Reading KARFE A WUTA Chapter 85 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ce "Amin ya haiyyu ya ?aiyyum, bari zamu cigaba da magana da jami'an tsaron, za a kama ainihin mai laifin, za a hukunta shi da yardar Allah, duk wata shaida muna da ita a kansa" suka din ga yi masa godiya, ya wuce ya fita.

Suka ?ara rungume juna, mama ta ce "Lokacin da yarinyar nan take tabattar mini da zata dawo mini da ke, ban zaci da gaske take ba, da zan ganta har ?asa zan dur?usa na yi mata godiya"

Ramma cikin kuka ta ce "Mama ina Sani?"

"Mutumin nan da ya saka aka ?aukkomu, ya kai shi makarantar kwana, ta ku?i"

"Mama wai waye shi? Meyasa ya ?aukko ki?"

"Yana da nasa dalilin, amma ban sani ba"

*MONTHS BACK*

Nabila sai sauri take yi, takalminta mai tsini yana ?ara, tana neman network, domin yin magana da sumayya, har ta dangana da rukunin ofisoshin da ba kowa a wurin.

"Hello, ke Sumayya T ladan, ba network ne, yanzu na samu wuri, ya ake ciki munafukan al'umma"

Sumayya ta ce "Nabila ki daina ce mana munafukai, aiki muke fa"

"Ba wani aiki, tsegumi wanda aka saka ku, da wanda ba a saka ku ba, duk ku ke samowa ku kwatsawa al'unma komai da?insa da ?acinsa"

"Zan ?ura miki ashariya wallahi"

Nabila ta ce "Sorry T ladan, masoyiyyar Nabila, bani labari"

Da sauri Ramma ta ajiye littafin hannunta, jin an ambaci sumayya T ladan, da sauri ta ?arasa gaban window tana zura kai.

"Baiwar Allah, baiwar Allah kin ganni ta nan baiwar Allah" Nabila ta hau waige-waige, taga ta ina ake magana.

"Baiwar Allah wadda take waya, dan ki ?araso wurin tagar nan"

Cikin dakewa Nabila ta ?arasa, ta ragar jikin window Nabila ta ga ramma, ta ce "Lafiya kuwa?"

Ramma ta ce "Ki taimake ni, kamar yadda Allah ya taimake ki dan Allah, na ji kina fa?ar sunan yar jaridar nan, mai aiki a radio"

Nabila ta ce "Eh ya aka yi, kin santa ne?"

"Ban santa ba, taimakona zaki yi, dan Allah ku sanar da jami'an tsaro idan kuna da dama, wani ne yayi mini fya?e, ya sace ni ya aure ni, ba da sanin mahaifiyata ba, ban san a wane halin take ciki ba"

"Yayi miki fya?e ya sace ki? Garin yaya?"

Nan ramma ta gaya mata komai, Nabila ta ce "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, kin san irin neman da muke yi miki kuwa? Ni nake shari'a a kan case ?in ki, har ya fita yana yawo da ke, amma baki yi masa ihu ba, a ?wace ki?"

"Tayaya zan yi masa ihu yana aurena? Kuma idan nayi ihu tamkar na ?ara tonawa kaina asiri ne, wanda ya sanni, da wanda bai sanni ba, sai kowa ya san abin da ya same ni, shi ne mai asibitin nan, shi yayi mini fya?e, sai an bi a hankali idan ba haka ba, ba zai ta?a rabuwa da ni ba, dan Allah ki taimaka mini dan Allah, ina son na je na ga mahaifiyata"

Nabila ta ce "Tsaya, yana baki ci da sha, ko yana dukanki da cin zarafi?"

Ramma ta ce "A'a, baya yi"

"Yauwwa Alhamdilillah, a ina yake ?oye ki?"

"Ban san ina ne ba"ta yi maganar tana kuka.

Samo abu na rubuta miki lambata, ki faki idonsa, ko sa?o ki turo mini, sai ki goge, nayi miki al?awarin zaki ku?uta in sha Allah"

Nabila ta bata lambarta, ta nufo hanyar tafiya, tana yi wa Allah godiya, yadda kayanta suka tsinke a gindin kaba, saboda tsananin addu'a da take yi.

Daga nan ta koma ?ofar ?akin Viper, ?an mama ya hanata shiga.

Kamar yadda suka tsara, Ramma ta yi mata message, Abdul na wanka, Nabila ta bawa Viper, ta ce masa wata lamba take so, a duba mata location ?in ta.

Yana dubawa ya ce "Wannan ai lambar ?an gidan indabo ce"

"Waye Indabo?"

"Mutumin da ya kashe mini jauhar"

Nabila ta rufe baki cikin tsananin mamaki.

"A ina ki ka sameta?"

Ta ce "Kar ka damu, manta kawai" sai da kanta ya sara, ta ina zata fara yi masa wannan mugun jawabin mara da?in ji, indabo ya kashe Nura guduma, kuma yanzu ?ansa ya saceta, bayan yayi mata fya?e.

Wurin barrister Habib ta je, ta sanar masa da abin da ya faru, sun da?e suna mamaki, barrister Habib ya ce "Wannan lamarin ba zamu mi?a shi kai tsaye ga 'yan sanda ba, dan bamu san a hannun wa zamu dan?a ba, yana bu?atar sirri sosai da sosai, kar wani yayi mana katsalandan ya ?ata mana aiki".

Bayan Nabila ta gano Alhaji mu'azzam, shi ya sama musu wanda suka cigaba da tracking in da ramma take, ta hanyar bibiyar lambar Abdul, har zuwa lokacin da aka yi nasarar gano in da take, jami'an tsaron Civil defense, suka je suka ?aukkota

****
Nabila na tsaye na le?en window, ta kasa gane a ina take, wurin shi ba jeji ba, shi dai gashi nan.

Ta koma ta nemi wuri ta zauna, Viper ya shigo da sallama, ta amsa masa, ya je gabanta ya tsaya, ya ajiye mata ledar abinci ya ce "Gashi nan ki ci ki sha magani"

"Vi"

"Mmm"

"Dan Allah ka mayar da ni gida, ina da abubuwan yi da yawa, yakamata na je ta'aziyyar malam garba, na rarrashi iyalinsa na basu ha?uri, bisa ga gazawata, dama ni ban ta?a shari'a na samu nasara ba, kullum fa?uwa nake yi, bani da sa'a" ta ?arasa maganar cikin damuwa.

"Dama yaushe masifaffen mutum zai yi sa'a?"

"Na ji, amma ka mayar da ni gida, ni ban san me ma zan cewa yan gidanmu ba, kwana biyu bana gida, dama ana yi mini i?irarin bin maza, ban san me zan ce musu ba"

Viper ya ce "Na gaya miki, na fisu bu?atar ki, zaki cigaba da zama a nan, har sai kin kammala aikina"

"Wai na cigaba da zama kamar yaya? Sai in din ga ke?ewa daga ni sai kai, ka san dai bai dace ba, idan mace da namiji suka ha?u na ukunsu shai?an ne, ka san bai kamata ba"

Ya sunkuyo dai-dai fuskarta, ya tsura nata jajayen idanunsa, da suke razanata wasu lokutan, zaro harshen sa yayi waje, wanda sai da ta tsorata, saboda ganin tsayin harshensa. Ya ?an ja numfashi ya ce "Lokacin da ki ke sintiri a gidan da nake, kina neman suna, baki yi tunanin na ukunmu shai?an bane sai yanzu? Sai dai kece macen kuma shai?aniyar, idan zamu shekara dubu, baki isheni kallo ba, wadda take halalina ma, sai da.... Sai kuma ya yi shiru.

Ya cigaba da cewa "Kamar yadda na gaya miki, duk wata mace idan ba jauhar ba, namiji ce a idona"

"Katako kake gani ba namiji ba" tayi maganar cikin ?un?uni.

"Ban ta?a ganin abin da ya raina ni ba kamar ke? Amm dama zan gaya miki, ina ganin zan canza lawyer, saboda na lura baki da sa'a ko ka?an, gashi baki wani goge ba, nafi son wanda zai din ga abin da nake so. Idan na biye miki, sai na koma prison, kuma ?ila nima a bini a kashe a can, kamar yadda aka kashe wannan mutumin, dan haka zan canza lauya".

?agowa tayi tana kallon Viper, cikin tsananin mamaki da takaicin abin da yake fitowa daga bakinsa.

Fuskarsa a ?aure, alamar da gaske yake yi.

"Bayan duk wannan wahalar da na riga na sha? Ka san zaka ?auki wani lauyan, amma ka wahalar da ni, nake ta dagewa ina ?o?ari a kan shari'ar ka na kasa zaune na kasa tsaye?"

Viper ya ce "Eh, muddin zaki cigaba da yi mini rashin kunya, tabbas zan sake saka miki ?arfe wataran, kamar yadda na saka miki da farko, na gaji kin kasa kawo ?arshen lamarin, kullum sai surutu da shirme ki ka iya"

Tamkar ta kwa?e shi, haka wani abu ya cunkushe mata ?irji, kawai ta kifa kanta a kan gwiwarta.

"Abla, ?ago ki ga" banza tayi masa ta?i ?agowa.

"Kin san magana ?aya nake yi" ta ?ago idanunta, da suka yi sharkaf da hawaye.

Ya ajiye mata takarda a gabanta, takardar umarnin kotu ce, da ta hana kama shi, ?agowa tayi ta kalleshi, ta rasa ihu zata yi na murna ko kuma me? Kawai ta cukuikuye takardar, ta jefa masa a ?irji, ta sauka daga kan gadon tana cigaba da kuka"

Murmushi ya yi ya tashi ya bi bayanta, cikin kuka ta ce "Amma a haka kake cewa zaka canza lauya?"

Ya ce "Sorry, am just kidding"

"A haka ake wasa Vi?, fuska a ?aure ana zare ido? Tayaya zan gane wasa kake yi?" Tayi maganar tana kuka cike da shagwa?a.

Ya ce "Viper baya manta halacci, ba kuma ya sa?a al?awari, ko da zaki yi failing sau dubu, ba zan ta?a barin ki ke ka?ai ba, al?awari ne da na ?auka"

Nabila ta ce "Look at you, i even save your life, amma da haka zaka yi mini albishir da 'yar ?aramar nasarar da nayi" ya girgiza kai ya ce "Ba ?aramar nasara ba ce Congratulations, and barrister Habib ya yi miki message, Civil defense sun ?aukko rahama" a take ta waro ido ta ce "Dan Manzon Allah, da gaske?" Ya jinjina mata kai, alamar eh.

Rikicewa tayi, ta dur?usa tayi sujudu shukur, ta tashi, ta shiga kaiwa tana komowa ta ce "Alhamdilillah, ko yanzu na mutu, na cika wani sashe na al?awarin da nayi, Allah sarki malam Garba, Allah ya yi masa rahama, ni me ma zan yi ne dan da?i Vi?"

Murmushi take yi, tana kuka, tana ta zarya a ?akin, kamar zata zare, shi kuma sai bin ta yake da ido. Ta je ta tsaya a jikin bango, ta jingina tana sauke numfashi.

Ya sake takawa, ya ?arasa in da take ya saka hannunsa ?aya ya dafe bango, yana cigaba da tsareta da ido.

"Thank you for saving my life 'yar suga" duk da ta takura, amma bai hanata yi masa murmushi ba.

Kallonta yake yi, yana tunanin a yaya zata ?auki ?addarar da take bibiye da ita? Ko zata iya jurewa, ko zata gaza kamar yadda yayi? A hankali ya ce "Wannan babbar nasara ce ki ka samu, kamar yadda nayi tsammani, ba kya gori, kamar yadda Jauhar take, na zata da na ce zan canza lauya, zaki yi mini gori, amma ba ki yi ba.
Akwai tambayoyi da ki ka yi mini a baya, da wasu wanda nake son na yi miki.
Da fari meyasa nayi yin?urin kashe ki karon farko da na ganki? Meyasa ki ka ga ru?ewa a fuskar liti da walid da suka ganki? Meyasa na din ga korarki idan ki ka zo wurina, nake yi miki barazanar mutuwa? Meyasa su liti suka amince su kawo ki wurina, duk da babu mahalukin da suke bawa damar hakan? Meyasa Indabo ya ke ?o?arin yi mini tarko da ke? A yanzu ko a baya, ba za a rasa mutanen da suka nuna miki sanayya ba, alhalin baki san su ba right?" Ta tsare shi da ido tana jiran amsohin tambayoyin.

"And as my lawyer, akwai abubuwan da yakamata na sanar da ke, but before then, Abla ni da ke ?addara ce mai ?arfin gaske ta ha?a ni da ke, dan haka dole mu yi ha?uri, mu kar?eta a yadda ta zo mana, saboda pain ?in da zaki shiga, zai iya fin wanda ni na tsinci kaina a ciki"

Tayi tsuru tana kallonsa.
Ya zaro wani hoto a aljihunsa, ya mi?a wa Nabila.

Hannunta na rawar rashin sanin wace ?addarar ce, ta sanya hannu ta kar?i hoton, wata 'yar ?aramar ?ara ta saki, ta saki hoton a ?asa, jikinta yana rawa, ta kalleshi ta ce "Soka ke sai na haukace sannan zaka daina yi mini wasa da hankali, menene wannan? Ni bani bace wannan, ni yaushe na sanka har muka yi wannan hoton tare?" Tayi maganar a firgice, tana neman ta ra?a shi ta wuce, amma ya ri?eta a jikin bango, idanunsa suka cika da hawaye ya ce "Matata ce a jiki, ita ce jauhar, 'yar madarata, mace mafi soyuwa a gare ni, matar da ba zan manta halaccinta ga rayuwata ba, matar aljanna da kullum nake fatan na farka daga mummunan mafarkin da nake yi, na farka na ganta a kusa da ni, Nabila meyasa ki ke kama da matata?" Jikinta ne yake wata irin rawa, ta zazzaro ido tana kallon sa.

Bu?e ?ofar ?akin aka yi, suka waiwaya gaba ?aya suna kallon ?ofar, Alhaji mu'azzam ne ya shigo tare da barrister Habib, da kuma ?an mama, da yake la?ewa a baya, yana le?owa.

Cikin mamaki Viper yake bin Alhaji mu'azzam da kallo, ba tare da ya saki Nabila ba.

Ayshercool
08081012143
???500 ne via 0009450228
Aisha Adam jaiz bank sai shaidar biya ta 08081012143
Wanda za su jira document 1K ne.

90009343
'Yan Nijar ku turo katin airtel na 300fcfa

https://whatsapp.com/channel/0029Va9QtrY4dTnBYG1hST2VHADARIN

*BRIGHT PENS SECOND BATCH*

Ku kasance da littatafan bright pens, second batch.
*?ARFE A WUTA (AYSHERCOOL)*
*MUTALLAB (NIMCYLUV)*
HADARIN GABAS (NAZEEFA NASHE)*
*ZAYTOON (ZEE KUMURYA)*



Cak Viper ya tsaya yana bin kankarofi da kallo, zuwa kan ?an mama da yake ta zazzaro idanu.

Kankarofi ya ha?iye wani abu mai ?aci, saura ?iris ya yi loosing control ?in sa, saboda yanayin da ya ga Viper da Nabila.

Viper ya a janye hannunsa a hankali, ya tsaya a tsakiyar ?akin, su kankarofi suka shigo.

"Meya kawo ka in da nake?" Yayi maganar a kausashe.

"Haba ?anina, mayar da wu?ar mana, abun rabo ya ?are, mi?a hannu na menene, bai kamata ace zuwa yanzu muna cigaba da wannan abubuwan ba, ko da ran jauhar, ko babu mallakinka ce, matarka ce dan haka ba zan din ga bibiyarta ba, balle yanzu da babu ranta, ka sassauta wannan kishin dan Allah. Ga Anas, wato ?an mama yaronka na hannun damanka, da duk wani nasarar aiki da muka yi a kanka, ya faru ne saboda ?o?arin sa, sai dai kan mu kai ga bayyana maka komai, ashe ka gano shi, ya gudo wurina hankali a tashe, ya ce na taimake shi, ba zai iya jure hukuncin da zaka yi masa ba, na zo on his behalf, na bayar da ha?uri kuma nayi maka bayanin komai"

Viper ya bi ?an mama da wani irin kallo, ?an mama ya ce "Na shiga uku, dan girman Allah Oga Viper kayi ha?uri, tursasa mini aka yi, wallahi bani da niyyar cin amanarka, ban ta?a cutar da kai ba, ka san ina yinka, kamar yadda ka ke yi na, kayi mini rai saboda Allah"

Alhaji mu'azzam ya ce "Ya isa haka Anas, ni yakamata na wanke ka" duk maganar nan, Viper idonsa na kan ?an mama, ?an mama ya sake ma?alewa a bayan Kankarofi ya ce "Gaskiya daga nan kayana zan tattara na gudu Cadi, kallon nan da yake yi mini, tsoro yake bani, bana tunanin zai yafe mini, da ?yar idan bai saka na gana da Russia ba"

Kankarofi ya ri?o hannun ?an mama, suka ?arasa gaban Viper, ya numfasa sannan ya ce "Lokacin da uban gidanka yana raye, Dodo, ka fi ni sanin waye shi, ka fini sanin hatsarinsa da imaninsa. Babu wanda ya bawa damar sanin sirrikan da yake da su, kuma ya sani sai kai.
Duk da shi ma mai aikata laifi ne, amma yana yi wa hukumomi amfani sosai wurin kama masu laifi, daban-daban.
Ya baka horo na musamman, ta yadda yake gane masu laifi, komai kamalarsu, yadda yake iya gane idan akwai kayan laifi a wuri, bai tsaya nan ba ya saka aka baka horo na musamman, a kan fasahar na'ura mai ?wa?walwa.
Manyan ?asar nan na mu'amala da shi sosai da sosai, dan ya san duk wasu hanyoyi da za a iya shiga da fitar da kayan laifi, ciki da wajen ?asar nan, ba tare da ta an kama kaya ba, sukan ha?a kai da shi, su bashi dukiyoyin su, ya yi musu kasuwancin ?wayoyi da sauran kayan laifi, ya ru?anya musu riba a shekara".

Viper ya ce "Duk meye amfanin dawo da abin da ya riga ya wuce, abin da na riga na sani, kar ka aibata gawar uban gidana"

Kankarofi ya ce "Ba aibata shi nake yi ba, kayi ha?uri na sadaka da ga?ar da nake son na kai ka. Dodo yayi shirin yin murabus, bayan ya koyar da kai manyan abubuwa, da ka iya zama makamin rusa wasu daga cikin manyan hanyoyin aikata laifuka da ba kowa ya sani ba.
Daf da zai mutu, ya dan?a amanarka ga manyan mutane da ya yarda da su, ciki har da shugaban hukumar NIA na wancan lokacin, ya basu tabbacin zaka iya basu gudunmawa ta kowane ?angare, suka?ai ne hukumar da ya yarda ya dam?a amanarka a hannunsu, duk da kasancewar baka ji, amma kai babban makami ne, ka san manyan sirrukan da bayan shi babu wanda ya sani.
Bayan mutuwar dodo, sun bu?aci kaje su baka horo, kayi aiki da su, amma ka ?i, saboda zuciyarka da tunaninka na kan ?aukar fansa a kan madaki, kuma rashin yadda ya sanya ka sake cewa ba zaka je ba, dan baka da tabbacin ta wace hanya zasu yi amfani da kai.
Bayan aurenka da jauhar, bayan na shiga damuwar rashinta, wataran muna hira da cousin ?ina, wanda shi ne aka dan?a amanarka a wurinsa, muna hira, yake bani labarinka, a nan na gano cewa lallai kai ne ake magana a kai, na cigaba da matsa masa, a kan lallai suyi ?o?arin su ga sun ?auke ka, zaka yi musu amfani sosai, a lokacin ina fatan silar aikin, ka daina wani abun, kuma ka samu hanyar kula da Matarka.
Har bincike na saka aka kuma yi mini sosai a kanka, a nan na gano kana aiki da Indabo, abin ya ?aure mini kai ya bani mamaki.
Bayan wani lokaci, ban san meyafaru ba, na samu labarin ka je ka basu ha?in kai, an kama ?an gidan indabo a Mexico, da laifin safarar cocaine, duk da babu wanda ya sani, amma ni ina da hanyar samun bayanai na a kanka.
Na cigaba da fatan Allah yasa daga haka su hilace ka, ka amince da aikin nan, amma sam baka da intrest a kan haka.
Wasu lokutan Hafsa kan bani labarin, irin soyayya da ?aunar da ka ke yi wa jauhar. Kwatsam na samu labarin mutuwar ta, wai ka sha miyagun ?wayoyi ka kasheta, sai dai sam ban ji na yarda ba.
Daga yadda na bibiyi case ?in silently, naga sam babu adalci, a yadda aka gudanar da binciken da gurfanar da kai ?in ma a gaban kotu, kuma na samu labarin abokin gabarka, Madaki shi ya maye gurbin aikinka, a wurin Indabo.
Ni na saka aka kamo Anas ?an mama, aka matsa mini shi, yadda yakamata kasancewar sa, yana cikin tsagerun dabar Madaki.
Shi ya tabattar mana da Madaki ne ya kar?i kwangilar kasheka a wurin Indabo, amma azal ?in ta hau kan matarka.
A lokacin shugaban ?asa ya samu nasara a tenure farko, kuma yayi mini S.A ?in sa na fannin tsaro, haka zalika ya tafi da ?an uwana a matsayin shugaban hukumar NIA.
Sosai nake biyan ?an mama, ya koma wurin su Walid, tun suna korarsa, suna hantararsa, har suka saki jiki da shi a dabar su, duk da kasancewarsa yaron madaki, suka bashi cikakkiyar kariya daga Madaki, yana reporting duk wani motsinka a gareni, da kuma hukumar NIA, hakazalika ni ne nake tura maka sa?onni. Tabbas nayi amfani da kai dan cimma nawa muradin a kan indabo, kuma taimakonka nayi, sauran abin da ya faru ka sani, ni nake sanya a goge duk wani sahun laifi daka aikata, ta hanyar amfani da jami'an Civil defense, kan daga baya, hukumarku ta kar?i ragamar cigaba da kula da kai, tare da turo maka gayattar dawowa ka cigaba da aiki da su ta hanyar ?an mama, da yake ajiye maka rigunan aiki, ina nema masa afuwa, shi ma umarni aka ba shi da dole ya bi"

Viper ya din ga ha?iyar wani yawu mai zafi, yana son yayi magana, Nabila ta dafe kanta ta ce "Wannan wane irin abu ne wai, gaba ?aya sai juya mini kaina ake yi, na kasa gane komai, wai menene haka" tayi maganar cikin ?aga murya, tana dafe kanta. Viper ya juya ya koma in da take, ya dur?usa ya ?auki hoton Jauhar da yake ?asa, kawai Nabila ta tafi zata fa?i, idanunta a lumshe, ya ri?e ta, amma ya kasa magana,a hankali ya ja ta, ya mayar da ita kan gadonta.

Ta ce "Bana gani, duhu nake gani, kaina zai fashe" kankarofi ya nufo gadon, amma Viper ya ?aga masa hannu, ya ce "Excuse us please"

Kankarofi ya tsaya yana kallon Viper, Viper ma ya ?ura masa ido.

Barrister Habib ya ce "Ina son zan yi magana da ita"

Viper ya ce "Ka jira tukuna" Kankarofi yayi musu alama, da su fita, haka duk suka fice.

Nabila ta dafe kanta, ta cigaba da kuka, ya ce "Wai kukan me ki ke yi haka?"

"Ni ka rabu da ni dan Allah, ka ?yale ni, so ka ke na haukace, gaba ?aya kun ru?a mini kai, sai ?ara bijiro da wasu abubuwa ku ke yi da ban san da su ba, ni ka rabu da ni".

"Ki tsaya ki saurare ni"

"Ba zan saurareka ?in ba, ba na son jin komai, ni ka rabu da ni"

"Am talking and you are misbehaving" yayi maganar cikin tsawa.

A razane ta dafe kanta, ta fa?o daga kan gadon, ta takure a wuri guda tana kuka.
Ya tashi ya sake dawowa gabanta, amma ta hau jifansa, da abun da duk ta samu a kusa da ita. Shiru yayi yana kallonta, yana tuna lokacin da jauhar ta burkice masa, da yayi mata laifi, ta din ga jifansa da kwanuka, yayi ajiyar zuciya ya kira wayar Asibiti. Mintuna ka?an likita ya shigo, ya tarar da Nabila kamar mai shirin zarewa, ya yi mata magana, amma tayi masa shiru.

Ya fita ya dawo da allura, ya kama damtsenta zai yi mata, ta?i tsayawa, sai da Viper ya ri?eta aka yi mata, sannan jikinta ya saki ta hau lumshe ido.

"Viper, garin yaya ta zama haka lokaci guda? Ba ta fara samun sau?i ba?"

Viper ya ce "Ta ?an samu damuwa ne, idan ta farfa?o ta samu sau?i, kawai a sallame mu"

Likitan da yake sanye da wandon sojoji ya ce "Viper, discharge kuma? Why? Ba haka aka shirya ba, tana ?ar?ashin kulawar hukuma, kai fa shegen taurin kai ne da kai, sai ka janyo wata matsalar tukuna?"

Viper ya ce "She's not safe here, zamu bar wurin nan"

"Zuwa ina kuma? Akwai wanda zai shigo cikin barrack, ya zo asibiti yayi mata wani abu ne?"

"John, i want her to be discharged"

John ya ce "Ko nayi discharging ?in ta, ka san ba zata bar wurin nan ba, sai an bamu izinin hakan. Let me help you put her to bed, she's already sleeping on the floor" wani irin mugun kallo Viper ya yi masa, ya ce "Ohh sorry" ya juya ya fice.

Viper ya sunkuya yana kallonta, fuskarta ta koma ja, sai tsatstsafar da gumi take yi, da gani baccin na dole ne kawai saboda allurar da aka yi mata.

Zai iya cewa ya bai ta?a ganin mace mai naci, da tsantsar jarumta, kamar Nabila ba.

Duk da baya son ta?a ta da yake yi, amma dolensa ya ?agata ya mayar da ita kan gadon, ya gyara mata kan gadon, ya juya ya fito.

A waje ya tarar da Alhaji mu'zzam da barrister Habib, da ?an mama a zazzaune.

Ya taka ya ?arasa gaban Alhaji mu'azzam, ya ce "Meyasa ka za?i irin wannan lokacin, ka gaya mini wannan maganganun a gabanta? Na gaya maka ni zan kawo ?arshen wannan lamarin, tun da ni ya shafa, abu ne mai nauyin gaske da ?aukarsa ba lallai ya zama abu mai sau?i a gareta ba. Dan haka bana bu?atar ka a cikin abin da ya shafeni ya shafi abin da ya shafe ni. Wadda ta ha?a ba rabonka ba ce ba, ban san dalilin da zai sanya ka din ga bibiyar rayuwata ba kamar kana bi na bashi ba"

"Muddin za a bayar da labarin jauhar, dole mu'azzam zai fito a ciki, ban cigaba da bibiyarka dan ina neman wani abu a wurinka ba, na bibiyeka na taimake ka ne, domin mu taimakawa juna, daga ni har kai, bu?atata ta biya kaima taka haka, naga bayan indabo, kai kuma ka ?auki fansar tozarci da zaluncin da aka yi maka.
Ban da ?addara ta Ubangiji, na rigaka ganin jauhar, kuma aurenta nayi niyyar yi, amma Allah ya nufa matarka ce, na so jauhar so na ha?i?a, amma na kawar da kai, duk na shiga tashin hankali jin irin mutumin da ta aura, yanayin zamanku daga baya ya sanya na samu kwanciyar hankali, kisanta da abin da aka yi maka ya bani ya sanya na tausaya muku nake bibiyarka.
Nabila ma na rigaka ganinta, ni ba a garin kano na fara ganinta ba, tun a Abuja wurin da aka basu rantsuwar zama cikakkun lauyoyi.

Please Login or Register in order to submit comment