Reading KARFE A WUTA Chapter 56 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

fuska ya ce "Yau ne amma baku tuna mini ba, ni na manta gaba ?aya".

"An yi booking ?in su, da wanda za su ganka, kusan wata biyu suna jira, ba su samu ganinka ba"

"Zan kira Doctor Anas,ya je yayi am sick, ba zan iya tiyata ba"

"Amma doctor... Cikin hargowa ya ce "Shut up, abun da na ce za ayi"

"To shikenan" ya ajiye wayar, ramma ta ce "Dama kai likita ne?"

"Ban sani ba, sai yanzu ki ga damar kula ni, saboda baki da imani, ki na kallo ko abinci na kasa ci".

"Kar Allah ya sa ka ci mana, kai har ka na bakin cewa wani bashi da imani Abdul yasar? Hala tsabar imanin ne ya sa kazo ka yi mini kurkuku a nan?"

"Ke fa taimakonki nayi, haka ki ka zo kalli yadda ki ka yi ?iba, ki ka yi kyau, sai ma mun ci gwamnati, zaki fi haka ?iba" yayi maganar yana ta?a damtsenta.

"Ni meye nawa idan ma kun ci gwamantin, in sha Allah ma ba zaku ci ba, ace a rasa wanda za su jagoranci al'umma, sai mutanen banza masu lalata yaran mutane " ya ce "Ok, Ai ba a wurinki muke nema ba"

"In sha Allah ba zaka ci ba, ko ?uri'a ?aya ba zaka samu ba"

Abdul ya ce "Ke ki ka sani, na je na ga yarinyar da aka ce zan aura, kyakykyawa nutsatiyya, tabbatar Allah ba ya kar?ar addu'arki"

Da sauri ramma ta kalleshi ta ce "Nutsatiyya, ai ba zaka ta?a auren macen kirki ba, sai wadda wani ya lalata kamar yadda ka yi. Ai ko ka ganta a nutse ma, in sha Allah irinka ce zaka aura. Ba zan yi fatan Allah ya baka lalatacciyar 'ya ba, dan ba ita tayi mini ba, amma in sha Allah sai ka auri lalatacciya" tayi maganar tana hawaye.

Abdul ya ce "A'a gaskiya ba lalatacciya kamar ke ba, Nutsatiyya ce sosai, idan na aureta kar ki damu, ba zamu rabu ba, ai ana mugun tare tun da kin zama 'yar hannu kema.

Ta ce "Kai da Allah, kuma in sha Allah sauran wani zaka aura"

Abdul ya ce "Nima saurana wani zai aura, balle ba zamu iya rabuwa da juna ba, mun riga mun saba, ni zan iya aure, amma ke ba zaki iya ba, kawai mu cigaba da rayuwarmu a haka rahma".

Hawaye wani na bin wani ta ce "In sha Allah, sai Allah ya ku?utar da ni daga hannunka azzalumi kawai" Abdul tamkar jin da?in tsinuwar da ramma take yi masa yake ji, ta zage shi tayi masa Allah ya isa, amma hakan ko a jikinsa, sai ma cigaba da tunzurata da yake yi ya ce "Ohhh kishi a fili, ki dai yi a hankali, kar ki yi zurfi a soyayyata, 'yan mata ne da ni burjik"

"Eh tun da ga ka bunsuru ba" ta tashi tsaye tana kuka.

Ya ?ya?yace da dariya ya ce "Bunsuru ya ajiye akuya ta mussaman a gidansa ba" kalmar akuyar tayi mata ciwo, kawai ta fita daga ?akin ta bar shi, yana ?ya?yata dariya.

***

Indabo yana ta shiri zai koma Abuja, hutunsu na majalissa ya ?are, ga shirye-shiryen da ake yi na fara za?en fidda gwani, wanda yake ta fafutuka a tabattar da yarjejeniyar da suka yi na ba wa Abdul takarar mataimakin gwamna. Sai dai sai fama yake da shi, idan yayi nan sai yayi can.

Naja'atu Bunkure ce ta kira shi a waya, ta ce masa tana office ?in sa na gidansa, tana son ganinsa.

Ya san muddin ta yi masa zuwan gaggawa ba bu sanarwa, akwai damuwa ne, dan haka ya ajiye abun da yake yi, ya fita.

Ya shiga ya zauna yana fa?in "Naja'atu masu ?asa ya ake ciki ne?"

Ta kalleshi ta ce "Ina Abdul?"

"Oho masa, yana can tasa shiririta ya tattara ya koma gidansa da zama"

"Akwai ?ura fa"

Indabo ya ce "Wace irin ?ura kuma?"

"Yaya yayi da yarinyar da ya yi wa fya?e?"

Indabo ya ce "Mun yi magana da shi, ya ce mini ya kasheta"

"Ka tabattar da hakan kuma? Akwai matsala fa. Wata shegiyar yarinya ta zo office ?ina, wai na bata bayanan in da aka tsaya da maganar yarinyar, wai zata tsayawa mai gadin nan, hankalina ya kasa kwanciya jikina yana bani, ba itaka?ai take wannan abun ba, akwai abun da ta taka, duk da na kira law firm ?in su na yi musu warning, amma jikina yana bani akwai wata a ?asa, kar ta zurafafa ta gano wani abu, dan yarinyar a tsaye take babu alamar kunya a tare da ita".

Indabo ya ce "Kin da?e kina magance matsaloli da rigingimun da Abdul yake ?aukkowa, amma ya aka yi na ga karaya a tare da ke yau?"

"Ba karaya nayi ba, ka san hausawa sun ce, rana dubu ta ?arawo, ?aya tak ta mai kaya, na so ?arasa aikin da kaina, amma ka ce na bari zai yi maganin abun, ka nemo ?anka ka tabattar da bai bar wani trace ba, gobe in Allah ya kaimu zan tafi conference ?in da shugaban ?asa ya tura mu, dan haka ba zan samu damar zuwa gidan su yarinyar ba, dan haka ka nemo shi"

Indabo ya ce "Naja'atu, idan aka samu matsala the blame will be on you, sakacinki ne"

Naja ta girgiza kai ta ce "Sakacinku dai, na yi iya yi na ni, yadda ku ka yi da shi, ka sanar da ni"

Indabo cikin hanzari, ya ?auki wayarsa yana kiran Abdul, sai dai wayar ta?i shiga gaba ?aya.

Nabila har wata ramar dole tayi, saboda zirga-zirga, gashi kwana biyu ba ta je wurin Viper ba, gashi tana cikin damuwa da tsananin son ganinsa.

Gaba ?aya yanzu ba ta doguwar shawara, kafin ta tafi gidan Viper, yau ma haka babu tsammani sai ganinta suka yi rana tsaka.

Duk suka bi ta da kallo, ta kalli Walid ta ce "Ina wuni"

"Lafiya ?alau"

"Ya mutumina, ina fatan yana lafiya?"

Walid ya ce "To da sau?i dai, yana ciki"

Liti ya ce "Wallahi ba zata shiga ba, ke ware, ni fa ban yarda da yarinyar nan ba".

Nabila ta kalli liti ta ce "Ka kiyaye ni fa, ba ruwanka da ni, ba wurinka na zo ba, wurin Viper na zo, zan duba lafiyar sa kuma mu yi magana"

Walid ya ce "Dan Allah liti ka daina haka, mana wai me ta yi maka ne, ta bayar da ha?urin abun da tayi ai"

Liti ya ce "Ni fa ba a iya yaudarata cikin sau?i, fita malama, ba zaki ganshi ba"

"Ba zan tafi ba sai na ganshi, ba ruwanka da ni".

Ya zazzaro mata ido zai yi magana, ya ji an hanka?e shi daga bakin ?ofa, Viper ya fito yana ?an?ance idanunsa.

Suna ha?a ido, ta sakar masa murmushi, mai cike da nuna farincikin ganinsa, duk kallon na sa tsoro yake bata.

Liti ya ce "Mai zamani mai hakan yake nufi? Kai ma ka yarda da wannan munafukar, ita fa ta saka aka kama maka ni, aka rufe ni so take sai an kama ka fa".

Walid ya ce "Kai ?in uwar me ka ke tsinana masa?"

Duk bai kula su ba, ya taka ya fito ya ?auki brush da toothpaste, ya matsa.

"Ina kwana" tayi maganar tana bin bayansa. Bai amsa ba, ya dur?usa yana wanke bakinsa.

Wayarta da take ta vibrating ta ciro, ta saka a kunnenta ta ce "Hello"

"Ke Sumayya ce"

"Ohh sumy, kullum cikin sauya lamba kamar 'yar yahoo?"

"Malama kwana nawa ina nemanki a waya ban same ki ba, kuma baki neme ni ba"

Nabila ta ce "Sorry na yi laifi"

Sumayya ta ce "Yaya ku ka yi da Naja'atu baki gaya mini ba"

Nabila ta ce "Ke zan zo gida na baki labari, ina wani abun ne yanzu, dan na kusa rubuta resigning na ajiye musu tsiyar su, na fuskanci Naja'atu Bunkure gaba da gaba, naga gani take ita wata jan wuya ce, ko ban kaita ?asa ba sai na razanata" gaba ?aya suka zuba wa Nabila ido, cikin hanzari Viper ya ?ago ya zubawa Nabila ido, ta katse wayar ta ce

"Meyafaru ku ke kallona ne?"

"Naja'atu Bunkure" ya maimaita yana kallon idon Nabila.

Cikin rawar baki, saboda tsorata da kallon da yake yi mata ta ce "Ka santa ne?"

"Mu je waje mu yi magana"

Ayshercool
08081012143
???500 ne via 0009450228
Aisha Adam jaiz bank sai shaidar biya ta 08081012143
Wanda za su jira document 1K ne.

90009343
'Yan Nijar ku turo katin airtel na 300fcfa

Arewabooks ayshercool7724


Jikinta ne ya hau tsuma, saboda irin kallon da yake yi mata, yayi gaba da nufin ta bi bayan shi, amma ta ?i, ya tsaya ya waiwayo yana kallonta, ta kalli Walid, ya gya?a mata kai alamar ta bi shi.

Kamar mara gaskiya haka ta bi bayansa, sai da suka ?an yi nesa da gidan ka?an, sannan ya waiwayo ya kalleta ya ce "Me ki ke nema a wurina?"

Ta kalleshi ta sunkuyar da kai. "Ki yi mini magana, me ki ke nema a wurina? Meyasa ki ke sintirin zuwa in da nake? Idan so ki ke a kama ni, ki kawo su su kama ni mana, wace irin yarinya ce ke ne?"

Yadda yake maganar cikin hargowa, sai da ta ja da baya, saboda tsoro.

"Talk! Me ki ke so, waye ya turo ki?"

"Ni ba wanda ya turo ni" ta yi maganar cike da tsoro.

"Me ki ke nema?"

A sangarce ta ce "Ni ka daina yi mini magana a haka, tsorata ni ka ke yi, ni ban san me zan ce maka ba"ta yi maganar tana kawar da kanta gefe.

Ya tsareta da idanunsa, ita kuma ta?i ?agowa, ta sunkuyar da kanta ?asa tana ha?e fuska cikin tsoro.

Ya sunkuyo dai-dai tsawon ta ya ce "Ki bani amsa" tayi shiru ta ?i magana.

Hakan ya ?ara hasala shi, ya buga ?afarsa ya ce "Ki yi magana kan na saka ki yi ta ?arfin tsiya"

Cikin rauni ta ce "Na gaya maka, ni babu wanda ya turo ni, ni na turo kaina, kuma ni tsoro ka ke bani ban san ta ina zan fara ba, tsorata ni ka ke yi"

Ba ta ?arasa maganar cikin nutsuwa ba, ta ji hannunsa a wuyanta. "Naja'atu Bunkure, meye ala?arki da ita? Ita ki ke yi wa aiki a kaina, da ita da Indabo ko?" Ba ta yi masa magana ba, sai idanuwanta da suka yo waje, ga hawaye na bin fuskarta, sai dai kallon da ta yi masa, ya sanya ?irjinsa bugawa da ?arfi, ya saketa ya ja da baya, yana dafe saitin zuciyarsa.

Dai-dai lokacin Walid ya ?araso ya ce "Viper meyasa ka ke haka ne? Ban sanka da cin zarafin mata ba, meyasa ka ke ?o?arin farawa yanzu?" Ya nuna Nabila da yatsansa, amma ya kasa magana sai haki yake yi, saboda zuciyarsa ta ?i nutsuwa. Ta ?ura masa ido, tana kuka.

Kawai ya juya ya bar wurin, Walid ya ce "Sannu, kin ga abun da nake guje miki a kansa ko? Shiyasa na ce ki daina zuwa anyhow. Mun gode da gudunmawarki ga ?an uwanmu, amma ki daina zuwan nan, ina tsoron yayi miki illa wataran".

Ta girgiza kai ta share hawayenta ta ce "Ina da kafiya wasu lokutan, haryanzu ban ji cewar zan karaya ba, da ya bi ni a sannu, da zan yi masa bayanin abun da ya ha?a ni da Naja'atu Bunkure. Kawai ji nake ya zame mini wajibi na taimake shi, ina son sanin ?arshen labarinsa, har cikin zuciyata nake son ba shi gudunmawa, na yi masa uzuri, wataran ba zai yi mini haka ba, bari na tafi. Ayyuka sun yi mini yawa ne sosai, amma ina nan zan je wurin likitan ?wa?walwar, zan kuma dawowa"

Walid ya girgiza mata kai ya ce "Rayuwarki fa, ke kanki zaki jefa kanki cikin hatsari"

Nabila ta share hawayenta ta ce "Kar ka damu da ni, shi ?in a ceto rayuwar sa da hankalinsa, a ?wato masa hakkinsa, ba a san amfanin da zai yi wa al'umma nan gaba ba, ina son kamo bakin zaren lamarin ne, bari na tafi" ta juya ta tafi.

Walid ya girgiza kai, duk haryanzu bai tabattar da manufar Nabila a kan Al'amin ba, amma a jikinsa yake jin ba zata cutar da shi ba.

Ya koma gidan su, ya tarar da Al'amin ya cika yayi fam, ya kalle shi ya ce "Mai zamani ba ka kyautawa gaskiya, shi ya?i ?an zamba ne, ko da turotan aka yi, sai ka bari mu bi komai a hankali, haka ?anwata tayi ta fama da kai, da wannan zafin zuciyar ta ka, ?arshe ta zame maka sanyin idaniyarka. Ka din ga bin komai a hankali, bamu san mai gobe za ta haifar ba, kar ka daki kwano. Ina son mu ?ara zurafafa bincike a kanta, wanda na yi bai gamsar da ni ba"

"Mai laya"

"Viper"

"Ka ?yale ni da maganar yarinyar nan"

Walid ya ce "Ba zan ?yaleka ba, sai ka fuskanci gaskiya Viper".

Nabila tana tafe, tana mamakin dalilin da ya sanya Viper yake son kasheta wasu lokutan, amma meyasa ya rikice haka da ya ji ta ambaci Naja'atu Bunkure?.

Gaba ?aya al'amuran case ?in Viper sar?a?iyarsu ta yi yawa, a labarin da Walid ya bata, ba ta ji in da Najar tayi masa wani abu ba, kodayeke haryanzu labarin bai kammala ba.

Gida ta yi niyyar tafiya, dan kanta ciwo yake yi mata, amma kwana biyu ba ta ha?u da sumayya ba, kuma gashi ba ta bata labarin karonta da Naja'atu ba, dan haka ta kira nufi gidan radiyon su Sumayya.

***
Ramma na zaune na karyawa take kallon Abdul, yadda ya sha kunu, yana video call da wani likita, yana yi masa bayani, a kan wani result na patient da ya turo masa, yanayin yadda yake bayanin ya tabattar mata da ya san abun da yake yi. Sai da ya gama sannan ya rufe tab ?in, ya kalleta ya ce "Kalli gabanki kar ki lashe ni"

Ta kwa?e baki ta ce "Ban ga abun lasa a jikinka ba, jiki duk najasa".

Cikin ko in kula ya ce "Haka dai ki ke zaune da ni" tayi guntun tsaki, ta cigaba da tauna a hankali.

Can ta sake kallonsa ta ce "Abdul yasar"

Ya ce "Your excellency"

Ta ?ata fuska ta ce "Ba na son wata your excellency".

"Ke ba abun alfaharinki bane ba, ace ke yarinyar deputy governor ce ba"

"Malam ka daina za?ewa ba zaka ta?a ci ba, ai shugaba nagari ake fata, kai idan ka zama shugaba ai ina ga sai ka halatta zina, tun da gaka bature, yahudawa ne abun koyinka"

Ya girgiza kai ya ce "A'a iskancin nawa bai kai nan ba"

Ramma ta ce "Ga wanda bai sanka ba ba, ni tambayarka zan yi, wai dan Allah da gaske kai likita ne? Mamaki nake yi" yayi mata banza yana shan tea.

"Ta?, kura da fatar akuya, ba su san har giya ka ke sha ba, ashe wataran zaka yi kisan kai, ko ma in ce kana yi. Saboda irinka wasu mazan suke raka mata asibiti, dan tsaf zaka yi wa matan mutane ?arna tun da ka saba" yadda ya dire kofin yana kallonta ne ya sanya ta sha jinin jikinta.

"Meyasa ba ki da ?a'a?"

"Saboda ?a'a muhalli ne da ita, nan kuma ba wurin da ya dace na nuna ta bane"

Ya jinjina kai ya ce "Haka ne, duk matar da na yi lalata da ita, ita ta kawo mini kanta, kar ki ?ara yi mini irin haka"

"Nima ni na kawo maka kaina kenan ko? Baka da kunya ko ka?an, sai dai idan ka gama kumburin ka fashe, har abada mutumin banza ka ke a idona, 'ya mace ba ta ta?a mantawa da wanda ya kawar mata da mutunci, ko da kuwa ta hanyar aure ne, balle ta mummunar hanya, irin wadda ka yi mini, wallahi ban da zuciyar musulunci da tuni na kashe kaina na huta, kaf danginmu babu mazinaci, amma ni kalle ni yanzu. Tsaki yayi, ya tashi ya zai fice.

"Wallahi duk in da zaka je, Allah ya isata, na nan na bibiyarka har kabarinka" Dummm ?irjinsa ya buga, ya waiwayo yana kallon ramma da ke ta uban kuka.

Bai ta?a dana sanin aikata duk wani laifi da yake yi ba, sai a kan fya?en da ya yi wa ramma. Galibin sa?on da yake yi, tsakaninsa da Ubangiji ne, ba a ta?a tsayawa gaba da gaba, ana tsine masa da yi masa Allah ya isa ba, ya sha attempting ya mayar da ita, amma sai ya ji ba zai iya rabuwa da ita ba, kuma kamar yadda take yawan fa?a, ya riga ya gama lalata mata rayuwa, ba za ta yi daraja a idon jama'a ba.

Motarsa ya shiga, ya tarar da wayoyinsa a ciki suka kwana, a buge ya dawo jiya tab ?in sa ce kawai a cikin gidan, missed calls ?in mahaifinsa babu adadi, ga na Naja'atu Bunkure, banda na mahaifiyarsa. Tunani yake yi ko lafiya ake yi masa wannan uban kiran hakan, shi ya san bai yi wani laifin ba balle ace.

Haka ya ja mota, ya nufi gidan su, yana jin yadda Allah ya isan ramma, ke ?ara yi masa amsa kuwwa.

Falon indabo ya nufa, ya na zuwa ya hau shi da fa?a, "Wane irin rashin mutunci ne zai sanya ka ?i ?aga waya tun jiya? Har na fara tunanin wani abun ne ya same ka? Kana can mashaya kana iskancin naka daka saba ko? Wallahi ka nutsu ba za ka lalata mini siyasa da shirina a banza a wofi ba, saboda shashancinka da rashin sanin ciwon kai ba, dole ka san abun da ka ke ciki ka shiga hankalinka"

Zama yayi ya ha?e rai, ya?i magana, har Indabo yayi masifarsa ya gama, sai da ya gama haki, sannan ya ce "Jiya Naja'atu ta zo mini hankali a tashe, yarinyar da ka yi wa fya?e, mutumin da aka ce shi yayi, wata lawyer za ta tsaya masa, ta je har office ?in Naja'atu neman in da aka tsaya a case ?in. Ina tsoron ranar da abokan adawa za su ?agomu, ko su banka?o miyagun laifukan da ka ke aikatawa. Yanzu ina ka kai yarinyar yaya aka yi da ita?"

"Ban sani ba, wace yarinyar nake magana a kai? Yarinyar da ka yi wa lalatar nake yi maka magana".

"Amm...m...wai ita rahama?"

"Kai ka sani, ina tambayar ka kana tambayata?"

Abdul ya ce "Ba Naja ce ta je ba, zata ba su ku?i a rufe zancen ba?"

"Zan kife ka da mari wallahi, uban najar, ba ta je ba suka ?i kar?ar ku?in, suka ce sai an kar?ar musu hakkinsu ba? Ka ce mini zaka kashe yarinyar yaya ka yi da ita? Sannna yaya ka yi da uwar yarinyar, muddin case ?in ya cigaba aka samu sani leakage mun ka?e, zan iya asarar wannan wahalar ta wa, takarar ma ba zaka samu ba".

Abdul ya dubi Indabo ya ce "Amma daddy ka ri?e mu?amai da dama a garin nan da ?asar nan, kai yakamata ace ka zama governor nan ba ma deputy governor ba da ka ke ?o?arin ?ora ni a kai ba, ni da ka bar ni da sabgar siyasar nan takura mini za ayi na kasa sukuni yadda nake so".

Indabo ya jinjina kai ya ce "Ta??ijan, bilki anya ni na haifi yaron nan kuwa? Kina jin abun da yake fa?a?"

Ta sha kunu ta ce "Wace irin magana ce wannan ka ke yi?"

"Ki na jin abun da yake gaya mini, Abdul siyasa lissafi ce, idan ya ?wace maka, babu wata fomular da zata yi maka solving duk wani hardship da zaka shiga. Na gama da jihar nan, sonake ka ri?a mini, sama nake tunani tawagarmu mu ?arasa mamaye ?asar nan, komai a lissafe nake yin sa".

Abdul ya yi ajiyar zuciya ya ce "Yarinyar ta mutu ai, babarta ce take nan"

"Ka tabattar?"

Abdul ya jinjina kai. Indabo ya ce "Dole aje a nemo babarta, ita ma a kawar da ita, kar su ?ata mana aiki"

Cikin tashin hankali ya ce "Ita ma wai kashetan za ayi?"

Indabo ya ce "To me za ayi idan ba a kasheta ba? Sai asirinmu ya tonu kuma, sannan azo a fara neman mafita?.
And na ?aga komawata Abuja, sai Allah ya kaimu weekends, kai kuma zaka tafi jibi in Allah ya kaimu, akwai meeting da shugabannin jam'iyya na ?asa da na jiha, sannan akwai meeting na musamman da deligates, dan dai a samu ayi nasara. Sai ka je ka yi shiri ka bar ni da sauran"

Gaba ?aya jikin Abdul ya yi sanyi, ya tsare mahaifinsa da ido.

"Menene kuma ka tsaya kana kallona? Kafin ?arshen watan nan kuma za a kai ku?in aurenka, gidan party chairman kai da 'yar sa".

Abdul ya murza goshinsa, saboda yadda kansa yake sara masa, gaba ?aya ya rasa abun yi.

***
A nutse sumayya take kallon Nabila ta ce "Arfa, idanunki sun nuna akwai damuwa, meyake damunki ne kamar ma fa kuka ki ka yi" kamar Sumayya ta soso mata wurin da yake yi mata ?ai?ayi, kawai ta saka mata kuka.

Sumayya ta ce "Matsalata da ke kenan, shagwa?a arfa" ta share hawayenta tana zum?ura baki.

Sumayya ta yi murmushi ta ce "?ila fa ba wani abin kirki ne ya saki kukan ba, ina jinki ko duk Najar ce, yaya ku ka yi da ita?"

Nabila ta ce "Wannan ai azzalumar mace ce" nan ta gaya wa Sumayya yadda suka yi.

Sumayya ta jinjina kai ta ce "To hakan ne ya saki kuka?" Nabila ta girgiza kai ta ce "Ke na gaji ne, kaina ya ?auki caji, kin ga rashin mutuncin da barrister Kabir ma yayi mini duk saboda ita, ni kamar na karaya ma, amma wallahi ba zan janye ba"

Sumayya ta yi dariya ta ce "Manya gatan wasa, karaya ba taki ba ce ba, akwai ?alubale sosai a duk wata nasara da ake son cimma, dan haka ki yi ha?uri ki cigaba da addu'a, In sha Allah sai kin cika burinki a kan Naja'atu".

"Wallahi sumy da kamar na karaya, amma ba zan karayan ba in sha Allah, sai na cika burina"

"Yauwwa mutuniyar Viper" da sauri Nabila ta kalleta ta ce "Me ki ka ce?"

"Mutuniyar Viper mana, ko shi yanzu kin ?aga masa ?afa, kin ha?ura da nemansa kin koma kan fansarki ta naja'atu bunkure?"

Nabila ta ?urawa fuskar Sumayya ido ta ce "Al'amin mai dogon zamani" tayi maganar tana murmushi.

Sumayya ta ce "Ban gane ba"

"Kawai sha?ar da yayi mini nake tunawa ne, na kusa she?awa".

"Amma haryanzu ba ki sanarwa DSP ba, yakamata ki tamakawa aikinsa fa"

Nabila ta ce "Ta? haka kurum ya gaya wa Abba, ya saka Abba ya harbe ni da bindiga har lahira, na je wurin ?an daba, ba dani ba bari na tafi gida, marata ma ciwo take"

Nabila ta tashi, sumayya ma ta tashi za ta rakata, a reception suka ha?u da P.A, gaban sumayya ya fa?i, ya din ga bin su da kallo, ita da Nabila.

"Malam ka kalli gabanka mana, ji jaraba zai saka na fa?i" Nabila ta yi maganar cikin ?aga murya tana kallon P.A

Sumayya ta ce "Na shiga uku, haba Arfa, babba ki ke yi wa haka?"

"To waye ya ce ya kalle ni?"

P.A ya ce "Yi ha?uri, wallahi kallon sani nake yi miki ne, kina yi mini kama da wata da na sani"

Nabila ta kwa?e baki, yayin da jikin sumayya ya hau rawa.

Ya ce "Sumayya wurinki na zo fa" gaba ?aya sumayya ta rikice, dan kar P.A yayi wani abun da zai sanya Nabila gane wani abun, dan sharp brain ce da ita sosai.

Nabila ta ce "Bar rakiyar kawai, ni na tafi sai mun yi waya, kuma ki daina ccacanza lambobi kina kirana, kamar wata mara gaskiya ko 'yar 419, idan na kira layinki ba zaki ?aga ba, sai ki yi ta canza lamba" gaban sumayya ya fa?i, mussaman kallon da P.A yayi mata.

Cikin ya?e Sumayya ta ce "Layina ne yake bani matslaa, sai mun yi waya".

P.A ya tasa ta a gaba, zuwa news room, in da take aiki, ya rufe ?ofa ya kalleta ya ce "Wato canza lamba ki ke yi ki yi waya da ita ko?".

Sumayya ta ce "Ban san me zaku iya yi mata ba, dole sai na tantance abun zan din ga gaya muku a kanta".

"Haka muka yi da ke? Kin za?i ki salwantar da rayuwarta kenan?"

"Ba zan salwantar da rayuwarta ba, kuma babu abun da zai same ta sai wanda Allah ya ?addara mata, ku bani a hankali ai ina sanar muku da duk wani abu da take aikatawa kamar yadda ku ka bu?ata. Menene na biyo ni nan kuma, ka yi mini magana a gabanta sai ta gane".

P.A ya ce "Ta gane me? Muddin ki ka bari ta gane, sai ta zama gawa, an sanar mini ta zo ne, kuma na san muddin ta zo, wani muhimmin abun ne ya kawo ta. Me yake faruwa? Dan kar ki yi zaton ke ka?ai ki ke yi

Please Login or Register in order to submit comment