Reading KARFE A WUTA Chapter 63 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

babu gudu babu ja da baya kenan, komai rintsi komai wahalarsa?"

Ta jinjina masa kai alamar eh.

"A'a ki sake tunani, mussman ranar da zata fasu kina ?oye shahararren ?an ta'adda kamata"

"Kai ba ?an ta'adda bane ba, ta'addancin da aka yi wa rayuwarka, shari'a ta kasa tsaya maka ya sanya ka zama haka. A labarinka da oga walid ya bani, da tun a lokacin da aka kashe yayanka, hukuma tayi abun da ta dace, da duk ba a zo wannan ga?ar ba.
Muna iya jure rashin makusantanmu ne, saboda ?arfin imani, da tuna wanda ya bamu ne ya kar?i abunsa, amma idan wani ya zama sila, na rasa mutane masu muhimmanci a rayuwarmu, wannan imani na yarda da ?addara ya kan yi rawa a zukatanmu, mu kasa yadda da wanda ya bamu ne ya kar?a. Kai ba ?an ta'adda bane ba mai babban suna, cin hanci a doka da shari'a su ne suka mayar da kai duk abun da ka zama a yau. Ba kowace zuciya ce zata jure tana kallon wanda ya cutar da ita yana rayuwa cikin kwanciyar hankali, alhalin ita an bar mata tabo mara warkewa ta jure ba.
Ban ce zan kai 'yar madara ba, amma na fuskanci gi?in da ka rasa nima akwai makamancin sa a rayuwata, da yake ci mini tuwo a ?warya yake damuna, ina ?uya in yi kuka wasu lokutan na ji na tsani komai, kamar na kashe kaina na huta.
Jin labarinka ya sanya, na fuskanci me ka ke ji a zuciyarka. Har abada duk tsanani ba zan sake kuskuren kallonka a matsayin ?an ta'adda ba, kuma zan tabattar wa da duniya haka, da izinin Allah. Sai an gyara fannin shari'a an mur?ushe rashawa da bambancin hukunci tsakanin ?an talaka da mai ku?i, mai ?arami da babban uban gida, idan ana son rage yawan 'yan ta'adda" tun da ta fara magana, yake kallonta, duk da tana yi tana zubar da hawaye, hakan ya tabattar masa da akwai wani pain a zuciyarta ita ma.

Ya juya ya cigaba da danna computer, ta kifa kanta tana goge hawaye. Ta kwantar da kanta a kan teburin, tana danna wayarta.

Ta ?aga idonta ta kalli, yadda yake ta sarrafa computer, bata san me yake yi ba.

Yanzun ma hotonsa take ?auka tana murmushi, kamar ba yanzu ta gama kuka ba.

"Master" yayi mata shiru.

Ta sake cewa "Maciji" tai maganar tana dariya.

"Viper, maciji mai hatsarin gaske, yau ka fito daga raminka, ka zo wurina, sarana ka zo yi ne?" Still bai kulata ba.

Ta tashi sosai ta ce "Da ni 'yar sugar da yar madara, wacce ta fi kyau ne? Kodayake na san ma ita zaka za?a, kafi sonta, amma dai kyakykyawa ce? Sannan fara ce ko ba?a? Doguwa ce ko gajeriya, ina son in ganta ka nuna mini hotonta, ko ba zaka bani ha?a ni da ita ba?". Sai da ya dafe goshinsa, Nabila bata gajiya da surutu, Jauhar akwai lokutan da ba ta kula shi da hira, idan ba ya cikin mood, shi wannan surutun nata ba zai bari su daidaita ba.

Ya fizge wayar hannunta, yana dubawa yana danna computer.

"Wai hacking ?in wani zaka yi ne? Ni baka yi mini bayanin me ka ke yi ba, sonake ma mu yi magana, amma ka ?i kulani, sai aiki kake yi kai ka?ai".

Ya tashi tsaye ya ce "Zan yi salla"

Ta nuna masa toilet, ya shiga yayi alwala, ya fito yayi sallar azahar, sanann ya kalleta ya ce "Tashi mu tafi"

Ta tashi tsaye ta ce "Ina?"

"In ?arasa miki labarina, amma bisa shara?in da na gindaya miki da farko, babu gudu babu ja da baya, duk tsanani da wahala" ta jinjina masa kai.

Ya ?auki facemask ?in sa ya saka, ya sanya ba?in glass ?in sa ya yi gaba.

Dama yau hijjabi mai ni?ab ta sako, dan haka ta saka ni?abin, ta bishi.

Cikin ikon Allah, chamber babu kowa, duk lawyoyin sun tafi kotuna, sai massenger da mai gadi.

Suka fito, ta ce "To ina zamu je? Ba zai yiwu ka ?arasa mini a nan ba?"

"I have to test you more, before i completely trust you" daga haka ya tarar musu napep, ya gaya masa in da za su je.

Suna tafe tana ta addu'a, Ubangiji Allah ya kare su, ya tsare duk in da za su je, Allah kar ya sanya ya cutar da ita, ko wani ya kama su.

Kasancewar rana ce sosai, layin shiru babu kowa, suka tsaya a ?ofar wani gate, ya ciro mukulli a aljihunsa ya saka ya bu?e, ya ce ta shiga. Ta shiga sannan shi ma ya shiga ya rufe ?ofa.

Ta tsaya tana kallon gidan, ya jingina da gate ?in ya tafi tunani.

"Waye yake mini kokowa da ?ofa zai karya mini gate?"

"?arawo ne ya zo sace matar gidan" tayi dariya ta ce "Da alama ?arawon nan, bai san gidan wa ya zo ba ko? Ka bari mijina ya zo ya same ka" tayi maganar tana fitowa daga falon, fuskarta ?auke da murmushi da tsohon cikinta.

"Wai da ke muka ha?a ku?i muka sai rigar nan ne? Ki din ga ?aukar mini kaya kina sawa"

Ta tura baki ta ce "Kai da kaya mallakar wuya ne, da kayan da mai kayan duk mallakin 'yar madara ne" tai maganar tana sakar masa murmushi.

Nabila ta ce "Ya naga ka tsaya, ina ne nan?".

Yayi firgita ya dawo daga tunanin da ya tafi.

Ya tunkari ?ofar falon, zuciyarsa na bugawa da sauri da sauri, ya saka mukulli ya bu?e.

Falo ne sosai, komai neat sai dai yayi ?ura sosai.

Ta tsaya tana ?arewa falon kallo, taji wani abu ya kama zuciyarta.

"Viper, nan ne gidanka da 'yar madara tana ina? Kuma baka tsoron azo a kama mu?"

Bai ce mata komai ba yama wuce ya shiga bedroom ?in, ya tsaya yana ?arewa ?akin kallo, komai ya din ga dawo masa, tamkar mai mafarki.

Tana tsaye, ya fito da wani riyo a hannunsa ya zo gabanta ya ajiye, yayi kneel down a gaban riyon, ya bu?e ya shiga fesawa kayan turaren florie. Ya din ga ?ago kayan, na jarirai ne, komai na haihuwa yana ciki intact, hatta zannuwa zamzam, bagaruwa, pad pampers komai akwai a ciki.

Duk wanda ya ?ago sai ya fesa masa turaren ya ajiye, muryarsa na rawa ya ce "?aya daga cikin ?amshi mafi soyuwa a wurin jauhar kenan".

Gaba ?aya zuciyar Nabila ta tsinke, gabanta ya tsananta fa?uwa, ta ?auki kayan, ita ma ta kai hancinta.

"Yanzu tana ina? Ina kuma jaririn naga kayansa na jariranta haryanzu?"

Ya ?aga kai, yana kallon in da Nabila take zaune, ya ga jauhar kwance a wurin, cikin jini, tana ?ago masa hannun tana la'ila ha illa la, ya Allah.

Daga nan bai sake sanin in da kansa yake ba, sai ji yayi an watsa masa ruwa mai tsananin zafi, da ratsa fata a jikinsa.

Ya yin?ura zai tashi a gigice, amma yaji shi a ?a??aure, tamkar huhun goro.

Ya bu?e idanunsa da ?yar cikin matsananciyar galabaita, amma ya kasa magana, haka zalika wuyansa ya kasa tsayawa.

"Idan ya watstsake, ku cigaba da tuhumarsa, har sai ya amsa laifin da bakinsa"

"Ok sir"

Suka cigaba da kwara masa ruwa mai zafi, amma sai dai ya zabura ya ?an?ame jikinsa, amma babu baki.

Suka kwance shi daga mugun ?aurin da suka yi masa, sai dai ana gama kwance shi, ya fa?o ?asa jikinsa a sake.

?aya daga cikin su ya ce "Haryanzu bai gama dawowa hayyacinsa ba, ku ?yale shi tukuna"

Indabo sai kaiwa yake yi, yana komowa a falonsa,ya rasa me ma yakamata yayi, gefensa ga P.A ga kuma madaki a zaune.

"Wallahi kayi mini hauka madaki, ni ban san zaka yi mini sakarcin ba. Bambancinka da Aminu kenan, abun da aka saka shi yake yi, idan ka ga ya canza, to ya hango abun da ya fi naka ne, yanzu idan ya farka ya tona mana asiri ya kenan?"

P.A ya ce "Honorable, ka kwantar da hankalinka C.P yana hanyar zuwa nan, zamu ji mai zai ce mana"

Madaki ya ce "Honorable, da ka san hatsarin da yake tattare da yaron nan, da baka ce haka ba, mugun shu'umi ne. Hodar nan da guba na ha?ata, kisa take yi har lahira, nayi mamaki da aka ce bai mutu ba, ba laifina bane ba, nayi iya ?o?arina".

CP ne yayi sallama, ya shigo falon, suka amsa tare da mayar da hankalinsu kansa, ya mi?a wa Indabo hannu suka gaisa. Cikin za?uwa indabo ya ce "Yaya ake ciki C.P?"

"Eh to, maganar gaskiya fa ya farfa?o, kuma yana daf da watstsakewa a ko wane lokaci. Abun da muka yi guda ?aya ne, a report ?inmu, mun shigar da cewa ya sha kayan maye ne, ya bugu ya halakka matarsa".

Indabo yayi shiru sannan ya ce "Kai naji da?i, amma kamar hanyar ba tayi ba sosai, idan ya bu?e bakinsa, zai iya fa?ar gaskiya fa"

C.P ya ce ba zamu bari haka ta faru ba, lokacin da muka je gidan, mun goge duk wani abu da zai nuna hujjar wani ne ya shiga ya aikata laifin ba shi ba. Sannan mun ajiye miyagun ?wayoyi har da hodar iblis, da sunan mun kama su a gidan. Idan za a fara sharia dole a samo ?wararrun lauyoyi, kuma a yi wa al?alin kyakykyawan gani, ni dai daga ?angarena komai zai tafi dai-dai da yardar Allah. Tun da dama ya riga ya shahara kowa ya san ?an daba ne"

Indabo ya yi ajiyar zuciya ya ce "Haka ne, na gode sosai da sosai C.P, zaka ga sa?o da yardar Allah, kuma zan cika alkawarin da nayi, muddin komai ya tafi cikin nasara, amma C.P ba zai yiwu ku yi masa wani abu, ku kashe shi ba kawai?"

Ya ce "No, muddin wani abu ya same shi, mu kuma zamu zama abun arziki, saboda sanarwar da kakinmu ya fitar mun tabattar da yana hannunmu cikin ?oshin lafiya"

"Shikenan babu laifi, na gode sosai da sosai" ya sallami C.P ya tafi, ya ce "Aikin Naja'atu ya zo, P.A kira wo mini ita".

***
"Ka yi magana ka amsa laifinka, ka sau?a?a mana kai ma ka sau?a?awa kanka, idan ba haka ba mu zamu bi hanyoyin da zasu sama mana sau?i"

Al'amin ya ?ago da kyar, saboda a cikin mayen da yake, suka yi dukan tsiya, tamkar sun samu jaki, jikinsa ya ?ara mutuwa, kowace ga?a ta jikinsa ban da ciwo, babu abun da take yi.

"Ka amsa, ka ce ka sha kayan maye ka kashe matarka"

Gefen bakinsa duk jini, sun tu?e shi, daga shi sai vest da gajeren wando, ya sake ?aga idonsa, karo na farko yayi magana ya ce "Ina jauhar?"

"Ban sani ba, ni kake tambaya ina juahar? Bayan ka kasheta?" Tsaki yayi, ya ta?ar?are ya yin?ura ya tashi tsaye, suka saka kokara suka daki ?afafuwansa, ya hantsila ya fa?i a wurin.

Duk abun nan da ake yi, da jibgar da yake ci, shi kawai mafarki yake yi, jira yake yi ya farka, dan ba ya son baccinsa ya cigaba da nisa, zai kai Jauhar asibiti da wuri.

A haka aka shafe kwanaki bakwai, amma Al'amin, ya?i sakawa ransa cewa gaske ne ba mafarki ba.

Kwanaki bakwan nan, babu wanda ya zo in da yake, ba wai dan ba a samu masu zuwan ba, an hana kowa ganinsa.

Liti da walid, da sauran jama'arsa babu irin sintirin da ba su yi ba, amma aka hana su ganin sa.

Mutuwar jauhar, ta kara?e kowane gidan jarida, unguwanni zuwa gidaje.

Abbu yayi kuka tamkar zai yi hauka, yayi dana sanin kasancewar sa mahaifin Al'amin.

Gidansu jauhar kuwa, ba su san sun yi rashi ba, sai da aka tabbatar da mutuwar jauhar, kowa kuka da zubar da hawaye.

Abbu yana kuka, ya sanya gwiwoyinsa a ?asa, yana ro?on Baba ya yafe masa, da ya san Al'amin zai kashe masa 'ya, ba zai yarda a aura masa ita ba.

Baba ya girgiza kai ya ce "Alhaji Ibrahim, ni wallahi haryanzu ban ji na yadda Al'amin zai kashe mini 'ya. Akwai abun da ya faru ni ban yadda shi ya kashe mini jauhar ba"

Abbu ya ce "Wace hujja kake nema ko shaida bayan wannan? Ni na haifi Al'amin, kuma kowa ya san yana ta'amalli da miyagun ?wayoyi"

Cikin kuka mama ta ce "Yaron nan ya cuce mu, bai yi mana adalci ba, haihuwar ?a irin jauhar a gidan nan, daga kanta an gama, ba ayi ba, kuma ba za ayi ba"

Hafsa ta girgiza kai ta ce "Baba nima ina bayan maganarka, ?an kwanakin nan, ina zuwa gidanta sosai da sosai, ina ha?uwa da shi, ita take bani labarin galabar da ta ci a kansa, da bani misalai daban-daban da aurenta. Son da yake nuna mata a gabana ba ya jin kunyata ko nauyina, suna matu?ar ?aunar junansu. Har take gaya mini na tayata da addu'a, yanzu sigari ce kawai damuwarta da shi, har sai da na ji raina ya biya, da irin kalar soyayyar da suke yi wa junansu, dan haka gaskiya ban yadda mai zamani zai kashe jauhar ba, mutumin da idan zata fita baya nan, yake sawa ana bibiyarta dan kar wani ya kawo mata farmaki, mugwayen karnuka ya ajiye a layinsu, suna gadinta lokacin da yayi tafiya, duk dan kar a ta?a ta, gaskiya ban yadda ba".

Anty ma tana kuka ta ce "Babu abun da mai shaye-shaye ba zai iya aikatawa ba, dan haka ba abun mamaki bane dan an ce ya kasheta, Allah sarki jauhar wannan wane irin mummunan ?arshe ki ka yi?"

A fusace Saifu yana kuka ya ce "Kar ki sake aibata mana gawar jauhar, wallahi ba ta yi mummunan ?arshe ba, ta bi Allah, ta yi wa iyaye biyayya, ta yi biyayyar aure, idan ana nuna ?an aljanna a duniya to jauhar ce, koma wane irin mutum ne shi, ai ku kuka yi bita da ?ullin da ta aure shi, kuma wallahi Allah ba zai bar kowane azzalumi ba, ita ta mutu ta huta". Haka aka din ga musayar yawu, har sai da Baba ya tsawatar tukuna.

Da taimakon Naja'atu Bunkure, suka ha?a kai da lawyoyin gwamnati, Indabo ya cika su da ku?i, har da al?alin kansa. Domin tsayawa tsayin daka wurin tattara shaidu da hujjoji.

Haka zalika ta fito ta bayyanawa duniya cewa, zata tsaya tsayin daka, har sai ta ga abun da ya ture wa buzu na?i, sai an bi wa jauhar hakkinta, na kisan gilla da viper ya yi wa jauhar, mussaman dama ya riga yayi suna a harkar sha da fataucin miyagun ?wayoyi da kuma harkar daba.

Ranar fara shari'a, haka aka zo da mai zamani a cikin sar?a, yana ?ingisa ?afa, saboda azabar da ya sha a hannun 'yan sanda, a kan ya amsa cewa shi ya kashe jauhar.

Aka fara gabatar da shari'a, wani lawyer ya gabatar da kansa a matsayin wanda zai kare Al'amin, bai ta?a ganinsa ba, sai ranar a cikin kotun.

Aka gabatar da charges ?in da ake yi wa Al'amin.

?angaren tawagar lauyoyin gwamanti, da su Naja bunkure, suka din ga gabatar da shaidun bogi, suka kawo ?wayoyin da suka samu a gidan Al'amin, tare da kawo bayanan likita, na cewa dukanta aka yi har ta kai ga rasa ranta, da abun da yake cikinta.

Abun bai tsaya a nan ba, sai da aka kawo malam lawan, bayan sha?a masa wasu muhimman ku?a?e, ya zo ya bayar da shaidar Al'amin ya saba dukan jauhar, idan ya je ya sha ya bugu, haka za su yi ta jiyo ihunta yana dukanta, a ranar ma sun ji kukanta, sai dai ba su yi zaton zai kasheta ba.

Muryar Liti ce ta dawo da Al'amin hayyacinsa, dan duk surutan da ake yi, bai san me ake cewa ba.

"?arya kake yi dan ubanka, Viper ba ya dukan yar madara, ba ita ba kowace mace ma baya duka, a matsayin ku na ma?ota idan yana dukanta, meyasa baku kai wa yan sanda ba, ?arya kake ma?iyin Allah la'ananne, Viper ba zai ta?a cutar da matarsa ba, ba shi ya kasheta ba" jami'an tsaro suka yi waje da liti.

Sai dai wani irin ihu da Viper yayi, sai da wasu suka fara gudu, ya daki katakon gabansa da ?afarsa ya ce "?arya ne, jauhar tana nan a raye, gobe zata haihu, matata bata mutu ba"

Da ?yar aka danne shi, Al?ali ya aika shi gidan prison, tare da ?age shari'ar.

Haka ya cigaba da buge-buge, tamkar zai jefar da motar gidan yarin, sai da suka sumar da shi, sannan suka samu nutsuwa.

Tun daga wannan ihun, bai sake magana ba, ba cin abinci, sai dai zai yi salla kawai.

Har aka yi zama na biyu a kotu, bai ce uffan ba, duk wasu hujjoji Bunkure ce ta samar da su, lawyern gwamanti gabatarwa kawai yake yi.

Sai dai juyin duniya, ya yi magana, ya?i yi.

Bunkure ta je gaban Al'amin ta tsaya ta ce "Amsa ?aya kawai kotu take bu?ata daga bakinka, kai ka kashe matarka jauhar?"

Ya ?ura mata rinannun idanunsa, ta din ga yi masa wani irin kallo, mai cike da rainin wayo.

Ya jinjina mata kai alamar eh.

A nan suka bu?aci a ?ar?are shari'ar, ba tare da wata hu??asa ba, lawyern Al'amin, ya ce ya yarda da duk abubuwan da masu gabatar da ?ara suka gabatar. Daga haka aka sake ?aga shari'ar zuwa wata guda.

Wata gudan da sai da ya shafe shekaru biyar a prison, ba a cigaba da shari'ar ba, ba kuma a sallame shi ba.

Kullum burinsa shi ne ya farka daga mafarkin nan da yake yi, shi dai ya san matarsa na raye, ba ya cin abinci baya iya bacci, ya koma tamkar mahaukaci.

Sai dai lokaci zuwa lokaci yana yi musu ihu, da kiran matarsa, ya kan kira sunan madaki da Indabo.

Lokaci lokaci, ya kan ga aiken abinci, hakan ya sanya ya ?ara sakankancewa jauhar ce ke yi masa aike, bai sake ganin wani yazo wurinsa ba, tsawon shekaru biyar ?in nan.

Rana tsaka aka ce masa ya fita ya tafi gida an sallame shi.

A ?ofar prison ?in ya tsaya, yana tuna lokacin da ta zo tafiya da shi, lokacin da aka rufe shi, aka ce an kama shi da cocaine.

Bai tsaya ko ina ba, sai unguwarsu, da ?afa ya taka ya tafi, amma ya tarar da gate ?in a rufe.

Sai yayi tunanin ta koma gida ne, dan haka sai ya fara tafiya gidansu, dan tabattar wa.

Gidansu ya fara zuwa, rahila da yaranta, gaba ?aya suka dare, suka gudu ?aki tana ihu ta ce "Ka fita ka kore shi, gashi can an sako shi, Allah wadaran yan siyasa, sun sako masifa da annoba, wanda bai san halacci ba".

Abbu ya fito ya kalli Al'amin, ya koma kamar wani mahaukaci, a gigice ya nufo Abbu ya ce "Abbu, ina jauhar? Ta haihu ne? Ina abun da ta haifa?"

Abbu ya ja da baya ya ce "Kar ka matso kusa da ni, Jauhar tana gidan uwarka da ubanka, dama ka gaya mini zaka kasheta, kuma ka cika al?awarin ka Al'amin, na gode da muguwar sakayyar da ka yi mini, da ?ata mana sunan zuriya. Ka fita babu ni babu kai, ka nemi wani uban bani ba, na sallamawa duniya kai, ba zan cigaba da rasa makusantana, mutanen da nake ?auna ba saboda kai, ka je na yafeka a duniya"

"Na ji na yadda, amma ina jauhar? Sun ce idan na ba su abun da suke so, zasu kai ni in da take"

"Sai dai ka bita kabari ka ?auki ?an naka, mara mutunci, ka fita ka bar mini gida, bana ?aunarka bana ?aunar ganinka"

"Ba zai yiwu ba, wallahi sai kun fito mini da matata" ya juya ya fita da gudu, ya tafi dabar su, incomplete building ?in da suke zaman shaye-shaye.

Su Walid suna ganinsa, suka rirri?e shi suna kuka, ya watsar da su ?asa, ya ce "Walid, ina jauhar? Na san ta haihu ko?"

Walid ya tashi tsaye ya ce "Viper ka nutsu mana, ya aka sako ka ne? Ba yadda bamu yi ba, a ?arasa shari'arka mu ?aukaka ?ara aka ?i"

"Dalla ina tambayar ku, ina jauhar, ko ta koma gidansu, ku bani kaya na canza na je wurinta, na san hanata ganina aka yi"

Hawaye na zuba a idon liti ya ce "Viper, ?ar madara fa ba ta raye, ta rasu"

Al'amin yana zuwa nan a maganar, yayi shiru, yayi fatali da kayan gabansa, ya fara wani irin haki, yana nema ya kurma ihu.

Nabila tana kuka, ta toshe masa baki tana girgiza masa kai.

Ya saka hannu, ya cire hannunta daga bakinsa ya ce "Ban cancanci na haukace ba? Ban cancanci na nemi fansa ko ta wane hali ba kenan?"

Nabila ta girgiza masa kai, kuka ya hanata magana.

"Na kashe matata, ni na kashe jauhar ?ina, halittar da ta nuna mini tsantsar so da ?auna"

"Ba kai ka kasheta ba"

Cikin tsawa ya ce "Ni ne, ni na kasheta. Meyasa da Abbu ya ce mini zai yi mini aure, na ce zan kasheta, ya ce mini Allah ya taimaka? Meyasa na kasa tuba na daina bangar siyasa da daba, a lokacin da zabra take ta ankarar da ni illarta, mai yasa sakamakon laifina ya fa?a kan matata?"

"Astagfirullah, Viper kar ka yi sa?o"

"Meyasa ban kar?i ?addarata ba tun da farko, na furta idan aka yi mini aure zan kasheta? Meyasa na jinkirta barin aikata laifi, sai da na rasa mutane masu muhimmanci a sanadin daba da shaye-shaye. Daba da bangar siyasa ta yi mini mummunan tabo, na kasa zubar da hawaye ko sau ?aya tsawon shekarun nan, meyasa ba zan haukace na huta ba.
Ina son matata, laifina ya shafe ta, ba ta ji ba bata gani ba, na kasa yadda ta mutu, haryanzu ina ganinta ina ganin ?ana a jikinta. Ko ban ?auki fansa ba, ina fatan na haukace, ko na bita na huta. Ina ma jauhar ba ta sanni ba, da yanzu tana nan tana rayuwa cikin farin ciki, bani da sa'a ko ka?an a rayuwata, duk wanda na saka sonsa a raina, sai Daba da bangar siyasa tayi masa illa"

Huci yake yi, idanunsa suka rine zuwa ja mai ban tsoro.

Ta sake mayar da hannunta bakinsa, ta rufe masa, tana kuka ta fara furta "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, Innalillahi wa Innalillahi raji'un, Innalillahi wa Innalillahi raji'un. Astagfirullah wa atubuilaihi"

A hankali ya fara maimaitawa shi ma, jikinsa na kyarma, kamar wanda ake ka?awa gangi.

Nabila ta ce "Ka yi i ajiyar zuciyan da kake dannewa" ya kama ?aya hannun nata, ya ?ora saitin zuciyarsa, yana wani irin haki, wani irin bugu zuciyarsa take yi mai ban tsoro.

A take ya saki wata irin nannauyar ajiyar zuciya, tare da hawayen da suka ma?ale a tsakiyar zuciyarsa tsawon shekaru shida!

Ayshercool
08081012143
???500 ne via 0009450228
Aisha Adam jaiz bank sai shaidar biya ta 08081012143
Wanda za su jira document 1K ne.

90009343
'Yan Nijar ku turo katin airtel na 300fcfa

Arewabooks ayshercool7724



Cikin matsanancin tashin hankali, Nabila tana kuka ta ce "Viper zuciyarka fa, dan Allah ka nutsu zata daina aiki, idan ta cigaba da bugawa a haka, ka cigaba da istigfari da maimaita Innalillahi wa Innalillahi raji'un" tayi maganar cikin damuwa, ?ara danna hannunta yayi a kan ?irjinsa, yana wata irin sha?uwa mai ha?e da haki, numfashin sa na fita sama-sama.

A jejjere zuciyarsa take bugawa da ?arfin gaske.

Cikin tausayawa take kallon sa, Al'amin yana bu?atar kafa?ar da zai kwanta yayi kuka, babu wanda ya fuskanci ainihin matsalar sa, kowa ?ora masa laifi kawai yake yi, iftila'in da ya fa?a masa, kowa ya dare ya bar shi, sai abokansa duk da suna iya ?o?arin su a kansa, amma ba abun da yake bu?ata suke yi masa ba.

Ji tayi ina ma tana da damar, da zata rungume shi, ta bashi dama yayi kuka yadda yake so, ko zai samu afuwa a zuciyarsa, tsawon shekaru shida, yana dakon ba?in ciki da damuwa, kuma ya kasa zubar da hawaye sai a wannan lokacin.

Haka yayi shiru ya sunkuyar da kai, sai dai bai saki hannunta ba, hawaye ne kawai yake zuba daga idonsa, taya shi take yi, sai dai ta rasa me ma zata kuma ce masa, a tsorace take da kar zuciyarsa ta buga.

A hankali ya saki hannunta, ya goge hawayen sa, ya tashi zumbur, ya tattare kayan ya mayar ?akin, hatta kayan jauhar suna nan, lokaci lokaci, su Walid ne ke zuwa su karka?e gidan su share, dan idan ya bushi iska yana zuwa cikin dare, yayi ta tuna irin rayuwar da suka yi.

Yanzun ma yana shiga ?akin, ?wa?walwarsa ta nuna masa ita zaune a kan gado, tana shirin dutse, gefe ga boti a kusa da ita a kwance, ya mimmi?e yana ta goge jikinsa.

Ta ?ago ta kalleshi tana murmushi ta ce "Manya gatan wasa, me ake so ne ake ta kallona? Ko fankar ce?" Tayi maganar tana kashe masa ido.

Gadon ya nufa da hanzari

Please Login or Register in order to submit comment