Reading KARFE A WUTA Chapter 22 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sa ba wani rashin jin zai je yayi ba.

Baba yana gida, aka aiko ana sallama da shi.

Yana fita ya tarar da 'yan uwan Alhaji mu'azzam da suka kawo ku?i.

Suka gaggaisa, ?anin mahaifin Alhaji mu'azzam ya ce "Gamu mun dawo, ?anka ne ya dawo da mu, ya ce a bayar da ha?uri, kar a ji mu shiru, ayyka sun yi masa yawa, ba zai samu dawowa nan kusa ba, shi ne ya ce mu zo ayi magana, a ?arasa shirye-shirye kawai, ayi auren a tura masa ita can".

Gaban Baba ya fa?i jikinsa a sanyaye ya ce "Alhaji dama ko da baku zo ba, zan neme ku ni na zo, an sami matsala ne, zan dawo muku da ku?in aurenku".

Suka yi turus gaba ?aya suka ce "Wace irin matsala ce haka?"

"Yarinyar nan, yau ta kusa sati biyu, ina mai baku ha?uri, a bashi ha?uri dan Allah. Zan kawo muku ku?in aurenku"

"Amma wani abun yayi ne, ko wani laifin shi mu'azzam ?in yayi?".

Baba ya ce "Ko ?aya, ka san matar mutum kabarinsa, mu'azzam bai yi mini komai ba, dan Allah a bashi ha?uri"

Suka ce "To shikenan, Allah ya tabattar mana da alkhairi".

Suka amsa da "Amin"

Baba ya ce "Ku bani account number, na mayar muku da ku?in auren"

?aya daga cikin su ya ce "A'a, a bar wannan maganar sai ya dawo tukuna, Allah ya basu zaman lafiya"

Ya amsa da "Amin".

Bayan la'asar yara duk suna islamiyya, babu 'yan aike, ta ce bari ta fita ta sayo maganin sauro, idan ya dawo sai ta gaya masa.

A ?ofar gida suka ha?u da maman su halimatu a waje da wata ma?wabciyar su, suka gaisa ta ce "Maman halimatu, ba ku shigo mini mun gaisa ba haryanzu".

"Wallahi Amarya, ba ?i muka yi ba, kin sa yanayin mijin naki sai a hankali, abun da tsoro, kar wani abu ya faru".

Ranta bai yi mata da?i ba ta ce "Haba dai, ina ruwansa da ku? Kawai dai a shigo a gaisa, shikenan a gaida su halimatu" tayi gaba zuciyarta babu da?i, a duk lokacin da ta ji an aibata shi, sai ranta ya sosu.

Har dare ba ta sake ganin Al'amin ba, gashi ita ba waya ba, wasa-wasa har dare yayi babu Al'amin babu dalilinsa har garin Allah ya waye, bai kwana a gida ba.

Sai abin ya fara damunta, gashi ba ta san a ina za ta ganshi ba.

Abu kamar wasa, aka sake shafe wuni, aka shiga kwana na biyu, babu shi babu labarinsa, nan fa hankalinta yayi mummunan tashi, gashi ba ta san wa za ta nufa ta gayawa ba.

Maman halimatu ce tayi sallama, Jauhar ta saka hijjabi ta fito tana murmushin ya?e ta ce "Maman halimatu, sannu da zuwa shigo"

"A'a ba shigowa zan yi ba, abbansu yana nan bai fita ba, bai san ma na shigo ba na ce kin kuwa san an kama mijinki?" Gaban Jauhar ya fa?i ta ce "Yaushe? A ina? Waye ya gaya miki?"

"A bakin Abban su halimatu na ji, cune suka yi masa aka kama shi, amma dan Allah kar ki gaya masa wanda suka saka aka kama shi ?in dan Allah, na gaya miki ne na san baki sani ba".

Tuni idon Jauhar ya cika da hawaye ta ce "Eyya, meysa abban su halimatu yayi haka? Wallahi babu abun da zai yi wa wani, ba ruwan shi da kowa idan ba ta?a shi aka yi ba, ina aka kai shi? Dan Allah ki gaya mini, ina gidan ban san ina zan nufa ba ma".

Tayi ?asa da murya ta ce "Yana anti daba can aka kai shi".

"Menene anti daba kuma? Ina ne?".

"Can in da ake kai 'yan daba, ki shirya ki je ki duba shi".

Ta ce "To na gode" bayan tafiyar maman halimatu, take ta ji haushin malam lawan ya kamata.

Tayi tunanin ko gidansu za ta je, ta fa?a, amma sai ta ga idan tayi hakan, kamar ta tozarta kanta ne, dan haka ta fasa ta ?ora girki, ta gama ta shirya, ta zuba a flask, ta bi kwatancen da maman halimatu tayi mata.

Su kansu yanayin jami'an tsaron wurin, tsoro suka bata, ba ta ta?a zuwa police station ba, ta gaishe su cikin girmamawa sannan ta ce "Dan Allah wani nake nema"

"Wa kenan?" Wani ya tambayeta.

"Al'amin sunansa"

?an sandan ya ce "Anya, babu wani mai irin wannan sunan da muka kama".

Ta ce "Dan Allah nan aka ce mini an kawo shi, dan Allah officer ka duba mini"

Na kusa da shi ya ce "Ko viper take nufi?"

Ta ce "Eh shi, mai dogon zamani"

"Ya aka yi me zaki yi masa?"

"Wurinsa na zo, ma?wabciyata ta ce mini cune aka yi masa aka kama shi, wallahi bai yi komai ba".

"Ke ya aka yi ki ka san bai yi komai ?in ba? Wacece ?in sa ke, ni tun da muke kama shi ma, ban ta?a ganin wani ya zo wurinsa ba, idan ba ire-iren sa ba ko yaran ubangidansa ba"

Ta ce "Mijina ne"

Saroro suka yi suna kallon jauhar, kyakywar yarinya ?arama da ita.

"Ke kuma auren soyayya ku ka yi? Jama'a kun ga matar Viper, yaushe ne kuwa zuwansa na ?arshe aka fito da shi aka ce aure yayi" waiwayowa suka yi suna kallonta, ta sunkuyar da kai tana fatan Allah ya sa su bar ta ta ganshi.

?aya daga cikin su ya ce "Ku fito da shi, ta ganshi, amma dai Viper yayi asara, daga aurensa ya saka 'yar mutane fara sintiri saboda shi".

Saroro yayi da ya hangota cikin hijjabi, 'yan sandan suna yi mata tambayoyi.

Tana ganinsa tayi ajiyar zuciya, ya ?araso gaban kantar ya kalleta ya ce "Me ya fito da ke?"

"Kwana biyu baka nan, ban san in da ka ke ba, sai yau ban san kama ka aka yi ba"

Ya sake kallonta ya ce "To ware ki koma"

Jauhar ta ce "To in koma, kai fa ba sakinka za su yi mu koma ba?"

Al'amin ya ce "Ki tafi na ce, kuma kar ki sake zuwa wurin nan kina mace, ware" haushi ne ya kamata, yadda yake korarta, shi ba ayi masa abun arziki sai hantara.

Ta ?ora leda ?uake da flask ?in Abinci ta ce "Gashi abinci ne na kawo maka" sai da ya ?an yi shiru yana kallonta.

Tun da ya fara rashin jin sa, babu mai tunawa da shi, ya kawo masa ziyara ko abinci, idan ba su walid ba, sai kuma ita yanzu.

"Ahh yau zamu ci girkin amarya, amma hajiya sai kin fara ci kafin ya ci"

Bai saurari ?an sandan ba, ya ?auki abincinsa ya koma gefe.

Ya bu?e, ta yi sauri ta zagaya, ta huda ruwa pure water, ta ce masa "Ka fara wanke hannunka"

Kamar ya shareta, sai kuma ta zuba masa ya wanke, ya saka hannu ya fara cin abincin.

"Akwai sauro ne wurin? Na ga kamar ya cijeka, jikinka duk cizon sauro?"

"Mmm" ya amsa yana cigaba da cin abincin.

"To yaushe zasu sake ka, kar ka yi rashin lafiya, saboda cizon sauro" shi dai yayi shiru yana cin abun sa.

Ya gama ci ta bashi ruwa, ya kar?a ya zu?e, ta ?ara masa wani ya shanye.

Ta ce "Officer, to zaku sake shi? Bai yi komai ba"

"Ke, da wiwi muka kama shi da ?wayoyi, sai kuma ki ce bai yi komai ba? NDLEA zamu kai shi".

Jauhar ta ce "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, dan Allah ku yi ha?uri, ba zai ?ara ba in sha Allah, Master ka basu ha?uri su ?yaleka mu tafi" mi?ewa yayi tsaye, ya nufi hanyar komawa cikin ceil.

"Officer to, idan na sayo maganin sauro da ashana, zaku bar shi ya kunna?"

Gaba ?aya sai ta basu tausayi, ya ce "Sayo"

Ta juya ta fita da sauri, shi kuma ya tsaya ya waiwayo ya bi bayanta da kallo.

"Viper, wai dan Allah ka bamu labari, wurin wani bokan ka kai 'yar mutane da iyayenta, suka aura maka 'yar su?"

Shi dai ya ?arasa ya koma cikin ceil, yayi zamansa, ba a jima ba, sai gata da maganin sauro, da ashana.

Suka kar?a a nan kan kanta, suka ce ta tafi.

"Dan Allah ku bari na sake ganinsa"

"Ke wuce ki bar nan, da ki ka samu ma aka bari ki ganshi?"

Ba ta karaya ba ta sske cewa "To ana bashi abinci? Ko ina kawo masa na dare ma"

"Au uban wa ki ka ajiye da zai bashi abinci a nan? Ware ki tafi"

Jiki a sanyaye ta ce "To, zan tafi ga wannan dan Allah officer ko buredi ku bashi" ta ajiye musu ?ari biyar sannan ta ce "Dan Allah kuma ku yi ha?uri, kar ku kai shi NDLEA, dan girman Allah in sha Allah zai daina, ba zai ?ara ba ma dan Allah"

"Ki je ki kawo dubu hamsin, sai mu sakar miki shi"

Tayi shiru, har ga Allah ba ta da ita, ba ta da dalilinta amma ta ce "To zan kawo, amma dan Allah kar ku kai shi, zan kawo muku in sha Allah"

Ta fito daga wurin, tana tunanin ina zata nufa ta samo dubu hamsin a sake shi.

Ayshercool
08081012143

???500 ne via 0009450228
Aisha Adam jaiz bank sai shaidar biya ta 08081012143

90009343
'Yan Nijar ku turo katin airtel na 300fcfa

Arewabooks ayshercool7724


Tun da ta hau adaidaita sahu, tunani take yi, yaya za ta yi ta samu dubu hamsin ta kai, a sako shi. Ta san muddin aka kai shi NDLEA case ?in tsayi zai yi, ba zata musa an ganshi da kayan maye ba, tun da yana sha.

Ta koma gida tayi salla, amma abun duniya ya isheta, ta kasa ko cin abinci, tausayinsa duk ya cika mata zuciya, jikinsa yayi ru?u-ru?u da cizon sauro, gashi almu sun nuna ba abinci ake ba shi ba.

Baba kuwa abun duniya ya dame shi, yadda ya ji kunya a idon iyayen Alhaji mu'azzam, ace sun kawo ku?i sun gama magana, amma ya aurar da ita ga wani, ko gaya musu bai yi ba, ya rasa me yake yi masa da?i, har sai da zakiyya ta fahimta ta ce "Baban su Saifu, wai lafiya kuwa? Tun da ka yi ba?i jiya, gaba ?aya ka rasa nutsuwar ka"

Ya sauke numfashi ya ce "'yan uwan Alhaji mu'azzam ne, suka zo suna bayar da ha?uri a kan jin su shiru da aka yi. Wai za ayi mata visa ayi auren a tura ta can"

Waro ido tayi ta ce "Sai kuma ka ce musu me?".

"Na aurar da ita" yayi maganar a sanyaye yana sake jinjina wautar da ya yi.

"Ba a haka fa, sai ka ce musu Allah ne ya ?addara a hakan, amma akwai yayyenta, ko hafsa ba sai a maye gurbinta da ita ba, hafsa ba ta fi jauhar komai ba ma? Ai bai kamata a bari ya tafi haka ya tsallake gidan nan ba".

"Zakiyya, kun saka na yi abun da yake damuna, na cuci 'ya ta ba gaira babu dalili, na aurar da ita ga mutumin da ba na kirki ba, na rasa yadda aka yi, lamarin nan ya faru, kunyar ha?uwa da jauhar ma nake yi, na kasa komawa gidanta, zuciyata zafi take yi mini"

Zakiyya ta ce "Jauhar fa an gama babinta, sai a fuskanci 'yan uwanta, bai kamata a bari mutumin nan ya tafi haka ba"

"Zakiyya, dan Allah ki bari na samu nutsuwa, ni ban san ma meyake damuna ba, dan Allah ki bari na ji da abun da yake damuna"

Ta kwantar da murya ta ce "Babu wani abu fa da yake damunka, kai ne ka ke neman ?orawa kanka matsala, amma komai mai sau?i ne, idan ya dawo ba sai a lalla?a shi a bashi Hafsa ba ya aura".

Baba ya ce "Na ji, amma dai yanzu ki ?yaleni" ya ?auki hularsa ya saka ya fita.

A tsakar gida ya tarar da su surayya, aiki duk ya kacame musu, aiki ba aiki, wanda da jauhar na nan, ita ka?ai take yi suna mimmi?e kamar kifi a fridge.

Suna ta yi masa a dawo lafiya, ya dawo da baya ya tsaya, ya kalle su ya ce "Surayya, kun je gidan ?anwarku kuwa kun ganota?" Duk suka yi shiru, suka kasa amsa masa.

"Yakamata ku je ku ga in da aka kaita, ita ma ta ji da?".

Mama ta fito daga kitchen ta ce "A'a fa, ka san dai yadda mijinta yake, ba zuwa gidanta ne ba za ayi ba, kar mutum ya je ya illata shi". Yayi shiru bai ce komai ba.

Jauhar kuwa kasa nutsuwa tayi, har sallar nafila tayi mussaman tana fatan Allah ya sa kar a kai Al'amin NDLEA.

Duk yadda ta kai ga tunani, ta rasa mafita, bacci ya gagareta, a gidanma ya ta ?are da sauro, ina ga shi da yake can, ta yi ta fatan Allah ya sa su saya masa buredin nan su bashi, sai kuma ta tuna ba ta bayar da ku?in da za a saya masa ruwa ba, gaba ?aya ta shiga damuwa, haka har garin Allah ya waye.

Ta ji ?arar babur ?in malam lawan alamar ya fita, tana ta tunanin ko shiga za ta yi gidan, ta yi wa maman halimatu magana, ko akwai taimakon da za ta iya yi mata.

Tana cikin tunanin, maman halimatu ta shigo, suka gaisa jauhar ta ce "Yanzu nake tunanin zuwa gidan wurinki".

Maman halimatu ta ce "Yaya kin same shi ?in?"

"Eh yana can, sun ce na kai dubu hamsin a bayar da belinsa, amma wallahi bani da ita"

"To yanzu ya za ayi?"

Jauhar ta ce "Wallahi ban sani ba, shi nake ta tunani"

"To ki kira gidanku mana ki fa?a" ta girgiza kai ta ce "A'a, daga yin auren sai na fara kai musu complain, a'a gara na rufa masa asiri na samu ya fito"

"Aikuwa Jauhar sai ki yi tunanin in da zaki samo ku?i".

Tayi saurin cewa "Dan Allah ko akwai wanda zaki ha?a ni da shi, ya sai carfet ?ina?"

Ta ?an yi shiru sannan ta ce "Eh akwai wata dillaliya, kusa da titi gidanta yake"

Cikin ?oki jauhar ta ce "Mu je ki rakani maman halima".

"Shikenan, amma Jauhar kina me ki ka auri mutumin nan, gashi daga aurenku kin fara wahala, da kyanki da ?uruciyarki, kin auri wanda zai wahalar da ke".

Jauhar ta yi murmushi ta ce "Maman halimatu ku daina aibata shi dan Allah, ku din ga yi mana addu'a"

"To Allah ya kyauta"

Jauhar ta saka hijjabi, suka tafi gidan dillaliya, sai dai bata nan, aka kirata a waya, ta ce sai yamma zata dawo, zata biya gidan maman halimatu, su je gidan Jauhar ?in.

Wunin ranar jauhar kamar ta yi hauka, saboda dillaliya ba ta zo ba, sai tunanin halin da yake ciki take yi.

Sai wajen ?arfe biyar sannan ta zo, ta ga carfet ta ce zata saya dubu goma.

Maman halimatu ta ce "Haba sahura, wane irin dubu goma, bai fi sati biyu ba ca carfet ?in sabonsa dubu kusan sittin ne fa".

"To ku ?auka ku mayar kasuwar mana, tun da an shimfi?a ai ya zama taoho".

Jauhar ta ce "Bakomai na yadda" ba ta da burin da ya wuce ta ga Al'amin ya fito.

Sahura ta ce 'Saboda kin ban tausayi, na saya dubu sha biyu, bari na baki ku?in.

Maman halimatu ta ce "Wallahi sahura shiyasa da yawanku ba kwa arziki dillali, duk cuwa-cuwar ta ku, a tsiyace ku ke mutuwa"

Sahura ta ce "Oho miki dai"

Ganin ta fito da ku?i da yawa, ya sanya jauhar shiga kitchen ?in ta, ta ?auko blender da set na tukwanenta masu kyau, ta cewa dillaliya su ma ta saya.

Maman halimatu ta ce "Jauhar, idan 'yan gidanku suka gane kin sayar da kayanki fa?"

Sahura ta ce "Wallahi uwar su halimatu ke 'yar ba?in ciki ce, ke kika saya mata?".

Jauhar kamar ta yi kuka ta ce "To ya zan yi maman halimatu, bana son zamansa a wurin nan, sauro ma kawai ya ishe shi"

Sahura ta ce "Allah sarki yarinya, Allah ya mayar da alkhairi, idan an tashi sayar da wasu ma ki kira ni"
Da ?yar ta bawa Jauhar dubu ashirin da hu?u gaba ?aya. Wanda a ?alla sun kai kayan dubu ?ari da wani abu.

?o?arin nemo wani abun take, maman halimatu ta hanata, ta ce ta bari gobe ta je station ?in, ta basu ha?uri ta ce musu abun da take da shi kenan.

Jauhar ta ce "Ki na ganin za su kar?a kuwa?"

"Za su kar?a mana, ai kin yi ?o?ari" kamar ta janyo wayewar gari, ta din ga addu'a Allah ya sa su kar?a su sake shi.

Da wuri ta gama komai, wurin ?arfe goma da rabi ta fita, shi ma maman halimatu ce ta hanata fita da wuri, ta ce mata ba da wuri suke zuwa ba.

Suna ganin Jauhar suka ce "Madam ya aka yi ne? Kin sake dawowa ganinsa ne?"

Ta ciro ku?in ta ce "Gashi dan Allah yalla?ai ku sake shi, suka?ai na samo dan Allah ku yi ha?uri"

Ya zuba mata ido ya ce "Shekarar ki nawa ne?"

Ta ce "Na kusa shiga sha bakwai, dan Allah ku yi ha?uri"

"To ai ba zamu iya baki belinsa ba, kin ga mace ce ke, kuma yarinya, Allah ya sa ya daina abun da yake ko dan saboda ke, kar?i ku?inki, ba zamu sake shi a kan wannan ?an ku?in ba, kotu ma zamu kai shi"

Kawai ta saka kuka, "Dan Allah ku yi ha?uri, ba zai ?ara ba dan Allah kar ku saka a kai shi prison"

?aya daga 'yan sandan ya ce mata "Yi ha?uri ki daina kuka, da wasa yake yi miki, an zo belinsa ma, ke ki ke tayar da hankalinki, ko mun kama shi zamu sake shi"

Kasa daina kukan tayi, hannunta ri?e da ku?in, wani ?an sanda ne ya fito, da alama babba ne, bayansa kuma walid ne da Al'amin da wani mutum.

Wata irin ajiyar zuciya ta yi, ta zubawa fuskarsa ido, da take a ?aure babu walwala.

Walid ya ce "Kai Viper, wannan ce yarinyar da na tarar a gidanka, tayi mini rashin mutunci"

"Wannan fa me aka yi mata take kuka?"

"Sir, matar Viper ce" ya kalleta ya ce "Hajiya me aka yi miki ki ke kuka?".

"Ce mini suka yi na kawo dubu hamsin za a sake shi, na kawo kuma suka ce mini wai kotu za su kai shi" ta ?arasa maganar tana sake fashewa da kuka cike da yarinta.

Ya kalli 'yan sandan ya ce "Waye ya ce ta kawo dubu hamsin"

"Sorry sir, dan ta daina zuwa aka gaya mata haka"

Nan ya hau yi musu fa?a, suka din ga bayar da ha?uri, Al'amin kamar bai santa ba, yayi gaba. Da sauri ta bi bayansa, tana ta yi masa magana yayi shiru.

Walid ya ce "Haba mai dogon zamani, ka tsaya ka saurareta mana"

A fusace ya waiwayo ya hau ta da masifa "Ban ce miki kar ki sake zuwa wurin nan ba? Kin san suwaye ake kawowa wurin nan? Mutuncinki ne a ganki a nan?" Sai da ta ja da baya a tsorace ta rufe fuskarta, saboda razana da masifar da yake yi mata.

"Wai Aminu meyasa ka ke yin haka? Da uban waye ya damu da kai, yake ta taka? Macen kenan haka zuciyarsu take, ko dan matar gidanku ba ta da kirki kowa ma haka yake?" Tsaki ya yi yayi gaba.

Walid ya ce "Yi ha?uri mu je, rabu da shi ya ?arata, kar ki sake tayar da hankalinki saboda shi" suka tari a daidaita sahu suka tafi gida.

Da suka je gida, ta shiga gidan ta bar shi da Walid.

"Aminu, dan girman Allah ka rage jaraba, kalli yadda duk ta rikice saboda kai, kar ka yi wasa da damar da ka samu, ka saka ta tsaneka dan Allah"

Ya tsaya ya ?arewa ?ofar gidan malam lawan kallo, yayi ?wafa ya shiga gidan, ba tare da ya tanka Walid ba.

Jiki na rawa ba tare da ta yi fushi ba, ta kawo masa tea da buredi.

Ya gama baccinsa ya tashi, ya yi wanka, ya gama ya ga ta kafa masa ?usar rataye soso a ban?akin, har zai rataye yayi tsaki ya yar da soson a kan sabulun ya fito.

Ya canza kayansa ya fito falo, Satar kallonsa take yi, kamar ya ?ara kyau, kwana biyun da ya yi a tsare ba ya shan komai, kamar ya yi kyau sosai. Sai murna take yi ya dawo gida.

"Ke!" Ta ?ago ta kalleshi.

"Meye sunanki ne?"

"Jauhar"

Ya kalleta ya ce "Me? Angela?"

Murmushi ta yi ta ce "Angela kamar wata mage, sunana Jauhar"

Guntun tsaki ya yi ya ce "A saka muku normal suna, sai dai a saka ?a?ale-?a?ale da iyayi, ni ba zan iya ba"

"To ka kirani da fatimata fatima zahra" wani irin zirrrr ya ji a jikinsa, fatima zahra, sunan mace mai girma da daraja a idonsa, Ummansa abar ?aunarsa, duk da ba ta duniyar, amma idan ya ji sunan har wata tsuma yake yi.

Ya maze ya ?arewa falon kallo, ya fita tsakar har zai wuce ya kalli kitchen ?in ta sannna ya ce "Zo nan"

Ta fito ta ce "Gani"

"Wa ki ka sayar wa carfet ?inki da kwanukanki?"

Gabanta ya yi wata irin mummunar fa?uwa, yaya aka yi ya gane ko ya sani? Sai ka ce aljani?

Ya ?are mata kallo ya ce "Ina jinki, ya aka yi ki ka samu wannan ku?in da ki ka kai? Ina kuma abubuwam da na tambayeki? Ki ka yi mini ?arya kuma jikinki ya gaya miki"

Kamar munafuka, haka ta zayyane masa komai.

Bai ce mata komai ba, ya fita.

Sahura na tsakar gida, tana hira ita da wasu coustomominta, kawai ta ga wasu irin zaratan matasa su uku, a tsakiyar tsakar gida da manyan gorori kamar za su farauta.

Ta tashi ta ce "Lafiya malam? Me ku ka zo yi mini a gida. Wannan ai.... Ha?iye maganar tayi, da ya sako ?afarsa cikin isa tsakar gidan.

Yana shigowa idonsa ya sauka a kan carfet ?in, a shimfi?e a falonta.

Ya ce "Liti, ku na?o mini carfet ?in nan"

Ta waro ido ta ce "Malam lafiya?" Walid ya zaro wu?a ya ce "Ki ka kuma magana, sai kin ?aware daga sararin nan yanzun nan" daga ita har sauran matan, suka hau tsuma.

Kamar abun banza, suka din ga yi mata cilli da kujeru, suka na?o carfet.

Viper ya ce "Dubu sha biyu ki ka saya ko?" Ta jinjina masa kai.

Ya ce "?aukko mini sauran kayan da ki ka kar?a a wurinta" jiki na tsuma ta shiga ta kwaso su.

Ta ajiye masa a tsakar gidan, ya ce "?arauniyar zaune, daga yanzu ki san abun da zaki din ga saya, ban da a nutse na zo miki, sai na saka an zana miki awarwaro a hannu, yadda gobe ba zaki sake zalunci ba. Liti ba ta ku?inta".

Liti ya zaro ku?i zai bata, Al'amin ya ce "Wait, ta riga ta shimfi?a a ?akinta, ka cire dubu uku a kai, sannan ka sake cire dubu biyu zan cika ku wanke mini carfet ?in ku kai mini gida.

Haka kuwa aka yi, suka cilla mata ku?i, suka kwashe kaya suka tafi.

Jauhar ta na yi wa wasu stone work, dan kuwa matar ta fara kawo mata kayan tana yi, hakan yana ?ebe mata kewa.

Ba ta yi aune ba, ta ganshi a tsakiyar falo, hannunsa da kaya, ya dungurar mata da su a tsakiyar wurin ya ce "Daga yau, ko cokali ki ka kuma sayarwa, saboda ni sai na ?ata miki rai, fiye da yadda ki ke tunani"

Baki bu?e ta ce "Master, kar?owa ka yi, ku?inta suna wurina fa, Allah zai kaman..."

"Na ba ta ku?inta, ko tsintsiya ki ka sake sayarwa, zan gane kuma ranki sai ya ?aci".

A hankali ta ce "Na shiga uku".

***
Matasa ne a ?alla su biyar, dukkanin su, babu wanda ya gaza ko ya wuce shekaru ashirin da biyu, suna sanye da tufafi masu nuna datti, gashin kansu da yanayin fuskarsu kuwa, babu tambaya sun bayyanar da tsantsar rashin ji a tattare da su, sai bushe-bushe suke yi, suna shewa.

Wani matashin ne ya diro ta saman katanga, gaba ?aya suka nutsu, suna yi masa sannu da zuwa.

"Kai gayu akwai matsala wallahi" gaba ?aya suka tattara masa hankalinsu suna sauraren sa.

Ya ce "Kaii, wai ashe mai zamani ne ya tare a unguwar nan kusan sati biyu bamu sani ba?"

?aya daga cikin su ya mi?e ya ce "?arya ne wallahi, me yake yi mana a unguwa".

"Nustu, ni ma ban sani ba sai ?azu, mai unguwa na ji yana maganar, sai za su je police station, ko a sasanta ayi zaman lafiya da shi, ko ya bar unguwar nan".

?ayan ya yada sigarin hannunsa ya tashi ya ce "Guduma gaskiya kar dagus ?in ka ya janyo mana matsala, ya san waye mai dogon zamani kuwa?".

"Guys mafita ?aya ce wallahi, kun san ba a sarki biyu a zamani ?aya ko?"

"Me ka ke nufi?"

Guduma ya ce "Dole ?aya ya bi ?aya"

"To waye zai bi wani?"

"Kwanciyar hankalinmu da nustuwarmu, shi ne mu yi mubayi'a, samunsa ma a unguwar nan wani security ne, zai

Please Login or Register in order to submit comment