Reading KARFE A WUTA Chapter 21 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

wanda ya cire, da wanda ta kwashe na wanki ?azu, ta fito ta ji?a su zata wanke.

Ta koma ta sake sharo falon, sai dai ta ga leda a in da Ya tashi, ta ?auki ledar, ta ta?a ta bu?e, tana tunanin ko ita ta ajiye wani abun, amma ta ga wani abu kamar ganye a ciki, ta sinsuna ta kasa gane ko menene, kuma a iya tunanin ta, ba ta ajiye ba. Ta samu wani wurin ta ajiye, ta cigaba da aikinta.

Sallama aka din ga ranga?awa a ?ofar gida, ta wanke hannunta ta ce "Waye"

Ya amsa da "Ni ne" ta saka mayafi, ta fita ta le?a.

Wani jibgegen ?ato ta gani, jiki duk a mur?e, duk bai kai girman Al'amin ba ba.

A ?an tsorace ta ce "Sannu"

Ya ce "Yauwwa, matar gidan tana ciki ne?"

Ta ce "Eh meyafaru?"

"?an je ki ce mata ana sallama da Boss"

Ta yatsuna fuska ta ce "Waye hakan?"

"Mai dogon zamani nake nufi, ba shi ne maigidan ba?"

Jauhar ta ce "Ba wani mai irin sunan nan a gidan nan, ba sunansa kenan ba"

Ya ce "Kee, ni fa nake rako shi har gidan nan, ki ce mini ba sunansa kenan ba?"

Ta tsuke fuska ta ce "To shikenan idan ba ka yadda ba"ta mayar da ?ofa ta rufe.

Walid ya koma gefe ya kira Al'amin ya ?aga ya ce "Ya mai laya".

Walid ya ce "Na kiyayi mai zamani, maza na zo gidanka wata 'yar cika, ta le?o ta raina mini hankali, na kusa kwarfeta, na ?yaleta ne kar na kwafsa"

"Wacece ya aka yi?"

"Kai na zo nema, ina ta jiranka, yaran nan za su kar?i kaya su rarraba, ba ka zo ba, na biyo ka gida, wata jar yarinya nunar rana mai kama da 'yan china ta ce mini wai ba mai irin sunanka a gidan, na ce mata mai zamani wai ba gidan ba ne"

Al'amin ya ce "Ita ce matar gidan fa"

"Kai haba maza, wannan ?in?"

"Yarinyar da ta suma, na ce ka saka a kaita Asibiti"

Walid ya ce "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, maza ka sha kwana wallahi, dama ita ce, kaga rabo, wata 'yar caras beauty ka ji muryarta".

"Kai dalla malam, ka buga mata ?ofa, ka ce ta duba in da na tashi, na bar leda ta baka, ka tsaya shirme".

Walid ya ce "To meye na yi mini masifa kuma, na ga dai auren dole aka yi maka" katse wayar walid ya yi, yayi ashar ya ce "Ina da wannan, ai kan a ganni a ?ofar gida, sai an sha wuya, kai Aminu kamar ba biladam ba" yayi maganar yana bubbuga ?ofar gidan.

Kamar ba zata bu?e ba, ta sake bu?ewa cikin mamaki ta ce "Malam lafiya?"

"Ya ce ki duba in da ya tashi, ya manta leda ki bani"

"Shi wa?"

Cikin mamakin yadda take neman raina masa hankali ya ce "Maigidan"

"Dan Allah ka yi ha?uri, bai bar mini wannan sallahun ba"

Ya ce "Saboda bai bar miki sallahu ba, ba zaki bayar ba?"

Ta marairaice ta ce "Idan na baka ya dawo, ya ce mini ba shi ya aikoka ba, kaga bani da abun da zan ce masa".

Ya ce "Gaskiya ne, shikenan" ya juya ya tafi, ta mayar da ?ofar ta rufe.

Duk da kayan suna da nauyi, haka ta zage ?arfinta a kan kayan nan, ta wanke su.

Sai a lokacin ta kalli window, ta ga mpn da ta ?aukko masa ta ce "Na shiga uku, da ya ganta fa me zan ce masa?" Ta ?auka ta mayar masa ?akinsa

Al'amin kuwa duk in da ya juya, sai dai ya yi gyatsa saboda yadda ya ?oshi.

Walid ya je ya samu Al'amin, ya din ga yi masa mitar yadda jauhar fafur ta hana shi sa?on nan. Yayi ya gama, bai ce masa komai ba, sai sakace da yake yi, yana cigaba da jin ?amshin miyar da ya ci a hannunsa.

"Yanzu mai zamani shikenan yau b za a sayar da kaya ba? Saboda ka yi aure 'yar yarinya ta hana aiki yau?"

Al'amin ya kalle shi ya ce "?ila"

Yayi tsaki ya ce "Yauwwa, na ha?a maka da mp ?ina a kayanka, ka kawo mini kayata kafin ita ma ta ce taka ce ba zata bayar ba"

Al'amin ya tuna ya ganta a kan window, kuma ya ga yadda ta gyara masa ?akin, ya tabattar ?auka tayi ta kunna.

A ransa ya ce 'Ashe ba tsoron ki ke da gaske ba'

"Malam magana nake yi maka, a kawo mini mp ?ina. Yunwa ma nake ji, ko zamu je cin garau-garau ne?".

Aminu ya mi?e ?afa ya ce "Sai ka dawo"

Walid ya fice yana tunanin asarar da za su yi, na rashin sayar da kayan nan yau, ya san ko zasu dambace da Al'amin, ba zai koma gidan nan ya ?aukko kayan ba.

?arfe tara na dare ya shiga cikin unguwar, tare da su liti, da Walid, sai dai ba su shiga cikin gidan ba, suka zauna a barandar kusa da gidan, suka din ga hira suna shaye-shaye.

Jauhar kuwa kamar a cikin falonta suke shaye-shayen, saboda yadda duk gidan ya gauraye da wari.

Yau da gari yayi haske ta fito, a falo ta tarar da shi, a kwance a kan doguwar kujera.

Ta dur?usa ta ce "Yaya ina kwana" waiwayowa yayi ya kalleta ya kawar da kansa, sai dai ba ta tashi ba.

Har ta fitar da ran zai amsa ya ce "Lafiya"

Ta mi?o masa leda ta ce "Ga abun da ka manta jiya, wani ya zo ya ce ka aiko shi, ni dai ban bashi ba. Na ga kamar ganyen shayi ne, ko na ?iba na dafa mana tea?" Afujajan ya kalleta, tashi ya yi zaune ya ce "Da me zaki dafa tea ?in?" Ta nuna masa ledar tana sunkuyar da kai ta ce "Naga kamar ganyen shayi ne, sai na dafa mana ko jallof ?in taliya ce?"

"Wiwin zaki dafa a matsayin shayi, saboda mahaukaciya ce ke?"

Da sauri ta kalleshi ta saki ledar da sauri, sai dai ba ta ji da?in mahaukaciya da ya kira ta da ita ba.

"Dan Allah ka yi ha?uri, ban sani bane".

"Jiya mai laya ya zo, ya ce miki yana neman mai dogon zamani, kin ce ke baki san shi ba, to ni ne mai dogon zamani, idan kuma jami'an tsaro ne suka ce miki Viper ni suke nema, idan ki ka cigaba da yi musu rashin kunya kuma, za su sassaraki ne a banza su bawa karnuka namanki"

Shagwa?e fuska ta yi zata yi kuka ta ce "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, dan Allah ka bashi ha?uri, ba zan sake ba, dama ban san me zai yi maka bane, shiyasa na ce masa ba kai bane ba shiyasa"

Ya saka hannu ya ?auki ledarsa ya tashi zai fita ta ce "To karin kumallon fa" ko waiwayowa bai yi ba, ya fita.

Bayan fitarsa, ta je ta kwaso kayansa da ta wanke, ta ninke su tsaf, ta shiga ?akinsa, tana shirya masa kayan, ta fito masa da guda ?aya da zai saka, ta ?aukko bedsheet tana canzawa katifarsa, kawai ta yi karo da wata irin zabgegiyar wu?a.
Gabanta ya fa?i wu?ar kawai abun tsoro ce.

"Innalillahi wa Innalillahi raji'un, jikinta na rawa ta hau kuka, ta kai hannu za ta ?auka"

"Idan ta ji miki rauni, ke ki ka sani".

A razane ta ?ago jikinta na tsuma.

"Fita ki bar mini ?aki, bincike ki ke yi mini ko?"

Ta girgiza kai ta ce "A'a wallahi, bedsheet zan canza maka na ganta, ba bincike nake yi maka ba"

"Fita to"

Ta ce "To, ga kaya na fito maka da su, wanda zaka saka".

Ya sake tsuke fuska ya ce "Ki fita na ce"

Ta zo fita, ta kasa saboda yana tsaye a wurin.

Yayi tsaki ya bata hanya, ta fita har da tuntu?e, a tsakiyar falon ta ga ledar buredi, da sugar da madara da Lipton.

Ta lalla?a ta fita ta kunna gas, ta ?ora shayi.

Buga gate ?in gidan ake yi da ?arfi, ba shiri ta tafi ta bu?e.

Wani matashin magidanci ta gani, a tsaye ya kima uwar hula, ya rufe kunnuwa.

Ta gaishe shi cikin ladabi, ya ce "Ina matar gidan?" Mamaki take yi, meyasa mutane suke neman matar gidan idan suka ganta.
"Lafiya?"

"Eh, megidan muke nema? Sunana malam lawan, ni ne mai wannan gidan na kusa da ke"

Jauhar ta yi murmushi ta ce "Allah sarki, baban su halimatu? Ai suna shigo mini".

"Eh, mai unguwa yana neman mijinki, ?ararsa muka kai"

Ta ce "Subhanallah, laifin me yayi muku?"

"Au jira zamu yi sai ya yi kan mu ?auki mataki, an ce mana mutumin banza ne, kuma da ya zo bai yi mana sallama ba, bamu san da wani irin mutum zamu zauna ba, jiya an hanamu sukunk da warin wiwi, ya tara mana 'yan iska a layi. An gaya mana gawurtaccen ?an daba ne da ya addabi in da yake, aka yi masa aure mu aka kawo mana bala'i. Gara aje a zauna da mai unguwa da 'yan sanda, ko ya tashi, ko ayi yarjejeniyar zaman lafiya da shi".

Jauhar ta ce "Haba malam, bai yi muku komai ba kuma sai a kai shi wurin 'yan sanda, ina laifin mai unguwar ma, in sha Allah ba zai sake sha muku komai a layi ba, kuma ba zai cutar da kowa ba ma. In sha Allah wataran sai labari zai daina".

"Ke rufe mini baki kan na kwa?e ki, nasiha zaki yi mini, ba zamu zauna da mutumin banza da wofi ba wallahi, ya lalata mana yara haka kurum ba"

Motsi ta ji a bayanta, tana waiwayawa ta ganshi a tsaye, ashe duk ya ji abun da malam lawan ke fa?a.

Da sauri ta le?a ta ce "Ka tafi kar ka bari ya ganka"ta waiwayo ta rufe gate ?in tana kallonsa.

"Ya tafi kar ya bari na ganshi ko? To ke bari na yi miki abun da zan yi masa".


Ayshercool
08081012143
???500 ne via 0009450228
Aisha Adam jaiz bank sai shaidar biya ta 08081012143

90009343
'Yan Nijar ku turo katin airtel na 300fcfa

Kafin ta yi wani yin?uri, ya janyeta daga jikin gate ?in, sai dai kasancewar ba ?wari ne da ita ba a kansa, sai da ta kai ?asa.

Ya bu?e ?ofar ya lelle?a, bai ga kowa ba, tuni malam lawan ya ?ace.

Ya dawo ya kalleta, ta sunkuyar da kai, sai murza yatsan ?afarta take yi, da yake yi mata zafi, saboda fa?uwar da ta yi.

?wafa ya yi ya wuceta, ta lalla?a ta tashi, ta shiga kitchen ta ?ora tea, ta ?ebi miyar nan da su Anty lubabatu suka kai mata, ta ?ara gyarata ta zuba ta kai masa falo.

Ya wani maze yana basarwa, nan kuwa jira yake yi, tayi ta kawo masa ya ci.

Sai dai yadda yake cin abinci ya goge mata a jikin kujera, ko carfet yana damunta, sai dai idan ya gama ya tashi ta goge.

Dan haka ta sayo toilet paper, take ha?o masa da ita, amma ko kallonta ba ya yi, idan Allah ya taimaketa ne, wani lokacin sai ya goge a jikin kayansa kamar wani ?aramin yaro.

Da daddare kuwa kullum, sai ya cika gidan da warin sigari, wasu lokutan ba zai dawo ba, sai sha biyu na dare, ya shige ?akinsa yayi ta shaye-shaye, da safe kuma idan ta ajiye abinci zai ci, idan ba ta ajiye ba ba zai tambaya ba, kuma ba zai sayo ya kawo ba.

Idan za ta gyara masa ?aki sau goma a rana kuwa, muddin ya shiga sai ya watsar da komai ya ?ata, yayi shaye-shayensa ya bar mata toka da sauran karan sigari duk a ?akin.

Wasu lokutan sai su shafe kwana biyu ba su ha?u ba, gashi zai kwana a gidan, amma ba zai shigo ba sai ta yi bacci, duk da wataran ba ta baccin sai ta ji shigowarsa, asubar fari kuma sai ya fice, ranar da ya ga dama kuma, sai ya bari gari yayi haske, ko za ta bashi abinci, dan sai yanzu ya fuskanci abincin waje wasu lokutan ga ?aurin haya?i gashi ba sa jin sinadaran ?an?ano, nata kuwa har cikin kansa yake jin su.

Yau ma dawowa ya yi rana tsage-tsage, walid ya sayo musu abinci, yana fara ci ya ji babu da?i, ya ajiye ya ce gida zai tafi.

Walid ya ce "Da ranar nan tsaka zaka fi gida?"

"Eh" ya amsa a ta?aice.

"Lallai, na fuskanci lamari yana ta daidaita to Allah ya sa mu ji alkhairi ya kawo zuriya ?ayyiba"

Ya ha?e rai ya ce "Mai laya"

Walid ya ce "Sorry maza, na kiyayi mai zamani" ya fice ya tafi gida.

Jauhar tana ta lissafin ku?in hannunta, sun kusa ?arewa, girkin ma duk da dabaru take yin sa, ga gogan babu ruwansa sai dai ta dafa ya lashe.

Da 'yan dabaru take yin ?an wake yau, ta aiki almajiri ya sayo mata kabeji da cucumber, tana jiran dawowarsa, Al'amin ya dawo, a duk lokacin da za ta ganshi sai ta razana, gashi ba sallama yake yi ba, ya hangota da tukunya a kan gas, ya yi ajiyar zuciya ya san zai ci abinci.

Ya shiga ?akinsa, ya tarar ta sake wanke masa kaya, ta gyara ?akin tsaf.

Tsaki yayi ya ce "Ita dai wannan an yi 'yar wahala"

Ya daidaici lokacin da ta gama girki, ya dawo falo ya zauna, aikuwa sai ga ta abinci bakinta ?auke da sallama.

Bai amsa na sai Alla-alla ta kawo ta ajiye, saboda yadda ?amshin manjan, ya cika masa hanci.

Ta ajiye masa ya ha?a abun sa ya fara ci.

Ta zauna a gefensa, cikin fargaba ta ce "Yaya" shiru ya yi mata, yana ha?iye ?an wakensa da hurhu?u biyar-biyar.

Ta sake cewa "Yaya magana nake dan Allah abu zan tambayeka".

"Malama sunana Aminu, kar ki sake ce mini wani Yaya" a ranta ta ce 'Ai na san a rina'

A zahiri kuma ta ce "Ai ba zan iya fa?ar sunanka ba, ya za ayi na fa?i sunan mijina kamar mara ?a'a" sai ya ji abun wani banbarakwai wai mijinta.

"To me zan din ga ce maka?" Ba ta jira amsar sa ba, dan ta san ba zai amsa ba, ita kuma zaman kuramen nan da suke yi ba son sa take yi ba, ace kana zaune a ?ar?ashin mutum, amma ba zai kulaka ba.

"Na ji abokanka suna ce maka boss, ni kuma sai na ce maka master, idan na ce master zaka amsa, ko nima boss zan ce? Tun da ba ka son yaya?" Ta tambaye shi tana murmushi ba tare da ta kalli in da yake ba, saboda kwarjinin da yake yi mata, yanzu haka ma ?arfin hali kawai take da take yi masa magana.

Kallonta yayi, tana murmushi dimple ?in ta na side ?aya ya lotsa, ya gane dakiya kawai take yi, amma a tsorace take yi masa magana.

Duk da bai bata amsa ba, amma matsern da ta ce zata din ga kiransa da shi, ya so yayi murmushi, amma ya?i ya sha kunu, yana su?e kwanon ?an wakensa.

Cikin hikima ta ce "Da da sauran garin ?an waken nan, da na dafa maka wani, ko na ?aro maka?"

"A'a" ya ajiye kwanon, cikin sauri ta mi?a masa wani tsumma mai kyau, ta ce "Gashi ka goge hannunka, manjan yana da kamu, sai mu je waje na zuba maka omo ka wanke sosai" ya kar?a ya goge, ya koma ya kashingi?a yana duba wayarsa mai madannai.

"Na ce, dan Allah sonake na shiga ma?wabta na yi musu sallama na tare, wai haka ake yi, ka ga mu bamu cewa kowa mun tare ba"

"Sauka lafiya" ya fa?a ba tare da ya kalleta ba.

"Yauwwa na gode sosai master, bari ayi la'asar, sai na je. Yauwwa mutumin ?azu ya ce wai mai unguwa na nemank..... Ba ta ?arasa ba ya tashi, dan surutunta ya fara isar sa.

Bayansa ta bi da kallo, 'Da sannu wataran zaka tanka mini ne, ni ba zan iya rayuwar zaman kurame ba' tayi maganar a hankali.

Hu?u da rabi, bayan ta yi la'asar, ta le?a ?akinsa ta ce masa za ta fita, ta tarar yana salla.

Wata irin ajiyar zuciya ta yi, tare da hamdala a zuciyarta, ba ta ta?a tsammanin yana kai goshinsa ?asa ba.

Ta zauna a bakin ?ofar tana kallonsa, duk da shaf shaf yake yi, kuma azahar da la'asar ya ha?a a lokacin, amma ta ji dadin ganin yana salla.

"Master bari na je, idan ka idar ka sani a addu'a, Allah ya sa ka daina jin haushina, ban san me nayi maka ba" dama ta san ba amsawa zai yi ba ta fita.

Matasan 'yan mata ne su biyu a gaban rahila suna cin abinci, da alama daga makaranta suka dawo, domin kuwa bayansu jibga jibgan akwatuna ne, na 'yan makaranta.

"Umma, nifa haryanzu na kasa daina mamaki, wai yaya ne yayi aure? Wai dan Allah ya aka yi aka samu aka bashi 'ya a yadda yake? Kuma ba a bari mun dawo ba aka yi bikin?"

Rahila ta ce "Ke dallacan, waye ya ce miki abun na shiri ne shahida? Neman mafita nake ba shiri faka-faka na saka aka samo wata yarinya ya je can ya ?arata, ya ?ara sako mini yaro a gaba, irin kallon da yake yi mini, tsaf zai halakka ni, cikin ikon Allah tun da aka yi auren, ban sake ganinsa a gidan nan ba, ya samu mace yayi luf"

Shahida ta ce 'Ni wallahi mai tsautsayin da aka aurawa nake jin tausyai, yaya za ta yi da shi dan Allah dan Annabi?"

Amira ta ce "Ke ina ruwanki ne shahida, ina ruwanki da ko ma wa ce ta aure shi, ba dai an samu ya tafi na, case close".

Shahida ta yi murmushi ta ce "Ina ne gidan nasa ne?"

"Yana can gidansa na ?orayi, ba kuma cewa na yi ki je ba, kar abun da ya kai ki gidansa, balle ya lalla?a ya dawo mana nan ya je can su ?arke".

"Ahh haba umma, sai mu yanke ala?a da shi duka kenan? Yayi aure muna school kuma mun dawo ba zamu ganshi ba?"

Amira ta ce "Wallahi a garin shishshigin nan da ki ke masa, zai kassara rayuwar ki, ki yi ta shige masa yana yarfaki"

"Wallahi ki ka je gidansa ma sai na ci ubanki shahida, na gaya miki, ke baki san sai ku kasa auruwa ba saboda mugun halinsa da mummunan tabon da yake da shi ba a unguwar nan?"

Shahida ta ajiye cokalin hannunta ta ce "Umma, shi fa jini ya fi ruwa kauri, the only male brother i have, sai ki ce sai na yanke ala?a da shi?"

"Au jayayya zaki yi da ni? Shi Abban uban meye idan ba yayanki ba?"

Ta tashi ta ce "Ai ba babanmu ?aya ba, Yaya Al'amin kuma babanmu ?aya, kowane ina son sa"

Rahila ta ce "La ila ha illalahu Shahida "

Amira ta ce "Dan Allah umma bar shashasha, za ta gane kurenta ne"

Rahila ta cigaba da salallami, a kan yadda ke adawa da ita wasu lokutan a kan Al'amin.

***
Juahar gidan malam lawan ta fara shiga, wato gidansu halimatu da walida, yaran da suke zuwa tayata hira, suka gaggaisa da maman, sannan su halimatun, suka rakata sauran gidajen ma?wabta, tayi musu sallama. Har wurin masu kayan miya, da masu shaguna suka nunnuna mata da wurin makar?e.

A bayan gidan suka je har gidan wata tela, da har da yaranta, su na shigarwa jauhar, suka gaisa jauhar ta tarar da yaran suna stone work a jikin ?inki, har ta kar?a tana taya su, saboda a rayuwarta tana son sana'oin hannu suna matu?ar burgeta.

Take cewa matar, idan an samu stone work ta din ga aika mata da shi tana yi mata.

Matar ta ce 'To nawa zan din ga baki, dan kuwa ina samun aikin su sosai da sosai"

Cikin tsananin murna, da jin cewa ta samu abun yi, ta cewa matar, ko nawa ne ta bata, tana son za ta din ga yi, nan hira ta ?arke, take gaya wa matar, ta iya shirin dutse, har adon da ake yi da shi a jikin ?inki, duk zata iya, suka yi yarjejeniyar matar zata din ga bata ta yi mata.

Ganin hadari ya fara ha?owa, ya sanya ta yi mata sallama, ta koma gida, sai dai tana komawa, ya zura takalmansa zai fice, ta ce masa kar ya fita, hadari ne a garin, amma ba ta gama rufe baki ba, ta ji ya bu?e ?ofa ya fice.

Ta kawar da abun da zata kawar, ta rurrufe ko ina, ta laluba ta ?auki mp a in da ta ajiye, ta tarar ya ?auke kayarsa, ta ce "Da sau?i, tun da ba ka yi mini fa?a ba".

Ruwan sama aka yi, kamar da bakin ?warya, ga wata irin iska da ta jefa jauhar, cikin razani da tashin hankali, yadda kwanon yake ?ara ji take tamkar zai kwashe ne, saboda ?arfin iskar da ruwan.

Ta takure wuri guda, tana ta addu'a, kasancewar lokacin da ake ruwan sama, lokaci ne na kar?ar addu'a, mafi yawan addu'arta a kan Al'amin ne, da take masa fatan shiriya.

Ko da ruwan ya tsagaita, ta fito falonta, ruwa ya shigo sosai, ya ji?e ?akin, ta bu?e ?ofar falon, rashin kyakykyawan magudanan ruwa, ya sanya kwatocin layin yin ambaliya, duk suka shigo mata gida, gashi ba ga da rariyar kirki, sai ta ban?kuna, dan haka babu wurin da ruwan zai fita, tsakar gidan ya shafe da ruwan kwatami, falonta ma duk ruwan ya shigo, gashi idan aka yi ruwan, tsigar jikinta tayi ta tashi.

Haka ta samo kwano, ta din ga ?ibar ruwan tana zubarwa, ta na?e carfet ?in ta, ta jingine, sai zallar buhun da aka shimfi?a a ?asa, ta din ga kwarfe ruwa a falon nan.

Ta je ta yi sallar magariba, Allah ya sa ruwa bai shigar mata bedrooms ba.

Ana sallar isha'i sai gashi ya dawo, ya tarar da ita, fitilarta babu batirin kirki, duk tayi duhu, sai kwashe ruwa take a falo.

A ransa ya ce "Iyayenki ne suka ja miki" tayi masa sannu da zuwa, ta cigaba da aikinta, har zai wuce ya dawo ya kar?i kwanon, ya ha?e mata kujerunta wuri guda, ya kunna fitilar ?aramar wayarsa, ya ?arasa kwashe ruwan.
Shi kansa ya san gidan nan kango ne, yana bu?atar gyara sosai, bai ci ace har an saka mutum a ciki ba, amma da iyayensa da na ta, ya rasa wannene uban garajen da ya saka aka yi haka.

Ya ?a??aga labulayen, saboda ?akin ya sha iska, daga nan ya tafi makwancinsa, ta tafi nata.

Da safe ruwan duk ya tsane, amma sai ?an?ame jikinta take yi, ?arnin ruwa da ya kwanta ya din ga damunta.

Haka nan ta daure, ta gyara gidan, ta zuba miya ta yi jallof ?in macaroni, kasancewar falon a ji?e yake, da danshi, da sauran Lipton ?in jiya, ta dafa shayi har da su citta ta yi sallama a ?ofar ?akinsa, bai amsa ba dama labulen a ?age yake ta shiga.

Ta ajiye masa ta ce "Ina kwana?" Ba ta jira ya amsa ba, ta ha?a masa tea, ta tashi ta fita.

Aka jima ta dawo, ta shiga ban?akinsa ta wanke, ta ?auki bokiti ta dawo, ta ha?o ruwan zafi na wanka, ta kai masa ban?akin ta ce "Master ga ruwan wanka nan na kai maka, mai ?umi ne" idan ta ce mastern nan, sai ya ?aga kai ya kalleta.

Ta ce "Yauwwa, master zan kafa ?usa a toilet ?in ka, idan ka gama wanka, ka dinga sa?ale soson, idan ba haka ba sabulun narkewa yake yi, sai ka ga ya ?are da wuri"

Ta zagaye shi, ta fara tattare kayan duk da ya watsar a ?akin kamar ?aramin yaro.

Ya gama cin abincin sa, ya fara shan tean, yana jin yadda ?amshin da yajin citta yake ratsa shi yana yi masa da?i.

Yana zaune ta gyare ?akin, ta kukkuna masa turaren wuta, sai dai kafin ta ?arasa, ya kunna sigari a ?akin.
Sai da ranta ya sosu, akwai sauran warin ta jiya da daddare ma da ya sha, ta gama aikin ?akin, ta kunna turaren wuta, ya kuma kunna wata sigarin.

Ta maze ta ce masa "Ruwan wankanka, kar ya huce fa, na ga garin da sanyi haryanzu, idan ka yi wanka da na sanyi, zaka yi mura"

A hasale ya ce "Ke, fita ki bar mini ?aki, kin gama tsegumin ai, kin sakani a gaba kin ga abun da nake yi, to fita ki bar min ?aki, ba zan wankan ba"

Ba ta sake cewa komai ba, ta juya ta fice, ta cigaba da ayyukan ta, tana tsaka da wanke-wanke, ya fito da sauri, hannunsa ri?e da waya yana cewa "Kar ku raga musu, gani nan zuwa" ta mi?e tana kallonsa, amma ta kasa yi masa magana.

A haka yana ?aurin sigarinsa da komai, ga kayan da su ya wuni jiya, ya wayi gari da su, amma bai canza wasu ba, ya fice cikin matsanancin sauri.

Ta koma ta cigaba da aikinta, tana addu'a Allah ya

Please Login or Register in order to submit comment