Reading KARFE A WUTA Chapter 72 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

marairaicewa ta ce "Wai baka san abun ya same ni bane ba? Kwana nawa baka ga kiran wayata ba baka neme ni ba, wrong connection na wearing aka yi a office ?ina, wuta ta shi, aka rufe ni ta waje fa"

"Na sani"

"Ka sani?"

Ya ce "Eh"

Cike da takaici ta ce "Kuma ka kasa nemana a waya, da mutuwa na yi fa"

"Allah ya ji?anki, zahra ma da mutu ha?uri nayi, balle ke. Sai ki ?ara taka tsantsan da abubuwan da ki ke yi"

Wani ?ululun takaici, ya tokare mata wuya, sosai ta ji zafin abun da ya ce mata, kawai ta katse wayar.

Walid ya ce "Viper, kamar baka kyauta ba fa" yayi masa shiru, hakan ya sa shi ma yayi shirun bai kuma cewa komai ba.

Ba?in ciki da ?acin rai ya sanya, babu wanda ta yi wa sallama a gidan ma, tayi tafiyarta.

Tana tafe a hanya ta din ga jin wani abu mai kama da kishi, da ?acin rai yana taso mata, har ga Allah ba ta san jauhar ba, amma tana son ta saboda Allah, amma abun da yayi mata yau, ya sanya ta ji ranta ya sosu.

"Meyake damuna ne? Wai son bawan Allah nan nake yi? Na shiga uku me yake shirin faruwa da ni ne? Idan ta tabatta son shi nake yi, na yi wauta, to yaya ma za ayi hakan ya yiwu abu daga wasa?" Har ta ?arasa wurin aiki, tunani take a zuciyarta. Tayi shiru tana sauraren zuciyarta dan ta tabattar da abun da take tunani gaskiya ne ko akasin haka, amma bata kai ga hakan ba, aka ?wan?wasa glashin motarta, masu gadi ne suke yi mata barka da dawowa, tare da yi mata sannu da jiki".

Ta saukko daga motar, suka gaggaisa, sannan ta shiga ciki, a cikin ma murnar ganinta suka din ga yi suna yi mata sannu.

Ko mintuna talatin ba ta yi a sabon office ?in ba, barrister Habib ya ?araso.

"Autar lauyoyi, ?aramar su babbar su, aminiyar sumy, ?aramar sauro ka da ?atuwar giwa, ba giwar ba hatta toron ma kayarwa ki ke yi"

Nabila ta yi murmushin ya?e ta ce "Ni har ka bani kunya ma"

"To yaya jikin naki?"

"Alhamdilillah yayi sau?i sosai"

Ya ce "Masha Allah, yanzu ya ake ciki da batun shari'ar nan? Zamu je prison ?in ne wurin mutumin?"

"Za a bari mu ganshi kuwa?"

Habib ya ce "Za'a bari mana ba dole ba, ai na je lokacin kina gadon asibiti, ba na son abun da zai kawo tsaiko a harkar shari'ar gaba ?aya"

"Kai amma na gode sosai yaya habib "

"Kar ki damu Nabila, ba ke ba, hatta ni na ji haushin yadda shari'ar nan ta gudana, kuma cin mutuncin harkar shari'a ne, a wannan karon zamu yi nasara in sha Allah "

"Allah ya sa yaya Habib" suka fito suka hau motar barrister Habib suka fita.

Nasir da yake bin Nabila a wata motar, ya ga fitar Barrister Habib da Nabila, ya sake rufa musu baya, sannu a hankali ba tare da sun san yana bin su ba, sai dai azabar kishi ya sanya ya ji har wani dishi-dishi yake gani.

A wannan karon Nabila tayi mamakin yadda aka basu damar ganin baba maigadi, ba tare da an raina mata hankali kamar yadda aka saba ba.

Suka gaisa cikin mutuntawa, duk ya rame yayi wani iri.
"Baba, ina mai sake baka ha?uri, amma ban karaya ba, in sha Allah zamu ?aukaka ?ara ne"

Jiki a sanyaye Baban ya ce "Kina ta ?awainiya, ni idan babu hali, kawai a bar maganar nan, na bar wa Allah"

Barrister Habib ya ce "No ba zai yiwu ba, ka manta yadda muka yi da kai wancan zuwan da nayi muka ha?u?"

Yayi shiru ya sunkuyar da kai.

"Ka yi magana mana, mun yi magana da kai fa sosai baba, ka bata ha?in kai dan Allah, a wannan karon muna fatan ayi nasara, ka yi mata bayani, saboda ?o?arin kamanta gaskiya har nema aka yi a sabauta rayuwarta, ka yi magana baba, ka yi mata bayanin komai.
Nabila let's record it Incase"

Ta jinjina kai ta ?aukko wayarta, ta danna recording ta ajiye.

Cikin tsoro ya ce "Dan Allah to kar ku gaya wa kowa, kun ga yarana duka mata ne, na aurar da wasu, ina da biyu ?an mata, an ce muddin na yi magana abun da ya samu ramma zai same su, koma su rasa rayukansu gaba ?aya tsoro nake ji" mamaki ya cika Nabila, dan ita duk bai yi mata wannan maganar ba.

"Baba, ni na baka tabbacin nan, babu abun da zai samu iyalanka, ka ba ta cikakken ha?in kai, idan ka bari ta sake fa?uwa a shari'ar nan, kaga magauta sun yi galaba a kanta, kuma yayan da ka ke yi wa, ka ?ata musu suna"

Ya jinjina kai ya ce "Ana saura kwana biyu uwar ?akin hajiya jidda, tayi waya ta ce aje garin su ramma, ta dawo su ha?u da ?aya mai aikin, ayi mata gyaran gida, saboda tana ji da Ramma sosai, tana da biyayya, kuma bata yi mata sata.
Ranar an ?aukko ramma, suna ta aiki, zulai ta tafi kasuwa, ?an yayar matar gidan ya zo, sunansa Abdul, ban da?e da fara aiki a gidan ba, dan babban mutum ne sosai mutumin, in da suka baro, jami'an tsaro ne suke yi masa gadi. Unguwar nan da suke ne, jami'an tsaro layuka suke gadi, ni kuma aka samo mini bu?e ?ofa da rufewa a gidan.
Bayan yayi mata, ya tafi zulai ta fito tana kururuwa, bayan ta dawo daga wurin sayen kayan miya. Bayan mun kai ta Asibiti, magana ta bazu, aka ce an sallame ni daga aiki, amma za a neme ni, daga baya yan sanda suka je gidana suka tafi da ni, wai zan ba da bayanin abun da na sani, muna zuwa aka rufe ni aka ce ni ake zargi, kuma aka yi mini barazana da muddin na ce bani bane ba yarana na cikin ha?ari"

Nabila ta ?ulu ta ce "Amma meyasa baka yi mini wannan bayanin ba ni, na san ta ina zamu ?ullowa lamarin? Nayi ta wahalar neman shaida ka kuma ?i bayani a kotu"

Barrister Habib ya ce "Kwantar da hankalinki, ki yi ha?uri kin san uba da 'ya'ya"

"Ki yi ha?uri na san nayi kuskure amma a tsorace nake ne nima"

Ta kalleshi ta ce "Ya sunan mai gidan?"

Ya girgiza kai ya ce "Ban sani ba"

"Ya za ayi ka yi aiki a gidan wanda ba ka san sunansa ba?" Yayi shiru ya sunkuyar da kai.

Barrister Habib ya ce "Tashi muje, ma ?arasa sauran aikin" haka suka fito Nabila tana mita, barrister Habib yana bata ha?uri.

Law firm ?in suka koma, suka fara arranging ?in yadda zasu yi appeal, sun gama ta fito suka ha?u da barrister Kabir, yayi mata sannu, tare da yi mata kashedi, a kan ta raba kanta da aikata duk wani abu da zai sanya ta shiga matsala, ta bishi da to, ta fita ta shiga motarta ta nufi gida.

Nasir bai ga wani abu ba a bibiyar Nabila da ya yi yau ba, amma bai ji zuciyarsa ta gamsu ba, ya sakawa ransa zai yi assigning wani wanda zai din ga bibiyar masa ita lokaci zuwa lokaci.

***
Su liti suna karyawa, Viper kuwa yana zaune yana yanke farcensa da nail cutter.

Wayar liti aka kira, ya kar?a ya ?aga ya ce "Ya ne?"

"Normal, kwana biyu ba ku shigo gada ba fa"

"Eh ka san yanayin ne, sai muna bayyana muna ?acewa, meye labari?"

"Baban Viper ne ya zo rumfa, ya na neman ka, ko kai ko walid" liti ya kalli walid ya kalli Viper.

"Meyafaru yake nemanmu?"

Ya ce "Ban sani ba, ya dai tambaye mu, ko Viper yana zuwa wurin, muka sanar masa rabonmu da shi, tun kafin a kama shi, shekara shida kenan"

Liti ya ce "Normal ne, zan faso fatan rumfa komai lafiya?"

"Lafiya ?alau tana ta garawa"

Ya jinjina kai ya ajjye wayar.

Liti ya cigaba da kallon Viper, Viper bai kalle shi ba ya ce "Ko dai ka yi magana, ko kuma ka daina kallona"

"Allah ya baka ha?uri, na daina kallonka" kamar ya gaya wa Viper, zuwan mahaifinsa rumfar shayinsu, sai kuma ya fasa ya ha?iye maganar.

***

Abdul ne yayi sallama a falon, ya shigo a gajiye, ta amsa sallamar tana tashi zaune daga kwancen da take.

Ya ajiye jakarsa, ya kwanta a jikinta ya ce "Wash"

Ta ce "Sannu"

"Yauwwa sweetheart" ta kama hannunsa, ta cire masa agogon hannunsa.

"Tashi a cire safar"

"Ki bari na huta na gaji"

Ramma ta ce "?ato da kai kana shagwa?a, wata?ila ma ba wani aiki ka yi ba kake wani wash"

Ya ce "Kaii, baby kin san mutum nawa na yi wa tiyata kuwa? Ga kusan asibiti uku naje na ga marasa lafiya"

"To tashi ka yi wanka, ka ci abinci" ya kalleta ya yi murmushi ya tashi zaune, ya shafa kanta ya ce "Allah ya yi miki albarka babyna, i so much love you" yayi maganar yana sumbatar goshinta.

Kallonsa take yi, tana son jin matsananciyar tsanarsa a zuciyarta, amma abu ya gagara, sai wani ma kyau da ta ga yayi mata.

Ya tashi ya tafi bedroom, yayi wanka, Ramma ta goge hawayenta tana fatan Allah kar ya jarrabeta da son Abdul.

Yayi salla ya fito, ta bashi abinci.

"Beb, in sha Allah komai ya kusa zuwa ?arshe, zan bayyanawa duniya ke, ina daf da gayawa babana maganarki, a san yadda za a gyara lamarin mu cigaba da rayuwarmu, am ready na ?auki kowane risk mu zauna tare in sha Allah my rahama"

Tayi ajiyar zuciya tare da murmushi.

"Dan Allah ko sau ?aya ki ce kina so na mana"

"A'a ni ban iya ?arya ba"

Ya ce "Zaki yi bayani ne"

***
"Hello masoyiyyata"

Nabila ta ce "Na'am sumy kalar kyau"

"Albishirinki?"

"Ku?i dubu goma"

Sumayya ta ce "Mayyar ku?i, ba za a bayar ba"

Tayi dariya ta ce "Fesa mini"

"Arfa ranar monday in Allah ya kaimu, zan fara aiki, ni da yaya murtala zamu bu?e gidan radion"

Nabila ta mi?e ta ce "Dan Allah masoyiyya"

"Wallahi da gaske, ke Allah ne ya kawo mana mafita, an bani damar ?ir?irar programs, har na sami program ?in da zamu din ga yi tare, mu ci karenmu babu babbaka, babu mai yi mana barazana da daka tsawa".

"Ke gani nan zuwa gidan naku ma, tare da ni za a bu?e gidan rediyon nan in sha Allah"

Duk wannan abubuwan da Nabila take yi, ?arfin hali ne kawai, zuciyarta na tare da Viper, tunaninsa kawai take yi, tama rasa wane irin tunani take yi a kansa, ga zuciyarta da take ta azalzalarta da son ganinsa.

Tare da Nabila aka yi bikin bu?e sabon gidan radio, mutane suka din ga kiran wayar suna yi wa Sumayya fatan alkhairi, tare da tabattar mata da duk in da ta tafi suna tare da ita.

A program ?in farko da suka fara yi da sumayya, suka sanya masa suna ?e?e da ?e?e.

Tun da sumayya ta gabatar da Nabila, kasancewar masu saurare sun santa a bakin sumayya, suke ta tura sa?onnin gaisuwa, wasu kuma suna tambayarta dalilinta na ?alubalantar bunkure foundation, duk da irin gudunmawar da take bawa al'umma.

Sumayya ta ce "Masoyiyya, kin ji tambayoyin masu sauraro mai zaki ce?"

Nabila ta yi murmushi ta ce "Babu abun da zan ce, sai su kasance da mu a sabon shirinmu, na ?e?e da ?e?e. Ba wai bunkure foundation ba, duk wani abu da ake kitimurmura a cikin sa, ko rashin adalci zamu yi bajekolinsa a wannan shiri, kuma program zai iya bi ta kan kowa, duk wanda ya ga kuma an yi masa ba dai-dai ba ya ?alubalance ni a gaban shari'a.
Manyan shari'oi da aka yi bita da ?ulli a ciki, yadda ake danne hakkin mara galihu ake tsayawa yaran masu ku?i, yadda ake wasa da hankalin talaka, da tauye masa hakki, shi fa wannan program ?in, kai har da shari'ar wani gawurtaccen matashi da ya shahara, jami'an tsaro suna nemansa, sai dai abun mamaki shi ne sai da ya shafe shekaru biyar ba ayi masa shari'a, a shekara ta shida aka sake shi, kuma yanzu an ce ba bisa ?a'ida aka sake shi ba wai nemansa ake yi.
Akwai tarin kwamacla a harkar shari'a a ?asar nan, a shirin ?e?e da ?e?e zamu fayyace abubuwa da dama, na ban mamamki" suka ?ar?are program ?in cikin wasa da barkwanci.

***
Alhaji wada hankali kwance yake zaune yana shan lemo a kofi, yana kallon indabo da yake ta ha?ilo yana magana.

"Karofi, ka shiga gonata da yawa, ka kiyayeni, muddin kana son yarinyar nan ta rayu, ya zama dole ka takawa shirin nan da zasu fara gabatarwa burki"

Karofi ya ce "Sabod me? Kai da kake ?aukar nauyin gidan radion ka ake abun da ka ke so waye ya hana ka? Ni na ?auki nauyin program ?in dan haka babu ruwanka da abun da ake yi"

"Karofi, ka san na fi ?arfin kafi ga bayana ko?"

"Ai ka san shi ?arfen cikin wuta sai da ?an uwansa ?arfe, babban mutum mai kima a ?asar nan, bai kyautu ace ka na ?ata lokacinka a kan wata ?aramar alhaki kamar wannan yarinyar ba.
Auuu ashe fa ta sako wani zance a maganarta, mai kama da maganar Al'amin Viper, wato mai zamani. Kana tsoron ta tona maka asiri cewa kai ne ka saka aka kashe matar Viper ko? Ka kwantar da hankalinka ba ta san wannan labarin ba, idan har ba tana ha?uwa da Viper ba ya gaya mata da kansa"

Wani irin shock indabo yayi, ya sandare a tsaye, jin yadda Alhaji mu'azzam wada kankarofi yake farke sirrin da bai ta?a tunanin wani mahaluki ya sani ba.

Ayshercool
08081012143
???500 ne via 0009450228
Aisha Adam jaiz bank sai shaidar biya ta 08081012143
Wanda za su jira document 1K ne.

90009343
'Yan Nijar ku turo katin airtel na 300fcfa

Arewabooks ayshercool7724




Indabo da ?yar ya iya bu?e bakinsa ya ce "Kankarofi"

"Indabo"

"Wace irin magana kake fa?a ne?"

"Irin wadda ka ji da kunnenka, ka zata daga kai sai wa?anda kuka aikata laifin ne ku ka sani? Kamar na so na fika iya playing cards ?ina ko?"
Indabo zai yi magana, Jidda ta shigo wadda ita ce matar kankarofi, kuma ?anwar indabo.

"Yaya yana ganka a tsaye ne? Ba dai har tafiya zaka yi ba?"

Kankarofi ya ce "Eh, ya ce tafiya zai yi, dama ziyarar ta bazata ce, mu je na taka maka" kamar wawa haka indabo ya bi kankarofi suka fito.

Ya sake kallon indabo da yake ta rarraba ido, kamar shege a rabon gado ya ce "Ka fa kwantar da hankalinka, kar ka yi zaton zan gaya wa wani wannan sirrin tsawon shekaru kenan, ina dakonsa ba wanda ya sani, ko ma na fa?a bani da wata ?wa??warar hujja a kai, ina gargadinka ne kawai ka kiyayi yarinyar nan".

"Kankarofi"

"Indabo"

"Hawainiyarka ta kiyayi ramata, sanin wannan sirrin ba shi yake nufin kana da lago na ba"

Kankarofi ya ce "Na sani, na ankarar da kai ne kawai, na san abun da kake yi, dan haka kar ka tsallake gona da iri".

Indabo kawai ya jinjina kai zai juya ya tafi, Kankarofi ya ce "Na san zaka yi mamakin yadda aka yi na sani ko? Ba abun mamaki bane ba, kar ka je ka sakawa kanka damuwa da dogon tunani" bai ce masa komai ba, ya yi gaba.

***
Abdul yana kwance yana bacci, saboda daren jiya bai yi bacci ba, ramma tayi bacci, aka kira shi asibiti, sai bayan sallar asuba ya dawo.

Ramma ce ta shiga ?akin a gigice, tana dukansa a kafa?arsa.

Ya bu?e idonsa ya ce "Meye haka kuma?"

"Ka tashi"

"In tashi in yi miki me? Rahama ban yi bacci ba fa jiya, ina asibiti".

A gigice ta ce "Ina ruwana? Abdul ban ga al'ada wancan watan ba, wannan ma lokaci ya wuce"

"Kuma shi ne zaki tashe ni ina bacci?"

"Dole na tashe ka, me hakan yake nufi ka tashi ka duba ni, ba zan sake ?aukar ciki ba, ni ka tashi ka duba ni"

Tashi yayi daga kan gadon, bai ce mata komai ba, ta bi bayansa tana kiran sunansa, amma ya rigata fita ya kulleta a ?akin, ya tafi wani ?akin ya yi kwanciyarsa.

***
Sosai sumayya take jan jama'a a sabon gidan radion da kama aiki, da ita da murtala.
Saboda bayan kasancewar ta sananniya, tayi ?o?ari wurin samar da sabbin shirye shirye masu ?ayatarwa, wanda za su tafi dai-dai da matasa da ma dattijai baki ?aya. Wasu daga cikin abokan aikinta da ta baro a can, suka din ga yi mata magiyar suma ta samar musu gurbi a in da ta koma, suma su koma. Yanzu sumayya ba ta da fargabar ta samo rahoto, a kushe ace mata ba irinsa ake bu?ata ba, saboda kawai bai yi dai-dai da abun da wasu suke son ji ba.

Ranar farko da suka gabatar da program ?in ?e?e da ?e?e ita da Nabila, program ?in ya yamutsa hazo, dan tayi sukuwa tayi zamiya, ta ?arewa bunkure foundation ta tas da hukumar shari'a, tayi bayanin yadda shari'ar baba mai gadi ta kasance a kotu, tare da jaddada idan har da gaske dan al'umma suke ayyukansu, ya zama dole a bayyana ina ramma take, idan kuma da gaske tana asibiti, a bawa lauyoyi da ?an jarida damar zuwa su ganota, kuma a kawo bayanin likita a kan abun da yake damunta zuwa lokacin da aka gaza ganinta a gaban kotu.
Hatta lauyan gwamanti ta din ga challenging ?in sa, a yadda suka din ga taka doka yadda suke so.

Nan fa mutane suka din ga tururuwar kiran waya, wasu suna sharhi, ciki har da wani lauya mai zaman kansa, da ya kira waya, ya tofa albarkacin bakinsa tare da tabattar da akwai jabun lauyoyi da suke yi wa doka hawan ?awara, a yi cuwa-cuwa a danne hakkin mai ?aramin ?arfi, a wanke yaran masu ido da kwalli, ire-iren foundations ?in bunkure suna da yawa. Ya ?ara fa?a?a bayanan da Nabila tayi, tare da fito da wasu abubuwa ma da ita hankalinta be kai, kai ba.

Nabila ta ji da?in program ?in sosai da sosai, dan kuwa ji tayi, zuciyarta ta rage ra?a?i da ba?in cikin abun da aka yi musu a kotu.

Bayan kammala program ?in, still cigaba da kiran wayar a aka yi, ?arshe sai kashewa suka yi.

Sumayya ta ce "Mutuniyata kin yi bala'i fa"

Nabila ta ce "Ke ni ?in ta wasa ce? Ai sai Najar bunkure ta zubar da hawaye, yanzu ta ?ar?ashin ?asa zan yi analysis nawa ?ungiyar take samu na tallafi a wata, da kuma abun da ake spending wurin tallafwa mutanen da ake i?irari. Ni ?in fa ba ta wasa ce ba"

Sumayya ta ce "Ba wani ta wasa ko ba ta wasa ba, dole mu daga da Addu'a fa, Allah ya tsaremu Masoyiyya"

"Amin dai, amma yanzu meye abun yi?"

Sumayya ta ce "Eh to, kamar yadda ki ke tunanin kawo ?arshen bunkure, ni kuma sonake na ci uban indabo, duk da ya fi ?arfina, amma zai ga abun da 'yar matsiyata zata iya yi, dan wallahi sai na kusa girgizo shi daga kan kujerar nan"

Nabila ta kwashe da dariya ta ce "Me yayi miki ne, ki ke wannan alwashin?"

"Zagin cin zarafi yayi mini, lokacin da ya ce na din ga bibiyar masa ke, kin san na ta?a zuwa na bayar da wani rahoto, a kan cewa an ce an yi wani aiki a yankinsa, kuma da na je ban tarar an yi ba, kin ga abubuwan da aka yi mini a kan hakan? Program ?in da zamu din ga yi da yaya murtala, irin su Indabo zamu din ga banka?awa asiri. Zamu fa?i abun da suke kar?a na consituency project duk wata, da kuma ayyukan da suka gabatar a watan, daga nan ya ragewa al'ummar yankin da ake wakilta, su yanke hukuncin da ya dace"

"Allah ya ?ara lafiya, ?ar gwagwarmaya amma shirin ya ?ayar da ni, Allah ya taimakemu ya ?arfafi gwiwarmu masoyiyya. Abun mamaki shekarun baya bamu ta?a tunanin samun wannan damarmakin ba, sai dai mu yi ta dama dama"

"Haka lamarin Allah yake, yanzu ya ara mana damar da muka ro?a, ya rage namu mu yi abun da ya dace da ita"

"Haka ne, Allah ya taimake mu ya bamu sa'a" suka ce Amin.

Ko da ta koma gida, Walida ce ta fara tararta ta ce "Arfa, yanzu muka gama jin program ?in ku, live ku ka yi shi, kina ta ?arin maganganu ko tsoro ba kya ji"

Nabila ta ce "Walida, wanda bashi da gaskiya ai shi ne yake tsoron a fa?eta, bamu fara dan mu daina ba"

"Zaki ga baki fara dan ki daina ba, yaya ya shigo a ?alla sau uku yana nemanki, ya kira wayarki ma, kin ?i ki ?aga"

"Duk a kan program ?in da na yi"

Walida zata bata amsa ya shigo, fuskarsa babu annur ko ka?an.

Ta tsaya tana kallonsa, ya ?araso gabanta ya kalleta ya ce "Arfa ba zaki ta?a yin hankali ba ko? Meyasa ki ke son yin wasa da rayuwar ki ne?"

"Dsp, rayuwa ta ka ce ai, nika?ai nake abuna ai, shiyasa nake takatsantsan kar baya tawa rayuwar, na saka ta wani a hatsari"

"Zaki rufe mini baki, ko sai na kwa?a miki mari, ni kike gaya wa ba kya saka rayuwar wani a hatsari? Duk tayar mana da hankalin da ki ke yi ba kya gani, yadda ki ke tayarwa da Abba hankali a shekarunsa ba wasa da rayuwarsa ba ce ba? To wallahi ba zaki kashe mana uba ba, muna da burin ganinsa a raye".

Aikuwa ta gyara tsayuwarta, ta ha?iye wani abu mai ?acin gaske, ?irjinta na yi mata zafi ta ce "Good, an zo wurin, kar na kashe muku uba, tun da ni ba nawa uban bane ko? To ku mayar da ni wurin nawa uban mana, meye na zama ana yi mini gori, how many years for now? kuna yi mini gori, kai ?in ma da baka yi yau gashi ka fara, alhalin kun fi kowa sanin bani na za?i hakan ba, da da yadda zan yi, da tuni na bar muku gidanku, ku nuna mini hanyar gidan nawa uban mana"

Ta baya ya fizgota, ya ?auketa da lafiyayyen mari.

Gigicewa tayi, jikinta ya hau rawa ta kalli Abba, da ransa yake a ?ace, fuskarsa babu annuri.

Ya ri?e hannunta, ya zazzaro mata ido ya ce "Me ki ka nema kika rasa? Me kike bu?ata a rayuwar nan da ban yi miki ba da ki ke zancen mahaifinki, menene shi Nabila?"

Ta sunkuyar da kai tana kuka, ta dafe kuncinta.

"Ki gaya mini, kafin na kasheki, me uban naki ya tsinanawa babarki ma, balle ke? Uban me ki ke nema a wurinsa?"

"Abba ka yi ha?uri, ba zan sake ba"

"Ba zan yi ha?urin ba, ki gaya mini ta ina na gaza, menene ba na yi miki"

Mama da jin hargowar su ya sanya ta fito ta tarar da su, ta ce "Mhmm, ai tsintacciyar mage ba ta ta?a yin mage major, kuma gurbin ido ba ido bane ba, muna nan da kai wataran sai ta saka ka zubar da hawaye"

Nasir ya ?arasa ya ce "Abba dan Allah ka yi ha?uri, ba zata sake ba in sha Allah, kar ka kuma dukanta"

"Shut up! Kai ma har da kai, ina yi maka kallon mai hankali ashe ba haka ba ne, ku kuke tunzurata take wannan zancen".

Ya ce "Ka yi ha?uri dai Abba, in sha Allah ba za a sake ba"

Ya saki hannunta ya fice daga gidan baki ?aya.

Nabila kuwa da gudu ta ?arasa ?akinta tana kuka mai cin rai.

***
?arfe sha ?ayan dare, liti yana ?ofar gidan su Al'amin, yana rarraba ido, babu yaron da zai aika cikin gidan, kowa ya watse.

Ya bubbuga gate ?in gidan, ya koma gefe.

"Waye?"

"Nine"

Ya bu?e gate ?in ya kalli liti ya ce "Ya aka yi?"

"Wurin Abbu nazo shi nake nema"

Jin muryar liti, ya sanya Abba gane jama'ar Viper ne, dan haka ya ce "Mai zamanin yana tsare ai, ka sani kake nemansa"

"Dan uwarka wurin mai zamani na ce maka na zo? Wurin mai gidan na zo, baka gane ni bane liti ne" yayi maganar yana cire facemask ?in fuskarsa.

"Na gane ka, amma a kan me zaka zo nemansa, ka gaya mini na je na gaya masa"

Wata uwar sha?a liti yayi masa, ya watso shi waje ya ce "Shege, kai ka isa in zo wurin maigida ka ce na gaya maka menene sa'anka ne ni, wallahi idan baka kiyayeni da abun da ya shafi mai zamani ba, sai na sassaraka na bar wa uwarka tabon daba, makira yar wuta" tamkar gidan ubansa, liti ya kutsa kai ya shiga gidan.

Ya tsaya a tsakar gidan yana kwa?a sallama.

Rahila ce ta fito ta ce "Wane mara mutuncin ne haka a tsakar gidanmu, malam balaggagen gardi ka shigo mana gida".

"?anki ne ya so na shigo, eh sarkin gida nake nema, an ce ya je gada bi?ata,

Please Login or Register in order to submit comment