Reading KARFE A WUTA Chapter 89 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kuka ta ce "Amira yau kwananta biyu bata gidan nan, ban san in da take ba, na yi wa babanku ?aryar tana gidan Yaya, Shahida na shiga uku"

Jiki a sanyaye ta ce "Mama baki shiga uku ba, ni fa daga kotu nake, na kai Anwar ?ara ya sauwwa?e mini, ba zan iya ba na gaji" A razane ta ce "Ya sauwwa?e miki? Shahida baki da hankali, a wannan ?adamin da ake ciki zaki kaso aurenki, ya ki ke so nayi, sai duniya tayi mini dariya?"

"Mama, kin kasa gane in da na dosa, wai so ki ke sai na halaka ne, saboda kawai yana da ku?i, nayi ha?uri fa iya ha?uri, ke fa uwata ce, ha?urina ya ?are, Allah da zan iya tunkarar Abba, da sai na tunkare shi na sanar masa".

"Shahida uban naki zaki tunkara da wannan maganar? Saboda baki da kumya?"

Cikin tsiwa ta ce "Idan ba irin Amira ki ke so na zama ba ki ?yale ni dan Allah"

Rahila ta kwantar da murya ta ce "Ki rufa mini asiri Shahida, shi wannan ya fara shaye-shaye, waccan bin maza, shi Nazifi ya gudu kudu neman ku?i, ban ma san a duniyar da yake ba, ke ka?ai ce a ?akin aure nake jin da?i, kar ki gurgu?e auren nan, ki ?ara tona mini asiri, ba ya ce miki yana neman magani ba? Baki san me Allah ya ?oye a lamarin nan ba, ga tarin dukiya yana da ita, sai ki ga ke kin haihu da shi, ki haifi namiji, wannan dukiyar ta zama tamu"

Ta kalli Rahila cikin takaici ta ce "Na haihu ta yaya, mama shekara uku fa, wane irin magani ya kasa nema a kan sauran matan da ya rabu da su? Ashe aurensa tara ni ce ta goma ya ?oye mana, ga shaye-shaye ga cin mutunci har da duka wasu lokutan, wallahi ba za a kashe ni da raina ba, gara na auri talakan tulus in samu nutsuwa da kwanciyar hankali" Rahila ta ?ora hannu a ka, ta din ga kurma ihu, tana kukaz Shahida ko a jikinta, ta tashi ta shige ?aki ta bar ta.


***

Abin duniya duk ya damu liti, da yayi juyi ya ga babu ?an mama sai yayi ta tsaki, da daddare ma kasa bacci yayi, sai tsaki yake yi.

Walid ya ce "Sarkin gida"

"Mai laya"

Walid ya ce "Wai ya ne?"

"Wallahi tunanin yaron nan nake yi, Allah ya sa ba suna can suna jibgarsa ba, ka san ba imani ne da su ba, kuma ga sauron wurin nan"

Walid ya yi dariya ya ce "Allah liti, kai ne kake tunanin halin da ?an mama yake ciki? Dama ka damu da shi har haka?"

Liti yayi tsaki ya ce "Wallahi ban san ya aka yi ya shiga raina haka ba, ka san ya iya ladabin makirci, wallahi da ya dawo wurinmu, rashin Nura ya sanya nake yin sa"

Viper ya yi gyaran murya ya ce "Ka yi ha?uri duk laifina ne, amma in sha Allah ba zai wula?anta ba zai fito"

"Idan ma cewa kayi ba zai fito ba, ya tafi kenan dai-dai ne Ogana"

Viper ya ce "Zai ma fito, ni kaina nayi mamakin yadda ya shiga raina, Allah sarki ?an uwana Nura, Allah ya sanyaya makwancinsu da shi da mahaifiyata, da Sadik, da uban gidana dodo, da kuma matata a bar ?aunata, da dukkanin wanda muka rasa" suka amsa masa da Amin.

Liti dai bacci gagararsa yayi, sai tsaki ya din ga yi yana juyi.


Gidan da Nabila take, aka gabatar mata da wata macen soja, a matsayin mamallakiyar gidan, ba ta gari ne ya sanya Nabila take zaune a gidan tare da masu aikinta.

Nabila ta zata zata ga matar masifaffiya, kasancewar an ce soja ce, amma taga ba haka ba, tana da matu?ar kirki da sau?in kai.

Nabila ta din ga jujjuya lambar mahaifin Viper tana son ta kira, amma tana tsoron tijarar Viper, kasancewar ya garga?eta a kan haka, tana cikin tunanin, sai ga kiran Viper sai da ta kusa katsewa ta ?aga ta ce "SPY"

"Idan ki ka sake suka ji abin da ki ke fa?a, zasu iya kashe ki, ban da ogana da ya zo wurnki da su Walid, babu wanda ya san kin san ni waye"

"Yanzu har su Oga Walid basu sani ba"

Ya ce "Mmmm"

"Ta?, sannu"

"Yauwwa, ya rahama da mamanta? Ina son zuwa da gaske kamar yadda ki ka ce, na ga halin da suke ciki"

Nabila ta ce "Akwai matsala, ciki ne fa da rahama"

"What ciki ta yaya?"

"Ya za ayi in sani, ciki dai, maman hankalinta ya tashi sosai da sosai, ta ce sai an zubar, wallahi na rasa yadda zan yi, gashi ta ?i magana rahaman, muna son mu ji, kafin ya aureta cikin ya samu ko bayan ya aureta, amma na fi kyautata zaton bayan auren ta samu cikin, duk da bamu san meyafaru da wancan cikin ba da ta samu bayan ya mata fya?e"

Viper ya ha?iye takaici, ya tsani ya ga an ci zarafin mace, mussaman mahaifiyar ramma da aka watsa mata yara gaba ?aya babu wani wanda ta amfana an watsa rayuwar su, kuma abin mamakin uba da ?a ne suka lalata mata rayuwar yara"

"Bani adress ?in in da suke zan je" yayi maganar a kausashe cikin damuwa.

"Ka bari muje tare, ina ga idan rahaman ta ganmu tare, ta yi magana, kayi ha?uri na san ranka a ?ace yake, amma babu yadda muka iya da ?addara" yayi shiru yana huci.

A raunane ta ce "Viper"

"Mmmm"

"Idan na mutu baka sadani da mahaifin jauhar ba, wanda nake kyautata zaton ina da ala?a da ita ba, ba zan yafe maka ba"

Dummm haka ya ji maganar Nabila ta dira a tsakiyar zuciyarsa.

Viper "Kin san me ki ke fa?a kuwa? Ta ina ki ke da ala?a da jauhar?"

Tuni ta fara kuka ta ce "Abubuwa da yawa, na fara sarewa, tun kan na ganka nake mafarkinka, bayan ban sanka ba, ban ta?a ganinka ba, ina da ciwon Athma da take gada nayi daga mahaifiyata, ita ce take da ciwon, familyn su na Jalingo da yawansu, Asma ciwonsu ne, ita ma ka ce ciwonta ne. Akwai abubuwa da dama, ba zan ?oye maka ba, Wallahi idan Allah ya kar?i rayuwata baka sada ni na mahaifina ba, ba zan yafe maka ba" ta ?arasa maganar tare da kashe wayarta.

***
Abba ya kalli Nasir ya ce "Nasiru, ya aka yi ne, an ce tun ?azu ka ke nemana, na je wani wuri ne, ya aka yi?"

"Na ha?u da Arfa"

Abba ya ?an yi sak, sannan ya ce "Tana lafiya" ya jinjina masa kai alamar eh.

"Haryanzu ba ta yi regreting abin da tayi ba kenan, shirun da nayi mata da zuru duk bata saduda ba kenan?"

"Babu alama, tare da ?an daban suka je CID jiya"

"What? Aka ce mini tana barrack wurin yarinyar nan Halima goza, ina sane da duk halin da take ciki ai"

Nasir ya ce "Tare dai na gansu, tare da wasu 'yan daban ma, da sumayya"

Abba ya yi shiru cikin takaici, wai 'yan daba.

"Nabila ba ta da hankali, kuma bana tunanin zata yi shi, zan je na taho da ita, duk wadda za ayi sai dai ayi, basarwa kawai nake yi, amma hankalina yana kanta"

"Abba" ya kalli Nasir.

"A harabar wurin, ga abin da shi wanda take karewar ya bani"ya mi?awa Abba envelope.

Cikin matsananciyar fa?uwar gaba, ya kalli Nasir ya ce "Hoton da ta kawo mini wancan karon dama ba Photoshop bane?, Har na fara tunanin waye ya gaya mata wani abu"

"Abba ka san babu wanda ya isa yayi fatali da umarninka a cikin gidan nan"

Muryar Abba har rawa take ya ce "Shi wannan ?in waye a jikin hoton?"

"Shi ne gayen, matarsa ce, ita ce ake shari'ar a kanta ai, ake zargin ya kasheta"

A zabure Abba ya tashi tsaye jikinsa yana rawa ya ce "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, kuma Nabila saboda mahaukaciya ce, ta tsaya masa take fafutukar a wanke shi, Innalillahi wa Innalillahi raji'un, Nasir kira mini Nabila a waya yanzun nan".

Nasir ya ciro wayarsa daga aljihunsa, ya kira lambar Nabila, amma line busy.

Ya ce "Abba line busy" Abba jikinsa na ta ?ari, ya ciro ta sa wayar, ya jefawa Nasir, ya ce "Kira ta maza" sai dai tun tana cewa line busy, aka ce wayar a kashe take.

"Abba ta kashe wayar"

"Nasiru, tashi ka ?aukko mota mu tafi barrack"

"Abba a daren nan, wajen gari ne wurin"

"Ka tashi na ce!" Yayi maganar cikin tsawa.

"Abba dan girman Allah kayi ha?uri, ka san ba zasu bari mu shiga yanzu ba, dan Allah ka yi ha?uri sai Allah ya kaimu gobe da wuri sai mu tafi.

Anty da ta fara bacci, a bedroom ?in Abba ta fito ta ce "Major lafiya kake ?aga murya a daren nan?"

Nasir ya ce "Bakomai"

Har Abba zai bar falon, ya dawo ya nuna wa Nasir hoton ya ce "Waye wannan ?in ne wai?"

Nasir ya ce "Abba, na ce maka shi ne ?an daban da nake nema, aka ce na kama, yarinyar jiki ya kashe.... Abba ya ?aga masa hannu ya dakatar da shi, ya shige ?aya ?akin nasa ya kulle ?ofa.

"Nasir meyake faruwa ne?" Anty ta sake tambayar Nasir cikin damuwa.

"Bakomai"ya sake bata amsa a ta?aice ya fice.

Abba ya ?aukko wani hoto tun Black and white, da hoton wata matashiyar budurwa a jikin bukka ta bu?e ha?ora tana dariya, aka yi mata hoton.

Ya ha?a da hoton da Nasir ya bashi, gabansa ya tsananta fa?uwa ya ce "Anya ban tafka kuskure ba kuwa? Hukuncin da na yanke bai yi muni ba? Kana naka Allah ya na nasa. Innalillahi wa Innalillahi raji'un, na yanke hukunci cikin fushi, bayan shekaru Allah ya jujjuya ?addara yadda yake so, ki yafe mini mairamu" yayi maganar cikin matsanancin rauni.

Kwana Abba yayi a zaune, yadda ya ga rana haka ya ga dare, cikin tashin hankali da rashin sanin abin yi, ya din ga jinjina girma da ?udurar Ubangiji.

***

Sojar nan sai mita take yi wa Nabila, ta ?i sakin jiki ta karya.

?arfe bakwai da rabi, Viper ya je gidan, suka gaisa da Madam, ya ce "Nabila ta shirya, za su fita"

Madam Goza ta ce "Ka kar?o permisson ne?"

"Eh sun sani, wurin aiki zata je, muna ta shirin shiga court"

Ta jinjina kai ta ce "Best of luck"

Ya amsa da thank you.

A wata ha?a?iyar mota helux mai fentin sojoji, aka ?auke su.

Da ?yar Nabila ta iya ce masa "Ina kwana"

Shiru yayi bai amsa ba, ita ma ta ja bakinta ta tsuke.

Gaba ?aya fuskarta mamaye da damuwa, kamar ma ba ta samu isasshen bacci ba.

"Meyasa ki ce ba zaki yafe ba, idan ban ha?aki da iyayen jauhar ba, Allah ya isa fa ki ka yi mini kenan"

Cikin rauni ta ce "Ya ka ke so na yi, ka ?i fahimta ta, Allah ke da yau da gobe, balle ka ce akwai lokacin da ka za?a, ka nuna mini iyayenta".

Ya numfsa ya ce "Kalmar tayi mini nauyi sosai, kasa bacci nayi" ta yi masa shiru, tana kallon window tana share hawayenta.

Ya kamo hannunta ?aya, ta kalleshi da sauri, ta fara ?o?arin ?wace hannunta.

"Ki daina kuka, jauhar ?ina nake gani, kar nayi ?arna dan Allah"

"Cika ni, ni ba ita ba ce, ni maganin kukana Allah"

Ko a jikinsa ya ce "Kar ki ce zaki yi kishi da ita, wahala zaki sha"

Shiru ta sake yi masa, tana duba wayarta.

Nasir ya turo mata message "Ki ?aga wayata, zamu zo ni da Abba" kasje wayarta tayi, saboda a jikinta ta ji Nasir ?arya yake yi.

****
A rikice maman ramma ta tashi, ganin Nabila tare da Viper, ta nufe shi da sauri ta fashe da kuka.

Ri?eta yayi, jikinsa a sanyaye yana tuno Nura guduma, ya ?agota yana share mata hawaye ya ce "Mama, ki daina kuka dan Allah, na san ni mai laufi ne, rabona da ke na da?e, amma ?addara ce ta janyo duk hakan".

Cikin kuka ta ce "Murnar ganinka nake yi Aminu, ashe zan sake ganinka? Ni da Hajiya mun zo wurinka sau uku, tun daga ?auye amma ba a bari mu ganka, Allah bai ?addara zaku sake ganawa da ita ba"

Aminu ya ce "Allah sarki, ki yi ha?uri ke gashi Allah ya ?addara ganawarmu ai" yayi maganar yana zaunar da ita a kan kujera.

Nabila ta gaisheta, ta amsa tana kallon Nabila tana kallon Viper, gashi an hanata magana.

"Jauhar a ina ki ka gano shi? Ya aka yi ki ka san muna da ala?a da shi?"

Viper ya ce "Nabila ce wannan, ita ce lauyar da zata tsaya mini nima, kuma take ta ?o?ari a kan shari'ar rahama. Komai da ake ciki tana gaya mini, ina son na zo na ganki na gaishe ki, amma kin san jami'an tsaro nemana suke yi, kuma ina tsoron ki yi mini kallon ?an ta'adda da ya kashe matarsa"

Cikin ?aurewar kai ta ce "Wai ni fa na rikice, tayaya Jauhar ta koma Nabila kuma?"

Viper ya ce "Zancen dogo ne, yanzu mu fara gamawa da batun rahama" yana maganar ramma ta fito cikin hijjabi.

Mammaki ne ya kama shi, har ya tafi prison yarinya ce ?arama sosai, amma yanzu ta zama wata uwar mata, tayi ?iba, tayi haske sosai.

Cikin matsanancin tsoro, ta gaida Viper, ita gaba ?aya taoro yake bata tun lokacin da ta ta?a ganinsa a asibiti da kuma lokacin da ya zo gidansu"

Viper ya yi mata alama da ta zo.

Ta ?arasa gefe kusa da Nabila ta zauna.

"Maganar me ake so ki yi ki ka ?i yi? Sai kin yi magana za a iya ?watar miki hakkinki"

Jiki na rawa Ramma ta kalleshi, amma ta yi shiru. Tsura mata ido yayi ba tare da yayi magana ba, babu shiri ta fara bayani tiryan-tiryan.

Nabila ta ce "Ta??ijan, wannan case ?in akwai sar?a?iya, cikin jikinta na halal ne ai"

Maman ramma ta ce "Dan girman Allah ku taimake ni a zubar da cikin nan, yaron nan ba shi da tarbiyya ko ka?an, babu ?an da zai yi alfahari da shi a matsayin uba, ni dai bana bu?atar sa".

Viper ya ce "Na goyi bayan haka, yakamata ta koma makaranta ne, ta fuskanci rayuwarta da ?alubalen rayuwa"

Ramma ta fashe da kuka, Nabila ta ce "A'a dan Allah ku yi ha?uri, laifi ne na kisan kai, ko kin yadda a zubar?" Tayi maganar tana kallon ramma.

Ramma ta girgiza kai ta ce "Mama dan Allah ki yi ha?uri, nayi masa al?awarin ko an kama shi, ba zan zubar da cikin ba, dan Allah ki bari na haihu, ya ce mini mutuwa ake yi idan aka zubar da ciki" tayi maganar cike da yarinta da wauta.

Salati suka hau yi, Viper kawai ya jinjina kai.

Ya tashi ya ?arasa gaban Ramma, ta sake takurewa gabanta na tsananta fa?uwa.

Ya ce "Kin san yayanki Nura ko da ya mutu?" Ta jinjina masa kai alamar eh.

"Baban wannan mutumin da yayi raping ?in ki, ya ci mutuncin ki, shi ne ya yi sanadiyar mutuwar sa, bayan ya yi masa fya?e ta wurin bayan gidansa, idan kin za?i ki rufa masa asiri ba zaki bayar da ha?in kai ayi abin da ya dace ba, ba kanki kawai ki ka cutar ba, har da marigayi ?an uwanki"

Toshe baki ramma tayi, tana bin Viper da kallo, jin maganar tasa kamar almara, sai yanzu wasu abubuwan suka din ga dawo mata.

Nabila ta ce "Vi da ka sani baka gaya mata a haka ba"

"Muddin aka tafi a haka, zata baki kunya a wurin Shari'a, alamu sun nuna zata iya ruf masa asiri"

Ya kalli maman ya ce "Mama, zamu tafi, akwai uzururruka da zamu yi amma zan dawo, ki yi ha?uri, na san na fama mana wani ciwo mai wuyar warkewa.

Ta jinjina masa kai ta ce "Gara da ka yi mata hakan, na gode Aminu, Allah ya kula da kai ya tsare mana kai. Kema Allah ya rufa miki asiri duniya da lahira". Tayi maganar tana kallon Nabila, bakinta fal maganganu, da tambayoyi, sai dai garga?in da aka yi mata ya hanata tambayar, amma har a wannan lokacin zuciyarta na bugawa cikin tsananin tashin hankali da mamaki, a duk lokacin da ta ga Nabila, mussaman a yanzu da ta gansu tare da Al'amin, kuma ya ce mata ba Jauhar ba ce.

****
Abdul yana tare da su Salim, ya sha ya bugu yayi mankas, dan abin da yake yi kenan ya samu sassauci, gaba ?aya nema yake ya haukace saboda rashin sanin in da ramma take.
Salim ya mi?e yana ?o?arin kama shi su tafi, kawai suka ga an kewaye su, wasu mutane sanye da kaya personal.

Ba su yi musu wani dogon jawabi ba, suka kama su gaba ?aya suka tafi da su.

Indabo yana Abuja, zuwa kano ya gagare shi, duk da zaman Abujan ba da?i yake yi masa ba, kotu ta yi seazing ?in passport ?in sa, babu damar fita ?asashen waje, har sai an kammala bincike, kwamiti biyun da aka kafa, na binciken ku?a?en da aka karkatar, duk sunansa ya fito a ciki, ga kuma tuhuma daga ?angaren EFCC.
Gefe guda kuma, a Kano mutanen yankinsa na shirin yin abin da ba a ta?a yi ba a Nigeria, shi ne yi masa kiranye, ya dawo daga Abuja ba su gamsu da wakilcin da yake yi musu ba, ya rasa wane tunani yakamata ya yi, wace mafitar yakamata ya fara nema.
Ana tsaka da haka aka kira shi a waya, aka sanar da shi an kama Abdul, ba a ma san wace police station ?in aka kai shi ba, abokansa ne suka sanar da kama shi.
Hakan ya ?ara gigita shi, da tayar masa da hankali, ya fara shirin tahowa Kano.

****
An so a kai ruwa rana kafin a bawa Abba damar ganin Nabila, sai dai kasancewar shi ma retired solder ne, aka bashi damar hakan. Sai dai suka tarar da Nabila bata nan. Gaba ?aya Abba ya rikice, ya din ga fa?a ya ce "Shi ba haka aka yi masa bayani ba, an ce za a ri?e masa 'ya ?ar?ashin kulawar hukuma, dan me zai zo ace bata nan"

"Sir, bawa yarinyar nan kariya baya nufin mu yi ta ?oyeta, akwai ayyukanta da take gabatarwa na aikinta. Sun fita an yi mata rakiya zuwa wurin gudanar da aikinta, rayuwarta na cikin ha?ari ne".

"Rayuwarta na cikin ha?ari, sai a kauwwameta a cikin barrack ma tukuna, ba 'yan sanda ne yakamata su bata kariyar ba ma, menene ha?inta da ku kuma?"

"Akwai dalili mai girma, da ba zamu iya gaya maka ba sir"

Ya sake kallon Nasir, ya ce "Kira mini ita"

Nasir ya sake kiran wayar Nabila, wayar na hannun Viper, Nabila kuma ta shiga cikin ma'aikatar Shari'a tare da barrister Habib.

?aga wayar ya yi ya saka a kunnensa "Arfa, tun jiya ake kiranki a waya kin ?i ?agawa, Abba yana son ganinki lallai kina ina yanzu?"

Kai tsaye Viper ya ce "Na tafi kaita wurin mahaifinta"

A sukwane Abba ya kalle shi, saboda a hansfree wayar take, ya ce "Waye wannan?" Abba ya kar?e wayar jikinsa na tsuma ya ce "Who are you, waye ya baka wannan damar? Kana ina? Ina 'ya ta?"

Cikin girmamawa Viper ya ce "Am sorry sir, wannan al?awari ne da nayi wa Nabila, a matsayin hakkinta na aikin da tayi mini. Na baku damar sanar da ita komai, saboda ban san dalilinku ba, amma ka bata damar ta je ta nemi mahaifinta.
Nima ina bu?atar sanin, menene ala?arta da matata".

"Stop it, kar ka kuskura ka kai Nabila wurin wannan mutumin"

"Am very sorry sir"

Cikin tashin hankali Abba ya ce "Ku san yadda zaku yi, ku dakatar da mutumin nan, ku gaya mini in da yake ya dawo mini da ya ta, bamu yi da ku ku bari tana yawo da yan daba a gari ba.

Viper ya tsurawa Nabila ido, tana nufo motar, ta ?araso ta bu?e motar tana yi masa magana.

"Lafiya kake kallona haka?"

"Shigo muje wani wuri, zamu ?auki su Walid mu tafi"

Jiki a sanyaye ta ce "Ina?"

"Zaki gani" ta ce "To"

Ta shiga motar ta zauna, hakanan sai ta ji jikinta yayi sanyi, kamar an zare mata laka.

A ransa ya ce "Yau komai zai zo ?arshe in sha Allah"

Indabo ne a hukumar yansandan farin kaya, kamar zararre, yana ta masifa da tambayar ba'asin menene dalilin da ya sanya aka kama masa ?a.

Da ?yar aka lalla?e shi ya zauna, "Honorable, ana zargin ?anka da aikata laifin fya?e, tare da ?oye yarinya ba da sahalewar iyayenta ba, sannan bayan mun kama shi, mun same shi da miyagun ?wayoyi ciki har da wa?anda aka haramta shigowa da su ?asar nan, wanda ta'amalli da su babban laifi ne"

"Wannan duk ?age ne da yarfe da son ?ata mini suna da siyasata, sharri aka yi masa, bai aikata ba, ku sakar mini ?a kawai"

"Distinguish senator, kai babban mutum ne a ?asar nan, kar mu yi ta jayayya da kai dan Allah. Duk wasu shaidu da hujjoji da ake bu?ata muna da su, shi ya aikata laifin, dan haka kotu ce take da damar wanke shi ko kuma hukunta shi, kayi ha?uri aikinmu muke yi.

Ayshercool
08081012143
???500 ne via 0009450228
Aisha Adam jaiz bank sai shaidar biya ta 08081012143
Wanda za su jira document 1K ne.

90009343
'Yan Nijar ku turo katin airtel na 300fcfa

*BRIGHT PENS SECOND BATCH*

Ku kasance da littatafan bright pens, second batch.
*?ARFE A WUTA (AYSHERCOOL)*
*MUTALLAB (NIMCYLUV)*
HADARIN GABAS (NAZEEFA NASHE)*
*ZAYTOON (ZEE KUMURYA)*



??????????????????????????

*_GYARA SHINE MACE_*

*_ZATA FASHE FA KARKU BARI AYI BABUKU ZAFAFAN KAYAN MATA MASU KYAU DA INGANCI KUMA AKAN FARASHI MAI SAUK'I ,MAMAN YUSUF YAR MUTAN SOKOTO TA SHIRYA TSAF DOMIN GWANGWAJEKU DA ZAFAFAN KAYANTA MASU MATUKAR INGANCI_*
??????????????????????????

*_'Yar uwa shin ko kin San lokacin sanyi lokaci ne da yake dask'arar da ni'imar mace , yake yawan bushe gaban mace , sannan lokacin ne maza sukafi bukatar matansu , lokaci ne da kowane lafiyayyen namiji yakeson ya jishi ajikin matarshi a kowane lokaci , to ya kike gani idan har mijinki Yana son kasancewa Dake Haka kekuma ga ni'ima a bushe , 'yar uwa mace fa Saida gyara , ko kinada kyau to ki k'ara da wanka don ci gaba da kankanrowa kanki daraja da k'ima a idon Mai gida ,. Ki tuna duk son da namiji ke maki in har kinada matsala a wannan wajan to wlh akwai matsala don son da yake maki bazai Hana kurinka samun matsala dashi ba ,idan kuwa har Yana samun yadda yakeso wlh ko baya sonki to Ina tabbatar maki da a hankali wata Rana sai ya soki Kuma zakiga kowane lokaci Yana tattalinki da gudun abunda zai 'bata maki Rai , Mata a kula*_ maman yusuf likitar Mata 07069711327

*Wannan dalilin ne yasa nazo maku da Kaya masu zafi kamar Haka*????????????????????????

Akwai ingantaccen maganin sanyi Mai fatattakar sanyi cikin kankanin lokaci na maza Dana Mata , kun dai San illar da sanyi yake da ita ku kula,

Akwai ingantaccen maganin nono hadin gargajiya na Sha Dana shafawa Mai taso da nono ya Kuma gyarashi Hadi da tsayuwarshi ,??

Sai maganin hips Wanda zaisa hips dinki ya ciko kema ki shiga jerin Mata masu aji??

Akwai maganin k'iba Wanda zai ciko da jikinki kiyi kiba Yar daidai Mai kyau wadda zata dace da yanayin jikin ki??

Ina bada Hadi na mussaman ga yarinyar da ta rasa budurcinta sanadiyar fyade ko yaudarar d'a namiji ,Wanda insha Allah akayi amfani dasu to yarinya zata koma normal Wanda duk zata aura Ba zai iya Gane komai ,
Mmn Yusuf likitar Mata????

Akwai hadin amarya Wanda zaisa ki ciko ki hade gam sannan su Baki ni'ima irin wadda akeso ingantaccen sirrin da zaisa ki Kara samun soyayyar mijinki cikin sauki??????

Akwai hadin sabon budurci da mukeyi ga wadda ta kasance bazawara hadine da ko haihuwarki nawa akayi maki shi Zaki koma tamkar budurwa Wanda ko Wanda Kika aura zaisha mamakinki Wanda hakan Kuma wata hanya ce ta kankanrowa kanki daraja da k'ima ne zawarawa ku matso karku Bari ayi babuku??????????

Akwai hadin Mai jego , kunsani mace na rasa mafi yawa ni'imarta yayin haihuwa wata ma Zara karu ne to indai kikayi wannan hadin Ina tabbatar maki da cewa Zaki hade ciki da waje gabanki zai ciko sosai in karuwa kikayi K'arin zaizo ya hade tsaf sannan Zaki samu dawamammiyar Ni'ima

KADAN DAGA CIKI WASU KALOLIN????????

Kalolin gumba
Kalolin matsi
Kalolin gari
Kalolin tsumi

Zumar dabino
Zuma Mai rubutu
Zumar goron Tula
Zumar ridi

Dahuwar kaza
Dahuwar zabo
Dahuwar zuciya
Dahuwar ciccibi
Dahuwar tsoka Tara
Dahuwar Yan shila
Dahuwar kwai Mai rubutu

Turaren mallaka
Turaren Mara
Turaren tsugunno
Turaren k'irji
Shuumar humra
HATSABIBI turare
Hatsabibiyar humra

Matan gaske
Maltinat Mata
Shayin Mata
Tsumin kankana
Sirrin tafin k'afa

Akwai sirrika na mallaka da hadin farinjini
Akwai sirrin samun farinjini ga wadda ta rasa mijin aure ko wadda takeson samun farinjinin sana'a
Akwai hadin farinjini na matar aure
Akwai kwallin mallaka
Zoben mallaka
Set na Jigidar mallaka

*Yar uwa abubuwan fa da yawa sosai , Wanda in nace Zan tsaya bayyanasu anan wannan page din bazai

Please Login or Register in order to submit comment