Reading KARFE A WUTA Chapter 77 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya kira shi a waya.
Embassy ?in Nigeria na Mexico ya kira, domin a bincika masa da maganar da Viper ya kira shi ya gaya masa, idan gaske ce.
Ya ma rasa wa zai kira ya gaya wa maganar, ashe da gaske yana sane da cewa, da shi yake sakawa ayi exchange a duk lokacin da jafar ya aikata laifi, to ko da sanya hannunsa aka kama masa ?a? Amma ya za ayi common ?an daban gari, ya saka a kama masa ?a a ?asashen ?etare?.

Waya ya ?auka ya kira IG, ya din ga masifa, a kan jan ?afar da ake yi, wurin kama Aminu Viper, tare da jadadda idan har ba za su yi abun da yake so ba, zai shiga ya fita a ?auke shi daga garin kano, a canza wani IG. Tun da suka kasa kama mutum ?aya, alhalin yana yawonsa a gari, da aikata abun da yake so.

Yayi ta bashi ha?uri, tare da bashi tabbacin suna iya ?o?arin su, amma komai ya kusa zuwa ?arshe. Ya ajiye wayar yana mamakin ya za ayi, ace senator guda ya tayar da hankalinsa haka a kan ?an daba guda ?aya tal har haka, ya din ga ?ata lokacinsa a kansa.

Yadda indabo ya kira shi, ya tayar masa da hankali, haka shima ya kira Nasir a waya, ya ce masa nan da kwanaki talatin, idan babu improvements a aikin nan, zasu kar?i aikin daga hannunsa su bawa wani, kuma hakan ka iya janyo masa demotion, da rasa wasu damarmaki.

Shi ma ha?urin ya din ga bayarwa, tare da bada tabaccin zai kama Aminu Viper.

***

Abdul da la'asar ya koma gidansa,ya tarar rahama na wanka, ya kwanta ya yi ?ai-?ai a kan gado.
Ta bu?e ?ofa ta fito, ta tarar da shi ta ?ata fuska ta ce "Abdul meye haka?"

Ya bu?e ido ya kalleta.

"Na gyara gadon, kawai ka hau ka ajiye mini shirginka, wata uwar jaka kamar wanzami, kalli takalmi har bedroom ba a wancan ?akin nake ajiye maka ba?

Lumshe idanunsa ya yi, ta ?arasa ta kwashe kayan, ta hau kan gadon ta kwance agogon hannunsa, dan ta san ?arshe ya cire, ya yar da shi a wani wurin, ya zo ya isheta da nema.

Ya kai hannu ya fara shafa bayanta, tayi masa banza, tana cikin ?alle masa labcourt ya cigaba da shafa gashin kanta, sai da ya kai hannunsa kan towel ?in ta, ta buge hannunsa da ?arfi ta ce "Tashi kayi sallar la'asar na san baka yi ba" ya bu?e idonsa ya kalleta.

"Eh kana wani manne ido, ka tashi kayi sallar la'asar"

"Zan yi in anjima, yanzu na gaji"

Ramma ta bu?e baki ta ce "Wace anjiman? Kai ke da anjiman? Waye ya baka guarantee kai wa anjiman? Abdul wallahi wutar duniya ma ba zaka iya da ita ba, balle ta lahira, kai a wuta kala nawa kake so a saka ka ne? Sa?ara fa, wutar marasa yin salla, ita ka ke so ka shiga ko? bayan ta shan giya da neman mata. Ba shiri ya tashi ya ajiye labcourt ?in ya ce "To naji, ai dama ban ce ba zan yi ba, zan yi Astagfirullah in sha Allah ba zan shiga wuta ba, shan giya da neman mata ai kin san na daina" yana maganar ya nufi ban?aki.

Sai da tayi dariya, Abdul ga tsoro ga iskanci, ta tabatta da ya samu kyakkyawar tarbiyya, da isashshen ilimin addini, da bai aikata wasu abubuwan ba.

Taje gaban mudubi ta zauna, mudubin fal da turaruka, da kayan gyaran gashi da na fata, wasu abubuwan duk shi ya koya mata amfani da su, har wasu supplement yake bata tana sha. Ita kanta ta san tayi ?iba ta yi kyau. Tayi ajiyar zuciya ta fara shafa man.

Ya fito ya tayar da salla, ta ce "A kyautata niyya da nustuwa idan ana salla, yadda ka yi ta haka zata zo maka a kabari" ta shirya cikin doguwar riga, yana idar da sallar, ta ?aukko masa azkar ta ce "Ungo, ka san shi yawan ambaton Allah, yana hana mutum aikata alfasha, abu ne mawuyaci kaga wanda yake da kusanci da Allah, yana aikata ?arna kala-kala" haka ta saka shi a gaba, ya idar suka je ya ci abinci.

Gaba ?aya rayuwa da ramma ya sanya ya ji tamkar an canza shi, zuwa wani na daban, haka kurum yake jin wata nutsuwa a tare da shi.

Mussaman saita shi da take yi a kan ibada, da yawan tsoratar da shi a kan yin ta, haka yana saka masa nustuwa da kwanciyar hankali, kuma ya rage aikata tsageranci da rashin ta ido. Hakan ya sanya yake ?ara jin raba shi da ramma, tamkar raba shi da rayuwar sa ne.

System ya kunna ya ce "Your excellency zo ki ga wani abu"

"Wanke-wanke zan yi na ?ora abincin dare"

"Karki damu, zan yi mana takeaway"

"Sai dai idan zaka yi wanke-wanken"

Abdul ya ce "Na ji zan yi"

Ta ?araso ta zauna, ya rungumeta a jikinsa, sannan ya bu?o wani form ya ce "Kin san na menene wannan?"

"No"

"Form ?inki ne na makaranta"

Ta kalleshi ta ce "Makarnta kuma?"

Ya ce "Eh mana, ko ba kya so?"

"Ina so, amma gida zaka mayar da ni?"

"Eh, zaki je ki ga gida, daga nan sai school, boarding ce, mai kyan gaske, saboda sonake ki nutsu ki yi karatu da kyau, yadda babu wanda ya ganki, balle yayi miki gori, da kin gama karatu kuma, ?asar waje zaki tafi jami'a, shiyasa nake tambayar ki me ki ke son zama, na biya komai, na yi rubutu, yadda ko bayan raina ba zaki tozarta ba in sha Allah, ko bana raye karatunki ba zai tsaya ba sai kin kammala in sha Allah"

"Yar uban wace ni da zaka yi mini duk wannan hidimar haka?"

"Ba yar kowa ba ce, amma komai zan yi miki, ba zai kai nauyin laifin da nayi miki ba, ba zai biya budurcinki da na kar?a ta ?arfin tsiya ba, da kuma rashin darajar da naje gidanku nayi ba, ba zan gaji da cigaba da neman afuwar ki ba rahama" ta sunkuyar da kai ta yi shiru, hawaye na zubowa daga idanunta.

Ya saka hannu yana share mata hawayenta ya ce "Ki yi ha?uri, na san na cutar da ke, dan Allah ki yafe mini rahama, soyayyar nan kawai da Allah ya jarabbe ni da ita, ta isheni, baki san tarin ?alubalen da yake a gabana nake ta ?o?arin karewa a waje ba, amma dai ki yi ha?uri dan Allah" a hankali ta zare hannunta daga nasa, ta tashi ta bar falon tana kuka.

***
Nabila kuwa da file ?in Viper ta tafi gida, ta kai shi ?akinta, ta cigaba da duba shi daki-daki, tana picking ?in kurakuran da aka tafka a cikin shari'ar ta sa. Kai da ganin fasalin shari'ar ka san cewa cike take da mugunta da zunzurutun zalunci.

Zafi ne ya isheta, babu wuta, ga solar sai ?ara take yi, kasancewar ranar ba ayi rana sosai ba.

Ta ?aukko system ?in ta, da wayoyinta, ta fita gareji, ta shimfi?a sallaya, da kayan ciye-ciyenta, ta zauna ta cigaba da aikinta.

Nasir ne ya fito yana waya, ba ta san da wa yake yin waya ba, sai dai yanayin yadda ya fito yana wayar, bai san tana wurin ba.

"Eh dan Allah, duk yadda za ayi a samo mana hotunansa, ko guda ?aya ne, nima na da?e da wannan tunanin, ban aiwatar ba, amma a yanzu naga hakan ne kawai mafita, a samo hoton nasa, dan IG ya kira ni ?azu, shi kansa distinguish sai da ya kira ni, ni duk na ru?e, nayi mamakin yadda aka yi mutum ?aya ya gagari hukuma. Duk wata hanya da na bi da zan sameshi, sai ta ku?uce mini.

Shiru ya yi, lokacin da ya lura da ita a wurin a zaune, ya ?ar?are wayar ya saka a aljihunsa.

"Dama har zuwa yanzu baka ta?a ganinsa ba, baka san kamaninsa ba?"

"Eh" ya bata amsa a ta?aice.

"Hmm"

"Ko zaki bani hoton nasa ne?"

"Ni a su wa?"

"Ke a 'yar kankamba mana, samunki da hotonsa ai ba abun mamaki bane ba"

Nabila ta yi murmushi, kawai ta cigaba da aikin da yake gabanta.

****
Mutumin da yake zaune a cikin ofishin sa, ya kalli P.A ?in Indabo ya ce "?an sake duba na da kyau mana malam"

P.A ya ce "Na kalleka"

"Shekaru hu?u rak idan Allah ya bani aron rai, suka rage mini nayi retire, a tarihin aikina, ban ta?a kar?ar cin hanci na aikata son zuciya ba, ban ?i ba wasu lokutan ina kar?a in yi abun da ya dace, duk da hakan ma sa?a doka ne. Ba za a ha?a kai da ni ayi rashin albarka ba, a tozarta harkar shari'a ba, idan na ci amana na tsayawa ?arya a duniya, wa zai tsaya ni a kotun Allah idan zai yi mini hisabi, a cikin kai da uban gidanka, waye zai ?wace ni? Tambayarka nake yi, na ce waye zai ?wace ni? Kotun Allah sa?anin tunanin ?an Adam ce, kuma wallahi dukkanin mu, sai mun tsaya a wannan kotun, kotun da bata bu?atar lauya, ?an sanda balle ka yi tunanin bayar da cin hanci.
Duk da na san bada?alar da ake tafkawa a cikin harkar shari'a, na yi mamakin wasu abubuwan da yarinyar nan ta din ga fa?a, yar cikina ce amma ina sauraron programs ?in ta, kuma ko ka?an ban ji haushin yadda take tsigalewa aikinmu ba, yadda ake amfani da mu, ake aikata abun da ake so. Babu wani rashawa da zaku bani na kar?a, zan yi abun da ya dace ne kawai, idan kuma aka sake zan yi abun da rai zai ?aci. Kai in ta?aice maka doguwar magana zuwa gajera, daga sama aka yi mini magana a kan lallai nayi abun da ya dace a kan shari'ar nan, ba a bu?atar kuskure a ciki, kuma ko ba haka ba, ni sonake na gama aiki na ajiye shi lafiya"

P.A ya jinjina kai ya mi?e tsaye, ya ce "Hakan ma babu laifi, muna godiya sosai" ya juya ya fita daga office ?in.

***
Missed call kusan uku Nabila ta yi wa Viper, amma bai ?aga ba, sai da ranta ya sosu, ta rasa irin wannan mur?a??en hali nasa, gashi ko zata yi fushi da shi, na ?an lokaci ne, ana jimawa ta manta.

Viper kuma fitowar sa kenan daga wanka, ya kalli wayarsa ya ga missed calls ?in ta, har guda uku.

Bai kula ba, ya fara ?o?arin neman kayan da zai saka, wayar Walid ta far ringing.

Walid ya ?aga yayi sallama, ta amsa ta ce "Oga walid barka da wannan lokaci"

"Yauwwa barkanmu barrister, ya aiki ya jama'a"

"Alhamdilillah, ina ta kiran Viper ya ?i ?agawa, wai ni ko wani laifin nayi masa ya tsane har haka ne?" Walid ya kalli Viper, sannan ya ce "Wanka yake yi yanzu ya fito"

Ta ce "Ai dama kai kare shi zaka yi, baka ta?a yadda yayi laifi, ko yayi laifin sai ka kare shi, dama magana nake son mu yi da shi, kuma na ma fasa barshi kawai, sai anjima"

Da sauri Walid ya ce "A'a ba za a bari ba, ko na ha?a ki da shi?"

"Ba zai kulani ba ai na sani, shiru zai yi mini kamar kurma, in dai yana lafiya shikenan sai anjima"

"Kin ga Nabila, tsaya ki ji mana, gaba ?aya ke ce baki fahimci Al'amin ba, ba wula?anta ki yake yi ba"

"Ba wula?anta ni yake yi ba kace? Idan ba wula?anci ba, mai zai sanya ya ce baya so na, wallahi ban ta?a cewa ina son wani ba, ina zaman zamana, ?addara da rashin ya ja ni ya kai ni har in da yake, yayi ta wula?anta ni bai damu da rayuwata ba, amma ko haushi bana ji na?i zuciya, ko kwana biyu nayi ban ji ?uriyarsa ba sai na damu" ta ?arasa maganar cikin damuwa, da alama abun ya na damunta sosai da sosai.

"No, Viper mutumin kirki ne, kuma abun so, in dai ka zauna da shi zaka so shi, saboda yana da halaye masu kyau sosai da sosai, kina kallon muma da muke tare da shi, wasu lokutan haka yake yi mana, amma muna duba halaccinsa a garemu ne, kema baki fahimce shi bane"

"Ba wani ban fahimce shi ba, kalli yadda na shiga sira?in gobarar nan, na zo nayi hatsari, amma sannu kawai ba wani abu ba, ya kasa ce mini"

Walid ya ce "Ki yi ha?uri, halinsa ne a haka, amma zan iya ce miki, bayan iyayenki, akwai wanda ya kai shi shiga damuwar abun da ya faru da ke"

"A hakan? In kusa rasa raina har karo biyu?" Babu tsammani Viper ya fizge wayar hannun Walid, ya kashe ya dire masa ita, ya fice. Walid ya bishi da kallo yana kallon ikon Allah, shi bai rarrasheta ba, kuma ya hana a rarrasheta.

Ko da ya fice daga gidan, wayarsa yake kallo, yana jin tamkar ya kirata, har ya ?aga ya kalli lambarta, sai kuma ya tsaya ya cigaba da kallon lambar, fasawa yai kawai ya mayar da wayar aljihunsa ya yi gaba.

***
"Arfa, wai meyake damunki ne duk kin wani rame kin tsotse" Sumayya ta yi maganar tana ?are mata kallo.

Baba magajiya ta ce "Gara dai ki yi mata, ko ta ji, ta?i gaya mini meyake damunta, sun samu sa?ani da babanta, kuma sun shirya, amma kwanan nan sai ?arewa take yi kamar ku?in guzuri, ko abincin kirki ba ta ci, duk ta zube sai uban nono da take kayansa kamar ya rinjayeta" Sumayya ta ?yal?yale da dariya ta ce "Wallahi kuwa baba magajiya, da 'yar ?ibarta tafi kyau, haba jarumar mu, idan ki ka saka damuwa a ranki, mu wa zai bamu ?warin gwiwar? Muje mu zanta na ji menene ya faru".

Suka tafi ?akin Nabila, Nabila ta zauna a gefen gado, sumayya ma ta zauna ta ce "Gaya mini menene? Naji baba magajiya ta ce kun yi fa?a da Abba, me ki ka yi?"

Ta kalli sumayya ta ce "Sumayya haka soyayya take dama?"

"Soyayya kuma, ita ta hana ki cin abincin ki ke ramewa?"

Ta girgiza kai ta ce "Ba ita ta hana ni cin abinci ba, damuwoyi ne kashi-kashi suka sha mini kai sumayya.
Da fari nifa zuciyata na azalzalata a kan son ganin mahaifina, ina son sanin waye shi, ko yaya yake a bani dama na san shi, ni zan fara bincike ta ?ar?ashin ?asa da kaina"

"A'a Nabila, kar Abba ya sani ransa ya ?aci"

"Sumayya ya zan yi, ni ba na son na mutu ban san babana ba, idan a gidan babana nake, wani abun ba za ayi mini shi ba"

"Naji, zamu dawo kan wannan batun, naji kina maganar soyayya"

Ta numfasa ta ce "?addara ta kaini ta baro sumayya"

Sumayya ta waro ido ta ce "Kamar yaya?"

"Son abun da ba zan samu ba nake yi"

"A'a kar ki ce haka, amma wa ki ke so ?in tukuna ma dai"

Nabila ta tashi, ta saka key, ta bu?e wardrobe ?in ta, ta ?aukko file ta zo ta ajiye a gaban Sumayya.

Sumayya ta ?auka ta fara bubbu?ewa, ta tsaya ta gama dubawa sannan ta kalli Nabila cikin matsananciyar ki?ima da tashin hankali ta ce "Ban gane me ki ke nufi ba haryanzu Nabila"

Nabila ta goge hawayen da ya gangaro mata, ta sunkuyar da kanta ?asa.

Ta daki kafa?ar Nabila ta ce "Kin san in da mutumin nan yake, da gaske ha?uwa ku ka cigaba da yi da shi, har ki fara son ?an daba?"

"?aga murya zaki yi, ki tona mini asiri Sumayya"

"Nabila wannan hauka ne, ga yaya Nasir a cikin gida, yana ta ha?ilo yana fama, ko ?azu an kawo mana sanarwa, yan sanda na cigaba da nemansa ruwa a jallo, duk wanda ya nuna in da yake, ko in da za a same shi, akwai kyauta, kawai ki ke zuwa in da yake, idan aka kama da ke fa? Menene sunanki bayan mun gama fitowa duniya muna ?a?atu da nuna mu masu goyon bayan gaskiya ne?"

"Ban damu da abun da duniya za ta ce ba, ko yadda za a kalleni ba, zan tsaya a bayan gaskiya ne duk rintsi duk wahala. Sumayya zan tsayawa Aminu Viper, kuma kamar yadda ki ka fa?a tabbas ina ha?uwa da Viper, kuma na san in da yake, amma ba zan ta?a bari hukuma ta kama shi ba"

Sumayya ta ce "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, wace lalacewar ce ta same ki har haka Nabila? Kina ya mace, ki ke zuwa wurin ?an daba mashayi, dan ta'adda?"

Ta girgiza kai ta ce "Sumayya ?addara ce, kamar yadda na gaya miki da farko, idan zaki rufa mini asiri ne shikenan, idan kuma tona mini asiri zaki yi, kina da za?in yin wanda ya dace". Ta tashi ta nufi wardrobe ?in ta, ta mayar da file ?in.

"Kai!! Nabila ki canza tunani, ni ba zan bari ki cutar da kanki, ina kallonki ba"

"Ai ba gaya miki na yi, dan ki bani shawara ba, na riga na yanke abun da nake ganin shi ne dai-dai"

Sumayya ta ?auki jakarta ta fice, tana zare idanunta, dan tabattar da ba mafarki take yi ba, dan bata ta?a tsammanin wauta da haukan Nabila ya kai wannan limit ?in ba.

Bayan tafiyarta, Nabila ta duba wayarta, ta ga announcement ?in jami'an tsaro, ta ?auki, jakarta ta saka kayanta, ta faki ido ta fice daga gidan.

Sumayya kamar za ta yi kuka, ta marairaice a waya ta ce "Sir dan Allah ka yi wani abu a kai, rayuwarta zata shiga cikin hatsari da matsala, za ayi mata kallon mutuniyar banza, ?an ta'adda take shirin kasadar karewa"

Yayi murmushi ya ce "Sumayya ?awarki ba ta ji, bar ta ai ?aukaka take nema, mu yi mata fatan nasara"

"A'a sir, dan Allah ba zata iya ba"

Kankarofi ya ce "Haka ta ce miki? She can do it, ni na bayar da file ?in sa aka kai mata, ki ja da baya ki tayata da addu'a, in da ki ka ga ana bu?atar taimakona kuma, ki yi mini magana kar ki yi ?o?arin dakatar da ita, wannan garga?i nake yi miki" ya kashe wayar.

Sumayya ta ce 'Naga ta ta kaina ni sumayya"

***
Suna zazzaune a ?akin, suna ta shan sigari, ya ?aga kai kawai ya ganta a tsaye a ?ofar ?akin, tana kallonsu, ko sallamarta bai ji ba.

Ta rame sosai da sosai, duk da fuskarta kawai ake iya gani, saboda facemask.

Ganin ya tsareta da nasa idanun, ya sanya ta sunkuyar da kai, waiwayawa su Walid suka yi, su ga me yake kallo, suka ga Nabila a tsaye.

Liti ya ce "Su 'yar anace ce da yamaccin nan ashe"

Walid ya ce "Afuwan barrister, kin zo mun cika wurin da haya?i, gashi ke ba kya son haya?i"

Viper ya yin?ura ya tashi, ya ce "Ki tsaya karki shigo, ki zo kina sumewa mutane sai an ta jagwalgwala ki" yayi maganar yana nufota, sai da ya tunkarota sosai, sannan ta lura rigar jikinsa sunansa ne a jiki, an rubuta Viper, da zanen kan macijiya a jiki ta fito da harshenta.

Ya fito ya tsaya, yayi crossing lega ?in sa, irin ina saurarenki.

Banza tayi masa ita ma, suka cigaba da tsayuwa, sai dai tsayuwar bata damunsa, ita kuwa ta fara gajiya, yana zu?ar sigarinsa, yana fesarwa a gefe.

Hannunsa ta kalla ta zare sauran sigarin ta yar a ?asa, ya kalleta amma ta ha?e rai.

"Ina jinki ya aka yi?"

"Alhaji mu'azzam da ku ka ha?u, dama ka san shi ne?"

"Haka ya ce miki?"

"A'a, tambayarka kawai nake"

"Ki bar maganar sa kawai"

"Saboda me?"

Ya ce "Saboda haka na ce"

"Nifa ina tsoron sai na je gaban kotu, in tarar da wasu abubuwa da ban san da su ba, na rasa yadda zan ?ullowa lamarin, ka gaya mini shi menene ala?arka da shi?".

A hasale ya ce "Na ce ki bar maganarsa ko? Na san shi, amma sanin waye shi ?in ba shi da wani amfani".

"Shhhh ka daina yi mini shouting, ka yi shiru ka saurare ni, aikina nake yi malam" tayi maganar tana kallon ?wayar idon Viper.

Ayshercool
08081012143
???500 ne via 0009450228
Aisha Adam jaiz bank sai shaidar biya ta 08081012143
Wanda za su jira document 1K ne.

90009343
'Yan Nijar ku turo katin airtel na 300fcfa

Arewabooks ayshercool7724


Cigaba yayi da kallonta, ita kuma ta kasa sake ?aga idonta ta kalleshi.

Yanayinta ya nuna sosai akwai damuwa a tare da ita.

"Kin fasa cewar ba zaki tsaya mini ?in ba kenan?"

Ta jinjina masa kai ta ce "Eh, idan ma na fasa, zuciyata ba zata nutsu ba, al?awari ne da nayi, yakamata na cika, ko ba dan kowa ba, dan wadda aka kashe ba da hakkinta ba" tayi maganar ba tare da ta kalleshi ba.

Ya jinjina kai, a hankali ya furta "Ina zuwa"

Ya koma cikin gidan, tana tsaye ta bi ?ofar da kallo, ya fito ?auke da jaka a hannunsa, ya ce "Muje" ba tare da ta san in da zasu ba, ta bishi. Sai da suka yi nesa ka?an da gidan, sannan ya ja ya tsaya ita ma ta tsaya.

Ya samu wuri ya zauna, yayi mata nuni, ita ma ta zauna, ta sauke tata jakar daga bayanta, hannunta ?aya an na?a mata bandeji, in da ta samu gocewar ?ashin, sai dai hannun rigarta ya rufe wurin.

Ta ciro system ?in ta, ta ajiye ta ajiye wayarta.

Ya zuba mata ido, bai yi magana ba, sai da ta ?an ?ago ta ce "Wace shaidar da wace shaidar ce da kai, and dan Allah kar ka ?oye mini komai, saboda kar sai mun je kotu, wani abu da ban san da shi ba, ya taso daga baya".

"Me ki ke son sani?"

"Shaidunka, da ka ce kana da su"

Ya ?an lumshe idanunsa, sannan ya bu?e ya ce "Madaki, duk na yi masa illa, sai kuma babban yaronsa lakwari, duk suna wurina"

"Garkuwa kayi da su kenan?"

"Kusan hakan"

"Laifi ne fa ka aikata yin hakan"

Ya tari numfashinta ya ce "In sake su kenan?"

Ta ?aga idonta, amma taga kallonta yake yi.

Jikinta ya ?ara sanyi, maimakon ta mayar da hankali a kan abun da take yi, sai hannunta ma ya hau rawa, wata irin ?aunarsa ta din ga fizgarta, ji tayi tamkar ta ?urawa kanta zagi.

Ya ?an matsa kusa da ita, yana kallon fuskar system ?in ta. Ta takure jikinta, ?amshin turaren sa da warin sigari suka cika mata hanci.

Murya na rawa ta ce "Viper"

"Mmm"

"Ka sha sigari ko?" Yayi shiru bai bata amsa ba.

"Kar ka bari lafiyarka ta ta?u bamu gama shari'ar nan ba, kuma kaga ya fara ta?a maka internal organs, an ce hantarka ta kumbura"

Yayi shiru bai yi magana ba, sai kallonta kawai da yake yi.

"Akwai abubuwa da yakamata ka gaya mini, amma kamar kana ?oye mini, yakamata idan kana ?oye mini ka gaya mini, kar wani abu ya bamu matsala daga baya"

Har ta fitar da ran zai yi magana ya ce "Kamar me?"

"Suwaye suke goge laifukan ka idan ka yi? Ranar da muka je gidanka, ya aka yi ka gane jami'an tsaro a fararen kaya, har muka tsere musu? Wannan rigar da ka yaga a asibiti ta mecece? Kuma me kake yi da wayata da kake connecting?"

Viper ya yi gyaran murya ya ce "Wasu tambayoyin ba su da ala?a da abun da yake gabanmu, amma na gane jami'in tsaro a farin kaya, saboda ni tsohon mai laifi ne, ba lokacin na fara aikata laifi ba, dan haka duk wani nu?u-nu?un jami'in tsaro sai na gano shi. Rigar da ki ke magana a kai, bata da ala?a da abun da zaki yi a court. Wayarki kuma ina connecting ina duba wasu location, da tura sa?onni. Mai goge laifukana kuma ban sani ba. Sai kuma me?"

Nabila ta ce "To shikenan, nan da kwanaki biyu zaka ji ni in Sha Allah, zan har ha?a abun da nake bu?ata, saboda yayana ya sakani a gaba da yawa"

"Good luck" ya fa?a a takaice, tamkar ta kurma ihu, ko sannu ya jiki bai iya yi mata ba, dan takaici ta tattare system ?in ta, ta yin?ura ta tashi ta ce "Sai anjima" ya jinjina kai.

Jiki a sanyaye take takawa, kamar mara karsashi, ya waiwaya yana kallonta, yadda take ?aga hannunta tana saukewa, ya tabbatar masa da kuka take yi. Sai da yaji zuciyarsa ta motsa, shi gaba ?aya tausayinta ma yake ji.

Tana tafe a titi, barrister Habib ya kirata, ta ?aga ya ce "Nabila kina ina ne?"

"Meyafaru?"

"Wai yayanki yaje ?aukar ki, an ce masa mun fita, ya kira ni, wai muna ina?"

Guntun tsaki ta ja, ta ce "Rabu da shi dan Allah"

"A'a kamar yaya na rabu da shi? Kina ina ne, ni ya addabe ni"

"Wani wuri naje, ina kan hanyata ta komawa gida, ina son ma ganinka urgent, amma sai Allah ya kaimu gobe"

Ya ce "To Allah ya kaimu"

Ta amsa da "Amin"

***
Naja'atu Bunkure ta dubi Indabo ta ce

Please Login or Register in order to submit comment