Reading KARFE A WUTA Chapter 86 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Sai da na kusa rasa hankalina da tunanina, saboda tsananin tashin hankali da ru?ewa, har sai da na zata ko matsalar ?wa?walwa na samu, saboda damuwar kisan gillan da aka yi wa jauhar.
A lokacin ban yi ?asa a gwiwa ba, na tashi yin bincike a kanta, har zuwa wannan lokaci, nake bibiyarku daga kai har ita. Muddin ba butulci zaka yi mini ba, na taimakeka Aminu, ko nayi maka laifi a wani wurin, wani wurin na taimake ka". Sai da ya gama tsaf Viper ya ce "Na nemi taimakonka ne? Wane irin taimako ne kayi mini kana yawo da hankalina, ka yi mini shi a munafunce? Ka din ga wasa da hankalina kana ?oye kanka? Madalla da abin da ka yi, amma ina bu?atar abin da ka ke yi ya tsaya a iya nan, Nabila da abin da ya shafi rayuwar ta hurumina ne, daga nan idan ta farfa?o zan bar wurin nan da ita"

"Waye ya baka wannan damar? A ?ar?ashin kulawata take ba taka ba, naje na samu mahaifinta ma, na sanar masa da hakan, sai dai kai ka bar nan wurin, amma Nabila na tare da mu"

"Don't cross the boundaries! Ban ?i ayi mutuwar kasko ba, ba na wasa da duk abin da ya shafi marigayyiya, a kanta ba abin da ba zan aikata ba, idan da na koma na ?auki wannan rigar ce, zan cireta na ajiye, kar ka sake kusanto in da nake, bana bu?atar taimakonka"

Kankarofi ya ce "Jauhar ce mallakinka, Wannan kuma Nabila ce"

"Na gaya maka Nabila ta haramta ga kowa muddin ina ganin fuskar matata a jikinta" Viper ya yi maganar yana zazzaro ido cikin matsanancin kishi, jijiyoyin kansa suka ?a??aga.

Cikin hanzari ?an mama ya fito, ya shiga tsakanin Kankarofi da Viper, barrister Habib gefe ya koma, dan gaba ?aya Viper tsoro yake bashi.

Hankalin sojojin wurin ne, ya fara dawowa kansu, suka tattaso suka nufo su, Viper sai huci yake yi.

"Easy oga, ka fahimci al'amarin nan dan Allah, wallahi Yalla?ai mai ?aunarka ne, ba ya nufin cutar da kai, ba ?aramin taimako ya yi maka b.....

"Shut up! Da na ?yaleka ban ce maka komai ba, ka ke gaya mini maganar banza, ka kuma yi mini magana, sai na tatsule ka a wurin nan, menene na cigaba da bibiyar rayuwata dan na auri wadda ya so ya aura, menene amfanin haka?"

"Wadda ake yi domin ta, ta bar duniya, ba shi da wata mummunar manufa a kanka, ka fahimci hakan oga dan Allah"

Ya nuna ?an mama da yatsansa, alamar kashedi.

"Viper wai me ka ke yi haka ne? Oga ne fa da kansa a wurin nan, ka ke ?aga masa murya ka ke fa?ar maganganu"

Viper ya ce "Bana bu?atar sa a rayuwata, ya bar wurin nan, ko kuma ni yanzu na bari"

?an mama ya koma wurin kankarofi ya ce "Dan girman Allah sir kayi ha?uri, wallahi Viper yana da kirki, kar ka ce zaka cire hannunka, tsabar kishi ne kawai, kar ka ce sai ka na son Nabila sai ka aureta"

Kankarofi ya ce "Yaron ba shi da kunya, ba kuma shi da ?a'a, ban yi zaton haka daga gare shi ba"

?an mama ya ce "Wallahi Viper yana da ?a'a da biyayya, kawai ka san soyyaya ba ta da gwani ko jarumi, na san dai yana da taurin kai da azabar fushi, amma wallahi duk fa?ansa yana da kirki, kar ka manta, da shi nake kwana nake tashi muke rayuwa. Amma ba haka yake ba, dan Allah kar ka cire hannunka a kansa, zan yi maka proving abin da na gaya maka, ai na san maganinsa, zai nustu bari ya gama hargowar".

Ana ta fama da Viper, ya ce sai ya bar Asibitin da Nabila.

Liti ne ya ?aga wayar Walid, ganin kiran ?an mama ne ya ce "Kai dan ubanka, ina ka shiga kwana biyu baka nan, baka sanar mana ina ka tafi ba, Viper duk ya addabe mu, ko wani rashin gaskiya ka fara ne?"

?an mama ya ce "A'a oga liti, akwai matsala ne, ina oga walid?"

"Yana ban?aki matsalar me? Tsokana ka yi ko me? Kana ina ne?"

"Ina cikin barikin sojoji"

Liti ya ce "Iyee, ba wurin yan sanda ba sojoji? ?an mama me da me ka ke sha ne? Sojoji fa ka ce? Me ka yi musu?"

"Dan Allah ku zo, da kai da Oga walid, ku ka?ai ne zaku yi solving case ?in nan"

Liti ya ce "Kai, duk iskancina, ban ta?a tsokanar wannan mutanen ba, da babu Allah a ransu, haka kurum su tumurmusa ni a banza, su sauya mini kamanni, Allah ya ?watoka, bari Walid ya fito ko zai iya ?watoka, dama ya fi ni imani da tausayi, ko shi ko Viper, dama shi ya saba da jure wahala. Dukanka suka yi ko kuma karairayaka suka yi?"

?an mama ya ce "Ba ?aya, matsala aka samu ne"

"To Allah ya yi maka maganinta, ya tsayar iya kanka, Allah ya sa idan su Walid ?in sun zo su ganeka, ba su sauya maka fasali ba, su mayar da kai gorilla ko wata halittar ba"

Walid ya ?araso, ya kar?i wayar daga hannun liti cikin tashin hankali ya ce "?an mama, kana ina ne? Meyafaru meya kai ka wurin sojoji ne?"

"Oga walid, lafiya ?alau fa, wani case ake yi, ina tare da oga Viper, ku yi sauri ku zo dan Allah, kar ya aikata wata ?arnar, ku ka?ai ne zaku iya shawo kansa"

Walid ya ce "Kai da Viper kuma a cikin barikin Sojoji? Garin yaya?"

Liti ya mi?e ya ce "Viper kuma? Ka gani ko? Viper wasu lokutan baya lissafi ko shawara, kawai ya ?ibi jiki ya tafi, Allah ka?ai ya san me ?an maman yayi musu, ya janyo an kama shi"

Walid ya katse wayar ya ce "Muje dai mu ji menene, ka san babu yadda za ayi Viper ya bar ?an mama ko wa ya tsokana kuwa"

Liti ya ce "Ai da yake ba mutunci ne da shi ba, kwana nawa muna nemansa, da ya tafka tsiyarsa kai tsaye kuma sai ya nemi Viper ba mu ba" haka suka tafi, liti yana ta masifa.

Al'amin na ?akin da Nabila take, shika?ai ya kasa ya tsare, ya zuba mata ido, tana ta bacci. Tun da aka yi wannan dambarwar ya?i fita, gani yake yana matsawa zasu ?auke Nabila.

Ji yayi an bu?e ?ofa, ya waiwaya.

Wasu manyan sojoji suka shigo, ?aya ya ce "Viper, taso muje ko"

"Muje ina? Am not going anywhere"

"Meyasa ka ke haka ne, kar ka saka mu yi fa?a da kai fa"

Viper ya ce "Wace azaba ce ni ba a gana mini ba, ba zan je ko ina ba, ban san me kuka ha?a kai da mutumin nan, ku yi mana ba" da ?yar suka lalla?a shi, suka fita zuwa wani sashe na barrack ?in.

Suna shiga wurin, ya ga liti da Walid, sai dai still ya ga kankarofi, take ransa ya kuma ?aci, yana mamakin taurin kai da rashin zuciya irin na kankarofi.

"Me kuma zan yi maka? Me kake so kuma yanzu?"

Walid ya mi?e ya ce "Mai zamani"

Viper ya ?aga masa hannu ya ce "Mai laya"

Walid ya ?arasa gaban Viper ya ce "Mai zamani, easy mana cool your temper" yayi maganar yana ?an dukan ?irjin Viper.

"Meyasa yake bibiyata, dan na auri matar da ya so aura?" Yayi maganar cikin damuwa.

"Ta rasu fa yake bibiyarka, da tana raye ya bibiyeka ne?" Viper ya yi shiru.

Walid ya ce "Kishi ne yake damunka, an fara yi mana bayani, bawan Allah nan, ya taimaki rayuwar ka ta fuskoki daban-daban, ka nutsu ka kwantar da hankalinka, mu taimaki rayuwar Nabila. Ba zai yiwu ta cigaba da zama a nan ba, tun da Asibiti ne, kayi ha?uri a samu kauwammanen wuri a ajiye ta, idan ya so kaima ya zamana kana tare da ita. Wancan abokin aikinta ne, kuna bu?atar ?awarta 'yar jarida, da sauran su, kai a tunaninka effort ?in ta kawai ya isa ya sanya ku yi Wannan nasarar? A Nigeria fa muke, dole sai da wa ka sani wa ya sanka, ka danne koma me kake ji, mu fuskanci gaskiya.
Butulci da manta alkhairi ba halinka bane mutumina, ka ajiye kishi a gefe, muna bu?atar a bi mana hakkin jauhar, muna bu?atar yi wa Nabila tukuici da abu mai muhimmanci, idan ka ?ata aikin nan saboda taurin kai, ba ka yi musu adalci ba, ciki har da ita da mu kanmu da muke tare da kai" Viper ya ja jiki ya zauna a hankali.

Liti ya ce "?an mama duk zaman da muka yi da kai, ashe aikin munafunci ka ke yi, amma kuwa ka yi asara dan wannan ba aikin yi bane ba, kuma saboda tsabar ?warewa, ko da wasa baka ta?a gaya mana ba. Ni dama na da?e ina zargin baka da gaskiya"

****
Mi?a tayi sosai tana addu'a, ta ji kamar gadon da take kai, ya sha bamban da wanda ta kwanta a kai, ta tashi zaune a hankali, ta ganta a cikin wani katafaren bedroom, bisa wani ?aton gado.
Tayi tsuru da ido, tana tunanin ko mutuwa tayi.

Wata mata ce tayi sallama, ta ce "Kin tashi? Ga ban?aki nan idan zaki yi alwala ki yi wanka ki rama sallolin da ake binki".

Nabila ta ce "Ina ne nan baiwar Allah? Ko mutuwa nayi ne?"

Matar ta ce "A'a, wanda suka kawo ki, zasu zo su yi miki bayani, ga kaya nan ko zaki canza".

Ta tashi a hankali tana addu'a, ta shiga ban?akin, ta yi wanka, ta yi alwala, ta fito ta din ga salloli, daga iya abin da ta iya tunawa, ga wata irin yunwa tana ji, gaba ?aya ta kasa tantance meyake faruwa gaba ?aya.

Matar ta dawo, ta kawo mata abinci, amma Nabila ba ta ta?a ba, ta takure a gefe.

Viper ne ya shigo, ta ?ago kai ta ?ura masa ido, har ya ?arasa gabanta, ya zauna ya ce "Sannu, ya jikin?"

Ta ?an yi shiru sannan ta ce "Kamar nayi kuskuren yin?urin taimaka wa rayuwarka, kana ?o?arin rusa tawa, ta hanyar ganin ka haukata ni, me nayi maka haka? Kuma ina ka kawo ni nan?"

"Ba ki yi kuskure ba, domin kuwa kin yi sara ne a kan ga?a, kuma zaki alfahari da ?addarar da ta ha?a ni da ke"

"In yi alfahari bayan na haukace ko?"

Viper ya girgiza kai ya ce "Ba zaki haukace ba, tambayoyin da nayi miki, haryanzu nima ina bu?atar samun amsarki, sai dai bani da tabbacin samun amsarsu duka.
Amma bari mu gani, ko a cikin abin da zan gaya miki zamu gano bakin zaren, rayuwata kamar ?wallon ?afa take, daga wannan ?afa zuwa wancan, daga wannan tudu zuwa wancan rami.
A ha?i?anin gaskiya, ban yi shekaru biyar a gidan yari ba". Nabila ta waro ido tana kallonsa.

"Nayi zaman gidan yari, cikin tsananin razani, cikin matsananciyar damuwa da ?uncin zuciya, tare da fatan Allah ya sa da an mayar da ni kotu, a yanke mini hukuncin kisa, na huta, amma ranar da aka saka a cigaba da shari'ar ta wuce ba a cigaba ba.
Azaba da wahalar da nake sha a gidan, bai ?aga mini hankali ba, kamar yadda halin da nake ciki, bai hana wasu din ga ?o?arin nemana da mummunar ?abi'a ta neman maza ba, ciki har da ma'aikatan wurin.
Abin da su madaki suka yi amfani da shi suka sha?a mini, ya cigaba da affecting ?ina.
Azaba da takura, ya sa na zame musu mahaukaci, na danne wanda suke cewa sarkin gida, na kusa janyo ma?ogwaronsa waje, nayi masa dukan mutuwa, saboda sun zata dolo ne ni, duk da sun san labarin waye ni, prsion ?in ta sha banban da wadda ake kaini.
Suka ajiyeni a wani wuri, suka din ga gana mini azaba, wai nayi yin?urin yin kisan kai, ba wanda ya duba abin da ya neme ni da shi. Aka ajiyeni, babu wanka, babu wanki, babu ci babu sha, sai azabar duka. Wurin ga ?azanta da rashin tsabta, a haka kuma a kan fito da ni, ace za a saka ni aikin wahala.
A halin da nake ciki, na tsinci wani ?an ?arfe, da zai iya zama makami, na farwa wani, dan fuskar madaki na gani, sai da aka ?wace shi da kyar, na huda masa wuya, sannan naga ashe ba shi bane ba, ?wa?walwa ta ce ta fara samun matsala, banda kururuwar da nake yi wasu lokutan, ina kiran matata da ?a na, tare da alwashin kashe madaki. Aka rabani da sauran fursunoni, aka ce na haukace.
Watarana, cikin dare ina kwance, na san idona biyu, amma bakomai nake ganewa ba, fatana na farka daga baccin da nake yi, na ganni tare da matata.
Kawai wani mutum ya saka mukulli ya bu?e in da nake, ya fara lalubena, duk a galabaice nake, kwana uku ba abin da aka bani na ci, sai na tsaya naga me zai yi mini, kar nayi masa wani abun, na je ?wa?walwata ce take gaya mini shirme, kamar yadda ta saba. Sai na ji bai nufi yi mini lalata ba, kawai ya soka mini wani abu, kamar allura a cinyata, ya fara zuba mini wani abu mai tsananin zafi a jikina, ruwan allurar na shiga, ina jin kamar ana fizgar naman jikina, a take na kurma ihu, na tashi na sha?e shi, ina dukansa, ina cewa shi ya kashe jauhar, sai na kashe shi. Ina dukansa jikina yana ?ara sanyi, kamar ana zare mini laka.
Aka zo aka raba ni da shi, nayi masa jina-jina, ni kuma na fa?i a wurin, basu bi ta kaina ba, suka fice da wancan. Ina kwance na ji wani abu mai sanyi na bin hancina, a ta?aice dai, kasheni yayi yin?urin yi mutumin.
Washegari ina kwance kamar gawa, ina jin duk abin da ake yi, amma ba zan iya motsi ko magana ba, aka ?auke ni, aka ce za a kai ni Asibiti, ayi mini magani, ashe wasa farin girki, maimakon a kaini asibiti, sai aka yi wani wurin da ni.......

Ayshercool
08081012143
???500 ne via 0009450228
Aisha Adam jaiz bank sai shaidar biya ta 08081012143
Wanda za su jira document 1K ne.

90009343
'Yan Nijar ku turo katin airtel na 300fcfa



*BRIGHT PENS SECOND BATCH*

Ku kasance da littatafan bright pens, second batch.
*?ARFE A WUTA (AYSHERCOOL)*
*MUTALLAB (NIMCYLUV)*
HADARIN GABAS (NAZEEFA NASHE)*
*ZAYTOON (ZEE KUMURYA)*





"Bana iya gane ina ake, saboda a matu?ar galabaice nake, amma naji a jikina, yakamata ace idan asibiti ne ya ci ace an je, duk da bana sanya ran zan rayu, a maganar da mutanen motar suke yi, jini nake ta fitarwa ta hancinca, ga azabar yunwa da datti, na gidan yari, tufafina tamkar mahaukaci, dan a mazaunin da aka ajiyeni kenan.
Aka yi parking ?in motar, aka canza mini wata, wadda nake kyautata zaton ambulance ce, dan a ciki aka toshe hancina da bandeji, saboda jinin da nake zubarwa, aka saka mini ruwa, muka cigaba da tafiya. Tun ina jin maganganun da ake yi a motar, tafiya ta?i ci ta?i cinyewa, har na daina gane komai, na bu?e ido na ganni a wani wuri, a kan gadon asibiti, an tu?e kayan jikina, sai gajeren wando, na tashi a gigice cikin matsananciyar ki?ima, ina ihu saboda ban san meyafaru da ni ba, na farka ina zaton zan ga madaki da jauhar, ina hana shi cutar da ita, wani ?angaren ina tunanin ko ina prison ne, wani yayi galaba a kaina. Sai dai na ji ni a ?aure da ankwa dukka hannayena, na din ga ihu saboda yadda naman jikina yake yi mini wani irin azababben zugi, kamar ba zan rayu ba.
Wasu mutane da ban san suwaye ba, suka zo kaina, da allurai suka yi mini, ?aya daga cikin su ya ce "A cigaba da kula da shi mu gani, will he survive the poison, duk yadda zaku yi, ku yi ?o?arin ceton rayuwar sa" haka na sake fita hayyacina na farka, sai dai a wannan karon, ban ji wannan ra?a?in ba.
Aka cire mini ankwa, aka tashe ni zaune, aka kawo mini abinci, kamar mayunwacin kare, haka na dirarwa abincin nan, kamar zan ha?a da kwanon saboda yunwa, ina ci ina jin kamar ana yayyanaka kayan cikina da wu?a, amma azabar yunwar da nake ji, ya sanya na?i daina ci, sai dai ban gama ci ba na din ga amai, ha?e da jini, wai duk cikin side effect ?in allura da aka yi mini ne, kashe ni aka so ayi.
Ba a sake bani abinci ba, sai ?arin ruwa da allurai, mutanen wurin ba kowa ke jin hausa ba, ni kuma bana magana, suna bani damar yin salla, aka fara koya mini cin abinci.
Ba wanda na tambaya dalilin kai ni wurin nan, kuma babu wanda yayi mini bayani, a haka har na shafe wata guda cif.
Duk yadda suka so nayi magana, bana yi, sai dai wasu lokutan ina rasa tunanina, na din ga ganin madaki da jauhar a zahiri, na din ga yin?urin sha?e duk wanda yake kusa da ni. Sai da na ?an samu nutsuwa, aka aske mini gemuna da sumar kaina gaba ?aya, aka kuma saka mini ankwa, aka rufe mini ido, aka sakani a mota, aka bar wurin da ni.
Wani wurin aka sake kai ni, mu hu?u ne a wurin, kowa da wurin da ake ajiye shi tamkar ceil. Na fauskanci nika?ai ne musulmi babu bahaushe, sai ?abilu, kullum bayan nayi sallar asuba, da sassafe haka za a kaimu wani wuri, ana bamu training na azabatarwa, wanda ka iya zama ajalin mutum.
Idan muka gama, zamu saka wasu riguna, masu tambarin dragon, za a kaimu wani wuri, in da ake bamu darasi, malamanmu turawa ne, class ?in mu hu?un nan ne, kowa da computer sa, ayi mana darasi ta online. Wa?anda suke kula da mu, wasu irin zaratan ?artin sojoji ne, sun kai su goma sha biyu, a kan mu hu?u kawai.
Azaba ta ishe ni, ban ga alamar za a mayar da ni gida ba, na gaji, gaba ?aya na rasa ina rayuwata ta dosa, bani da wani burin da ya wuce na mutu na huta. Za a bamu abinci mai kyau, a bamu abin sha mai kyau, amma azabar da ake mana ta ishe ni. Wataran ana tsaka da bamu training, na fizgi bindigar wani, nayi yin?urin kashe kaina, suka ri?e ni, aka ?auke ni aka kai ni wani ?aki, da ban zaci zan fito da rai ba. Sai da na kwana bakwai a ?akin, ko class bana zuwa. Ranar na takwas, ogansu ya zo ya same ni, yake tambayata meye matsalata na yi yin?urin kashe kaina.
Na ce masa su mayar da ni garinmu, ina son ganin matata.
Ya ce mini muddin ina son komawa gida, sai na basu ha?in kai, na yi wa ?asata aiki, sun san ni yaron dodo ne, kuma akwai amfanin da zan yi musu, dan haka dole na mayar da hankali a kan training da kuma karatun da nake yi, ku?i aka ware masu nauyi, saboda mu yi wannan karatun.
Na ce ni ba zan yi ba, su kasheni kawai su daina wahalar da rayuwata.
Ya ce ba zasu kashe ni ba, in yi abin da suka umarceni, idan ina son na ga matata. Sai na tambaye shi, matata na raye? Ya ce tana raye, zan ganta idan na daina taurin kai, nayi abin da ake so. Kuma ko ina so ko bana so, ubangidana ne ya nema mini wannan aikin, tun kan ya mutu, dan haka sai dai na mutu a process ?in, tun da na san sirruka masu muhimmanci da zasu taimaki ?asa. Na din ga tunanin, wane irin laifi na yi wa dodo, zai za?a mini wannan azabar, sai dai tsananin ?oki, da da?in bakin zan ga matata, ya sanya na saduda, gashi suka saka mini ido sosai da sosai, saboda suna i?irarin bani da lafiyar ?wa?walwa, kuma bana ji.
Wata makaranta muke yi a russia, ilimin na'ura mai ?wa?walwa kawai ake bamu, duk da na san abubuwa da yawa ni, ta online muke makarantar, a training ?in nan aka koya mana duk wani nau'i na ha?awa da wargaza bindiga, ilimin makamai, le?en asiri, da duk wani nau'i na abin da ya shafi harkar tsaro.
Suka ce mini ?wazona, shi zai bayar da damar komawata garinmu, har naga matata, na ro?e su ko a waya, a ha?ani da matata tun da sun ce tana raye, suka ce ba zasu ha?amu ba, zan ?ata musu aiki.
Na zage damtse, lokutan jarrabawa, ina cikin overollers, ina tashi da points masu kyau, na fara sabawa da wahalar training, jikina duk ya mur?e, sai dai babbar matsalata bana cikakken bacci, bana iya bacci, da na rufe idona, zan ganni a falo, tare da jauhar madaki zai kasheta, gaba ?aya sai na tubure musu, na hau ihu. Ko abincin da nake ci, bana cin sa ta da?in rai, saboda damuwa da tunani. Abokan karatuna a kan basu damar shan giya, har mata a kan kawo musu, amma ni duk ba wannan a gabana.
Tun ina lissafi da sanya ran ?arewar wannan wahala, naga babu rana babu wata, na zauna nayi tunani, babu yadda za ayi, jauhar na raye a gurfanar da ni a gaban kotu, a tuhume ni da laifin kisan kai, naga kawai raina mini hankali suke yi, sai kuma wata zuciyar ta ce mini ai mafarki nake yi, sai dai na rasa wanne ne mafarkin wanne ne zahirin?.
A haka na shafe shekaru a wurin nan, ban ta?a barin kewayen in da muke ba, na rayu da matsanancin ?unci da damuwa a zuciyata, wasu lokutan sai an yi mini allurar bacci nake iyawa.
A haka muka kammala karatu, sauran ukun aka ce, za ayi posting ?in su, in da ake son su gabatar da ayyukansu, ni kuma sai an yi settling issue ?ina. Mun zama sojojin le?en asiri.
Ni dai jinsu kawai na din ga yi, sauran suka din ga murna, aka shirya mana walima, sauran duk sun saba da su, ni duk yadda aka so ja na a jiki, a yi raha da ni, a saba ban yadda ba, dan ni kaina na san rabi mai hankali rabi mahaukaci nake. Abokan karatuna kuwa, basa shiga harkata, dan duk lokacin da ?wa?walwa ta ta haska mini fuskar madaki, a jikin ?aya, sai na kusa kashe shi, dan duk da training ?in da aka bamu, na fi su ?arfi nesa ba kusa ba, kuma ba addinmu ?aya ba, ba ?abilarmu ?aya ba.
Sai da na ji haushin dodo, duk da baya raye, na ji ya sakani a masifa, duk da ina fatan sanya indabo, biyan bashin abin da ya aikata ciki har da kisan dodo.
Ana gobe za a mayar da ni kano, ina ta murna zan koma naga jauhar, naga ?ana, dan na san a lokacin ya yi wayo, ban san meyafaru ba, ko me suka yi mini ba, sai farkawa nayi, na ganni a prison. Hakan ya ?ara burkita ?wa?walwa ta, na fara tunanin wani mafarkin na kuma yi, na din ga kiran sunayen shugabbaninmu da suka bamu training, ina cewa su zo su cika mini al?awarin da suka yi mini, su ha?a ni da jauhar ?ina da ?ana kamar yadda suka yi mini al?awari, gashi ko za a kashe ni, ban san sunan garin da aka kaini ba.
Gandirobobi, suka yi mini dukan tsiya, wai na cika musu kunne da hauka, matar da na kashe da hannuna, bayan na sha na bugu, na amsa hakan a kotu, yanzu kuma na zo na ishe su da shirme. Suka yi mini dukan tsiya, amma na kasa daina kururuwar kiran sunaye da magiyar su ha?ani da jauhar, gaba ?aya na zama mahaukaci, ni kaina a lokacin na yadda ni mahaukaci ne. Wasu lokutan idan na bu?e jikina, ina ganin tabon raunuka da wahalar da na sha a wancan garin, amma fafur aka nuna hauka nake yi, da sambatun ?arya.
Tun da suka tabattar mini ni na kashe jauhar, na ?ara rasa tunanina, damuwa da tashin hankali suka koma sabbi fil.
Kusan watanni uku, cikin dare ina kwance, dama ?akina daban, aka tashe ni aka ce na fito, na fita na bi bayan wanda suka kira ni, aka fitar da ni wajen gate, wai an kar?i court order na tafi.
Na tsaya ina kallonsu, ina mamakin wane mafarkin kuma na sake shigowa, suka rufe gate ?in prsion ?in, suka bar ni a tsaye.
Zuciyata ta raya mini maza kafin na farka daga baccin, na je na ga jauhar, ko zan farka dai na ganta.
Na fara tafiya a duhun nan, har garin Allah ya waye. rana ta ?aga, na isa unguwar mu, ban manta hanya ba. Sai dai Abbu ya tabattar mini da jauhar ta mutu, ni na kasheta, na tafi na

Please Login or Register in order to submit comment