Reading KARFE A WUTA Chapter 53 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya bu?e ?ofar falon suka fito.

Da kansa ya sakata a mota, ya rufe sannan ya zagaya ya kunna motar ya fita da ita.

Sai kallon gari take yi, duk da dare ne ko ina da hasken fitila, tun da ya kawota a sume, ba ta sake fita ba, kuma ba ta san a ina take ba.

"Gida zaka mayar da ni?"

Ba tare da ya kalleta ba ya ce "Ai na ce ki daina wannan tunanin ma"

Cinema ya kaita, wai kallon film, bayan tv suka baro a gida, ta din ga waige-waigen yadda za ta yi ta gudu, amma a in da suke zaune, yana rungume da ita, ga wurin duk ?abilu ne, abun da ta fuskanta, ba iya cinema ne wurin ba, dan daga can wani wuri, ka?e-ka?e na tashi.

"Naga ki na ta waige-waige, ba mahaukaci bane ni, da zan kawo ki inda zaki iya guduwa, ko ki yi wa wani magana ba, kowa sabgar gabansa kawai yake yi a wurin nan, gara ma ki nutsu"

Tayi ajiyar zuciya ta ce "Ko bangon duniya zaka kai ni, idan Allah ya yi niyyar fitar da ni ba ka da dabara".

Yayi murmushi kawai, sai da ya gama abun da yake yi, ya ?auke ta, suka tafi ya kulleta a mota, ya sayo mata abinci, ya mayar da ita in da suke.

***

Nabila kuwa tana ta bin kwatancen da dattijon nan yayi mata, na gidan zulai ?aya mai aikin da suke aiki tare da ramma, amma ta kasa gane kwatancen, ganin ta gaji, kuma ta hanyar ake bi, a je in da Viper yake, ya sanya ta tare abun hawa, ta sake tafiya.

A wannan karon da ta sauka, google map ?in ta bu?e, tana duba abubuwan da suke wurin, ba tare da gazawa ba, ta cigaba da yawon bulayin neman gidan, cikin sa'a bayan shafe mintuna talatin tana bulayi, ta hango gidan.

Wata irin ajiyar zuciya ta yi, sannan ta nufi gidan.

?ofar gidan a rufe, ta saka hannu ta tura ?ofar, tayi sallama.

?ofar ta bu?e, sai dai ba ta ji motsi ko alamar mutum a gidan ba.

Duk da gabanta fa?uwa yake yi, amma haka ta ke ta addu'a ta shiga. Tsakar gidan ko ina shirgi, can bokiti, ga tukunya can kaya sauran sigari tsakar gidan kaca-kaca.

Ta ?arasa ta le?a ?akin, ta hango Viper dur?ushe a kan gwiwarsa, yana ?o?arin yi wa kansa allura, sai dai hannunsa sai rawa yake yi, gashi ya huda jijiyar, jini ya fara zuba.

Da sauri ta ?arasa, ta dur?usa, ta gyara masa sirinjin, ta cigaba da zuba masa ruwan allurar.

Rintse idanunsa yayi, jin yadda allurar take ratsa jikinsa.

Babu tsammani, ta zare sirinjin ta ce "Wannan abun da ka ke yi, zai iya shafar ?wa?walwarka fa" ba ta gama maganar ba, ta ji ya fa?o a jikinta, ta fa?i a wurin saboda nauyinsa, ?o?arin ture shi take yi, dan ji ta yi tamkar wani ?aton dutse ne ya fa?o mata.

Ya ?ago idanunsa ya kalleta, ya saka hannu ya sha?e wuyanta.

Numfashinta ya fara fita sama-sama, ta rirri?e hannunsa idanunta suka yo waje.

Walid ne ya fa?o ?akin da gudu, ya fara ?o?arin janye Viper daga kanta.

A tunaninsa jikin Viper yayi sakin da zai ture shi kawai, amma ya ji da ?warinsa.

A wahale ta ce "Zaka kashe ni fa" a hankali ya saki wuyanta, Walid ya ?ago shi da ?yar, ya kalli walid, ya kalleta ya sake mayar da idonsa kan Walid da ?arfin gaske ya ce "Walid"

"Na'am Al'amin"

"Walid matata, matata walid! ?a na Walid mata ta" yayi maganar yana wani irin ?araji, tare da jan rigar walid da ?arfin da sai da ta yage.

"Easy maza, easy yi ha?uri"

"Walid zan haukace, walid kaina zai tarwatse, me zan yi ne wai, ka fitar mini da yarinyar nan, ba na son ganinta matata walid" yayi maganar yana girgiza kansa.

Nabila ta tashi da kyar, tana ta haki, ta ce "Zaunar da shi zan yi masa magana dan Allah"

Walid ya ce "?auki jakarki ki tafi, yi sauri"

Kawai Viper ya shammaci Walid, ya buga kansa da ?arfi a jikin bango, take jini ya fara biyo hancinsa, ya fa?i ya suma a wurin.

Nabila ta ?wala ihu, saboda sautin da kansa ya bayar, da ya buga kan, Walid ma a rikice ya ?ago shi, amma ko motsi baya yi.

Ayshercool.
08081012143
???500 ne via 0009450228
Aisha Adam jaiz bank sai shaidar biya ta 08081012143
Wanda za su jira document 1K ne.

90009343
'Yan Nijar ku turo katin airtel na 300fcfa

Arewabooks ayshercool7724



Cikin matsanancin tashin hankali Nabila ta nufe su, Walid ya rikice, ya rasa me ma yakamata ya yi ya taimakawa Viper.

Cikin azama Nabila, ta ?aga kan Viper yana kallon sama, ta ciro hular kanta, ta toshe hancinsa da yake zubar da jini, ya zamana ta gefen bakinsa yake numfashi.
Cikin kuka ta kalli walid ta ce "A kai shi asibiti mana, ya bugu da yawa, tun da abun ya kai ga zubar da jini ta hancinsa"

Walid ya ce "Ba za a kai shin ba, uban waye ya ce ki kuma zuwa ai duk ke ki ka ja?"
Cikin rashin fahimta ta ce "Ni kuma? Ni me na yi? Zuwa na yi na bashi ha?uri a kan abun da na yi bisa kuskure, wallahi ban yi masa komai ba, tarar da shi na yi yana yi wa kansa allura jikinsa yana rawa, na kar?a amma wallahi ban yi masa komai ba. Ko duk haushin abun da na yi wa ?an uwanku ne? Na je station ?in ai, kuma na yi magana da shi, dan Allah ku yi ha?uri rashin sani ne ya sanya na aikata abun da na yi masa, abun da ake fa?a a gari a kansa daban, ni kuma ban san gaibu ba, amma dan Allah ku yi ha?uri" tayi maganar hawaye wani na bin wani a fuskarta.

Walid ya ce "ya isa haka, tashi ki tafi"
"A haka za a bar shi, ba zaka kai shi asibiti ba?"

"Ta yaya zamu kaishi asibiti ana nemansa a kama shi?"

Fizge-fizge Viper ya fara yi, yana ?o?arin tashi, Walid ya daddane shi, cikin ?aga murya ya ce "Walid"

Ya ce "Na'am Al'amin"

"Liti" walid ya ce "Ya shiga ban?aki".

Viper ya sake cewa "Mai laya"

"Na kiyayi mai zamani, Allah ya ?ara maka lafiya"

"Gobe zamu je asibiti da ?anwarka 'yar madara, sun ce inducing za su yi mata 'yar madara za ta haihu, ragonta yana ?auye wurin Hajiya"

Walid ya ce "Masha Allah, Allah raba su lafiya"

"Walid"

"Na'am mai zamani"

"Cikin nan yana ba ta wahala, nima na ?agu ta haihu, na ga yarona, sunan ?anina nura zan mayar, idan ta kuma haihuwa na saka sunan Sadik".

Walid ya ce "To Allah ya kawo mana su lafiya da albarka"

Wani irin ihu ya hau yi, yana ?o?arin ture Walid, cikin ?araji ya ce "Walid matata ?a na, ba zan iya komai ba, ka ri?e madaki, kar ya illata mini mata, ka ri?e shi walid wai me ka ke yi ne?"

Sosai suke kokowa da Walid, ga hancinsa na cigaba da zubar da jini, ga damuwa da fita hayyaci a dalilin allurar nan.

Walid ya ce "Sai na ci uban ?an mama idan ya dawo, bai ji me na gaya masa a kan kawo maka kayan maye ba, sai ya saka mun yi babu ka rasa ?wa?walwarka tukuna".

Nabila kuwa iya ?arfinta take kuka, tsananin tausayinsa ya mamaye zuciyarta, da ?yar walid ya danne shi, a hankali jikinsa ya saki, ya daina motsi, amma yana motsa idanunsa, a buge yake ya fita hayyacinsa amma ba bacci yake yi ba, abubuwan da suka wuce ne suke dawo masa cikin mayen.

Nabila ta ce "Dan girman Allah ka gaya mini ?arashen labarin nan, ina jauhar ina abun da yake cikinta?".

Walid ya ce "Kin ga ni ba wannan ne a gabana ba, lafiyar ?an uwana da taya shi ?aukar fansa ita na saka a gaba, dan haka ki tashi ki tafi kawai"
Nabila ba ta sake magana ba, ta tashi jiki a sanyaye, ta ?auki jakarta, har ta kai bakin ?ofa, ta waiwayo ta sake kallonsa, hakan yayi dai-dai da bu?e idanunsa, sun yi jawur gwanin ban tsoro, ya tsura mata ido, a hankali ta juya ta fice.

Cikin maye ya ce "Mai laya"

"Allah ya taimaki mai zamani"

"Ba na son ganin yarinyar nan, zan iya fara kisan kai a kanta".

Walid ya girgiza kai ya ce "Ba ka ta?a yi ba, kuma ba zaka fara a kanta ba" surutan da Viper ya cigaba da yi ne, ya tabattar wa da Walid ba ya cikin hayyacinsa.

***
Ramma ta na zaune, ta na cin farcenta, tana zancen zuci, ta ji Abdul ya kama hannunta.
Sai da ta firgita, kasancewar tayi zurfi a zancen zuci.

Hannunsa ri?e da nail cutter, ya fara cire mata faratan ya ce "?azama kawai, da baki ki ke cin farce" janye hannunta ta yi ta ce "Ni kar ka shafa mini cuta" tayi maganar tana ha?e rai.

"To cuta ta nawa kuma, in dai ina da ita da tuni kin ?auka ta can wurin. Duk rashin ji na, ina using protection, a kanki ne kawai nake gaba ga?i, shi ma dan na san am safe na killace ki" tsaki ta yi ta kawar da kanta gefe.

Ya kama hannunta, ya cigaba da yanke mata farcen ta ce "A banza, wallhi ko ha?iyeni zaka yi, ka fito da ni, ba zan yafe maka zaluncin da ka yi mini ba"

Bai kalleta ba ya ce "Dama ban ce ki yafe mini ba ai" ya na cikin yanke mata, ta ga yana ?an yamutsa fuska, ya gama ya tashi ya koma ?aki, ta kalli falon komai tsaf solomon yake gyarawa, a ranta ta ce "Dama aure ne da ni, ace nan gidana ne ba wannan ?azantar ba. Tunanin hakan kawai ya saka idanunta cika da hawaye.

Ta ?aukko magazines ?in da ke falon, tana ta kalla, har ta manta da shi a gidan, ta shiga bedroom ?in, ta tarar shi a kan gado yana mur?ususu.

Ta kalleshi ta ce "Menene?"

A wahale ya ce "Kira mini solomon" ta juya ta fita, ta kiro shi.

Ya ?aga kai ya ce masa ya kawo masa biro da takarda.

Ya kawo masa, yayi rubutu a jiki, ya ce yaje ya sayo masa.

Solomon ya fita cikin sauri, ta kalleshi ta ce "Wai menene?"

Ya ce "Epigastric pain ne"

"Me kenan" ya nuna mata cikin sa.

Ramma ta ce "Sannu Allah ya sa mutuwa zaka yi na huta"

Yayi mata shiru, ya cigaba da juyi, ya dun?ule hannunsa yana dukan gadon a hankali, yana yi yana mi?a alamar yana jin jiki sosai.

Ta tsaya tana kallonsa, gumin da yake yi, ya sake tabattar mata ya fara galabaita.

Yayi mata nuni da hannunsa ta je, ta ce "In zo in yi maka me?"

Girgiza kai ya hau yi, yana kiran "Mummy, rahama cikina am in pain"

"To sannu"

Ta samo jarka da ruwa, ta tofa masa bisimillah ?afa 19, da suratul fatiha ?afa 7, ta hau kan gadon ta ce "To tashi ka sha ruwa" ya tashi da ?yar ya kar?a, ya shanye, yayi jifa da jarkar, ya kwanta a kan cinyarta ya ce "Rahama cikina"

"Allah ne yayi maganinka, a cikin sakans idan ya ga dama, zai rabaka da rayuwarka, ka ga idan mutuwa zaka yi, ga sa?o kana yi, ga zaluncin da ka yi mini, Allah ya sa ka mutu".

Abdul ya ce "Da na mutu shahidi, ciwon ciki ne ya kashe ni, kuma ?arshe ace ke ki ka kashe ni".

"Ko shahidi ka mutu kan ka shiga aljanna, sai ka shiga .... Sai kuma ta yi shiru. "Allah dai sai ya ?watar mini hakkina a wurinka na zalunta ta da ka yi"

Solomon yayi knocking, Abdul ya ce ya shigo, ya shigo da leda a hannunsa, Abdul ya kar?a, ya sakawa kansa butterfly needle, ya saka ramma ta ha?a allurar da aka kawo, ya ce tai masa.
"Ni ba zan iya ba, tsoro nake ji"

"Tsoron me malama, ciwo zai kashe ni"

"To ni ta?a yi na yi?"

Cikin tsawa ya ce sai ta yi, hannunta na rawa, ta zuba allurar a cikin butterfly needle ?in.

A haka ya nuna mata yadda za ta sa?ala masa ruwa, yana yi suna fa?a, ta saka masa ya sa hannu ?aya ya janyota, ya sake kwanciya a kan cinyarta.

Yadda yake wash wash da kiran sunanta, sai ya ?ular da ita kamar ba namiji ba.

"Ni ka daina kiran sunana tun da ba ni na ?ora maka ba"

"Wash rahama cikina" tsaki ta yi ta ce "Wai shekarunka nawa?"

"36yrs" yayi maganar yana kallonta.

"Amma an yi asarar ?uruciya, idan ba ka yi wasa ba kana cikin wanda annabi ya ce kun yi asara, ka tafiyar da ?uruciyarka a shirme da shashanci, a mintuna ashirin ?in nan da Allah ya ga dama, da yanzu babu kai, me zaka ce wa Allah, ka sha giya ka kwana kana zina da 'yar da ka raba da uwatta, ka canza tunani da halaye, ko Allah ya yi maka rahama".

Ya lumshe idanunsa ya yi shiru, bai ce mata komai ba.

***
Nabila kanta tamkar zai tarwatse ita ma haka take ji, so take ta kamo bakin zaren tallafawa Viper. Babban abun da yake bu?ata yanzu rehabilitation ne, a fara nesanta shi da shaye-shaye, sannan a kwantar masa da hankali da ?o?arin tirsasa masa kar?ar ?addararsa ta hanyar da ya dace. Sannan a fuskanci kamo zaren tsaya masa, ya ?auki fansar abun da aka yi masa ta hanyar doka, ba ta hanyar da yake tunanin ?auka ba, sai dai alamu sun nuna mata ba zai sarrafu cikin sau?i ba, balle a samu fahimtar juna da shi, sai dai ta ?udurce a ranta, duk tsanani da wahalar lamarin, za ta tsaya a kan sa, ko da kuwa sanya rayuwarta cikin hatsari ne, za ta yi domin taimakon Viper.

Sai dai hakan ba zata yiwu ba, sai ta ji ?arshen labarinsa, amma ta yaya?. Da ta tuna yadda yake kururwa yana kiran matarsa, ?ansa sai ta ji ta karaya, tausayinsa ya ?ara kamata.

Ringing ?in wayarta ne ya katseta daga tunanin da take yi, ta ga lambar sumayya, ta ?auki wayar ta kara a kunnenta.

Sumayya ta ce "Na yi wa Uncle murtala kwatancen gidanku, zai zo ya same ki, sai ku yi magana".

Nabila ta ce "Kai sumy, ban da ni ki bari na je na same shi, ni da nake nema?"

Sumayya ta ce "Ya zo ya same ki is more safe, ba wanda zai kawo wani abu, kin san yanzu rayuwa babu tabbas mussman irin aikinmu".

Nabila ta yi murmushi ta ce "Hakane masoyiyya, na gode sosai, saura ?aya aikin"

"Wanne kenan?"

"Waye indabo?"

"Kin ga ki raba kanki da indabon nan, wai me ki ke nema a kansa ne? Ba dai kin yi masa wula?anci kin ?i gaishe shi ba, menene na bibiyarsa"

Nabila ta yi murmushi ta ce "Ba zaki gane ba, ki taimaka kawai"

"Nabila kamar kina ?oye mini wani abu fa".

"Ba abun da nake ?oye miki, mamakinki kawai nake yi, duk kin canza kina abu kamar mara gaskiya kwanan nan sumayya"

Dummm gaban Sumayya ya fa?i ta ce "Ban gane ba"

Nabila ta yi dariya ta ce "Kar ki manta fa ni lawyer ce, idan na so zan gane idan ma baki da gaskiya, don't mind me kawai dai na ga kina ?o?arin kawar da maganar indabon nan ne, shiyasa nake tsokanarki, am about to do something big, zan gaya miki menene daga baya"

"Nabila Please, kar ki je ki yi abun da ba shikenan ba, ki raba kanki da duk wani abu da zai sake ha?a ki da Aminu Vipern nan, kar ma a cetare ku ke. Ki bar DSP yayi aikinsa dan Allah"

"Ni ba maganar Viper nake yi miki ba, case ?in dattijon nan nake magana a kai, amma ki binciko mini maganar indabon nan, ko na binciko da kaina".

Sumayya ta ce "To shikenan na ji zan yi, amma ki san in da zaki din ga zuwa da abun da zaki din ga yi kin ji arfan Abba"

Nabila ta yi murmushi ta ce "Ji sai ka ce wata uwata, to na ji sai anjima" ta kashe wayar tana murmushi, a duniya bayan Abba ba ta tunanin akwai wanda ya kai Sumayya damuwa da ita, da tsoron ta aikata wani abu, da zai janyo mata matsala.

Bayan sallar magariba, Murtala ya kirata a waya, ya sanar mata da ya zo, yana ?ofar gidan su.

Ta saka hijjabi ta fita, suka gaisa ya ce "Sumayya ta ce "Ki na nemana"

"Au ba ta yi maka bayani ba?"

Murtala ya ce "Tayi mini, daga bakinki nake son ji".

"Haka ne, ka ga wani case na samu, na wani dattijo, an yi framing ?in sa, wai yayi wa wata yarinya 'yar aikin da yake gadi fya?e, na je na yi magana da shi, yayi mini bayani, ya ce ba shi bane ba, ?an yayan matar gidan ne, so abubuwa da yawa are similar to rahoton da ka bayar kwanakin baya, shiyasa na ce bari na neme ka, ka ?ara yi mini bayanin yadda abun yake".

Murtala ya numfasa ya ce "Kin san duk abun da aka ce, harka ta manya ce, sai dai a lalla?a a yi komai a ?oye ko ba haka ba, an ce yaron nan ?an manya ne, kar mu je ki yi wani abun da zaki sakamu a matsala fa"

Nabila ta ce "Uncle murtala, ba zan saka kowa a matsala ba, dattijon nan nake son na taimakawa, kunna mini recording ?in matar, na sake ji".

Ya kunna mata recording, ta saurara tiryan-tiryan, Nabila ta ce "Uncle murtala, case ?in dai ai wannan, ba shi ne aka ce Naja'atu Bunkure ta shiga case ?in ba, ai da na ce zan shiga case ?in yarinyar".

Ya ce "Shikenan, fa?uwa ta zo dai-dai da zama, amma dan zatin Allah don't mention my name".

Ta jinjina kai ta ce "Kar ka damu in sha Allah ba zan yi mentioning ?in ka ba. Naja'atu Bunkure ko da me take yawo a kanta, sai ta gaya mini in da case ?in ya tsaya, ka san ina station ?in da aka fara case ?in, aka ?wace file ?in daga hannuna, wai ba zan duba ba".

Haske su aka yi da fitilar mota, Nabila ta tura baki, tana kare fuskarta, Nasir ya gyara parking ?in sa, ya fito ya nufo su.

Ta ce "Yaya sannu da zuwa" bai amsa mata ba, ya kalli murtala ya ce "Malam ya dai, ya aka yi?"

"Yaya idan saurayina ne, haka zaka yarfa ni dan Allah? Abokin aikin sumayya ne, muna tattaunawa ne a kan wani case".

Nasir ya sake tsuke fuska ya ce "Kuma da daddaren nan?"

"Eh, saboda shi ?oyayyiyar shaida ne, da ba zan bayyana shi ba, ba na kuma son a samu trace, na wani ya ganshi, shikenan uncle murtala ka gaida gida"

Yayi wa Nabila sallama ya tafi.

Ta cigaba da yi wa Nasir mita, "Gaskiya yaya na fuskanci saboda kai wasu samarin namu suke tafiya, da haka za a aure mu, kana zare musu ido, kamar wasu 'yan ta'adda".

"Eh, gara a zare musu idon, su san nan ba wurin da za su zo su kawo wargi bane ba" kawar da zancen ta yi, ta hanyar bashi labarin case ?in dattijon nan, da yadda aka ?wace file ?in.

Sosai ya din ga mita, har yayi alwashin rakata sake komawa station ?in, a bashi tun da tana lawyer, dole a bata dukkan ha?in kan da take bu?ata.

Bayan ta koma ?akinta, ta din ga murmushi itaka?ai, abu zai case zai ha?a ta da Naja'atu Bunkure, "Sai na ga abun da ya ture wa buzu na?i kuwa" sai dai walwalarta ta ?auke, bayan tuno wa da Viper, kar ta shagala da ramuwar gayya a kan Bunkure ta sakankance ta gaza samo mafita a kan nasa case ?in.

Tana bu?atar wanda zata tattauna case ?in da shi matu?a, amma ba ta ga wanda ya dace tayi maganar da shi ba. Dan ko da wasa ba zata tunkari DSP ba, balle sumayya tsfa zata ce za ta gaya wa Abba, dama ban da su biyun nan, ba ta wanda ya dace, ta sanarwa wannan gangancin da take shirin yi ba.

Sai dai kwana ta yi, tana tunanin ko yaya Viper, ya farfa?o gaba ?aya ya warware ko kuma yaya?

Washegari da safe, da DSP suka tafi station ?in nan, a hanya yake sanar mata da an yi belin Liti, ta tambaye shi waye ya yi belin Litin, ya ce mata bai sani ba, waya kawai aka yi masa aka ba shi umarnin ya sake shi.

Nabila ta ce "Nigeria ?asata"

Suka isa police station, Nasir ya nuna musu id card ?in sa, sannan ya nemi su bashi file ?in da Nabila ta nema, amma suka tabattar masa da an zo an kar?i file ?in an mayar da shi babbar headquarter.

Nabila ta ce "No wonder, hakan ya sake tabattar mini da lallai wanda ya aikata laifin, ?an manya ne, kuma ba dattijon nan ne yayi ba" ta cewa Nasir kawai su tafi dama ta san a zaman farko sai an aike da baba prison, kafin ta gama tattara hujjojinta.

Sai dai duk da haka, Nasir ya nemi a ba su in details, statement ?in, da Asibitin da aka kai yarinyar, amma suka ce ba a ba su wannan umarnin ba, komai da komai yana babbar headquarter.

Suna tafe take ce masa "Kar ka damu yaya, zan baka mamaki ?o?arin da zan yi a kan lamarin nan, zan tattara hujjojina na shiga kotu" yayi murmushi tare da ccigaba da ba ta ?warin gwiwa, ya biya ya ajiyeta a wurin aiki sannan ya tafi.

Cak ta tsaya a harabar wurin, tana ?arewa motocin kallo, ta tsayar da idonta a kan ba?in motocin da ta gani guda uku, sai dai ?ayar ita ce motar da ta din ga bin ta, har ta tsaya tayi knocking ?in glass. Ta ?arasa ta zagaye motar, ta sake tabattar da ita ce, ta jinjina kai ta shiga.

Ta je office ?in ta, ta ajiye jakarta, ta fita ta tafi office ?in Barrister Habib, a hanya ta ci karo da MD barrister Kabir da wani babban mutum, da ta ta?a ha?uwa da shi a office ?in sa.

Cikin girmamawa ta risuna, ta gaishe su, suka amsa, Barrister kabir ya ce "'yar ?walisa in ji habib, an shigo kenan?"

"Eh sir, na biya neman wata shaida ne, ban samu ba ma, na taho"

Ya ce "Sai ha?uri, haka lamarin aikin dama yake, wataran nasara wataran sai ha?uri, na ji da?i da na ga kina mayar da hankali yanzu kin rage kwalliya".

Mutumin ya zuba mata ido, yana ta murmushi kamar an yi masa kyautar kujerar makka, dan sai da ta faki idon Barrister kabir, ta galla masa harara, sannan ta yi gaba.

"Yaya Habib"

Ya ce "Yau kuma?"

Ta ce "Eh mana, yau ba?i muka yi ne?

Ya gya?a kai ya ce "Dama wurin nan ai kullum cikin ba?i yake"

"Wasu motoci na gani, wata farar mota ta waye?"

Ya ?ura mata ido sannan ya ce "Hala na samu demotion ne zuwa mai gadi?"

Tayi dariya ta ce "Am very sorry, ka san wani abu?"

"Sai kin fa?a"

"Ka san shi Allah, mai son bawansa ne, da kuma jin ?an sa"

Barrister Habib ya ce "Wannan haka yake".

"A wannan karon, ba tare da na yi tsammani ba, akwai yiwuwar case ya ha?ani da Najar bunkure, to kuma ka san ni yanzu kai ne mentor ?ina, na zo mu yi magana "

Yayi dariya yana mayar da wasu files, drower gabansa ya ce "Nabila 'yar ?walisa, haryanzu ba ki san wacece Bunkure ba ko?"

"And ba na bu?atar na sani, kawai i need your support, i want expose her hidden face to the world "

"How?"

Nan ta bashi labarin duk abun da yake faruwa, da case ?in da yake hannunta.

Ya ce "Nabila"

"Na'am barrister yaya Habib"

Yayi murmushi ya ce "Zaki ga yaya, aradu ki ke shirin tara da ka fa"

"Na shirya mata".

"Tana da wanda suka tsaya mata matar nan "

"Ni ma Allah ya tsaya mini"

Ya jinjina kai ya ce "Kin gama magana"

Nabila ta ce "Yauwwa barrister, and i want you to support me, dan Allah ka taimaka mini"

"Ba ?i nayi ba Nabila, matar nan manyan mutane da manyan ma'aikata sun kasa ja da ita, ke kin san ba haka nan take ba"

Nabila ta sake gyara zamanta ta ce "Support me, you will be proud of me"

Ya sauke numfashi ya ce "Duk abun da ki ke bu?ata na taimako, ki yi mini magana kamar yadda na taimaka miki ki ga file ?in Viper, zan cigaba da taimaka ki, amma ya zama sirri tsakanina da ke" tayi shiru tana kallonsa, ji tayi kamar ta yi masa zancen Vipern, sai dai a zuciyarta ta ji, ba ta gama amincewa da shi ba, kuma ba kowa za ta yi wa magana a kan case ?in sa ba, dan haka ta

Please Login or Register in order to submit comment