Reading KARFE A WUTA Chapter 62 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

murmushi, itama murmushin ta yi, ta ce "Yan garinmu za su ji da?i, mun gode Allah ya saka da alkhairi, mun gode sosai, yan garinmu mun da?e muna koken rashin hanyar nan, amma ba ayi mana ba, mun gode"

"Yau ba Allah ya isan?"

"Ai wancan abun da ka yi mini daban, wannan ma daban, amma Allah ya isa tana nan"

Abdul ya yi ajiyar zuciya ya ce "Ki yafe mini mana sweetheart "

Ramma ta ce "Ka mayar da ni wurin mahaifiyata, ka nemi afuwarta, amma haryanzu a zuciyata ban ji zan iya yafe maka ba, daga kai har anty maijidda, da wannan bayahudiyar matar"

Yayi shiru ya sunkuyar da kai, zuciyarsa babu da?i, ta ?aga kai ta kalli fuskar sa, ta ce "Oho, ba zaka bani tausayi ba, ka tuba ga Allah ka gyara halayenka, dan ka samu kyakkyawar makoma. Ka cigaba hannun ya fara zafi" bai ce mata uffan ba, ya cigaba da shafa mata hannun.

Ta saka ?aya hannun ta juyo da fuskarsa, taga idanunsa sun yi ja, sun bayyanar da tsantsar damuwa.

"To meye kuma?" Ya girgiza kai alamar babu komai.

"Ka tabattar?" Ya jinjina mata kai alamar eh.

"Shikenan, to kayi ha?uri dai, ni gaskiyata na gaya maka, baka san zafin abun da ka yi mini bane, amma naga kamar ka ji haushi"

"Meyasa zan ji haushi, carbi zan sayo ki zauna ki yi ta jan Allah ya isan son ranki" ta murgu?a masa baki, ta kawar da kanta gefe.

***
Madaki ya zuba wa cinyarsa ido, yadda ciwon da Viper ya ji masa yayi wani irin mugun rami, maimakon ya yi ja ma, sai ya koma yayi kore, wasu irin jijiyoyi duk suka ?a??aga a gefen ciwon, ?afar ta ?ara ri?ewa, ba ya iya takata sai dai ya dinga jirgata.

Ya kalli babban amintaccen yaronsa ya ce "Lakwari, ciwon nan fa cigaba yake yi, kenan ta tabatta alkadarina ya karye?"

"Nima na gani maigida, kaga ana ta saka maganin, amma sai cigaba yake yi. Ba zamu yi saurin yanke hukunci ba, mu bi dare kawai, muyi makabeli mu ?ace mu yanka gabas, mu koma in da aka fara, ya duba mana, idan da wani abu da za a yi a kai, idan ba haka ba, mai zamani ya yi maka muguwar illa, kuma yana sane yayi hakan".

Madaki ya jinjina kai ya ce "Haka ne, babban abun da ya bani mamaki, bai wuce wanda suka zo suka ?auke shi ba, ban san suwaye ba. Ta tabbata yana da wa?anda suke goge laifukan da yake aikatawa, yakamata na sanar da indabo"

Lakwari ya ce "Haka ne, amma mu fara neman mafita, a karya dafin nan da ya saka maka, kafin duk wata magana ta biyo baya".

Ya jinjina kai ya ce "Shikenan".

***
Sumayya da murtala ne a zaune a gaban MD sun yi fi?i-fi?i da idanu, gefe ga lawisa a zaune.

"Abun da ku ke yi, da kai da sumayya ya fara yawa a wurin nan, ko dai ku bi tsarikanmu, da abun da muka ce dan cigaban tashar nan, ko kuma ku ajiye mana aikinmu. Duk jajircewarku akwai wa?anda suka fiku. Gashi kun saka hankalin mutane gaba ?aya ya yo kanmu, saboda recording ?in da ku ka saki a duniya da yake bayyanar da zargi ga Naja'atu Bunkure, wands duniya kowa ya shida mutuniyar kirki ce, mai yi wa mutane hidima".

Murtala ya ce "Tuba muke, muna neman afuwa in sha Allah ba zamu sake ba"

"Daga kai har ita, wannan ne karo na biyu da kuka aikata mana laifuka, muna ?yaleku, na uku kora ce. Yanzu dole mu san yadda zamu yi mu gyara wannan shirmen da kuka yi" Murtala yayi ta bayar da ha?uri, sumayya kuwa fafur ta yi shiru, ta?i cewa komai.

Sun fito daga ofishin MD, tana hura hanci, ta tarar da Nabila.

Sumayya ta ?arasa ta zauna a kusa da ita, ta ce "Ke kuma daga ina? Kin je kin ha?a kai da Uncle murtala, mun saka recording ?in da yayi miki, a kan shari'ar nan, yanzu aka gama sauke mana kwandon jaraba a ka.

Nabila ta ?urawa sumayya ido, ta ce "Sumy why?"

Cikin rashin fahimta ta ce "Kamar yaya?"

Nabila ta yi murmushi ta ce "Don't mind me, mota fa ta iso, na zo na sanar miki"

Ihun farinciki sumayya tayi ta ce "Are you serious, ko kuma jirgani ki ke yi?"

"Da gaske nake, amma Abba ya ce ba zan hau ba, sai driving licence ?ina ya zama ready, kin san shi da ?a'ida"

Cikin farinciki ta ce "Alhamdilillah, summa Alhamdilillah yawo ba kama ?afar yaro, Allah ya saka wa Abba da alkhairi, uban marayu mai uban ma goyawa yake yi. Amma dan Allah arfat ki kula, ki san in da zaki din ga zuwa, banda rigima da fa?a da mutane a titi" ta din ga kallon sumayya, da son tabattar da abun da Viper ya gaya mata, yanzu sai ayi amfani da ita, a cutar da ita, sam ta kasa yarda gaba ?aya.

Wada M karofi ne ya kira Nabila a waya, ta ?aga ta ce "Hello sir"

"My beautiful angel, ya kike yau bamu gaisa ba gaba ?aya, kin ?i bari mu ha?u, gashi na koma wurin aiki"

Ta ?an kashe murya ta ce "Ba haka bane ranka ya da?e, ka san aikin namu ne babu zama, amma very soon zaka zo har gida mu gaisa" yayi murmushi ya ce "To shikenan, na san maybe kina wurin aiki, da daddare zamu yi waya in sha Allah"

"Ok Allah ya kaimu, ka kula da kanka sosai, kar ka yi aiki ka gaji da yawa"

Yayi dariya ya ce "Thank you my dear"

Sumayya ta ce "Ohh wa kuma ake yaudara, wa aka kwaso mana?" Nabila ta bata labarin wada M karofi.

Sumayya ta ce "Allah ya sa shi ne mijin, kakarmu ta yanke sa?a, kin san waye mutumin nan kuwa Arfa? Allah ya tsaga miki farinjinin manyan mutane, kar ki yi mana bu?ulu dan Allah".

Nabila ta tashi ta ce "Ta? gaskiya ba na son shi, ki zo gida kiga motarmu"

Sumayya ta ce "Dolena" Nabila tayi mata sallama ta fito, zuciyarta na cigaba da wasi-wasi a kan Sumayya, har ga Allah tana ?aunar sumayya har cikin zuciyarta, ta kasa yadda da abun da Viper ya gaya mata.

Nabila na tafiya aka kira Sumayya a waya, ta ?aga tayi shiru.

"Sumayya meyasa ki ke wasa da rayuwar ki, da ta ?awar taki ne? Bayan ?an waken zagaye da ki ke yi, Ki ke kiranta da wasu layukan daban, shi ne ki ka yi disconnecting ?in bibiyar kiranki da ita da muke yi ko?"

"Ni kuma, ban gane nayi disconnecting ba? Wallahi ban yi disconnecting ba"

"?arya ki ke yi, some hours back, aka yi disconnecting, zaki ga matakin da zamu ?auka a kanki da ita, sannan zuwan da tayi me kuka tattauna?"

Sumayya ta dafe kanta ta zauna, sannan ta ce "Mota aka saya mata, sai labarin sabon saurayinta da tayi, Alhaji Wada M karofi, sai ?orafin rashin nasara da take hangowa a kan shari'ar da suke yi".

P.A ya maimaita "Ki ka ce Alhaji wada M karofi?"

"Eh, shi"

"Ki cigaba da sanya ido a kanta, kina kawo mana rahoto, akasin haka zaki ga abun da ba kya so " ta kashe wayar ta dafe kanta.

***
"Indabo ya ga yarinyar nan"

Gaba ?aya suka kalli Al'amin, liti ya ce "Shikenan, ai na san a rina"

Walid ya ce "Ya aka yi ka gane haka?"

"Mun yi magana da ita sosai yau, ana bibiyar ta, ana bibiyar kiranta da wata ?awarta, na yi disconnecting duk wata hanya da za a cigaba da bibiyar kiranta. Amma rayuwarta na cikin hatsari, kuma idan ta cigaba da zuwa za a gane inda muke".

Liti ya ce "Shiyasa tuntuni na ce, a sallameta ta daina zuwar mana nan, amma walid ya nace".

"I think i will sealed a deal with her"

Suka ha?a baki suka ce "Kamar yaya?" Yayi shiru yana lissafa yatsun hannunsa.

Liti ya ce "Ka yarda da ita ne? Ni haryanzu tantama nake yi a kanta ne"

Walid ya jinjina kai ya ce "Lallai a tafawa mata" Viper bai sake ce musu komai ba daga haka, ya tashi ya fita.

***
M karofi yana zaune yana shan shayi, wani jami'in tsaro, ya shigo da Indabo cikin falon.

Karofi ya kalli Jami'in tsaron ya ce "Zaka iya tafiya" ya mayar da idonsa kan Indabo ya ce "Barka da zuwa sirikina, kwana da yawa, muna ha?uwa a Abuja, amma da ni da kai, babu wanda yake ziyarar wani. Duk ni yakamata ace ina kawo gaisuwa. Bisimillah zauna mana.

Indabo ya zauna, ya kalli M karofi ya ce "M karofi"

"Ma'aruf Indabo"

"Sabo da kaza fa, baya ta?a hana a yanka ta"

Karofi ya ce "Wannan haka yake, ko a siyasance, ko ma a normal life"

"Auren 'yar uwata maijidda da kake yi, ba zai hana idan kayi mini kan kara nayi maka na itace ba, hawainiyarka ta kiyayi ramata"

Yayi murmushi ya ce "Yakamata kayi mini fashin ba?i, akan wannan kurman ba?in da kake ta karanta mini"

Indabo ya yi wata ?wafa ya ce "Soyayya da ka je ka fara da 'yar cikinka, saboda abun kunya, kuma yarinyar da take ta gwagwarmayar sai ta tona mana asiri, wadda ka tsayawa, wallahi muddin asirin Abdul ya tonu kaine ba wani ba, kuma sai nayi maganinka a siyasance da duniyance"

M karofi ya ce "Iko sai Allah, kana nufin Nabila wai? Ta? ai ni ban ta?a sani ba, banda yanzu da kake gaya mini. Ina da lawyer a law firm ?in su, shi naje gani, na ganta naji ina sonta, kai idan nayi niyyar tonawa ?anka asiri, da wani zancen ake yi ba wannan ba.
Kuma ni ban yi abun kunya ba, sonta nake yi da aure. Tun da ?anwarka ba yar gwal bace, da zata hanani zama da mata ba.
Naji da?in wannan garga?i da kayi mini sosai da sosai, amma ka kwantar da hankalinka, babu ruwana da shari'arku, nima aikina nake yi. Zaka iya tafiya idan baka da abun cewa".

Indabo ya tashi, ya kalli idon kankarofi ya ce "Kifi yana ganinka mai jar koma"

Karofi ya ce "A juri zuwa rafi dai " Indabo ya fice yana baza babbar riga.

***
Nabila ta sake komawa gidan abokiyar aikin ramma, amma still bata same ta ba, aka sake gaya mata ta koma garinsu, sai dai samun sunan garin ma ya gagareta, ta kasa samu.

Tana kwance a kan gadonta, ta bu?e videos da hotunan da ta yi wa Viper, ta zuba masa ido, tana jin da?in tsokanarsa da take yi, na cewa tana son shi, tana son zama kishiyar 'yar madara, mugun kallon da yake yi mata, ba ?aramin dariya yake bata ba.

Mussaman da ta samu ya kulata, a ha?uwar su ta ?arshe, duk da a ?arshe, korarta yayi.

Tana kallon hotunan tana murmushi, ta ?auki ?aramar wayarta, ta saka lambarsa ta kira.

Sai da ta kira da ainihin lambarta, sannan ya ?aga.

"Ohh Allah, kayi saving lambata ne?, Ina ta kiranka da ?aya layin amma baka ?aga ba. Ina ta kallon hotunanka, ina son in yi bacci .
Ka san ranar da nayi maka hotunan nan, har murmushi fa kayi, ka din ga fara'a murmushi yana yi maka kyau sosai dear. Yaushe zaka ?arasa bani labarinka ne? Yakamata ka gabatarwa jauhar ni, a matsayin amarya, zan yi mata biyayya sosai da sosai, in tayata sonka. Ba zan yi kishi da ita ba, ina sonta sosai da sosai, dan Allah ko sau ?aya ka ha?ani da ita mana" kamar da iska take, haka yayi shiru ya ?i magana.

Ba ta gaji ba, ta sake cewa "Ina ?aunar yar madara saboda Allah, dan Allah ka ?arasa mini labarin ta".

"Meyasa ki ka shigo rayuwata?"

Tayi ajiyar zuciya ta ce "Labarin dogo ne, ba zan ?oye maka ba, da dai ina taya Yayana nemanka ne, saboda nayi suna, na rama abun da Bunkure ta yi mini, na wula?anta ni a gaban jama'a. Shi ne na din ga up and down, har na ha?u da wannan litin, mara kirki".

"Saboda ki yi suna ki ke son taimakona?"

Nabila ta ce "Eh, a da ba, amma jin labarinka gaba ?aya ya canza mini tunani, nake jin zan iya yin komai, dan na ga na ?wato maka hakkinka, da kai da yar madara, duk da ban san ?arashen labarin ba. Amma gwiwata ta fara sanyi, na fuskanci Naja'atu Bunkure nan, tana da goyon baya daga sama, kuma indabo babban mutum ne shahararre sosai, ina bu?atar support sosai, kai kuma sai korata kake yi kana hantarata".

"Idan na ?arasa miki labarin, that means duk tsanani babu gudu babu ja da baya, zaki tsaya a shari'ata komai wahala da sar?a?iyarta?"

"In sha Allah, i promise it"

Ya sake cewa "Kin tabattar zuciyarki zata iya ?auka komai muni, komai da?in abun da zaki ji?"

Cikin ?warin gwiwa ta sake cewa "Eh zan iya"

Viper ya ce "Take your time to think, ki yi comparing da ?alubalen da ka iya biyo bayan hakan"

Ta lumshe idonta, hatta muryarsa, mai da?i ce, duk a bu?e take saboda bayan naturally yadda take, wiwi da shaye-shaye sun ?ara making ?in ta deep.

Ba ta bashi amsa ba, ya kashe wayar.

Walid ya ce "Mai zamani, ka yadda da maganarta kenan? Zaka ?auki fansa ta hanyar shari'a"

Mai zamani ya girgiza kai ya ce "Ta riga ta shiga tarkonsu, kuma na fuskanci ba ta ji ko ka?an, zata iya salwantar da rayuwarta". Walid ya yi murmushi mai cike da jin da?i ya ce "To ?aya maganar fa? Zaka gaya mata?"

Al'amin ya kalli walid, yayi shiru bai ce komai ba.

***
Jikin ramma da sau?i sosai, tana zaune a gefen gado, Abdul yana bata abinci, gefe ga magungunan ta. Wayarsa da take ringing ya ?aga ya saka a hansfree ya ajiye ya ce " 'yar mutanen bunkure, ya ake ciki ne?"

"Abdul"

"Na'am"

"Ya ka yi da yarinyar nan ne da ka yi wa fya?e? Wata yarinya ta tsaya kai da fata, sai ta wanke dattijon nan, mun yi duk abun da yakamata, ta koma tana amfani da social media against me, hankali na ?o?arin dawowa kaina, sai sintiri take yi wai lallai sai an kai yarinyar gaban shari'a, ga wani voice message da yake yawo na uwar yarinyar...... Abdul ya cire wayar daga hansfree, ya saka a kunnensa, yana kallon ramma.

"Ka gaya mini yaya ka yi da ita? Tana raye ko ta mutu? Mu san abun da zamu shirya a kan shari'ar, an je gidansu babarta bata nan an nemeta an rasa"

"Kina ji? Zan zo in anjima yanzu ina wani uzurin ne" ya kashe wayar, ya kalli Ramma zai yi magana, amma ya kasa saboda mugun kallon da tayi masa.

"Rahama ki tsaya ki saurare ni ki ji"

"Kayi mini shiru tun ba sha?eka ka mutu na huta ba, azzalumin banza da na wofi, in sha Allah sai Allah ya tarwatsa ka da kak kai da duk masu goya maka baya kuna cutar mutane"

Fafur ta ?i saurarsa, tayi watsi da kayan karin kumallon, ta tashi ta bar masa ?akin.

***
Nabila ta daina shiga harkar Nasir, dan sosai ya sakata a gaba, da masifar lallai sai ta daina case ?in bunkure, saboda lafiyar ta da rayuwarta, ita kuma ta ce babu wanda ya isa.

Sumayya ce ta kirata da wata lamba, ta ?aga ta ce "Waye?".

"Ke ni ce"

Nabila ta ce "Yar 419, yau kuma da lambar wa ki ka kirani, ko aiki ki ke yi a kaina ne?"

"Nabila, bar wannan maganar kin san menene?"

"No"

"Maganarki da muka saka a radio, a kan bunkure, wata mata ta zo mini, ta ce lallai ke take son gani, akwai information da zata baki a kan bunkure, ta ce macuciya ce, abun babu da?in ji, bama itaka?ai ba, akwai gwarama, mutane sun fara magantuwa fa"

Nabila ta ce "Abubuwa sun fara yi wa kaina yawa, zan zo har gida na same ki"

Ta ajiye wayar ta dafe kai tana tura baki. Duk da tayi farinciki da haka, dan kuwa gagarumin cigaba ne, amma gaba ?aya ba ta yadda da sumayya ba yanzu, dole tana bu?atar ganin Viper kafin tayi wani yin?uri.

Babu tsammani ta ga Nasir ya shigo office ?in ta, ta tashi tsaye ta ce "Yaya lafiya?"

"Nabila wai ke meyasa a duniya ba kya nemawa kanki zaman lafiya ne? Gaba ?aya na kasa gane kanki a 'yan kwanakin nan, menene yake damunki ne?"

Cikin rashin fahimta ta ce "Me kuma nayi?"

"Comment ?in da ki ka yi da safe nake magana a kai" yayi maganar yana ciro wayarsa ya daddana, ya bu?e facebook ?in sa, ya tura mata wayar.

Ta kalli wayar, posting ne da hukumar yan sanda tayi, na cigaba da neman Aminu Viper ruwa a jallo, saboda ayyukan ?arna da yake cigaba da yi.

Tayi comment da "Wannan abun kunya ne ga rundunar tsaron Nigeriya, ace kuna tsare da mutum a prison, a sake shi kuma a dawo ana nemansa, ba shi ne abun bincike ba, hukumar 'yan sanda, da prison, da ta shari'a su ne abun tuhuma da zargi" aikuwa mutane suka yi caa a kan comment ?in ta, suna reply.

"Yanzu yaya fisabilillahi menene laifina a cikin wannan comment ?in nawa, ita hukumar 'yan sandan, dan ayi comment ai suka yi posting ?in, kuma gaskiya na fa?a. Akwai ayar tambaya a kan ma'aikatar Shari'a, hukumar yan sanda da ta gidan yari a kan case ?in nan, kar ka yi wani tunani daban, ina goyon bayan gaskiya ne kawai"

"Nabila ba kowane lokaci gaskiya take tasiri a ?asar nan ba, yanzu ki ka shigo cikin system ?in nan, ?asar nan ta wuce duk yadda kike tunani".

"Na sani, amma rashin yin wani yun?uri na kawo gyara, shi ne ke kawo mana koma baya yaya, ba wai ina goyon bayan Aminu Viper ba ne ba, menene gaskiyar abun da yake faruwa nake son sani"

Cikin takaici ya girgiza kai ya ce "Idan kin ?i ji, ba zaki ?i gani ba arfa".

Ya ?auki wayarsa ya juya ya nufi hanyar fita, ya kama handle ?in ?ofar office ?in ya mur?a ya bu?e. Sai dai wanda suka yi ido hu?u da shi a tsaye ya sanya gabansa wani irin mummunar fa?uwa. Ya ra?a jikin Nasir ya shiga cikin office ?in, Nabila ta waro ido tana kallonsa tana kallon Nasir.

Ayshercool
08081012143
???500 ne via 0009450228
Aisha Adam jaiz bank sai shaidar biya ta 08081012143
Wanda za su jira document 1K ne.

90009343
'Yan Nijar ku turo katin airtel na 300fcfa

Arewabooks ayshercool7724



Kallonta yake yi ta cikin ba?in glass ?in idonsa, duk da ya saka facemask, babu yadda za ayi Nabila ta kasa gane shi.

Nasir ya tsaya ya waiwayo, yana son sake ganin waye, duk da fuskarsa a rufe take da face mask, amma ya tsaya ?yam a tsakiya, ya juya wa Nasira baya, yana fuskantar Nabila.

A hankali ya ?arasa takawa, yaje ya samu wuri ya zauna a kan kujera, ba tare da yayi magana ba.

Nabila kuma ta kalleshi ta kalli Nasir.

Nasir ya juya ya tafi, yana fita da saurin gaske ta ?arasa, ta rufe ?ofar office ?in ta saka mata key.

Ta dawo ta kalleshi, ya cire facemask ?in sa da glass ya ajiye a kan teburinta.

"Su maciji an fito daga rami, kuma kai tsaye aka yo wurina, dan Allah meyasa ka ke son lallai sai ka ha?u da yaya Nasir ne? Da ya gano ka da ni da kai zai ha?a duk ya kama, dan ban san me zan ce masa ba"

Ta dafe ?irjinta ta ce "Wayyo Allana, haryanzu zuciyata racing take yi, ranka ya da?e irin haka sai ka kirani a waya, ka ce in zo kana son ganina, amma wannan dirar mikiyar da ka yi mini ohh my God me ma zan ce ne? Allah ya sa babu wanda ya sanka" ta zagaya ta bu?e fridge ?in office ?in ta, ta ?auki plate ta ?oro masa apple, ayaba da lemo ta zo ta ajiye masa.

Ta tsiyayo ruwan zafi a dispenser ta ha?a masa tea mai zafi, ta bu?e jakarta ta ?aukko ?an ?ara min flask, ta juye masa dankali a kan plate da ?wai, ta ce "Bisimillah, fara cin abincin sai mu yi magana naga yanzu safiya ce" yayi shiru yana danna wayarsa.

"Ka ci abinci, wanne zaka fara ci?"

Still bai yi magana ba, har ta fara jin haushi.

"Sweetheart, magana nake fa, 'yar suga na magana" ya ?ago ya kalleta.

Ta saka hannu ta kar?i wayarsa ta ajiye, ta ?auki kofin shayin ta mi?a masa ta ce "Ba dan ni ba, dan Allah ka sha, a gabanka na ha?a, ban kuma son da zuwanka ba, balle ka ce na zuba wani abu a ciki dan Allah" tayi maganar cikin kwantar da murya.

Ya saka hannu ya kar?a, sai dai kamar ?aramin yaro, ya zubawa kofin ido.

Ta ?aukko plate ?in dankalin, ta ri?e a hannunta, ta kalle shi ta ce "Sha mana" ya tsareta da idanunsa masu ban tsoro.

Ta sauke nata idanun, saboda yadda nasa suka yi mata nauyi.

Ta saka hannu ta kai kofin bakinsa, ya bu?e bakinsa a hankali, ya fara sha.

Tayi ?oyayyiyar ajiyar zuciya, ya sauke kofin, ta mi?a masa dankalin, kamar mai koyon cin abinci, haka yake ?auka yana ci.

"Yauwwa My dear" yana ci, Adam apple ?in ma?ogwaronsa, na kaiwa na komowa, sai yayi kamar zai yi magana, sai ya fasa ya ha?iye maganar tare da abincin, da ?yar yake ha?iye abincin, a duk lokacin da ya saka abinci a gaba zai ci, haka yake ji, sai ya cakala ya bar shi, tun su liti suna lalla?a shi ya ci abinci, har sun ha?ura sun ?yale shi, sun zuba masa ido.

"Master, ciwonka ya gama warkewa, Alhamdilillah Allah ya ?ara tsarewa, ka daina zuwa in da za a cutar mana da kai dan Allah"

Yayi mata shiru, yana cigaba da cin abinci.

"Ko in ?ara gudun AC naga kana gumi" ya girgiza mata kai alamar a'a.

Tana tayi masa hira, har ya cinye abincin tas.

Ta ce "Alhamdilillah" ta mi?a masa tissue ya goge hannu.

"Wai dan Allah meyasa kake ta kallona ne? Ko wani abun nayi?" Nan ma ya girgiza mata kai.

"Kamar bacci ka ke ji fa, ko an sha ne?"

"Me fa?" Yayi maganar yana kallon ta.

Ta ce "Bakomai"

"Aiki na zo yi" ya fa?a a ta?aice.

Ta ce "Aikin me?"

"Computer zaki bani"

Ta ce "Ok, desktop ta aiki ce, bari na baka laptop ?ina" ta ?aukki laptop ?in ta ta bashi, ya bu?e ya fara dannawa.

Ta zauna a kusa da shi, tana kallon mai zai yi, sai dai ta kasa gane me yake yi ?in, wasu irin lambobi da alphabets kawai take gani a screen ?in system ?in.

Sunan Yaya Nasir ne ya fito a kan wayarta, ta ?aga ta kai kunnneta, tayi shiru.

"Arfa"

"Na'am"

"Waye mutumin da ya zo office ?in ki?"

Ta kalli Viper sannan ta ce "Ba?ona ne"

"Wane irin ba?o?"

Nabila ta ce "Client ?ina ne, ya zo muyi magana ne a kan wata shari'a meyafaru?"

Nasir ya ce "Gaba ?aya ban yadda da shi ba"

"Daga fara ganin mutum yau ka ce baka yadda da shi ba yaya? Ka san shi ne?".

"A'a kawai jikina ya bani wani abu ne, amma akan case ?in menene?"

"Is confidential, and against my professional ethics, ba zai yiwu na gaya maka ba, idan na dawo mayi magana" ta katse wayar.

"Meyasa ki ke tsoron gaya masa ne? Shi ne DSP Nasir ?in? Shi a yadda yaken nan matsoraci yake son kama ni, ai karo da karo sai rago, na raina jarumtarsa"

Ta tsuke fuska ta ce "Ya haka? Yayana ne fa, banda cin fuska"

Ya ?aga kai ya kalleta ya ce "Da lokacin da nake mai zamanina ne, aka bashi aikin kama ni, sai na yi masa karayar da zai shafe shekara yana zaune yana jinya. A yanzun nan da muka ha?u, ba zamu rabu lafiya ba.
Tarbiyyar Jauhar ce da girma ya sanya wasu abubuwan nake kawar musu da kai".

Ta ce "A hakan? Yanzun ma fa kana zuwa ka sari mutane, ka yi fa?a da neman magana"

Ya matso da fuskarsa saitin ta ta, ta ja da baya. "Lokacin da nake mai zamanina, bana bin ?ofa komai girmanta, sai dai na kama katanga kamar ?arawo, bana biyo hanya ayi gaba da gaba da ni. Bana tsoron kowane irin nau'i na fitina ko tashin hankali, idan aka kwana biyu ban ji ni cikin rigima ba, sai na ji ni kamar mara lafiya.
Aiki tu?uru da jajircewa tayi a kaina, ba dan ?addara ta rusa tanadi da burikan rayuwata ba, ta ci kaso mafi yawa na tarbiyantar da rayuwata a kan tafarki madaidaici. Ki daina ha?a kanki da ita"

Ta lumshe idonta ta bu?e ta ce "Shiyasa na ce tun da ita 'yar madara ce, ni kuma sai na zama 'yar suganka, amma ka ?arasa mini labarin ta dan Allah" ya zauna sosai ya cigaba da danna system sannan ya ce "Idan na ?arasa miki labarin ta, hakan na nufin we sealed a deal, da

Please Login or Register in order to submit comment