Reading KARFE A WUTA Chapter 44 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

son ya ga tana zubar da hawaye.

Jauhar ba irin addu'a da ba ta ja wa indabo ba, dan shi ne kanwa uwar gamin ?ara ta'azzara rashin jin Al'amin.

A washegari hukumar za?e, ta sanar da soke za?en ?aramar hukuma uku, ciki har da ta su Al'amin wadda kuma take ta indabo, sakamakon tashe-tashen hankali da aka samu, da kuma ?ona wasu daga takardun da aka ka?a ?uri'a.

Tuni P.A ya sanar da Indabo sa?on su Walid, kuma kansile ?anan hukumomin, babbar barazana ce ga nasarar indabon.

Babu shiri, washegari da daddare suka shirya suka tafi wurin malamin su, da shi da P.A, malamin ya tabbatar musu da cewa, an samu tangar?a a aikin da aka yi ne, yarinyar da yayi amfani da ita, ta haura shekarun da ake bu?atar, kuma a yanzu ba abun da zai iya yi musu, sai dai a bi wasu sabbin dabarun, a samu a haye.

Suna tafe a hanya P.A ya ce "Honorable, wallahi yakamata ka duba mai zamani, da ?yar idan ba yaransa ne, suka tayar da tarzoma ba, ka san dole zamu sake bu?atar su, mussaman yanzu da za?en ya zama inconclusive".

Indabo ya ce "Matsalar yaron nan na ta ?arewa wallahi"

"To ya zamu yi, ha?uri zamu yi tun da muna amfanarsa". Indabo ya amince da hakan, P.A ya kira liti ya tambaye shi in da suke kwance

Al'amin so yake Jauhar ta zauna a kusa da shi, ya ji ?uminta su yi hira, amma alamu suka tabattar masa da fushi take yi, dan da tayi masa abun da za ta yi masa sai ta koma gefe, ta ?auki wayarta tana karanta Alqur'ani.

Ga kawo-kawo ?in da ake yi, ku?in hannunta duk sun ?are, dan ma su liti suna tsaye suna tallafawa, kuma idan Abbu ya zo ya kan ba ta ku?i, duk da zuwan nasa biyu ne kawai.

Wajen ?arfe ?aya na dare ne, Ranar Walid da liti duk suna nan, duk da da facemask, a fuskar Indabo sai da suka gane shi, suka tashi suka ni bayansu.

Jauhar ta ?aga kai ta kallesu, Al'amin ya bu?e idonsa da yake a rufe a da.

Jami'an tsaron suka bashi kujera ya zauna, yana kallon Al'amin da satar kallon jauhar.

Ta tashi ta ce "Lafiya?"

P.A ya ce "Baki gane ni bane, wanda ku ka zo wurina lokacin yana prison, honorable ne wannan, ya zo da kansa ba sa?o duba shi" ta ha?e rai sosai, kamar ya make shi ta huta haka take ji.

Ya sauke facemask ya ce "Sannu kin ji, ya mai jikin?"

Shiru tayi tana cigaba da ha?e rai.

Ya kalli Al'amin ya ce "Wannan ce 'yar madarar kenan?" Al'amin ya ?ura masa ido, bai yi magana ba.

Ya kalli Walid ya ce "Ba ya iya magana ne?"

"Yana yi"

"Dama cewa na yi bari na zo na ga yanayin jikin naka, Allah ya ?ara sau?i. Ban sani ba ko ka samu labarin an soke mana wasu ?uri'un abun bai yi da?i ba, muna nan dai muna ta addu'a "

Ya karkace ya ciro ku?i kaya guda, ya mi?awa jauhar ya ce "Ga wannan a sai magani"

Ta girgiza kai cikin takaici ta ce "Ba ma so, ka ri?e ku?inka ni babban burina da fatana, ka fita daga rayuwar mijina, nima ina burin na ga ya shiryu ya zama mutumin kirki, kai ne ka ke saka shi aikata duk wani abu na rashin kyautawa. Idan ya shiga matsala kuma ka zame ka bar shi. Yanzu an riga an cuce ni, an tsugunar da shi. 'ya'yanka su suka fi cancanta su yi maka irin aikin da yake yi maka, tun da sun fi morarka, idan abun na Allah ne ka kar?i takardunsa ka sama masa abun yi mana, amma babban burnku yaran wasu su sha su bugu su sayar da rayuwarsu a banza gare ku".

?aya daga cikin jami'an tsaron ya daka mata tsawa, ta ce "Wallahi ko zaku kashe ni sai na fa?i gaskiya, nima 'ya ce, kuma na cancanci zama da nagartaccen miji, na san akwai iyaye da yawa da suke da burin ganin yaransu a hanya madaidaiciya amma duk hana hakan, ni dai dan Allah ka rabu da mijina, ka ?yalemu"

Maimakon ya ji haushi, sai yayi murmushin ya ce "P.A wato duk isa da kwarjinin namiji ya je gaban mace, sai abun da Allah ya yi, kalli Mai zamani a gaban matarsa. Aishikenan yarinya haryanzu baki san rayuwa ba, wannan yanayin mafita kawai ake nema, ki daina yi wa manya rashin kunya. Kuma mijinki zaki gaya wa ya daina abun da yake yi ba ni ba. Tun da a haka na ganshi, ki kar?i ku?in nan".

"Ba ma so, ba zamu kar?a ba" tayi maganar tana kuka.

Ya mi?awa P.A ku?in, ya kar?a ya mi?awa Viper, shi kuma ya kar?a.

Indabo yayi murmushi ya fice da tawagarsa.

"Master ni ka dizga ka kunyata a gaban mutane, gara ka cigaba da kar?ar ku?insu kana shaye-shaye ana yi maka lahani, ni ko? Kai am tired na gaji, ba zan iya ba na sare. Na ?auka abun mai sau?i ne, amma ya wuce yadda nake tunani, you are not willing to change. Kana samun sau?i gida zan koma, na gaji da auren"

Liti ya ce "Subhanallah, dan Allah kar ki yi mana haka anty ?ar madara, muna murna Allah ya saya mana shi, kuma ki tafi ki barmu, ba fa shika?ai ba har mu zamanki tare da shi muna amfana"

"Eh, kuma har da ku ai, kullum ku kuke ?ara ha?uwa da shi, ku ke ?ara abun da bai kamata ba, Allah ya sa na mutu na huta".

Duk wannan abun, yayi burus ya?i magana.

"In sha Allah, ba zaki mutu ba, ana mugun tare ai"

"Ba wani tare, ku daina shaye-shaye mana, kuma kullum a kansa tsautsayi yake fa?awa, ni na gaji, yana warkewa tafiya zan yi na ha?ura da zaman da shi" tayi maganar tana kuka, har ta fara tari mai ha?e da haki.

"Mai laya"

"Allah ya ?ara maka lafiya"

"Ayi wal?iya, sai da safe"

Walid ya ce "Iya wuya, yadda ka ke so haka za ayi" suka tashi suka fice, ya juya ya saukko daga kan gadon.

Kamar ba ciwo ne a cikin sa ba, ya tunkaro in da take ya zauna, ya ?ura mata ido tayi shiru ta sunkuyar da kai, tana haki sama-sama.

"Ki ka ce tafiya zaki yi?"

"Eh" ta bashi amsa kai tsaye.

"Yaushe?"

"Kana warkewa gida zan koma, tun da ba ka so na, kullum cikin sakani ka ke a tashin hankali, na ce maka ba na son ka din ga zuwa in da za a ji maka ciwo, amma ka ?i, ka dizgani a gaban wannan mutumin. Wallahi ba zan ta?a yafe masa ba, duk shi yake ?ara ?ata ka".

"Yanzu abun da ki ka yi dai-dai ne? Ubangidana ne fa, ki ka tsaya kina yi masa rashin kunya".

A ?ule ta ce "Shi dai-dai ?in yayi mini, ba dan Allah ya yi da sauran kwananka a gaba ba, da yanzu wani zancen ake ba wannan ba, ni na rasa in da zan saka raina, abun da nake ta tunanin zan iya ashe ya fi ?arfina, shikenan".

Gyara zamansa yayi, ya janyota jikinsa, yana kissing ?in ta a hankali.
She's not in mood, ta so ta ?wace, sai dai kuma raunin jikinsa ya hanata yin hakan, kar ta fama masa.

A hankali ya cire bakinsa daga nata yana kallon ta, amma ta ha?e rai tayi kicin-kicin.

"Ki gaya wa likitocin nan su sallameni gobe, ko kuma na yi tafiyata"

Da sauri ta kalleshi ta ce "A hakan ba ka warke ba?"

"Eh na gaji da yadda ake zuwa ana magana da ke, haushi nake ji, shi kansa indabo shirun da nayi masa, shi ne mafi alkhairi da mummunan naushi zan yi masa"

"Dan Allah ni ka daina ta?a ni, asibiti ne fa, idan wani ya shigo fa?"

"To je ki rufe ?ofa ki dawo, zafi nake ji, ina bu?atar fankata, lamba uku kawai, ba sai an ?ure mata gudu ba"

"Ko mafici ba zaka samu ba, ni rabu da ni" tayi maganar tana sake ture shi.

Ya ?i tashi ya din ga takura mata, duk dan ta sake ta ?an samu nutsuwa daga fushin da take yi.

"P.A wane mahaukaciya ne ya aura wa yarinyar nan mai zamani?"

"Allah masani honorable"

"Ikon Allah, kalarta kalar muryarta, ai rannan na kira ta ?aga, kai ka ga yarinya zu?e?iya kamar ita tayi kanta. Amma kamar ta dace da aikin da malamin nan fa ya bayar, ya aka yi ba ka yi mini zancenta ba, gashi wannan an samu matsala"

P.A ya ce "Honorable, kai ka san ba kowane kaya ne yake ta?uwa ba, idan aka ta?a wannan za a iya samun matsala, kuma na manta da ita ne gaba ?aya wallahi"

Indabo ya ce "Wace irin matsala? Ai tsaf za ta ta?u, ba tare da ya sani ba, idan ma ya sani na san yadda zan yi da shi. Lallai 'yar madara tayi kalar madarar sosai. Wannan yarinyar ita ce rauninsa kenan?"

"Sosai kam, dan alamu sun nuna yana mugun sonta"

Indabo yayi wani irin murmushi yana shafa tumbinsa.

Ma?wabtan su Jauhar sun yi mata kara, na zuwa duba Al'amin, suka kakkai mata abinci, daga gidan su Baba ya je Saifu sai mama, sun je sun duba shi, duk da maman ta gaggaya mata ba?ar magana a kansa.

Satinsa ?aya da ?yar, ya uzzura akan lallai, sai an sallame shi, haka aka sallame su suka koma gida.

Cikin ikon Allah, Indabo yayi nasara, bayan fa?i tashi, da shige-shige yayi nasarar samun kujerar ?an majalisa.

Har gida Abbu ya sake zuwa duba Al'amin, sai dai kamar wurin jauhar ya zo, da ita suka ?an yi hira, ya tashi ya tafi.

Hafsa kuwa abun duniya ya hanata sukuni, da ?yar ta samu Alhaji mu'azzam ya fara saurararta, sai dai yadda yake bin matarsa sau da ?afa, yake ?ona mata rai, sai abun da ta tsara yake yi a gidan, idan ba ta ga dama ba, sai ya shafe kwana goma bai taka wurin Hafsa ba, amma ku?i akwai su, komai take bu?ata akwai shi, sai dai fa tsakaninta da miji sai an ga dama a bata aro, wataran yana wurin nata ma, za ta kira shi, kuma haka zai tsallaketa ya tafi wurin matarsa, ga yaransa marasa kirki, sun rainata rashin kunya kala-kala.

Da ta matsa ma da ?orafi, ya ce idan ta gaji ta tafi, shi fa duk lokacin da ya zo wurinta, baya gane komai, ha?uri kawai yake yi shi ma, ta ?yale shi.

Ta gaji tayi yaji, Anty ta din ga yi mata masifa, a kan dan me zata dawo gida, sai asirinsu ya tonu, dole ta cigaba da zama har zuwa lokacin da za a samu mafita.


Al'amin ya warke sarai, ya cigbaa da harkokin sa, sai dai jauhar kusan kullum tana garga?insa a kan indabo.

Gashi ta ri?e masa wuta a kan yin salla a kan lokaci, da yin azkar, har zama tayi ta ciro masa addu'oi na musamman ta rubuta masa su.

Ita kanta ta san ikon Allah ne, da ?arfin addu'a da take yi, da kuma yadda take bin sa da kyautatawa da biyayya, ya sanya take iya sarrfaa Al'amin, har yake jin nauyin aikata wasu abubuwan saboda ita.

Da asuba idan ya je salla ya dawo, da kanta take ajiye masa sigari, kara biyu ko uku, ta ce masa ya sha banda shan ?waya kuma.

Ta jira ya gama sha, yana ?aurin yana komai, ta nani?e masa a jikinsa, dan mantar da shi damuwa, kewar kayan shaye-shayen sa.

Da daddare suna kwance, ta ce "Master, ka san abun da matar nan tela tayi mini?"

Ya ce "A'a"

"Wai na cewa matar nan dan Allah, ta koya mini ?inki, idan ta yarda zan tambaye ka, na din ga zuwa, ta ce mini za ta yi shawara, wai daga baya ta ce mini mijinta ya ce a'a bai yadda na din ga zuwar masa gida ba, ko kara ba ta yi mini ba, duk wahalar da nake yi mata, wani abun ta biyani wani sai dai na yafe ku?in, na ji haushi dama kuma ba ta zo tayi mini jajen abun da ya same ka ba"

"Saboda ni me mijin ya ce bai yadda ki je gidansa ba?"

"Wallahi ban sani ba, na dai ji babu da?i gaskiya, amma ban san dalilinta ba"

Al'amin ya ce "Manta da ita, Allah ya baki wani abun da ya fishi, uwar son ku?i"

"To wa ya ?i ku?i master" yayi murmushi yana shafa bayanta.

Da asuba, mutane sun fito daga masallaci, faruku tela ya ga Al'amin a ?ofar gidan sa.

Gabansa ya fa?i ya ce "Lafiya kuwa?"

Al'amin ya ce "Sa?onka na ji, 'yar madara ta ce a koya mata ?inki ka ce a'a, fine idan na kuma ganin 'ya'yanka sun tako mini gida, sai na daddatsa su, na zuba a leda na kawo maka.
Na kuma yi suspending ?in shagonka, na wata guda, wallahi ka bu?e sai an sassara mini kai" yayi tafiyar sa ya bar faruku a wurin, cikin tashin hankali.

?arshe sai da aka ha?a da zuwa har gida, magidanta suka zo ban ha?uri, jauhar tayi mamakin abun da yayi, ita kawai hira tayi masa abun miji da mata, amma ya je yana yi wa mutumin barazana. Ta ce zata yi masa magana ba wani abu, malam faruku ya cigaba da bu?e shagonsa.

Ya dawo da daddare, ta sha kwalliya, kamar yadda ta kan caccanza tare da ?ir?iro da sabbin abubuwa, domin sabunta abubuwa da yawa a rayuwar auren na su, saboda rage barazanar gundurar juna.

Ya nemi wuri ya zauna a falo, yana ta sauke numfashi, ta fito ta na murmushi ta haye kan cinyarsa, ta zuba masa ido ya lumshe idonsa yana ta huci kamar kumurci.

"Nawan" tayi maganar tana shafa sajensa.

"Yau kuma me aka sha haka? aka ?i kulani" yayi shiru bai ce mata komai ba.

"Master"

"Mmm"

"Me ka sha yau?"

"Wiwi"

Jauhar ta ce "Da me?"

Ya girgiza mata kai alamar babu.

"Ba ka saba ?arya ba" ta saka yatsanta a bakinsa, ta ciro guntuwar ?wayar da take ?asan harshensa, la??ansa sun yi fari.

"?waya ko? Meyasa. Na ce fa idan an ?ata maka rai ne, ko kana cikin damuwa ka yi ta ambaton Allah, kana azkar, meyasa za aje a sha ?waya, ka ?ata mini shirina na yau gaba ?aya"

Babu tsammani, ya mi?e da ita a jikinsa, ya tafi da ita ?akinsa, rabi a buge yake, rabi a cikin hayyacinsa, yayi ?o?arin kissing ?in ta, ta ce "Ba zaka sumbace ni, da sauran ?waya a bakinka ba master, me aka yi maka?"

"Mhmmm bakomai, i need you"

Ta ce "A hakan, a buge fa ka ke"

"Ina hayyacina, kin yi mini kyau ne sosai" kasa hana shi tayi, ya gama ya cigaba da yi mata surutai.

Ta rungume kansa a ?irjinta tana shafawa ta ce "Na san wataran zaka daina master, Allah ya shirya mini kai mijina"

"Madarata"

Ta ce "Idonka biyu"

"Mmm"

"Me zaka gaya mini?"

"In sha Allah zan daina, ki cigaba da yi mini addu'a" yayi maganar cikin muryar maye sama-sama.

"Addu'a kullum ina yi maka master, Allah ya nuna mini ka daina"

"Madarata"

"Master na"

Ya ja jikinsa, ya kai bakinsa saitin kunnenta, ta yi shiru, tana jiran ya yi mata magana.

Kawai ya fara murmushi, yana yi mata numfashi a kunne.

"Zaki koma makaranta"

"Allah ya ja zamaninka, godiya nake"

Cikin mayen ya sake cewa "Ki daina yawan kuka ba na so"

"To ka daina sakani"

"Allah ya bani ku?i na kai ki makka"

"Amin Mijina, da alama ?wayar nan nisha?i take sawa"

"Ke ce nisha?in nawa" yayi maganar yana dariya.

Ita ma murmushin ta yi masa, ya kwanta a gefenta, bacci ya ?auke shi.

Da Asuba ya rigata tashi, ya tasheta shi kuma yayi wanka yayi alwala ya fita.

Da wani irin tashin zuciya ta tashi, kamar za ta yi amai, ta danganta hakan da awarar da ta yi wa cin ?oshi jiya da daddare ulcer ta tayar mata.

A ?akinsa ta yi sallar ta idar, idonta ya sauka a kan robar cocala da ke gefen katifarsa.

A take ta ji idan ba ta sha coke ?in nan ba, akwai matsala.

Ta ?aukko, ta bu?e ta kafa kai ta fara sha, sai da ta shanye tas, sannan ta ajiye jarkar, still ta din ga jin kamar za ta yi amai. Ta yin?ura ta tashi, ta tafi ban?aki, ta yanke jiki ta fa?i, jini ya fara gangarowa daga hancinta.


Ayshercool
08081012143
???500 ne via 0009450228
Aisha Adam jaiz bank sai shaidar biya ta 08081012143

90009343
'Yan Nijar ku turo katin airtel na 300fcfa

Arewabooks ayshercool7724



Al'amin a masallaci, magidanta suka tare shi suna ?ara bashi ha?uri, a kan abun da ya ce wa faruku tela.

Ya koma gida ya shiga ?akinsa, yanayin kwanciyar da ya ga jauhar ne ya sanya ya tsaya yana kallonta.

"Wace irin kwanciya ce ki ka yi haka, ko baki da lafiya ne?"
Ya ga shiru ba ta motsa ba.

Ya ?arasa gabanta, ya ?agota, gabansa ya fa?i, ganin hancinta na ta zubar da jini, bakinta ma jinin ne yake fita ha?e da wata kumfa.

"Innalillahi wa Innalillahi raji'un" ya furta cikin tashin hankali yana jijjiga jauhar.

Amma shiru ba ta amsa ba, ya ?aga hannunta ya ga ya saki, ya kai hannunsa hancinta amma babu alamar numfashi a tare da ita.

"Jauhar, meya same ki haka? Meya sameki ne?"

Jijjigata yake iya ?arfin sa, amma ba ta motsa ba, kawai idonsa ya sauka a kan robar cocala. Ya kai hannu ya ?auka ta shanye komai tas.

A wurin Nura guduma ya ?wace, ganin yadda ya ha?a uban ?wayoyi a ciki zai sha, ya ?wace ya ?are masa zagi, ya ce idan yana wannan ha?in kashe kansa zai yi. Ya taho da shi gida ya ajiye a bayan katifar, ya kai kwana uku a ?akin, shi ya ma manta da ita a ?akin.

Da sauri ya ?aukota ya fito da ita falo, ya kwantar da ita, ya fita da gudu, ya rasa wani gidan ma zai dosa, saboda ba shiga harkar mutanen layin yake ba, amma kasancewar a ki?ime yake, ya saka ya nufi gidan wasila, dan maigidan ya sai mota.

Wani irin mahaukacin bugu ya din ga yi wa gate ?in gidan, ba shiri mijin wasila ya fito daga shi sai gajeren wando, ya bu?e yana rarraba ido.

"?aukko mota matata babu lafiya" ya ce "To" dan a yanayin fuskar Al'amin ko ba'asi ya tsaya tambaya, bai san me zai yi masa ba.

Jin bugun gate ?in, ya sanya wasu daga ma?wabtan su fitowa, su ji ko lafiya.

Mijin Wasila ya fito da mota, yanayin halin da ya fito da jauhar, ya sa gaba ?aya jikinsu yin sanyi, dan babu alamar rai a tare da ita.

Mijin wasila ya ce "Bari ya taso matarsa a tafi da ita, asibitin"
Cikin ikon Allah suka yi wa Al'amin kara, mussaman da jauhar tana girmama su da jan yaransu a jiki, ma?wabcin mijin wasila ma ya shiga motar ya ce su tafi tare.

Asibitin da ya ta?a kaita aka bu?e mata file suka tafi.

Suna tafe yana girgizata yana ta tashi.

"Malam Al'amin ka yi ha?uri, ka daina jijjigata kar ka ?ara gajiyar da ita"

Al'amin bai bi takansa ba, ya ri?e hannun jauhar, "Dan Allah ko motsi ki yi Zahra, dan Allah ki tashi" su dai duk suka yi shiru, yanayin tashin hankalin da yake ta tattare da Al'amin ya ?ara bayyanar da tsantsar soyayyar da yake yi wa jauhar.

Suna zuwa Asibitin, Al'amin ya nufi emergency da ita, sai da aka bishi aka tambaye shi file numbern ta.

Mijin wasila ne ya biya ku?in ganin likita, dan ba ya cikin nutsuwar da za a tambaye shi ku?i.

Likita ya ce "Malam, meyasame ta?"

Al'amin ya rasa ta ina zai fara.

"Guba ta sha"

"Guba kamar yaya? Wannan ma ai kamata yayi sai an zo da 'yan sanda, ya aka yi ta sha guba?"

"Ka fara ceto mini ranta, duk wani bayani na yi maka daga baya, ka ceto rayuwar ta tukuna".

Likitan ya ce "Ai sai ka fara gaya mini meyafaru?" Ya juya kan jauhar, ya duba pulse ?in ta, tana bugawa a hankali.

Aka samo bandage, aka toshe hancinta, saboda jinin da yake fita, aka ?agota ?irjinta a sama a kan gadon.

Likitan ya ce "A cire mata hijjabin nan"

Al'amin ya ri?e hijjabin, ya yi shiru.

Nurse ?in ta ce "Malam ranta za a ceto, ka yi ha?uri"

Mijin wasila ya cewa ma?wabcinsa su fita.

Suka fita daga emergency, kayan bacci ne kawai a jikinta, doguwar riga iya gwiwarta.

Halin da take ciki, bai hana shi jin matsanancin kishinta ba, likita kuwa aikinsa kawai yake yi, zu?e jinin da yake bakinta, da kumfar da take fita.

Sannan suka fara yi mata CPR, a hankali take ajiyar zuciya, zuciyarta na ?o?arin responding.

Wasila ta ce "Likita wani jinin na bin ?afarta"

Wani likitan aka kuma kira, aka tafi da ita scanning room, nan suka ga akwai ciki, sai dai shi ma ya fita.

Al'amin ya rasa in da zai saka ransa, Nurses suna aikinsu, likitoci na nasu, aka ce Al'amin ya fita ya ce wallahi ba zai fita ba.

Haka aka din ga ?aga jikinta, ana ?o?arin tsayar da jinin da yake fita ta ?asanta, allurai kuwa tsira mata kawai ake yi, ban da wanda ake zuba mata a cannula.

Al'amin ya ji da ma shi tsautsayin nan ya fa?awa ba jauhar ba, ko a iya haka ta galabaita.

Sakamakon gwajin jini, ya fito jininta ya yi ?asa matu?a ana neman a ?ara mata wani.

Ya fita hankali a tashe, mijin wasila ya ce "Al'amin ya ake ciki?"

Idonsa jawur ya ce "Jini za'a bayar, ku bani aron waya dan Allah, na kira a kawo mini ku?i, da kuma wanda za su bayar da jinin".

?aya ma?wabcin na su hadi ya ce "Ai sun ce sai an yi depositing dubu hamsin za su ganta, mun je reception mun biya, yanzu jinin a fara dubawa a namu, ko za a dace".

Ya ce "To, amma a bani aron wayar dai, na yi kira".

Walid ya fara kira ya ?aga da ?yar ya ce "Maza"
"Kana ina ka nemo ku?i ka zo asibitin da nake kai ?ar madara cikin hanzari ba ta da lafiya"

Tuni Walid ya ware ya ce "Meya same ta?"

"Ka zo kawai".

"Gani nan"

Likitocin suka kira Al'amin, suka zauna da shi suna tambayar sa meyafaru da ita.

"?waya na ajiye a cikin cocacola ta ?auka ta sha ba ta sani ba"

"Kwanakin baya fa, haka nayi ta counselling ?in ka, a kan ka daina yi mata abun da yake saka jininta ya hau. Yau kuma ka bari ta sha ?waya wannan sakaci ne baka kyauta ba, idan ka yi silar rasa yarinyar nan, Allah ba zai barka ba"

Al'amin jikinsa yayi sanyi matu?a.

"Ko ka san cewa tana ?auke da juna biyu? Yanzu dai ciki ya zube babu shi, kuma a shawarce, idan Allah ya bata lafiya, yakamata tayi tsarin iyali, mahaifarta ta sake hutawa, dan ?wayoyin sun yi wa jininta ?arfi fiye da kima"

"Innalillahi wa Innalillahi raji'un, ba zata sake ?aukar ciki ba kenan?"

"A'a zata iya ?auka, amma a shawarce, mahaifarta ta huta, dan ya yi affecting ?in mahaifar, akwai bu?atar ta huta kan ta sake wani cikin "

Daga shi har jauhar babu wanda ya san da cikin, tsananin son da take yi wa yara, ya sanya ta mayar da boti kamar ?an da ta haifa, dan ma kwanan nan ya hanata ?aukko yaran mutane, tayi ta fama da su tana yi musu hidima.

Ya tashi jiki babu ?wari ya fita, su Walid suka ?araso Asibitin, a ki?ime suka nufe shi "Mai zamani ina take? Meyafaru?"

Bai ?oye musu komai ba, ya gaya musu.

Cikin tashin hankali Walid ya ce "Amma wallahi ?an kutm..... Ne kai, wane irin hauka ne zai sanya ka ajiye abu in da zata ?auka ta sha, kuma ba ka gaya mata menene ba? Ka san jikinta ba zai iya ?aukar abun da yake ciki ba wannan ai hauka ne"

"Mai laya" yayi wa Walid tsawa.

Sai dai walid ya kuma narka masa ashariya ya ce "Ba za a kiyayeka ?in ba, idan ka ji haushi ka saka mini ?arfe, idan ta mutu kai ka yi asara, wannan ai ganganci ne da wauta"

Wata irin zuciya ta yin?uro Al'amin, ya nemi ya huce takaicin sa a kan Walid, amma Walid ma ya hayyaya?o masa, dan ba ?aramin mutunta su Juahar take yi ba, yarinyar was very simple and innocent.

Security ne suka shigo, suna ?o?arin korar su Al'amin, suna nema su tayar da hayaniya a cikin Asibitin.

Liti ya kalli security ya ce "ko dai ka ?yale su, ko abun ya ?are a kanka"

Walid a fusace shi ma yake yi wa Al'amin martani "Saboda ka ga ba ta da baki, iyayenta ba tuhumarka za su yi ba, shi ne zaka yi musu ganganci da rayuwar 'ya, wallahi daga nan gidan su zan je na fa?a, idan ma kashe auren za su yi, su ?auke 'yar su" Al'amin kawai yayi shiru, dan da makami a jikinsa sai ya yi wa Walid illa.

"A ina za a duba

Please Login or Register in order to submit comment