Reading KARFE A WUTA Chapter 123 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ka ce ya tafi a banza" Bunkure ba ta iya mayar da martani ba, aka zunku?ata cikin motar masu laifi, aka tafi da ita.

*****

Duk ?umbiya-?umbiyar da ake yi, da ?o?arin rufe abin da ya faru, sai da abun ?oye ya bayyana na kama Indabo da miyagun ?wayoyi a ?asa mai tsarki.

Ramma tana zaune a falo, tana assignment, Abdul ya shigo babu ko sallama, ya wuce ?aki.

Ta bi bayansa tana fa?in "Yau kuma waye ya ta?o mini bokan turai" idanunsa ne suka tabbatar mata akwai damuwa gagaruma.

"Doctor meyafaru kuma? Wani abin ne ya faru?"

Ya ha?iye wani abu mai ?aci, ya dubeta ya ce "Daddy aka kama a Saudiyya"

Ramma ta ce "Subhanallah, me ya yi aka kama shi?"

"Da miyagun ?wayoyi aka kama shi, abin takaici wai a ?asa mai tsarki"

Ramma ta ce "Subhanallah, abin bai yi da?i ba. Addu'a ce yanzu ya kamata ayi, Ubangiji Allah ya fitar da shi"

Ya kalli ramma idonsa fal hawaye ya ce "Allah ya fitar da shi how? Saudiyya ba fa Nigeria ba ce ba, duk laifukan da yake aikatawa ba su isa ba, sai ya tsallaka ?asa mai tsarki?. Har tsoro nake ji, ko idan ya koma ga Allah idan na ro?a masa rahama Allah zai kar?a? Tarin mutanen da zalunta saboda kujerar nam, a ina zai gansu ya nemi afuwarsu? Ni iyayena ne jarrabawata, da ina da iko, da ban zo a tsatsonsa ba"

Cikin kulawa ramma ta fara rarrashin da bai kai zuciyarta ba ta ce "Doctor, ba a yanke tsammani da rahamar Allah, kuma shi mai rahama ne, dole a ro?a masa rahama tun da musulmi ne"

"Amma kin san Allah baya yafe hakkin wani a kan wani ko? Yau ko tuba yayi ya daina laifukan da yake yi, wa?anda ya zalunta fa wasu ba sa duniyar nan, sun bar ta, a wurin wa zai nemi yafiyar? Mutanen da ya dasawa damuwa da ba?in ciki su na da yawa fa.
Allah mai rahama ne da jin ?ai, amma sai da ya haramta shi a kan kansa, sannan ya sanya shi abin haramtawa a tsakaninmu, ke ki ka biya mini wannan hadisin, ni babu wani abu da za a gaya mini yanzu na ji sanyi, ina tausaya masa ha?uwarsa da Allah"

Jiki a sanyaye ramma ta ce "Ka yi gaskiya, amma yanzu ai ba mutuwar yayi ba"

Ya kalleta fuskarsa duk hawaye ya ce "Kin san hukuncin ace an kama mutum da irin abin da aka kama shi da shi a ?asa mai tsarki? Muddin suka tabattar hukuncin kisa ne" gaba ?aya sai ta rasa me ma za ta ce. Har ga Allah Abdul ya bata tausayi, amma ita ba ta ji ta damu ba ko ka?an, albarkacin Abdul ?in ne ma bai sanya ta ce Allah ya ?ara a zuciyarta ba.


****

Hafsa ta biyo Alhaji mu'azzam, domin kawo ziyara gida, sai dai ta tsorata da yadda ta ga jikin mama ya ?ara tsananta, ta zama wata irin miskiniya abin tsoro.

Sai dai ta tsorata da ganin ita ma tata mahaifiyar ta yi wata irin muguwar rama, gashi duk kau?inta yanzu ba ta son yin magana.
Ga zaman ?aki, cikin mamaki take tambayarta ko lafiya?

Ta fashe da kuka take gaya wa Hafsa abin da yake faruwa.


Tayi shiru sannan ta ce "Ikon Allah, kin ga ka?an daga illar biye-biye anty, yanzu an ce Anty Rahila tana gidan masu rangwamen hankali, ni na fara yin ciwon hauka a sanadin shaye-shaye, ke ma kuma ga alamu"

Ta waro ido ta ce "Hauka kuma?"

"Eh matsalar ?wa?walwa, wannan alamomi ne na depression"

"Wallahi na yarda da maganarki, wasu lokutan ji nake kamar na fita da gudu ina ihu, duniyar tayi mini zafi, amma ni sai nake tunanin ko matar nan ce duk da tana kwance, ta ha?a kai da yaranta suke banko mini asiri"

Hafsa ta katseta ta ce "Mama babu wanda yake banko miki wani asiri, ganin Jauhar da mahaifiyarta da ki ke yawan yi, yana alamta miki, kin tafka mummunan laifi a rayuwarki, da babu lallai sun yafe miki, gashi ba sa duniyar. Shawara ?aya zan baki, ki din ga yi musu addu'a, sannan ki dage da istigfari kuma ki daure, ki nemi afuwar Baba, sannan ki nemi afuwar ?an uwanta babansu Nabila, da ita kanta Nabilan, tun da duk su na da ala?a da su, idan ki na so ki samu nutsuwa. Sai kuma mu dangana da asibiti ki fara ganin likita"

"Tab?ijan, kawai kuma sai na je ina cewa wani su yafe mini, da na yi musu me? Wallahi ba zani ba"

Cikin takaici da mamaki, take bin Antyn da kallo, ta ce "Ba zaki ba Anty, sai abin da ya samu babar su Shahida ya same ki tukuna?"

"Ya da?e bai same nin ba, ba zani ba, ni na san asiri kawai ake yi mini, kuma ni dai-dai nake da kowane mara mutunci" Duk yadda hafsa ta so ganar da ita, ta rufe idonta ta?i ganewa.

"To mu je asibiti, tun da nima kin ga da haka na warke, da aka din ga kai ni Asibiti"

"Ba zani ba shi ma, ni na san maganin matsalata" haka Hafsa ta ?yaleta, dan babu yadda ta iya da ita".


Washegarin zuwanta ta tafi gidan Nabila, tayi sa'a Sumayya ma tana can, ha?uwar ta su ta yi musu da?i, sai dai a kallon farko ta ga Nabila ta rame sosai, ba ta yi magana ba, Nabila nata nu?u-nu?u da hijjabi, amma sai da Hafsa ta gano ta.

"Abla, wai me ki ke ?oyewa ne? Duk ?oyonki ana gani ai"

Kunya ta kama Nabila ta ce "Ake gane me?"

"?an baban mana"

Sumayya ta kwashe da dariya ta ce "Ai na gaya mata ana gani, ta?i yadda, mai cewa sai ta yi good 2yrs a gidan miji, kafin ta ?au ciki, amma farawa da bisimillah"

Hafsa ta kwashe da dariya ta ce "Ai kura ta san gidan mai babban sanda, ai ita ta san in da za ta iya cewa, sai ta shekara biyun ba ta haihu ba, ba dai a gidan Viper ba"

Nabila ta ce "Baku da aikin yi ne, ulcer ce ta kumbura mini ciki"

"Viper dai yayi ajiya, shi ya kumbura miki cikin" Hafsa tayi maganar tana dariya.

"Ku da Allah, kuna munafuncin mijina a gabana, wanda idan yana nan, ko tarin kirki ba zaku iya ba, a ?yale mini shi kar a saka ya ?ware, yana can yana aiki, kuna nan ku na gulmarsa"

Hafsa ta ce "Ke abin alkhairi ne ai, Ubangiji Allah ya inganta miki ?anwata, ya rabaku lafiya"

"Amin Anty hafsyna"

Sumayya ta ce "Shahida ma na ga kamar an gamu"

Hafsa ta ce "Nima ma gani, ai na je gidanta"

Nabila tayi dariya ta ce "Mijinta ce mini yayi baya son saka ido mura take yi" suka yi ta hirarsu gwanin sha'awa, hafsa ta ce "Dan Allah ku tayani da addu'a, nima Ubangiji Allah ya sa ina da rabon ganin jinina a duniya, ni haryanzu shiru" suka yi ta kwantar mata da hankali da yi mata fatan alkhairi.

Aka koma maganar bikin Sumayya, Hafsa na ta ?ara nanata mata, kar ta kuskura ta je ta sha wani abu da ba ta san menene ba, alhalin ga likitar mata.

Nabila ta ce "In dai ki na son daga shiga kema ki ?aukko magana, ki ri?e wa kayan likitar mata wuta, zaki gane baki da wayo, laulayi is not your mate "

Hafsa ta ce "Rabu da ita, ta ji da assignment ?in da Viper ya bata"

Nabila na daga kwance a kan cinyar Sumayya ta ce "Wuta balbal idan aka ?ira sunan mijina"

"An fa?a Aminu Viper, mai zamani"

"Ku da Allah"

Nabila ta dage ta din ga lalla?a hafsa, sai da ta kira Alhaji mu'azzam, suka kwana a gidan.

Ita dai kaf 'ya'yan babansu, da aka nuna mata, babu wanda take jin tana so, kamar hafsa, ita dai tana ?aunarta sosai.

Sai kuma suka koma hirar ?alubalen rayuwar gidan auren, tare da ba wa junansu shawarwarin da za su fishshe su.


Kwana biyun da suka yi mata ta ji da?i sosai, bayan tafiyarsu zaman ka?aicin ya ci gaba da damunta.

Babu tsammani taga Viper ya dawo, aikuwa ta ji da?in hakan.

"Vi ya na ganka ka dawo yau?"

"Shi ne lokacin da aka ce ki fara zuwa awo, ina lissafe ni ai"

Tun daga Abuja ya taho mata da amala, saboda ya san tana sonta, aikuwa ta ji da?in amalar nan.

Ta ci ka?an ta ga tayi awa biyu ba ta yi amanta ba, aikuwa ta rufar mata, ta cinye tas.
Kwana tayi amai, ba ta yi baccin kirki ba.

Da safe ya buga wa Abdul waya, ya ce masa zai kawo Nabila asibiti, ya ce masa to.

Abdul ya yi mamki, ganin cikin Nabila wata hu?u, amma ya ?ago sosai.

Suka gaggaisa, ya yi mata sannu.

Viper ya ce "Ya ?anwata?"

"Tana gida sun yi hutu, ga sa?o ma ta bani, wai na kawowa yayarta" yayi maganar yana nuna musu fulas ?in abinci.

"Ko menene a ciki, in dai yaji yayi yawa ba zaki ci ba, bar rawar jiki" yayi maganar yana harar Nabila.

Tashi Nabila ta yi, ta bu?e flask ?in, ?amshin miyar jajjage ya daki hancint, tayi maza ta rufe dan da alama miyar mai yaji ce.

Abdul ya ce "Ina ce mata zaku zo, ta zaunar da ni sai na taho miki da abinci"

Viper ya ce "Duk in da muka je, har rawar jiki take ace mata ga abinci, kamar ba na ba ta abinci a gida"

"Bana ?oshi ne" tayi maganar tana dariya.

Abdul ya ce "Maybe na gidanta ba ta iya ci, idan suna irin wannan halin sai ha?uri ai"

Viper ya ce "Haka ne, amma ya na ganka wani iri, ko baka da lafiya ne?"

Bai ?oyewa Viper ba, ya gaya masa komai, Viper ya ce "Irin haka sai ha?uri, kuma ka ci gaba da addu'a, kuma kai ka kiyaye aikata makamantan laifukan da ya aikata"

Kalaman Viper dai babu tausayawa ga Indabo, amma rarrashi ne ga Abdul.

?akin scanic suka tafi, bayan an yi wa Nabila gwaje-gwajen masu ciki.

Viper yana tsaye a kan Nabila, yana ri?e da hannunta.

Abdul yake gaya wa Viper, doctor Muktar ya tafi ?aro karatu malesia.

Abdul yana cikin maganar ya yi murmushi, ya kalli Viper ya ce "Congratulations bani goron Albishir"

"Albishir ?in me? Bayan dama can na san da akwai cikin?"

Abdul ya ce "Ba zan fa?a ba ne, sai ka bani tukuici"

Viper ya ce "Fa?i sai a baka"

"Na?i wayon, kawo kawai"

Viper ya yi murmushi ya zaro dubu ?aya ya ajiye masa ya ce "Fa?i idan yayi mini sai na ?ara maka"

Abdul ya ce "Ai kai ne mayar da tukuicin, ai albishir ?in namu ne gaba ?aya. Twins ce dama ita ai ko?" Viper ya jinjina masa kai.

"So congratulations, babynta biyu ne a cikinta, twins ne yaran"

Waro ido Viper ya yi yana kallon screen ?in injin scanic ?in, tamkar zai gane menene a jiki.
Jikinsa ya hau wata irin tsuma ya ce "Dan Allah da gaske ka ke ko da wasa?"

"Yaya zan yi maka wasa da abu mai muhimmanci har haka? Wallahi da gaske nake, twins ne, kuma duk su na cikin ?oshin lafiya"

Viper ya mi?e ya yi sujudar godiya ga Allah, ya mi?e ya rasa me ma zai yi ko ya ce.

Ya kwance agogon hannunsa, ya ajiyewa Abdul, ya zaro ?aya daga zobensa na azurfa shi ma ya ajiye masa.

Ya fara laluba aljihunsa, Abdul ya ce "Haba Viper, yanzu mun zama ?aya sirikina ne fa kai, ina tayaka murna, Allah ya inganta ya raba lafiya, amma ku yi shiru kar wanda aka gaya wa biyu ne. Ga agogonka da zobenka ba zan kar?a ba"

Viper ya yi ajiyar zuciya ya ce "Kar mu yi haka da kai, yarana biyu na rasa, ?aya aka yi ?arinsa, ?aya kuma bai ma zo duniyar ba, yanzu Allah ya ha?a mini biyu. Na ma rasa wane irin farinciki zan yi ne, ba kai ka bani ba, sa?on kawai ka gaya mini, amma ba ka ji zuciyata ba, Alhamdilillah ala kulli halin.
Na rasa jauhar, ga Nabila, na rasa yarana ya bani biyu Allah Alhamdilillah. Yayi maganar yana goge ?walla.

Jikin Abdul ya yi sanyi, da ya tuna babansa ne silar ajalin matar Viper.

Ya tuna lokacin da yake yi wa Viper kallon ?an jagaliya, ?an maula ?as?antaccen mutum da yake zuwa maula wurin mahaifinsa, yau gashi Allah ya canza komai, ya nutsu ya zama mai bayar da gudummawa ga al'umma.

Ya ?arasa ya ?ago Nabila, yana mata sannu.

"Abincina" tayi maganar kamar ?aramar yarinya tana kallonsa.

"Ai dole ma a ?aukko abincin nan Abla"

"Kuma ka gaya musu su daina damuna, ko in ?i haifarsu"

Cikin murmushinsa da yake ?ara masa kyau ya ce "Za su daina in sha Allah"

Abdul ya ci gaba da yi musu fatan alkhairi, da taya su murna.



Tun da suka koma gida, duk in da Nabila ta yi sai ya bi ta da kallo, yana tunanin yara biyu ne a cikinta.

Addu'a ya din ga yi, Allah ya sa yana rabon da ganin yaran, tare da yi musu fatan shiriya tun kafin su zo duniya, da fatan Allah ya sa kar laifukan da ya aikata su shafi yaransa.


Nabila tunani ta din ga yi, na abin da za ta yi, da zai wayar wa da al'umma kai, a kan muhimmancin neman 'yancinsu, da ?ir?iro abubuwan da za su taimaka wurin ?a?i da harkar daba da shaye-shaye da kuma bangar siyasa.

Yanayin shirin bikin Sumayya da suke yi, ya hanata zama su tattauna yadda yakamata, ta na son ta yi magana da Viper ma, domin za ta so goyon bayansa ?ari bisa ?ari a kan abin da take ?udurin yi ?in.


Aka yi taron bikin sumayya lafiya, aka gama lafiya, ita ma mijinta mutum ne mai rufin asiri, ya na da mace ?aya da yara uku, cousin ?in Alhaji mu'azzam ne, shi ne ya ha?a shi da ita ma.

Major yana ta mitar Nabila kwana biyu ba ta zuwa gaishe shi, ya kirata ya ce mata shi zai zo ya ganta, amma ta ce masa ba ta nan, sai dare zata dawo.

Bayan sallar isha'i kuwa sai gashi shi da Anty, tun da suka zo ta manne a wuri ?aya ta ?i tashi.

Viper ya yi wa Major zancen rabon gadon Jauhar, za a sayar da kayanta, Nabila ta ce ba ta son kaya.

Abba ya ce "Ni idan an yi wa kayan ku?i a bani na saya, sai mu bayar sadaka Allah ya kai mata ladan".

Viper ya ce "Ita ma ta ce ku?in, ayi wani abu da su, Allah ya kai ladan kabarin Jauhar"

Major ya ce "Hakan ma yayi kyau, amma a ajiye wani abu da za a din ga tunawa da ita dai"

"Eh in sha Allah, ko ma muje gidan tare, sai na yi wa Baba magana muje a duba"

Major ya ce "Duk yadda ka yi yayi, Allah ya saka maka da alkhairi kai ma, Allah kuma ya ?ara bamu ha?urin rashin Jauhar da mahaifiyarta"

Har suka gama abin da za su yi, Nabila ta?i yi musu rakiya, sai Viper ne ya raka su, suna tafe a hanya Major yake mitar Nabila duk ta zama so silent, ko dai akwai wani ne da take ?oyewa.

Anty ta ce "Ciki ne fa da ita, take ta wannan nu?u-nu?un"

"Kaii ciki, tun yanzu?"

Anty ta ce "Ahh ikon Allah, wata nawa da yin auren?"

"Lallai Major, wato Arfa ce 'ya, mu a shekara nawa muka haihu?"

Ya ce "Ai ku tun zamanin baya ne, ita kuwa kamar yayi wuri, haryanzu ?an?antarta nake gani"

"Shekara ashirin da shida?"

"Eh mana, rainon ciki akwai wahala, kin ga ita ga ba uwa, ku ba tayi sakewar da za ta tunkaroku da wannan maganar ba, balle ma idan wani abin ne ku taimaka mata ba, bari na koma gida, zan kirata a waya, ko da wani abu da take bu?ata"

Waro ido ta yi ta ce "Sai ka tambayeta a kan cikin?"

"To shi ne me? Ni uwar ni ne uban, ai cikin halak ne, mijinta ba mazauni ba ne ba, cikin fari ba ta san kan komai ba"

"Amma ai ka bari mu mu tambayeta ko"

"Tsakaninki da Allah yaushe rabonki da ita, ban da yau da na ce ki zo ki rako ni wurinta? Ni ba abin kunya ne a wurina ba, idan ta kama na dawo da ita gida, gani gata magajiya ta din ga kula mini da ita, ba ruwanku" Anty ta ja bakinta ta tsuke, dan ba ta ga tsari a hakan ba.

Aikuwa kamar yadda ya fa?a, hakan aka yi, bayan ya koma gida ya kira Nabila yake tambayarta. Kasa ba shi amsa tayi, ta ji tamkar ta nutse a wurin, saboda kunya.
"Idan kin san akwai matsala, ni sai na yi wa mijin naki magana, idan baya gari ki taho gida, ko na turo miki magajiya, ta din ga kula da ke"

"Abba yana kula da ni, baba Magajiya kuma yakamata ace zuwa yanzu ta huta ita ma, ina iya yin komai ma"

"Kin tabatta?"

"Eh Abba"

"Arfa ba na son kawaicin nan naki, Ni babu kunya a tsakanina da ke, baki da uwa a raye, kar ki bari wani abu ya shige miki duhu, idan ba zaki iya kirana a waya ba, ki yi mini message kin ji ko?"

"To Abba"

"Allah ne mai komai, amma ba zan so ki sha wahalar da mahaifiyarki ta sha ba"

"In sha Allah"

Ya ce "Yauwwa, sai da safe, ki gaida mijin naki, Allah ya yi muku albarka gaba ?aya"

"Amin mun gode, ayi wa Anty ya ta je gida" ta kashe wayar, Viper ya na kusa da ita, ya na saurarenta.

"Abla" ta waiwayo ta ce "Na'am"

"Kowane dangi, idan aka samu irin Abba ko guda ?aya ne, mai jajircewa a kan zumunci, ba tare da kallon ?ora wa kansa ?awainiya ne ba, da an rage wani abin. Mutum ne mai zafi, amma jajirtacce ya san abin da yake yi. Ke ka?ai sada?atul jariya ce a gare shi ko bayan ransa. Banda ladan zumunci hatta taimakon da ki ke yi wa al'umma yana da lada. Kin tsayawa dattijon nan babu ko sisi, kin tsaya wa rahama, kin tsaya mini duk babu ko sisi, kin siffantu da wasu daga cikin kyawawan ?abi'unsa, da shi da Alhaji mu'zzam, da Walid da liti, mutane ne da al'umma ke bu?atar irin su."

Nabila ta ?ata fuska ta ce "Ban da liti dai"

"Haba masoyiyya, ya fa baki ha?uri. Wallahi Abdallah mutumin kirki ne fiye da yadda ki ke zato, kawai dai mutum ne da babu ruwansa da kara, zai yi abin da yake so ne, ko yayi maka da?i ko ya kashe ka, bai damu ba"

"Ai na ga alama, ni fa ban ta?a zaton ya na barkwanci ba, ranar da na fara ganinsa, a tal'udu wurin da yake sayar da katin waya, amma kayan maye yake sayarwa, sai da na tsorata.
Babu alamar ?igon imani a tattare da shi, sai fa da ya ce sai ya kashe ni, idan na sake zuwa"

"Wallahi ba haka yake ba, sharrin ?waya ne kawai da kayan maye, Allah dai ya ?ara shirya mu, rayuwa duk ta fi yi mana da?i a yanzu. Mutane kowa yana sonmu, yana son ha?a ala?a da mu, har ana ?ora mana wasu nauye-nauye.
Duk a baya, mu kanmu bamu jin cewa, a duniyar da mutane suke muke, hango duniyarmu muke yi daban, saboda kowa kallon mutane marasa amfani yake yi mana. Marigayiyya ce ta fara ?o?arin ankarar da mu, muhimmancinmu a cikin al'umma."

Nabila ta jinjina kai ta ce"Jauhar ta yi namijin ?o?ari ?warai da gaske, kuma in sha Allah, yana daga cikin abin da na ?udurce a zuciyata, ci gaba da ya?i da shaye-shayen miyagun ?wayoyi, ta hanyar nuna wa wanda suka tsinci kansu a harkar, su ma 'ya'ya ne, kuma akwai amfanin da za su yi wa al'umma.
Ina son da ni da kai, sa sumayya, barrister Habib, da wanda suka kamata, mu ga abin yi, idan ta kama ko ?ungiya ce mu kafa, ko mutane goma ne suka shiryu a sanadinmu, mun yi nasara"

"Duk a bar wannan maganar, sai Allah ya saka kin sauka lafiya, sai ayi ta, tunani mai kyau sosai da sosai. Sumayyan nan taki ma 'yar aljanna ce da yardar Allah, na ga tana yinki saboda Allah"

"Ko ba Sumayya ba, ba ka ga Abba ne yayi waliccin aurenta ba ma, ?awar amana kenan, ina alfahari da ita"

Haka Viper suka ci gaba da tattaunawa da shi da abar ?aunarsa.


Kwanci tashi asarar mai rai, cikin Nabila ya yi watanni shida, amma kamar zata haihu a lokacin, saboda girma, hakan ya saka ta daina fita gaba ?aya, saboda nauyin cikin.

Shahida kuwa matar Walid, ta fita nauyi, dan ita nata ya kusa shiga watan haihuwa.


Ramma na gida ta dawo daga makaranta, tana ta sauri ta gama abin da take yi, ta san Abdul ko ya dawo, ko ya aiko a ?aukar masa abinci.

Kiran waya ta gani, da ba?uwar lamba, ta ?aga tare da yin sallama.

"Matar doctor Abdul ce?"

"Eh nice"

"Ok, dan Allah maza ki taho Asibiti, Doctor ne ya yanke jiki ya fa?i"

"Innalillahi wa Innalillahi raji'un" ta furta jikinta yayi wani irin sanyi.




Ayshercool
08081012143
https://chat.whatsapp.com/Jw9x9Jylpwo65O7OXBCVvL

Kunaneman group din dazakuringa sarin kayan kitchen afarashin sari yanda duyanda zaku karade kasuwa bazakusamu kasa d farashinmuba!!! Kuyi joining a mai nono kitchen utensils and household domin siyan dai dai ko sari dukkanin kayanmu available ne kuma farashi daidai aljihunku siyan nagari....maida kudi gida...gaskiya d amana sune takenmu!!! Zaku iya tintibarmu t wnn number 09135298054


Jikin ramma tsuma ya din ga yi cikin matsanancin tashin hankali da damuwa, fargabarta Allah ya sa ba wani mummunan abin ne ya faru da shi ba, dan kuwa yanzu a duniya tana matu?ar bu?atar Abdul a cikin rayuwarta.
Ko rasa shi tayi, ta san abu ne mai wahala samun mijin da zai tsaya a kan lamuranta kamarsa.

Hijjabi kawai ta zura ta fice daga gidan ta tafi asibitin da ya ce mata zai je ganin marasa lafiya.

Har an bashi ?aki, yana kwance ana ?ara masa ruwa. Cikin tashin hankali da damuwa, take tambayar meyasame shi.

Wani likita yake yi mata bayani "Bamu sani ba, ya gama ganin marasa lafiya, aka kira shi a waya, ba mu san me aka ce masa bai fi mintuna sha biyar ba ya fa?i, amma ya farfa?o ?azu har yake ta kiran sunanta, aka yi masa allurar bacci.

Ta ?auki wayarsa, ta saka thumb print ?in ta, ta bu?e wayar.

Call log ?in sa ta duba, ta ga wanda suka yi waya ta ?arshe da shi Honorable speaker ta gani.
Ta kalle shi, ta san ba zai wuce a kan maganar mahaifinsa ba ne ba.

Tausayin sa ya kamata, ta matsa kusa da shi tana shafa kansa, yanzu da ya nutsun nan, har wani kyau ya yi na musamman.

Rashin ji da gagara ba su da wani amfani.

Aka kira sallar la'asar, ta shiga ban?aki ta yi alwala, tana fitowa taga Mummy da Anty Jidda a ?akin.

Mummy ta ce "Ga shai?aniyar yarinyar nan"

Jidda ta kalli ramma, yarinyar da take mata aiki, wahalalliyar 'yar ?auye tayi ?iba, fatar nan tayi kyau.

"Ramma, ke nake gani haka?"

Ramma ta dake ta ce "Eh, nice anty Jidda, kin yi zaton tozarcin da ki ka yi mini Allah zai wula?anta ni ne? Ai shi Allah yana kishin bawansa"

"Ramma ni ki ke gaya wa haka?"

"Ai ba tun yau ba, na da?e ina fatan Allah ya ha?a ni da ke, na gaya miki abin da yake raina. Duk bauta da wahalar da nake yi miki da yaranki, iftila'i ya same ni a gidanki, ki nuna baki sanni ba, in ha?u da ke ma, ki ka toshe kowacce irin kafa, ki ka wula?anta ni, aka hana mu shiga gidan ma, babu wata magana mai da?i ko rarrashi, saboda ni baitil mali ce mara galihu. To da yake shi Allah ba yadda ba ya juya lamuransa ai yanzu ku na gani, ko iftila'in zawarci ma ya ishe ki"

Bu?e baki suka yi su na kallon ramma.

Ko a jikinta ta sake cewa "Wallahi darajar mijina ki ka ci anty Jidda, amma niyya na yi na ro?i Allah ya sa yi wa 'yar ki abin da aka yi mini, a kan idonki ki ji abin da ni da uwata muka ji, sai dai kash ?addara ta riga fata, yaranki ba su suka yi mini laifin ba, kuma wanda ya yi laifin ya yi tuba na ha?i?a, kuma na yafe masa har gaban abada, amma ba dan haka ba ba zan gushe ba ina yi miki fatan Allah ya jarrabeki ke ma, ko alhakin mai gadinki da aka kashe, ya isheku nauyi".

Mummy ce ta fara zage-zage, ramma kuwa ta tayar da salla, tare da jin sassauci a zuciyarta ko ba komai yau ta amayar da wani abu da yake ci mata zuciya.

Wani likita ne ya zo yayi musu magana, a kan ko su yi shiru

Please Login or Register in order to submit comment