Reading KARFE A WUTA Chapter 35 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

san me zan ce ba"

Ta ce "Ai shikenan"

"Yauwwa, na ce ba ka ga azumi saura 'yan kwanaki, yakamata ace ko sugar da lemo mu saya mu je mu gaida su Abba"

"Sai kin dawo" ya fa?a yana shan kunu.

"Master meyasa?"

"Kawai".

"Na san akwai dalili, amma koma menene ka yi ha?uri, ba a fushi da iyaye, kai fa ka gama yi wa wani nasiha ?azu, meyasa ba zaka yi amfani da ita a kanka ba?"

Juya mata baya ya yi, irin idan kin gama kya yi shiru.

Zuciyarta cike da fargaba, ta taka ta je kusa da shi ta zauna ta ce "Masu sunanka manyan mutane ne, dattawa, ba sa haka, dan Allah kar ka saka mu shiga fushin Allah, iyaye ba abun watsarwa bane ba, ranar da babu su da ku?i ba zamu gansu ba, mun rasa iyaye mata, mazan sai mu nemi albarkar su"

Ya ?aga hannunsa ya ?ora a kan kunnensa, ta kalli dogwayen yatsunsa, faratansa sun yi tsayi.

"Gobe in Allah ya kaimu friday ce, a yanke farce, sumar nan ma tayi yawa yakamata a rage ta, ayi maka gyaran fuska kafi kyau idan aka aka rageta"

Juyowa yayi gaba ?aya, ya ?ureta da idonsa.

Sai jikinta yayi sanyi, tsigar jikinta ta tashi yarrr.

"Kin fa dame ni" yayi maganar a hankali, amma muryar da yayi amfani da ita, har cikin zuciyarta.

"To me nayi maka na takura?" Shiru yayi bai yi mata magana ba, ya cigaba da ?are mata kallo.

Ja tayi da baya, ta ce "Dama wainar fulawa zan yi mana mu sha da tea, bari na ?ora"

Ta fita tsakar gida, ta hura kurfoti, ya biyo ta gaban kaskon ya zauna, sai dai kallon da yake yi mata duk ta takura.

"Master, kamar fa akwai ?era a gidan nan, dan Allah ka sayo maganin ?era"

"Shi m tsoron nasa ki ke ji kenan?"

Tayi murmushi ta ce "Eh, amma ba sosai ba"

"Ya ha?a nasa shayin, tana soyawa yana cinyewa"

"Master ban gane ba, idan ka cinye ni fa?"

"Sai ki soya wata"

"Ko kuma ka soya mini ba, ?ullin fa bashi da yawa, ka ?oshi gaskiya" ta janye plate ?in.

Ta gama ta ha?a nata tea ?in, ta fara ci.

Ya zuba mata ido, cin abincin ma yanga take yi masa.

Yana zaune yana kallonta, ta gama ta ha?a wanke-wanke ta yi.

Ta gaka komai, zata shiga ?aki ta ce "Na gama taso mu tafi, kar sauro ya saka maka zazza?i".

"Dama na ce miki ke nake jira ne?"

Jauhar ta ce "Eh dole ka ce haka, tun da na cika maka cikinka, aishikenan sai da safe, dan Allah kar ka sha komai ka ji master".

Yayi mata shiru, ta ce "Master, magana nake fa, na san kana ji na, dan Allah kar ka sha komai ka ji Mai zamani"

?agowa yayi ya kalleta, tayi masa murmushi, tasowa ya yi, ya biyo bayanta. Tsayawa tayi ta ga me zai yi mata.

Yana zuwa ya ri?e kunnenta ya ce "Me ki ka ce?"

"Master na ce"

"In kuma jin kin fa?i wannan sunan" sai dai duk wannan abun fuskarsa ba fara'a.

Cikin shagwa?a ta ce "Kunnena zai cire fa" ya tura ?eyarta, har ?ofar ?akinta, ta ce "Kar in sake ganinki sai gobe in Allah ya kaimu".

"To na ji, amma dai kar ka sha komai dan Allah" wucewa yayi ?akinsa, ta ?arasa gaban gadonta tana murmushi.

Ta yi wanka, ta shirya ta shafa turarukan ta, ta nemi wuri ta kwanta. Sai murmushi take yi, tana jin da?in cigaban da ake samu a kan zaman su.

Ta kalli pillown da take rungume da shi, ta shafi pillown a hankali, tana tuna hirarrakin da aka yi ?azu da su Anty wasila.

Tabbas abun da take ji game da aure ya sha banban da abun da ta tarar, to ko ba haka abun yake ba? Sai kuma ta tuna har a littatafan addini ta karanta.

Hakan yana nufin Al'amin ba shi da lafiya ne? Ko kuma ita ?in ce ba ta gabansa, sai dai ya ci, yayi shaye-shayensa ya je yawonsa, ko kallon kirki ba ta ishe shi ba.

Tunani take yi ko dai tana da wani na?asu ne, da ya sanya ba ta gabansa, ko da wasa


Ayshercool
08081012143
???500 ne via 0009450228
Aisha Adam jaiz bank sai shaidar biya ta 08081012143

90009343
'Yan Nijar ku turo katin airtel na 300fcfa

Arewabooks ayshercool7724

https://chat.whatsapp.com/E3bH5OKBh9jH2aYygj0ArA

Kina bukatar kaya masu kyau da inganci??

Kina bukatar kayan kitchen wnd suke available ba order ba??

Kina bukatar adashin gata wnd zaki dauki kaya kamar kyauta??

Kiyi joining wnn group din namu insha Allah xakiji dadin kasancewa a ciki.

Muna da kaya available masu kyau da rahusa????????
Ko kimin mgn ta????????
08093932955Jiki a sanyaye jauhar ta ce "Master, dama rigima ka je ka yi, ka ji wai a nemoka"

Bai tanka mata ba, ya ?auki kofin shayinsa, ya kai bakinsa.

"Dan Allah ka yi magana, menene abun yi yanzu? Ko zuwa zamu yi mu ba ta ha?uri" kallon Allah ya kiyaye ya yi mata.

Ta gyara zamanta ta ce "Ka san wani abu? Uwa uwa ce, kuma duk lalacewar ?anta tana son shi, ba zata ta?a mantawa da kai ba, illata mata ?a da ka yi, babu fa?uwa a ciki idan mun je mun bata ha?uri, idan dan ?an wani abu mu bata. Ba yanzu ake ji ba gaba ake ji master, duk rintsi duk wuya kar ka bari wani ya ?ullaceka, sai ka manta ka cutar da mutum, amma nauyin hakkinsa yayi ta ?awainiya da kai".

Ya shanye shayinsa tsaf, kamar a mafarki ta ji ya ce "Alhamdilillah"

Ta ce "Masha Allah, Allah ya ?ara mana wadatar zuci da rufin asiri, mu koma waccan maganar master, dan Allah ka yarda mu je mu bata ha?uri"

?wan?wasa gate ?in gidan aka fara yi, Al'amin ya tashi ya je ya bu?e.

?aya daga cikin yaran unguwar ne marasa ji, ya risuna ya ce "Allah ya ja zamaninka"

"Ya aka yi?"

"Wallahi guduma ne suka yi fa?a da dattijonsa jiya, ya kore shi daga gidan ya ce ya bar masa gida, ya sallamawa duniya shi, shi ne yau ya je ya sha wani abu, gashi can ya kulle mai unguwa a gida, da makami ya ce sai ya sara shi, an kirawo jami'an tsaro an kasa bu?e gidan"

Ya ce "Mu je in gani"

Suna zuwa gidan mai unguwa suka tarar da mutane cirko-cirko a ?ofar gidan, ga 'yan sanda su hu?u, ana ta fama a bu?e ?ofar gidan an kasa, sai kururwar mai unguwa ta cikin gidan, yana a taimake shi, a raba shi da ?an sa kan ya kashe shi"

Al'amin ya zagaya, ya kama katanga ya dira cikin gidan, ya tarar da guduma a tsaye a ?ofar ?akin mai unguwa, ri?e da wata shar?e?iyar wu?a, sai ?yalli take yana dukan ?ofar ?akin, yana maye yana sai ya kashe mai unguwa babansa.

Sauran matan gidan da yara, duk sun rufe ?akuna suna neman ?auki.

Al'amin ya tunkare shi, yana zuwa ya ri?e shi, ya kar?i makamin hannunsa ya kwa?a masa mari, hakan ya sa ya ?ara gigicewa, ya dan?o rigarsa ya bu?e ?ofar ya fito da shi sai tanga?i yake yi.

'yan sandan suka yo kansu, za su kama guduma, Amma Al'amin ya ce "Zamu zo da shi station anjima idan ya dawo hayyacinsa.

Mai unguwa da ya tsira da ?yar ya ce "Ofusa kar ku bari ya tafi da shi, dama shi yake goya musu bayan iskanci a unguwar nan, da ?a na bai kai haka lalacewa ba, a ha?a a Kama har da shi".

Al'amin bai kalleshi ba ya ce "Ko ya gudu ni a kama ni, ba zai gudu ba, idan ya dawo hayyacinsa zan kawo shi da kaina, mu ha?u a station zuwa ?arfe biyar na yamma ina son a zauna da babansa"

"Shikenan, mu na jiranka"

Mai unguwa ya ce "Ofusa ya zaka yi mini haka, yaron da ya nemi rayuwata"

"Mai unguwa ka jira ya dawo hayyacinsa mu gani, Allah ya kaimu ?arfe biyar ?in.

Jauhar na wanke-wanke, Al'amin ya turo ?ofa, hannunsa ri?e da guduma, ta tashi tana bin sa da kallo.

"Sako hijjabinki, ki kawo mini tabarma"

Ta jinjina masa kai, ta sako hijjabi, ta kawo masa tabarma, ya kwantar da guduma, ta ?are masa kallo ta ce "Wannan ai shi ne ya hana wani ya sare ni, lokacin da na je gida da aka tsare ka"

Al'amin ya ce "Kawo mini ruwa a bokiti da kofi"

Ta kawo masa ruwa, ya ?iba ya dinga she?awa guduma a ka, ya din ga zabura kamar zai zare, ya ?aukko gawayi a kurfotin Jauhar, ya daddaka ya ka?a a kofi, ya matse guduma ya dinga ?ura masa a bakinsa, ya sha wani ya zubo da wani, ya gama ya hanka?a shi ya kwanta.

"Master wai meya same shi ne? Ba shi da lafiya ne?"

"?wayar da ta fi ?arfin kansa ya sha, ya kusa halaka mahaifinsa"

Waro ido ta yi ta ce "Mahaifinsa kuma? Subhanallah lamari ya ?aci"

Bayan mintuna arba'in, guduma ya wartsake, ya din ga kallon gidan, sai da yayi ido hu?u da Al'amin, sai ya ?ara nutsuwa.

"Ka farfa?o?" Guduma ya sunkuyar da kai.

"Ka san me aikata ko?" Yayi shiru bai ce komai ba.

Al'amin ya yi ajiyar zuciya ya ce "Me ka sha?"

"Sigari ce"

"Da me?"

"Itaka?ai"

A fusace ya ce "Zan saka maka ?arfe wallahi, uban me ka sha ka ke yin?urin kashe mahaifinka?"

"Wiwi ce kawai ban sha komai..... Ba rufe baki ba, Al'amin ya ri?e ma?ogwaronsa ya ce "Zaka fa?a ko sai ni na kashe ka?"

A rikice jauhar ta ce "Dan Allah Master ka ?yale shi, kar ka kashe shi"

Cikin kakari guduma ya ce "Ba?in capsule ne"

"Waye ya baka, kuma waye yake dillancin sa a unguwar nan".

"Botorami ne"

"Botorami, yaran da suka sareni, na ?yale shi, shi ne ya fara sayar muku da wannan muguwar ?wayar? To wallahi sai ya bar unguwar nan. Uban me babanka yayi maka ka nemi kashe shi? Bayan sharrin ?waya har da iskanci, uban meyasa ba ka yi yin?urin kashe kowa ba sai shi?".

Cikin damuwa guduma ya ce "Kora ta yayi, ya ce kar na sake zuwar masa gida"

"Ba dole ya kore ka ba, tun da abun naka babu hankali a ciki, in anjima zamu je police station, ka bashi ha?uri, idan kuma ka bari yayi maka baki, ka shirya lalacewa da ta?ewa fiye da wadda ka ke ciki yanzu" ya jinjinawa Al'amin kai.

Al'amin ya ce "Ka zauna a nan kar ka fita ko ina"

Jauhar mamaki ta din ga yi, dama Al'amin ya san abun da ya dace, amma shi yake wanda bai dace ba.

Jauhar ta gama abincin rana, ta zuba ta bawa guduma, ya kar?a ya ce "Ya gode"

Al'amin ya zaunar da shi yana yi masa tambayoyi, sai dai bayanin da ya yi wa Al'amin, a kan irin rayuwar da ya tashi a kai, gaba ?aya jikin jauhar yayi sanyi, wato wasu lokutan mutane na yin gaggawar yankewa wasu hukunci, ba tare da sanin ainihin abun da ke ?oye ba.

"Da la'asar suka tafi police station, tun da suka je mai unguwa yake bala'i, har da cewa 'yan sanda su kama guduma su yi masa duk abun da za su yi masa shi yafi ?arfinsa.

"Uwarsa ce ta lalata shi, sannan ta dawo mini da shi, baya sana'r komai sai shaye-shaye na tsiya da ya ?orawa ransa, yau kuma rayuwata yake nema, to wallahi ba a haifi ?an da zai kashe ni ba, waccan shashashar uwar ta sa ita ce silar komai, bayan ya lalace ta nanna?o ta kawo mini shi"

Al'amin ya ce "Ina mamakin yadda aka bawa mutum irinka jagorancin al'umma alhalin ba ka iya jagorantar gidanka ba.
Kai da ka haife shi, baka iya bashi tarbiyya ba hukuma ce za ta tarbiyantar maka da shi? Ka san ba zaka iya kula da shi ba meyasa ka haife shi? Da ka saki majaifiyarsa ka maye masa gurbinta? Sakinta ka yi ka bar mata shi, ba ka san cin sa da shan sa ba, balle iliminsa da lafiyarsa, baka nuna masa sana'a ba, baka bashi jari ba, ita ba cikakken ?arfi ba itaka?ai tayaya zata iya yi maka rainon ?a?
Ka san jikinka yana bu?atar ka auri mata barkatai, ka yi jima'i ayi ta haifa maka 'ya'ya amma ba ka tunanin inganta rayuwarsu, ko bu?atar ka kawai ita ce bu?ata?"

"Kaga Al'amin ya isa hak.... Al'amin ya ?aga masa hannu ya dakatar da shi, ya cigaba da magana.

"Babu in da za shi, tun da ka haife shi, dole ka kula da shi, ka yi masa role ?in uwa tun da ka saki uwarsa a lokacin da ya fi bu?atar ku rayu tare, idan ba haka ba ko ba shi ba, a cikin wannan tulin 'ya'yan zaka samu mai halaka ka.

Ya mayar da idonsa kan Guduma ya ce "Kai kuma ya muka yi da kai?"

Guduma ya dur?usa ya ce "Baba dan Allah dan Annabi ka yafe mini, ka yi ha?uri ba zan sake ba in sha Allah, dan Allah ka janye korar da ka yi mini daga gidanka, nayi kuskure ka yi ha?uri "

Sai dai mai unguwa yayi tsit, dan kuwa Al'amin ya gama kwaikwaye shi a gaban mutane, yayi mamakin maganganun da suka fito daga bakin Al'amin ?in.

"Officer, zan kawo yaron da yake sayar da wannan capsule ?in, a ri?e shi a matsa shi, ya fa?i ina yake samota" ya sake kallon guduma ya ce "Ka shelanta, cikin unguwar nan, duk wanda na kama da sayar da irin wannan nau'in kayan, sai na lahira ya fi shi jin da?i"

Ya jinjinawa Al'amin kai.

"Yanzu dai ina nema masa afuwa, yayi nadama in sha Allah ba zai sake ba".

"Idan ya sake fa, ni fa gaskiya rayuwata tana cikin hatsari"

"Ayi rubutu, duk abun da ya yi zan ?auki laifin"

Ba mai unguwa ba, har Guduma Nura sai da ya kalli Al'amin.

Aka yi sulhu da rubuce-rubuce, suka fito, guduma ya risuna yana yi wa Al'amin godiya.

"Manta, mu je ka rakani asibiti, kan waccan uwar mitar ta sakani a gaba"

Guduma ya ce "Antynmu ayi mata godiya, abinci yayi da?i na gode master" bai ce komai ba, suka tafi asibiti.

Ko da suka je emergency, Al'amin har gaban gadon yaron da ya karya ya je, ya tarar da shi a kwance, ana saka masa ruwa.
Yana ganin Al'amin ya rikice, ya yin?ura zai ?ago, Viper ya mayar da shi, ya kalle shi ya ce "Na ji babarka na kururuwa na nakasta ka, a ?aukar mata mataki, kai ba ka gaya mata babu mai iya ?aukar mata mataki ba? Yanzu ka dawo hayyacinka ka tuna abun da ka yi ko? Ba ka sanni ba ko? Saboda ka sha ta gaya maka ?arya, ni ka tunkara zaka sara ko? Wai ba kai ne ?an mama ba, da aka rufe kwanaki madaki ya saka ka kashe wani yaro a dabarku ba? Ya shiga ya fita an sake ka, yanzu kuma da ka nakasa ya kasa taimakon ka ko?".
Ya sunkuyar da kai ya yi shiru.

"Za a zo a biya ku?in maganinka, nan gaba ka sake zuwa ka tari gaban tirela, ta kanka zan bi"

Ya kalli guduma ya ce "Tashi mu ware"

Ya tashi suka tafi, kamar wa da ?ani, suka bar mai unguwa da kunya.


Bayan fitar su Al'amin, jauhar ta kaiwa telar da take yi wa aiki kaya, ta rage mata wani abu a cikin ku?in, amma ba ta bata duka ba.

Ta tarar da yaran matan layin, suna ta bajekolin magungunan mata, ana ta shewa.

"Jauhara ba za ki sayi abun arziki ba, ga kaya nan sai wanda ki ke so, ku?i ku?i iya ku?inki iya shagalinki"

Kawai tayi murmushi ta basar da su.

Wasila ta ce "Wai sai an yi magana sai ki wani din ga mazewa kamar baki san komai ba? Ke an daina irin wannan abun kamar a zamanin da, idan baki zanzare kin fitsare ?afafuwanki ba,bar ganin mijinki a haka ba ruwansa da kowa, wallahi sai ki ga ya fara 'yan le?e-le?e, ki zo ki ?auki gyara hajiyata, ita mace sai d gyara, wannan kyan fuskar ta ki ba shi kawai yake so ba"

Jauhar ta ce "Hmm Anty wasila kenan"

"Ba wani anty wasila, malama ki rage ma?o dan Allah, kin iya neman ku?i sai aukin saka turaren wuta a gida, da goge goge, amma ba zaki sai kayan gyara ba, ina ta tallata miki kayan maman neehal ?in nan, baki ga kyan su ba, amma sai ki yi burus".

Suwaiba tela ta ce "Wai wasila ki ?yaleta mana, ki ka sani ko tana abun ta, idan tana yi gaya miki zata yi?"

"Ba wani, ni fa jauhar ?anwata ce, ?anwa na ?auketa, kunyarta tayi yawa Allah ya sa ba haka ki ke yi masa ba, babu yadda za ayi ki je ki ganta da shirt da wando, sai uban hijjabi da dogwayen riguna kamar zata yi ?awafi. Ki tsuke ki ci zamaninki tun da ?uruciyarki, ni ga wani tsumi nan na baki, na maman neehal ne, tested and trusted, ki gwada zaki bani labari.
(0706 677 4630 ga lambar da zaku samu maman neehal, domin samun kayanta)

Kamar sokuwa haka Jauhar ta kar?a, kasancewar ta san ba wani amfani da zai yi mata.

A gurguje ta kammala abun da za ta yi a gidan, ta fito saboda irin manyan karatun da ta ji suna yi, da suka fi ?arfin kanta.

Ta koma gida, ta din ga kallon robar abun da anty wasila ta bata, na wurin Anty lubabatu ma suna nan, ko kallonsu ma ba ta yi.

Aka fara kiraye-kirayen sallar magariba, tana salla, ?arar wani babur ya cika mata kunne, bayan ta idar tana cikin lazumi, ta ji ana kokowar shigowa da abu, ta tashi ta fito tsakar gida, ta tarar da Al'amin yana shigowa da wani tsohon babur jincheng, hannunsa ri?e da salansar babur ?in.

"Master, wannan kuma fa?"

"Jaki ne" ya bata amsa.

"Wai sai ka yi ta gaya mini ba?ar magana, wai ko shi ne ya cika layin nan da ?ara?"

"Eh"

"To meyasa ka cire masa salansa? Ka ji ?arar kuwa ba da?i, kamar ya shekara ba a kunna ba".

Ya jingine salansar, duk ya ?ata jikinsa da ba?in mai, ya ce "Na fi son sa a haka"

"To wai a ina ka samo babur?"

"Sata na fara" yayi maganar zai shigar mata falo.

Ta ce "Allah ya baka ha?uri, amma tsaya na kai maka ruwa ban?akin tsakar gida ka yi wanka, idan ba haka ba zaka ?ata carfet ?in da ba?in mai"..

"Na?e abun ki na wuce, ba zan yi wanka a tsakar gida ba"

Ta shagwa?e ta ce "Ba fa a tsakar gida ba, toilet ?in tsakar gida".

"?o?arin shiga falon yake, tayi sauri ta ?aukko tsumma, ta dur?usa ta ce "Bari na goge maka, kar ka ?ata mini carfet" ta gogge masa, sannan ya shiga.

Warin sigarin da yake yi ya sanya ta bin sa da ruwan zafi, ta matsa masa toothpaste a kan brush, ta ajiye masa.

Allah ya taimake ta, babu musu yayi wanka yayi brush, ya fito yana goge jikinsa, ya bu?e wardrobe ta shigo da sauri ta ce "Saura ka watso mini kaya ?asa, na sake gyarawa, nuna mini wanne zaka saka na ?aukko maka?"

Ya nuna mata, ta ciro masa su, kafin ya kar?a ta mi?o masa kwalbar turare ta ce "Ka shafa turaren, sai ka saka"

Ha?in da take amfani da shi ne, ta daka alumun, da farin muski na gari, da kanumfari, ta dafa su suka tsumu ta ta ce, ta zuba madarar turare a ciki.

Ya kar?a ya shafa, ya mi?a mata, ta kar?a ta ce "Ai naka ne, na bar maka"

Ya kar?a zai ajiye, ta ce "Baka ce ka gode ba" sai ya mi?o mata abun ta, da ya ce ya gode gara ya dawo mata da abun ta.

Tayi dariya ta ce "Hukuma sai da rarrashi, na janye ba sai an yi godiyar ba"

Ya ajiye, ya fara ?o?arin saka kayan, ta fita ta bashi wuri, shi kansa ya ji da?in jikinsa sosai da sosai, ga ?amshin yayi masa da?i sosai da sosai.

Ya fita ya kame a falo, ?amshin turare sai ?ibarsa yake yi.

Akwai English wears a cikin kayanta, sai dai ba ta ta?a gwada sakawa ba, dan kunya ma take ji, domin kuwa sai kwanan nan ta daina yawo da hijjabi a cikin gidan.

Da ?yar ta iya fitowa da doguwar rigar atamfa, da ta ?an kamata cif jikinta, ta zo ta zauna a falon, ta ce "Master ya ku ka yi a police station kuwa?"

"Labari zan baki ko yaya?"

Ta ce "Eh mana"

"Kunna radiyonki, ki ji labarai idan shi ki ke son ji".

Cikin shagwa?a ta ce "Ni naka nake so"

Ya ce "To ni ban san me zan ce ba"

Ta ce "Ai shikenan"

"Yauwwa, na ce ba ka ga azumi saura 'yan kwanaki, yakamata ace ko sugar da lemo mu saya mu je mu gaida su Abba"

"Sai kin dawo" ya fa?a yana shan kunu.

"Master meyasa?"

"Kawai".

"Na san akwai dalili, amma koma menene ka yi ha?uri, ba a fushi da iyaye, kai fa ka gama yi wa wani nasiha ?azu, meyasa ba zaka yi amfani da ita a kanka ba?"

Juya mata baya ya yi, irin idan kin gama kya yi shiru.

Zuciyarta cike da fargaba, ta taka ta je kusa da shi ta zauna ta ce "Masu sunanka manyan mutane ne, dattawa, ba sa haka, dan Allah kar ka saka mu shiga fushin Allah, iyaye ba abun watsarwa bane ba, ranar da babu su da ku?i ba zamu gansu ba, mun rasa iyaye mata, mazan sai mu nemi albarkar su"

Ya ?aga hannunsa ya ?ora a kan kunnensa, ta kalli dogwayen yatsunsa, faratansa sun yi tsayi.

"Gobe in Allah ya kaimu friday ce, a yanke farce, sumar nan ma tayi yawa yakamata a rage ta, ayi maka gyaran fuska kafi kyau idan aka aka rageta"

Juyowa yayi gaba ?aya, ya ?ureta da idonsa.

Sai jikinta yayi sanyi, tsigar jikinta ta tashi yarrr.

"Kin fa dame ni" yayi maganar a hankali, amma muryar da yayi amfani da ita, har cikin zuciyarta.

"To me nayi maka na takura?" Shiru yayi bai yi mata magana ba, ya cigaba da ?are mata kallo.

"Baka saka mini lambarka a wayata ba"

Ya mi?a mata hannu, ta bashi wayarta, ya saka mata lambarsa, ta ce "Yauwwa na gode, zan din ga yi maka flashing, kamar sau arba'in a rana"

"Iya arba'in?"

"Eh, ko yayi ka?an?" Ya girgiza mata kai alamar a'a.

"To ?an yi mini downloading ?in game"

Ya ce "Sai kin gama jarrabawa tukuna"

"Ai mun kusa in Sha Allah" ya lumshe idonsa ya ce "Allah ya bada sa'a"

"Amin ya haiyyu ya ?aiyyum master, 'yar madara na godiya"

Ta sake cewa "Dama wainar fulawa zan yi mana mu sha da tea, bari na ?ora"

Ta fita tsakar gida, ta hura kurfoti, ya biyo ta gaban kaskon ya zauna, sai dai kallon da yake yi mata duk ta takura.

"Master, kamar fa akwai ?era a gidan nan, dan Allah ka sayo maganin ?era"

Ya ce "Shi ma tsoron nasa ki ke ji kenan?"

Tayi murmushi ta ce "Eh, amma ba sosai ba"

"Ya ha?a nasa shayin, tana soya waina yana cinyewa"

"Master ban gane ba, idan ka cinye ni fa?"

"Sai ki soya wata"

"Ko kuma ka soya mini ba, ?ullin fa bashi da yawa, ka ?oshi gaskiya" ta janye plate ?in.

Ta gama ta ha?a nata tea ?in, ta fara ci.

Ya zuba mata ido, cin abincin ma yanga take yi masa.

Yana zaune yana kallonta, ta gama ta ha?a wanke-wanke ta yi.

Ta gama komai, zata shiga ?aki ta ce "Na gama taso mu tafi, kar sauro ya saka maka zazza?i".

"Dama na ce miki ke nake jira ne?"

Jauhar ta ce "Eh dole ka ce haka, tun da na cika maka cikinka, aishikenan sai da safe, dan Allah kar ka sha komai ka ji master".

Yayi mata shiru, ta ce "Master, magana nake fa, na san kana ji na, dan Allah kar ka sha komai ka ji Mai zamani"

?agowa yayi ya kalleta, tayi masa murmushi, tasowa ya yi, ya biyo bayanta. Tsayawa tayi ta ga me zai yi mata.

Yana zuwa ya ri?e kunnenta ya ce "Me ki ka ce?"

"Master na ce"

"In kuma jin kin fa?i wannan sunan, zamu gauraya da ni da ke" sai dai duk wannan abun fuskarsa ba fara'a.

Cikin shagwa?a ta ce "Kunnena zai cire fa" ya tura ?eyarta, har ?ofar ?akinta, ta ce "Kar in sake ganinki sai gobe in Allah ya kaimu".

"To na ji, amma dai kar ka sha komai dan Allah" wucewa yayi ?akinsa, ta ?arasa gaban gadonta tana murmushi.

Ta yi wanka, ta shirya ta shafa turarukan ta, ta nemi wuri ta kwanta. Sai murmushi take yi, tana jin da?in cigaban da ake samu a kan zaman su.

Ta kalli pillown da take rungume da shi, ta shafi pillown a hankali, tana tuna hirarrakin da aka yi ?azu da su Anty wasila.

Tabbas abun da take ji game da aure ya sha banban da abun da

Please Login or Register in order to submit comment