Reading KARFE A WUTA Chapter 110 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ka bari sabgar nan ta juye zuwa wani abu daban, ka fito da shi, duk in da ka kai shi"

"Ta da?e ba ta juye ba, ka manta tare ku ka din ga yi mini aiki a baya, ai ina ganin kamar shi haryanzu ba shi da wani muhimmin tabo, da bangar siyasa tayi masa kamar kai.
Ai talaka ba shi da wani amfani, ban da ku yi mana hidima, amma kun dage zaku kai ni ?asa, zan saki Walid ne, a lokacin da wa'adin zaman Abdul yasar ya ?are a gidan yari. Sannan zan sake duba abu mai muhimmanci a gareka, na yi masa ?aurin talala, yana raye amma kamar matacce, kamar yadda ka saka aka ?aure mini ?a a ?asashen waje. Na samu labarin kana aiki a kaina, sai ka ga bayana, gani gaka, ?an halak ka fasa".

Viper ya ce "Wannan shi ne kuskure na biyu mafi muni da ka aikata Indabo. Ni da kai muke har?alar nan, kuma batun ?anka, hukunci aka yi masa dai-dai da abin da yayi. Ina mai garga?inka da kakkausar murya ka saki Walid, idan ba haka ba zan razana duniyarka da abin da baka ta?a zata ba, awanni arba'in da takwas kawai ka ke da su, kuma ka fara ?irgawa daga yanzu" yana gama maganar ya kashe wayar, ya dafe kansa, cike da wata irin nadama da danasanin biye wa Indabo ya din ga aikata ?arna.

Wato a duniya idan amfaninka ya ?are kai ba a bakin komai ka ke ba, meyasa zai ?auki Walid maimakon ya ?auke shi, tun da da shi yake yi, ba Walid ba.

Da sassafe Viper ya tafi barrack, saboda Nabila, yana tsoron ita ce next target na indabo, tun da tare suke yin komai da ita, sai dai tayi noticing rama da kuma damuwa a tattare da shi.

Tana ta shiri, yana falon madam yana jiranta, gani yane da ya kawar da kai, komai na iya samunta.

"Vi" ya ji ta kira sunansa.

"Ka karya sai mu fita" ya girgiza mata kai bai ce komai ba.

Ta fuskanci damuwa na ?ara saka shi miskilanci da rashin magana.

Nabila ta sake marairaicewa ta ce "Dan Allah ka ci ko ka?an ne, duk ka yi wani iri"

"In ci Abinci ban san halin da ?an uwana yake ciki ba? Shi ya ci? Duk a dalilina, shikenan duk wanda ya ra?e ni a haka rayuwarsa za ta ?are a wahala da tashin hankali, menene laifin Walid ne?"

Cikin rauni ta ce "Na sani, na kuma fahimce ka, amma hakan babu abin da zai canza. Addu'a da ci gaba da jajircewa ce kawai za ta kawo mafita, ka yi ha?uri dan Allah Vi ka saka wani abu a cikinka" ya ?ura mata ido na wani ?an lokaci, kawai ya tashi tsaye ya ce "Idan kin gama ki same ni a mota" sosai tausayin sa ya mamaye mata zuciya.

Jiki a sanyaye ba tare da ta samu ta yi breakfast ?in ba, ta bi bayansa.

Da suka kai ta wurin aikin ma, har ta shiga ta ji kamar ana bin ta, ta waiwaya ta ga shi ne ya biyota. Ba ta ce masa komai ba, ta shiga office ?in ta ya bi bayanta.

Kujerar cikin office ?in ya samu ya zauna, bai kulata ba, ita ma ba ta ce masa komai ba, ta ci gaba da aikinta, gani yake yi yana kawar da kai, wani abun zai sameta ita ma.

Har ta gama aikinta na ranar yana zaune, sannan Liti ma ya saka an mayar da shi cikin barrack.

Duk yadda ya bi wayar Indabo abu ya gagara, sai ta?i shiga, gashi gani yake yi kamar babu wani ?o?ari da ake yi a kan neman Walid ?in.

Kwatsam Nabila na shirye-shiryen tafiya, ya sake jarraba wayar Indabo, cikin sa'a ta shiga kuma ya ?aga, Viper ya mi?e cikin zafin rai ya ce "A karo na ?arshe, ina Walid yake?"

"Babu wata barazana da zaka yi mini Viper, sharu??a zan saka maka, wanda dole sai ka bi su. Na farko ka saka wannan yarinyar ta janye ?orafin da ta shigar a kan Bunkure a ma'aikatar Shari'a, sannan ka tattaro duk wani bincike da ka yi a kaina, na yin?urin tona mini asiri, da wannan wayar da ka ke amfani da ita ka bani, sai a saki Walid, idan ba haka ba wannan banzar yarinyar ita ce next target ?ina a kanka, sai na saka an wula?anta ta, wula?anci mafi muni na tagayyara rayuwarta, fiye da yadda ka ke tunani" Viper ya ?aga kai ya kalli Nabila da take kallonsa, amma ba ta san me ake cewa ba.

Viper ya ce "Saboda abin da nake shiryawa a kanka ne ya sanya ka kashe P.A?"

Indabo ya ce "Eh, ban damu da a in da ka samu labarin hakan ba, iyaka na san ba ka da wata cikakkiyar shaida a kan ni ne kashe shi, duk wanda ya ci amanata, sai na kawar da shi. P.A ya ci amanata ya ha?a kai da kai, domin yana ganin ya zame ya bar ni shi ne zai sanya ka ?yale shi".

Viper ya sauke numfashi mai zafi, cike da dana sanin, sanin Indabo a rayuwarsa ya ce "Idan kuma ina da shaidar kisan kan da ka yi wa P.A da hannunka fa?"

"Gwargwadon yadda ka ci gaba da zurafafawa, gwargwadon yadda zan ci gaba da hura wutar da ka ke ciki, ba dai kana yi wa kanka i?irarin ?arfen cikin wuta ba, idan ba zaka ?akku da hannu ba, zan ci gaba da iza wutar da ka ke ciki, sai ta kai matakin da zata narka ka"

Viper ya datse la??ansa na ?asa, ya fesar da wani zazzafan numfashi, ya ce "A ina zan kawo maka abin da ka bu?ata?"

"Zan turo maka adireshin wurin, kuma ba kana bayarwa za a sake shi ba, sai na ba wa ?wararru sun tabattar da ingancin abin da ka bayar, kuma a yau ba gobe ba, yarinyar nan ta janye maganar Bunkure"

"Na ji, zan yi abin da ka ce, amma yarjejeniya ?aya idan ka sa?a, wutar da kake ?o?arin narkani da ita, kai zata ?ona" Indabo ya katse kiran.

Viper ya kalli Nabila, ta ce "Vi wai lafiya?"

"Zamu je ma'aikatar shari'a, ki janye ?orafin da ki ka shigar a kan Naja'atu Bunkure"

A razane Nabila ta ce "Saboda me?"

"Saboda haka na ce" yayi maganar a fusace.

Nabila ta ce "Akwai dalili dole, ka gaya mini, idan ba haka ba zan iya janyewa ba gaskiya, gaba ?aya wahalata a kan lamarin matar nan na ?ata lokacina, kawai kuma sai na janye?"

"Sai kin janyeta, babu wani bayani da zan yi miki, dolenki ki janye" yayi maganar yana kallon Nabila, yana hasko cikin bala'i da tashin hankalin da zai shiga, idan aka ta?a ta.

****

Goye yake da Jaka a bayansa, a dajin Allah shika?ai, sai waige-waige yake yi.
A kan babura da manyan bindigu, wasu mutane suka ?ullo, suka zagaye shi.
"Ka ajiye jakar, ka ?aga hannayenka sama" wani yayi masa umarni.

Ya ajiye jakar, ya ?aga hannayensa, ?aya ya kar?i jakar, ya zazzage, ya dudduba ya ce "Kayan ne"

Wani daga cikinsu ya ce "Za a aika shi ne?"

"A'a kai ba a ce ba, jami'i ne, asirinmu zai iya tonuwa, mu ware kawai".

Suka ja baburansu, suka yi gaba, suna tafiya aka turo masa sa?o.

"Ke je dutsen da yake in da kuke, ka ?auki gawarsa" kamar mahaukaci, haka Viper ya sake gigicewa, daga in da aka saka shi kai kayan, bai isa in da Walid yake ba, sai bayan awanni uku.

Yana zuwa ya lura da ba a lokacin aka yar da shi a wurin ba, kamar ya kwana a wurin, an ?aure masa hannu da ?afafuwa, an tura masa tsumma a baki, an ?aure wuyansa da wayar cable, ga jikinsa ko ina a farfashe saboda duka.
Fuskarsa ta kumbura suntum, duk jini, ?anan ?wari sai bin sa suke yi.

Kamar yaro ?arami, Viper ya fashe da kuka yana kwance Walid, ya kwance wayar da take wuyansa, ya ?aga shi yana kuka, yana kiran sunansa.

Ya ?an?ame shi a jikinsa, kawai ya ji zuciyarsa na bugawa, a hankali.

Zumbur ya mi?e, yana ambaton Allah, ya goya shi a bayansa, gani yayi idan ya tsaya buge-bugen waya, zuciyarsa zata daina bugawa, haka ya kwashi tafiya, har rukunin kamfanunnukan nan, ya ce su taimaka masa su kai Walid Asibiti.

Kai tsaye barrack ya tafi da shi, ya kai shi asibitin cikin bariki, babu wani jinkiri aka rufu a kansa, yana da rai bai mutu ba, sai dai babu tabbacin ya tashi.

Duk da Nabila tana cike da ?acin rai da damuwar sakata janye ?orafi da yayi, ba tare da ya yi mata bayanin komai ba, amma tana ganin sa?onsa na yana Asibitin cikin barrack tare da Walid, ta tashi tana tsuma, ta saka hijjabi ta fita.

Yanayin da ta ganshi ne ya karya mata gwiwa. Ta ce "Vi ya ake ciki?"

"Yana ciki sai dai babu ya rayu" yayi maganar yana zubar da hawaye.

"Kayi ha?uri vi, ka kwantar da hankalinka, in sha Allah Walid zai tashi da ikon Allah"

Sai ita ta kira su Alhaji mu'azzam, da Liti ta sanar musu an ga Walid.

Babu jimawa wurin ya ?inke da jama'a.

Hatta Abbu yana wurin, Shahida ma kasa zama tayi, sai da ta biyo Abbun.

Abbu sai shi ya kama hannun liti, yana ta rarrashin sa, gaba ?aya ya firgice, an tu?e Walid daga shi sai gajeren wando, duk jikinsa shaidar duka, aka yi dressing ?in raunukan jikinsa, aka ?ebi jininsa ana ta gwaje-gwaje.
Duk wani abu da za a bu?ata wurin bincike, sai da suka ?auka, kafin a ta?a shi.

?aya daga cikin likitocin ya fito, ya ce "Ku kwantar da hankulanku, Alhamdilillah. He's responding to treatment. Vitals ?in sun dawo normal, in sha Allah muna saka ran ya farka a kowane lokaci. Idan ya farka zamu tura shi sauran gwaje-gwaje.

Sai a lokacin suka ?an samu nutsuwa.

Cikin dare aka kira Viper wurin ogansa, Ya sha fa?a a kan abin da ya yi ba tare da ya sanar musu ba. Shi dai yayi shiru, dan a halin da yake ciki, babu umarnin wanda zai iya tsayawa saurara, ya sha fa?a duk da yayi bayanin abin da ya faru a yanzu.

Ya numfasa ya ce "Jami'anmu sun tafi, za su dawo da wayar, duk wanda aka kama da wayar ?atar da shi zamu yi, cin amanar ?asa da ?o?arin tonon asiri ne, duk wanda aka kama da wayar ba jami'inmu ba" Viper dai yayi shiru, domin an ce ya saurari punishment ?in da za ayi masa.

****

Sai da Walid ya kwana a Asibiti, ya wayi gari, sannan ya motsa ya farka.

Liti ne ya ga ya motsa hannunsa, ya tashi da sauri, ya nufe shi yana zazzare ido yana kiran sunansa.

Walid ya bu?e ido ya kalli Liti, ya yin?ura zai tashi Liti ya ce "Kai kar ka tashi, a asibiti kake"

Ya ?aga kai yana kallon ?akin, Viper ya ?araso, yana cewa "Mai laya, kalleni ka gane ni?"

Murmushi ya yi ya ce "Na kiyayi mai zamani"

Viper ya rasa me ma zai yi dan farinciki, ya zuba masa ido, yana ha?iye ?walla.

"Na kasa tashi ku ?aga ni"

Viper ya sako hannu ya ?ago Walid, sai da ya yi ?ara saboda ji yayi kamar su na kakkarya shi.

Liti ya ce "Wai dan Allah meyafaru, suwaye suka ?auke ka?"

"Jama'ar Indabo ne, wai sai na gaya musu abin da Viper yake shiryawa a kansa. Na ce ban sani ba, na daku tun da suka ?auke ni, a ?aure nake, sai ranar da suka sha?e mini wuya da cable na zata mutuwa ma nayi wallahi"

Viper ya ce "Muhsin, ka yi ha?uri, duk ni ne sila ka yafe mini dan Allah"

Walid ya ce "A'a rashin jinmu ne dai sila"

Likitoci sun yi mamakin ganin Walid a zaune yana ta magana.

Sai dai aka yi masa wanka, aka saka masa kaya, ya ci abinci, aka je aka yi masa hoto, aka tarar da karaya a hannunsa na dama.

Da yamma Viper yaje har gida, yake gaya wa Abbu yanayin jikin Walid, suka yi ta murna, Shahida tana son ta ce masa tana son sake zuwa duba Walid, amma ta kasa.
Babban abin da ya tsaye mata, bai wuce jin yadda yake bawa Abbu labari cewa Walid ba shi da uwa ba shi da uba, ba wa ba ?ani, shika?ai yake gararambarsa, dangin iyayensa ba masu zuciya bane ba, duk ba su da ?arfi, amma babu wanda ya damu da shi a cikin su.

Lokacin da Viper ya yi wa Shahida tayin auren Walid, ita dai ba ta ji tana son shi ko akasin haka ba, amma abin da Viper yake gaya wa Abbu, na cewar maraya ne gaba da baya, sai ta ji wani irin matsanancin tausayinsa, ya cika mata zuciya. Ta ji zata iya kowace irin sadaukarwa, domin rayuwa da shi.
Sai dai ta sha mamaki jin cewa wai har ya farfa?o ya tashi yayi magana, dan lokacin da ta je, baya cikin hayyacinsa.

A cikin daren ranar, aka yi wa Walid ?ori a hannu, wajen ?arfe biyu aka fito da shi, liti ya ce Walid sai ya matsa masa saman gadonsa sun yi squating, tun da shi ne zai kwana da shi, kar yaje yana bacci a zo a sake sace shi bai sani ba.
Abin ka da an kwana biyu babu bacci, yana hawa gadon, sai bacci, Walid kuwa zugi ya hana shi bacci, tun bayan da alluran da aka yi masa suka sake shi.

Da Viper ya zo ya tarar da su, fizgo liti ya so yi daga kan gadon, amma Walid ya hana shi.

Duk wata sangarta da rashin mutunci, idan suna tare liti ya iya ta, amma idan aka fita fagen rashin mutunci na 'yan daba, babu wasa.

Viper ya ce "Shahida na gaisheka, ta ce ayi maka sannu"

Kawai yayi murmushi yana kawar da kansa gefe.

"Au ba zaka ce kana amsawa ba? Aishikenan. Ni dai ina ta sake yi wa Allah godiya, da Allah sa ka farfa?o, da ka mutu ba zan yafe wa kaina ba, kuma da tarayyar mu, ba ta da wani amfani, Allah ya ?ara tsare mini ku, ya baka lafiya".

Walid ya ce "Tarayyar mu tayi mini rana ni, Viper nifa abin da ka yi mini, ban ga wani abu da zai sameka na ja da baya na barka, babu shi. Ka yi mini da aljihunka da jikinka, da lafiyarka babu wanda baka wahalata mini....

"Ka daina wannan maganganun, bau ne past ya riga ya wuce, kuma ni mahaifiyarka tawa ce, a haka na ?auki abin"

Yayi murmushi ya ce "Mai zamani, wanda zai tsaya maka, a lokacin da baka da komai, ka ke neman taimako, ba tare da tsangwama ko tunanin samun wani abu daga gareka ba, baka da babban masoyin da ya wuce shi, shiyasa da kai da mai gida dodo, ba zan gushe ba ina yi muku fatan alkhairi, da ro?a mana gafarar Allah"

Viper ya ce "Nima hakan take ai, a duniya yanzu bani da tamkarku, da kai da wannan garujen" yayi maganar yana nuna liti.

Walid ya kalli liti yana dariya.

"Ya fi ni shiga tashin hankalin rashin ganinka, baya bacci, baya iya cin abinci wai ina zai saka kansa, babu kai ?an mama" dariya suka yi tare, liti kuwa bai san suna yi ba.

****
?aton ?aki ne babba sosai, ?auke da computers, da wasu na'urori, Viper yana zaune a kan computer da shi da wasu a cikin wurin.

Wani video ya kunna, aka saita a jikin majigi, Videon babu murya, amma Imdabo ne a ciki, yayi wasu maganganu, P.A yana ja da baya, kawak ya harbe shi sau uku da bindiga.

Viper, mutumin nan ya?arsa sai da techniques, ba za su ta?a bari a hukunta shi a cikin ?asar nan ba, ya aka yi ka samu Videon?.

"Eh kamar yadda na gaya maka da farko ne, P.A ?in sa ne ya samo mini wasu informations ?in a kansa, saboda a zaman kotu ya ?auka za a ambaci sunansa, yayi hakan da a wanke shi.
Lokacin da Indabo ya bu?aci ganinsa, na bashi cameran, na ce ya saka a gaban rigarsa, zan din ga ganin komai, ni kaina ban yi zaton zai kashe shi ba".

Mutumin ya dafa kafa?ar Viper ya ce "Ka kwantar da hankalinka, na san yadda ka ke ji a zuciyarka a kan mutumin nan, kuma na san legally ba zasu hukunta shi ba, tun da yanzu ayi shiru da maganar tuhumar da ake yi masa. But you have my support hundred person, either legally or illegally sai mun ?auki mataki a kansa. Saboda ba shi da amfani a cikin al'umma ko ka?an, da kunya ace irin wannan ne suke mulkar al'umma, amma ba wani abu in sha Allah"

Cikin damuwa Viper ya ce "Sir na baku recording na wayar da muka yi da shi, yarinyar da zan aura, tana cikin hatsari sosai da sosai, ban san me zai iya yi mata ba, ba zan iya jurewa ba idan ya ta?a ta, ga aikinta da ta sha wahala a kai ya salwanta"

"Bai salwanta ba Viper, kuma ina baka tabbacin babu abin da zai sameta, babu kuma abin da zai samu wani naka, kar ka damu" Viper ya jinjina kai yana jin ?warin gwiwa.

Asibiti ya koma wurin Walid, ya tarar da Shahida, ta yayyanka masa ayaba a kan plate, ta ajiye masa yana ?auka da hannun hagu yana ci, yana ganin Viper ya zabura, kamar wanda yake aikata rashin gaskiya, sai da Viper ya so yayi dariya, amma ya maze.

A haka Nabila ta zo ta tarar da su, tayi masa sannu, Walid yayi ta yi mata godiyar suna ?awainiya da shi.

Nabila ta ce "Vi ai su suka sha ?awainiya, dan Allah tun da ka farfa?o ka saka shi ya ci abinci Please, haryanzu baya mayar da hankali, duk ya rame. Ya fi yi mini kyau lokacin da kumarinsa"

Walid ya ce "Vi an ce ka din ga cin abinci ka rame"

"Zan zageka da kai da Vi ?in"

"Allah ya baka ha?uri, an hanamu fa?ar master, Vi ?in ma an hanamu, to ai shikenan"

Nabila ta rausayar da kai ta je bayan Viper ta yi ?asa da murya ta ce "Zamu je ganin likita kar mu makara fa" ?agowa yayi ya kalleta, kamar ba zai tashi ba, sai kuma ya tashi ya nufi hanyar fita.

Fitarsu ke da wuya ya tsaya cak, ya waiwayo ya kalleta ya ce "Kar ki sake ?o?arin yi mini yawo da hankali, ko kuma nuna kin damu da ni, bana son yaudara" yayi maganar yana nunata da yatsansa.

"I don't fake it, kai baka san halin da ka saka ni ba, lokacin da na nuna maka so saboda Allah. Na ji da farko i fake it, daga baya kuma da gaske na ?aunace ka Vi, yakamata ?wa?walwarka ta tunatar da kai, abubuwan da ka yi mini, kuma ka gaya mini. A gabanka abokinka har ce mini yayi bani da class, ina yawo a cikin maza, duk dan ina sonka, ina fatan daga kaina, zaka din ga kiyaye abin da zaka gaya wa mace, mata bama mantuwa.
Duk motsin da nayi ban ta?a burgeka ba, kullum cikin kyarata ka ke yi, amma haryanzu ina yi maka kallon abu mai muhimmanci a gareni, mussaman kulawar da Jauhar ta samu a wurinka, ka yi mini afuwa Vi, bana fatan ?untata zuciyarka".

Cikin tsananin dakiya da jarumta, ya jinjina kai, ya ce "Na fahimta"

Duk yadda ya so cire Nabila daga zuciyarsa abu ya gagara, sai a lokutan nan, da ta fara yi masa wula?anci ya ga ashe ya sha?u da ita, sha?uwa ba ta wasa ba.

Cikin ikon Allah Walid ya samu kulawa sosai da sosai, gashi ba shi da ?an jiki, nan da nan jikinsa ya fara warkewa, sai dai ya kan manta da ba shi da lafiya, idan yana ri?e da wayarsa, Shahida tana turo masa sa?onnin, babban abin da ya ?ara yi wa Shahida da?i, ita kanta kunyarta Walid yake ji, balle yayi kule-kulen mata, sa?anin mijin da ta rabu da shi, saboda yana da ku?i, yan mata kowa ma kulawa yake yi, kishi kamar ya kasheta, gashi ba abin da yake iya amfana mata.

***
Sallamar da ake ta dokawa a tsakar gida ne, ya sanya dattijon mutumin, sauke farin tabarau ?in fuskarsa ya ce "Waye ne?"

Ya banka?o cikin ?akin ya ce "Nine, ko har an manta da ni ne, nake ta sallama aka yi shiru?"

Dattijon ya ce "Ina fa, waye ya isa ya manta da sarkin gida? Maraba lale da Abdallah"

Liti ya ?arasa ya na fa?in "Likkafa ta ci gaba, gida ya sha gyara"

"Yau kai ne a gidan ka tuna da mu kenan?"

"Ai kullum kuna raina, na san ina zuwa dattijuwarka za ta tayar mini da hankali, ta saka ka kore ni"

"Hmm sannu, na samu labarin ?aya uban naka yayi free, kotu ta wanke shi ko?"

"Aiba shika?ai ta wanke ba, har mu, ai bamu da wata nutsuwa idan yana cikin damuwa. Ban ga tsohuwar nan ba, ko ta rasu"

"A'a ni uwata ba ta mutu ba, tana nan ?alau, sun fita da gyatumarka"

Liti ya ce "Lallai ta sha miya, amm Alhaji, dama na zo ba?i ne, wata bazawara ce take so na, shi ne ta turo iyayenta, suka zo nema mata aurena wurinka, tana fatan zaka bata ni"

"Ikon Allah, ita bazawarar"

"Eh, amma dan Allah kar ka yarfa ni, ko ka tona mini asiri ka ce wai ba na ji, abu ne da aka yi shi ya wuce, yanzu na shiryu na daina, dan Allah kar ka ce musu wai bana ji, kaga sirikaina ne"

Alhaji ya yi dariya, ko bayan shekara dubu, Abdallah ba zai canza hali ba,duk da Ya lalace yana son abin sa, amma gwaggo mahaifiyarsa ke nema tayi masa baki, saboda soyayyar da yake yi masa, kuma hakan yana da ala?a da tsanar da ta yi wa babar litin ya ce "To Baba, ba zan yarfaka ba"

Liti ya fita waje, yayi musu iso, Abbu ne tare da Baba, mahaifin jauhar, da kuma Viper.

Alhaji ganin Liti da manyan mutane, ya tashi ya kar?e su cikin girmamawa. Bai fi sau biyu ya ta?a ganin Viper, yanzu da kyar ya gane shi, saboda lokacin da ya san shi yana da ?uruciya sosai.

Nan Abbu ya gabatar masa da kansu, tare da gaya musu abin da ya kawo su, a kan yayi ha?uri, ya yafewa Liti, tun da yanzu duk sun watsar da shirirtar da suka yi a baya, dama har da ?uruciya.

Nan Alhaji yake sanar da su, yadda ya kai liti ?asar waje karatu, amma ya dawo an koro shi, sai ma shaye-shaye da ya koyo, ga rashin kunya da yake yi wa kakarsa, wanda hakan ya ?ara tunzura shi a kan litin.

Viper ya ce "In sha Allah Alhaji, Abdallah ya shiryu ba zai sake ba, dan Allah ayi mana afuwa, ayi ha?uri"

Alhaji ya ce "Dama baku muke ?i ba, halayenku ne ba ma so marasa kyau, Ubangiji Allah ya ?ara rufa mana asiri"

Nan kuma hira ta ?arke a tsakanin su Abbu, tare da tattauna manyan matsalolin da ya jefa yaran nasu ga halaka.

Bayan sun gama da gidan su liti, suna tafe, tausayin Walid ya mamaye zuciyar Viper, su duk sun daidaita da iyayensu, shikuwa ba shi da kowa, sai Allah sai barba?a??un danginsa marsa amfani. Yayi Addu'ar Allah ya sa Shahida ta rayu da abokin nasa cikin aminci da mutuntawa, mussaman da ya ga ya fara sakewa da Shahidan.

Maganar Baba ce ta dawo da shi hayyacinsa da ya ce "In sha Allah, gobe zan je gidan Major, mu yi wadda za mu yi, ya bani 'ya ta, na ?arasa ri?onta na aurar da ita, na fuskanci bai san zuru ba".

Ayshercool
08081012143
Abbu ya ce "A'a Alhaji Bashir, abi komai a hankali, zamu je mu same shi sai a tattauna".

"Alhaji Ibrahim, na san na yi wa maitama laifi, amma yadda yayi reacting ban ji da?in hakan ba. Gaba ?aya ya tsaya mu fuskanci juna ya?i, ya mayar da ni kamar ma?iyinsa nima fa a ?a'ida yayi mini ba dai-dai ba".

Sai a lokacin Viper ya ce "Baba dan Allah ka yi ha?uri ku sasanta, wannan rashin jituwar taku, yana ta?a Nabila sosai da sosai.
Kuma haryanzu tana cikin barrack a zaune, ta rasa yadda ma zata yi dan Allah ku yi ha?uri ku sasanta".

Baba ya ce "Ba ?i na yi ba Aminullahi, na bashi duk wata dama, a matsayin sa na wanda yake uba a gareta, kuma ya raineta, idan ya gaji ni ya bani abata, nima na rayu da ita ko yaya"

Viper ya ce "Haka ne, kana da gaskiya. Amma ka yi ha?uri dai, a bi komai a sannu, aje a same shi, ayi masa bayani, na san zai

Please Login or Register in order to submit comment