Reading KARFE A WUTA Chapter 54 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yi murmushi ta ce "Na gode Allah ya saka da alkhairi ya raya maka zuriya. Amma yanzu ya kake ganin za ayi? Office ?in ta zan je, a kan ina son bayanai daga gare ta, da bakin yarinyar?"

"Eh mana, go as a barrister, ke ma lawyer ce, go with your full confidence"

Tayi murmushi ta ce "Na gode sosai ranka ya da?e" ta juya ta fita cikin farinciki.

Sai dai kuma tunanin Viper ya cika mata zuciya, ko yaya jikinsa? Ya warware gaba ?aya ko kuwa?

Ba tare da dogon tunani ba, ta ?au jaka ta fita, ta samu mai sayar da fruit, ta sai uban kayan marmari ta tari abun hawa ta tafi.

Sai dai ta sha wahala, tana ta bulayi, ga uban kaya a hannunta, ta kunna Google map, yau sai ya fara yi mata hauka ta ce "Wai shi wannan ma anya ba aljani bane ba?"

Har ta fitar da rai, kawai ta hango roofing gidan, haka ta cigaba da tafiya, har ta isa ?ofar gidan.

Duk da tsoro da fargabar waccan sha?ar da ta sha, na neman kashe mata gwiwa, ta tsananta addu'a tare da neman kariyar Ubangiji.

Jin sallamar mace ya sanya gaba ?aya suka ?ago suna kallonta, liti ya zabga ashar ya ce "Ke uban me ya kawo ki nan, munafuka macuciya?"

Ta ce "Ashe kuma ka fito"

"Ban sani ba, uban me ya kawo ki?"

"Wurin Viper na zo" ta bashi amsa kai tsaye. Ya tashi tsaye zai zare wu?a, Walid ya hana shi, ya ce mata "Me zaki yi masa, kin manta abun da yayi miki ne? Ki bar ta?ama da baya kisan kai, zai iya farawa a kanki, dan yanzu ?wa?walwarsa sai a hankali "

Nabila ta ce "Shi ne dalilin sake zuwana, in ji ya jikinsa kuma na ji ?arshen labarin nan"

Walid ya ce "Jiki yayi sau?i mun gode, amma ki tafi kar ki sake zuwar mana, saboda zuwan da ki ke yi zamu canza wuri"

Liti ya fusata ya ce "Ke dalla fita"

"Ka daina hantarata, ba wurinka na zo ba. Ni dai ku taimaka ku ha?ani da shi, yakamata na ji da bakinsa ya yafe mink"

"Ke! Ni ki ke gaya wa haka?"

Walid ya ?ara dakatar da Liti ya ce "Ya riga ya yafe mikin ai"

Ta girgiza kai ta ce "Ban ga alama ba, akwai bu?atar sama masa nutsuwar ?wa?walwa kafin tunkarar duk wani abu, a ?an zuwan da na yi, na fuskanci kuna amfani da ?arfi wurin tursasa masa kar?ar abun da ya zo masa a yadda yake.
Baku da raunin, da zaku tausasa masa yadda yake bu?ata"

Walid ya ce "Kamar yaya?"

"Kamar yadda nake fa?a yanzu, a fara samo ?wa?walwarsa, ta hanyar daidaita gangar jikinsa, da hana shi ta'amalli da miyagun ?wayoyi, a saita tunaninsa da tunatar da shi shi wanene, ko ba duka ba, ayi ?o?arin samar masa da wani abu na farinciki ko yaya, a gwada canza masa tunani ba ta ?arfin tsiya ba, kuma a sama masa likitan da zai din ga duba ?wa?walwarsa"

Walid ya ce "Ta?, ke zaki iya duk wannan ?in?"

Cikin ?warin gwiwa Nabila ta ce "Ku bani dama, na san kuma a ba a karon farko ya kar?e ku ya saba da ku ba".

Kafin wani ya kuma magana, ya turo ?ofa ya shigo.

Walid ya ?ure shi da ido, dan kar yayi wa Nabila wani abu, ko nuna ya ga mutum a wurin bai yi ba, balle ya yi wani abu, ya shige ?akinsa ya nemi wuri ya zauna a kan katifa.

Babu fargabar komai, ta bi bayansa, tare da yin sallama a ?akin, bai amsa ba kuma bai ?ago ba.

Ta je gabansa, ta dur?usa da gwiwoyinta a ?asa, ta ce "Ranka ya da?e, wurinka na zo fa" ya cigaba da 'yan dube-dube.

"Duk da na san, ba zaka amsa mini ba, amma na san kana ji na, wannan zuwan da na cigaba da yi, ina yi ne don neman afuwar kuskuren da na tafka bisa duhun kai, da rashin sani, amma dan Allah ka yafe mini ka yi ha?uri dan Allah" tayi maganar muryarta na rawa.

"Dan Allah ka yi magana, wallahi na kasa sukuni, a dalilin jahiltal abun da ya sameka, ban san haka abun yake ba, ka yi magana ka ce ka yafe mini please"

Still bai yi magana ba, sai dai ya ?ago ya kalleta, hakan ya sanya ta saurin cire idonta daga nasa.

Ya mi?a mata hannunsa ya ce "Bani"

Jakarta ta ?aukko ta bu?e, ta ?aukko wayarsa, ta mi?a masa, ya saka hannu ya kar?a, sannan ya ce "Sai da nayi kaffara a dalilin rantsuwa da na yi zan kashe ki, ban kashe ki ba, ki ka sake na sake rantsewa sai na aiwatar"

"Da kuwa ka ci amanar 'yar madara"

Ayshercool
08081012143
???500 ne via 0009450228
Aisha Adam jaiz bank sai shaidar biya ta 08081012143
Wanda za su jira document 1K ne.

90009343
'Yan Nijar ku turo katin airtel na 300fcfa

Arewabooks ayshercool7724

Cikin hanzari ya kalli Nabila, yana mamakin a ina ta san wannan sunan, dan sam bai san Walid ya gaya mata labarin sa ba.

Ya ?ureta da ido, ta kawar da kanta gefe, ta ce "Eh, idan ka kashe ni, ka ci amanarta, ta barka ka kusa dawowa hanya, amma ka koma ruwa fiye da baya. Zan so na ji ?arshen labarinta, amma kafin nan bari na tafi yanzu, ga kayan dubiya nan na kawo maka, Allah ya ?ara sau?i" sai da ta gama maganar sannan ta ?ago ta kalleshi, still ita yake kallo.

Ta sake cewa "Ina fatan zaka yafe mini laifin da nayi, rashin sani ne" ta tashi a hankali ta ?auki jakarta ta fita, tana yi wa Allah godiya da wannan karon, ba ta sha sha?a ba, hakan ya sa ta ?ara kin ?warin gwiwar cigaba da gwagwarmayar da ?uduri aniya.

Bayan fitar Nabila, Viper ya ?aga kai yana kallonsu ?aya bayan ?aya, Walid ya ce "Ko ba ka yi magana ba, na san menene a ranka, ba kowa bane ba, ni ne nan na gaya mata labarinka".

Ya tsayar da idonsa a kan Walid ya ce "Saboda me?"

"Saboda dalili mai ?arfi, cigaba da cusa kanta a lamuranka cikin duhun kai, tamkar ?ara yawan matsalolinka ne, zuciyar mace ta na da rauni, fiye da dukkaninmu, ina ganin hakan zai iya yi mana am..... Bai ?arasa ba, viper ya katse shi ya ce "Ta yaya? Na ce ta yaya? Meye amfanin gaya matan, na gaya maka bana bu?atar cigaba da ganin yarinyar nan, sai an ha?a baki da ita an ?ara rusa ni kenan? Da raunin na su ake amfani a sarafasu a cuci mutum, halittu ne su marasa imani....

"Raunin 'ya mace, da tausayinta irin na halitta, kar ka manta shi ya jefa ka a cikin halin da ka ke ciki, idan mace ?aya zuwa goma sun cutar da kai, ?aya zuwa biyu sun yi maka abun da ba zaka ta?a iya biyansu ba, wanda tausayi da soyayyar da mace ta nuna maka, gi?in da ta bar maka ne, ya ?ara assasa tunzura zuciyarka ka ke fama da jinyar da muka rasa bakin zaren yi maka maganinta. Idan zaka yi adalci, ka yi musu hukunci da halin ?anwata, Jauhar ko ba dukkansu ba. Yarinyar nan gaskiya ta gaya maka, idan ka yi kisan kai ka ci amanarta, wannan miyagun ?wayoyin da ka ke ?ara ?urawa kanka, su ma ba ka yi mata adalci ba".

Al'amin da ya ji maganganun Walid sun ishe shi, sai ya mi?e tsam ya sake ficewa.

Walid ya yi wa ?an mama inkiya ya bi bayan sa ya ga ina zai yi.

***
Ramma ce take dukan gefen fion da Abdul yake "Abdulyasar Abdul yasar" ya bu?e idonsa da kyar ya kalleta.

"Ka tashi ka yi sallar asuba, gari yayi haske, sallar ma baka yi" ya ja tsaki ya sake juyawa.

Ta sake cewa "Ka tashi gari fa yayi haske"

"Kin san jiya da daddare fa ban yi bacci ba, ki ?yaleni"

Ramma ta ce "Haka ne kam, dama ba ka da lafiya, wata?ila a cikin baccin za a zare maka rai, ban sani ba ko kana da abun da zaka gaya wa Allah a kan rashin salla" kan ta rufe baki ya tashi zaune yana ?ifta ido.

Ta girgiza kai ta ce "Kai yanzu baka shirya wa mutuwa ba, ka ke rashin mutunci? Allah sarki ?an Adam abun tausayi" ji yayi jikinsa yayi mugun sanyi, kamar mutuwar ce ke tunkaro shi, ya je ya yi alwala, ya fito ya tarar tana gyara gadon da ya tashi.

Wayarsa ce ta fara ringing, ya tashi da sauri, ya ?auka, ya saka a kunnensa "Hello mummy"

"Kana ina ne?"

Ya ce "Ina gidana"

"To zuwa anjima ka zo gida, zaka yi magana da babanka, shugaban jam'iyya ya ce ka je ka ga 'yar sa, ku daidaita kanku, ayi magana dan ba za su yadda a baka takara ba, baka da aure".

"Haba mummy, aure kuma? Ni wai dole ne auren nan, a ha?ura mana"

"Ban gane a ha?ura ba, waye zai yadda ka yi deputy governor ba ka da aure, lallai ka zo anjima ku yi magana dama yana cewa ni nake hure maka kunne"

Abdul ya ce "Ba ni da lafiya fa"

"Ka sha magani ka zo, ulcer ce?"

Ya ce "Eh, kuma wallahi ina jin jiki, dan Allah ki bashi ha?uri zan zo ne"

Cikin damuwa ta ce "Ko na turo a ?aukko mini kai, ba na son ciwon cikin nan naka fa"

Ya kashingi?a ya ce "A'a, zan warware, idan na ji sau?i zan zo, sai anjima zan ?an kwanta" ya ajiye wayar. Tun da ya fara wayar, ramma ta ?ura masa ido har ya gama.

Ta ce "Ka ga banbancin rayuwar mace da ta namiji ko? Kaga duk abun nan da ka ke yi, kai an samo maka mata ni mecece makomata?"

Ya kalleta ya ce "Kishi ki ke yi ne?"

"Allah ya rufa mini asiri, na rasa a kan wa zan yi kishi sai kai, ka wula?anta mini rayuwa ka cuce ni, kai ka yi aure ka tara iyali, ni kuma babu wanda zai kalleni, ka yi mini fya?e ka mayar da ni ?aramar karuwa, har ciki na ?auka duk ta ?azamar hanya ka wula?anta rayuwata"

Abdul ya zauna sosai ya ce "Ke ki ka fara wula?anta rayuwarki, da ku ka yi yin?urin cewa zaku nemi hakkinku a kotu, alhalin ba zaku iya ja da ni ba"

"Sannu tsohon azzalumi, dama mai ku?i shika?ai Allah ya ce ya ji da?i a duniya? Yanzu duk wannan abun ta?amarka kana da ku?i ni 'yar talakawa ce? In sha Allah sai Allah ya ?as?antaka da kai da masu goya maka baya, suka tsaya maka kake rashin mutunci. Na san akwai ire-irena da yawa yaran talakawa da kuka zalunta, Allah ya na kallonku. In sha Allah sai Allah ya nuna maka iyakarka tun a duniya Abdul yasar"

Duk da ya ji zafin maganganunta amma sai cewa yayi "Ko wanda ya ra?a mini sunan nan, bai kai ki iya fa?ar sunan ba Rahama, Abdul yassar"

Kallonsa tayi tana kuka, haushin kanta yakamata da lokacin da yake waya, ba ta yi ihu a wayar ta ce a taimaka mata ba sace ta yayi. Yanzu ko wayarsa ta ?auka ba zata iya operating ?in ta ba, kuma ba ta da lambar wanda ta haddace balle ta kira.

***
Abba yana zaune yana kallon labarai a Aljazeera, Nabila ta shiga da sallama, yana kashingi?e, ya tashi zaune yana murmushi ya ce "Barrister, kin yi mini wuyar gani da yawa fa, kullum na dawo kina aiki, baki dawo ba aiki ya hana mini arfana sukuni"

Tayi murmushi ta ce "Abba ni kaina ina kewarka, bana samun zama, yanzu na shiryu ai, ina aiki sosai da sosai, na san addu'a ka ke yi mini"

Ya ce "Kullum Addu'ata a kanku take, mussaman ke arfana, Allah ya yi miki jagora a dukkan lamuranki".

"Eh mu ma Allah ba zai tagayyara namu ba" Umma tayi maganar tana harar Nabila.

Nabila ko a jikinta ta ce "Abba dan Allah abu na zo ro?onka"

Ya ce "Ina jinki ?ar albarka"

"Abba dan Allah mota nake so, wallahi wahala nake sha samun napep, ayi ta ha?ani da maza, ga zirga-zirga na yi ta kashe ku?in mota, kuma haryanzu ni ba na yi wa client ?ina charges mai yawa"

Yayi dariya ya ce "Nawa ki ka tara?"

Tayi shiru sannan ta ce "Ina da 400k"

Ya kwashe da dariya ya ce "400k, sai dai a gyara miki tsohuwar honda ta"

Cikin shagwa?a ta ce "Haba Abba, big girl kamar ni, da tsohuwar mota, ka taimaka Please"

"Babu komai, za a sai mota in sha Allah, amma da shara?i ba na son yawon babu gaira babu dalili, kuma ke zaki din ga zuba manki, ba zan sai mota na din ga cacar mai ba"

Cikin takaici Umma ta ce "Major mu fa? Muna zaune zaka saya wa Arfa mota, wannan wane irin rashin adalci ne?"

Ya kalleta ya ce "Da walida zan saya wa mota, ba zaki fa?i haka ba, ku fa da me? Ga mota nan ana kai ku unguwa a ciki, meye na kishi da 'yar cikinku? Ku daina ha?a kanku da ita, kun san abun da nake nufi".

Arfa ta tashi ta ce "Abba sai da safe" ta juya zata fita, ta yi wa Umma gwalo, a ranta ta ce "Saura ma babar su DSP idan ta ji, sai dai ku mutu".

Ta koma bedroom ?in ta tana murna, ta ?auki wayarta, Viper ya fa?o mata a rai.

Lambarsa da ta saka a wayarta, ta lalubo, ta zubawa ido, murmushi ta yi, ta kira lambar ta saka a kunnenta.

Yana zaune a kan katifa, yana ta shan sigari, zubawa lambar ido yayi, ya gaji ya ajiye wayar, ya cigaba da abun da yake gabansa. Ba ta gaji ba ta din ga kiransa babu ?a??autawa, har sai da ya hasala, ya ?aga wayar, amma bai yi magana ba.

"Har na kusa fushi sannan ka ?aga, na san da 'yar madara ce, ko ba ta san mai lambar ba, zata ?aga kuma za ta saurareni, haka zalika zata yafe mini laifin da na yi mata. Akwai abubuwan koyi sosai da sosai a rayuwar ta, da ya ci ace ko ba duka ba, ka yi koyi da wasu, ba ta wula?anta ?an Adam da tana yi, da ba ta ri?e ka da amana da tausayawa ba. Ina sake ro?onka yafiya, da kuma fatan samun ha?in kanka, ka ?arasa mini labarinka da kanka, ina sha'awar kasancewa wani ?angare na labarin nan, mai ban tausayi da ratsa zuciya Viper, sai da safe" tun da ta fara maganar, ya sunkuyar da kai, ya saki sigarin da take hannunsa, ya sunkuyar da kai hannunsa yana rawa. Ta gama maganar ta katse wayar, amma ya kasa ajiye wayar.

Sai da liti ya dafa shi ya ce "Maza yane?" Ya ?ago idanunsa ya kalli liti.

"Kamar Muryar wannan shegiyar yarinyar na jiyo a wayar, duk Walid ne da wannan she?ancin"

Ya cigaba da ?urawa Liti ido, babu abun da yake fata, banda ya zubar da hawaye ko na mintuna biyar ne, amma ko na sakan ?aya ya kasa tsawon shekarun nan.

Murya a sanyaye ya ce "Liti"

"Na'am mai zamani".

"Ina kewar jauhar sosai"

Walid da da yayi musu shiru, dan ya lura daga Viper har liti haushin sa suke ji, amma maganar da Viper yayi yanzu ta sanya jikinsa ya yi sanyi, tausayin Viper ya ?ara kama shi.

"Da yanzu yarona ya isa shiga makaranta, wata?ila ma ta kuma haifa mini wasu"

Walid ya taso, ya dawo gaban Al'amin, ya ri?e hannunsa ya ce "Ka ?ara ha?uri mai zamani".

"Zuwa yaushe? Ko na ?auki fansa kamar yadda nake buri da fata, kashe kaina zan yi saboda ba ni da wata makoma, idan kuwa hakan ba zai samu ba, zan koma in da na fito na ?arasa rayuwata".

"Dan Allah maza ka daina irin wannan maganganun, kana karya mana zuciya wallahi " liti yayi maganar cikin damuwa.

Viper ya girgiza kai ya ce "Ba zaka gane ba"

Kawai ya gyara ya kwanta, gaba ?aya suka kewaye shi suna kallonsa.

Nabila kuwa kallon wayar ta cigaba da yi, ta ce "Allah ya bani nasara a kanka, ya bani ikon taimaka maka".

Kira ne ya shigo wayarta, ta ?aga ta saka a kunnenta, ta yi sallama.

"Wa'alaikum Salam da 'yar ?walisa".

"Wa ke magana?"

Yayi murmushi ya ce "Bawan Allah ne"

"To, ai kowa ma bawan Allah ne, wanne daga ciki?"

Yayi gyaran murya ya ce "Wani case ne da ni, nake so a taimaka mini"

Nabila ta yi hamma ta ce "Office zaka zo, ba ta waya ba" ta katse kiran, dan a zatonta irin samarin nan, ne masu kiran wayar mata anyhow, duk da Muryar wannan ba ta yaro ba ce.

Wani nannauyan bacci, yayi awon gaba da ita wanda babu abun da take yi ban da mafarkin Viper, dan sai da ta kusa makara yau.

Kwanaki uku da zuwanta wurin su Viper, ba ta sake zuwa ba, she's very busy, tana ta off and down na tattara hujjoji, duk da ana ta ta?iyeta, duk in da za ta bi ta samo shaida, sai a rufe, sai da aka aike da dattijon nan gidan kaso.

Gashi sai tayi ta sintiri a hanata ganinsa.

Kamar uba da ?a haka Walid yake ta lalla?a Viper ya ci abinci, sai dai ya cakala ya bari, ba ya cin abinci.

Private numbrn nan da ake kiransa da ita ce, ta kira shi, wayar tana ta ringing liti ya ce "Maza ka ?aga mana"

"Me zan ce?"

Walid ya ce "Ko ba ka da abun cewa, ka ?aga kawai"

Ganin ba shi da niyyar ?agawar, ya sanya Walid ya ?aga ya sakata a hansfree.

"Aminu Viper, kwana biyu. Ashe ta dawo maka da wayar. Alamu sun nuna kwana biyu ka yi sanyi, Kodayake kai sai an sakankance ka ke ?arna. Garga?i nake sake yi maka, ka nesanta yarinyar nan da ga gareka, za a iya cutar da kai ta hanyarta".

"Ni nake da ikon yanke hukuncin abun da yake daidai da rayuwata, babu wanda ya isa ya juya mini rayuwa yadda nake so, ka cigaba da ?uya ko ka bayyana kanka, zan yi abun da nake ganin shi ne dai-dai da rayuwata.

Mutumin yayi murmushi ya ce "Aminu Viper, shikenan idan ka ?i ji, ba zaka ?i gani ba ai"

"Babu abun da ban gani ba, dan haka na shirya ganin koma menene" ya katse wayar.

Liti ya ce "Duk walid ne ya janyo komai, ni na san a rina, wannan yarinyar idonta kawai zaka kalla ka gane munafuka ce"

Kallon da Viper yayi masa ne, ya sanya shi yin shiru, Walid yayi dariya ya ce "Ayi dai mu gani, za a gane waye mai gaskiya tsakanina da ku".

Liti ya ce "Ba wata gaskiya da ka ke da ita, ka dakatar da mu daga making moves, wallahi mun kusa fita operation kwanan nan"

"Ku fita ya?i ma ba operation ba"

Haka liti da Walid suka kusa yin fa?a.

Tun ana gobe Nabila zata je wurin Naja'atu Bunkure, suke waya da sumayya, take bata ?warin gwiwa, a kan za ta iya, kar ta ji tsoro.

Da safe sai da ta fara zuwa wurin aikinsu, ta samu barrister Habib, shi ma ya ?ara mata ?warin gwiwa, da yi mata fatan alkhairi.

Cikin ?asaita take fiya a farfajiyar office ?in, har ta ?arasa, mutane ta tarar jingim. Wanda galibin su mata ne, suna jiran shiga wurin Barrister Naja'atu Bunkure.

Kai tsaye Nabila ta shiga wurin sakatariyarta, ta nuna mata ID card ?in ta, nan da nan ta bawa Nabila wurin zama, na ciki na fitowa ta yi mata iso zuwa wurin Barrister Naja'atu.

Tun a hanya take maimaita "la hula wala ?uwwata illa billa". Har ta shiga wurin Bunkure.

Tayi sallama, ba tare da ta ?ago ta kalli Nabila ba ta amsa mata, ta ?arasa ta zauna ba tare da an yi mata umarnin hakan ba.

Kayan jikin Nabila kawai ta kalla, ta fuskanci ba kalar gajiyayyun da suke zuwa wurinta bane ba.

Ta gyara zaman gilashin fuskarta ta na kallon Nabila.

"Sannu da aiki ma" Nabila tayi maganar tana murmushi.

"Yauwwa sannu"

Nabila ta ?aga mata id card ?in ta ta ce "I am barrister Nabila Yusuf maitama"

Bunkure ta jinjina kai ta ce "You look familiar to me"

Nabila ta jinjina kai ta ce "Na yi mamaki ma, da ki ka iya tuna kamar kin sanni, saboda na san jama'ar ne da yawa. Ni abun da ki ka yi mini ba zan ta?a mantawa ba har abada"

Bunkure ta ce "Ohh really"

"Yeah and i have a promise to fulfil, a dalilin abun da ki ka yi mini"

Ta kashingi?a da jikin kujerarta ta ce "That's very good, ina son mutane masu yarda da kansu, ba na bu?atar sanin me nayi miki, ko kuma wani alwashi ki ka yi ba, ga ki ga bunkure Allah ya ida nufi "

Nabila ta ce "Na ji da?i da ki ka ce Allah, dan kuwa shi ne gaba da komai, na gode sosai barrister"

"Mentioned not"

Nabila ta gyara zamanta ta ce "Yauwwa, ba komai ne ya kawo ni ba, na zo ne a kan wani case, duk da ba mu ha?u a court ba, an kai wanda nake depending prison, amma ban ganki a court ba sai wakilanki"

Bunkure ta ?arewa Nabila kallo, sannan ta ce "Wane case ki ke magana a kai?"

"Yarinya da aka yi wa fya?e, ki ka ce kin tsaya mata, ni ce lawyer wanda ake ?ara, na je wurin 'yan sanda ana ta yi mini yawo da hankali, ina son doctors report, kuma ina son zan ga yarinyar zan yi magana da ita".

Naja ta yi wa Nabila kallon baki da hankali sannan ta ce "Kin san a gaban wa ki ke?"

"I am barrister Nabila, ba ruwana da a gaban wa nake, ina neman hujja ne da zan kare client ?ina"

"Nawa suka baki, ki ka samu ?warin gwiwar yin wannan kasadar? Zan ninka miki, ki ajiye case ?in, kafin ki kunyata a idon duniya "

"Watch your words, it can be use against you a kotu, kin san me nake nufi, you are also a lawyer"

"Who the hell are you?" Bunkure ta yi maganar tana tashi tsaye, Nabila ma ta tashi tana sake ?aga mata id card ?in ta "Sai da na fara gabatar miki da kaina, sannan na gaya miki meya kawo ni.
Ko dai ki bani abun da nake bu?ata kawai, ko kuma na fasawa duniya wacece ke?"

"Ni ?in? Yaushe ki ka yi grduating, da me ki ke ta?ama ki ke jin karanki ya kai tsaikon da zaki tunkare ni kina gaya mini maganar da ki ka ga dama?"

Nabila ta girgiza kai ta ce "Cikin dukkanin girmamawa ta seniority a aiki, nake fa?ar duk abin da nake magana a kai. You were my mentor before, abun da ki ka yi mini ya tabattar mini you are green snake under green grass. Keep your eyes open, Barrister bunkure, zan iya baki mamaki a lokacin da baki zata ba. Zan cigaba da bibiyar case ?in ramma, da ?o?arin wanke wanda nake karewa har sai na yi exposing ainihin gaskiya ko da kuwa ita ce ajalina" tun da ta yi face to face da ita, ta ji duk wata fargaba da tsoron da take ji sun kau.

Ta ?auki jakarta, ta fita daga office ?in.

Tsaki Bunkure ta yi ta daki tebur, ta ?auki wayarta, ta danna ta kara a kunnenta.

"Yauwwa barrister Kabir ya kake?"

"Lafiya ?alau manyan ?asa ya aikin?"

"Normal ne, wacece Nabila a ma'aikatanka?"

Ya ce "Lafiya kuwa? Ya aka yi ki ka santa?

"Wacece ita, a id card ?in ta na ga a wurinka take aiki"

Ya ce "Barrister Nabila, a law firm ?ina take".

"Ta zubawa kanta fetur a jiki, tana kuri, idan na ?yatta ashana, ba ita ba har kai, zaka ?one ?urmus ka ja mata kunne, ?era ba ya taka rawa a gaban mage, ko da kuwa tana kan gargara ne"

Kabir ya ce "Subhanallah, me ta yi?"

"Ka bincike ta, ba na bari ayi mini kuskure biyu, ko yin?urin yi aka yi, ina da?ile duk wani abu da zai kawo mini cikas".

Kabir ya ce "Na fahimta, ki yi ha?uri dan Allah zan yi magana da ita, zan kuma ja mata kunne" ta ajiye wayar tana tsaki.

Cike da annashuwa ta fito daga wurin, tare da jin kanta tamkar ta yi facing ?in babban abun tsoronta.

Ta tsaya a gefen hanya, ta ciro wayarta, ta kira Viper, ya ?aga sai dai bai yi magana ba.

"Hello, ya jiki? Na san ba zaka yi magana ba, dama so nake na ji ya jikinka, na so zuwa na ganka amma rana tayi sosai, zan je wani wuri ne, ka kula da kanka sosai" ta katse wayar, ji yayi tamkar ya aikata wani uban zunubi, ya din ga bin wayar da kallo, yana tunanin yarinyar nan tana da hankali kuwa?.

Gida ta tafi cikin matsanancin farinciki, duk da

Please Login or Register in order to submit comment