Reading KARFE A WUTA Chapter 52 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ma'aruf Indabo"

Sumayya ta kalleta ta ce "Kamar yaya?"

"Kamar yadda na gaya miki, taimaka mini nake son ki yi, ki binciko mini duk wani labari da yakamata a kansa"

"Me ku ke so ku mayar da ni ne daga ke har shi?"

Nabila ta ce "Shi wa?"

Sai kuma sumayya ta farga da kato?arar da ta kusa tafkawa.

"Indabon yayi miki wani abu ne?"

Sumayya ta ce "No kar ki damu, haushi ki ka bani ne, kin ce Naja'atu Bunkure, kin ce Aminu Viper yanzu kuma kin ce Indabo, Nabila me ki ke son ki zama ne?"

Nabila ta tashi tsaye ta ce "Zan je wani wuri yanzu, Ina jiranki dan Allah sumayya, da tarihinsa da tarihin siyasarsa komai da komai da yakamata ina son sani a kansa"

Sumayya ta ce "Wai me zaki yi da shi to?"

"Amfani mai muhimmancin gaske, sai anjima, ki gaida umma zan zo har gida na gaisheta, kwana biyu ba mu gaisa ba. Ina jiranki dan Allah" ta ?auki jakarta ta yi waje.

Kamar ta tafi gida, sai ta fasa ta ?aukar mai napep, ta tafi police station ?in da aka ce mata dattijon nan yana tsare, da ta je ta tarar an canza masa wuri, an mayar da shi sashen kula da manyan laifuffuka.

ID card ?in ta kawai ta nuna, aka bata damar ganinsa, aka fito da shi, dattijo ne amma ba tsoho cancan ba.

Suka gaisa ta ce "Baba ni ce, wadda 'ya'yanka suka same ni, a kan maganarka, yaya meyafaru?".

Nan ya ba ta labarin duk abun da ya faru, ta ce "To baba yaya sunan shi ?an yayar matar?"

Yayi shiru ya ce "Wallahi ban sani ba, yana dai zuwa gidan da yake ban da?e da fara aiki a wurin ba"

Ta ce "Yanzu ina ne gidan da ka ke aikin, sannan ina yarinyar take, dole zan ganta "

Ya share hawayensa ya ce "Wallahi ban sani ba" Nabila ta tambayi 'yan sandan suka ce sai dai ta koma can in da aka fara binciken case ?in"

Ta ?auki bayanan da zata ?auka, ta yi musu sallama ta tafi.


***
Kasancewar Abdul da wuri ya fita, solomon ma baya nan, Ramma ta din ga yawo tana neman hanyar fita tana kuka, amma ta rasa, tayi-tayi ta samu hanya ta rasa, ?arshe ta koma falo ta zauna tana kallon Tv.

Wata magazine da tarin takardu ta gani, ta ?auka tana kallo, signing ?in sa mai kyau, Abdul yassar ma'aruf Indabo.

Shiru ta yi tana tunanin, kamar ta san sunan nan.

?ofar falon ya saka key ya bu?e ya shigo, yayi sallama ta amsa a hankali, sai dai yayi kissing ?in kumatunta sannan ya zauna, ta tsuke fuska tana matsawa.

Ya kuma matsawa kusa da ita ya ce "Kin ci abinci kuwa?" Ta yi masa shiru.

Ya ?ago mata jakar hannunsa ya ce "Yakamata ki san menene a jakar nan" ta?i kula shi.

Ya bu?e jakar, ya zazzage mata, kayanta ne a ciki, da kuma wasu sababbin kayan ya sayo mata.

"Babarki tana gaishe ki"

Ta kalleshi idonta fal hawaye ta ce "Me ka ke nufi?"

"Na ce ta sallama mini ke, ba sai ta cigaba da nemanki ba"

Ta sake kallonsa ta ce "Waye indabo?"


Ayshercool
08081012143
???500 ne via 0009450228
Aisha Adam jaiz bank sai shaidar biya ta 08081012143
Wanda za su jira document 1K ne.

90009343
'Yan Nijar ku turo katin airtel na 300fcfa

Arewabooks ayshercool7724




Queen collection, dealers of all kind of textiles, bedsheet, Adashi stock fish and others.
Follow this link to join my what's app group
https://chat.whatsapp.com/Hp4ZLNtrNXvJQkAV8UWZcv
Ya kalleta ya ce "Meye ala?arki da sunan? Kin san shi ne?" Ta girgiza masa kai alamar a'a.

"To a ina ki ka ga sunan?" Ta ?ago masa takardar ta ga signing ?in sa, da full name ?in sa.

Ya ce "Well babana ne, ba abun mamaki bane dan kin san shi, ?an siyasa ne"

Cikin rauni ta ce "Me ka ce wa mamana da ka je?"

"Ba na gaya miki ba, na ce kar ta sake nemanki, kin zama mallakina"

"Saboda ba ka da tausayi da imani ko? Wallahi idan ba?inciki ya kashe mahaifiyata ba zan yafe maka ba"

"Ikon Allah, me zai sa ba?in ciki ya kasheta, na kai mata kayan bu?ata a matsayin ina tare da 'yar ta. Ku ne haryanzu ku ke wannan kidahumancin, kun ?i ku waye, turawa duk in da mace ta kai 18yrs tana da ikon zuwa in da take so tayi rayuwa, amma ku da an yi magana sai ku ce aure aure, in anjima kuma ku yi ta surutun wahala ku ke sha a auren"

Ramma ta ce "Saboda yahudanci ko? Mu ai ba turawa bane, musulmai ne ba?ar fata, hausawa masu ri?o da addini da al'ada. Ni ban shekara sha takwas ?in ba, idan ma na yi ai sai da yadda ta da amincewa ta. Kawai saboda bamu da ku?i ka yi mini fya?e ka je har gidanmu gaban uwata ka ?aukko ni, ka rabani da ita, kuma ka koma ka kar?o kayana ka ce mata ta daina nemana kai ba aurena ka yi ba, kai ba wani abu ka yi da zaka taimaki rayuwata ba, ka ?auki hakkinmu ba ka yi mana adalci ba"

Ya ce "Ke kin isheni, sai ka ce ke ka?ai ce 'ya? Ni fa ban ta?a ?aukar wata mace na ajiye ina lalla?ata ba sai ke, kuma ma ku da ake haihuwar ku barkatai babu tsari, har wani damuwa za a shiga dan an ?auki ?aya? Kashe ki fa na yi niyyar yi na ?yale ki".

"Mu ba ai haife mu barkatai ba, mu uku ne, yayanmu ya rasu, ?anina ba shi da cikakkiyar lafiya, ni kuma ka ?auke mata ni, ban da dalilin maraici babu abun da zai saka ka ganni a birni aikatau, har ka keta mini haddi, bayan ka turo mana wata azzaluma, da fari ta ce zata taimaka mini, ta koma gaya mana yahudanci, ka ?auke ni a gaban uwata, ka zo ka mayar da ni karuwa ka yi wa kanka adalci dan Allah kuma nima ka yi mini?"

"Naja'atu Bunkure ba ?arya ta gaya miki ba, tun a lokacin da ba ku nuna taurin kai ba, da ba a zo nan ba, ku ku ka janyo koma menene ai"

Ramma ta ha?a hannayenta biyu, ta rufe fuskarta tana kuka ta ce "Ka cuce ni, ka lalata mini rayuwa, dama kasheni ka yi na huta, ka wula?anta rayuwata a matsayina na 'ya mace musulma da addinina ya suturta. Da ?anwarka ce ni ko 'yar ka, ba zaka zuba mini ido ka ce na je na yi tarayya da wani ba aure ba, kayi amfani da ku?i, ka wula?anta ni dan ni 'yar talaka ce ba ka kyautawa rayuwata ba" ga ta yarinya ?arama, sai iya tsara magana.

Abun da bai ta?a ji ba sai a wannan karon, kukan ramma a cikin zuciyarsa, maganganun ta suka tsaya a zuciyarsa, amma a zahiri ya nuna ko a jikinsa, ya tashi ya bar ta a falon ya tafi ?aki.

***

?an mama yana ta kaiwa yana komowa, tsakanin ?akin Viper da tsakar gida, yana jiran Walid ya fita, amma ya ?i fita ya zauna ba shi da niyyar fita.

Viper kuma sai bin ?an mama yake yi da ido.

Walid ya ce "Kai ?an mama, kamar ba ka da gaskiya"

?an mama ya ce "Haba Oga walid me ka gani?"

"Ba sai na gani ba, alamun hakan na gani, wallahi na ga abun da bai yi mini ba, sai ranka yayi mugun ?aci"

?an mama ya ce "Kar ka damu Oga walid, babu wani abu da zaka gani wanda zai ?ata maka rai"

Walid ya jinjina kai, ya cigaba da shan sigari.

Al'amin ya yin?ura ya tashi, Walid ma ya tashi ya ce "Ina zaka?"

Al'amin ?ura masa idanunsa da suka yi wani irin mugun jaa.

"Ba wai tuhumarka nake yi ba, ko wani abu ba, kawai dai ba na son ka yi wani abu da zai wargaza mana shiri ne"

"Iska zan je sha, ko yau ma yin?urin kashenin zaka yi?"

Walid ya girgiza kai ya ce "Last time ?in ma, ni ba niyyar kasheka na yi ba, ?o?arin hanaka abun da ka yi niyya na yi, a dawo lafiya" Al'amin ya nufi ?ofar fita, ?an mama ya ce "Oga Viper, bari na zo mu je na taka maka" Walid ya ri?e rigarsa, ya tsare shi da ido.

Ya sosa kai ya ce "Dama raka shi zan yi"

Al'amin bai waiwayo ba, kawai ya fita, Walid ya fara saka hannu a aljihun ?an mama yana caje shi, ?an mama ya ri?e hannunsa ya ce "Dan Allah ka yi ha?uri zan yi maka bayani".

"Sakar mini hannu, ko na kwa?a maka mari"

?an mama ya sakar masa hannu ya ce "Amma dai da ka tsaya na yi naka bayani"

Walid ya ciro ba?ar leda a aljihunsa, ya bu?e, ampoules ?in allura ne da sirinji, sai ba?in capsule.

Walid ya kalleshi, ?an mama ya ce "Wallahi cewa yayi sai na nemo masa su, idan ba haka ba, ba ya iya bacci, kansa zai fashe ni kuma sai ya bani tausayi, daga ?arshe kuma ya ce wallahi idan ban samo masa ba sai ya kashe ni"

"Sai ya kashe ka, kai ka ta?a ganin ya kashe wanin?" ?an mama ya girgiza kai.

"Wallahi idan ka kuma sayo wannan hard drugs ?in ka kawo masa, sai na saka maka ?arfe ka ji na rantse" ?an mama ya ce "To, amma dan Allah shi ma ka gaya masa, ka san idan na ce masa a'a ba zai yi mini da da?i ba".

Walid ya ce "Idan ya ce ka kawo masan, ka ce masa to, ka gaya mini" ya jinjina masa kai.

Viper yana zaune a kan dutsen, ya zubawa wuri ?aya ido, kansa kamar ya tarwatse haka yake ji, ga ?irjinsa kamar an ?ora masa dutse, da ?yar yake iya numfashi, ga jikinsa sam babu ?wari, banda kashe masa jiki babu abun da ?wayoyin nan suke yi, soyake yayi bacci mai sunan bacci, ko ya manta komai da yake cikin ?wa?walwarsa amma abu ya gagara.

"Madaki! Indabo!" Ya fa?a a hankali yana sunkuyar da kai, ya ?aga kai kamar a mafarki ya hangota, ta sauka daga adaidaita sahu, sai waige-waige take yi, yana saman dutsen sosai, dan haka yana hangota. Ta tsaya tana kallon hanya, in da yake take facing, amma ita ba ta ganinsa.

Dogon hijjabi ne a jikinta yau, a hankali take tafiya tana cigaba da waige-waige, mamaki ne ya kama shi, me kuma ya dawo da ita wurin nan yau? Zuciya ce ta tinziro shi, ya ji kamar ya sauka ya je ya na?a mata shegen duka. Mata halin su ?aya, cin amana 'yar madarar sa ce kawai ta fita daban sai umminsa, ta sace masa waya ta gudu, ta saka an kama liti, saboda tsagwaron rashin kunya ta sake dawowa, ko uban me ta dawo yi oho?.

Hakan ya ?ara tabattar masa he's not safe, za ta iya kawo jami'an tsaro su kama shi, sai dai kash, shi ba ya fargabar a kama shi, a kama shi ko a ?yale shi, shi ba wannan ne a gaban shi ba yanzu.

A yau ma ba ta iya gane hanya ba, bulayi take ta yi, tana nema, amma ta kasa ganewa.

Babu tsammani suka yi kici?is da ?an mama, ya kalleta ta kalle shi, ya ce "Ke! Me ki ke yi a nan wurin?"

Ta ce "Yauwwa, kai ne wanda na gani a gidan Viper ranar ko?"

"Ke, ki ka kuma kama sunansa, sai na ?ara wa ?ofar bakinki fa?i wallahi, kar ki sake ambatar sunansa ko ki kama sunansa".

Nabila ta ce "Tom, ba zan sake ba, dan Allah taimakona nake son ka yi, ganinsa nake son yi dan Allah"

?an mama ya ce "Ka ga wata mayyar kuma, baki ji kashedin da yayi miki ba kenan? Kin ?auka da wasa yake yi da ya ce "Ya sake ganinki zai kashe ki, kin san waye Viper kuwa?"

"Ba zai kashe ni ba, muhimmiyar magana nake son mu yi da shi, na san na yi muku laifi, ku yi ha?uri dan Allah, ka taimaka mini ka ha?ani da shi dan Allah"

?an mama yayi mata wani irin mugun kallo ya ce "Ya aka yi ki ka san ba zai kashe ki ba?"

"Viper ba ya kashe mutane, mussaman mata da ?anan yara, dan Allah ka ha?a ni da shi na kasa gane gidan".

"Ke bar nan wurin, na ha?aku ki saka a kama shi ko, to ta Allah ba taki ba, wuce ki bar wurin nan"

Ta sake marairaicewa za ta yi magana.

Ya zaro wu?a ya ce "Idan shi ba ya kisa ni ina yi, ware ko na zaro hanjinki yanzun nan" wu?ar sai ?yalli take yi, ya fara tunkarota, yana wulwula wu?ar, ba shiri ta juya, gwiwa a sanyaye ta bar wurin.

Har ta mi?e ta ?acewa ganin Al'amin yana hangota, ya mi?e ya kwanta a kan dutsen, ya lumshe idanunsa rana tana dukansa, yana jin yadda zafin ranar ke ratsa shi, yana ?ara masa ciwon kai, amma ba shi da niyyar tashi.

***
"P.A"

"Na'am honorable"

"Ka tabattar binciken da ka yi a kan yarinyar nan daidai ne, babu kuskure a cikin sa?".

P.A ya jinjina kai ya ce "Babu fa, ka san ba na yadda a samu kuskure a irin wannan lamarin, mussaman a irin wannan ?adamin, ba a samu kuskure ba, yadda na gaya maka hakan ne"

Ya jinjina kai ya ce "Shikenan, ina ita ?awar ta ta, ana cigaba da bibiyarta?"

"Eh, a wurinta muka samu wasu abubuwan ma"

Indabo ya ce "Haryanzu ina mamakin yadda aka yi ta ce ayi mata bincike a kaina ne, shiyasa nake ta tantama anya ka yi binciken a kanta dai-dai?"

P.A ya ce "Haba honorable, ya ma za ayi wannan ?aramar alhakin ta yi wani bincike a kanka, wata?ila hakan yana da ala?a da harkar siyasa ne kawai, ko kuma sakata aka yi".

"Ba ita ce a gabana ba, Viper mai zamani, shi ne babbar barazanata, shi ne damuwata, ku cigaba da aikinku kawai, duk abun da ake ciki, ka din ga sanar da ni "

P.A ya ce "In sha Allah, ai yaronsa ?aya yana hannu, sai dai na bincika an ce Haryanzu bai yi magana ya fa?i in da yake ba"

Indabo ya ce "?yale 'yan sandan nan, sonake na riga su samunsa, idan na riga su kawai kashe shi za ayi salin alin, duk madaki ne yayi mini shirme wallahi, amma yanzun ma komai zai daidaita"

"Kar ka damu honorable, ai kai maganin kowane shege ne a ?asar nan, ba ma ?an daba ba, zamu yi maganinsa, amma da alama kamar kana da maguatan ?oye, da suke tallafa masa"

"Na sani, amma yanzu duk ba wannan ba, a cigaba da abun da yakamata"

P.A ya ce "To shikenan, na barka lafiya "

Bayan fitarsa Indabo ya shiga cikin gidansa, ya tarar da Abdul a falo, tare da mahaifiyarsa.

Ya kalli indabo ya ce "Welcome"

"Thank you" ya zauna ya kalli Abdul ya ce "Dama nemanka nake yi".

Abdul ya ce "To gani"

"Ya maganarmu ta rannan?"

"Daddy maganganun namu ai da yawa, wacce daga ciki?".

"A'a, ka san wanda suka fi muhimmanci ai, mun daddale da jam'iyya, kai za a tsayar mataimakin gwamna, tun yanzu yakamata ka fara harkar campaign, da buga pastoci. Amma ka san dole ka daina duk wani shashanci da kake aikatawa. Sannan maganar da nake yi, maganar aure, shekara talatin da biyar, uban me ka ke jira? Muddin lokaci ya cigaba da gabatowa, abokan adawa suka san baka da aure, sai ku samu matsala a harkar takarar nan, amma da na yi maganar auren sai ka din ga gocewa"

Ya ?an tsuke fuska ya ce "Wai constitution ne ya ce dole sai mutum yayi aure zai yi shugabanci meye amfanin auren mutum a cikin siyasa to?"

Indabo ya ce "Ban sani ba, idan ba zaka yi ba, ni ina da wadda zan ha?aka aure da ita, ga 'ya'yan abokai da yan uwa nan sai dai ka ji an yi".

Hajiya Bilki da tun ?azu ba ta yi magana ba sai yanzu ta ce "Haba distinguish, ka bi shi a hankali mana, zai yi, ba sai an yi masa dole ba".

"Ba zan bishi a hankalin ba, na gaji da wannan shirmen nasa, rayuwarku nake ?o?arin ingantawa, wata?ila idan ya zama mataimakin gwamna, shi ya fi ni samun dama, ya ku?utar da ?an uwansa".

Hajiya Bilki ta ce "Distinguish, kai da ka fishi da?ewa a harkar, ba ka samu yin hakan ba sai shi, ni na karaya da lamarin jafar"

"No, kar ki yi mamaki ya fi ni samun authority, da damar fitar da shi, da dai a nan Nigeria ne, da tuni an da?e da wuce wurin"

Ta ce "Haka ne, Abdul dole ka yi ha?uri ayi maganar auren nan, tun yanzu za a fara share fagen samun damar yin nasarar ka, dan idan ku ka gama tenure ku, kai zaka yi gwaman nan gaba"

Cikin sangarta ya ce "Mummy ba ?i na yi ba, auren ne ba na so"

"Aikuwa haka zaka yi ha?uri" suka cigaba da tattaunawa a kan yadda tsare-tsaren za su kasance.

***
DSP Nasir na tsaka da aiki, aka sanar da shi yayi ba?uwa, ya ce ace ta shiga, tana shiga ya ga Nabila.

Yayi murmushi ya ce "Ke ce ba?uwar dama?".

"Eh mana, ko na koma ba ka san ganina?"

"A'a ni na isa na na ce haka. Zauna bari na kawo miki lemo, daga wurin aiki ko daga ina?"

Nabila ta kashingi?a ta ce "Na je wani trial ne"

Ya ?aukko mata ruwa a fridge ya ce "Sannu"

Ta ce "Yauwwa" ta kar?i ruwan ta sha, ya ce "Amma kin bawa kanki wahala da yawa, wace court ?in ki ka je, har ki ka iya biyowa nan?"

Ta ajiye robar ruwan ta ce "Wani wuri na je, na ga wani client, DSP"

"Na'am barrister Nabila maitama "

Tayi murmushi ta ce "Wai ina mutumin nan?"

Ya ce "Wanne?"

"Wanda ku ka kama, haryanzu bai fa?i in da Vipern yake ba?"

"Ina fa zai fa?a, yana ta wahalar da mu".

"Dan Allah ka nuna mini shi"

"Ki yi masa me?"

"Babu komai, ganinsa kawai zan yi"

Nasir ya ce "To bari na gama aikina, sai mu je ki ganshi"

Nabila ta zauna ta jira Nasir ya gama abun da yake yi, ta ?auki jarkar ruwanta suka fito, yana ta nuna wa abokan aikinsa ita, yana gaya musu ita yana gaya musu ?anwarsa ce, lawyer ce. Suka gaggaisa da abokan aikinsa, sannan suka ?arasa in da liti yake.

La?ensa duk ya bushe, saboda yunwa da ?ishirwa, yana ganin Nabila ya ganeta ya ?ura mata ido, ta kawar da kanta ta ce "DSP tun da ya ce bai san in da yake ba, haka zaku cigaba da ajiye shi?"

"Eh har sai ya yi magana tukuna"

Ta girgiza kai ta ce "Amma a doka, ai kotu za a kaishi ko a sake shi, ina ga fa tun da ya ce bai sani ba, bai sani ?in ba"

Nasir ya ce "Ya sani ba zai yi magana ba ne" ta mi?a wa liti ruwan hannunta, ta ce "Ga ruwa" banza yayi mata, Nasir ya juya ya fita yana amsa waya daga wurin ogansa.

Tayi ?asa da murya ta ce "Na san na yi muku laifi, amma dan Allah ka yi ha?uri, zan san yadda zan yi ka bar wurin nan".

Ta ciro wani ruwan a jakarta ta bashi, ta ce "Dan Allah ka yi ha?uri, na fahimci kuskuren da na yi, ban kyauta ba amma zan gyara komai"

Nasir ya dawo ya ce "Mu tafi?"

"Eh, amma gaskiya, yakamata a san abun yi, kar a taka doka da yawa"

Ya ce "To masu doka, mu je gida"

"Da gaske fa nake, ko mu shigar da hukumarku ?ara".

Ya mayar da abun wasa, suka tafi gida.


***
?arfe hu?u na yamma, Nabila ta shirya ta fita, ta tafi gidan matar da aka ce an yi laifin fya?en nan a gidanta.

Ganin Nabila cikin shiga mai kyau, ya sanya masu gadin ba su tsaya tuhumar wacece ba, suka bata damar shiga gidan.

Sai da haushi ya fara kamata, saboda jiran da aka bar ta tana yi, daga baya matar gidan ta fito, suka gaisa da Nabila.

Nabila ta ce "Na san baki sanni ba, sunana barrister Nabila Yusuf maitama, lawyer ce ni mai zaman kaina. Akwai mai gadin gidan nan malam isyaku, da ake accusing da laifin fya?e, ni ce lawyer sa. Na zo ne dan Allah in ji details ?in abun da ya faru".

Matar ta tsuke fuska ta ce "Ke, ni ki ka zo ki yi wa wannan tambayar? Wurin 'yan sandan na je na fara kar?ar report, an ce na dawo station ?in da aka fara case ?in, amma na ga dacewar fara zuwa gidan nan, tun da an ce yarinyar 'yar aikinki ce, kuma ainihin wanda ya yi laifin kina da ala?a da shi, ku ka yi framing ?in sa aka ce shi ne. Yanzu duk ba wannan ba a matsayinki na uwa kuma 'ya mace nake so mu fara magana. Ina yarinyar take? Ina ne gidan iyayenta? Ban damu da sanin koma waye yayi laifin ba, fatana kawai a wanke mai gadi, tun da kun san wanda yayi laifin "

Matar ta mi?e ta ce "Ki koma wurin jami'an tsaro, su zaki yi wa wannan tambayar, kuma ba ki da wata hujja, da take tabattar da ba shi yayi ba, idan kin gama kina iya tafiya"

Nabila ta mi?e tsaye ta yi murmushi ta ce "Na gode sosai antyna da bani lokacinki" ta juya ta fice.

Station ta sake nufa, wanda a nan aka fara case ?in, aka nemo statement ?in da aka rubuta, da sunan Asibitin da aka kai ramma, na cikin gari, tana tsaka da dubawa, wanda yake evening duty, shugaba a wurin, ya fito afujajan, ya ?wace file ?in wai ba a ba su damar su bata file ?in tayi bincike ba.

Cikin mamaki da takaici Nabila ta ce "Waye zai bayar da damar, bayan wadda ?asa ta bayar, lawyer ce fa ni, dan me za a hana ni damar dubawa, doka ta bani damar neman hujjojin da zan gabatarwa kotu, na wanda zan kare, yaya za ayi a hana ni"

Fafur suka hanata, suka ce ta tafi, ta kira Nasir a waya, amma wayarsa ta ?i shiga, ranta yayi mummunan ?aci.

A gajiye ta koma gida, ana ta kiraye-kirayen sallar magariba, ta yi wanka tayi salla, ta ?aukko wayarta ta kira sumayya.

"Ke ya ki ke aikin?"

"Sumy raina a ?ace yake, kin san menene?" Sumayya ta yi sauri ta katse wayarta, ta saka a Flight mode, ta ?auki wayar ummanta, ta kira Nabila ta ce "Sorry wayar ce caji ya ?are"

Nan ta labartawa Sumayya abun da yake faruwa.

Sumayya ta ce "In dai ?asar nan ce, ai ka?an ki ka gani d.....

Cikin sauri Nabila ta katseta ta ce "Sumayya few months back, ina wannan case ?in da yaya murtala ya saka, har aka kusa korarsa? The case are similar".

Sumayya ta ce "How?"

"In so many ways, dan Allah ki sake binciko mini labarin, ko ma ki ha?ani da yaya murtalan, ke zan ma zo na same shi, the same yadda matar ta ce an yi wa yarinyar fya?e, ?an yayan matar gidan, shi ma dattijon nan haka ya ce mini, ?an yar matar gidan ne yayi abun ba shi ba ne ba, shi asibiti kawai suka kaita, da shi da ?aya mai aikin da wani mai yi musu hidima a gidan, definitely duk case ?in ne but i want to confirm"

Sumayya ta numfasa ta ce "Ban ?i ta taki ba, amma ki bi a hankali, kin ga a kan case ?in, sai da Murtala ya kusa rasa aikinsa, ke daga ji kin san case ?in babba ne"

"Sumayya tsoron da muke ji, da ja da baya shi ke saka wasu ma suke Fuskantar irin matsalolin, idan na gama bincike na, i will raise the case, hatta 'yan sandan nan da abun da suka yi mini, duk sai na ya?a, just support me sumy, Allah zai taimekemu, ke 'yar jarida ce, zaki iya kema".

Sumayya ta ce "Haka ne, amma kar ki kira ni a wayata, zan ki ra ki da wani layin, sai mu ha?u da yaya murtalan" ta yi wa sumayya godiya, tana sake bawa kanta ?warin gwiwar lallai za ta tsaya wa wannan dattijon kuma za ta yi nasara.

***
Abdul ne yake kallon ramma, yadda duk take a takure, tana kallon tv, amma hankalinta ba a kan tv yake ba.

"Rahama"

"Na'am" ta amsa tana kallonsa.

"Meyake damunki ne?" Tayi shiru ta sunkuyar da kai.

Ya kwanta a kan cinyarta, ya ?ora ?afarsa ?aya kan ?aya yana danna remote.

Ya tashi ya ce canzo hijjabinki ki zo, ta yin?ura jikinta na rawa, ta sako hijjabi, ta fito.

Ta tarar da shi a tsaye da mukulli a hannunsa yana waya.

Ta ?araso jikinta yana tsuma, tunaninta ko gida zai mayar da ita, ya ri?e hannunta,

Please Login or Register in order to submit comment