuma hakan aka yi.

Ya yi ta yi wa Al'amin fa?a, a kan dan me, ya zauna a hannunsu, bai saka an neme shi, ya fito da shi ba?.

Ta kai ta kawo, Dodo yana tafiya da Al'amin wurin 'yan siyasa, dan a nan ne suka ha?u da Indabo, a lokacin baya shan komai.

Duk da wannan abubuwan da suke wakana, Al'amin yana zuwa gida, ya ga Abbu, ko da kuwa zai yi masa fa?a ya kore shi, yana zuwa ya ganshi.

Yaran dodo sun sha attempting koya masa shaye-shaye, amma ya ?i, tun Walid yana jin haushin Al'amin, har ya ha?ura, manyan yaran dodo suka saka masa mai zamani, ya kori gwamantin Walid dan haka idan yana son zaman lafiya ya kiyayi mai zamani"

Dodo ya din ga dariya, ya ce "Kuma zamanin Aminullahi dogo ne a wurin dodo ba, bana tunanin akwai wanda zai ture gwamantin sa a wurina, dan mai dogon zamani dan haka mai laya" yayi maganar yana kallon Walid.

Aka ha?a baki aka ce "Ka kiyayi mai zamani" suka yi abun da sigar raha.

Al'amin ya je gida, domin ganin Abbu, amma ya tarar baya nan, Rahila kuma tayi ba?i, ya shiga kitchen ya ga an yi uban abinci, ya kwaso fulasan yayi gareji da su, ya zauna ya hau ci, duk da ya san na ba?in ne.

Yana cikin ci, sai ga wata 'yar yarinya ba ta fi shekaru biyu ba, ta zo in da yake tana kallonsa, ta tsuguna ta saka hannu a kwanon, tana tsintar abincin tana ci.

Ya kalleta, sai ya tuna jaririyar ummi da ta rasu, yanzu ga shi duk su ukun babu su.

Sai ya din ga bata abincin a baki, amma hakan bai hanata saka hannu a kwanon miya ba, haushi ya kama shi, kamar ya kwa?e ta, ya kama rigarta yana goge mata hannun, kawai ya ji salatin Rahila.

Ya ?aga kai ya kalleta ta ce "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, na shiga uku jama'a ku taimake ni, zai lalata 'yar mutane, Allah ya sa ba yi mata komai ba"

Sai yayi saroro yana kallonta, ya rasa gane mai take nufi, wanda ta yi hakan ne, dan huce takaicin tozarcin da yayi mata, na cinye abincin ba?i.

Shahida ta ce "Mama wanke wanke nake yi, ina hango su ba abun da yayi mata, abinci kawai yake bata"

"?arya ne rufe mini baki dan ubanki, ke kin ta?a ganinsa yana ?aukar yara ne, balle ba da abinci a baki, ni na ga abun da na gani" dama 'yar ta ma?wabta ce, uwatta ta kawota ta fita.

Ta tara wa Al'amin jama'a, wai ya saka wa yarinyar hannu a wando, da idonta abun da ta gani kenan.

Duk dakiya da dauriyar Al'amin, jikinsa ya hau rawa, ya kasa ko motsi daga wurin, mutane suka taru a garejin gidan, Abbu dama sallar la'asar ya fita, a masallacin yana lazumi aka je aka kirawo shi.

Cikin tashin hankali ya dan?o Al'amin, ya kwa?a masa mari ya ce "Me ka yi wa 'yar mutane? Al'amin lalacewar taka har ta kai ga haka? Ni zaka zubarwa mutunci a idon duniya"

Shahida tana kuka za ta yi magana, Rahila ta hanata, wata mata ta cire pampers ?in yarinyar ta duba ta, ta ce "Wannan yarinyar fa babu abun da aka yi mata, lafiyarta ?alau da ya ta?ata ma, ba za a ganta a haka ba"

Al'amin ya ?wace rigarsa daga hannun Abbu, ya fice, yana jin zuciyarsa zata tarwatse, bai zarce ko ina ba, sai gidan dodo, suna ganin sa suka din ga tambayar sa, menene saboda yadda idonsa ya yi jawur, amma ya yi shiru ya ?i kula kowa.

Walid ya kira dodo a waya, ya sanar masa ga mai zamani ya zo, cikin ?acin rai da tashin hankali.

Ba a ?auki lokaci ba, sai gashi, ya ce "Waye ya ta?a zuciyar magajin dodo, wa ya ta?a mini Aminullahi?"

"Al'amin ya ?i magana sai huci da ajiyar zuciya, ga wani gumi da yake yi"

Dodo ya ce "Walid"

"Allah ya taimaki babban sarki"

"Narka jan tablet, ka bani" Walid ya narka ya bashi, ya mi?a wa Al'amin.

Ba tunanin komai, ya kar?a ya shanye ya ajiye kofin, wani zuuuuu ya fara ji a kansa, ya fara ganin hazo-hazo, a hankali ya fara ganinsu bibbiyu, daga haka bai sake sanin abun da ya faru ba, sai sha biyun dare ya farka.

Yayi sallolinsa, ya ci abinci, dodo ya ce "Magajin dodo, ba zan takuraka na ji menene ba, amma ya ka ke ji yanzu damuwar ta tafi gaba ?aya?"

Al'amin ya girgiza kai alamar a'a.

"Duk wannan dogon zangon da ka yi? Bari na baka wani ha?in"

Ya na?a masa wiwi, ya kunna ya bashi, sai dai zu?a ?aya Al'amin ya hau tari, kamar zai shi?e ya ce "?ara gwadawa, ba zaka yi ba" ya din ga zu?a a hankali, tun yana tarin har ya daina.

Ayshercool
08081012143


A din ga yi, ana sauke hakki ?500
0009450228
Aisha Adam jaiz bank
???500 ne via 0009450228
Aisha Adam jaiz bank sai shaidar biya ta 08081012143

90009343
'Yan Nijar ku turo katin airtel na 300fcfa

Arewabooks ayshercool7724

https://chat.whatsapp.com/E3bH5OKBh9jH2aYygj0ArA


Kina bukatar kaya masu kyau da inganci??

Kina bukatar kayan kitchen wnd suke available ba order ba??

Kina bukatar adashin gata wnd zaki dauki kaya kamar kyauta??

Kiyi joining wnn group din namu insha Allah xakiji dadin kasancewa a ciki.

Muna da kaya available masu kyau da rahusa????????
Ko kimin mgn ta????????
08093932955


Tun daga lokacin, Al'amin ya fara shaye-shaye. Shiga layinsu ya gagare shi, saboda tsananin kunyar abun da Rahila ta yi masa na sharri.
Sai da ya shafe wata guda bai sake takawa gidan su ba, sai dai kewar Abbu ta din ga damunsa, da asuba ya tafi masallacin da Abbu yake salla, ya yi sallar asuba a waje, ya jira ya fito, Abbu yana tafe ya ji kamar ana bin sa a baya, ya tsaya ya waiwaya, duk da gari bai gama yin haske ba, da sauran duhu, amma hakan bai hana abbu gane Al'amin ba.

Ya tsaya, jiki a sanyaye ya ?araso, Al'amin ya risuna ya ce "Ina kwana"

"Kai daga ina? Ina ka tafi tsawon kwanakin nan? Duk yawonka ba ka wuce kwanaki ka?an, amma ban sake saka ka a idona ba" kallon Abbu yayi, yana tunanin da ma yana jin wani abu idan bai saka shi a idonsa ba?.

"Ina nan"

Abbu ya ce "Kana can kana shashanci, gaishe ni ma ba zaka iya zuwa ka yi ba ko?"

Ya ce "Korata ka ke idan na zo"

"Ba dole in kore ka ba? Tun da kai a rayuwarka ba ka gaya wa kanka gaskiya, kuma duk in da ka zauna sai an yi fa?a da kai. Ka yi salla ne?" Al'amin ya jinjina kai.

"To wuce mu tafi" yayi maganar yana nuna masa hanya, sai Al'amin yayi ajiyar zuciya, tare da tuna masa baya, da yake ?ora shi a wuyansa idan suka dawo daga masallaci, har tsere suke yi da Abbu, duk yadda Abbu yake ji da shi, yanzu ya zama tarihi.
Yana tuna abun da ya faru ?arshe, sharrin da Rahila ta yi masa, sai ransa ya ?aci, ya ?i shiga layin ya tsaya.

Abbu ya waiwayo ya ce "Ya ka tsaya kuma?"

"Tafiya zan yi"

"Zuwa gidan uban wa?"

Al'amin ya ce "Da wani idon zan kalli sauran mutanen layin, bayan ga sharrin da aka yi mini, idan na ga matar nan, zan iya kasheta, sai anjima kawai na tafi, dama ganinka nake son na yi, tun da kana lafiya Allah ya ?ara lafiya" ya juya ya tafi, Abbu ya tsaya yana kallon Al'amin har ya ?ace wa ganinsa.

Ko da ya koma gidan da suke, walid ya fuskanci Al'amin yana cikin damuwa, yayi masa tayin sigari, ya girgiza masa kai, can ya ce "Walid"

Ya amsa da "Na'am"

"Dan Allah ya aka yi ka fara Shaye-shaye?"

Walid ya ?an yi shiru sannan ya ce "Wan babana ne ya cinye mini gado, nake ta wahala ina fama da rayuwa, matsin rayuwa ya isheni, kuma shi ba tallafa mini yake yi ba, kawai na fara dafar kan kayan mutane, kuma da nasa na fara, aka kama ni aka kulle, rodi ma na sata lokacin, aka ?aure ni watanni shida, da aka kai ni prison ban saba ba, nake ta kuka saboda wahala, a can na ha?u da mai gida, sarki dodo, ya din ga kula da ni, bayan ya fita ya dawo ya biya mini tarar aka yanke mini, sake ni, kawai ya cigaba da kula da ni"

"Ina mamanka?"

Walid ya ce "Ta? tana can tana fama da rayuwarta, kinko ya kananna?e rayuwarta, wannan tsohon auran wan baban namu, ya tattare gadonmu ya cinye, Sakandire kawai nayi, ita ma ba ganewa nake yi ba da kyar na kai. Tana fama da kula da ?annena, ga bata da cikakkiyar lafiya, ni kuma bana iya tallafa mata, har gara yanzu mai gida ya kan bani ku?i ya ce na je na gaishe ta"

Al'amin ya jinjina kai ya ce "Ka cigaba da kula da ita, dan duk ranar da ka rasata, za ka yi kuka, kuma kar ka bari ta san irin rayuwar da ka ke yi"

"Na nawa kuma, ai wancan tsohon munafukin tuni ya gaya mata, tana yi mini nasiha sosai da addu'a, ba ta ta?a fushi da ni ba"

Daga haka Al'amin yayi shiru, yana cigaba da tunani.

Da sannu Al'amin ya zama gawurtaccen mashayi, duk in da dodo za shi, da Al'amin. Ta kai ta kawo har kudancin Najeriya yake tafiya da Al'amin, ba fatauci ba, har wuraren sarrafa miyagun ?wayoyi Al'amin ya sani, har manyan mutane a ?asar nan da suke ta'amalli da su da kasuwancin su ya sani.

Ya ha?a Al'amin da wani inyamuri, ya ?ara gogar da shi a kan harkar na'ura mai ?wa?walwa, yadda ake amfani da ita a aikata laifuka daban-daban, suka sake danganawa da wani bature, ya ?ara koyar da Al'amin sarrafa computer wurin yin laifuka.

Ya zamana kasuwancin miyagun ?wayoyi, na ?asashen da suke ma?wabtaka da Nigeria, Al'amin ke tafiyar da kasuwancin su ta online.

Bai tsaya a nan ba, har cikin manyan 'yan fashi, dodo yake shiga da Al'amin.

Dodo ba ya fashi da makami, amma zama a gidajen gyaran hali daban-daban ya sanya ya san masu laifuka kala-kala da yadda ake aikata su, bai fiye harkar daba ba, yafi gane wa safarar ?wayoyi da makamai.

Idan aka cewa Al'amin magajin dodo, sai dodo ya ce "Wannan dodon, da sauran imani a ransa, ?an ?aramin dodo ne, ba zai iya zama kamar ni ba, sonake ya horu, yadda zai iya tunkarar kowane ?alubale, ciki har da babban burinsa na son ganin bayan madaki, dan kuwa madakin ma ya ?wafe shi a rai, na cewar sai ya ga bayansa, tun da na saka ya sanya gwiwar sa a ?asa wurin bashi ha?uri".

Duk wani sirri na dodo, babu wanda Al'amin bai sani ba, kallon abu dodo yayi Al'amin ya san me yake nufi.

Kai tsaye ya kan tura Al'amin wurin indabo, a lokacin yana fafutukar neman kujerar ?an majalisa, sai dai wasu lokutan baya son dodo ya aika masa Al'amin, dan idan yayi masa abun da bai yi masa ba, tafiyar sa yake ya ?yale shi, ba ya jure cin zarafi ko wula?anci, komai ?an?antarsa, ya ya?awa indabo ba?ar magana ya ?ara gaba, duk ba abu ne mai wahala a wurin Al'amin ba, Indabo ya kai wa dodo ?arar Al'amin.

Amma ya ce "Ina nema masa afuwa, ka ri?e Al'amin yaro ne mai amana, kuma duk cikin yarana babu wanda zai iya yi maka aikin da ka ke so bayan shi, yaro ne mai amana sosai da sosai, kuma ba shi da surutu, hakazalika yayi hannun riga da tsoro.

Dodo ne ya nuna masa makamai kala-kala samfurin wu?a?e, da in da in ka sakawa mutum zaka kashe shi, da wanda za ka yi masa illa.

Dodo yana yawan fa?ar, Son da yake yi wa Al'amin daga Allah ne, bai ta?a son abu sosai da yake jin sa a ransa kamar shi ba. Ya san son da yake yi masa, ba zai kai na ?a da uba ba, dan haka ya din ga mamakin yadda aka yi, mahaifin Al'amin ya wofantar da shi, duk da soyayya irin ta ?a da uba.
Ba yadda bai yi da Al'amin ya ?ora karatu ba ya ?i.

Ya ce "Aminullahi, harakar daba da shaye-shaye ba abune da nake yi maka fatan ka ?ore a kai ba, yakamata ka koma makaranta.

Al'amin ya ce "Ni ma ba na fatan na ?ore, ina ?aukar fansar abun da madaki yayi mini zan bar daba".

Ya dafa kafa?arsa ya ce "Ina maka fatan hakan, sai dai haryanzu ba ka kai ?arfin da zaka tunkari yaron nan ba, dan kuwa shi har da tsafi yake yi, kai kuma na san komai za a yi maka, ba zaka yi tsafi ba, amma ba a shiga dawa dan ?arya, ko na kare kai, zan nema maka".

Duk da an ?auki lokaci, yaran madaki ba su shiga unguwar su Al'amin ba, sai rana tsaka, suka shigo unguwar neman fa?a, a karon farko Al'amin ya ?auki makami, jikinsa na wata irin tsuma, zuciyarsa na tafasa, wanda hakan ya faru ne a sakamakon abubuwan da yake ta'amalli da su.

Dan shaye-shaye nasa, kala-kala ne, kowanne akwai lokacin amfaninsa. Idan wani aiki yake son yi, ba ya son gajiya da wuri, sai ya banki wiwi sai ya da?e yana abun da yake so, ba tare da ya gaji ba. Idan kuwa rashin mutunci yake son yi, haka zai yi mata ha?e-ha?e na mussaman, haka ma idan so yake ya bugu. Bai fiye ta'amalli da ?waya sosai ba, ya fi ?arfi ga wiwin.

Ya je ya samu yaran, kan mai uwa da wabi, yayi musu ?arna, sannan ya taka har dabar madakin, ya yi masa warning, "Ka garga?ai karnukanka, a kan shigar mini area su nemi fa?a, idan ba haka ba, kan babban karen zan zo, na yi masa takunkumi, yadda haushi ma sai ya gagare shi"

Madaki tun da dodo ya sanya ya bawa Al'amin ha?uri, ba su sake arangama ba, kusan shekara biyu, sai a wannan lokacin, sai da gabansa ya fa?i, saboda yadda kamannin Al'amin suka juye, ?arara alamun shaye-shaye suka bayyana a tare da shi, yadda ya sake zuwar masa kai tsaye ba tsoro ko fargaba, ya sanya shi gane kuskuren da ya yi na barin Al'amin a raye.

Tun da Al'amin yake tare da dodo, bai ta?a rashin ku?i ba, ku?i yake kamawa manya da ?anana, kuma bai ta?a ci wa dodo amana ba.

Har a cikin ma'aikata, ana samun ?ata gari wa?anda suke sayar wa dodo kayan maye, idan sun kama, duk wani salo na yadda ake sayar da kayan, ba tare da an gane ba, Al'amin ya goge, haka idan kana ta'amalli da su, kallo ?aya zai yi maka ya gane.

Yan kwamutin unguwa, suka kai ?arar Al'amin wurin hukuma, a kan yana tayar musu da tarzoma, ba tare da la'akari da yaran da suke rashin jin tun kafin ya fara ba.

Dodo ya je ya samu shugaban 'yan vigilant, ya ce masa "Wallahi duk wanda ya sake ?aukar ?afa, ya kai ?arar Aminullahi sai ya ci ubansa, lokacin da aka kashe ?an uwansa ku nawa ku ka tashi ku ka je wurin jami'an tsaro domin ganin an ?watarwa yaron hakkinsa, saboda ba yaranku aka kashe ba. Lokacin da yake ragaita ba shi da sana'a, mutum nawa ne suka mayar da shi makaranta? Ko suka bashi sana'a, dan mahaifinsa ya wofantar da shi, kuna 'yan unguwa ba ku ga dacewar ku nusar da shi kuskuren sa ba? Ai duk society da suka yi watsi da yaran su irin su Aminullahi muna nan muna jiran su, mu zamu kar?e su, mu mayar da su abun da ya dace. Garga?i nake yi, ni dai an san ba zan kamu ba, to haka Al'amin ma, ko bayan raina, ina da masu fito mini da shi idan ya shiga cakwakiya. Ku shirya Al'amin bai fara yi muku rashin ji ba tukuna"

?an unguwa suka rasa abun yi, yaransu da suke ?anan rashin ji, suka fara bin Al'amin, yana ba su kayan wiwi suna sayarwa, yana ba su ku?i, dama gashi da kyauta kuma ba shi da ba?in ciki.

Duk yaran dodo, suna shakkar Al'amin, ko dan saboda masifar dodo idan aka ta?a shi, dama Al'amin ya fi yin fa?a da Walid, dodo ya kan ce masa Mai laya, ka kiyayi mai zamanin nan, idan ka ?ure shi, ba zan saka baki ba, idan ya tashi yi maka ?arna ba. Su yi fa?a su yi da?i.

Tafiyar gaggawa ta kama dodo, zuwa kudancin Najeriya, sai dai ya ce wa Al'amin ya zauna, ya kula masa da har?allarsa ta kano, ba zai tafi da shi ba.

Abun da Al'amin bai ta?a yi ba, sai a wannan karon ya ce "Meyasa ba zaka tafi da ni ba?"

"Aminullahi, tafiya ce mai hatsari, ka kula mana da har?allarmu, sannan kar ka manta rules ?in, a tafiyarmu babu BODMAS, idan ka ji wuta, ka wargaza komai ka ?ace"

Al'amin ya jinjina kai ya ce "Allah ya taimaki sarki babban dodo"

"Na gode, Allah ya ja zamaninka, zuwa in da ba ka zata ba, a cigaba da ri?e amana Aminullahi" haka nan Al'amin ya ji baya son dodo ya tafi.

Kwana uku da tafiyar Dodo, suna zazzaune, suna shan sigari, aka jefo wata jaka ta katanga.

Walid ya ?aukko jakar, wasu daga cikin yaran wurin, suka fita da gudun tsiya, suna neman wanda ya jefo jakar, ba su ga wanda ya jefo ba.

Al'amin ya ja jakar ya bu?e, kawai yayi tozali da kayan dodo a ciki, face-face da jini, har da takalminsa.

Cikin ?araji Al'amin ya ce "Nooooo" ya tashi jikinsa yana tsuma ya girgiza kai ya ce "Impossible, ba zai yiwu ba, sarki yana raye, raina mana hankali kawai ake yi"

Walid ya ri?e Al'amin ya ce "Al'amin ka nutsu mana, musulmai ne mu, idan ba a kashe sarki ba, babu yadda za ayi a ciro kayans jina-jina a kawo mana".

Al'amin ya fara neman ya fita hayyacinsa, Walid suka danne shi, suka sha?a masa wani abu, jikinsa ya saki ya hau bacci.

Al'amin ya razana, ya shiga tashin hankali, ya ?imauce sosai da sosai, da mutuwar dodo, ba zai manta gudunmuwar da ya bashi ba, duk da ba ta arziki ba ce ba, Al'amin kamar zai zare.

Duk wata hanya da zai bi ya gano wanda ya kashe dodo, ya rasa, damuwa ta ?ara yi masa yawa.

Ya ?aukko makaman da ya saka aka ?era masa, sweazland, Russia da kuma ira?i, ya zuba musu ido, bai ta?a zaton ya sha?u da shi haka ba.

Mussman madaki ya zo ya sami Al'amin, yana ?ya?yata masa dariya, wai garkuwar da fake a bayanta, an samu wani gwanin saitin ya rusata, yanzu zai koma Al'amin ?in sa matsoraci na ainihi.

Sai dai cikin sa'a, Al'amin yana tare da sweazland, dan haka madaki ya fara yi wa rauni da ita ya ce "Dan an fasa garkuwata, ba ya nufin zaka cim mini, *?arfen cikin wuta nake* na fi ?arfin ?auka da hannu, ko da mari?in roba, daga yau ka rubuta ka ajiye, ?aya ya riski ajalinsa ne kawai zai kawo ?arshen gabata da kai".

Madaki ya kalli cinyarsa da ke jini ya ce "Meyasa ba ka kawo ?arshen gabar yanzu ba, ka kashe ni?"

"Saboda na fika sanin waye kai, akwai lokacin da ya dace da hakan".

Yaran dodo, sun so Al'amin ya gaji har?allar dodo, ba ita ba har manyan hada-hadarsa da manyan mutane. Amma Al'amin ya?i, ya ce baya bu?atar duk wani abu da zai din ga tuna masa da dodo, kuma zai yi abun da zai Allah zai gafarta masa, ba ?orar da laifukansa a bayan ?asa ba.

Da yawa sun so su ya basu sirrikan dodo, su cigaba da sana'arsa, amma Al'amin ya ?i, ?arshe ma suka bar wannan gidan gaba ?aya, ya je ya kafa masa sansanin.

Walid suna zuwa da Al'amin duba mahaifiyarsa, da ciwon Cancer ya kama, aka kwantar da ita a asibiti, kullum cikin neman jini ake, duk wani ku?i na Al'amin, sai da ya ?are a wurin kula da mahaifiyar Walid.
Liti dama shi isaknci ne da abokai, suka saka ya lalace, dan har waje babansa ya kai shi yin karatu, bai koyo komai ba sai shashanci ya dawo.

Kasancewar jinin Al'amin da na babar Walid iri ?aya ne, ya bayar da jininsa sosai an saka mata, kullum cikin Kwantar wa da Walid hankali yake, tare da bashi tabbacin zata warke.

Har zariya suke kaita Asibiti gashi, amma cikin ikon Allah ta koma ga Allah, abun nan da Al'amin ya yi wa walid, ya sanya ya sanya duk abun da zai yi masa baya fushi da shi, ko yayi sai ya huce.

Suka koma ?aramar har?allar sayar da wiwi, idan kuma aikin ?arfi ya samu su yi.

Al'amin ya numfasa sannan ya ce "Ban kuma ta?a kashe kowa ba, duk rashin ji na, wanda ki ka ganni da shi, liti ne, yaran madaki suka soka masa wu?a, kar ki sake cewa na yi kisan kai".

Jauhar wani irin kuka take man ban tausayi, rayuwar Al'amin akwai tarin ?alubale, sai ta ga ita tata rayuwar nafila ce.

"Ki yi ha?uri, da yawan furta miki zan sake ki da nake yi, baki cancanci mutum mai tarin laifuka irina ba, wallahi ba zan iya yafewa madaki ba, da shi da wanda suka kashe dodo. Ban yi miki al?awarin daina abun da nake nan kusa ba, binciken da na ?ara yi akan ki, na fuskanci kusan ?alubale ?aya muka fuskanta, dan na san duk wani abun alkhairi wannan shegiyar matar ba zata bari ya ra?e ni ba, dan haka na yi zaton ta shirya mini wata ma?ar?ashiyar ne, dan haka ta aura mini ke, ashe wai wani mai ku?i zaki aura, suka hana ita da wannan banzar matar ta gidanku, ban manta lokacin da take zuwa gidanmu ba ita ma. Haryanzu a shirye nake, mu rabu ki auri mutumin kirki, baki dace da ni da rayuwata ba, rayuwata ta riga ta gur?ace, kullum kina cikin tashin hankali bai kamata ba, duk a sanadina. Dama kin ga ke kalar matan masu ku?i ce, in da zaki huta a kula da ke sosai. Ni kuma na gurgura na ?arasa rayuwata"

Jikinta na rawa, ta toshe masa baki, ta kalleshi, hawaye

Please Login or Register in order to submit comment