Reading KARFE A WUTA Chapter 67 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ji muryarka, ka ji Oga" wani irin mugun kallo yayi mata, ya nausa ya bi wata hanyar, ita kuma tayi gaba tana murmushi.

***
Ramma na zaune a kusa da Abdul, yana kallon ball, ita kuma ta kunna radio a wayarta, tana ji.

Ya kalleta ya ce "Dan Allah ki rage radion nan"

"Ina ruwanka da ni ne, ka yi kallonka mana"

"Kin cika mini kunne da radio ne"

"To ita ball ?in magana ake yi? Ba ihu bane ba kawai?"

Abdul ya ?ure volume, ita ma ta ?ure volume, ta kara masa radion a kunnensa.

Yayi mata shiru ya ce "Kya yi kya gama"

Sumayya ce tare da murtala a studio, suka gabatar da program, kasancewar an samu akasi masu gabatar da program a dai-dai lokacin ba su samu zuwa ba.

Program suke yi akan abubuwan da suka shafi rayuwa, suna yi suna karanto sa?onnin masu sauraro.

Murtala ya ce "T ladan, ga wata tambaya daga masu sauraro, wai an ce a tambayeki, wace irin ala?a ce tsakanin ki da Nabila Yusuf maitama, da kullum ba kya ta?a aiki ki tashi, baki ambace ta ba, baki tsokane ta, ko saka wa?o?i domin jin da?inta ba?"

Sumayya ta yi murmushi ta ce "Barrister Nabila, voice of voiceless a lady of her words, a hardworking, strong minded young barrister, she's exceptional, lovely and simple sister of me" tayi maganar tana jin zafin sa?anin da suka samu a tsakanin su.

Murtala ya ce "Tir?ashi, duk wannan kirarin itaka?ai?"

"Sosai, Nabila mutum ce ta mussaman a rayuwata, ina yi mata son fisabilillahi"

"To yanzu da saurayinki, da Nabila wa ki ka fi so?" Ta kwashe da dariya ta ce "Uncle murtala wannan ai ha?a fa?a ne"

"To yanzu kafin muyi sallama da masu sauraro, gaya mana kalma ?aya tak a kan Barrister Nabila"

"Mai gaskiya ce, ina yi mata fatan nasara, ya ?aukaka mini ita, ya kuma kare mini ita a duk in da take, ya dauwwamar da ita a kan gaskiya"

Murtala ya ce "Amin ya haiyyu ya ?aiyyum, Allah ya bar wannan ?auna, kafin mu ?ar?are shirin, mun kar?i takardar wata baiwar Allah da za a yi wa ?anta aikin ?aba, amma ba ta da hali, tana neman taimakon bayin Allah. Akwai kuma wadda take neman ku?in sayawa mahaifiyarsu magani mai fama da hawan jini, muna fatan zaku taimaka"

Nabila kuwa tana driving, ba ma'abociyar jin radiyo bace ba, amma saboda sumayya take sauraren radio. Hawaye ta din ga sharewa, tare da tuna abun da ta yi wa sumayyan.

Ramma kuwa cewa ta yi "Allah ya ?arfafi wannan baiwar Allah, ya tabattar da ita a gaskiya, kar ya kauce hanya, kamar waccan munafukar mara imani" Abdul yana jin ta, yayi mata shiru. Ganin bai kulata ba ya sa ta ce "Ba zaka ce amin ba"

"Ni fa ball nake kallo"

"Allah ya sa a cinye club ?in da kake yi"

"Ba amin ba" ya ?auki wayarsa, ya kira admin ?in asibitin sa, ya ce a je gidan radion su sumayya, a kai yaron nan ayi masa aiki kyauta, mai hawan jinin ma a kai ta a bata magani.

Ramma ta ce "Kalle shi kamar na Allah" duk ya?i kulata, ta tashi ta nufi ?aki, ta saka hannu ta kashe tv ta riga ?aki da gudu, kawai yayi dariya.

***
Kwanaki biyu, Nabila ta daina samun Viper a waya, sai dai da ta kira walid, ya tabattar mata da lafiyarsa ?alau.

Nabila ta fara gazgata zancen Viper, duba da yadda Nasir yake kashe-kashen ku?i, ya canza mota ya cigaba da gininsa, kuma salarynsa gaba ?aya ba wani shahararre bane ba.

Nabila tana kwance tana waya da Alhaji Wada M karofi, yadda yake lalla?ata yake yi mata magana, har kunya yake bata.
Fuskar viper kawai take hangowa, yanzu da shi take yi wa kalaman nan, da tuni ya ha?e rai yana hararta. Bayan sun yi sallama ta ajiye wayar, Walid ta shigo ?akin ta ce "Arfa, isa ne ya shigo yanzu, wai ana sallama da ke a waje"

"Kai, wane ?an ba?in cikin ne zai hana mini jin da?i a magaribar nan? Ni fa ban yi da kowa za a zo wurina ba"
Walida ta ce "Ace ya tafi kenan?"

"A'a gani nan zuwa"

Ta yafa mayafin abayarta, ta fita, a ?a'idar Abba a cikin gida suke zance, ganin bai shigo ba, ya sanya ta gane lallai wanda ya zo ?in ba?o ne.

Ta zira kai ta le?a ?ofar gida, dan duba waye.

A opposite ?in gidan ta ga Viper a tsaye yana kallon ta.

Ayshercool
08081012143
???500 ne via 0009450228
Aisha Adam jaiz bank sai shaidar biya ta 08081012143
Wanda za su jira document 1K ne.

90009343
'Yan Nijar ku turo katin airtel na 300fcfa

Arewabooks ayshercool7724

Gaban Nabila ya fa?i, cikin matsanancin tsoro da tashin hankali, ta din ga waige-waige tare da dubawa, idan akwai wanda ya ganshi, amma layin babu kowa, sai manyan security light da suka haska ko ina.

Ta sake kallonshi, ta tabattar shi ne, ta ?arasa in da yake da sauri ta ce "Viper, waye ya nuna maka gidanmu? Yau kuma ba office ba har gida?"

"Akwai matsala ne?" Yayi maganar yana ?ara ?ureta da ido.

"Au tambayata ma ka ke yi? Amma dai ka san yayana nemanka yake yi ko meyasa zaka zo gidanmu, lallai sai ka tona mini asiri ne? Waye ma ya nuna maka gidanmu?"

"Shi yayan naki, ki shiga ki gaya masa gani ya zo ya kamani mana, shikenan ki daina wahalar da kanki da fargaba mana. Kina tunanin zan yi aiki da wadda ban san wacece ba?"

Ta ce "Yanzu dai duk ba wannan ba, dan Allah mu je daga wancan lungun, mu yi magana"

Ya sha kunu ya ce "Ban gane muje lungu ba"

"Eh mana, mu je can mu yi magana kar a ganka"

"A'a ni ba zan shiga lungu a daren nan ba"

"Innalillahi wa Innalillahi raji'un, to ai ba wani abun na ce ayi a lungun ba, magana kawai zamu yi kar a ganka nake tsoro"

"Kuma sai ki ce in shiga lungu"

"Na shiga uku, sai ka ce wata 'yar iska, kar ka yi mini wata mummunar fassara mana"

Viper ya ce "Ke da duk baki yi wannan tunanin ba, ki ka amince da aiki tare da ni, ki ke i?rarin zaki taimake ni? Ki tsaya ki saurare ni" ya yi maganar fuskarsa ?auke da matsananciyar damuwa. Duk da bai kasance mai fara'a ba, amma yau akwai damuwa sosai a tare da shi.

"Amma dan Allah waye ya nuna maka gidanmu"

"Ba wannan ne ya kawo ni ba"

"To Allah ya baka ha?uri sir, me yake tafe da kai?"

"Nura" ya fa?a a ta?aice.

"Waye hakan?"

"?anina Nura guduma, bayan mutuwarsa ina duba mahaifiyarsa, sai dai bayan an tsare ni ban samu damar yin haka ba, amma su Walid sukan je amma ba ko yaushe ba, bayan fitowa ta kuma, bani da cikakkiyar nutsuwa, kuma ina matu?ar jin nauyinta ban je ba, ban kuma saka su walid sun je ba"

Nabila ta nutsu tana sauraronsa, duk a tsorace take, kar wani ya ganshi, duk da akwai facemask a fuskar sa.

"Mijin da ta aura bayan baban Nura ya rasu, shekaru biyu da suka wuce, tana ta fama da rayuwa, ga yaranta guda biyu, a ta?aice dai jiya da su Walid suka dawo daga garin, sun tabbatar mini da 'yar ta aka yi wa fya?e ita kuma ba a san in da take ba" Nabila ta zabura ta ce "Kuma?"

"Yarinyar da ki ke bincike a kan case ?in ta, Naja bunkure ta shiga case ?in"

Nabila ta ce "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, kalmar nan ko da?in ji ba ta da shi, dama ita ce? To ba su gano in da maman take ba?"

"Ina gaya miki kina tambayata, na baki nan da sati biyu rak, tun da kin ce wanda ake zargi ba shi bane ba, ki fito da mai laifin, ko kuma ni na fito da shi ta ?arfin tsiya".

Cikin rashin fahimta ta ce "In fito da mai laifi kuma ta ina? Nima bulayin nemansa nake ai saboda in wanke client ?ina"

"Sai fa kin nemo shi, ko kuma ki tabattar an yankewa mutumin nan hukunci dai-dai da abun da ya aikata"

"Amma dai ka san ni lawyer ce ba 'yar sanda ba ko? Jami'an tsaro sune za su yi maka wannan aikin, ni kuma na tsaya na tabattar kotu ta yi adalci"

Ya tsare ta da idanunsa ya nuna ta da yatsansa ya ce "Ke zaki yi, ba wanda zai yi sai ke, ki nemo ainihin mai laifin, ko kuma ki bari a hukunta wannan mutumin"

"But he's not guilty, he's innocent, ka bari na bi komai a hankali"

Ya ?an yi shiru sannan ya ce "No matter what it takes, ki binciko ainihin mai laifin nan, an cutar da matar nan fiye da yadda ki ke tunani"

Nan ya warware mata ?angaren labarin sa na Nura, da ba ta sani ba.

Rawa ?afafuwanta suka fara yi, jikinta yayi wani irin sanyi, ta kasa magana.

"Ki din ga yi mini uzuri wasu lokutan, ni mutum ne mai tarin laifuka ga mutane, bana son in ga wani a cikin damuwa, ina tsoron ace matar nan guduwa tayi saboda ba?in ciki, ba haka ba ma, voice message ?in da ki ka kunna mini, sai a yanzu na sake tabattar da muryarta ce, ta tabattar da har gida wanda yayi rape ?in yaje ya ?auke 'yar, dan haka ramma tana tare da wanda ya yi mata fya?e, kuma Naja'atu Bunkure ta sanshi, ba dan ta tsayawa yarinyar ta shiga case ?in ba, dan ta bawa mai laifin kariya ne".

"Yanzu ka yadda wanda nake karewa ba shi da laifi?"

"Na sani, amma dole ki yi wani abu, a nemo yarinyar nan da mahaifiyarta"

Nabila zata yi magana, aka haske su da fitilar mota, ta saka hannu ta kare saboda hasken fitilar, shi kuwa yayi ?uri yana kallon fitilar.

Viper ya ce "Ko dai ki gaya masa ya kashe fitilar nan, ko na ha?a idonsa da na motar na ?auke musu wuta gaba ?aya"

Fitowa yayi daga motar ya ?araso in da suke, ya kalli Viper, sai dai a wannan karon ma ya ji wannan fa?uwar gaban. Kallo ?aya ya yi wa Viper, ya tuna a in da ya ganshi.

Ya kalli Nabila ya ce "Arfa waye wannan? Irin wannan samarin kuma ki ka koma kulawa?"

Ta kalli Viper sannan ta kalli Nasir ta ce "Yaya me yayi maka ne? Na gaya maka tun waccan ranar he's my client"

"Client like how? Shi ne zai din ga biyoki har gida? Get inside kafin na kwa?eki a wurin nan" Addu'a take Allah ya sa kar Viper ya hasala.

Viper ya ciro wata fitila daga aljihunsa, ya haske idon Nasir, ya matsa daf da shi, Viper ya fishi tsawo sosai ya ce "Talk to me, like a man, baka din ga yi mata shouting ba"

Ya ja da baya ya kalli Nabila ya yi mata alama da hannunsa na i will call you.

Ta jinjina masa kai, shi kuma ya juya zai tafi.

"Waye kai?" Nasir yayi maganar cikin dakewa, dan muryar Viper kawai a bar tsoro ce.

Viper ya juyo, ya kalli Nabila, da ta bashi tausayi, ban da tana wurin, kuma bai san me abun da zai aikata ka iya haifarwa ba, da sai ya sakawa Nasir ira?i sannan ya gaya masa waye shi, kamar yadda ya yi wa tijjani yayan yar madara.

Ya kalli Nasir ya ce "A man" ya fa?a a ta?aice.

Nasir ya waiwaya, ya kalli Nabila zai fara masifa, amma ta zura da gudu ta shige gida.

Rufa mata baya yayi, yana masifa har ?akinta ya bita, yana yi mata bala'i, ganin yana neman ya tozarta ta a gabam mutanen gidan ya sanya ta fara kiran sunam Abba da ?arfi.

Aikuwa Abba ya saukko daga kam benensa yana fa?in "Wai waye yake ta?a mini yarinyar nan, kai Nasir menene haka? Dukanta zaka yi? Shekara Ashirin da biyar sai ka kamata kana duka dan rashin mutunci?"

"Abba ba dukanta zan yi ba"

"To me ka yi mata take wannan kururwar haka?"

"Abba gaba ?aya Arfa ta canza, ta tsiri wasu irin ?abi'u na rashin gaskiya, rannan na je ofishin ta, na tarar da ita da wani mutum, gaba ?aya bai yi kama da mutanen kirki ba, yauma still ta tsaya da wani a waje, maimakon cikin gida tana zance, kamar dai wancan mutumin ne, gaba ?aya bai yi kama da mutanen ?warai ba"

Abba ya kalli Nabila ya ce "Arfa, yayanki a kan gaskiya yake, ni kaina shige da ficen samarin nan naki, ya fara isata".

"Abba, wallahi ba mutumin banza bane ba, kuma ko mutumin banza ne, ba wata muguwar ala?a ya gani tsakani na da shi ba, na gaya masa client ?ina ne kawai, amma ya?i yadda kwanan nan komai nayi sai ya din ga zargina na rasa me nayi masa gaba ?aya"

"A'a Arfa, Nasir yana cikin masu goyon bayanki a gidan nan, tun da har ya magantu, to ya fiki gaskiya, ki san irin mutanen da zaki din ga tsayawa, kuma ki din ga mu'amala da su, yanzu a cikin samarin nan naki, lallai ki duba mai nutsuwa ya zo in ganshi, nima zan fi samun kwanciyar hankali ace kina ?akinki" Nabila ta yi shiru, Abba yayi ta yi mata nasiha, bayan ya gama ya fita, Nasir ya bi bayansa.

Nasir ne ya bi bayan Abba, suka shiga ?akinsa ya ce "Abba, yakamata ka ja wa arfa kunne, wasu abubuwan take yi kwanan nan, shishishigi a kan wasu abubuwa. Ta sako wannan barrister Naja'atu Bunkure a gaba, kar ta je ta janyo wa kanta wata matsalar"

Abba ya ce "To ai ni kaga ban sani ba, ban san me take aikatawa ba wasu lokutan, amma babu komai, zan yi mata nasiha, ka san ba kowane lokaci fa?a yake tasiri ba".

Nasir ya ce "Haka na, sannan kuma Abba"

"Sannan kuma me, ina jinka"

Ya ?an muskuta ya ce "Abba dan Allah ka bani auren Arfa"

Take annurin fuskar Abba ya ?auke, ya ce "Auren arfa kuma?"

Ya ?an yi shiru yana wasa da yatsunsa.

Abba ya numfasa ya ce "Kenan kishi ne ya saka ka shigo kana yi mata fa?a?" Ya girgiza kai ya ce "A'a Abba, ba haka bane ba"

"To, Nasir kai ?a na ne, hakazalia arfa, babu wani banbanci a tsakaninku, dan haka ba zan so abun da zai cutar da ?ayanku ba. Ba zan manta abun da mahaifiyarka tayi mini a kan yarinyar nan ba, kuma haryanzu ina kallon irin ?iyayyar da take nuna mata, na da?e da gane kana sonta, amma ina fatan ta samu wanda hankalinta zai kwanta da shi. Muddin ka aureta mahaifiyarka ba zata ta?a barinta ta zauna lafiya ba.
Ni bani da matsala da son da kake yi mata, amma ka nemi yardarta, da ta mahaifiyarka tukuna"

Nasir ya ce "To Abba, na gode sosai" ya tashi ya bar ?akin.

Nabila ban?aki ta shige, ta rufe ?ofa ta kira Viper.

"Yanzu fisabilillahi ka kyauta mini kenan? Ka saka an yi mini fa?a, Allah ne ya rufa mini asiri, dan Allah ka daina zuwa in da nake, gara ka kirani na zo da kaina"

"Ki je ki yi tunani a kan abun da na saka ki, ki san abun yi sati biyu kawai ki ke da shi"

"Ya kake bani umarni ne a haka, ka din ga lalla?ani mana, why are you always bossy ne? Sai da safe zan duba na ?ara effort, ina iya ?o?arina a kai, tauye ni ake yi, ka san ba ni da kowa sai Allah ni, amma ka yi mini addu'a in sha Allah ni zan kawo ?arshen bunkure"

"Allah ya sa" ya kashe wayar.



***
Ramma ce ta ?urawa wayar Abdul ido, ta kalli ?ofar ban?aki, yana ciki yana wanka, ta mi?a hannu ta ?auka ta bar ?akin.

Bai jima ba ya fito daga ban?akin, sai dai ya nemeta ya rasa a ?akin, ya fita nemanta, ya tafi kitchen, ya tarar da ita a tsaye a kitchen, da wayarsa a kunnenta cike da rashin gaskiya.

Babu tsammanni ta ji ya fizgota, ya kwa?a mata mari, har sai da ta fa?i ?asa.

Ya duba call logs ?in sa, ya ga ba a ?aga kiran da ta yi ba, ya kalleta a matu?ar fusace ya ce "Saboda kin ga ina ?aga miki ?afa shi ne zaki tsallake gona da iri, zaki wuce maka?i da rawa? Bari na koma miki ainihin Abdul ?ina, kuma wannan huakan da ki ka yi, dai-dai yake da sake nesanta kanki da iskar 'yanci. Kuma bari na sake gaya miki, babu wani mahaluki da ya isa ya rabani da ke a duniyar nan ko waye shi, idan kin ga dama ki cigaba da ?o?arin lallai sai kin bar gidan nan, zaki ga yadda zan yi da ke"ya fice daga kitchen ?in ya bar a zaune, hannunta ri?e da kuncinta, hancinta har ya fara zubar da jini, saboda azaba.

Ta rasa me ma yakamata tayi, saboda zuwa yanzu zuciyarta ta ?e?ashe, kukan ma ba iya yin sa take yi ba.

Ta ja wuri ta zauna sosai saboda jirin da take ji.

***

Sallama take yi a tsakar gida, ta ce "Na shigo ko na koma?"

Umma da take ?ofar kitchen ta ce "Idonki kenan arfa? Yaushe rabonki da gidan nan?"

"Tuba nake umma, ayyuka ne sun yi mini yawa sosai, amma ayi mini afuwa dan Allah"

Umma ta ce "To Allah ya yi jagora"

"Amin umma, ina sumayya?"

"Tana ?akinta"

Nabila ta nufi ?akin sumayya, ta sameta tana ta aiki a cikin computer, sallamarta kawai ta amsa, ta mayar da hankali ta cigaba da abun da take yi.

"Sumy, dan Allah ki kalleni mana"

Sumayya ta ?ago ta kalleta ta ce "Idan na kalleki mai zai amfana miki, ni da nake munafuka?"

Jiki a sanyaye ta ce "Dan Allah ki yi ha?uri, nayi kuskure abun ne ya bani mamaki ya ?aure mini kai"

Tuni hawaye ya cika idon sumayya ta ce "A yadda muke da ke, ban ta?a tunanin wani zai kawo miki aibuna ki yadda ba, ba tare da kin yi bincike ba, amma kai tsaye ki ka danganta ni da kalmar munafunci, baki san wahalar da nake ta yi dan kare rayuwarki ba"

Nabila ma sai ta saka kuka ta ce "Dan Allah masoyiyya kiyi ha?uri ki yafe mini, ?acin rai ne, kin ga sam baki yi mini bayanin komai ba, na samu labarin an saka ki kina bibiyata, dole na shiga damuwa kuma ke baki gaya mini ba"

Sumayya ta dubeta ta ce "Waye ya gaya miki ana bibiyarki ta hanyata?"

"Ba shi da amfani fa?ar, amma dan Allah waye ya saka ki bibiyeni, ki din ga kai masa rahotona?"

Sumayya ta kalli Nabila da take ta share mata hawaye, Nabila cikin jin kunya da sanyin jiki, take ta ?ara bawa Sumayya ha?uri.

Sumayya ta numfasa ta ce "Honorable indabo ne"

Nabila ta waro ido ta ce "Indabo kuma? Meye ala?ata da shi? Me na yi masa?"

Nan Sumayya ta warware wa Nabila yadda suka yi da Indabo, lokacin da ya ce taje gidansa su yi program.

Hankali a tashe Nabila ta ce "Amma meyasa baki gaya mini ba Sumayya?"

"Ya za ayi na gaya miki? Ya ce muddin ki ka sani, zaki iya rasa ranki, kuma na san dole zaki iya aikata wani abu, da zai sanya su yi miki illa, babban abun da ya bani mamaki bai wuce lokacin da muka yi waya da ke ba, ki ka ce kin ha?u da Viper, ya ?ara rikicewa gaba ?aya, amma na tabattar masa da ?arya ki ke yi, baki ha?u da shi ba, ina tunanin akwai wani abu a tsakanin sa da Viper, dan cewa yayi, zai yi wa Viper tarko da ke, ya kama shi"

Gaban Nabila ya fa?i, gaba ?aya sai kanta ya kulle.

"To tayaya zan zama tarkon da za a kama Viper? Meye ala?ata da shi?"

Sumayya ta ce "Ban sani ba, amma dan Allah ki nutsu, kar ki aikata wani abu da zai saka ya cutar da ke, wallahi rashin imanin mutumin nan ya wuce tunaninki, ke hatta a wurin aikina akwai masu saka mana ido, da kin zo sai su kirani, su ce me muka tattauna, har wayar da nake yi da ke suke bibiya shiyasa nake kiranki da wasu lambobin"

"Na shiga uku, to ni uban me na yi masa? Sumayya da wace lambar suke kiranki?"

"Private number ce, ba sa kirana da lamba" zumbur Nabila ta tashi.

Sumayya ta ce "Ina zaki je?"

Tayi waje da sauri ta ce "Zamu yi qaya kawai" a tsakar gida ta yi wa Umman Sumayya sallama ta fice.

?aramar wayarta ta ?auko, ta kira Viper, ya ?aga a rikice ta ce "Kana nan ne, gani nan zuwa"

"Ke tsaya mana, ki zo ina?"

"In zo wurinka mana ina cikin ru?ani da rashin fahimta"

"Koma menene ki nutsu, ki yi mini bayani ina jinki"

"Ni ba wani bayani da zan yi maka, kawai zan zo gani nan".

Ya ce "Hanya babu kyau, na gaya miki kar ki zo fa"

"To a ina zamu ha?u? Rayuwata tana cikin hatsari, ni kawai kana ina, na shga uku"

Viper da yake zaune ya tashi tsaye ya ce "Malama ki nutusu ki yi mini magana, kina cikin hatsari kamar yaya?"

A fusace ya ce "Na gaya miki hanya babu kyau, ana bibiyarki ko kin manta? Za a fara tracking wuraren da ki ke zuwa yanzu haka. Ki tsaya ki saurare ni.

"To ina jinka"

"Zan tura miki adress ?in da zaki same ni, idan kuma ni in zo shikenan"

Ta ce "A'a kar ka zo"

"Ki samu wuri ki ajiye motarki, zan turo miki adress ?in in da zaki same ni".

"To ka yi sauri" ta cigaba da tafiya a motar, tana waige-waige ko zata ga wani yana bin ta.

Ya turo mata adress ?in da zata same shi, ta ajiye motarta, ta bi adress ?in.

Wurin kamar garden haka yake, ba kowa a wurin, sai manyan bishiyu, ga wurin sanyi mai da?i.

Tana tsaye tana waige-waige, ta ciro wayarta, tana ?o?arin kiransa, kawai ta ganshi unexpected a bayanta, sakin wayar tayi ta hau ihu.

"Menene?"

"Ba tsorata ni ka yi ba, sai ka zo kana wani san?a da na zura da gudu fa, ka daina wannan san?ar".

Ya kalleta ya ce "Idan ban yi san?a ba, ban amsa sunan Viper ba, sai da aji hucina, ko bayan nayi ?arna a ankare da na zo wuri, gani menene?"

Ta ?are masa kallo ta ce "?an beauty"

Ya tsuke fuska ya ce "Neman me ki ke yi mini?"

Cikin damuwa ta ce "Mu zauna, na gaji da tsayuwa"

Suka samu wuri suka zauna, ta ce "Dan Allah Viper meye ha?ina da Indabo? Shi ya saka sumayya take bibiyata. Ta gaya masa yadda suka yi da sumayya.

Ya numfasa ya ce "To me zan yi miki?"

"Ban gane ba, ka gaya mini meyasa Indabo yake bibiyata, me nayi masa?"

Cikin ko in kula ya ce "Ya za ayi in sani?"

"Dan Allah ka gaya mini, kai ma fa ka tambayeni ko na ha?u da shi, me kake ?oye mini ne? Dan Allah ka gaya mini mana"

"Meyasa liti ya rikice ranar farko da ya ganki, ya amince ya kawo ki ma?oyata?"

Ta ce "To ya za ayi in sani, ina tambayarka kana tambayata? Ka gaya mini mana"

Ya ?ago ya tsura mata ido.

"Ka yi magana mana, dan Allah meyasa yake bibiyata, ta ce ya rikice lokacin da ya ji na ce na ha?u da kai" still bai yi magana ba.

"Talk please"

Zuciyarsa ya ji tana harbawa da sauri, ya girgiza kai ya ce "Kamar na ji kin ce mamanki ta rasu ko?"

Tur?une fuska ta yi ta ce "wai ina ta rayuwata, kana tambayata wani abun daban".

"Nan gaba zaki so jin dalilin da ya sa na tambaye ki, bana surutun banza ni"

Kamar za ta yi kuka ta ce "To ni yanzu ya zan yi da wannan indabon?"

Viper ya ce "Ba ruwanki da shi, ni ne dai-dai shi, ki ji da bunkure karki manta, sati biyu kawai na baki ki yi mini aikina"

Ta narke murya ta ce "Nawa zaka bani ne da ka sakani aikin, ka san dai ba lawyer gwamanti ce ni ba"

"Nawa ki ke so?"

"Kai nake so" gabansa ya fa?i, da ya tuna Jauhar sararta ce fa?ar haka.

"Kina wuce gona da iri" yayi maganar yana kallon in da yake facing.

"Daga zuwanka, ka saka DSP ya ha?a ni da Abba, an ce sai na duba samarina na fito da miji, sai ka aureni, tun da duk kai ka janyo koma menene"

"Are you serious? ?an ta'addan zaki aura kina gidan masu kaki?"

Ta ce "Eh mana, ka bani dama na zama yar suganka"

Ya ?ora hannunsa a kan ?irjinsa, ya ce "Ki daina wannan wasan ba na son sa ko ka?an, haryanzu ina jin motsin jauhar a cikin zuciyata. Idan ki na irin wannan maganganun ji nake tamkar na aikata zunubi mai girman gaske, babu wani abu da zan iya ha?awa da soyayyar jauhar a zuciyata, ki kiyaye wannan ki daina wannan wasan, kar ya zama gaske".

"Ba ka son

Please Login or Register in order to submit comment