Reading KARFE A WUTA Chapter 98 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ku yi"

"Babu abin da ya yi miki zafi" ?aya lauyan ya yi maganar a kausashe.

Abdul yasar ya ce "Dan Allah kar aje a wahalar da ni, ni dai na yi dan Allah ku bar ni haka"

Nan dai aka yi ta muhawara da musayar yawu, Abdul ya nemi a bashi ko mintuna goma ya yi magana da ramma, amma Viper ya ce ba za'a bayar ba.

Nabila ta ce "Mijinta ne fa, haryanzu da aurensa a kanta, ka ?auki komai a hankali mana"

Wani ofishin aka kai Abdul tare da ramma, bai tsaya jin nauyi ko kunyar ?an sandan da yake kansu ba, ya rungumeta ?am a jikinsa, yana wata irin ajiyar zuciya.

Cikin kuka ta ce "Ka yi ha?uri Abdul, al?awari ?aya zan yi ?o?arin cika maka, ganin cewa cikin jikina bai salwanta ba, ka yi ha?uri dan Allah"

"Rahama, ni mai laifi ne, na da?e ina aikata laifuka iri-iri ba a hukunta ni, sai a kanki, da ki ka zama ?addarata, rahama so masifa ne, kwanakin da na yi babu ke kamar zan yi hauka. Tsare mahaifina a Abuja, bai yi mini zafin rasa ki da na yi ba. Na san hakki ne yake bibiyata, ni ko da za a hukunta ni, dan girman Allah ki yafe mini, wallahi yanzu na fi tsoron Allah da irin hukuncin da za ayi mini. Kin kwa?aitar da ni, da nuna mini muhimmancin tsoron Allah, Astagfirullah".

Na ta hannun ta saka ta zagaye gadon bayansa ta ce "Ina ma ba ta haka ?addara ta ha?a mu ba, da zan jarraba jurewa na zauna da kai, na yi kamar yadda na ji tarihin rayuwar matar Viper, duk da na santa amma ba ni da wani wayo sosai lokacin. Ka yi ha?uri hukunta ka kawai shi zai rage mini ra?a?in da nake ji, da tabon da ku ka yi wa ahalinmu"

Ya jinjina mata kai ya ce "Na fahimce ki, zan so jin tarihin rayuwar matar Viper, duk da shi na sani, shi ya yi wa mahaifina aiki, ban san wace irin tsatstsamar ala?a ce a tsakaninsu ba, har yake son ?aukar fansa ta ?arfin tsiya a kaina ba. Idan kin kawo mini ziyara prison sai ki bani labarin" tayi shiru ba ta ce masa komai ba.

"Zan ba wa lauyana lambar wayar su saifu, su tuntu?i lauyar ki, a dam?a miki ku?inki, da ku?in kula da kanki da zuwa asibiti da rainon yarona, yayi maganar yana shafa cikinta da ya ?aga ka?an.

Ajiyar zuciya kawai take ta saki, ya ?agota a hankali yana kallonta, ita ma ta yi rama sai dai fatarta ta ?ara kyau.

"Dan Allah ko an yanke mini hukuncin, dan Allah rahama kar ki bari a raba aurenmu, na san ba lallai na yi tsawon rai, ciwo nake har da aman jini, dan Allah kar ki bari su rabani da ke, dan Allah"

Ramma ta gya?a kai ta ce "Allah ya sa kar su fi ?arfina"

"Amin sweetheart" ba ta yi aune ba, ya ha?e bakinsa da nata cikin tsananin kewarta.

?an sanda ya kawar da kai gefe, duk dambarwar bala'in da aka gama yi, bai dame su ba.

Ya dafo kafa?arta su ka fito, Viper ya na tsaye, kamar ya fashe, Babar ramma ce wa take "Wallahi Aminu ka yi mata duk hukuncin da ya dace, ban ta?a tunanin ramma za ta aikata abin da ta yi ba".

Nabila ta ce "Mama ni fa na fuskanci ramma, wallahi ki ka bar ta da shi, za ki iya dawowa daga baya ki yi da na sani, ku yi ha?uri na yi magana da ita na fahimceta"

Can ma babar Abdul masifa take yi, "Wace irin jaraba ce haka Abdul, yarinyar da su ka gama tozartaka yanzun nan, shi ne ka wani dafo kafa?arta ka na ?us-?us?"

Babu wanda Abdul ya kula, ya sunkuya dai-dai kunnenta ya ce "Dan Allah rahama kar ki auri wani, sai dai idan mutuwa na yi, ina sonki your excellency" murmushi ne ya su?uce mata, ta ?wace kafa?arta, ya yi murmushi ya ?arasa wurin yan sandan da su ka zo da shi.

'yan sanda su ka tabattar musu da cewa za su kai su kotu, bayan sun kira Naja'atu Bunkure ita ma sun ?auki statement ?in ta, domin kuwa har da ita su Nabila shigar da ?ara.

Kunnen ramma Viper ya ri?e, ba wani ri?on kirki ya yi mata ba, amma kamar ta yi fitsari.

"Ashe ba kya ji ba ki san ciwon kanki ba ko? Ba kya tausayin kanki ba kya na mahaifiyarki, babu yayanki sunanki ya ?aci, amma duk hakan bai ishe ki ba ko? Idan ki ka kuma misbehaving, ko kuma ki ka sake yin wani abu da sunan a raga masa, sai kin bi shi prison ?in"

Nabila ce ta din ga yi masa magiya, da kyar ya saki kunnen ramma, da take ta uban kuka.

Nabila ta yi ta rarrashinta, ta saka su a mota, tare da ba wa mahaifiyar ramman ha?uri, a kan kar ta je ta ce za ta yi mata fa?a a kan abin da ta aikata, lamari ne na sun yi zaman aure mata da miji, babu wanda ya san irin zaman da suka yi, da haka su ka tafi, Nabila su ka yi sallama da Sumayya.

Ita kuma tare da Viper su ka tafi ma'aikatar Shari'a, sai dai ya cika ya batse dan daga ita har rammar a ?ule yake da su, gani yayi ma kamar Nabila goyon bayanta ta yi, idan ya yi wasa, biye wa Ramma za ta yi, su kasa ta?uka abin arziki a kotun.

"Vi" ta kira sunansa. Bai amsa ba, ba ta damu ba, tun da ta san ya na jin ta.

"Ka yi ha?uri, ba na nufin yin wani abu da zai ?ata muku rai, amma ka kalli abin da na yi cikin tsanaki, ban ji dadin abin da ka yi wa rahama ba. Sai kuma abu na gaba, ina sake yi maka tuni game da mahaifinka, ya na cikin tsantsar damuwa, jiya na da?e ina waya da shi, ya na bu?atar ka a cikin rayuwarsa, kai ne sitiyarin da ya rage, na saita gidanku, ya na kewarka, kuma ya na neman afuwarka" yayi mata shiru, ita ma ta na gama yi masa bayani, ta fice.

****
Major ya na zaune a ofishin sa na gidan gonarsa, ya jera hoton Nabila, da na chuba?o da kuma na Jauhar da Viper da Nasir ya kawo masa.

Duk rabonsa da jauhar, tun ta na jaririya, amma babu in da kamaninta su ka bar na Nabila.

Hakazalika babu in da su ka bar kamanin chuba?o, mamaki ya din ga yi yadda aka ce masa jauhar ta na raye, bayan an tabbatar masa da ta rasu. Kuma ya san wanda ya gaya masan ba zai yi masa ?arya ba. Amma da ya san za ta rayu da bai kai wa Bashir ita ba, duk ha?awa zai yi ya ri?e su, amma saboda tsabar rashin mutunci bayan azabtarwar da Bashir ya yi wa chuba?o, ?arshe ya rasa abin da zai yi wa 'yar ta sai ha?a aurenta da ?an daba, wanda ya yi ajalinta, kuma yanzu wai Nabila take kare wanda ya kashe ta ?in, kuma har ya na goyon bayan kare wanda ya kashe yarinyar, a take ya ji ya ?ara tsanar Bashir, gaba ?aya yayi dana sanin saninsa a rayuwarsa, ya rusa musu dukkanin farinciki da walwala.

***
Ma'aikatar Shari'a ta sahalewa Nabila damar tsaya wa Viper a kotu, dan haka bakinta ya saka rufuwa, saboda murna.

Sumayya kuwa tuni ta watsa hirar da su ka yi da ramma, yadda ta yi bayanin, yadda Naja'atu Bunkure ta din ga yi musu sintiri a kan lallai, su kar?i ku?i su yi shiru da bakinsu.

Hakan ya ?auki hankalin mutane, wasu su na cewa ?arya ne, hayar yarinyar aka yi, domin ?atawa Bunkure suna, wasu kuma su na Allah wadai da abubuwan da ta aikata.

Hannun Bunkure na karkarwa, ta ke karanta takardar gayyatar da aka yi mata hukumar 'yan sanda, amma ta yayyaga takardar, ta watsar ta na huci, babu wata hanya da za ta bi, ta fitar da kanta, duk ma su tsaya matan take zuba rashin mutunci, duk sun watse sun barta.

Viper ya na zaune a falon madam Halima, ya na ?arasa aiki a wayarsa, kafin ya tafi.

Nabila ta fito ta tarar da shi, ta ?auka tuni ya tafi, tun da ba su dawo ba, sai magariba, har wurin aikinta su ka je, ta ha?u da barrister Habib, sannan abokan aikinta sun ?ara mata ?warin gwiwa sosai da sosai.

Ta zauna a kujerar gefensa, ta ce "Vi" ya amsa da "Mmm" ba tare da ya kalleta ba.

Ta ?ura masa ido, ta na tunanin ta ina za ta fara cire ?aunar bawan Allah nan daga cikin zuciyarta, a yanzu haka cikin tsananin sauri zuciyarta take bugawa, ya yi kyau sosai da sosai, duk da ba ma'abocin fara'a ba ne, amma a nutse yake gudanar da aikin. Bai damu da kallon da take yi masa ba.

Ganin ba zai ce komai ba ya sanya ta ce "A ina ka ke kwana ne yanzu?"

"In da ki ka sanni"

"Ba za su baka wuri a barrack ka zauna ba, zamanka a wurin can, akwai hatsari fa"

Ya girgiza kai ya ce "Wuri ne mai tarihi a rayuwata, ba zan iya barin su Walid suka ?ai a wurin ba"

"Ka na da al?awari wasu lokutan"

"Wasu lokutan fa?"

Ta ce "Ka na da zafi sosai" ya gya?a kai kawai.

Shiru ya yi ya na kallon wayar, sai kuma ya ?ago ya na kallonta, "Meyafaru?" Ta yi maganar a hankali.

Ya girgiza mata kai sannan ya ce "Yaushe za ki je gida wurin Abbanki?"

Nabila ta ce "Ina son zuwa, saboda ina kewarsa, a duniya ina matu?ar ?aunar Abbana, duk da na yi farinciki da ganin mahaifina, amma so da sha?uwar da nake yi wa Abba ya mamaye ilahirin zuciyata, amma a ?adamin da ake yanzu, Abba ya na matsanancin fushi, ban ga alamar sassauci a tare da shi ba, kuma akwai ziga da ga ?angaren Nasir, da mutanen gidan.
Ai na kira shi mun yi magana, ya ce muddin ina son farincikin sa dole na bar shari'arka, tun da kai ka kashe 'yar uwata, kuma sai na fita harkar mahaifina dan ba mutumin kirki ba ne ba. But na ga kamar akwai magana a bakin babana, amma ban ga alamar Abba zai ba shi damar hakan ba, ya sake ?aukar zafi sosai da mutuwar jauhar.
Am confused now, na rasa me ma yakamata na yi, har ga Allah ina son mahaifina, kuma Abba ma ina ?aunarsa, na yi ?o?arin fahimtar da shi, amma ya?i fahimta ta, dama ni na mutu na huta ba jauhar ba, ina nema na sare na gaji wallahi"ta yi maganar tana share hawayenta.

"Ita jarrabawa ba a cewa an gaji, keep trying you will succeed " yayi maganar ya na mi?a alamar gajiya. Ya kashingi?a da jikin kujera ya lumshe idanunsa.

Sosai ya ?ara kyau a idonta, ba ta san lokacin da murmushi ya su?uce mata ba, a hankali ya motsa ya tashi ya ce "Ki cewa madam Halima na tafi, sai da safe"

"Allah ya tsare hanya, ka gaishe da oga walid"

Ya jinjina mata kai ya fice. Wurin da ya tashi ta ?urawa ido ta yi shiru cikin damuwa, da ta warware wannan matsalar sai wannan,a haka tayi bacci a wurin, ba tare da komawa ?aki ba.

Da Viper ya koma gida, sai ya kasa bacci, juyi kawai ya din ga yi a kan katifarsa.

Ya ?aukko wayarsa ya duba lambar Nabila, ya din ga kallon lambar, sosai take ba shi tausayi, duk da ta tashi cikin gata, rayuwarta na ?auke da ?alubale na musamman, ya sarawa juriyarta da gwagwarmayar ta.

Ya san da Jauhar ce, babu lallai ta iya jure duk wannan abubuwan, ba ta son tashin hankali, duk wani abu da zai janyo mata damuwa ba ta fiye son sa ba.

Nan ya sake jinjina girman Ubangiji, ya ci burin sanya Jauhar zama lauya, dan ya samu ta rage tsoro da kuma taimaka masa, a kan wasu abubuwan, dan ya san al'umma za ta amfana da ita, kwatsam burinsa bai cika a kanta ba, Allah ya kar?i a bar sa, kuma kwatsam ya ha?u da 'yar uwatta a matsayin cikakkiyar lauya, kuma kowacce ta taka muhimmiyar rawa a rayuwarsa, rawar da ba zai ta?a mantawa da ita ba. Duk da Jauhar rayuwarsa da ita ta mussaman ce, amma shigowar Nabila rayuwarsa ta ?ara haska masa, zai iya zama mutum ya nemi hakkinsa. Sai da maganganunta na baya bayan nan, haka nan su ke sukar zuciyarsa lokaci zuwa lokaci, cewa da ta yi, su yi zumunci kawai. Ya lumshe idanunsa a hankali tare da ?ora wayar a kan ?irjinsa.

***

Alhaji mu'azzam ne a tsaye tare da Baba su na tattaunawa.

"An so zuwa tun a last week ?in, amma Allah bai yi ba ina Abuja, ashe Nabila 'yar uwar jauhar ce?"

Baba ya ce "Eh, 'yan biyu ne amma ya aka yi ka sani?"

Ya numfasa ya ce "Tun shekaru uku baya, na ganta a Abuja, na cigaba da bibiyarta, amma a iya binciken da na yi na tarar da Jauhar ba ta da wata 'yar uwa. Ba na son zuwa gidan nan, saboda jin nauyin abubuwan da su ka faru.
Ha?i?a na ci gaba da bibiyar rayuwar Viper bayan mutuwar jauhar, kuma kwatsam na ga Nabila ta shiga rayuwar sa, shi ya yi ta yi mini kashedin, kar na kuskura na sanar wa wani har ita Nabilan, ta na kama da matarsa, na ?yale su, sai kuma nake samun labarin ya kawo maka ita ina taya ka murna"

Baba ya ce "Na gode, Na gode sosai da sosai Allah ya biyaka da gidan Aljanna, tabbas ba ni da bakin yi maka godiya" sun da?e su na tattaunawa kafin ya tafi.

Nabila na ta shiri, za a fita da ita a kaita wurin aiki, sai ga kiran waya, ba ta san lambar ba, amma ta ?aga su ka gaisa da mutumin ya ce "Sunana barrister Nazifi Bala, lauyan Abdul yasar ma'aruf Indabo"

Nabila ta yamutsa fuska ta ce "Yaya aka yi?"

"Eh dan Allah lokaci za ki bamu, ki taho da ramma, zamu tattauna da Abdul za'a dam?a miki dukiyarta"

"Wace irin dukiya kuma, ni fa ba na son salon yaudara da cin hanci, idan ku ka bamu corruption zamu kar?a, but use it against you guys"

Barrister Nazifi ya ce "Ba corruption ba ne ba"

Ta ce "Shikenan, zan zo nan da ?arfe sha biyu na rana, amma ba zan zo da ramma ba, ban san me za ku yi mata ba"

Ya ce "Shikenan, ta zo itaka?ai ?in"

Ba ta je office ba, ta tafi gidan su sumayya, sun sha hira da umman sumayya, umman ta din ga yi mata addu'a, tare da yi musu fatan alkhairi da addu'oi.
Yanzu tare su ke komai da Sumayya, Sumayya na biye da Nabila domin samo labarai kala-kala.

Babban abin da ya ba wa Nabila mamaki, bai wuce ganin Saifu a wurin ba.

Cikin mamaki ta ce "Wannan ba a gidanmu ka ke ba, yaya saifu ko?" Ya mi?e ya ce "Nabila, me ki ke yi a nan?"

"Ni ce lauyar rahama, wadda Abdul ya yi wa fya?e, me ka ke yi a nan?"

Jiki a sanyaye ya ce "Abdul abokinmu ne, tare muke da shi"

Cikin takaici Nabila ta ce "Tare da ku ya yi garkuwa da yar mutane kenan bayan ya yi mata fya?e? Kun san in da ya ?oye ta, amma ku ka rufa masa asiri? 'yar uwar Viper ce, sister ce a wurinsa yanzu ba su da kowa sai Allah sai shi"

Sai yanzu Abdul ya samu amsar sa, ya rasa dalilin da ya kawo Viper cikin shirgin ramma, da ya zo ya na ta za?ewa.

Cikin ?arfin hali ya ce "Ba su san duk abin da na aikata ba, ki zauna ki ji menene. Amma saifu a ina ka santa?"

"?anwar nan ta wa da Viper ya kashe jauhar, 'yan biyun ta ce, bamu sani ba sai just recently" ya jinjina kai ya ce "Ga lauyana, na ga ke ce lauyar rahama, kuma jikina ya bani zaki yi amana, dan haka ku?i nake son mu dam?a miki, na kula da rahama, zuwa lokacin da za ta haihu, dan Allah a duba asibitin da za a kaita dan kula da rainon cikin, kar wani abu ya same su. Ban sani ba ko zan rayu ko ciwo zai yi ajalina dan Allah ki tsaya iya yinki ki kula da ramma ta yi karatu, na lalata rayuwarta, ko ba duka ba, ina fatan ta zama wani abu a rayuwarta"

Ita kanta Nabila duk da ta ?auki zafi sosai a kan shari'ar, amma ta fahimci abubuwa da dama bai san an yi su ba, Nabila ta kar?i kwafin takardun, ta ce masa za ta je ta yi nazari, idan ta ga da yiwuwar saka hannu, za ta saka ta kar?a.

Su ka fito tare da Saifu, cikin damuwa ya ce "Nabila, dan Allah meyasa ki ke tsayawa wanda ya kashe mana 'yar uwa, Vipern nan mutumin banza ne, maimakon ki tsaya a ?wato mata hakkinta, amma ki ka ?uge da a wanke shi?".

Nabila ta ce "Idan da wanda ya aikata laifi bai wuce mahaifinmu ba, da ya ?auki aurenta ya ba shi, alhalin ya san ga halin sa ba, amma duk da haka, shi ma mahaifinmu bai yadda shi ya kasheta ba, meyasa ku ku ka kasa yadda da hakan?"

Saifu ya ce "Idan ba shi ya kasheta ba waye? Dama kowa ya san ?an shaye-shaye ne ya sha ya bugu ya halakata amma kalli yadda yake yawo a gari"

Kawai ta yi murmushi ta ce "Da yawa kallon mara inani ake yi mini, duk mai son sanin ha?i?anin abin da ya faru, mu kasance a kotu sati mai kamawa, amma yanzu dole zan bika, ina son tattaunawa mai muhimmanci da shi, a kan shari'ar da zan fara ta Viper da kuma game da rayuwar mahaifiyata da 'yar uwata a gidan".

Ya yi shiru ya na kallon Nabila, kamar ranta akwai wani abu, amma a sanyaye ya ce ce "Babu laifi mu je" ya tafi a motarsa, ita kuma a wadda aka kawota.

Su na tafe a mota, ta tsinci kanta, da kallon hotunanta na kammala makaranta, tare da Major.

A duniya ta sha?u da major, duk da yadda yake cin ?aniyarta, a duk lokacin da ta aikata ba dai-dai ba, dan ta zuba rashin ji.
Shi ne uwa shi ne uba, duk da ta sha?u da magajiya, amma major na musamman ne, hatta lokacin da ta fara al'ada, a makaranta ta na jss 2, tayar musu da hankali ta yi, sai da aka kira major ya je har makaranta, ya ?auke ta su ka koma gida, ya kai ta asibiti ya zauna ya ?ara yi mata bayani. Duk abin yake yi, aka ce ga wani abu da ya shafeta, zai ajiye ya je kanta.

Zaman kudancin Najeriya ya sanya Nabila gaba ?aya ba komai take ?oye wa Abba ba.

Ranar graduation ?in ta, dubu ?ari biyar ya ba ta, hotunan da suka yi kawai, suka ?ara tabattar da akwai sha?uwa a tsakanin su.

Ta shafi screen ?in wayar, ta ce "You will forever remain in my heart, kar ka yi fushi Abbana, ka bani lokaci ka?an kawai".

Viper ya na zaune, ya kunna aiki ya na aikin tracking ?in wasu kayan laifi da ake ?o?arin barin kano da su, notification ?in sa ya nuna masa Nabila ta nufi hanyar gidansu. Mamaki ne ya kama shi, me za ta je yi ba tare da ta gaya masa ba? Kawai jikinsa ya ba shi akwai wani abu.

Ayshercool
08081012143
???500 ne via 0009450228
Aisha Adam jaiz bank sai shaidar biya ta 08081012143
Wanda za su jira document 1K ne.

90009343
'Yan Nijar ku turo katin airtel na 300fcfa

*BRIGHT PENS SECOND BATCH*

Ku kasance da littatafan bright pens, second batch.
*?ARFE A WUTA (AYSHERCOOL)*
*MUTALLAB (NIMCYLUV)*
HADARIN GABAS (NAZEEFA NASHE)*
*ZAYTOON (ZEE KUMURYA)*

??????????????????????????

*_GYARA SHINE MACE_*

*_ZATA FASHE FA KARKU BARI AYI BABUKU ZAFAFAN KAYAN MATA MASU KYAU DA INGANCI KUMA AKAN FARASHI MAI SAUK'I ,MAMAN YUSUF YAR MUTAN SOKOTO TA SHIRYA TSAF DOMIN GWANGWAJEKU DA ZAFAFAN KAYANTA MASU MATUKAR INGANCI_*
??????????????????????????

*_'Yar uwa shin ko kin San lokacin sanyi lokaci ne da yake dask'arar da ni'imar mace , yake yawan bushe gaban mace , sannan lokacin ne maza sukafi bukatar matansu , lokaci ne da kowane lafiyayyen namiji yakeson ya jishi ajikin matarshi a kowane lokaci , to ya kike gani idan har mijinki Yana son kasancewa Dake Haka kekuma ga ni'ima a bushe , 'yar uwa mace fa Saida gyara , ko kinada kyau to ki k'ara da wanka don ci gaba da kankanrowa kanki daraja da k'ima a idon Mai gida ,. Ki tuna duk son da namiji ke maki in har kinada matsala a wannan wajan to wlh akwai matsala don son da yake maki bazai Hana kurinka samun matsala dashi ba ,idan kuwa har Yana samun yadda yakeso wlh ko baya sonki to Ina tabbatar maki da a hankali wata Rana sai ya soki Kuma zakiga kowane lokaci Yana tattalinki da gudun abunda zai 'bata maki Rai , Mata a kula*_ maman yusuf likitar Mata 07069711327

*Wannan dalilin ne yasa nazo maku da Kaya masu zafi kamar Haka*????????????????????????

Akwai ingantaccen maganin sanyi Mai fatattakar sanyi cikin kankanin lokaci na maza Dana Mata , kun dai San illar da sanyi yake da ita ku kula,

Akwai ingantaccen maganin nono hadin gargajiya na Sha Dana shafawa Mai taso da nono ya Kuma gyarashi Hadi da tsayuwarshi ,??

Sai maganin hips Wanda zaisa hips dinki ya ciko kema ki shiga jerin Mata masu aji??

Akwai maganin k'iba Wanda zai ciko da jikinki kiyi kiba Yar daidai Mai kyau wadda zata dace da yanayin jikin ki??

Ina bada Hadi na mussaman ga yarinyar da ta rasa budurcinta sanadiyar fyade ko yaudarar d'a namiji ,Wanda insha Allah akayi amfani dasu to yarinya zata koma normal Wanda duk zata aura Ba zai iya Gane komai ,
Mmn Yusuf likitar Mata????

Akwai hadin amarya Wanda zaisa ki ciko ki hade gam sannan su Baki ni'ima irin wadda akeso ingantaccen sirrin da zaisa ki Kara samun soyayyar mijinki cikin sauki??????

Akwai hadin sabon budurci da mukeyi ga wadda ta kasance bazawara hadine da ko haihuwarki nawa akayi maki shi Zaki koma tamkar budurwa Wanda ko Wanda Kika aura zaisha mamakinki Wanda hakan Kuma wata hanya ce ta kankanrowa kanki daraja da k'ima ne zawarawa ku matso karku Bari ayi babuku??????????

Akwai hadin Mai jego , kunsani mace na rasa mafi yawa ni'imarta yayin haihuwa wata ma Zara karu ne to indai kikayi wannan hadin Ina tabbatar maki da cewa Zaki hade ciki da waje gabanki zai ciko sosai in karuwa kikayi K'arin zaizo ya hade tsaf sannan Zaki samu dawamammiyar Ni'ima

KADAN DAGA CIKI WASU KALOLIN????????

Kalolin gumba
Kalolin matsi
Kalolin gari
Kalolin tsumi

Zumar dabino
Zuma Mai rubutu
Zumar goron Tula
Zumar ridi

Dahuwar kaza
Dahuwar zabo
Dahuwar zuciya
Dahuwar ciccibi
Dahuwar tsoka Tara
Dahuwar Yan shila
Dahuwar kwai Mai rubutu

Turaren mallaka
Turaren Mara
Turaren tsugunno
Turaren k'irji
Shuumar humra
HATSABIBI turare
Hatsabibiyar humra

Matan gaske
Maltinat Mata
Shayin Mata
Tsumin kankana
Sirrin tafin k'afa

Akwai sirrika na mallaka da hadin farinjini
Akwai sirrin samun farinjini ga wadda ta rasa mijin aure ko wadda takeson samun farinjinin sana'a
Akwai hadin farinjini na matar aure
Akwai kwallin mallaka
Zoben mallaka
Set na Jigidar mallaka

*Yar uwa abubuwan fa da yawa sosai , Wanda in nace Zan tsaya bayyanasu anan wannan page din bazai Isa ba , Ina sokoto Ina aikawa kowane gari dake cikin Nigeria da Niger ,kwatano da Ghana , karku manta adade anayi sai gaskiya , ga Mai sayen d'ai d'ai ko masu siyan sari , ku tuntubeni ta wadan nan numbers????????????

07069711327 Whatsapp ,Ina maraba daku customers??????????

Masu buk'atar ganin kalolin kayana to kuyi sarving wannan number 07069711327 sannan kuyi min magana Nima nayi sarving number ku ta hakanne zaku dinga ganin kayana da zarar na d'ora, ngd sosai taku maman yusuf likitar mata??????????????????


Sake kallon wayarsa ya yi, ya ga location ?in wayarta ya na harba hanyar gidan mahaifinta.

Kasa nutsuwa ya yi da hakan, kawai ya tashi ya sanya kaya ya fita.

Saifu ya riga su Nabila ?arasawa, Allah ya sa Baba bai kai ga fita ba.

Saifu na sanar masa, Nabila ta na hanya, bakinsa ya ?i rufuwa, ya fasa fita, ya ce a ha?a mata kayan abinci.

Ya ce "Saifullahi ita da wa za ta zo nan ?in?"

Saifu ya ce "Itaka?ai ce, kai take son gani"

Cike da fara'a ya ce "To Allah ya kawo mini ita lafiya cikin aminci"

Ana haka Nabila ta yi sallama, hafsa ta fito da gudu daga ?aki, ta rungumeta ta na "Oyoyo ga jauhar"

Nabila ta yi murmushi ta ce "Nabila dai, ba jauhar ba" ta yi shiru ta na

Please Login or Register in order to submit comment