Reading KARFE A WUTA Chapter 42 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

har na kai wa mai solar ku?in, ya zo ya saka miki solar, ya kawo miki fankar solar zafi ya fara yawa kuma ba wuta".

"Solar kuma master? Da mun sai kayan abinci, zafi lokaci ne zai wuce, solar fa da tsada".

"An ce masu asma, ba sa son zafi" ya yi maganar yana tashi tsaye, tashi ta yi ita ma, sai ta rasa me za ta ce masa, ya nufi ?akinsa, ta rasa ta ina yakamata ta fara ma. Akwai abubuwa masu muhimmanci da yakamata ace yana yi da ku?i, da solar da ya saya, kamata yayi ace ya sai musu kayan abinci, ya ?inka sutura da ko ?an takalmi ne mai kyau na kwalliya. Duk in da ya kwashi taklminsa soso haka yake ?arawa gaba da su, kayansa ma ita ta ware masu kyan ta kai ?akinta, sai idan za shi wani wuri na musamman ko juma'a ta bashi ya saka. Sai dai ta san bai kyautu, ta nuna ba ta ji da?in abun da yayi ba, domin ko ba komai, yayi ne dan ya kyautata mata.

Ya nemi wuri ya kwanta, ta zauna a kan katifar, ta ?ora hannunta a kansa, tare da karanto masa addu'oin kwanciya bacci.

Abun da jauhar ba ta sani ba, bayan ciyar da shi da ta din ga yi farkon auren su, Addu'ar da ya ji tana yi masa cikin magagin ciwo, tayi matukar tasiri a zuciyarsa, Addu'a ce da idan ba uwa ba, ba kowa zai yi maka ba. Addu'oin da take yi masa idan yayi mata wani abu na kyautatawa ma, ba ?aramin da?i yake ji ba. Ga uwa uba kirarin da take yi masa wasu lokutan, da suke fasa masa kai. Duk wani abu da zai yi baya manta tarin alkhairin ta.

"Allah ya saka maka da alkhairi, ya bu?a arzikin ka, ya wadata mu da halal ya nesanta mu da haramun. Na gode sosai da sosai Allah ya biya ka da gidan aljanna, ya ji?an iyayenmu"

Idonsa a lumshe ya ce "Amin 'yar aljanna, addu'ar ta yi da?i" tayi murmushi ta tashi.

Washegari da wuri ta shirya, tana ta murna za ta je gidan hafsa, ta wanke laifinta na rashin zuwa biki.

Shi kuma ya ce zai kaita, amma ya din ga yan?wanata.

Ba su fita ba sai sha ?aya saura, tiryan-tiryan, har gidan hafsa.

Gida ne babba na gaske, Al'amin ya ce "Ba da?ewa zaki yi ba, da wuri zan dawo mu tafi"

"To Allah ya dawo da kai lafiya, take care".

Ya ce "To, ki shiga, sai na tafi"

"Saboda kar in gudu?"

"Idan kin gudu ma zaki dawo" yayi maganar yana tayar da babur ?in sa.

Juahar ta shiga har falon Hafsat, ta din ga bata ha?uri na rashin zuwanta bikin nan ta ce "Kin san halik maza wasu lokutan sai a hankali, babu yadda ban yi ba, amma ya hana, ba shi da lafiya lokacin" Hafsa sai ?an fizgar kai take yi, wai ita dole ga matar mai ku?i.

Har la'asar tana gidan hafsa, bayan ta gama shan ?amshin, ta saki jiki kuma suka hau hira, da yake ita ce sakuwar jauhar, daga ita sai jauhar.

Ta din ga ko?a mata irin son da Alhaji mu'zzam yake yi mata, dan ta tura mata haushi. Jauhar kuwa ko a jikinta, ta ce "Wallahi yaya hafsa idan Allah ya baka miji mai sonka tsakani da Allah, duk wani ?alubale mai sau?i ne"

Ta ce "Aikuwa shiyasa nake tausyinki, aure ba soyayya, ga miji sai a hankali"

Jauhar ta ce "Aikuwa ke da ki ka yi na soyayyar ma, ba ki fi ni samun kulawa ba, da farko a tsorace nake da shi, tun da muka saba Alhamdilillah"

"Ta?, haryanzu yana safarar cocaine ?in?"

Duk da jauhar ta ji haushin maganar ta ce "Da safarar cocaine yake, ai mun girmi zaman Kano sai Abuja"

Al'amin ya kira jauhar, ya ce ya zo ta fito su tafi.

Ta le?a ta window falo ta hango shi, a cikin harabar gidan.

Ta ce "?ago kanka sama ka ga" ya ?aga kai, ya hangota.

"To ka tafi, ba yau zan dawo gida ba, sai gobe"

"Wallahi idan ba ki fito ba, zan shigo har ciki"

"Kaikaikai, gidan mutanen za ka shigo?"

"Sai na shigo ?in tukuna kenan?"

Tayi dariya ta ce "A'a, rufa mini asiri, kar ka saka da ni da kai a zanemu, gani nan"

Hafsa ta yi ?uri da ido, tana kallon jauhar, tana le?en Al'amin kuma suna waya, tana ta dariya.

"Yaya hafsa, bari na tafi"

Hafsa ta tashi ta ce "Mu je na raka ki".

Suka fito harabar gidan tare, yanayin Al'amin a yanzu, akwai nutsuwa a tare da shi, ba kamar lokacin da ya je gidan su ya ?auki jauhar ba.

Hafsa ta ce masa "Ina wuni?"

"Lafiya ?alau" ya amsa idonsa a kan jauhar.

"Ya ka ke hararata ne, ba gani na fito ba"

Ya ce "Zaki yi bayani" motar Alhaji mu'azzam ce ta shigo gidan, yana hangen jauhar, ya ci wani irin wawan burki ya bu?e motar ya fito.

Ya ?araso ya kalli Jauhar ya ce "Jauhar, dama kina nan?"

Tayi murmushi ta ce masa "Eh, ina wuni?"

"Lafiya ?alau jauhar, sai dawowa na yi aka ce mini kin yi aure, na ce ko wani laifin na yi miki? Hafsa ta ce mini dama akwai wanda ki ke so, shi ki ka aura, ni kuma baki gaya mini ba lokacin da nake neman aurenki"

Kallo ?aya jauhar ta yi wa Al'amin, ta ga ya murtuke fuska, idonsa ya fara ka?awa zuwa ja.

Ta ce "Eh, gashi nan a gabanka mijin nawa, Allah dama ya ?addara yayata zaka aura. Yaya hafsa sai anjima".

Ya ce "Tsaya na baki na mota" ya saka hannu a aljihunsa ya ?ebo ku?in da bai san yawan su ba, ya mi?a mata ta girgiza kai ta ce "A'a na gode"

Hafsa ta ce "Baby kawo ka ga" ta kar?i ku?in ta turawa jauhar a jakarta, ta ce ba a mayar da kyautar manya, ku gaida gida. Tuni Al'amin ya juya ya fice, idan ya cigaba da tsayuwa, zai iya yi wa Alhaji mu'azzam illa, da wu?ar da take cikin rigarsa a soke.

Tun da suka tafi hanya, bai ce mata uffan ba, hakan ya sanya ta cikin matsanancin tashin hankali.

Da ya ajiyeta a gidan ma, tafiyar sa yayi, bai ko shiga gidan ba.

Ta din ga addu'a Allah ya sanyaya masa zuciyarsa. Duk yadda ya so ya sarrafa kansa ya kasa, sai da yayi shaye-shaye, domin rage ra?a?in abun da yake ji, dan zuciyarsa har wani tururi take yi.

Har sha biyun dare, idonta biyu tana zaune, tana jiran dawowarsa, ya koma mata Al'amin ?in sa, dan ko sallama bai yi ba ya shigo, ya wuceta ya tafi ?akinsa.

Cikin fargaba, tana addu'a, ta bi bayansa, warin wiwi duk ya cik wurin.

"Sannu da zuwa, nan zan kawo maka abincin?"

"Fita ki bani wuri, kafin na kakkaryaki na zubar. Idan ba kya son zama da ni, ba sai kin wula?anta ni, ta hanyar kai ni wurin tsohon saurayinki ba, shiyasa nake ta baki za?i tuntuni a kan zama da ni, ba dan na sarrafa zuciyata ba, sai na kashe mutumin nan har lahira yau, fita ki bani wuri, bana ?aunar ganinki ma".

Ta marairaice ta ce "Dan girman Allah ka yi ha?uri, wallahi da na san zamu ganshi da ba mu je ba, ni saboda 'yar uwata na je".

"Saboda 'yar uwakki, ko kuma saboda ki ganshi?"

"Ya za ayi na je ganin wani, alhalin ina ?auke da igiyar aurenka a kaina"

"Ki daina wani kwantar da murya, na riga na gane abun da ki ke nufi, da in da ki ka dosa, if you still loves him zan iya sakin ki, ki iya koma wurinsa, tun kafin na illata ki, ba zan juri wannan cin fuskar ba, nan gaba ban san me zaki aikata ba"

Cikin tsananin ?acin rai ta ce "Idan ka sake ni, hakan baya nufin rayuwata ta zo ?arshe, jaririn da ya zo duniya ma Allah ya na iya kar?ar rayuwar mahaifiyar sa, kuma ya raya mata shi. Ka yi mini duk hukuncin da ka ga shi ya dace ni" ta fice daga ?akin, cikin tsananin ?acin rai da damuwa.

Ransa yayi matu?ar ?aci, jin yadda ta gaya masa maganganu, gashi dama a cake yake, ya nemi wata ?waya ya ha?iya ya kwanta, dan kar ayi ?atacciya. Da asuba ya farka, ya saba ta zo tayi ta fama ta tashe shi, amma yau ta?i zuwa.

Yayi sallar asuba, gari yayi haske ya fito, amma ba ta fito ba, ya gaji da zama ya fita.
Da azahar ma, abincinsa ta ajiye masa ta yi zamanta a ?aki, idan yana falo tana ?akinta, idan yana ?aki sannan zata fito.

Ya shareta shi ma, yana jiran ta zo ta bashi ha?uri kamar yadda ta saba, amma ta?i, sai ya ji gidan yayi masa duhu babu da?i. Kusan kwanaki uku, ba wanda yake shiga harkar wani.

Yau har ya cire kaya ya kwanta, ya tashi ya zauna yayi shiru yana tariyo maganganun da ya gaggaya mata, sai ya ji sun ?an yi nauyi da yawa.

Ya tashi ya tafi ?akinta, kasancewar babu wuta, ya kunna fitilar wayarsa, ya shiga.

Tana ban?aki tana wanka, ta jingina fitilarta a kan mudubi, tana haska mata cikin toilet ?in.

Ya ?arasa gaban mudubin, ya ?auki wayar ya kashe fitilar.

"Waye a nan?" Tayi maganar cikin tsoro, dan ba ta san ma ya dawo ba.

"Waye?" Yayi shiru bai yi magana ba.

Da sauri ta gama kwara ruwan a jikinta, ta fito sai dai ?akin yayi duhu, ba ta ganin komai.

"Wai waye ne?" Tayi maganar tana laluba hanya.

Direction ?in da yake ta nufo, cikin tsoro, kawai ta ji ya zaunar da ita a kan cinyarsa. Cikin tsananin tsoro ta ware baki za ta yi ihu ya tsohe mata baki ya ce "Shhhhh, Al'min ne"

Ayshercool
08081012143
?? LITTAFIN KU?I NE ?500 VIA 0009450228
AISHA ADAM JAIZ BANK
SAI SHAIDAR BIYA TA 08081012143
YOUR RECEIPT VALIDATE YOUR PAYMENT.








Cikin cunkusa baki ta ce "To kuma shi ne zaka tsorata ni? Ko gama wankan ban yi ba na fito"

Ya ce "To mu je na ?arasa miki"

Tsuke bakinta ta yi ta kasa magana, jin abun da yake yi, da ba ta yi zato ba.

Kasancewar bayanta, yana jikin ?irjinsa, yana jin bugun zuciyarta yana fita da sauri-sauri.

"Meyasa ki ke shareni? Kwana uku kin yi mini laifi, kuma kina gaba da ni ko?"

Ba ta yi mamakin ?arfin hali, da ?warewa a iya rainin hankali, irin na Al'amin ba, wato ma zaman jiran ta bashi ha?uri yake yi.

"Kin san zaki yi gaba da ni, meyasa ki ka bari muka saba? Ba ni da saurin sabo, ki ka yaudare ni ki ka sa na fara sabawa da ke, shi ne zaki wani din ga mazewa. A din ga manta abu a kwana ?aya ya wuce kawai a cigaba da life. Ni kaina ban san dalilin da ya sanya nake matu?ar jin ba?in ciki idan na ga wani abu ya ra?e ki ba"

Da ?arfi ta ce "Master" tayi maganar tana ?o?arin mi?ewa.

Hankali kwance ya ce "Yes" ba tare da daina abun da yake yi ba.

Cikin rauni ta ce "Wai meye haka?"

"Aure" ya bata amsa kai tsaye.

Shiru yayi, jin yadda zuciyarta ke cigaba da bugawa da sauri, tana nema ta fara haki, saboda tsoro.

A hankali ya ce "Common, relax mana"

"Babyn roba" tayi masa shiru, "Kodayeke yanzu babyn ?arfe ce, ki amsa mana" still ta yi masa shiru, yana jin yadda ta saka ?arfinta ta ri?e hannunsa.

Fito yake yi mata a kunne, hakan ya sanya ba shiri, ta saki hannunsa, ta toshe kunnenta.

"Ki amsa mana, tambaya zan yi miki mai muhimmanci. Kin san bana mantuwa, kamar na'aura mai ?wa?walwa nake, in dai ka ajiye zaka zo ka ?auka. Idan ban manta ba kin ce kina so mu rayu tare. Ina ta tsoron ta?a abun da nake ganin ban dace da shi ba. Ba na son cutar da rayuwarki, in yi silar gur?acewarta kamar yadda tawa ta gur?ata, duk da kin da?e ki na nuna mini ina rintse ido, Al'amin ba ya abu bisa zalunci"

"Na nuna maka me?"

"In fa?a kenan, ko shekaranjiya meya kawo zancen zuriya? Ke 'yar yarinya kallonki kawai nake yi, amma kar ki damu da hakan ai lafiya ce" wato da wani ne yake ba wa jauhar labarin maganganun nan daga bakin Al'amin suke fitowa, sai ta ?aryata, amma ?iri-?iri, ya shige duhu yana sakin maganganu yadda yake so, alhalin ya ce ba ya jin komai.

Tana cikin tunanin ta ji ya ce "Kin amince mu rayu tare, a matsayin abu guda? Ba na son cutar da ke, ke ma kin shiga ?alubale da dama, bana son ki sake shiga matsalar rayuwa, rayuwarki ta tafi a haka kawai. Idan kin amince, zan yi iya ?o?arina wurin zama da ke da zuciya ?aya, amma sai kin yi wa yanayin rayuwata uzuri, duk da a yanzu ma kin taka muhimmiyar rawa a rayuwata. Be mine"

Haka kurum ta fara kuka, kukan da ba ta san na menene ba ma.

"Talk babyn roba".

"To ka ?yale ni, gobe da asuba sai na gaya maka"

Cikin bu??iyar muryarsa, da take fitowa daga ?irjinsa, ya ce "Na ?i wayon, yanzu zamu gama maganar"

"Master"

"Mmmm"

"To zaka daina saka ni kuka?"

Ya ce "In sha Allah"

Ta ce "Zaka daina shaye-shaye?"

"In sha Allah, ina iya ?o?arina, ba abu ne da zan daina lokaci ?aya ba. Mu bar wannan maganar, baki bani amsa ta ba, zaki cigaba da zama da ni, a yadda nake, ina talaka marayan da ya rasa kulawa, sai bayan shigowar ki rayuwata?"

Tana kuka ta ce "Dama ai kai ka ke cewa zaka sake ni, ka ke sakani kuka, ina son in zauna da kai"

Yayi ajiyar zuciya ya ce "Duk wani abu da ki ka yi mini na alkhairi, yana rubuce a ?irjina, ba zai ta?a gogewa ba, ban ta?a mantawa da ko guda ?aya ba, babu wata mace da ta ta?a playing role ?in uwa a rayuwata sai babyn roba, bashi ne a kaina kulawar da ki ka yi mini".

"Ni saboda Allah nake kula da kai"

"Ni na isa in biya ki ne dama?"

Jauhar ido yayi tsilli-tsilli, bayan da Al'amin ya ?aryata tunaninta na ko ba shi da lafiya ne.
Ya tabattar su a matsayin miji da mata. babu tsammani aka kawo wuta, haske ya gauraye ?akin, Jauhar ta takure jikinta, sai rawa jikinta yake yi, yayi murmushi ya ja bargo ya rufeta.

Ya zuba wa gashin kanta ido, ba ba?i ne wuluk ba, amma mai laushi irin na fulani, ya hargitse, ta cusa kanta cikin bargo sai gashin a waje.

Ya da?e yana kallonta, kafin ya kai hannunsa yana shafa gashin ya ce "Amm ya ma sunan angela ko?" Tayi masa shiru, ta sake dun?ulewa wuri ?aya.

Ya cire bargon daga fuskarta, amma ta rintse idanunta.

"Kalleni mana, abu zan gaya miki fa"

Ta cunkusa baki, tana ta jan majina a hancinta, fuskarta duk ta yi ja saboda kuka.

Wani nisha?i yake ji, ya cigaba da kallonta yana ta murmushi, kamar wanda aka yi wa Albishir da kujerar makka.

Wayarsa da ta fa?a ?asan gado ce, ta fara vibrating, ya juya ya zura hannunsa ya ?aukota, ya sake matsawa kusa da jauhar, ya ?aga wayar.

"Maza" muryar liti tayi amsa kuwwa a wayar.

"Mmm"

"Kana ina ne?"

A ta?aice ya ce "Gida" yayi maganar yana cigaba da shafa gashin jauhar.

"Wai me ka ke yi ne? Ko baka da lafiya ne?"

Al'amin ya ce "Meyafaru?"

"To ai ji nayi kana amsawa kamar ana yi maka dole"

"Ina jinka ya aka yi?"

Liti ya ce "Akwai matsala ne fa"

"Ta me?"

"Yaran madaki, duk sun cire pastocin indabo, ka san ?azu Walid da su guduma suka gama sasskawa, mu na dawowa muka tarar duk sun cire, ya tambaya aka ce masa yaran madaki ne, gashi can ya tafi, nayi-nayi ya ?yale su, ya ?au wu?a ya tafi, shika?ai kar su yi masa wani abun, ka san Walid da ba?in taurin kai, kamar jinjirin jaka, dan yafi jaki taurin kai"

Al'amin ya ja guntun tsaki ya ce "Gani nan, bari na tafi cikin garin, maza ka kira yaran nan, ka yi magana da su guduma ma, zan kira yaran unguwar mu, maza su bishi kar su yi masa wani abun, gani nan" ya yin?ura zai tashi, jauhar ta ja jikinta ta ri?e shi ta ce "Rigima zaka je ka yi ko?"

Ya girgiza mata kai ya ce "Ba rigima zan yi ba, amma idan har ba a kai masa ?auki ba, za su iya kashe shi"

Cikin takaici ta ce "Kana ganin halin da ka sakani, a haka zaka tafi ka bar ni, a wannan yanayin da nake ciki?"

Ya ?agota ya ce "Ki yi ha?uri, bana son a sake asarar rai saboda ni, wallahi suka ga Walid shika?ai, za su iya kashe shi, am sorry yanzu zan dawo, ki kwanta kar ki tashi kina bu?atar hutu" ya ?arasa maganar yana kwantar da ita ya bar ?akin.

Ta lumshe idonta, hawaye suka cigaba da zuba, sai da ta yi ta gaji, sannan ta saukko daga kan gadon da kyar, ta ha?a ruwa mai ?umi sosai ta tsarkake jikinta, ta nemi wuri ta kwanta.

Da asuba da ?yar ta tashi, ko alwala ba ta yi ba, ta tafi ?akinsa ta duba, ko ya dawo cikin ?oshin lafiya.

?arar buta ta jiyo a ban?akinsa, alamar yana alwala, wani ?an sanyi ta ji a ranta, yau da kansa ya tashi sallar asuba, ko yaushe ya dawo ma oho.

Ta koma ta yi salla, ta sake fitowa ta le?a, ta ga yana salla, ga kayan shaye-shaye a kan katifarsa, ganin yana salla, ta shiga kanta tsaye, ta tattare kayan ta fice.

Bacci ya ?ara kwasheta, tana cikin baccin ta ji ta a takure, ta yi mi?a ta bu?e idonta, ta saka a nasa.

"Kalli agogo ?arfe sha ?aya, yunwa duk ta yi mini illa, na sayo ?osai na kasa ci, ya ja mai, kuma farin maggi ya yi yawa a ciki sosai.

'ikon Allah, shi ko ?an rarrashin nan ma ba zai yi bs, zancensa kawai abinci.

A ?ule ta ce "In da ka tafi ba su baka abincin ba?

"Me ki ka ce?"

Ba tare da ta kalleshi ba ta ce "Na ce in da ka tafi ba su baka abincin ba?".

Ya ce "Ba su bani ba, ke zaki tashi ki bani yanzu"

Kawai ta juya masa baya, dan daren jiya ta ?ulu yadda ya tafi ya bar ta.

Ba ?aga ?afa, ba komai, ya ?ara huce ba?ar maganar da ta gaya masa, ya gama ya tada kai da jikinta, ya lumshe ido ya hau bacci.

Ta gama koke-kokenta, duk iya ?o?arin da tayi, ta ture shi ta tashi, ta kasa sai ma ji da tayi tana haki, Al'amin ya gama raina mata hankali ta ko ina.

A haka har baccin dole ya sake yin gaba da ita.

?arshe har azahar ko wanke-wanke ba ta yi ba.

Ta yi wanka, ta canza kaya, ta fito ya basar da ita, kamar babu abun da ya faru, ta tarar da shi da wayarta a hannunsa, yana game, ta share shi ta wuce, sai da ta fita ya bi bayanta da kallo yana murmushi.

Ta tarar yayi wanke-wanke, ya share tsakar gidan tsaf, har marka?en kayan miya ya kai.

Ta dawo ta koma ?akinta, ta ?aukko bedsheet, zata fita ya ce "Me zaki yi ne?"

"Wanki"

"Me ya same shi, zaki wanke? Ko karyawa ba ki yi ba? Ki saka shi a baho, zan wanke, ki samu ki karya"

Sai cika take tana batsewa, mazewa kawai yake yi, don dariya yake son yi, amma ya maze shi ma ya sha kunu.

Tun da ya kai marka?en nan, ya dawo bai sake fita ba, wuni guda yana gida, duk da babu wanda yake kula wani, amma zaman kula da ita yake yi.

Har isha'i, kowa ya koma ?akinsa, har ta kwanta, ta ji ya shigo ?akin, kan tayi magana ya ?araso kan gadon ya hau.

"Malam ya ne? Menene kuma?"

"Kamar yaya?" Yayi maganar yana janyo bargonta, ya rufe ?afarsa.

Kamar tayi ihu ta ce "Menene kuma?"

Ya ce "Da na kawo miki kajin mutum goma sha biyu, ki ka cinye ki ka yi kyautar wasu, kin tambayi ta mecece?"

Cikin rashin fahimta ta ce "Ban gane ba, ka ce a gidan oganka ka kar?o".

"To gaba sai ki dinga tambaya, kwa?ayayyiya, ki ka din ga ci kina rabarwa, ni sai dai ki sammini, yanzu kuma tambayata lafiya? Ba lafiya ba"

Cikin rauni ta ce "Master" ya ce "Yes"

"Dan Allah ka koma ?akinka" ya kwanta ya ?ora ?afarsa ?aya kan ?aya ya ce "Zuriya fa ki ke so, ki ke wani basarwa" Jauhar ta yi danasanin fa?ar maganar nan.

Kawai ta zauna a zaune tana kallonsa, sai ka?a ?afa yake yi.

"Zo ki kwanta, na ga lokacin da baki da lafiya, har wani ?ara lafewa ki ke yi, bisimillah" yayi maganar yana nuna mata ?irjinsa.

Pillow ta gyara ta kwanta a kai, ta ?i kula shi, mutumin da suka wuni ba sa magana, saboda tsabar son tayar da tarzoma, ya lalla?o yana tayar da wani tsohon zance.

Da asuba ta riga shi tashi, ta shiga ta yi wanka, tayi alwala ta zo tana tashinsa, ?arshe sai kusan shida da rabi suka yi sallar, bayan ya saka ta canza wani wankan da alwala. A wurin da tayi salla, ta kwanta a kan sallaya ta cigaba da bacci.

Iya ?o?arin sa yake yi kar ya sha komai, ya kasa jurewa, kamar zai fita hayyacinsa, ya lalla?a ya dawo ?akinta, ya tarar tana kwance a ?asa tana bacci, boti ma yayi lakur a kan sallayar yana bacci.

Tanka?e boti yayi can gaba, ya kwanta a kusa da ita, ya ?ura wa fuskarta ido, ya kai bakinsa ya sumbaci goshinta.

A ranar aka saka wa jauhar fankar solar, da ?wai, ta din ga murna tana yi masa godiya.

Sai dai Al'amin ya uzzura mata, duk dare, sai ya ce mata wai shan fanka ya zo, zafi yake ji, sai da ta gaji ta ce "Dan Allah master ka ?auke fankar nan taka ka mayar ?akinka , ko na huta"

Ya ce "A'a ai dama ke na sayawa, dan haka gara na din ga zuwa nan kawai ina shan isakar, idan na mayar da fankar can, bayan iska kuma takura mini za ta yi din ga yi".

Ta ce "A ta?aice dai, ni ce fankar kenan?"

Ya ce "Eh mana, ke ga taki fankar, ni kuma ga tawa" yayi maganar yana nuna ta.

***
Kwanaki suka cigaba da tafiya, sai dai tsakanin Alhaji mu'azzam da Hafsa sai dai kallo, ranar da uwargidansa ta bari ya zo ?akin hafsa, kawai ta ga ya nemi wuri ya kwanta.
Duk da irin kunya da kawaici irin ta 'ya mace, sai da ta cire kunya ta ce "Wai ni Alhaji, menene matsayina a wurinka ne? Na kasa gane kan wannan al'amarin"

Ya kalli hafsa ya ce "Jauhar, yakam...

A fusace ta ce "Wace irin jauhar kuma? Wula?ancin naka da rashin mutunci har ya fi da, ga mari ga tsinka jaka? Tun ranar da jauhar suka zo, ka rasa sukuni, ka ke kirana da sunanta ba na so"

Ya ce "Am sorry mistake ne, ki ?ara ha?uri ki bani lokaci, na yi wa Safiyya Al?awarin babu abun da zai shiga tsakanina da ke, har sai lokacin da ta samu nutsuwa hankalinta ya kwanta, tana cikin damuwa sosai da sosai, kin san tana da kishi ne sosai da sosai ".

Kamar ta ?ura masa ashar ta ce "Au har gaya mata ka ke ba abun da ya shiga tsakanina da kai, har sai ta yadda? Ita take aurena kenan? Bakomai na gode, ta ci lokacinta when it comes to my turn, zata gane shayi ruwa ne" ya girgiza kai ya ce "Kin ga ba na son rigima, ba zaki zo ki sameni, ina zaune lafiya da iyalina ki ?aga mini hankali ba Please, ina respecting farincikin matata sosai da sosai "

Hafsa ta ja tsaki, ta fice ta bar masa ?akin.


Al'amin na zaune a falon Indabo, ana ta tattauna yadda al'amura za su tafi kafin lokacin za?e, dan wata ?aya kawai ya rage babban za?e, wanda yake dai-dai da lokacin sallar layya.

Ya rage daga Al'amin sai P.A da Indabo yana ta sake jaddadawa Al'amin, idan aka ci kujerar nan za su ji da?i, dan tun yanzu an ce masa idan ya samu senator ?in nan, akwai vacancyn mutum uku za a bashi a NNPC.

Al'amin ya ce "A cikin yarana, ko Nura guduma ne, ina son a samo masa aiki ko direban manyan motoci ne, yana can na saka ana koya masa jan manyan motoci"

Indabo ya ce "Ba ka da matsala, kawai ku yi aikinku, duk akwatin da ku ka ga zata bayar da matsala, ku tayar da tarzoma. Maganar da nake yi maka, a yarjejeniyar da muka yi da uwar jami'iyya ta ?asa, kan na dawo cikinta, nan da wasu shekaru, za a tsayar da Abdul takarar mataimakin

Please Login or Register in order to submit comment